YANCIN KI Page 1 to 10

“wata yarinya wace bazata wuce kimanin shekara tara zuwa goma ba, ke kwance a saman cinyar wannan matar ,tana fidda numfashi sama sama tamkar me cutar asma .
kuka sosai wannan matar take hannuta rike da gorar ruwan roba tana shafawa yarinyar a fuskarta, saboda numfashinta dake barazanar d’aukewa daga gangar jikinta .
Cike da matsanancin tashin hankali wannan matar tace “Dan Allah malam ka taka motar nan sosai,” kayi sauri dan Allah mu samu mu isa asibiti nan da wuri ,tun kafin wani abu yasamu yarinyar nan nashiga uku takarasa maganar tana sake yayyafawa yarinyar ruwa ,direban yace “Baiwar Allah gudu fa nakeyi sosai …
ganin numfashin yarinya yayi kasa sosai fiyye da d’azu al’amunta numfashinta na daf da tsayawa ,yasa wannan matar sake yin magana a matukar firgice.
“Dan Allah malam k’ak’ara sauri kar kabari yarinyar mutane ta mutu a hannuna, dan Allah dan Annabi ka k’ara gudu idan yarinyar nan ta mutu zan shiga tashin hankali mara misaltuwa ….
A tsawace direban yace ” what are you saying?
“do you want me to be involved in a car accident because of you ?
“da kikewa wa mutane zancen banza…
“Wayyo Allah nashiga uku “wannan wani irin maseefa ne haka, ke kokari samuna?
“me zancewa iyayen yarinyar nan ?
” me zance yasamu ‘yarsu?
“Dan Allah malam, ba dan halina ba saboda Allah kayi hakuri kayi sauri..
” see I have already gotten to my speend limit, how much did you me?
“da kike kokarin na kashe kaina akan matsalarku ya ja tsaki tare da meida hankalinsa da natsuwarsa kan tukinsa …
Numfashin yarinyar sai sake yin kasa yakeyi gabadaya idanunta sun gama birkicewa yasa matar tace “oh my goodness God have mercy on me “malam ,kindly speend up plz !
Direban yace ” I can’t speend more than this in this area.
cikin zafin rai yacigaba da magana “Oh my God which kind of people boarded my car this morning .
“sai da zuciyata ta gargad’eni akan d’aukarku da zanyi, amman naki bin umarninta “me yasa na d’aukeki da irin me wannan ciwon alhalin ban makance ba ?
“gasky daga yau zan dinga lura da irin mutane da zan dinga d’auka most especial irinki, ko dayake na yi mark din face dinki bama zan sake wautar d’aukarki a motata ba.
Gabadaya matar nan tagama firgicewa ta rud’e iya rud’ewa sai gumi ne ke keto mata ta koina a gabadaya ilahirin jikinta, banda sambatu babu abinda take “, wayyo Allah hummm …am..am “malam Dan Allah karkaji haushina kayi hakuri ka duba halin da yarinyar nan take ciki ,kayi gudu ko dan gudun abinda zai sameta..
“Dan Allah matar nan karki dameni , ki shafamin lafiya mana “ina kan yin iyakacin bakin kokarina ,I can’t kill my self for you..
fly kikeson nayi akan titi ko me ? inji cewar direban .
Muryarta cike da matsanancin kuka tace” bance ka kashe kanka ba, ko kazama tsuntsu akan titi ba ,but at least ka duba yanayin da karamar yarinyar nan take ciki ” karkayi silar shigata maseefa da tashin hankali ,na gaya maka idan wani abu yasamu yarinyar nan karshena yazo, domin zan rasa aikina akanta ” kaga kalli ga wani traffic can gabanmu ..
“Eh nagani me za’a yi da trafic?
” idan kakaraso gurin ka karya hannunka na hagu .
“Na karya hannuna hagu kuma ya tambayeta a wulakance?
Tace “Eh .
shi kuma sanin da yayiwa hanyar bata da kyau, yasa yaki bin hanyar hagu kamar yadda tace yasoma kokarin bin dama.
tasaka wani irin firgitaccen kara “Ina kuma kake kokarin bi ?
” kai da nace maka kabi hannunka na hagu .
