KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

KALLON KITSE -END

[: KALLON KITSE

®NWA

©Zainab Y Hussein

Dedicated to Feedoh Yar ficika nd ZAHRA Bukar

1⃣1⃣to2⃣0⃣

Adaidaita yana ajiye ta jakarta ta bud’e 1k tabashi ta juya, Hajya canjin ki? ko juyowa batayi ba ta bud’e gate d’in gidan ta shige

  Amaa taci karo da ita, da sallama ta shiga oyoyo Aunty Beeboh ashe kinzo?

 Eh ke kuma fa daga ina?, hhhh makaranta mana nan tagayamsu yadda akayi dariya suka saka nan ta shan take saidataga lokacin tashi yayi sannan tayi musu sallama ta ware

   Batajima da shiga gida ba, tajiyo wayarta ZAHRA Bukar ce 

“Hello qawas yah?

  Malam Fiqh yace mun wai bakida lafiya?

 Eh hhhh wallahi nasan qarya kike nan take taga yamata yadda akai suna dariyar sukai

   Maman Feedoh na sama, bataji shigowar taba, saidata sakko taganta tana sana’ar tata wato chat ta jona wayar tana charge itakuma tana aiki akanta

  Oh ni Asma’u Allah ka shiryamun Firdausi, Mama Firdausi nidai Wallahi banaso haba saikace wata mai tallan zogale, nidai Feedoh zakinacewa dan Allah, ko su Aunty suma haka suke cewa

  To naji Feedoh, Yauwa mumcy na Yanzu naji bayani, nashigo kina sama? Eh maza a tashi ai Sallah

  Haka ta mik’e Addu’a ma batayi wani dogon lokaci tana yiba, tashafa aka fara chat, 2go tahau Zahra itace online, anan aka fara hira, kafin wani lokaci saiga Auta aifa nan aka baje dagacan aka hau WhatsApp sai NAGARTA official

  Sun fara surutu kenan, saiga Aunty Lubie da gudu suka koma gidan hira

  Anan akafara zancen jumping da hiran su dai, basu suka saukaba sai 12:30 alokacin kowacce taje Sallah 

   Washe gari, anan azahar Feedoh aka tafi makaranta, yau tayi abin kai,

Ta gaida kowa, amma wani rashin M ko kallon Malam Ahmad baitai ba, tashiga aji

  Shine first period kowa ya d’akko Fiqh, an bud’e Yau Babun fil janabati za’ayi, Anma yi bayani zaiyi akan yadda ake wankan janaba da wanda ya tabbata akansa da kuma abubuwan da zaiyi da wanda bazaiyi ba

   Wanka ya wajaba ga wanda janaba takama, Firdausi tashi Ki fad’an wanka kashi nawa ne?

   Ido ta zaro tace Malam nashiga uku, ni fa Wallahi bansan janaba ba, ko mai Ita babtab’a gani ba, ka tambayi Zahra ko inda take bamazuwa koh?

  Dariya ce ta kwasemasa sosai aka dara, yace niban tambayeki ba, gayan wanka nawa ya kasu, kuma ki gayan wad’anda yakama?

   Mutsikka ido tafara tana yarfe hannu, a hankali tace wanka yakasu kashi 11, 4 ya wajaba dole tilas ne akan wanda Yakama

 7 shima wajibine amma bawai dole bane, Idan kayi fani’ima Idan bakayi ba babu laifi amma yin yanada fa’ida
1 wankan janaba

2wankan Haila

3 wankan Matacce(jana’iza)

4 wankan juma’a.

5 wankan sallahr Kisfewar wata

6 wankan sallahr kisfewar rana 

7wankan dan Sallahr EDI

8 wankan Shiga Makkah

9wankan jinin istikhaba

10wankan Shiga musulunci

11 wankan Haihuwa(nifa’si)

Sannan kuma wankan Haila wajibine. sannan Idan kayi tarayya da matar ka shima zakayi wanka, ko mafarki kai ko kaida kanka ka tsikanowa kanka to wanka ya wajaba a kanka

   Gawa anamata wanka, sai ranar juma’a shima ana wanka, da kuma Idan za’ashiga Makkah.gasu nan dai

  Tunda tafara magana gaba d’aya bakinta yake kalla, yana yaba tsarin hallitar ta, mamaki yake dama duk karatun da yake tana d’auka taburgeshi matuk’a

   Jin tayi shiru, yasa yaqara kallon ta khabbara akamata, zata zauna yace to zo gayamun tsarki nawa ya kasu?

