KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

@ut@r h@jiy@

[12/12, 9:02 p.m.] ‪+234 809 308 3613‬: KALLON KITSE

°°°°°°°°®NWA°°°°°°°°
©Zainab Y Hussein
Dedicated to Feedoh & ZAHRA Bukar

6⃣6⃣to7⃣0⃣

    9:30am agogon Nigeria da Niger ya buga, a wannan lokacin ne kuma motar Yaya KITO ta danno kan kwanar da zata sadaka da gidan su Deedoh.
  “Yaya KITO saurayi ne matashi kyakyawan gaske wane a wajan Deedoh da Mamansa da Abban ta wa da qanwa ne, suna zumunci daidai gwargwado, bakajin kansu, suma yaran suna k’aunar junan su, wannan kenan.
  Horn yayi maigadi yazo ya bud’e, shiga yayi yasamu waje ya ajiye motarsa sannan ya shiga ainihin cikin gidan, sallama yayi, Deedoh dama taji tsayuwar mota jin sallamar sa yasaka ta fito da gudu oyoyo d’an uwa lallai kacika alqawari waih basa banba sannu kasha hanya?
   Nasha kam, dan da wuri na fito ko breakfast banyi ba, saboda d’okin zuwa wajan ki….. inaa!! badai niba, kace dai zamu taimaki juna nabaka ZAHRA kawai amma maganar kazo ganina bata taso ba

 Dariya yai yace hoo Deedoh kin d’ago jirgi na ashe, to ya kuke yasu Mama banji taba tana ina?, au Mama ta tafi Daura amma yau zasu dawo itada Abba ne ma, saidai Aunty Sady jegal Ita tazo muka kwana tana sama kasanta da bacci, hhhh Wallahi kam to nidai bani abinci kafin afara maganar.
   Acici kai kullum cikin abinci Allah yasa nayi da yawa plantain ce sai yamballs, na had’o ko namaka wani?, haba dai had’o su duka da tea d’in nan mai dad’i, zubo maza nafara bawa cikina hakkinsa
    Tray ta d’akko komai ta had’a masa ta kawo, suna hira yanaci harya gama, bakinsa ya wanke ya dawo yace yuafa zamu fara planing d’in mu, tunda yau Saturday kuma akwai makarantar kinga sai afara koh?
 Eh mana dama yanzu zan saka Adamu jumping ya amsomin d’inki na, yauwa yar gari. Haka ya zauna hira suke harkawo lokacin da akayi Sallah ta Azahar sannan ta tashi tai shirin Makarantar tai kyau sosai ansha make up da takalmi da jaka komai ras haka tafito suka kama hanya.
 15 minutes shine ya kaisu makarantar suna dosa kwanar kuwa akayi sa’a yana tsaye yana kuma fuskan tar hanyar, haba wa wani irin d’aci da firgici ya shiga lokacin dayaga ta tsaya da tafiyar ta juya suna fuskantar juna hira suke akan ZAHRA da yadda yace dan Allah Deedoh ta gayamata yana sonta dariya take tace shi ya fad’a shikuma yana rok’on ta.
  Dariya take tana sane kamar basusan yana gun ba, su Malam Ahmad an shaqa dan kansa jiyayi kamar zai rabe. Lallai dama Deedoh tanada saurayi wahalar sa kawai take?, abin takaici harwani murmushi da bai tab’a gani a face nata ba, yau shi takewa wanccen. KITO ne yace Deedoh kitafi mutumin ki ya shaqa naga sai kallon mu yake kada yazo, tom kasan kuwa lokaci yafara tafiya, bara naje amma tawo mu tafi saikaje k’ofar wajan saika juya. Haka sukai kuwa gaisarshi tai batajira amsawarsa ba tai gaba.
   Kwafa yayi kana yabi bayan KITO da kallo, dame yafi shi wannan amma take sonsa ta barshi, batasan kwana kin nan har rashin lafiya yayi ba?, kuma duk a dalilin ta.
   Lokacin daya fito daga gidan su, a Mota har kusan kuka yayi, dama yayi zaton bazata soshi ba, Idan ta ganshi.Gashi kuwa magana ma ta arziqi bataimasa ba. Shi anasa tunanin fa, shiyasa kodata kira bai d’aga ba, kada tace zatagayamasa bata sonsa ko taimasa rashin kunya. Shiyasa yaji tsoran answer calling nata badan wani abu ba.
   Jikinsa asanyaye ya shiga ajujuwa kafin ajinsu na k’arshe. Test ya raba musu tunda jarrabawa ta kusa, ba karatu saidai bayani Deedoh agaba ta zauna itada ZAHRA magana d’aya biyu ya kalleta amma Ita ko a jikinta, duk da tai missing nasa amma kuma ai ta kirasa bai d’aga ba.
    Har aka tashi basu had’a Ido ba, saidai kallon juna qasa qasa ZAHRA dariya take Idan taga yadda MALAMIN FIQH yake kallon love, dama ya Iya tazata a MALAMIN sa ya tsaya ashe har MALAMIN LOVE ne.
   Yaringa su fita, waih yana zuwa bakin gate yaga KITO acikin Mota bada kayan d’azu ba, ga earpiece a kunnan sa yana tsaye a jikin motar yana karkad’a mukulli murmushi yakeyi azuciyar sa yace Malam Ahmad saika dawo amma fa ya had’u over dole Deedoh ta rikice kallon juna suke babu wanda ya d’auke idon sa har saida Feedoh itada bestyn ta suka fito murmushi suka sakarwa juna kana ta bud’e gaban motar ta shiga ZAHRA a baya kuma

