NOVELSUncategorized

KUNGIYAR ASIRI 3-4

p3-4

Da sunan Allah mai Rahama Mai jin ƘAI

   
     Jiki a matuƙar sanyaye take ƙoƙarin kai hanunta ƙasa inda jinin yake da niyar dan gwalawa wai irin jiri taji ya ɗebe ta nan take ta zube ƙasa sumammiya…  Jininna daɗa kwararowa daga ƙasan ƙofar zuwa inda take kwance ya mamake dukan jikinta!

  ɗumin jinin ya farko da ita daga suman da tayi nan take falon ke juya mata  kujeru na canzawa daga muhalin su zuwa gefe ɗaya kuru kuruwa ke tashi daga cikin ɗakin mami na muryoyin mutane suna magana cikin wani irin yare da bata fahimta baa.

Allah cikin ikon shi ya bata sa’a tana maimata”Auzubikalmatillahi tabbat min sharri ma kalaƙa…”

Wani irin ƙarfi ne yazo mata cikin zafin nama ta nufi ɗakin baccin mijinta a guje wanda ke sharar bacci hankali kwance(dama idan ranshi ya ɓaci da ya samu bacci shike nan).

Saman jikin si ta faɗa tana jijjiga shi”my happiness  ka tashi kaga abun da nake faɗa maka kullum yana yawan faruwa a gidan nan idan kayi tafiya,amma kana ƙaryaata wa!”

Cikin bacci yake jinta sama sama bakin shi ɗauke da salati ya buɗe idanu a hankali fes a kanta yana nazarin wani abu duba da yadda ta firgice lokaci ɗaya.

Rumguma mai kyau ya mata tare da sauke ajiyar zuciya! 

Mum mami meke damun kine wai?, kullum idan baki tayar mana da hankali ba naki hankalin baya taɓa kwanciya ko?

Wani kuka mai cin rai ya kufce mata….,saboda Allah menene yasa a kullum kake ƙaryata ni ne?,menene ribata idan na aibata mami?

Ɗan yatsan shi ya ɗaura saman lips nata”shiiiii” ya isa haka  yanzu meke faruwa kuma?

Ɗago kanta tayi tare da yunkurin sauka daga saman jikin shi tana riƙe da hannun shi”muje ka gane wa idanun ka”…,babu musu yake biye da ita baki sake kamar wani soko har zuwa falo.
Wani abun al’ajabi,koda ta duba da kyau wuri ya koma tsaf dashi kamar babu wani abu da ya faru!
Ni banga komi ba a nan zee!”cikin ɗaga murya yake magana”.

Ware idanu tayi da kyau ta duba ko ina fes har jinin dake ƙasan ɗakin mami ko alama babu.

Ƙasa ta zaun dabas tana nazari….,tambayar ki nke fa?

Cikin wani irin jarumta da ƙarfin hali ta miƙe,kayi hakuri na ɓata maka bacci in SHAA ALLAH ko kashe ni za ayi cikin gidan nan ba zan sake magana ba”tana kai Nan ta nufi hanyar ɗakin baccin su!”.

Jikin shi yayi sanyi saboda baya jin daɗi yadda a kullum zee ke ƙoƙarin aibata nashi gudan jinin shi wanda suka samu a wahalce.

Ɗakin mamin ya buɗe a hankali ya shiga hankalin ta kwance tana sharar bacci ..,wuri ya samu saman gadon ya zauna yana shafa kanta a hankali cikin so da kulawa har ta buɗe ido fuska ɗauke da murmushi.

Daddy na!

Na’am mamin daddy a tashi haka nan ayi sallah ko?
Tau ta furta tana ƙoƙarin sauka daga saman gadon…

ɗakin baccin su ya koma kasancewa magrib ya gabato….,koda ya shiga zainab na ban ɗaki alamar wanka take yi ya nemi wuri ya zauna zuciyar shi cike da sake sake,yana ganin ya kamata ya dubi lamarin zainab da idon basira.

Tunda mami ta fara wayau kullun cikin tayar masu da hankali zainab keyi tun yana biye mata har ya tattara ya watsar.

A dalilin irn wanan saɓani da suje samu yasa hajiyar shi tayi niyyar ɗauke mai ta koma wurin ta ya bata hakuri da zasu duba lamarin a tsanake.

A iya sanin shi dai sun kai ta asibitoci iri iri an dubata baa ga wata matsala tattare da ita ko ƙwaƙwalwar ta baa!

An dangana da mallamai babu wani jinnu ko iska dake jikinta!

Tun daga lokacin ya yiwa zainab gargaɗi mai ƙarfi da kakausar murya akan duk abunda ya sau ɗiyar shi ba zai kyaleta baa,idan ta sake tayar wa yan uwan shi da hankali bai yafe baa!

Fitowar ta daga wanka ya mai do da hankalin shi wurin ta yadda tayi wai irin sanyi ba kamar zainab ɗin da ya sani ba.

