KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

@ut@r h@jiy@

[30/12/2016 11:32 pm] Re@l @ut@r h@jiy@????????: KALLON KITSE

®NWA

©Zainab Y Hussein

Dedicated to Zahra Bukar & Deedoh Yar ficika

THE END

   Rayuwa Ita dama haka take, tana juyawa yadda taso, gashi Allah yayi auren Deedoh da Malamin ta, Allah yabasu zaman lafiya mai d’orewa
    Da safiya wajan 11 naje gidan, tundaga gate nakejin hayaniya, ba kowa bane face su ZAHRA da Anee sai Auta sunbaje kan dadduma sunashan tea ga tsiran jiya dasu kayi reheating nasa suke ci, sai shakiyanci suke mata wai ya sukaga tai laushi, ga tafiyarta ta canja ko ciwo taji?
   Itadai murmushi tai tace kwaji da gulmar ku, amma bazakuji bakina ba, ZAHRA ce tace, muma mun kusa mushiga daga ciki, kike wani yank’wana mu, zamuji mai akeji ehe”
   Ah to garadai ku

shiga, aini fatana da burina kenan a kullum, yau ace babu saura cikin mu, duk muna d’akin mu, amma fa kusani Wallahi babu abinda yakai aure dad’i da ni’ima, jin nauyi da tsantsar kunya wadda ba ara kayi ba, saidaran farko

   Ina muku fatan Allah yabaku mazaje nagari, Ameen suka ce duka.

  Hira aka zauna anayi, saidaga baya yayi mata waya akan su shirya motar da Ita zaizo abokin sane zai kaisu gida.

 Ango baishigo ba, sai 2 lokacin d’aya shigo sallah suke, d’akin sa ya zarce yana maijin wani farin ciki, shima gashi da Matar sa, Allah abin godiya.
    Bayan sun idar da Sallah aka fara shirin tafiya, kwalla suka fara, nan ya fito ya same su, dariya yayi yace oh su ZAHRA da Anee mene na kukan bayan zatana zuwar muku, kuyi shiru shidama aure ya gaji haka, ya d’auke ka daga garinku ya kaika wani garin, ya d’auke ka daga kasar ku ya kaika wata, so kuyi hak’uri zata kamuku ziyara yana magana yana share mata hawaye

     Sallama sukaimata har Auta suka tafi, ZAHRA tafi kowa shiga damuwa tunda sabone sukai tun yara, gashi zaman amana sukai, batada gidan zuwa sai wajan Deedoh gashi yau itama bata nan

  A Mota duk sunyi tsit, kowa na begen aminiyar kwarai Deedoh.
    Rayuwa tayiwa Deedoh dad’i, mijinta daidai yana bata kulawa baya barinta tai kad’aici, ko wajan aiki yaje suna manne a waya, Ita har mamaki take dama Malam yasan takan love haka?, yakanyi murmushi Idan ta fad’i haka kusa da shi.
    Mahaifan sa sun rik’e amana, suna kulawa da Ita, batada matsala a wajan mijin ta, daidai yana mata komai take so
   Tasan lokacin dawowar sa, kafin ya dawo tagama aikin ta, duk da akwai yar aiki, amma bata barinta shiga kitchen indai ba wanke wanke ba, ko mopping na tiles.

     Tana kula da cikin sa, ga tsafta, kwalliya ba’a magana, shiyasa yanzu Ahmad kullum yana mak’ale da Ita, bata nuna gajiya ko gazawar ta akan bukatun sa.
     Kafin yace yanason abu, Idan ta fuskancin abin, maza take taimasa, madallah da yara nagari, wad’anda suka sami tarbiyya ingantacciya.
     ZAHRA ankawo kud’i itada Yaya KITO da sa rana, Anee itama ankawo, Auta dama already da magana akan ta, suna waya zumuncin su daram yana nan.
    Yau bayan sungama aikin lada, suna gado a kwance Deedoh tai matsahi da kirjin sa, shikuma yasa hannun sa duk biyu, ya zagayeta da shi, hira suke mai ban sha’awa, da labarin da yadda yafara sonta itama itace masa nima fa inason ka, amma bansan inason kaba, saigashi Allah yaban kai kuma.
    Juyowa yayi yace, kin jiki Deedoh na, aibani kike so ba, wannan d’an uwan naki kike so?, dariya tai tace haba dai shiya kaiwa Zahra kud’in aure fa

  Plan muka had’a a lokacin, nan tabashi labarin komai, dariya yayi sosai, yace amma kunya kan, zan rama kuma akaci sa’a kunci gari, dan hankali na tashi yayi matuqa, baran Idan naga ya shiga gidan ku, Ashe wana ni akeyi.
   *

