KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

   Hhhh lallai ke Malamai 2 kika had’a, yimun shiru, amma fa gayen ya had’u duk da banga fuskarsa ba

   
@ut@r h@jiy@

[12/12, 9:00 p.m.] ‪+234 809 308 3613‬: KALLON KITSE
•••••••®NWA•••••••
©Zainab Y Hussein
Dedicated to Feedoh Yar ficika & ZAHRA Bukar
3⃣4⃣to3⃣6⃣

Feedoh dai tsabar haushi ko  online bata koma ba, tana zaune saidai ta tuno Ahmad Insta tsaki kawai take

   Shikuma daga can yana zaune dariya kamar ta kulle masa ciki, yanda yaga tayi yasan tanacan tana masifa ko ana bada labari

   Wayar sa ya janyo wadda ya ajiye ta, dialling number nata yayi, tana toilet tajiyo ringing d’in tazata Kwaiseh ce amma saitaga new number

   “Hello”

  “Hy ya kike Yar ficika shine kika gudu koh?

  Bangane ba a ina na gudu?, waye kai

   Daga d’aya b’angaren yace Ahmad ne, ai na d’auki number naki, naga kin sakata kekuma daga magana idan ya b’atawa yammatan rai tayi hak’uri bazan Kuma ba

   Baki ta zob’aro tace ai Kaine daga had’uwa sai maganar wani Akhbari ko Ishmawee, hala kana koyarwa ne?

  Eh inayi menene?

   Ba komai, amma banga alamara kana teaching ba, tunda some of Malaman Islamiyya basa wani karatu few ne cikin su, amma kai gaka handsome Indai har pics naka kake sawa 

   Gaka da ilimin ka da wayewa abin dad’i, ga ilimin addini da kake dashi, kaga kuwa yaushe zaka tsaya b’ata wa kanka lokaci kana koyarwa

   Huum, haka kuke gani, bamuda aikin yi tunda muna zuwa koyardaku?, kuma kuna bada kud’in wata ko term, amma baku tunanin da safe maimukeyi

   Munada abinyi taimaka muku muke, dariya tai tace nidai ban yadda kai Malami bane, Idan kai malamine ya akayi kake chat, ai su daga gafaka sai littafi

   Dariya sosai tabashi, Lallai kenan ke baki iya auren malami?

   Waih rufan asiri, Deedoh batama kula samari karatuna shine saurayi na

   A nan suka shan take sunata hira muryarsa mai dad’i, ga wani slight English dayake zubawa, kusan raina nata English d’in tayi amma bata nuna masa ba

    Basu fargaba saida sukaji kiran Sallah sannan sukai sallama, amma Ji sukai dama suyita hira

   Ido Deedoh tazaro ganin 2 hours suna magana, Lallai wannan to Waye shi?

  Batada ansa Illa,kwanciya da tayi, tana tuna muryarsa tayimata kama da ta MALAMIN FIQH amma wannan yes ne, shikuma NO ne

    Wasa wasa cikin kwana 2 sunyi sabo sosai, baiqara mata maganar wani FIQHU ba, labarai suke akan Korean series da Indian film yawancin duk film din data gani yagani, wani ma Ita a season 2 or 3 take amma shi yafice nan

    Sai hira akan wasu garuruwa da k’asashe, sosai sabo yashiga tsakanin su wanda Ita Feedoh batasan lokacin da sabon ya shiga ba

   Yau da akwai Islamiyya hakan yasaka ta duk wani iri, ga ZAHRA bata nan taje J TOWN Anee kuma ta dena zuwa saboda Exam

    2:00 tayi shirinta yadda tasaba, ta d’akko wayarta da Jakarta, tana cikin fesa turare taji vibrating nata, dakatawa tai ta ciro wayar

   A haf tasan shine, hakan yasa tai murmushi 

 “Hello yammatana doguwa hallitar Allah Yar ficika”

  Dariya tai tace kaganka, ya kike to feel fyn munata shirin makaranta

   Wacce makaranta kuma?, Islamiyya mana, ok time yayi fa. eh yayi

   Kuma yau Malam Ahmad garemu first gashi namasa laifi Kuma banson duka ko d’aya

   Ah aikam Idan kinyi laifi dole adakeki, dama nizan zaneki, naga ya zakiyi

   Lol Allah ni banson duk, amma fa shi baya duka Idan anyi laifi ma ba kullum yake dukaba gayen yanada kirki

   Dariya ya kyakyale da ita, yace ashe harda gayu cikin malaman?, haba dai shine kawai fa, shima ina ganin diploma ko NCE gareshi, shiyasa yake d’an wani ji da kai, amma wani gayu

   Yanada kyau sosai, ga fatarsa mai haske da d’an bakinsa abinda yasa zaka k’ara ganin kyau nasa tabon Sallah dayake dashi

  Lallai amma kunmasa kallon k’urilla, irin zano suffarsa haka?

