NOVELSUncategorized

KUNGIYAR ASIRI 19-20

MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)

REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)

????19-20

      Duk abinda na faɗa ki maimaita,”yu tun daga asibiti ban sake tuna komi baa,banji komi ba haka ban tuna komi ya faru a babban gida baa,sashin hajia lanti zuwa sashin hajia mariya,kawai naga jini ya ɓalle mun ne!, Ta maimaita.


Tashi muje kiyi wanka,”haka ta miƙe tana biye da ita a baya kamar raƙumi da akala har suka fito a tare zainaba ta shige ban ɗaki,sanan ta koma ciki ta adana komi a muhallin shi ta fito tare da mai da wardrobe  ɗin daidai yadda ba za’a gane akwai wani abu a wurin baa.

zainab ta buɗewa kanta shower cike da zafin nama domin wani ƙarfi take ji yana shiganta!,ta jima tana chuɗa jikinta sosai daga bisani ta ɗauraye jiki tare da tsuggunawa domin tayi tsarki,sai taji hanunta ya ɗauki ɗum,dubawan da zata yi ai kuwa hanun dumu dumu da jini. Wani irin faɗuwar gaba da Mamaki ya ziyarci zuciyarta domin idan ta rasa wanan ciki tamkar ta rasa rayuwarta ne!,” wanan kuma jinin menene?”,ta tambayi kanta!.  Iya saninta dai tunda suka samu saɓani da muhammad  akan ɓatan mami da rana ta fara jin ciwon mara mai tsanani har aka kira likita ta dubata daga nan bacci ya kwashe ta,jinin menene kuma ya dawo mata a wanan dare data kasa tantance ko ƙarfe nawa ne,ina muhama ɗin da mami?.

Tarin tambayoyi ne fal cikin zuciyarta amma ta rasa wanda zata tambaya ya bata amsa,haka dai ta fito…

Hajia mariya na zaune gefen gado sai istigfari take cikin zuciyarta ga wani faɗuwar gaba na musamman ke taso mata duk lokacin data tuna abunda ta aikata!,ganin fitowar zainab yasa tayi saurin miƙewa tana mata sannu ya jiki?,ta amsa babu abunda nake ji a yanzu.

Allah ƙara tsare gaba ai ciwon mara babu daɗi gashi kin sha bacci tun kafin azahar,likita ta hana a tayar dake wai sai kin tashi da kanki. Barin baki abun sallah da riga ki sauya ko?.

Ɗan jimmm tayi!,kanta na ƙasa tace,”hajia inaga akwai matsala domin jini ya tsinke mun!”. Innalillah wane irin magana ce haka zainab?,bayan an duba ki an tabbbatar kina cikin ƙoshin lafiya har abunda ke cikin ki?.

Wallahi hajiabda nake wanka naga jini sosai”ta sake faɗa wanan karo muryarta ya soma rawa kamar zata yi kuka dokin ta karaya ƙwarai”.

Ai kuwa bamu ga ta zama ba karfe nawa ne yanzu sai a kira muhama ɗin a waya mu koma asibiti likita ya duba ki da kyau!. Ɗaga kai zainab tayi tana kallon agogon bango(da yake akwai wadatacen haske a ɗakin),karfe biyu da rabi ma dare.

Hajia dare yayi sosai da an haƙura har da asuba sai mu tafi koda driver ki ne…,’aa zainab wanan ba ƙaramin magana bane ya zama dole mijin ki ya sani kuma a tagi asibitin tare dashi ayi komi gaban shi gudun zargi.

Hajia bata san zainab fushi take da muhammad  baa,domin shine sanadin shiganta wanan hali ace mai leƘo sashin ya duba ta baa!,kenan bai damu da cikin ba saboda yana da mami.

Kinyi shiru zainab?,hajia ban iya tafia yanzu jiri ke ɗiba ta da anyi hakuri ha r da safen.

Shike nan shiga zainab ki duba chest of drawer akwai pad ki saka sai  ki kwanta  Allah ya inganta yasa rabo ne.

Idanu cike da hawaye ta nufi inda akace ta ɗauka sanan ta wuce ban ɗaki domin tsaftace jikinta…,nan take hajia mariya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da gode wa Allah da yasa zainab ta manta da komj da kashin su ya bushe.

Kasancewerta mace mai mugun wayau yasa ta ƙirƙiro dibarar nan na zuwa asibiti tare da muh domin komi ya koma can tsakanin su da uwar shi.

Daga zainab,hajia mariya zuwa Muhammad a daren ranar basu samu wani baccin kirki ba!,banda hajia lanti da duniya ta koma mata sabuwa a ganinta taci galaɓa akan hajia mariya,nata burin ya cika na salwantar da abunda ke cikin zainab da rayuwar taa,ga mami a ƙarƙashin kulawarta sai yadda ta juyata domin yarinyar na tattare da wata baiwa na musamman da ba kowa zai iya ganowa ba sai ire iren su tsofin yan
ƘUNGIYAR ASIRI!.

Kiran sallar asuba  a kunen zainab,tana jin motsin hajia mariya ta tashi zuwa sallah itama ta nufi ban ɗaki domin tsaftace jikinta..,wanan lokacin jinin gunduwa gunduwa yake faɗowa har da kitse kitse abun babu kyaun gani.

Wasu hawaye masu zafi suka wanke mata fuska,duk da bata taɓa yin ɓarin ciki ba amma ta san banbancin jinin haila da wani jini na daban.

