KANWAR UWACE KO KISHIYAR UWA COMPLETE NOVELS

KANWAR UWACE KO KISHIYAR UWA COMPLETE NOVELS

                 ????

????K’ANWAR UWACE ????
Ko
????KISHIYAR UWA❓????

????NA BILLKISA IBRAHIM????????

  " Da sunan ALLAH mai Rahma mai jink'ai"
 "Ya ALLAH ina Rok'onka nasara, ya ALLAH ka Ni'imtar dani fad'in abinda xai amfani Al'ummarka, katsareni fad'in abinda zai cutar da Al'ummarka Ameen.


 ????????ina farin cikin sake had'uwa da FAN's d'ina awannan sabon ????????????.

»« Zuwaira! Zuwaira!! Wai ina Zuwaira ne ?? Dan ubanki bak’yajinane, shegiyar yarinya kaiyita yimata magana tayi maka banza.
“Tafito cikin rawar jiki har tana tuntub’e zata fad’i”
Tace”” dan ALLAH inna kiyi hak’uri wlhy ina SALLAH ne.

“”SALLAH ubammi kikeyi da ranar nan gatse~gatse??””

Cikin rawar murya tace inna ina SALLAHr walhane

Taja tsaki kekika sani, nidai ga Awara nan nagama zubawa ta dubu d’ayace da d’ari tara, wlhy yau kota nera d’aya tab’ta saina karyaki agidan nan, bare kuma kidawo min da kwantai, aisai kin tarar da uwarki ALAHIRA.
“”Dan labari yaxomin wajan su amuru mai rake kike zuwa kizauna to bazan hanaki zuwaba, insunje sun dank’ara miki ciki kekika sani, dan ubanki zaki jama abin kunya baniba”.

Kanta nakasa tana zubar da hawaye saboda jin munanan kalamin da innar tata take jefamata………✍????

????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I ???? U MY FAN’s
[10/25, 11:09 AM] ‪+234 809 777 0370‬: 17~ july~2016
????????????????????
????????????????
????2⃣????
????????
????

????K’ANWAR UWACE????
ko
????KISHIYAR UWA❓????

????NA BILLKISA IBRAHIM????

»« malam usman yafito daga d’aki, dayike dama tun d’azu yana jin duk kalaman matar tasa akan d’iyarsa.
“Yace haba Asabe wai miyasa kike hakane ?? Koba komai Zuwaira ai d’iyarki ce, ke mai karemata mutunci ce aduk inda kikaga mai wulak’an tata.

Eh malam ai dole kace haka, nidama tuni nafahimci kana nuna mini bani nahaifi Zuwaira ba.
“Nifa bahaka nake nufiba Asabe, ina nuna miki kiringa gyara kalaminki akan Zuwaira ne, ki daina jifanta da miyagun kalamai, duka nawa Zuwairan take daza’a ringa jifanta da wad’an nan kalaman”.

Inna asabe tamik’e cikin matuk’ar masifa, kai malam ina dai dai dakai wlhy, nafara gajiya da rainin wayonka…
Da sauri Zuwaira ta d’auki botikin Awarar ta tai waje, dan bazata juri ganin ana cima babanta mutunciba.

Haka Zuwaira taita zagayen tallah, ga garin da Rana mai zafi, amma takasa zama, dan tana son ta saida Awaran, saboda garga d’in da innar taimata na karta dawo mata da kwantai.

Sai wajan La’asar ta saida Awarar, tasamu guri ta xauna tana k’idaya kud’in cinikin nata, tagama k’irgawa naira dubu d’ayane da d’ari takwas da naira sittin, saura naira arba’in, ????tai shiru tana tunanin ina sauran suka mak’alene, dan tasan itadai bata sai komaiba, kuma bataci Awara ko d’ayaba, dukda tana matuk’ar jin yunwa.
Dan har wani jiri jiri take gani, tunda duk yau kokone kad’ai acikinta shima d’in kabirune yasha ya rage yabarsa a tsakar gida tad’auka tasha………✍????

????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I ????U MY FAN’s
[10/25, 11:10 AM] ‪+234 809 777 0370‬: 18~ july~ 2016
????????????????????
????????????????
????3⃣????
????????
????

????K’ANWAR UWACE????
Ko
????KISHIYAR UWA ❓????

????NA BILLKISA IBRAHIM????

»« da sauri tad’ago kai danjin antab’ata, tasaki ajiyar xuciya dan ganin Safare k’awarta, tace kai Safare wlhy har kinbani tsoro, tun d’azu naketa jiranki daga amso kud’i kinje kinyi xamanki, kinsanfa wanke wanke nacan yana jirana.
“”Kiyi jak’uri Zuwaira kinsan wancan d’an iskan shabbal d’in in yacimaka abu, saiya gadamar baka kud’in””
Sau uku yana cimini taliya amma bakud’i, shiyyasa yau naje naturke shi.
“”To yabaki ??”
“Eh yabani naira cassa’in d’ina, kema gashi lawandi yace nabaki naira ishirin d’in Awararki”

Yauwa wlhy harnaji dad’i, danni nama manta yacimini Awarah, bai bani kud’iba, yanxu saura naira ashirin.
“”Na manta wanda nakebi nasan kanta sai an dakeni wlhy””
Safare tace aina manta nima kina bina naira goma.
Kin manta kuma kina bin Lami naira goma.