Bai wani tsya ɓata  lokaci ba ya shige ban ɗaki domin an fara kiraye kirayen sallah a wasu wuraren….,a hanzarce ya watsa ruwa tare da ɗauro alwala ya nufi masallaci.

A tsanake ta gama shirin ta daga bisanj ta gabatar da sallah…,bayan ta idar take nazarin littafin hisnul muslim cikin natsuwa sai taji ana buga ƙofa a hankali.

Gyaran murya tayi tare da furta”Bismillah”,Mami ta shigo bakinta ɗauke da sallama ta nemi wuri kusa da mumyta ta zauna.

Rufe littafin tayi suka shafa addu’a tare”ina wuni mummy?”

Shafa fuskarta tayi fuska ɗauke da murmushin yaƙe”lafiya lau mamin mu ya akayi ne kin yi sallah?”

Eh mumy yunwa nake ji!

Bari daddyn ki ya shigo muci abincin ai.

shigo na ɗan lokaci tna nazarin yanayin taa…,babu wani alamana tashin hankali ko damuwa a tattare
d

a ita.

Mummy yaushe zamu tafi wurin kakan kazaure?

Kina son ganinta ne?

EH mummy dasu mumy safiyya(sister zainab).

Zanyi magana da daddyn ki tau sai mu shirya a tafi haka ya maki ko?

Cike da farin ciki ta amsa da kai tare da miƙewa ta ɗauko wayar zainab dake a gefen gado”zan kira mummy safiyyah in faɗa mata zamu zo”.

Murmushi ta saki”daɗi na da mami zumuɗi”.

Tun daddyn ki bai amince ba zaki yi shela!

Hello mummy safiyyah ina wuni?,lafiya lau yariyar kirki ina mummyn ki?,gata nan kusa nace mata inaso a kawo ni wurin ki da kakan kazaure.

Yawwa Allah yasa kada su maki wayau yanzu dai hutu ake ba wani uzuri da zasu bamu ko?,”gyaɗa kai tayi kamar tana ganin ta”.

Bama kaka waya….,kakan kazaure me da me zaki aje mun zan zo?,duk abunda kike so yar albarka ina iyayen naki ne?.

Daddy na masallaci ga mummy nan!,bata wayar tau.

Assalamu alaikun ma ina wuni?

lafiya lau ya kuke da fatan ba wata matsala kuma?,ajiyar zuciya ta sauke!
Da sauƙi dai,idan Allah yasa ya aminta mun zo zamu sake tattaunawa domin ba magabmnar waya bane ma lamarin kullum gaba yake tafiya.

A sanyayye ta furta,kada ki karaya zainab Allah na sane damu in Shaa Allah komi zai zo ƙarshe,matsalar dai maigidan kine kwata kwata yaƙi bada haɗin kai da an kaita wurin wani mai maganin mayu da naji ana magana cikin gari ko za a dace.

Ma kema kin san halin shi ba zai taɓa yadda ba hasali ma gani yake na tsane ta ne shi yasa nake laƙaba mata abubuwa yanzu haka ma….

Jin alamar shigowar shi yasa ta miƙawa mami wayar wacce ta ƙure ta da idanu”cigaba da magana zan haɗa abinci daddyn ki ya dawo”.

Hijab ɗin ta cire ta nufi hanyar palo…”ina mami?”,shine tambayar da ya fara jeho mata.

Taso mayar mashi da ɓakar magana sai taga yin haka ba zai haifar masu da ɗa mai ido baa,dole ta rarashe shi ya aminta da zuwan su kazaure.

Fuskar shi ta shafa cikn wani irin salome,daddyn mami tana ɗaki na suna magana da ma ne.

Cike da zargi yake kallon ta”ba dai wani labarin kika shirya masu akan ƴa ta ba?”,uhm ko ɗaya!mamin ce m ta kira safiyyah.

Ranka ya ɗaɗe barij shirya mana abinci ko mami najin yinwa?.

Ba damuwa barin duba ta…

Kulolin abinci  data shirya  a kichen ta shirya saman teburin cin abinci gaba ɗaya dai dai sun fito a tare kowa ya zauna.

Plate biyu ne;ɗya mami da daddyn ta wanda a baya duka a wuri ɗaya suke ci kwatsam da matsalolin ta suka fara bayyana ya hure mata kunnu wai mummynta bata sonta shi ɗaya ya damu da ita saboda haka kada su sake cin abinci a tare.

Ranar daya faɗa wanan magana matuƙa ya mata ciwo tayi kuka daga bisani ta bar wa ALLAH!

Tana gama zubawa suyi addu’a kowa ya fara ci cikin natsuwa…,daddy!

uhm ya furta bakin shi cike da abinci.

Inason zuwa wurin kakan kazaure kaga an daɗe ban ganta baa,mummy safiyyah kuma kullum tace zata zo har yanzu taƙi zuwa.

