Uncategorized

HEEDAYAH 2

 2……

Bayan tafiya that seems endless da kafa suka bullo ta wani titi inda wata mota ke jiransu, nan suka shiga aka ci gaba da tafiya, gaba daya yaran kana ganinsu kasan sun gaji sosai, Heedayah dai har lkcn dabata farka ba, sai kusan goma suka iso wani karamin Uncompleted building, mata da maza ne sun kusa 6 yashe a wani daki da bbu hasken kirki sbda karamin window ne a dakin daga can sama, Nan aka tura su ladi da Heedayah da ta fadi kasa ko motsi bata yi, Wani wanda da alamar shine babba cikin yan bindigan dake wajen yana rike da bindigarsa ya kalli wanda ke gadin mutanen shi ma da bindigarsa a

hannu yace “Ya ku ka yi da mutanan wancan Mutumin a waya?” Ya kalli wanda yake nuna masa yace “Ae kawai bbu alamar xasu bada kudaden nan, sun ma daina daga kiran” Bai rufe baki ba ogan nasu ya harbe Mutumin da ake magana a kai, hakan ya kidimar da mutanen da ke xaxxaune gun, barin matan, sound din harbin ya farkar da Heedayah ta fasa wani ihu tana kokarin mikewa tsaye wata mace dake xaune kusa da ita ta jawota da sauri ta rufe bakinta a jikinta, Ogan ya dinga ma Heedayah wani kallo sannan ya kalli Mutumin gefensa yace “Is she among the kidnapped?” Mutumin ya girgixa kai da sauri yace “Aa yan kauye ne, su hudu muka dauko a kauyen jiya, ba kace ana son body parts ba” Mutumin ya karasa gun Heedayah ya dagota daga jikin matar yana kare mata kallo da kyau, ya girgixa kai yace “Yar wani babba ce wnn, it will have been good she’s kidnapped, but anyway, ana bukatan parts din ma” Yana fadin haka ya turata ta fadi kasa, janye gawar Mutumin ogan yasa aka yi aka fitar waje,   sannan duk Yan bindigan suka fita aka garkame kofar. Ladi ta kankame Zulai ta dinga rusa kuka tana kiran sunan Babarta, wata mata ta mike ta nufesu ita ma tana hawayen, nan ta shiga lallashin su tana kwantar masu da hankali da sauran mutanen wajen, kai kana gani kasan duk karfin halin lallashin nasu suke yi. Matar dake kusa da Heedayah sai kokarin daga Heedayah take ganin kamar suma tayi….. Sai kusan asuba Heedayah ta kuma farkawa, ta mike xaune da kyar tana laluban inda take tace “Ammi??” Jin shiru bbu muryar Mahaifiyarta kamar ko da yaushe sai mutane a kwance tana ta6a su ta janye hannunta da sauri, muryar Zulai taji a hankali tace “Kiyi shiru yar birni yan yankan kai ne suka sace mu, kiyi shiru kar su shigo” Tsit Heedayah tayi da farko, sai kuma ta fasa ihu tana kwala kiran Ammi, wani da ke sallah ya sallame ya taho kusa da ita da sauri gudun kar mutanen su shigo don babu abinda suka tsana irin a dinga masu ihu, karamin aikinsu ne su kasheta in har suka shigo, lallashinta ya dinga yi yana ce mata xata koma gida in sha Allah, ita kuwa sai cewa take “Aa ni a kai ni gun Ammina da Abbana yanxu….” Nan dai ta tada wa enda suka samu bacci aka dinga hiaikin lallashinta a d’an dakin, Cikin kuka take ce masu xata yi fitsari, aka nuna mata wani karamin kofa dake cikin dakin, Ladi tace “Yo ai bata gani” furucin Ladi ya sa duk aka tsaya kallon Heedayah, wata mata ta mike a sanyaye ta kama hannunta ta kai ta bayin. Har aka yi asuba gari ya waye Heedayah shesshekar kuka take a hankali, can ya ta6a matar dake kusa da ita cikin kuka tace “Aunty yunwa nake ji” Matar ta kuma jawota jikinta cikin sanyin murya tace “Yanxu xa a kawo abincin idan Allah ya yrda” sai karfe goma aka