KALLON KITSE COMPLETE NOVEL

“Cak ta tsaya sakamakon kiranta sunan ta da My Sugar da yayi, bata motsa ba har ya juyo saitin ta, Kallon ta yayi sosai sannan yaja numfashi ya d’ogo
KALLON KITSE
®NWA
©Zainab Y Hussein
Dedicated to Feedoh Yar ficika &ZAHRA BUKAR
7⃣6⃣to7⃣8⃣
“Assalamu alaikum sallama itace first kafin komai, a ciki ta amsa kana ta gyara tsayuwar ta, kansa ya sunkuyar tace Firdausi anawa tunanin ko albarkacin cewa MALAMIN kine ne yakamata ki gaisheni koda baki duba d’ayar alak’ara ba.
Kuma tunda kikaga nazo gidan ku kinsan wajan Ki nazo ba wajan wani ba, tunda ke nasani a gidan. Baki ta tunzuro tace nifa bangan kaba shiyasa ina kwana?
Saidana rok’a ban amsawa kuma kin ganni da wannan idon naki mai kama dana mage, batasan lokacin da tayi dariya ba tace Allah idona ko na Jabo da Auta albarka suda suke gani kamar sunada ido
Anya zan yadda kuwa. Allah kuwa idona yanada kyau, ok amma haka ake tarbon bak’o a barshi tsaye?, hannu tasaka ta rufe fuska tace I’m sorry tawo muje, tafiya tarafa yana bin ta abaya yana yaba yadda yaga take tafiya a nutse a hard’ewa ko wani abu da za’a kushe.
A haka suka k’arasa cikin sitting room bud’ewa tai sannan ta nunamasa kujera a hannu, tace 5 minutes zan shiga gida kaji?, da hannu yamata alama ba komai, murmushi tai tanajin k’aunar bawan Allah a zuciyar ta.
Da gudu ta shiga daidai nan Yaya KITO ya shigo shima, zama tai tana haki tace munci gari yammata
Bamu gane ba?, zayyanamusu komai tayi, waih murna harda tsalle, Yaya KITO ne yace bravo aikin mu yayi amma kinsan kada ki sakar masa fuska kad’an ja ajinki ki
Wah?, tab nakara sakiyar daba ruwa?, wallahi dariya zanyi na washe hakora, zakaban fake advice nakara jawa kaina
Au nid’in kuma?, eh kai fa, hhhhh yarinya zaki k’ara zuwa wallahi saina rama, habadai karame dai ance maka ni zan k’ara yadda musake fad’a?
Munji tashi ki je wajan sa, ko baku ce ba, Anee angama komai?, eh angama Besty Anker Ita sunada test so bazata zo ba, amma tamun transfer ta 10k tace a baki gift. Wow tnq bara nadawo nayimata godiya lallai Anker gaskiya mun more, sauri tai ta d’ebo cake da samosa ta d’ora gorar ruwa da juice ta tafi kaima sa
A kan d’an stool ta ajiye, cup ta d’auka lemon ta zuba masa sanann ta bud’e plate d’in tace bismillah?
Da kallo ya bita ganin yadda take komai a nutse, gashi sai yake gani kamar matar sa ma sukutum, hmm yace sannan yayi bismillah yafara ci.
Yana k’arewa tabashi tissue yana goge hannun ya fuskance ta, yace Firdausi nasan kina tuna abinda yafaru kwanaki, amma inason komai ya wuce muyafi juna ko ni keda laifi ko kece ayiwa juna afwaa kinji?
Kai ta kad’a, sannan yace Deedoh Wallahi kinji na rantse banda abinda nake so a hallita ta mutane na wanann k’arnin bayan iyayena sai ke. Najima ina Dakon son ki, nakasa gayawa kowa ina kishin ki shiyasa kika d’auka tsana ce ko wani abu, ina alfahari a yadda kika sami kyakyawar sheda a Makaranta da unguwar Ku, a kullum burina Allah yaban mace daidai ni, bangantaba banji taba sai akan ki, inafatan bazaki bulan k’asa a ido ba, Idan kuma bakida ra’ayina zanyi farin ciki kin gayan gaskiya
Idan kuma angama komai na bikin ki, fell free kifito ki gayan, amma zanyi bakin ciki Idan har kika furta cewa ankusa auren ki da wani, duk maganar dayake idonsa na kanta.
Kallon sa tai ta gefen ido kana ta juya kanta gefe, tace nifa banmaka komai ba rannan kayi zuciya katafi, kuma nakira wayar ka wajan 10× baka d’auka ba, nayi maka magana a chat ba reply to ya zanyi?
Sakkowa yayi ya tsuguna a gabanta yace, nace bartuna baya koh?, kai ta kad’a yauwa to yanzu sauran magana d’aya ankusa bikin ki ko kuwa?, nifa banda saurayi Allah ma yasani, saurayina d’aya Malam Ahmad shi kuma yayi fushi bayan Ita masoyiyar tasa tana begen sa
Lah to ina d’ayan nan fa, kuma naji ance bikin ki za’ayi tunda har rabon card ake, ni ba wani biki sauka zanyi ta Dalailu fa, kuma Yaya KITO wana ne
Kenan banda rivals?, a kunyace ta kad’a kai, alhamdulillah inafatan yau za akaini wajan Baba mu gaisa gobe na turo iyaye na?