  Bakinta ta zub’aro tace Malam ni…..bata k’arasa ba yace maza ina jira

   Ba yadda tai tace 2 na Hadasi dana kabari, shikenan ai

  Yauwa to nawane kaidojin musulunci?

   Hararsa tai tace Malam wannan ko jinjiri yayisu a ciki, bare ni 

  Naji gayan dai , biyar ne5

 Bravo alaiki ya Firdausi, sauran ki abu d’aya, gayan farillan sallah da sunnuni da mutahabai

  15 ne farillai, sunnoni goma sha takwas 18, mustahabi kuma laya’alamu  adaduhum illallah tana fad’a tana mugud’a baki

   Duk abinda take yana kallon ta, zama tai 

  A’a aibance ki zauna ba, fito kowa yana kallon ki kiyi mana bayani ki kuma gwada yadda ake  alwala da wanka wanda kikayi rannan baiyi ba

  Malam ni wai zanyi, bala’i, wai nizany?

Eh, aiba qarasa ba ta kwashi takalmin ta ta d’iba a guje

  Kiranta yake amma ina takai, aji me za’ayi inba dariya ba 

  Shima kansa saida ya dara, shifa gaskiya yanason Feedoh yadda take so a kira ta da shi
Haki take tana duqawa harta shiga gida
@ut@r h@jiy@ ce

KALLON KITSE
®NWA
©Zainab Y Hussein
Dedicated to Feedoh Yar ficika & ZAHRA Bukar
1⃣to1⃣0⃣

Yarinya ce doguwa mai kyan fasali da kyan tsari, tafiya take cike da yanga da tak’ama kaikace d’iyar Sarki ce 

  Bayanta nagani, uniform na Islamiyya ne ajikinta Ash colour riga da wando da hijab, wanda kayan daga gani sabbine ko ince tsabar kyan guga ya maidasu sabbi

  Takalmi ne a k’afarta irin peep toe d’in nan, shima Ash sai jakarta swaga itama Ash tafita take d’ai d’ai zataje Madarasatul gwadabe Maitasa 

   Tanason makarantar amma matsalanta d’aya Malam Ahmad mai Fiqh ya fiya jida kai gashi da bayanin iskanci jiya ma haka yace ta mik’e ta koya wankan Haila saikace bata Iya ba

  Mts wallahi sainasaka janbakin nan naga alama baison asaka Shege

  Magana take harta qarasa bakin makarantar, malamai ne a zaune amma ko kallo basu ishetaba illa d’aga kai datayi ta shige

   Firdausi sunan dataji ankirata dashi kenan, cak ta tsaya tasan ba kowa bane Illa Malam mai Fiqh ta tsani acemata Firdausi

  Juyowa tai, ganinsa tai cikin jallabiya fara ga hularsa samarin Madina sai farin glass nasa, u look so muah tace a zuciyar ta

  Firdausi bakida hankali kiga malamai ki wuce amma ko gaisuwa, kina tafiya saikace wadda zata gidan party ga takalmi mai tsini makaranta cefa ba gidan biki ba

  Maza d’ebi k’asa ki goge wannan janbakin Yanzu

  Kallon sa tai tace k’asa Malam?

 Eh ita, had’e rai yayi yace kina b’atan lokaci inada aji, maza yi sauri kuma kin makara ga omo can wankin band’aki ya tabbata a kanki, wannan acuci mazan a kunceshi yanzu

  Idonta ne yai raurau tace Malam Fiqh Plx I’m sorry don’t give me dis hard work ooo I….. Bata qarasa ba yace ke! is not Modern school is Islamic so u better keep ur small broken a side

   Ido ta bud’e jin wai broken, kut amma ya yanketa Ita datake degree na biyu shine zaice mata haka

  Tukunnama a ina ya koyi turanci haka?

   Huum a wajan ki na koya tunda ni banda iyayen dazasu sani makaranta

  Kunya taji ta lullub’eta, amma haka ta maze tace dan Allah malam kayi hak’uri Wallahi bazan kuma ba dama Sis Lubie ce tasiyo new cosmetic shine nad’an shafa amma bada nufi naiba

   Ganin yace a kamasa bulala yasa tasaki wata qara osh wayyo Allah tana magana tana dafe cikinta

  Da kulawa ya dubeta yace ke lafiya?

  Malam wata ne yakama dama naji alamar sa, inallillah Zahara Bukar kina ina kuka tafara wiwi tana dafe da ciki

  Hannu yakai zai kamata da sauri ya d’auke yace bara akiramiki ZAHRA saita rakaki gida kinsan kina ciwo kika zo

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Leave a Reply

Back to top button