NOVELSUncategorized

KUNGIYAR ASIRI 17-18

REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)

Masoya wanan littafi ina ganin saƙonin ku,comments da addu’oi ina maku fatan alheri,Allah saka da alheri ya bamu ikon ɗaukan darussan dake cikin littafin,munanan abubuwan dake ciki Allah bamu ikon ƙyamatar su ya kare musulunci da musulmai a duk inda suke a faɗin duniya amin❤ 


????17-18

   
            Huci hajia Mariya ta shiga yi zuciyarta na tafasa kamar an rura mata wuta a ciki!,tabbas hajia lanti ta gama da ita domin zai wuya ta samu cikar burinta a wanan karo!.

Me kike tunani hajia mariya?,inace ni ɗin ce dai ku ka ɗauki tsawon shekaru talatin kuna musguna wa?,ko kin manta lokacin da na shiga irin wanan hali,a ƙasƙance ina neman agaji a wurin ki,saboda tsabar butulci kika ƙeƙashe ƙasa a ta fau sai kin aiwatar da mugun nufin ki a kai na,wani irin magiya ne ban maki ba a lokacin?.

Yanzu lokaci yayi da zaku girbi abunda ku ka shuka”cikin ɗaga murya take magana”,ita zainab ɗin da kike nan nan da ita,wallahi da tasan mugun nufin ki a kanta ba zata taɓa tunkarar inda kike ba,domin kece musababbin shigar wanan ahalin 
QUNGIYAR ASIRI.

Lokaci yayi da zan fallasa komi kowa ma ya sani idan yaso zuri’ar ta tarwatse kowa ya kama gaban shi!.

Girgiza kai hajia mariya ta shiga yi”kada ki mana haka lanti!,kada ki manta alƙawarin da kika ɗauka zaki riƙe sirrin mu har ƙarshen rayuwar ki”.

Ke ɗin nan har kin san ALLAH da girman ALƘAWARI?,babu sauran imani a zuciyar ki domin a bushe ta ke ƙeƙas ,duniya kika saka a gaba,baki tunanin akwai ranar da zaki mutu a saka ki cikin kabarin ki kowa ya watse a barki daga ke sai abunda kika shuka!.

Zaɓi ya rage naki,idan har kin yi alƙawari ba zaki sake shiga tsabgata dana ahali na ba kamar yadda mijin ki ya zuba mun ido,zan cigaba da riƙe maki alƙawarin ki har ƙarshen rayuwata.

Shiru tayi na ɗan lokaci zuciyarta cike  da baƙin ciki akan rashin nasara da tayi a karo na farko tun da suka fara karawa da hajia lanti!,shike nan na aminta amma ki kyale zainab da ranta kada ki cutar da ita,bata maki laifin komi baa.

Mariya barin zainab a raye babban barazana ce a gare mu baki ɗaya,ta riga ta san sirrin mu wanda muka daɗe muna ɓoyewa,shi yasa na zuba guba a jikinta a hankali zai rinƙa cin ta har ta mutu!,shi abunda ke cikinta sai idan ana haihuwa a lahira tayi a can domin na riga na ba dodon tsafi na ya cinye!.

Yadda jariri yake sabon jini fal, haka zan koma kamar wata yar sha shida!,
Wanan shine sirrin kyau na hajia mariya ko kina ƙoƙonto ne?.

Duk naji wanan amma don Allah kiyi wani abu akan zainab ta tashi koda ace zaa daburta ƙwaƙwalwarta ta manta duk abunda ya faru a yau ne ,in har zata tashi babu matsala.

Sanin kanki ne hajia mariya bamu tayar da mutum haka nan dole sai an kawo mana ƙaramin yaro a bawa dodo jinin shi yasha ranshi zai zama fansar a gareta.

Girgiza kai ta shiga yi…,ki duba lamarin nan dai yara suna waje suna jiran fitowar mu,idan aka same ta cikin wanan hali zargin su zai ƙarfafa a kan mu,ina maganar abunda zai yiwu yanzu ne!.

Abu ɗaya zan iya taimaka maki dashi yanzu shine,in bata jini na tasha nan take zata tashi amma ki sani da zarar  jinin yabi jikinta zata iya tsintar kanta a irin halin da nake ciki a yanzu!.

Ban aminta baa!,domin bana burin wanan muugun abu ya cigaba da yaɗuwa a cikin zuri’ar gidan nan.

Ɗaga kafaɗa tayi,yanzu ai ya rage naki duk shawarar da kika yanke ki same ni  a inda ya kamata kuma a lokacin da ya kamata ina fatar kin gane?,shiru tayi mata.

Wasu irin surkule ta shiga yi nan take hanunta ya dawo dai dai har jikinta kamar babu abinda ya faru a sashin sanan ta nufi hanyar fita hajia mariya na zaune a ƙasa tana kallonta.

