Labarai

Ku Karanta Sabbin Dokokin Hada-hadar Kuɗi Da Aka Samar A Nijeriya Da Za Su Fara Aiki A Farkon Shekarar 2023

Ku Karanta Sabbin Dokokin Hada-hadar Kuɗi Da Aka Samar A Nijeriya Da Za Su Fara Aiki A Farkon Shekarar 2023

 

Ga dokokin kamar haka:

 

1. Duk wanda zai cire kuɗi a asusun ATM, iya Naira dubu ashirin (₦20,000) kawai zai iya cirewa a rana.

 

2. Haka kuma Naira dubu ashirin ce kacal (₦20,000) mutum zai iya cirewa a rana a asusun POS.

 

3. Naira dubu ɗari ce kacal (₦100,000) mutum zai iya cirewa a ATM ko POS a cikin sati daya.

 

4. Mafi girman kuɗin Naira za za’a dinga sakawa a dukkanin ATM itace Naira ɗari biyu (₦200).

 

5. Mafi yawan kuɗin da mutum zai iya cirewa a cikin banki wato Counter a wuni shine Naira dubu ɗari (₦100,000).

 

6. Idan kuma wata ma’aikata ce zata cire kuɗin a cikin banki wato Counter, mafi yawan kuɗin da za’a iya cira shine Naira dubu ɗari biyar (₦500,000).

 

7. Dukkanin kudaden da aka samu dalilin mai karfi na fitar da sama da abinda doka ta amince dashi, Tou za’a biya kuɗin processing fee na cirar waɗannan kudaden.

 

Idan mutum ne zai cire sama da adadin ba kamfani ko ma’aikata ba, zai biya kudin kamisho wato processing fee na kashi biyar cikin dari da adadin kudin da zai cire wato 5%.

 

Idan kuma kamfani ne ko ma’aikata, zasu biya kudin kamisho wato processing fee na kashi goma cikin ɗari wato 10% na abinda zai cire.

 

8. Dukkanin kuɗin da za’a cire ta hanyar wani ya baka Cheque wato 3rd Party Cheque na kudin da ya haura naira dubu hamsin (₦50,000) dole sai a kanta za a cire.

 

Wadannan wasu ne daga cikin sabbin dokokin hada-hadar kuɗi da bankin CBN ya fitar.

 

Sabbin dokokin za su fara aiki ne a watan ɗaya na sabuwar shekara (9/01/2023).

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button