KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

   Wanka shine gaba, tunda Idan har yarinya ta kai minzalin da zatayi al’ada wanka ya wajaba akanta, to Idan bata Iya bafa?, ko ta Iya amma bata cikakken sani akan yadda zata cud’e can tasawa nan ruwa ai anyi ba’ayi ba kenan

   Haka zaka jewa Allah kanamai najasa, kayi masa bata bacikin tsarki ba, (dan Allah mata adaure Wllh akwai wadda ko yanda akeyi bata sani ba, even niyya ta wankan wata bata iyaba, amma tafito tana gwalli)

  Kana iyayi kana turancin banza kana kashe kud’i kuna zuwa cinema ko malls ko yaukaine nan qasa Kaine can, Ka daure ka Iya wannan abubuwa badan komai ba, saidan Ibadarka ta cika kuma ka kasance cikin tsafta

   Yazo garin katsina badan komai ba, saidan kara dayaga mutanen suna dashi, kuma katsina tayi kusa da Kano zai iya zuwa gida lokacin da yaso

  Abokinsa shine yayimasa hanyar da aka d’aukeshi amatsayin MALAMIN FIQH

   Shekaransa d’aya da wata uku cikinta, yana jin dad’in yadda kowa ke yabon sa akeson period nasa, Illa FEEDOH dayaga bata so 

   Yayi tunanin irin ajebo ce, amma jiya tabashi mamaki yadda tasan sharuddan komai, yanason mace mai shagwaba da ilimi Feedoh duka ta had’a

  Gata ba laifi kyakyawa black beauty, ga hanci bakinta maikyau hak’oranta farare k’al garaigarai

   Siffarta ke masa gizo, yana hango yadda take cuno baki gata taiwa sai tsoro

 Idonta namasa kyau, haka yazauna yana sunbatun son Deedoh

   Wayarsa ya janyo, a zuciyarsa yace aji irin na Deedoh nasan dole tana insta bara naga

  Searching sunan ta yafara, yasaka Feedoh nan ya laluba ba Ita, yasaka Deedoh nan ma no, Firdausi zaisaka anan dariya takamshi yadda ta tsani sunan aiba zatayi using dashi ba

   Haushi ne yacika shi, har zai fita saiyace bara yaga yaji ZAHRA nacemata Yar ficika nan yasa shima no, OK bara na raba naga 

Yar_ficika yes

  Nan yai following nata, Pics nata yashiga nan yafara cikin karo da ita aisaiya rud’e yaga yadda take real zuba gayu wani photo ne yaja ra’ayinsa wanda tai kusa da bishiya ta bud’e garaigarain hak’oranta ta dafa kugu tayimasifar tafiya dashi

   Komai ya tuna naga yayisauri yayi unfollow nata, wayar sa d’ayan k’iran Motorola new Yar yayi, Ita yaimaza yai download na  insta ya bud’e shi

   Posting pics nasa yai guda 2 nasa amma duk irin yakare fuskar sa, sai ragowan kuma duk irin me love d’in nan ne

  Sunanta yasaka, sallama yayimata

  Batajimaba ta amsa anan yace mata nice short, tnx tace 

    Yar ficika sunan yamun sweet abaki

“Koh tace masa, eh shima wajan posting nasa tai, pics sunmata kyau baran wani mai kalamai sanyayyu 

    Basu qara magana ba, kowa yacigaba da sabgarsa

   Nan fa akafara saving pics, yanayi yana qara jaddadda sonta cikin zuciyar sa

@ut@r h@jiy@

[12/12, 9:00 p.m.] ‪+234 809 308 3613‬: : Assalamu alaikum My Fanc
Amadadin dogon nazari da kuma dan abubuwa da hangen wasu al’amra nacanja wa littafina NI DA MALAMIN FIQH suna zuwa KALLON KITSE.


