KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

 Wato duk irin kara da akewa Katsina kirari da Ita, yau Kano ta doke wannan kirarin, dan babu wanda baiga karamci ba, baiga kirki na mutan Kano b
  Family na Ahmad sunyi masa kara, sun nuna shi d’in d’an dangi ne, dan yadda sukaita d’awainiya da jama’ar amarya abin sai San barka, Uwar Ango inatakasa saka Ita taka ajiye, amarya mai kunya a haka dinner ta tashi lfy ba kace nace saima kowa daya tafi da murnar abinda akai musu.
  Flight suka bi, dan bazata kwana ba, gobe ne d’aurin aure shiyasa itama kanta Maman sa bata rok’i ta tsaya ba. Ango ansha kyau shida abokan sa yaran manya, kowacce shiga Idan yayi amsarsa take yana cike da murna Allah ya cika masa burin sa
@ut@r h@jiy@

[30/12/2016 11:32 pm] Re@l @ut@r h@jiy@????????: KALLON KITSE

®NWA_

©Zainab Y Hussein

Dedicated to Firdausi Jeeboh (Deedoh) & Zahra  Bukar
Second to the last page

   K’arfe 10:00 Allah yayi ikon sa akan Deedoh da Ahmad, inda aka d’aura auren su a k’ofar gidan su, akan sadaki naira 100k lakadan ba ajalan ba.
  D’aurin auren daya sami hallartar manyan k’ososhi na k’asa Attajirai da manyan Malamai kar harma da manyan ma’aikata
  Badan komai d’aurin auren yasami jama’a ba, saidai kyauta tawa da zama da mutane lafiya, mahaifin sa yau jinsa yake kamar ya sauke nauyi babba dayake kansa, yau yaga d’aurin auren d’ansa wanda yake so kamar ransa
  Ango yasha babbar riga ta d’anyan Pultos fari sai takalmin sa da hula bak’ake bakaramin kyau yayi ba, shida tawagar abokan sa da kuma Malamai na Makaranta daya koyar.
  A can gida Deedoh ce cikin  blue d’in Senator tai masifar kyau ga simple make up da ta sha sarka itama blue tana zagaye cikin kawayen ta da dangin ta, anata raha da labarai irin na aminan juna.
   Dariya takeyi ana ta hiran Anker ita yau batazo ba,cake ta tsaya saboda wata faduwar gaba data Ji, saboda fatihar dataji an anbata kuma anshafa, sak tai, hawaye tafara zubar wa. ZAHRA itace a kusa da Ita juyawar da zatayi saiganin ta tayi tana hawaye da sauri ta juyo duka tace Deedoh lafiya?, yaufa ranar murna ce, ranar da zaki d’aga hannu ki godewa Allah, kizuba ruwa a k’asa ki sha, Allah ya baki miji na nunawa a sa’a, ya lamincemiki miji nagari d’an nagartattu, mai hankali da sanin ya kamata, burin kowacce mace tasamu miji nagari mai arziqi, ke gashi Allah ya kashe ya baki, mene to na kukan?
   Jikin ta, tafad’a tasaki kuka mai k’arfi tace ZAHRA ke k’awa tace, kuma kin sanni sosai, amma na b’oye miki wasu abubuwa a rayuwa ta
   Dangina na sona, amma abin takaici wasu daga ciki basu duba Kansu, kullum burin su, suyimaka habaici wai a karatu zaka k’are, kaine can kaine nan ba miji, inajin bakin ciki Idan naji anfad’i haka

  Nakanyi kuka saidai Mama tace nayi hak’uri, akwai lokaci, shi aure, mutuwa, Haihuwa da samun lafiya duk lokaci ne, Idan duniya zata taru akan su baka miji Wallahi bazaka auru ba, matuqar ubangiji bai so ba, ko kuma lokacin ka baiyi ba.
   Ko kuma Idan zasu taru akan su hanaka aure, matuqar lokacin ka, yayi Wallahi saika yi, da haka nake share hawaye na naci gaba da harkata.
  Yau gashi lokacin yayi ba bikin ake ba, d’aurin auren akayi, godiya ga rabbis samawati
  Hawayenta ZAHRA ta share, tace Besty bake ba Wallahi yawancin yammata Kallon da ake musu Kennan basusan aure, basusan kafisu son ka d’aga kabar gaban iyayen kaba, kana danne damuwar Kane, Allah yaimana mai kyau. Ameen yammatan d’akin suka ce.
  Aunty maijidda Musa ce, tace Bena wai yammata ce?, Autace tace kinganmu duk OSB ne mu, Original Single Babies, masu auren kad’an ne, kuyimana fatan samun miji wanda yafi Malam Ahmad na Deedoh.
  Ameen tace itada Aunty Lubie da Aunty Sady Jegal, Maman twince itada Maman Haneep ne suka ce Ameen kannenmu Allah yayi muku zab’i na alkhairi
   Angwaye ne suka shigo, nan kowacce tafara murmushi, d’akin Mamanta suka shiga nan akayi addu’a da nasiha da nuna musu mahimmanci hak’uri da kuma jaddadamusu mai auren ya k’unsa
   Anyi pictures na tarihi, da kawaye da ‘yan uwa da abokan arzik’i, Beibi Isah anata iyayi Ita ga kawar amarya, komai yatafi cikin tsari, angwaye na shirin fara tafiya Abban Deedoh yace su tsaya su tafi da amarya ne ake jira
  Nan fa Deedoh akasaka kuka itafa babu inda zata, Wallahi tafasa auren amma ina aikin gama ya gama, wanka aka shigar da Ita, kafin ta fito ma wasu sun fara tafiya, su da yawa.
   Motoci sunfi 30 aka d’auki yan kai amarya, sannan akafito da Amarya aka shigar da Ita d’akin Abban ta nasiha ta gaskiya iyayen ta sukai mata, da kuka suka rabu.
  A ka d’auketa sai Kano ta dabo mai sarki Ado d’an  Abdallah, mai sarki Sunusi jikan Sarki Sunusi, tafiyar  awa d’aya da rabi Ita takasu garin na Kano
  Gidan iyayen sa aka kaita, suma dai fad’a akai mata, Maman sa tace ta d’auketa matsayin uwa ita zata zamar mata uwa, danginta su zamar mata dangi.

