KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

   A’a bansan fa zaizo yanzu ba, naji dai alama breath d’ina yafa…… Uskut yace mata jin zata b’aromasa magana

   Tana sane ta gantsare tace Malam yana juyowa ai da sauri ya d’auke kansa, yace mik’e a hankali kitafi gida yana magana kansa a sunkuye 

   Gwalo tamasa ta fara tafiya tana cije baki, harta fita

  Adaidaita sahu ta tara sai gidan Lubie aminiyar kwarai aje asha shafta

   Tana cikin adaidaita tana tuna yadda taga Malam Fiqhu yayi, dayaga ta gantsare dariya tasaki tace kaikuma cemun Firdausi, saikace wata villager kai amma zan maka rashin m

  Yana wani kanne ido kamar abokina jumping????

   Saina b’aromaka tambayar dazata gigitaka, tunda kai kullum cikin bayanin mata kake har kana wani banbance Maniyyi da maziyyi hhhh zaka banbance wani abu kuma
Muje zuwa
     

  Kallon KITSE

®NWA
©Zainab Y Hussein
In Dedication to ZAHRA Bukar, nd Feedoh Yar ficika
2⃣1⃣to2⃣5⃣
A parlour ta tarar da Maman su, Shiga tai tana haki ta fad’a kan kujerun da ke zagaje a manyan parlour nasu

   Da Kulawa Maman tace Deedoh lafiya?

  Mama kedai bari wallahi MALAMIN FIQH ashe d’an iskane kullum maganar sa ta janaba da haila da wasu abubuwa ko wanka ko tsarki, yanzuma wai wanka zan koyawa yan ajinmu nikam na gudo

  Kika gudo ai abin alfaharinkine ace gaki kin Iya wad’annan abubuwan a wannan zamanin mata nawane wad’anda basu iya ba, kuma koyan ya gagare su

   Ilimin Fiqhu ai bayan Al Qur’an babu kamar sa, dashi zaka koyi yadda zakajewa ubangijin ka a tsarkake, ya ko yamaka yadda zakayi bautar Allah, yadda zakayi alwala da adadin ta, yadda zaka cud’e ko ina najikinka yayin wanka

   Deedoh wallahi kiyi alfahari da wannan ilimin naki, kudena cewa Malam Fiqhu wai basuda kunya

 Idan ba’a koyamuku ba, a ina za’a koya muku, haka zakujewa Ubangiji Ku kunamasu daud’a?

  Menene babbar Mara barmu da kafurai? Sallah to Idan ba’a koyamuku ba ya za’ayi ku iya kusan adadin ta da kalar karatun da akewa ko wacce da inda za’a bayyana da inda za’a sirrin ta da inda za’ayi ta mai tsawo da gajeriya da daidai misali

   Kafurai duk inda suke suna wari, amma mu meyasa bamayi? Saboda muna wanka su kuma basayi, wanka bana kullum ba a’a wanka wanda addini ya halasta

  Lallai Madallah ga Malamai nagari wad’anda zasu bayyana wa ‘ya’yayen mu karatu da bayani na gaskiya

   Jikin Feedoh sanyi yayi, tace Mama kenan duk abinda yake fad’a akan gaskiya yake?

 Tabbas kuwa Deedoh na, yanzu nasan bazaki koma ba, amma gobe tabbas saikinje tashi kiyi maza kije kicire uniform ashiga kitchen Iya Kwaiseh tana ciki kije kiga mai takeyi

  Tom tace, sannan ta haura sama, bakin gadonta pink colour ta zauna wayarta ta janyo, nan tashiga Dandalin Auta, readers ke hira ba writers ba shiyasa tafita sai gidan albarka wato NAGARTA nan taga Aunty Lubie ma tafara programme nata

    Gidan hira ta gudu, nan taga su Auta da Munay ga Sahaf ahaf bajewa tai ta d’ora akan hiran su

   Lokacin data fita bayan angama dariyar, cak naga kowa ya tsaya na juya sainaga Malam Ahmad ne ya d’aure fuska

  Xahra Bukar ya nuna yace mik’e, cikin sanyin jiki ta mik’e yauwa 

    Malama ZAHRA bani adadin kwanakin damai Haila da mai janaba suke d’auka kafin sunyi wanka

   Ido ta bud’e tace Malam lokaci yayi ma, Malam Nasmal garemu dana fad’a

   A’a aiyau double na keda, fad’i munaji

   Qunquni tafara, tanacewa kai wannan bakwai d’an iska ba, daga ya tambayi wannan sai wanccen

  ZAHRA yadai? Oh ai Yanzu dama zan fad’a

  Shi jinin haila kwanaki ne dashi, bayan d’aukewar jinin keyinsa wata tana kwana 3, wata 6 har zuwa kwana 15 a wata ruwayar akace har kwana 40 ana yinsa

    Hallita ne, kowa da yadda takeyi

  Janaba kuma shi ai baya d’aukan lokaci, kana Iya wankan ka alokacin dakasamu kanka, kuma ba’ajinkirta shi

   Alhamdulillah ZAHRA, to ya akeyin niyyarsu ko duk dayace?