“Wayyo Allah ni dai yau nashiga uka nashiga motar wahala , kana bukatar kabi hannunka na hagu ba dama ba ..
” wai me ke damunki ne wannan matar ?
“baki da ido da hankali ne ko me ?
” bakiga hanyar bata da kyau bane dazaki dinga min ihu akai ,wallahi idan kika dameni zan saukeku anan ku nemi wata motar.
” ni dai Dan Allah ka koma Kabi hannunka na hagu idan baso kake kayi silar rasa rayuka guda biyu ba alokacin daya acikin motarka ba..
” yaya kike son nayi I have told you this road is not good yayi maganar a zafafe ..
ihu da masefa take masa ganin yaki sauraronta sai tuki yake hankali kwance, cikin kankanin lokacin taga ya bullo wata hanya wanda yayi daidai da hospital din, take ta sauke wata irin naunayen ajiyar zuciya “yauwa a she dai kasan abinda kake, ga hospital din da zamu shiga can mun iso ta nuna masa da hannunta “ai na d’auka wawa ne kai bakasan hanya ba shiyasa kaji ina ta maka maseefa “kayi sauri tunda mun karaso plz .
“Dan Allah karki dameni da shirmenki din banza da wofi ,ba gashi kokarin danake yi ba kenan, yayi maganar tare da sanya hancin motarsa Cikin harabar hospital.
matar tace “Ni dai ban nemi jin wani dogon turanci daga gareka ba, ka..ka daidaita tsayuwar motar kawai ,gama daidai tsayuwar motar keda wuya ta bud’e murfin motar da sauri tana ihun kiran”doctor!nurse! “Dan Allah malam taimaka ka fito ka d’aukar min yarinyar nan..
dareban yace ” Dan Allah gani nan fitowa karki dameni,” ko ni ne ubanta?
yayinda ita kuma tashiga ihun kiran doctor da nurse jikinta na wani irin kirma ta zame Kan yarinyar dake kwance saman cinyarta, ta kwantar a kujera tasoma yunkurin fitowa tana kiran” hhh uhmm tana ‘barin jikin fitowa da yarinyar ,a daidai lokacin da shima direban ya fito daga mazauninsa har ya bud’e bayan motar yace ” kinga Dan matsa na taimaka miki ,da sauri jikinta na kyarma tabar jikin motar tayi baya .
Direban yashiga kokarin fito da yarinyar yana kai hannunsa jikin yarinyar yaji yanayinnta ya sauya tayi nauyi sosai,yayi saurin cewa ” ai sai matso ki d’auketa kin wani tsaya kamar wata dolowa kina kallon mutane .
jikinta na rawa ta matso tasoma kokarin janyo hannayen yarinyar amman ta k’asa sai kyarma take tana kuka. “ki fito daita man kin wani tsaya kina rawar jiki ko ba yarki bace?
Cikin rawar murya tace “zan d’auketa tana sake kai hannuta amman tsoron ganin yanayin yarinyar yasa ta kasa d’aukarta, ta matsa baya da sauri “shikenan abinda nake gudu ne ke shirin faruwa dani.
direban ya dubeta a matukar firgice “naga alamun kina son sakani cikin tashin hankali ba?
” ,ki d’auketa daga cikin motata ki sallameni na kara gaba neman abincina, ” kayi hakuri abinda nake kokarin yi kenan sai dai bazan iya d’aukarta ba tayi nauyi sosai .
Wani tunani direban yayi kar fa ya tsaya sanya yarinyar tazo ta mace masa acikin mota yashiga uku,wannan tunanin dayayi yasa ya tattara gbdy karfinsa yasoma janyo hannunwan yarinyar ya fito da rabin gangar jikinta yayin kafafunta ke cikin motar “oya kamata mu fito daita .
fito da yarinyar keda wuya, ta dinga yin wasu abubuwa tamkar macijiya yayinda matar nan sai ihu take tana kuka tana kiran sunan yarinyar “NASREEN dan Allah ki rufa min asiri karki mutu “domin idan wani abu yasameki madam bazata barni a raye ba, kuka take sosai tana biye da bayan direban “look at how she curling like a snake may God have mercy inji cewar direban .