Kai aiko hakane Safare, saidai yanzu ta tafi gida, ga gidansu da nisa.
“To kibari sai gobe mana, tunda dai muna tare, nasan itama ta mantane”
Humm baxaki gane bane Safare inna tace inhar nab’atar da kud’i saita karyani, wlhy Safare ina tsoron duka.

Safare tazaro naira goma akwagirinta, tace karb’a ni gobe idan Lamin tabaki saiki bani.
“”Takarb’a tana murna kai Safare nagode ALLAH ya barmu tare””
Amin Zuwaira, tashi mutafi kar innata taimin fad’a, dan baba yakusa dawo wa daga gona.
Haka matasan ‘yan matan suka rankaya xuwa gidajen nasu.

Safare tace dama kinzo munje gidanmu munci abinci, dan yau innata danbu takeyi, nasan yanzun kuma ta gama.

Safare bazuwanne bana son yiba, ina tsoron jarabar inna ne, kartace naje nazauna dan kar nayi mata wanke wanke, da shara kiyi hakuri, gobe kafin natafi tallan koko zanzo nagaida innarki kinji.
To shikenan Zuwaira ALLAH ya kaimu goben lafiya.
“To amin”
“Kowacce tanufi gida……..✍????

????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I ????U MY FAN’s
[10/25, 11:10 AM] ‪+234 809 777 0370‬: 18~ july~2016
????????????????????
????????????????
????4⃣????
????????
????

????K’ANWAR UWACE????
Ko
????KISHIYAR UWA❓????

????NA BILLKISA IBRAHIM????

»« duk da yau tanada karfin gwuywa tunda tasayar, kuma bata b’atarba, amma tana fargabar shiga gidan, dan batasan mizata tarar ba, amma bayanda zatayi dole tashiga.

Cikin sanyin jiki tashiga gidan da sallama, su Atika ne kawai a tsakar gida, suna cin taliya ‘yar murji, itada Hak’ila da kabiru.
“”Tace Atika ina inna??
Cikin masifa Atika tace ban saniba, kiduba mana, aikinada idanu ko, keba makauniya bace ba, daxaki tanbayeni inna.
“”ALLAH yabaki hak’uri Atika””
“Hakuri kayane nad’a gammo na d’ora miki””

Bata sake cewa komaiba, tanufi d’akin inna Asabe.
SALLAH ta tarar tanayi, daga ita sai d’aurin k’irji, dawani yabu d’ad’d’en zani, mai shegiyar daud’a, shima xanin jikinta daud’arne dashi, dan yakai kwana uku ajikinta, kuma kullum dashi take aikin Awarah.
Da sauri ta sallame SALLAH, dan inagama bata gamaba, ko addu’a bataiba.
“Tace ya akayi ? Inji dai ansayar kuma kud’i cif cif.””
Zuwaira””tace eh inna ;

Toki bani mana kinbi kin kankane kud’i kink’i bani, sai zaremin ido kikeyi, kamar na mujiya.
Jikin Zuwaira na rawa ta ciro kwagiri ta mik’ama inna Asabe.

Tasa hannu ta fisge tana mita.
Tafara k’idaya kud’i, naira dubu da d’ari tara cif cif.
????” tawangale baki eh lalle ‘yar gidan RAKIYA yau kinyi abin kai, ALLAH ya jikan RAKIYA, gobe kuma kika b’atar min da kud’i, nace ALLAH ya k’ara mata azaba????.

Tashi kije tuwo na nan arumfa ki d’umama kici, ga wanke wanke nan yana jiranki da sharar tsakar gida.

Da sauri Zuwaira ta mik’e tanufi rumfa, tad’auki tuwo, ta d’ebi miya taja gefe ta hau ci, bata nemi d’und’umawar ba, dan saboda azababbiyar yunwar datakeji, ga tuwon da sanyi , amma wannan bai dametaba.

Saidai kasan zuciyarta tana tunanin inna Asabe,
“”K’ANWAR UWACE ko KISHIYAR UWA ?””
Da wannan tunanin tagama taje tahau wanke wanke……..✍????

????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I ????U MY FAN’s
[10/25, 11:10 AM] ‪+234 809 777 0370‬: 19~ july~2016
????????????????
????7⃣????
????????
????

????K’ANWAR UWACE????
ko
????KISHIYAR UWA❓????

????NA BILLKISA IBRAHIM????

»« kuluwa bata son malam Usman ko kad’an, dan tace me nasama yaci bare yaba na k’asa, kullum yaxo zance sai a aiko Asabe wajansa, ace yabada kud’i.
“Wannan abu yana bama Rakkiya haushi dan ita bata tare da ra’ayinsu ko kad’an.
Rakkiya tasamu baban ta tasanar masa abinda yake faruwa.

Baice da kuluwa komai ba, dan yasan jarabarta, sai yasamu malam Usman yace yaturo iyayensa.
Aiko wannan magana tay masa dad’i.
Malam Usman yasanar da maga batansa, akai komai, akasa biki wata biyu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Leave a Reply

Back to top button