  Eh niyya kusan d’a yace saidai zaka banbace wajan fadar Haila ko janaba

  Takhbeer nan akayimata kabbara 

   Haka yacigaba da tambayar yan ajin d’aya bayan d’aya

  Baisami mishkila da kowa ba, amma fa Deedoh tasa is d best

    Ta gidan su ZAHRA ta biya nan tafara gayamata yadda sukai dashi, Dariya sukayi nan Feedoh tace Wallahi sainayimasa tambayar da zai kasa gayan amsa d’an rainin hankali

  Yana magana kamar dole aka masa, ke gayen ya had’ufa black ne amma daga gani hutu ya zauna masa

   Hhhhh ZAHRA a ina hutu ya zauna yana koyarwar ai ni Wallahi banga abinda zanyi da MALAMIN Islamiyya ba, me suka Iya banda qala rasulu ko afara maganar lahira

  Me sukaci bare suba ka, kedai hala son Malam Fiqhu kike?

  Haba dai Allah ya kiyaye, amma wayar dayake rik’ewa kaf unguwar nan albarka nandai suka shan take rabin hiran duk ta Malam Fiqhu ne

   A chat databawa Auta labari ai nan tafara d’orata Wallahi kiyi masa tambaya wadda zai gigita, yama  rai naki, nan ta d’orata akan wanda Zahar ta gayamata
Autar Hajiya

KALLON KITSE

®NWA

©Zainab Y Hussein

Dedicated to ZAHRA Bukar and Feedoh Yar ficika
2⃣5⃣to3⃣0⃣
Bata sauka a chat ba saiga Kwaiseh da STYLICH nan akafara hiran ana cewa lallai shima tayimasa gyad’a tayimasa irin tambayar da yakeyi

   Aunty Jegal ce tace kunganku baran Auta kinfi kowa d’orata menene aibun sa, akan yanagayamuku gaskiya Feedoh kada kice masa komai kinji

  Dariya akasaka, Kwaiseh tace haba big Yaya ai kamar tayi tagama

   Haka ta manta da wani kitchen saida Maman ta shigo kana ta mik’e da sauri

   Malam Ahmad yana kwance ad’aki ya saka hannunsa ya bayan yayi matashi da shi, idonsa yana kallon fankar dake wulwulawa, idonsa k’ur tunani yake shifa Wallahi yaga type nasa, dama yanajin wani abu gameda Deedoh amma na yau ya zarce komai nata yayi masa

   Gata da addini ga Iya speach shifa ya more, bazai tsaya b’ata lokaci ba ko Jan aji ayi bashi kamar yadda yayi akan budurwar sa ta farko Ashnur saijin aurenta yayi 

  Best solution is to go nd tell her ina sonta, to Idan tace bata sonka ya zakayi?

Waye Malam Ahmad
Ahmad d’ane ga Alhaji Isah Kadara wanda yake attajirine yanada matan aure biyu inda kowacce cikin su Allah baibata Haihuwa ba, sai daga baya uwar gidan ta haihu akasami Ahmad

   Murna d’oki babu wanda basuyi ba, Ahmad wajan amaryar Abban sa yatashi tayimasa rik’o na gaskiya da amana ta tarbiyantar dashi

    Yayi makaranta sa a Musa Ilyasu daga nan yatafi ABU inda ya karanci Medicine zallah yanada kokari, Allah yabashi sa’a arayuwa shiyasa har ya k’are karatun sa baisami matsala ba 

   Ahmad yanada farin jini sosai, kuma ga sakin fuska dangi kowa nason shi, yammata ma haka

   Ahmad yanada kwarjini yanada burin taimakon mata shiyasa yakaranci aikin likita, Yanzu haka yana aiki a AKTH bayan wanda Abban sa ya bud’e masa a unguwar tasu ta Janbulo

  Mata da yawa nasonsa amma kowacce badan Allah take sonsa ba, wata dan kyau nasa wata dan kud’in su, gashi nan dai, shiyasa yace zaije inda ba’asanshi ba, yanemi matar aure kuma zainemi islamiyya yayi koyarwa aciki, ya lura mata sunada k’arancin Ilimin Fiqhu, sau dayawa zaiga wasu cikkakar alwala basayi daidai bare akai ga batun yadda zasu tsare dokokin wanka 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Leave a Reply

Back to top button