KALLON KITSE COMPLETE NOVEL
To Malam mene yake wajabta wankan, Kuma meyasa sai nan gaba zamuyi?
Tana magana idonta a k’asa, shi mamaki take bashi lallai yarinyar nan, zaiyi maganin ta
Bayani yafara mata, yace Yanzu danaji kince gayen ya had’u, idan azuciyar ki kikaci gaba da kiyasta hallitarsa dole zakiji wani abu to anan ma wataqil wanka yakamaki
Cigaba yayi Tuntana ji harta dawo kwanyarta tafara rufewa yana gani tafara rife Ido shikuma yak’i yadena jin ba alamar tsayawa tace Malam nafa gane ka barshi haka dan Allah .
Ai bawaike nakewa ba duka yan ajin, suma su fuskanci me ake nufi da haka, to ai sun fuskanta
Shiru yayi dariyarsa yasha azuciyar sa ganin tamakasa d’aga Ido ta dubeshi
Yana sane yace, yan aji kuna raina malaman Islamiyya bansan mai yasaba, kodan bamiyun swaga kuma bama hawa motoci, bamu Iya turanci ba, ba yan gayu bane mu, shiyasa ma bakwa son kuji wani yace yana sonku?
Ai arziqi na Allah ne, kuma bayan haka, itama wayewa haka, da yamma kawai muke zuwa bakuyin tunanin da safe muna wani abin plx ku canja, wato ku sai gayu sune mutane?
Nan yai musu nasiha afakaice kuma da Deedoh yake.
Nagama sauran ke Firdausi meyasa kika gudu daga tambaya?
Ido tafara mutsikawa tace Malam fitsari nakeji lokacin fa, kuma Kuma……
Kuma me?, ai saina zaneki Yau, rashin kunya koh?, Wallahi a’a ancema kada ka dakeni Wallahi tana magana idonta taf kwalla. Yar gata wayace kada na dakeki? Ya Ahmad mana.
Waye shi? duka ya tabbata akan ki kuwa. bulala uku ya tsulamata masu zafi yanayi yana dariya aikam tajita a jikin ta.
Kuka tasaka tana kare jikinta har ya gama, tunda tasa kanta a cinya bata d’ago ba harya fita hak’uri akafara bata haba Yar ficika kiyi haquri mana daga wannan dukan dukan
@ut@r h@jiy@
[12/12, 9:01 p.m.] +234 809 308 3613: KALLON KITSE
®NWA
©Zainab Y Hussein
Dedicated to ZAHRA Bukar & Feedoh Yar ficika
4⃣1⃣to4⃣3⃣
Duk maganar da suke batace komai ba, illa ma kara kukanta da tacigaba dayi, yana zaune a kujera a saitin tagar ajinnasu duk abinda ake yanaji saiyanzu yayi danasanin dama bai doketa ba, tabashi hak’uri.
To yariga yayi ba yadda ya Iya, to ko hak’uri zaibata no aizata gane shine amma yasan yadda zai mata haka yayita saqawa yana warwarewa gashi yau tai kyau batasaka komai ba.
Ko da aka fito Sallah bata tashi daga inda take ba, qawarta Kwaiseh itace ta zauna a wajanta tanata bata haquri akan ta taso, amma taqi. Zama tai akusa da ita tanacigaba da rarrashin ta
Har akaje aka dawo bata dago ba, Kuma yana hankalce hankalinsa duk yabi ya tashi saiya tuno lokacin datace zata makara muryarta mai sanyi tana d’an dariya amma yanzu ya sa taji rashin dad’i.
Gidan gaisuwa za’a shiyasa aka tashi da wuri, gida ta tafi ahanya tanaji wayarta na ringing amma bata d’aga ba, niqab tasaka a fuskarta haka ta qarasa gida.
Bai daddaraba yayita kiranta amma ko alamar d’aga wa ba’ayi, hankalinsa duk ya tashi a gida ko abinci baici ba harwajan isha’i baisamu ta d’aga ba.
Ita kuma tsabar haushi ko qasa bata sakko ba, tana d’akin ta Mama ma dakanta ta shigo tace yammata na yakai naga ko qasa bakije ba Abban ki yana cewa ina Deedoh d’ina take?
Mama Wallahi bazan kara zuwa wata Islamiyya ba, dama zaman banza yasaka nake zuwa, ace kamar ni wai Yau aka doka, kuma wai MALAMIN Islamiyya mara class tab Wallahi ban qara zuwa.