  Anyi raha da barkwanci, sannan aka d’auketa gidan ta ‘yanci. Kowa yashiga gidan saiya yaba da tsarin sa, da kuma dukiyar da aka kashe, kitchen kansa qaramin store ne, anyimata Kaya nagani na fad’a, kayan gadon ta biyu kujeru suma two set ga verses da aka qawata, parlour da bedrooms ba makusa.
   Yan uwanta basu jima ba, Abban ta yayo waya su dawo tunda sun kaita, Allah sarki kukan dai baya k’arewa haka suka tarkata suka tafi, Illa Beibi da ZAHRA Anee da aka bari, sai Auta da Queen Meemi tunda su dama suna Kano
      8:00 suka ce ta tashi tai wanka,batayi musu ba kuwa, wanka tai tayafa lafaya red, batayi kwalliya ba, Illa turare da aka bala, suna zaune a bedroom anata mata fad’a dai da ko yamata kissa, da kula da miji, tunda yanzu wata sabuwar rayuwa ce.
   Duk abinda kake Ji, ba haka yake ba, hasashene yanzu be zakaga reality, so komai saika kauda kai, kamaida komai ba komai ba, kaji abokan arziqi, Allah ka had’a mu da qawayen arzik’i
    Ango shida abokansa sunzo, anyi wasa da dariya, addu’a kuma ta biyo baya, abokan sa, tare dasu ZAHRA suka tafi, zasu ajiye su, agidan su Ahmad, k’asa musu sallama tai illa hannu data d’aga musu
     Kusa da Ita ya koma, yace Alhamdulillah, Allah abin godiya inakara godewa jalla wa azza da yaban ke amatsayin mata, inafatan Allah yaban ikon kula dake duniya da lahira.

   Allah ina rokon ka kabani ikon da zan nunawa wannan baiwarta ka kulawar danake fatan bata, Allah yayi wa auren mu albarka ” Ameen tace
    Tashi yai tsam ya janyo ledar da suka shigo da Ita, ciro takadda yayi, yana bud’ewa tsire ne gasashe mai roma roma yaji tumatir da albasa amma kad’an, sai kiwi milk itama daya Ciro
    Baijira komai nata ba, ya mik’e lifayar kanta ya warware, duk nuku nukun ta, haka ya gama ware ta, yace sakko, da hannu ya d’akko kwara d’aya yace oya open ur mouth, saidata ja aji sannan ta bud’e sannu a hankali yake ciyar da ita , Har saida yaga alamar ta k’oshi, sannan ya tsiya ya kiwi milk yabata, shima zama yayi yaci
    Hannun ta yakama yakaita bakin toilet, yace wanke bakin nasan kinyi wanka, kuma Bayan  haka garin da sanyi, Bata jira cewar sa ba, ta shiga Maclean da brush tagani, nan ta janyo d’aya ta wanke bakinta sannan tai alwala tafito
   Shima shiga yayi, ya fito, atakure take Ita duk kunya takamata, tarasa da wanne ido zata Iya kallon sa, ashe wuce ne mutumin
 Kayan bacci ya kamata, basharara bane suna d’an kauri, haka tasaka tayafa hijab, ya tasa Sallah tanabinsa a baya
 Suna idarwa tambayoyi yayi mata, kamar yadda addini ya koyar, duk da yasan Matar tasa ba baya ba, amma saidaya tambaye ta, tanajin kunya tagayamasa komai ya tambaye ta, a haka sukai addu’a suka Shafa da fatan d’orewar zaman lafiya a junan su.
   K’arshen gado Hajiya Deedoh aka koma, shi dariya take bashi, duk bakinta amma yau ya mutu, zama yayi yace My Sugar taso kiji, batakawo komai ba, taje janyo hannun ta yayi, yace wannan kunyar fa?.
   Ai cuta ta zatayi, beat solution shine a cireta kawai, ajikinsa yasata Tana sunne kai tana k’ok’arin kwace wa amma ina yan mazan ya hana, haka ya mik’e hannu ya kashe fitilar d’akin.
   To nidai sainace Asubah tagari Ango mijin amarya, MALAMIN FIQH da aka tsana yau gashi shizai angwance, wankan da akace ba’a iyaba Yau za’ayi shi. Lol

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Leave a Reply

Back to top button