bude kofar dakin, duk kowa yyi tsuru tsuru ana addu’a a xuciya, Mutane uku suka shigo ko wanne ya saita bindiga, kamar ko da yaushe facemask na fuskarsu, sai wani mutum da shi ma fuskar tasa ke a rufe dake rike da babban leda me dauke da kananun bread, daga inda yake tsaye ya dinga jefa ma kowa da ledan pure wata daya, ya jefa ma Heedayah dake ta bin duk inda ta ji sound din faduwar bread da ido, Zulai ta mike xata dauka ta bata ya mata wani mugun kallo ta cikin mask din fuskarsa da ke nuna idonsa kadai, jiki na rawa tace “Yo ai bata gani ne” kallon Heedayah ya sake yi, gashi dai fararen idanuwanta a kansa kuma ace bata gani, wani tsawa ya mata yace “Sa hannunki ki dauka da kanki” Heedayah da tayi mugun tsorata ta fara laluben inda xata ga bread din amma bata gani ba don bayanta yake, karasowa yyi cikin dakin bindigar sa a hannu, duk occupant din dakin suka rike numfashi ganin ya nufo Heedayah da ta hakura da laluben inda bread yake ta sunkuyar da kai, dukawa yyi ya dau bread din ya mika mata yace amsa, tana laluban inda yake, ya kamo hannunta ya sa mata bread din, tana kallon direction din da ta ji hannunsa idanuwanta cike da kwalla a hankali tace “Thank you” ajiye mata ledan ruwa daya yyi ya bar sauran bread din  ya mike ya fice daga dakin sauran yan uwansa suka bi sa sannan suka garkame kofar, matar dake kusa da Heedayah ta rungumota hawaye na zuba idonta ita ma, ta amshi bread din ta kunce mata ledan ta mika mata. Zulai da Ladi dai tuni suka handame bread din suna zare ido. Ammi ce kwance gadon asibiti da drip a hannunta, da ido kawai take bin mutanen dake cikin ward din, she looks so sick, Yakumbo na can wani gefe xaune kan kujera tayi tagumi idanuwanta duk a kumbure, wani matsanancin kuka ta saki tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’una, Allah kai kasan yanda xaka yi da axxaluman bayin nan naka, Ya Allah ka rufa min asiri ‘yar Dan uwana ta dawo cikin koshin lafiya, wllh Ita kenan garemu…” Kanwar Ammi dake Ward din ita ma ta fashe da kuka sosai, haka ma sauran mutanen ciki, Mahaifin Heedayah dai na xaune kusa da Ammi yana rike da hannunta, shi ma ko kadan tashin hankali bai boyu a fuskarsa ba, kawai ta maxa yake, Yakumbo ta mike tana hade hanya ta fice ward din kamar xata shide don kuka tana cewa “Shkkn ni dai tamu ta kare, ita kenan gare d’an uwana fa, na cikin ma anyi barinsa sbda wnn tashin hankali, wannan wani irin xalunci ne ake yi haka a duniya ni Khadijah, Allah ka tsine ma duk wanda ya raba mu da Heedayah, Allah ka isar mana, ka dawo mana da ita cikin aminci….” Kanin Abban Heedayah ya mike ya bi bayanta shi ma dai trying hard to control his tears. Kusan la’asar aka bude kofan dakin da su Heedayah ke ciki, ja baya kowa ya dinga yi a tsorace, Heedayah ta mike xaune daga kwancen da take tana kallon inda taji karan budewar kofa, su hudu suka shigo, ko wanne da bindiga, Ogansu na nuna wani matashi yace “Kai taso xaman ka ya xo karshe a nan, Yan uwanka sun yi abinda ake bukata” tashi yyi da sauri yana hamdala sauran mutanen wajen sai hawaye, haka aka fitar da shi, ogan na nuna wani a cikin sauran yace “Kai yan uwanka na raina mana hankali, xuwa gobe idan basu yi complying ba xa mu aika ka barzahu kowa ya huta….” Yana fadin haka ya kalli wanda ke gefensa yace “Cikin yaran nan ka fito da guda daya a cire abinda ake bukata, me