Haba dai kefa kikace aure shine zai rabaki da ita yanzu kuma kice haka?, eh mama Wallahi banzuwa ko inane gara na zauna a gida abina, to Allah ya kyauta halinki sai ke ko yanzu ma wataqil kice gobe zaki.
Niban zuwa tana magana tana diddira k’afafu, murmushi Maman tai ta ce oya azo aci abinci kinji.
Allah sarki Ahmad yanacan yacika waya da massage akan yajita shiru tayi hak’uri ko anduketa amakarantar? Ba amsa tunda tana off. A daddafe yai Sallah yaci abinci ya kara bugawa Ita jin andameta da kira yasa ya janyo wayar takara a kunne
“Hello ” wata ajiyar zuciya ya sauke yace My Deedoh meyasa kinsan tashin hankalin da kika samun?, inata kira shiru Allah yasa lafiya?.
Maimakon tabashi amsa sai kuka tace kaga fa ya dokeni Kuma nace masa kace kada adaken, Wallahi bani baqara zuwa yaje yayita dukan wasu amma bani ba, mugu kawai yana bayanin iskanci nama ganesa dan kawai yayi hiran iskanci yasa yace a bashi class d’in mu.
Habadai ai karatune wataran kuma zaki gane, kidena cewa haka kinji?, naji amma dai banqara zuwa. Rarrashin tai da kalamai masu dad’i saigata ta ware anan ya furta yana sonta gaskiya Wallahi pics nata kawai yagani yaji yana k’aunarta.
Ance ka auri mace dan kyau nata, dan nasabarta dan addinin ta dan kud’inta amma ka auri mafi addini dayafi.
Kyau yana gushewa, dukiya tana k’arewa, nasaba wataran zata qare tunda akwai mutuwa addini kuma baya qarewa yana zaune cikin kwanyarka.
Halayenki da maganar ki tason zuwa makaranta duk da ayanzu budurwa kamar Ki maiji da kanta Wallahi bazata b’ata lokacin ta ba wajan zuwa Islamiyya boko shine a gabanta.
Kiyiwa magana kyakyawan gani Wallahi inason ki da aure Kuma bada wasa ba, plx accept my request Deedoh mai kyau na.
Kasa magana tai, jikin ta duk yayi sanyi, maizata cemasa?. Naji kinyi shiru ko nabaki lokaci?
Eh kaban,tom bara nabarki haka, saboda nasan bakicin yanayi mai dad’i Malam ya tab’amun ke, danasanshi ai fad’a zamuyi
Nan sukasha hira tama manta da wani Malam Ahmad mai FIQH, tanajin son Ahmad Insta yanabin jikinta muryarsa kad’ai abar so ce komai dalla dalla yake fad’a bashida hayaniya kamar Malam Ahmad na Islamiyyan su saidai shi mugu ne
Sannu sannu kwanaki sukaja, soyayya bakama hannun Yaro Feedoh yar gari an had’u da dan gari irin type nata. Makaranta kuwa ta rufeta tace Bata qara zuwa saiyau dai tace bara taje, tunda kowa yazo akan ta koma.
Koda sukai waya tagayawa Ahmad zata je Makaranta Yau, yayimata addu’a Allah yasa baza’a doketa ba
Huum babu mai tab’amun ke, ko KALLON banza, Wallahi wanda ya taban ke fad’a zamuyi, kada kiyi kwalliya ina kishi Kuma Idan kikai zanji ajikina
Tom tace daga nan ta tashi tai abinda ba’arasaba tafara shirin zuwa makarantar
@ut@r h@jiy@
[12/12, 9:02 p.m.] +234 809 308 3613: KALLON KITSE
®NWA_______
©Zainab Y Hussein
Dedicated to My ZAHRA BUKAR (jumping) & Phirdauce Jeeboh{ Deedoh, yar ficika}
4⃣4⃣ to5⃣0⃣
Wanka kawai tai sai lotion data shafa na company’n oriflame, dan yanzu batada mayukan shafawa sai na wannan company’n badon komai ba saidon ingancin su da kuma saukin su.
Pawder ta janyo Tara itama mai kyau ce, ta shafa sai kwalli da white lip da tasaka, humrah tasa sannan ta janyo jaka sai Islamiyyar su.
Lokacin data qarasa ba kowa a k’ofar makarantar haka ta shige, ajinsu itace ta uku a zuwa, tana shiga suka saka sowa oyoyo Deedoh anyi missing juna, Wallahi ajin so silent dabaki nan, hira suka fara yi har ajin yafara cika.