Haba dai yayi wuri, awajan ki ba, amma ni waje na ko Yau a d’aura aban ke, bakisan yadda nake son kiba, shiyasa zakice haka, nan ya zauna yana bayyana mata asirin zuciyar sa, tuntana jin wani iri saigata itama Tana gayamasa yadda take sonsa tunkafin tasan shine, da kuma wani iri datakeji Idan ta gansa
Kaf sun manta da wani nauyi na Malami da d’aliba, sai hira suke, harda tsokanarta yace tagayamasa meyasa Ita bata wankan janaba (, kunsan tamasa wannan tambayar abaya can)
Kanta ta sunkuyar tana dariya ciki ciki, basu Ankara ba, saijin wazifa sukai, basu tashi ba, ZAHRA da Anee sukai sallama
Waih hardasu akasha hira, saiga Malam Ahmad ya ware ya aje malunta gefe yana hira da kawayen budurwar sa, ashe d’an gari ne, KALLON KITSE akewa rogo, suna masa Kallon ustaz ashe kansa a waye yake
Da kyar sukai sallama ya tafi, da daddare kwana cur sukai ana hira, a washe gari yace mata zai koma kano yafara shiri, yana dawowa zaiyi bankwana da ISLAMIYYA da komai da kowa tunda yasami muradin sa
Bayan Sati d’aya
Magana ta zama babba, kowanne b’angare sunyi na’am da kowanne, kuma ba’a saka lokaci mai tsawo ba wata biyu kawai aka saka, lokacin ta had’a saukarta ta Al Qur’an.
Yan Makaranta sunsha mamaki lokacin da sukaji labarin soyayyar su, Malamai duk sunmasa murna, tunda Deedoh mai kyan hali ce.
@ut@r h@jiy@
[30/12/2016 11:32 pm] Re@l @ut@r h@jiy@????????: KALLON KITSE
®NWA_
©Zainab Y Hussein
Dedicated to Zahra Bukar and Fiddausi Jeeboh Deedoh
7⃣9⃣to8⃣0⃣
Ahmad ya koma kano dan shirye shiryen bikin su, lokaci saidai kajirashi badai ya jiraka ba, shiyasa yake shirin sa tun yanzu.
Gidan sa da Mahaifin sa ya gina masa a unguwar Gidado road, gida ne mai kyau, da benen sa, ga gate har biyu baya da gaba, wajan wasan yara ashirye yake, pink da milk shine paint na gidan, ciki ma yayi kyau POP ne a gidan.
Duk inda ake expecting gida mai kyau, to gidan Ahmad yakai, gyaran kad’an ne shima dada kawatawa ne, komai sai sanbarka da fatan mutu ka raba Idan anshigo gidan.
Dangin sa ko’ina suka zauna yaba halin dattako na gidan su Deedoh suke, yadda suka amshe su hannu bibbiyu da fara’a da kayan motsa baki, lokacin da sukaje kai lefe, akwatu set biyu aka kai, kaya ko shugaban mahassada na k’asa baki d’aya ya jinjina bare muda basu bane
Anyi bajin ta, Maman sa baki yak’i rufuwa itama zatayi sirika mai kirki, suna gaisawa a waya dagaji yarinyar zatayi hankali da tarbiyya
Deedoh itama ba zama goma da Ashirin ta had’e mata, ga sauka ga biki, shiyasa bata zama qawayenta sun mata kara, ZAHRA Anee, Meemi itama ba’avarta abaya ba, tunda kawayen su na Kano, ta gaya musu
Gidan Aunty Lubie nan aka tare, anawa amarya gyaran jiki ciki da waje, su ZAHRA ana d’an korawa itama Idan taji bashida karfi abinda akabawa Deedoh
Kullum cikin waya suke, da tsara yadda abin zai tafi. A katsina zatayi bikin ta, sai suma suyi Kano, dinner guda ce zatayi a Kano a Appicent shima Mamansa ta had’a tace yakamata tazo shiyasa amma komai a Katsina gidan kara za’ayi.
Lokaci mai wucewa, gashi yau Deedoh akasata a lalle, a NAGARTA Hole, inda Adamu gwanja ya baje kayan kid’an sa akasha rawa.
Yammatan amarya sunyi Ashobe na wata orange nd blue Atamfa sai roses da suka d’aura, matuqa sunyi kyau Fatima ta annabi itace tazo tai musu make up qawayen amarya kawai.
MK takanas ta taso daga Kano dan kawatawa amarya fuska, k’unshi yar Maiduguri ce tai mata, duk inda ta gifta k’amshi kamar rabon sa akeyi awajen
Ango baizo ba, tunda kamu ne, iyaye duk ana wajan, anyi taro na ranar antashi lafiya sai na gobe kuma, ZAHRA ana mak’ale da KITO Ita tana tsoran yammata shima yana tsoran samari
Washe gari akayi lunch, waih taron writers babu wadda bataje ba, bare Auta ana gaba itada ZAHRA gakuma STYLICH agefe Anee Anker, ana can filin rawa, Aunty Lubie itace kusa da amarya kai anyimata kara dan writers badai kirki ba
Taro yai taro, sautin kid’a ya mik’a amarya harda Ita a rawa, Ango da qyar ya shiga, saida yaga za’a masa taron dangi sannan yafara d’an takawa, liki dai anyi shi, writers ansaki bakin aljihu, ba’ayi mako ba
Rana ta uku, itace akayi dinner, wadda akayi ankon material see green da milk head, kai masha Allah komai yatafi cikin tsari, babu makusa, anci ansha ankuma tafi da na tafiya
A ranar asabar ne aka tafi Kano, dan zuwa wadda uwar Ango ta had’a. Kano ta dabo tumbin giwa koda mai kazo anfika mai Malamai da Attajirai da waliyyai da sufaye, mai Dala da Goran Dutse mai kyawawan mata da maza