Tana buɗe ƙofar yaranta suka taso mata fuskokin su ɗauke da alamar tambaya,”ku kwantar da hankalin su zainab na cikin ƙoshin lafiya domin likita yazo ya dubata bacci take yi”.

Ajiyar zuciya muhammad  ya sauke,sauran ma suka shiga hamdallah ana faɗin”saura mami”.

In shaa Allah itama zaa ganta kada ku ɗaga hankalin ku,muje kuci abinci ko?,muham dai hankalin shi bai kwanta ba tunda bai ga zainab da idanun shi baa.

Sama sama dai suka ci abincin jikin ko wanne a sanyayye baa wani jima ba suka mata sallama banda muhammad  wanda bai san inda zai nufa baa.

Sai da hajia mariya ta tabbatar hajia lanti ta fita sanan ta rufe ƙofar ɗakin gam ta janyo zainab wacce take kwace  kamar matatta zuwa wani  ɗan lungu bayan wardrobe  a cikin ɗakin wanda ba kowa ne yasan dashi a wurin ba. Sai data janye wardrobe  ɗin ta shige da ita lungun wanda ke cike da duhu,kwantar da ita tayi saman wani akwatin katako,gefe ta janyo wani babban riga ja kamar abaya mai hula ta saka yadda ba a ganin fuskarta,wani babban ƙwarya ta ɗauko da ƙahon saniya ta ɗaga sama sanan  ta fara maganganu cikin wani yare a hankali,a hankali har ta fara ɗaga murya!! nan take haske ya bayyana jikin bango nan  hoton mami ya bayyana tana ɗaure jikin tsaunin ta fita hayyacin ta.

Daka mata tsawa tayi”ashe ban faɗa maki kiyi nisa da ahalin ki baa,ya akayi kika zo nan!?”,kuka ya kwace mata…,magana zaki yi domin bamu da isasshen lokaci,dubi halin da mahaifiyar ki take ciki a dalilin taurin zuciyar ki!.

Duk maganganun nan da hajia mariya keyi kanta na rufe da hula yadda babu wanda zai iya ganin fuskarta bare a gane itace.

Mami na ɗago fuskarta da ƙyar sai kan mummynta dake kwance kamar gawa!,ihu ta fara tana fizge fizge amma ta kasa kwance wa..,bamu da isashen lokaci ya zama dole ki bar wurin zan kula da mahaifiyar ki amma dole sai an sadaukar da rai domin ya zama fansa akan nata rayuwar da tsiratar dake cikin asiri ta yadda ba zaa taɓa gano inda kike baa,mun rasa cikin dake jikinta ba zan bari ta rasa ranta ba duk da ban taɓa shan jinin kowa ba amma zan fara a kan zainab domin ceto rayuwar taa.

Kuka kawai mami keyi cike da takaicin kanta domin ta ɓata biyu ɗaya bai gyaru baa!.

Ki zauna cikin shiri anjima da dare zan gabatar da duk abunda ya kamata,dana kamala zaki tafi da father john idan kika sake dawo wa rayuwar ki zai kasance cikin hatsari babba babu ruwa na!.

Cikin ƙarfin hali ta furta”godiya nake ya shugabata”,ba zan taɓa manta irin dumbin alherin ki agare ni baa duk da har yau ban san ke ɗin mutum ce ko aljan baa,haka ban san dalilin ki na taimaka mun ba.

Wanan ba damuwarki bane kawai ina taimkon ki ne domin cikar nawa burin!.

Tunani mami ta shiga yi yadda ta tsinci kanta a wanan jejin;
Bayan shugabatarta ta ɓace ta zauna cikin wurin tana saƙa da warwara yadda zata ceci mummynta kafin ta bar garin…,kawai taji anyi wuf da ita idanun ta sun rufe sai duhu take gani kamar makauniya har aka iso jejin aka ɗaure taa!,sai da wurin yayi shiru babu motsin kowa sanan ta iya buɗe idanunta amma wayam ba kowa kuma ta kasa ƙwatar kanta a wurin!

Surkulle hajia mariya shiga yi bangon ya shafe ta cire kayan sanan ta bar zainab a ciki ta fito tare da rufe wurin yadda babu wanda zai gane akwai wani a ciki.

Cikin ban ɗaki ta ɗauko mopper ta goge wurin da jinin zainab ya ɓata,ta feshe ɗakin da turaren ɗaki sanan ta saka babban hijab ta buɗe kofa ta nufi palo…,mai aikinta ta sama ta gama jera abinci duka.

Ki shirya yanzu driver ya aje ki gidan hafiza zaki kwana can da safe zai dawo ya ɗauko ki!.

Tau hajia ta amsa tana mamakin wanan fita da aka shirya mata da rana tsaka!,barin kai wa maman mami abincin ta ɗaki.