Malamai ne sukaita shigowa ana karatu, yau basuda Malam Ahmad sai andawo Sallah shine ma last, Deedoh jikinta duk yai sanyi tasan dole ya daketa tunda tai kwana biyu ba tazo ba, gashi yayi test haka ta zauna.
ZAHRA ce tace ke dallah kisaki jikin ki, babu abinda zai miki, ai ran nan akace da ba kizo ba, yayita raba idanu, Huum bamafa ya wani dad’e wa a aji tunda kikadena zuwa.
Kanbu, to mezaimun?, yama raina ni, ni idanma baiyiwasaba wallahi saina dena zuwa gaba d’aya, dama Only ne yace nazo.
Hhhh su only manya, shima yace kizo to da saiki zauna yar rainin sence, hira ta jata harta ware akafara zancen Autar Hajiya da abokinta jumping, dariya suke lokacin da sukazo kan labarin Auta afagen soyayya, Ita Deedoh tace tafi Auta Ita love ke zahra kikace Lallai su ai manyane Auta da ake kukan love ai kinga abin ya yi girma.
Dariya suke kwasa sosai baran Deedoh dama akwaita da dariya.
Sallama yai ya shigo babu wanda yaji dalilin hargitsewar ajin da yayi da surutu, wata ya qarayi amma shiru, ya fusata sosai harya juya zai d’auko bulala, saiya tuno da Only batason duka haka ya maze ya shiga daga ciki.
Da ita yafara had’a Ido wani asirtaccen kallo yamata wanda Ita kanta saidataji a jikin ta, shiru kowa yai, nan ya zauna karatun su yau akan rabon gado akai, tunda sun shiga Izziyya, baiyiwa kowa magana ba, saidaya gama sannan yayi fad’an surutun da suke, hak’uri aka bashi.
Phirdauce me yahanaki zuwa Makaranta kwana biyu bayan lafiyarki lou?, shiru tamasa, saidaya qara maimaitawa sannan ta d’azo tace Malam banda lafiya fa. Lailah k’arya haram bakida lafiya amma kina Iya rik’e waya kuma kina fita bakin ki yana Iya magana, wannan cuta ta gayu ce kenan?
Itadai shiru tai, saboda yanda yake magana saitaji kamar only, suna kamanceceniya akan wasu abubuwa, amma Ahmad d’anta yafi wannan tunda shi handsome ne, bayan haka only has all d qualities that any gal wanted to became good husband for her, ga Iya kalami da tarairaiya yasan kan ta sosai, ko fushi tai yasan yadda zai shawo kanta.
A chat yanamata magana masu dad’i, Huum bazance Malam baiyi ba, ya had’u daidai auren yar Malam.
Shima ya d’an Iya speak, amma ina Iya love ko tarairaiya awajan MALAMIN Islamiyya, barsu dai da janyo aya, ana magana amma maganar wani, love, kiss, need duk basuje part d’in ba.
A wajan hadith dai sune gaba, gaye har gaye amma kalli ya b’ige da koyarwa, nikam sai Ahmad kana mun wani kallo to kwalelenka.
Duk maganar nan tanayin tane a zuciyarya cikin yan sakanni.
Feedoh yammata adaure aringa zuwa Islamiyya kinji?, Tom tace kana yafara kiran suna aka tashi, komai na Deedoh abin so ne, tafiyarta ma abar kallo ce, a fakaice yake kallon ta yanajin sonta na ambaliya a zuciyarsa da ko’ina ma na jikin sa.
Da Ido ya bita, dan harsaidata kamashi yana kallon ta saiya wayence, tana fita taji karan wayar ta.D’an halak Ahmad ne aifa earpiece tasaka tafara waya tana bashi labarin abinda akayi, harda satar Kallon ta da malamin yayi.
Dariya yayi yace, Deedoh is my, ba wanda zai rabamu, kiyimun alqawari duk rintsi kina tare dani?, kuma bayan haka kimun alqawari Idan kika ganni face to face bazaki gujeni ba?
Insha Allah inason ka fa, maizasa nak’ika Indai ba halinka ne bashida kyau ba, Kuma inamaka fatan alkhairi bazan so asami matsala a wajanka ba.
Yauwa matar albarka, nasan kinzo gida bara na barki, nima nafara shirin tawowa wajan sanyin Idaniya ta, hannun sa ya irga kamar tana kallon sa yace nan da 3 days zaizo Kuma insha Allah yana zuwa Indai sin aminta da juna washe gari iyayensa zasu zo.
Tom kawai take cewa, har saukai sallama tashiga gida, batasan ma lokacin da Zahra ta tafi ba, tasan zatasha tsiya wajan ta