  Haba dai kawai kasan Idan ka kalli mutum zaka Iya fad’i, kai bara nabarki haka kada ya dokarmun ke

  Huum ai Idan ya dakan kaima yaja maka, dan yaji zanyi nadena kula kowa tunda sunan ku d’aya

  Lalala to zanyi addu’a kada Allah yasa ya dokeki, Ki kamun yaji ai ba kanta ina zan ringa sauraron golden voice naki

   Maza ayi shiru atafi, agaidamun shi, kice mijinki na gaidashi

   Kai miji Kuma, eh mana, tsaya Malam bangane ba?

  A’a kije kawai mayi magana anjima, kafin tace wani abu ya datse layin shima da sauri ya fito ya hau machine nasa ya tafi yau shi kansa yaso yayi latt 
@ut@r h@jiy@

[12/12, 9:00 p.m.] ‪+234 809 308 3613‬: KALLON KITSE

••••••®NWA••••••

©Zainab Y Hussein

Dedicated to Feedoh Yar ficika & ZAHRA Bukar

3⃣7⃣to4⃣0⃣

Bakinta sake tana al’ajabin wannan mutumin lallai wai matar sa kwafa tai, tamaida wayarta jaka ta fito downstairs taga Mama sallama tamata akan ta tafi makaranta

   Allah ya kiyaye hanya, ki kula Autar mama.Tom Mama saina dawo

   Yadda take tafiyar ta kullum haka take yanzu ma haka, tanayi tana tuno Ahmad Insta da muryar sa afili tace ka had’u.

   Karyar kwanarta keda wuya wadda zata sadaka da makarantar taga Malaman abakin gate kowa sa k’atuwar bulala a hannu cikinta ne ya d’uri ruwa ita ko bulala batason gani bare Kuma ace ta hau jikinta.

   Agogon hannun ta ta duba, sauran 4 minutes afara taran makara ai da sauri ta saita tafiyar ta tafara da sauri amma ta maze irin d’in nan, haka ta shiga cikin makaranta hankalinta bai kwanta ba saidatajita a aji, sannan tasaki ajiyar zuciya.

   Ko zama batai ba, akafara Deedoh yau zakushata shine kika gudu ran nan?, Ido ta zaro tace banson gulma yama manta inajin, ku nama gudu haka kawai za’arunga mun tambaya kamar naci bashi ko a koto sai  haka, NI nama kusa daina zuwa aure zanyi na huta.

   Dariya suka saka amma a hankali, saboda tun lokacin data fara magana yana tsaye Ita bata ganshi ba.

   In baku labari na had’u da wani shima, nan ta zayyonomusu abinda yace, ku amma guy d’in ya had’u irin na aure ne.

   Mukuma ba irin na aure ba koh?, da sauri ta juyo a tsaye yake da bulala a hannun sa, Malam ina yini” lafiya lou magananniya.

   Guri tasamu ta zauna tace yau zakasha tambaya Wallahi, muje zuwa dai. Shi kallon ta yake yi yana murmushi shi kad’ai yasan mai yake saqawa a zuciyar sa.

    Yauwa yau ba karatu zamuyi ba, filin tambaya da amsa saboda haka kowacce tai tambayarta zan amsamata daidai gwargwado, kun gane? Eh su kace

    Haka kowacce tafara tambaya akan karatun su, wata akan abinda yashige mata gaba na al’amra daidai yana amsawa

  Malam inada tambaya? Deedoh ce tai magana, mik’ewa tai tace Malam ya ake wankan janaba ni bantaba yi ba, Kuma naji kusan kullum saikace Gusulul Janabati, shiyasa nakeson sani kuma inaso nafara yi tunda gaskiya bantaba yiba?

   Ido ya zaro yace Firdausi ai bawai ina nufin kuyi ba, a’a ku iya kafin ta same ku, kuma kusan menene yake kawota Idan kayi d’aya daga cikin abinda yake wajabta wankan ta dole kayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Leave a Reply

Back to top button