   Ina wuta Malam Ahmad yasaka motar kawai, machine nasa yaja a fusace ya tafi gida, yanajin takaici lallai mata mayaudara ne KALLON KITSE yake mata yaganta mai hankali daidai kai dole ya koma tunda zuciyar sa na sonta amma kuma zata yarda?, ba amsa.
    A Mota dariya suke ganin yau kad’ai yadda yayi kicin kicin yazama wani silent, KITO yace wallahi wannan wataran zai Iya bigeni anya zanci gaba da zuwa?, Haba dai kada kabada maza mana a cigaba game yanzu aka fara, sauke ta yayi kana yatafi kai ZAHRA.
    Lokaci nata tafiya Deedoh suna masa wasa da hankali, abin tausayi harta wa rama ya fara akan yaga ba wata mafaka dazai Iya qara gaya mata, amma yau yayi alqawarin tabbas saiya gaya mata yana sonta har yanzu, yaji maizatace Idan bata amince ba, a yau zaibar katsina ya koma Kano maybe yasamu acan

@ut@r h@jiy@
[5/23, 7:44 PM] @UT@R H@JIY@????????:    KALLON KITSE*
®NWA
©Zainab Y Hussein
Dedicated to ZAHRA BUKAR & DEEDOH YAR FICIKA

7⃣1⃣to7⃣5⃣

   Gama tunanin sa keda wuya, ya janyo wayar sa WhatsApp ya shiga yad’an yi hira har zai sauka saiya tafi wajan sunan ta, dp ya gani yayi mutuqar kyau ka kad’an ba, amma abin takaici itada wannan saurayin ne daya ke ganin su tare, kuma har gidan su yaga yana shiga tunda yana binsu a baya yagani.
    Haushi ne ya kamashi, ganin yadda kafad’arta ta kusa gogar jikin sa, gashi ba mayafi kishi ne ya motsa, status kuwa shine yasaka yayi cilli da wayar gefe

   Kalaman k’auna zalla ta rubuta abin takaici wai da shidai saurayin na kan dp take, leb’ensa ya lashe yana furzar da iska mai zafi, tsam ya mik’e ruwan swan gora guda ya juye a cikin sa, saboda bushewar mak’ogaran ta.

   Cire kayan sa yayi, towel ya d aura sannan ya shiga toilet, wanka ya calla, kafin nan ya shirya cikin wani d’anyen boyel sky blue Ga glass yasaka turarensa ya fesa kansa yasha mayuka masu K’amshi, takalmi d hula iri guda yayi kyau .matuqa key nasa ya d’akko ya shiga mota ya zauna kafin lokaci yaja yatafi
    Su kuma can dariya suke akan yadda suke ganin sa kullum kamar abin tausayi, duk Ita yanzu Deedoh tafara sarewa batason ya wahala tana sonsa itama.
   Saukar makarantar Dala’ilul khairat zasuyi shiyasa hankalin ta duk yanzu ba’a kwance ba, ana ta sabga, gefe guda kuma soyayyar MALAMIN FIQH tana mata katutu a zuciya.
4:00 ya kama hanya zuwa unguwar su Deedoh hankalin sa a tashe yana jin tsoran yadda zai tunkareta tabbas yayi wauta data kirashi dama ya d’auka, haka yayita zancen zuci har ya k’arasa.
   A waje ya ajiye motar sa ya taka da k’afa zuwa bakin gate d’in, sallama yayiwa maigadin amsawa yai sannan yace masa yana neman Feedoh kotana ciki?, anya kuwa naga kamar sun fita amma ka kirata kaji ko sun dawo. Tom yace, kafin yayi wata magana yaji a bayan sa ana hira dubawa yayi ZAHRA ce da Anee Allah yasa basu ganshi ba, Ji yayi suna hira akan yadda bikin zai kasance ZAHRA ce tace Wallahi MK za’a kirawo taiwa Deedoh kwalliya gaskiya zatayi kyau zamusha bidiri, Anee tace ke nifa nagaji da rabon card d’in nan haba, ko gidan masu kayan snacks zuwana biyu yau fa, gashi Ita sunfita da KITO tabarmu da wahala, Huum aike dai ayi shaani kawai a haka suka shige shi.
  Gumi ne ya jikamasa kayan sa innalillah! kardai bikin ta za’ayi?, no bashi bane Deedoh dama mayaudariya ce?, amma kin cuceni duniya da lahira, bakisan nafi wannan gayen son ki ba, nashiga dad’i ni Ahmad haka kuma rayuwa zata juyani?
   Gaba d’aya jikin sa a sanyaye yake haka ya zauna zaman jiran dawowar ta, Insta ya shiga yana duba hotunan ta masusashi cikin nutsuwa.
   K’arar bud’ewar gate dayaji yasashi juyawa itace cikin wata red doguwan Riga ta yane kanta da yellow mayafi tai kyau, da alama ya ajiyeta ne ya tafi, tunda yaji tashin Mota.
    A gajiye take a hankali tafara tafiya tana d’an wulla jaka sama, shikuma tashi yayi daga inda yake ya nufota, bata kallon gaban ta shiyasa bata ganshi  ba illa tashin turaren sa data Ji
  Ido hud’u sukai dashi, dam zuciyar ta ta buga anya shine kuwa?, kara kallon sa tayi, really shine, shima kallon ta yakeyi idonsa akan fuskar ta yana karantar yanayin ta ba k’aramar murna ce ta kamata ba, amma a fuska waskewa tai tazaga ya ta bayansa zata wuce

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Leave a Reply

Back to top button