              ***

                          * 

KALLON KITSE
®NWA
©Zainab Y Hussein
Dedicated to Feedoh Yar ficika & Madam ZAHRA Bukar
3⃣1⃣to3⃣3⃣          

Yau Thursday ba Islamiyya shiyasa Feedoh bata da wata fargaba, akan MALAMIN FIQH, tasan bamakawa saiya doketa wannan gudun datayi, gashi  ZAHRA tace ansiyo Manyan bulale da aka tashi

    Amma ganin ba Islamiyya yasaka ta bararraje tafara chat, brush tai da wanka, tasaka yar vest haka da wani milk skirt ta janyo pillow ta d’ora kan cinyarta ta aka soma sana’a  sa’a

    Tana hawa da Maganar Lubie tafara cin karo, nan sukai hiran su irin ta amintattun k’awaye, sannan ta shiga group nata, yau rashin Mutunci zatayi shiyasa ko d’an abokin mu jumping bata saka ba, tafara duba wad’anda basa comment removed tai na wajan 10 peoples kafin aka shiga gidan hira dandalin karya tattalin Data 

    Hira suke sosai ana Shafa, saiganin abun Insta tai ya shigo, da sauri ta duba, Mohd Ahmad ne na jiya, yayi liking pic d’inta ga comment da yayi mai dad’i, tnz tace masa

   Magana yayi mata, zai iya samun contact nata, ko WhatsApp suyi, yaga tanada hankali

  Later tace masa kawai, bata fita ba, taga yayi posting photon sa, wow he look so nice da kayan NYNC yayi amma yasaka fulan ya rife idonsa

Huum, amma kai mai yasa baka fidda ainihin fuskan ka?, naga yawan cin pics naka kana cover na face why?

   Ba komai, kawai inason photo a haka, ok

  Am nace naga kinsaka author kina rubutu ne?

  Eh inayi, but social not publishe one

  Ashe ina tare da marubuciyane, wanne book kika rubuta?

  Ba yawa, amma dai Kunya Adon Mace dashi nayi popular

  Kai zanso na karanta, Kunya tabbas Adon Mace ce, amma sainaga kamar wasu matan basuda kunya, baran na wannan zamanin Kuma kunya tanacikin musulunci

  Da alama littafin ya fadakar, ya za’ayi nasame shi?

  Kai maza dama suna karatu?, eh to wasu sunayi, inacikin jerin wad’anda basu yi, amma tunda kece zan iya karantawa

  Huum, ni kuma yaushe kasanni da zakace haka?

   Ai kinsan ana iya sabo na one hour ma, bare mu harmun kwana ma

  Haka!, harnafara d’okin nakaranra nasan anyi aiki da ilimi wajan yinsa daga gani kinada ilimi daidai gwargwado

  Hhhhh, saikace munzauna ko katab’a ganina?, kufa kanawa kunfiya Iyayi komai karatu, da alama kunason karatun addini sosai

  Wallahi kuwa bare na Qur’an da FIQHU dan sune ja gaba, rashin sanin ilimin FIQHU ai babbar asara ce ga d’an adam Wallahi

   Na farko kinga shi Qur’an yagayamana zamuyi alwala muyi Sallah muyi wanka, mu bautawa Allah, amma baifad’i yadda zamuyi bai fad’i adadi ba

  Amma FIQHU shiya fad’a kuma ya tantance ya ware Sunna da Farilla da Mustahabi, ya ware Sunnah mu’akadda wadda sunnah ce amma maik’arfi

  Ya…..a’a Malam afwaan, wannan zuba haka, da alama kagama typing d’in abin kafin kafara

  Waih wa’azi amma kana fama, Kuma shine kake Insta da WhatsApp?

  Da alama malami ne kai?

  Kwarai kuwa MALAMIN FIQHU Kuma na Islamiyya ba

   Tab, kaga sai anjima da kafara hira mai dad’i amma zakasako wani zance, muma munada irinku a garin mu

   To kai inbaka shawara, Idan kana magana da mace kama dena cewa kai MALAMIN ISLAMIYYA ne, dan ba wadda zata soka, ahaka dai kamar wice kai amma ina ashe ….tab a hakan zanbaka number na?

  Dama FB kaje Ka bud’e page akan haka, amma daga had’uwa zaka fara zuba

   Ku zancen ku d’aya, wanka tsarki haba, ninama fara ganoku, duk iskanci ne a fakaice kukeyi 

  Bye

   Tana gama fad’a, ta sauka tana tsaki, kut da harna fara zurmawa kalarsa tamun, duk da banga face nasaba, ashe ajebo ne

  Amma Idan hakane Malaman Islamiyya suna kyau, saidai ba Money a hannu, gasu wayewarsu kad’an ce

   Amma suna kyau, kaya kuwa kala 5 ko 6, kai a tafe su a tafe

   Waya ta d’auka ta bugawa ZAHRA, tace ke qawa nahad’u da Malam a Insta, haryafara maganar tasu ta wanka tsarki saikace ba’a iyaba 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Leave a Reply

Back to top button