A’a bta tashi daga bacci ba,idan kinci naki kawai ki shirya,”tana gama magana wuri ta samu a palon ta zauna tana daddana waya”.

saƙo ta turawa babbar ɗiyarta hafiza kamar haka;
driver zai kawo mai aikina ta kwana wurin ki kuma bana son dogon bincike sai anjima 
tana turawa ta kashe wayar gaba ɗaya.

Zuciyarta cike da saƙe saƙe domin yau zata aikata abunda bata taɓa aikatawa ba a rayuwarta!,ba wai don bata iya bane kawai sai don bata ra’ayi amma ya zama dole ta dubi zainab da mami.

Yau duk wanda ya kalle hajia lanti zai gano tsantsar farin ciki da take ciki domin burinta ya fara cika akan zainab!,bata da wata matsala a rayuwa da ya wuce zainab da abinda ke cikinta,idan har zainab na raye ba zata taɓa samun biyan buƙata ba domin ta kasance mace mai yawan ibada,zai wuya ayi galaba a kanta?,tsatsson zainab zai kasance rufin asiri ne a gareta sai akayi rashin sa’a zainab nada bin ƙwaƙwafi da taurin kai ga ibada wanan dalili yasa namanta da abunda zai fito daga cikin ta zai zamto mai ɗaci a gareta!,cin nama mai ɗaci a gareta na nufin wargajewar duk wani shiri nata!,abunda yasa tayi tasiri akan mami saboda ba jinin zainab bace kuma muhammad  ya sauƙaƙa mata duk wani aikinta ta hanyar sagarta mami ,hakan ya bata daman cusa ƙiyayya mai ƙarfi a zuciyar mami wanda yasa bata burin shan inuwa ɗaya da mahaifiyarta!,bata burin garin farin cikin mahaifiyarta!,burinta kullum ta ganta cikin baƙin ciki da tashin hankali!.

Lokaci yayi da zata rama abunda hajia mariya tayi mata a lokacin baya koda hakan na nufin tonon asirin su gaba ɗayan  ne!.

   Mai aikin hajia mariya ce ta fito cikin shiri..,ƙasa ta zube”na fito hajia”,sama da ƙasa ta kalle taa. Idan kin fita ki turo mun driver.

Fita tayi, zuwa can driver ya shigo da sallama.
Gidan hafiza zaka kai ta daga nan ka tafi maraba inda ake gasa kifin nan ka samo wa zainab.

Hajia ai akwai masu yin irin shi a nan bakin kasuwa…,bana son na wurin a maraba zaka tafi ,inace dai nike da mota kuma biyan ka albashi nake yi ko?, Allah huci zuciyar hajia zaa yi yadda kike so.

Tashi yayi ya fita…,sai data tabattar ya wuce an fara kiraye kirayen sallar magrib gidan yayi shiru maza sun nufi masallaci,ta ɗauki niƙab da makulin wata ƙaramar motar ta shiga tare da bata wuta babu kowa a gate don haka a buɗe yake ta fice…

Motar  data saya wa jikanta na farko nee a nan gidan yake barin shi sai ya shigo yake fita dashi yaron bai wuce sha shida baa,mahaifin shi ya nuna rashin amincewa da kyautar motar a cewar shi yaron yayi ƙarami ina laifi ya kamala secondary school,sai ta aje a wurinta aka mashi tintec idan yazo wurinta yana shiga ya tafi yawo

Jabi ta nufa har ciki irin  gheto area ɗin nan  ta nufa a guje take sharar gudu yadda zata dawo da wuri…,ba’a jima ba ta isa har cikin wata anguwa da tasan akwai yara sosai,ta samu gefen hanya ta parker tana kallon yara suna wasan su.
Sun fara watse wa ne  ɗaya yazu giftawa ta wurin motar,da sauri ta buɗe ta fito tare da chafko shi sai  cikin motar ta rufe, a zafafe ta zaga gefen driver ta zauna  yaro na ihu amma babu mai ji saboda tintec ce kamar walƙiya ta bar wurin!.

Ganin yaron bai bar kuka ba ta buɗe aljihun motar ta fito da wani mai ta shafa mai a fuska nan take yayi ajiyar zuciya tare da ɓingirewa sai bacci har ta isa gida lafiya ba matsala.

Cikin sauƙi ta samu nasarar shigowa cikin gidan har wurin aje motoci babu kowa, ta sungumi yaron ta saka cikin babban hijab ta rufe motar tana waige waige sanan ta nufi sashinta da sauri kada wani ya ganta….

Har inda ta ajiye zainab bayan drawer   ɗin ta adana shi ciki sanan ta fito.