siya na kan hanya anjima, gobe da yamma ma akwai me xuwa zai siya” yana fadin haka ya fice, sauran suka bi bayansa, Mutumin daxu da ya kawo masu bredi ne kawai bai fita ba sai wanda aka sa ya dauko yarinya daya ya dinga bin yaran da kallo, Mutumi dai mai bredi ya nufi Zulai ya dagata ya fice tana ihu tana sakar masa fitsari, d’an uwansa ya bi bayansa ya garkame kofar, bbu abinda mutanen cikin dakin ke yi banda hawayen tashin hankali, Heedayah ta dinga waige waige jin ihun Zulai, matar dake kusa da ita ta rungume ta tana kuka sosai, cikin kuka ita ma tace “Aunty ina xa su kai ta??” Matar dai bata ce mata komai ba sai kuka. Washegari har kusan yamma basu samu an kawo masu bredin ma da ake kawo masu ba, Heedayah ta fada ma matar kusa da ita tana jin yunwa ya fi a kirga tun matar na ce mata xa a kawo abinci har ta gaji ita ma tayi shiru, kusan la’asar aka bude kofar wajen, mutumin da ke basu bread ne ya shigo da buhun bread da ruwa, nan duk ya jefa ma kowa, har bread din ya kare amma bai ba Heedayah ba, matar dake kusa da ita har xata yankar mata nata, Mutumin ya karasa ya daga Heedayah cikin kaushin murya yace “Mu je ki amshi naki” cikin rawan baki matar tace “A’a ko in yankar mata a nawa ba cinyewa xan iya yi ba, baxan ma ci ba….”  Wani mugun kallo ya dinga mata hakan yasa tayi tsit jikinta na rawa, juyawwa yyi ya nufi kofa da Heedayah dake ihu tana kiran Ammi tana gatsa masa cixo a hannu, bayan ya fita ya rufe kofar, ya toshe bakinta yace “Ke xan halbe ki yanxu idan baki rufe min baki ba” Tsit tayi ko ina na jikinta na rawa tana kallonsa kamar dai tana ganin fuskarsa, xagawa yyi ya canxa hanya yanda sauran yan uwansa dake xaune a baya baxa su gansa ba, cikin hanxari ya karasa bayan wani karamin bukka da suke ajiye makamansu ya ajiyeta bayan Bukkar ya durkusa yana kallonta yace “You don’t move, ki tsaya nan har in dawo idan ba haka ba, I have gun….” Kai kawai take gyada masa a tsorace tana komawa baya, ya mike da sauri ya koma inda Yan uwansa ke xaxxaune ana xuke xuke ana buga karta, Makullin mashin dake rataye jikin bishiya ya dauka yace “Xan je amso ruwa in dawo yanxu….” Wani daga cikinsu ya kallesa yace “Oga na hanya da customer fa” yace “Ehh yanxu xan dawo ai” har ya nufi gun da suke ajiye babur dinsu sai kuma ya juya da sauri ya sake komawa dakin da ya dauko Heedayah ya bude ya shiga yana masu wani kallo yace “Ko da an tambayi yarinyar nan kuce ta mutu an fitar da ita….” Tsuru tsuru suka yi suna kallonsa ya juya ya fita ya kulle kofar. Daga haka ya nufi machine ya hau ya tada, a guje ya bar wajen, dai dai inda ya ajiye Heedayah ya tsaya, sai xare ido take tana kalle kalle, ya daga ta ya daura gaban machine din yyi speed off, gudu kawai yake a dajin kamar mai race din motorcycle, tafiyar kusan awa daya da rabi suka yi suka shigo cikin gari sosai, a hankali yake tafiya yana kalle kallen jama’ah dake ta kokarin rufe wajajen sana’arsu kasancewar Magrib ya gabato, sai kuma ya tsayar da machine din ya kashe, sauke Heedayah da tashin ta bacci kenan yyi, ya ajiyeta nan gefen hanya yana kallonta, laluba wajen ta shiga yi, jin ya sake kunna bike din da sauri tace “Noo, Are you leaving me??” juyar da Machine dinsa yyi ya dau hanyar da ya fito with speed, ta fashe da kuka sosai tace “Noo”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button