Cigaba yayi da cin abinci yana zancen zuci domin baya so tana yin nisa dashi bare irin wanan tafiya mai nisa ABUJA zuwa KAZAURE!

Daddy bakace komi baa?,ba a magana idan ana cin abinci ko mummynki bata faɗa maki baa?

Kallon ta tayi cikin ɓata rai”ni bata faɗa mun komi!”

Ya za ayi ta sani kuwa tunda kayi kane kane ka hana yarinya zuwa islamiyya!”ta bashi amsa a tsanake”.

Ko a jikin shi ya juya yana fuskantar mami”kazaure kike son zuwa ko?”

Eh daddy!,yau laraba zamu tafi jumaa mu dawo lahadi ya maki?.

Haba wa daddynta aƙalla na kai wata shida banga iyayena ba mai zai hana mu tafi gobe sai mu dawo monday tunda kana hutu wurin aiki,na samu break a makaranta.

Dakata don Allah tafiyar nan ba dake zamu yi baa!,inace ai cewa kika yi mami na son ganin su ko?,zan kai ta nasan kwana biyu ya isheta ganin kowa mu dawo.

Cikin ɗaga murya take magana wn ahin adalcin ya ishe ni fa!, ya zan raini ciki in haifi yarinya a rinƙa ƙoƙarin cusa ƙiyayya a tskanin mu!

Na rantse da ALLAH idan kaga ban tafi kazaure ba sai dai idan kashe ni zaka yi domin nima haihuwa ta akayi kamar kowa ai…

Cikin Ɗaga murya mami ta furta”idan kika tafi kuwa gawar ki za a dawo dashi na maki wanan alƙawarin!”

Dariya ya kece dashi irin abun ya mashi daɗi….

Miƙewa zainab tayi cike da ɓacin rai”gawata zaa dawo dashi mami?”

Ni dana haife ki kike ƙoƙarin ganin baya na?,murguɗa baki tayi eh ɗin na faɗa ai kema rashin kunya kike yiwa daddyna kullum!

BAata san lokacin data finciko ta daga kujerar ba ta sharara mata wsu irin mari masu lafiya guda uku tare da haɗata da tebur ɗin nan taeke goshinta ya fara fitar da jini…

Barin fara kashe ki idan yaso ki dawo daga lahira ki kashe ni nima!

Tsawa ya daka mata yana ƙoƙarin ƙwace mami a hanun taa….,kina hauka ne zainab?,na rantse da Allah idan wani abu ya same ta kotu zata raba mu!

Daidai lokacin daga samu nasarar hankaɗe ta gefe ɗaya.

Sai me?,ai na jima da sanin wanan ba sona kake yiwa,wanan aljanar ƴar taka ta fini muhimmanci a wurin  na!
Da wanan zaman ƙuncin na gwamma ce  ka bani takar data in ƙara gaba sai ka aureta idanzaka iya dama ai ba jini na bane maniyin ka ne dana wacce aka haɗa ku ni kariga ka lalata mun rayuwa saboda a dalilin ka ƙwan haihuwata  ya samu matsala!

Mari mai rai da lafiya ya wanke ta dashi kafin ta ankara ya ƙara mata tare da jan hanunta zuwa ɗakin baccin su ya wurga ya ƙalgame ƙofa.

Huci yake kamar mahaukacin zaki kamar shi zainab zata na yiwa guri da gasa mai baƙaƙƙen maganganu a gaban ƴar shi?,
Ai kuwa sai ya nuna mata shi ka ɗai keda iko da mami!

bugun ƙofar ta shiga yi taba kuka….,banza yayi yace da mami ta ɗauko hijabinta su fita.

Ta window ta hango fitar motar shi daga gidan!

share hawaye tayi ta nufi ban ɗaki ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah wandta ɗauki lokaci tana kai kukanta wuri n mahallici.

Taso ta kira Mamansu ta faɗa mata amma bata don tayar masuda hankali a daren amma tabbas tayi alƙawarin sai ta tafi kazaure a gobe goben nan.

Shiru shiru har goma na dare basu dawo gidan baa!,tun tana duba agogo har ta haƙura tayi shirin bacci…


Fitan su daga gidan yawo ya rinƙa yi da ita cikin garin abuja har ya gaji don kanshi ya dawo gidan.

Horn ya rinƙa watsawa kamar wani mahauci domin mai gadi ya fara bacci mac.., da sauri ya buɗe mashi taba tsaye jikin window tana kallon ikon ALLAH”anya kuwa muhammad baya shan wani abun maye kuwait?”shine tambayar da take yawan yiwa kanta idan taga yana wasu abubuwan.

wani irin fincikota taji anyi ta baya tare da haɗa ta da da dressing mirror sai daya tarwatse duk glass ya soke mata baya, tana ƙoƙarin tayi aka sake janta sai banɗaki tayi tayi ƙofa ya buɗe yaƙi!


-Halimatus sadiya muhammad-

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button