Tana tsarki tana kuka wanda yaci ƙarfin ta sosai domin ta riga ta cire rai akan wanan ciki da suka ƙallafa wa rai daga ita,mijinta har yan uwanta da har yanzu bata samu magana dasu.

Sai data yi kuka mai isanta sanan ta watsa ruwa ta fito domin ta canza pad,wanda ta saka ya lalace sosai. Tana shiri ne taji sallamar hajia mariya wace ada alama waya take yi..,sannu zainab ya jikn?,da  sauri ta zube a ƙasa,”da sauƙi sosai”,Allah baki lafiya yanzu na gama magana da moha ɗin gashi nan shigowa sai ki shirya domin nan gidan ya kwana ashe.

Uhm kawai tace tana ƙoƙarin miƙewa ta shirya..,hajia ta koma palonta tana jirar fitowar zainab ɗin.

Moha na  zaune a palon maman shi cike da tunani iri iri domin yayi wai irin mumunnar mafarki akan zainab ɗin shi!,sai ga kiran hajia mariya ya shigo..,bayan sun gaisa ne take mashi bayanin halin da zainab ta kwana ciki nan take ya shga ruɗani!.

Bai tsaya jiran fitowar hajiyar shi ba ya figi makulin motar shi tare da kama hanyar sashin hajia mariya…,da sallama ya shiga wanda yanayin shi a burkice yake sai zaran idanu.


Jin su take a palo yana tambayar ta ,ai kuwa tayi banza dashi!,har cikin ɗakin ya biyota…,tana zaune bakin gado ta haɗe kai da gwiwa.

A hankali ya taka tare da zubewa bisa gwiwowin shi,jike a mace ya kwantar da kanshi a bayanta tare da amfani da hanun shi ɗaya yana shafa kanta a hankali..,kamar jira take ai kuwa ta fashe da wani irin marayar kuka a hankali!,zee ta”shiru ya biyo baya domin bai san da wani irin kalma zai amfani wurin rarashin ta ba”,ga mijin ki mai matuƙar ƙaunar ki a gaban ki duk hukuncin daya dace ki yi a kanshi!.

A zafafe ta miƙe tsaye tana huci kamar wata mai iska!,”ƙasa ya faɗi daɓas yana kallonta a tsorace…,langwaɓar da kai yayi gefe ɗaya alamar yayi nadama.


Hajia mariya ta katse yanayin dasu da sallama”a’a har yanzu baki kintsa baa?”

Share fuska tayi,na gama hajia!,haka suka fita jiki a sanyayye…,yaso kwarai hajia ta bisu asibitin amma ta rinka kawo uzuri iri iri.


Har suka isa asibiti babu wanda yayi magana a tsakanin su,nurse ta tambaye ta abunda ke damun taa?,yadda abun ya fara tayi mata bayani!. Nan take aka kai ta dakin hutu..,koda akayi ya nuna cikin ya fita wanda dama dai a wajen mahaifa yake(ectopic ),akwai ragowar datti a cikin ta haka ya basu daman ganin ya kamata ayi mata wankin mara.


Bayani suka yiwa muhammad cikin ya lalace sai dai suyi hakuri!. Wani irin ɓaci rai ya ziyarci zuciyar shi nan take domin yaci ma wanan ciki ALLAH kaɗai ya sani.

Zainab tun data ga anata safa da marwa a kanta kawai ta tsinke da lamarin haka kawai taji zuciyarta ba daɗi sai hawaye wasu na bin wasu ba kakkautawa….

Umurtarta akayi ta hau wani gado ta ɗaga rigart,ga wasu ƙarafuwa ana shiryawa saman tray..,kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata sosai domin ta tabbatar zarginta gaskiya ne cikin ya lalace!.

Ganin an ɗauko wani ƙarfe kamaf ƙugiya yasa ta zabura ta miƙe zaune!,cikin rarashi nurse ɗin tace;kiyi hakuri madam wanan abun da zan maki shike kawai samun sauƙin ki domin idan ban kwashe jinin da sauran dattin ba zaki yita fama da ciwon mara da kuma zuban jini!.

Me ya same ni waist?”shine tambayar data watsa ma nurse ɗin!”,ɓarin ciki kike yi shine sanadin zuban jinin da kike gani.

Hawaye ne kawai ki fitadaga idanunta nurse ɗin na rarashinta har aka fara cike da dauriya sosai aka kamalla aikin.

Wurin muhammad  suka koma ska faɗa mai bill sai maguguna ds zaa saya da allurai domin ta samu isashen hutu mahaifar ya huta.


Tana dai kwnce abun duniya ya cika mata zuciya har aka gama komi aka salame su ya shigo inda take..,bata kula shi ba kawai ta gyara rigarta da hijab ta fice waje tana tafiya aƙasa..,da saurin ya biyo ta”ina zaki zee?”,gidan iyaye na ta bashi amsaa gdarance!.


Faɗuwar gaba ya ziyarce shi!,kiyi hakuri zainab mu koma gidan mu sai mu fahimci juna kinji?,bazan tɓa koma wa gidan ka ba muhammad ya zama dole ya sawaƙe munwanan ƙadararren auren naka!,ayi zuria kamar arnan farin?,ba mami babu labarin taa,ɗan cikin da ALLAH ya bani anyi sanadin lalacewar shi tsakanin ƙarya da gaskiya!. A’A wallahi na gaji.


Zainab kiyiwa girman Allah mu tafi gida a warware wanan matsala…,muhammad  babu inda zan tfi sai gidan mu!.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button