Hankalin ta kwance buƙatar ta zai biya,zata yi amfani da ƙarfin tsafin su ta dawo da zainab domin galabaita tayi yasa tayi dogon suma gubar na cin jikinta a hankali,aƙalla zata iya ɗaukan kwana biyu kafin ta mutu. Wanan ritual ɗin da zata yi da taimakon wasu shugabanin ta zai dawo da zainab cikin hayyacinta cike da ƙuzari.

Wa’iyazubillah!,saboda neman duniya kana ji kana gani ka zama mushiriki/mushirika!,duniyar da za’a mutu a bari menene na zari ko haɗama?,idan dukiya kake nema anyi ƙaruna wanda ya fika dukiya da shahara a duniya baki ɗaya!,amma ƙarshen shi bai yi kyau ba daga shi har dukiyar nashi!,idan mulki kake nema,anyi fir’auna wanda shima ya ƙare a wulaƙance!.Idan muka zaunamuka yi nazari,duba da dalilin da yasa Allah ya hallice mu sai kaga ɗan adam ba a bakin komi yake baa,wanda yafika daraja da ƙima a idon ubangiji ya bada baya ya bar duniyar kai me kake yiwa haɗama da neman dukiya kota halin yaya?,wata rana mutuwa zaka yi ka bar duniyar da abunda ka tara!,cima zauna su taru ayi wawason dukiyar da ka gama wahala da saɓawa ALLAH wurin tara ship!,baka ci ba sanan baka yi tanadi mai kyau na haɗuwa da ubangijin ka baa.Allah ya shirya mu akan tafarki na gaskiya amin.

   Sai da dare ya raba sosai bayan hajia mariya ta gama duk wasu abubuwa da ta saba na al’adanta sanan ta rufe sashin gaba ɗaya wanda ita ɗaya ke ciki sai abubuwan data ɓoye.

Wurin da su zainab suke ta buɗe ta shiga tare da saka rigar nan ja da ta saka da rana,ta ɗauki ƙwarya da ƙahon tare da fara surutan data sama a hankali..,a hankali har ta shiga ɗaga murya nan take haske ya bayyana jikin bangon wurin ya ɗauki haske kamar lantarki!.

Hoton mami ne ya bayyana tana nan cikin halin da take a ɗaure!,kirari hajia mariya ta fara yi cikin yaren yarbanci wanda ta daɗe sosai tana yi kamar ba zaa amsa mata ba sai ga wani tsoho kutuf ya bayyana a ɗaya bangon riƙe da sanda.

Bukatar ta ta zayyano mashi cikin harshen yarbaci tana jaddada mashi muhimmancin samun nasararta a wanan lokaci koda zai zamto sanadin bankaɗo duk wani sirrin ta.

Girgiza kai ya shiga yi cike da jimami daga bisani ya ansa mata;

Kin yi sake sosai mariya da har kika bari lanti taci galaba a kanki!,har guda nawa take?,inace kece kika reneta har ta kawo inda take?,mai zai saka ki karaya ne?.

Zaa yi aikin nan yanzu kuma zaa dace  zan tafi da yarinyar nan,amma fa dole ki fallasa wanan sirri da kuka daɗe kuna ɓoyewa idan ba haka ba kinabiya rana rayuwar ki a kowa lokaci nan kusa!.

Na amince ya shugaba na!, ayi koki nayi alƙawarin zan fallasa komi a gaban kowa!.

Yaron ta cicciɓo sama tare da duƙar da kanta mami dai nagefe tana kallonikon ALLAH ,ya fara surkullen shi cikin yaren yarbanci tana amsawa har aka ɗauki lokaci sanan ta ɗauko ƙahon nan ta datsa wa yaron a duburar shi nan take jini ya fara fartsowa ta dama ƙwaryar nata ƙasa!,jinin na zuba ciki yaro nata kakarin mutuwa har yayi shiru.

Sauke zainab tayi gefe tare da shafa mata jinin a cikinta,ƙírjinta da kuma saman kanta!,saura ta watsa a bangon inda hoton mami yake,sai igiyar ya kwance tsohon nan ya buɗe hannuwa idanun shi rufe mami ta dawo jikin shi yana cigaba da surutai wanda shi da hajia mariya kawai suka san me yake faɗa.

Yaron data ɗaua yanzu saman akwatin tsohon ya makawa sandar hanun shi duka su ukun suka ɓace bat!,ya rage daga zainab sai hajia mariya.

ba’a daɗe ba kuwa ta buɗe idanun ta tas tana kallon hajia mariya wacce bata gane ko wacece ba kuma a ina take.

Idanu ta wre sosai tana kallon zainab domin ta ɗaga hular,zainab ma tana kallonta amma ta rasa tuna inda ta santa.

Duk abunda na faɗa ki maimaita,”yau tun daga asibiti ban sake ganin komi baa,banji komi ba haka ban tuna komi ya faru a babban gida baa,sashin hajia lanti zuwa sashin hajia mariya,kawai naga jini ya ɓalle mun ne!”.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button