                   **

    3 Years Later
Gidan Deedoh na koma, ido nazaro ganin wai har anyi dare gari ya waye, Deedoh ce itada Ahmad da kayan sport ajikin su, ga ciki kato Haihuwa ko yau ko gobe, amma wai a haka take ball, da k’arfin Hali
    Kusa da Ita Babyn tace mai kyau, kamarta d’aya da Ahmad, suna zaune kan dadduma fifita yake mata, sai agwaluma da muruci datake ta ci, suna d’an tab’a hira 

  Ikon Allah lallai haihuwar ba wuya, ta haife ta k’ara k’unso wani, idona nakai ga Malam Ahmad yayi wani k’ato yayi fresh da shi, kamar bashi ba, lallai Deedoh KALLON KITSE kikewa Ahmad, Ashe duk inda ta d’auke shi ya wuce nan

   Gaye ne sosai, sajen sa yana nan saima gyara daya ke sha. A hankali ta mik’e tace kutaso nagaji da zaman nan, Huum yarinya ke kikace sai nan, ina ruwana yanzu kuma, badan halin kiba muje

  Wayar duka ya kwaso, ya tattara komai ya d’auki yarsa a kafada suka shiga ciki.

   Bata jima da zama ba, wayarta tayi tsuwa, sunan Zahra tagani, da sauri t d’aga 

 ” hello mai ciki, ko saina rigaki juyewa?, daga can ZAHRA tace Haba dai ninarigaki tunda kinyi d’a. Da gaske? Wallahi kuwa muna Asibiti ma yanzu ko baccin banyi ba nabugo

  Ah lallai Allah ya inganta sannu Zahra kinyi aiki. Nayi kam saidai fatan samun lafiya mai d’orewa
   Suna gama waya, da sauri tabishi d’aki tace My Sugar ZAHRA ta haihu, munada suna koh?, murmushi yayi yace ikon Allah ta rigaki, me aka samu?, kune. Mu to Allah ya inganta

  Hannun ta ya janyo, yace kwanta kin gaji da yawa Ga baby ZAHRA tai baccin ta sauran Momma itama ta kwanta.

  Batai musu ba, kwanciyar tai, sannan tace to yaushe zamu tafi?, ina zaki? Suna mana, tab a hakan zan barki, lallai kinyi wauta, kinga kadama ki b’ata ranki maza yi baccin Ki.

  Hannun sa yakai yanamata tausa, itakam baya ta juya hawaye harya fara sulalowa, yagani sarai ya kyaleta rigima takeji amma banda hauka Tana cikin kila wa qala tace zata suna har Abuja

   Bacci a haka ya d’ebeta, shi dariya yayi ma, sannan ya rungumota sukai bacci. Ko da Asubah bata kulawa ba, fushi takeyi

  Kwana wajan hud’u, za tamasa komai amma babu hira, a yadda suke da ZAHRA ace ta haihu amma ace bazata suna ba?, shiyasa take fushi, shikam ko ajikinsa tunda ba’a hanashi hakkin sa 

   Yau gashi sauran kwana biyu Suna, Sai waya ake mata wance tazo wane yazo amma Ita shiru, shiyasa tun safe take hawaye, girkin ma k’inyi tayi, gidan ba shara ba wanke wanke, mai aikin ma ta sallame ta, yana lura da Ita, ganin bata dena damuwar ba, yasashi tunanin tana da ciki kuma ba’ason masu ciki da damuwa shiyasa yau yace zai kawo k’arshen fad’an nasu.
   Da magreeb ta gaji da ganin gida haka, shiyasa ta mik’e tafara gyara gidan, girkin ma yi tayi, sannan tai wanka tasaka Riga da wando, harda bellet ta d’aura ta kame a kujera abinta.

   Da sallama ya shigo gidan, ko kallon sa batayi ba, amma ta amsa, gurinta yayo tsam ta mikar da Ita, yace lallai saboda ana fushi da Abban Baby shine shima za’a wahalar mun da baby kinwani saka zan zaro?, to ayimun afwaa Abban baby yaje booking flight ne gobe zaki tafi, dats all?

   Ido ta bud’e tace da gaske?, eh mana dariya tafara harda rawa Tana masa godiya sosai, rungumeta yayi yace waih Ashe kina nan da rigimar ki?, kin dagan hankali, dan ma baby ZAHRA tanawajan Mama da harda Ita za’ayi fad’an

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Leave a Reply

Back to top button