NOVELSUncategorized

KUNGIYAR ASIRI 7-8

REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)

MACE MAI NEMAN ALJANNA WATTSAPP GROUP ina miƙa saƙon gaisuwa ta musamman a gare ku ALLAH SAKA MAKU DA ALHERI A KAN HIDIMA DA KUKE D AL’UMMA❤ ????7-8

      Yaran da suka sha zoɓo su biyar ne reras jere tsakiyar  yan 
ƘUNGIYAR ASIRIN sai kuka suke yi saboda tsabar ruɗewa!.
Tsawa mami ta daka masu mai firgitar wa wanda ya saka su duƙe wa aƙasa kamar zasu faɗa cikin wutar dake ƙara kuruwa kamar ana zuba mai fetur.

Kuyi ma mutane shiru ai ƙwaɗayin ku ya ja maku!,dama ina haƙe da ku irin cin zarafin da iyayen ku ke yiwa mummyna saboda rashin aihuwa,sai na kashe ku kuwa ma ya huta!.

Abunka da yara ne duka basu haura shekaru goma baa,ukun ma basu kai baa,ko wanne ya shiga rera marayar kuka mai ban tausayi sun ji an ambaci mutuwa ko wanne ya fara kiran”mumy,daddy!”.

Suna ji suna gani mami ta bada umurni a ɗaure ko wanne cikin su jikin bishiyar dake jejin wanda ko wane bishiya akan babban rami a ƙasa mai zurfi wuta na tashi,saman bishiyar kuwa ƙarfuna ne masu tsini kamar allurai da ka ɗaga kai suna kallon ka jira suke kayi motsi su fara nasu aikin.

Dama saman tsaunin nan mami ta tashi sama kamar balbela hanunta riƙe da takomi,hannu ɗaya kuma babban ƙwarya ne ta nufi wurin da suke da zubar chaka ma kausar nan take zainab ta zabura daga baccin da ya fara ɗaukar ta a guje ta nufi sashin hajia lanti tana faɗin”kausar!”..

Koda ta shiga palon cike da ɗan mutum kowa yayi cirko cirko ana jimamin abunda ke faruwa,kutsawa tayi cikin mutane har ta isa tsakiyar palo inda  yaran nan biyar ne kwance a ƙasa ciki ya haye kamar mai shirin haihuwa yau ko gobe!,mami na zaune saman kujerar data fara zama tun farko babu alamar tsoro ko damuwa a tattare da ita.

Ɗaya bayan ɗaya ta shiga jijjiga su babu mai motsi har ta iso wurin kausar ta  ɗaga rigar ta,fasa ihu tayi tare da fido idanu a waje ganin alamar wuƙa an suke ta har jini ya bushe a jikinta!.

Cike da zafin nama ta nufi mami gadan gadan….,kawai ta kauce mata ta bugu da bango juwa ya kwashe ta ƙasa ta zube!

Mami ta isa wurin da take kwance tana shafa jikinta…,idan baki daina shiga hurumi na ba wata rana zaki yiwa rayuwar ki mummunar ila ne mummy!

Tana ƙoƙarin ɗagowa ta danne ta sosai!,a haba wanan ne kuma baki isa ba kawai kisha bacci lafiya sai da safe.

Babu wanda yabi ta kan zainab domin ba sonta ake baa,chirko chirkon da akayi jiran isowar jami’an tsaro ake yi an buga masu waya.

Abunda ya faru bayan fitar zinab a sashin hajia lanti shine;bayan mami ta gama ɗura masu zoɓon da yan mintuna suka fara amai!,idan wanan ya gama wanan ya fara tun ana ɗauka da zauƙi har suka galabaita kafin a nufi asibiti sun fita hayyacin su ba mai motsi.

Nan wuri ya kachame da koke koke sai kiraye kirayen waya…,aka tasa inna mardiyya mai aikin hajia lanti a gaba sai ta faɗa abunda ta zuba a ciki??

Rantse rantse ta shiga yi bata zuba komi ba domin ba aƙalla sun share shekaru tana aiki a gidan wani abu makamancin haka bai taɓa faruwa baa!.

Iyayen yara suka tirje akan lallai mami zaa bincika domin dai tare suka sha me yasa babu abunda ya faru da ita?.

Mami kau tace ai nan suke tare babu wanda yaga tasha zoɓo,hasali ma a gaban kowa ta basu har ya ƙare bata sha baa!,baa sake bita kanta ba hajia tace lallai ne a kira jami’an tsaro su tafi da inna mardiyya.

Mutame da dama dai basu goyi bayan a tafi da ita ba domin dattijuwa ce mai gaskiya da amana.

Ana haka ne zainab ta shigo!,amma abun mamaki cikin su babu wanda ya  ga alamar yanka a jikin kausar sai zainab shi yasa ake ganin shirme kawai take yi bata cikin hayyacin ta.  Ubannin yaran sun iso gidan har da muhammad dama an jima da kiran su a waya….,da kyar aka rarashi hajia tayi hakuri kada a tafi da inna mardiyya,a fara zuwa dasu asibiti idan an tabbatar guba suka ci sai a shiga bincike.

kwasan su akayi zuwa asibiti,iyaye mata na gida saboda ruɗewa muhammad  bai nemi zainab ba har suka fita tana kwance wurin data faɗi!

Duk wanda ka gani a wurin hankalin shi a tashe sun sha kuka banda hajia lanti duk da abun ya taɓa zuciyar ta amma ta daure kada ta karya masu zuciya. Mami kau daɗi fal ranta ko ba komi sun ɗanɗana kwatan kwacin ciwon da mummynta keji idan suna mata gorin haihuwa.

Katse shirun tayi”kukan me ku ke yi wai?”,ku kwantar da hankalin ku babu wanda ya mutu a cikin suboats,kawai Allah ya jarabce ku ne domin ya gwada ƙarfin imanin kurt(za ku kasance masu tawakkali ko zaku zama butulu marasa godiyar ALLAH?).

Hajia lanti tace kwarai kuwa mami,yarinya ƙarama da kaifin basira kuma naga dai haihuwar nan lokaci near, ALLAH ke bayar wa ga wanda yaso kuma ya amsa idan lokacin ka yayi!,sai muyi tawakkala Allah da ya bamu su idan ya amshe su zai bamu wasu.

Granny inace ko mutum ke ba kanshi haihuwa ai?, wane mutum!,haihuwa,aure,arziki da mutuwa duka lokaci ne babu wanda ya isa ya baka shi.

Amma kun san da haka kuke cima mummyna mutunci akan rashin haihuwa granny?, cikin palon babu wanda bai sha jinin jikin shi ba domjn basu yi tunanin mami tana gane abubuwa haka baa,yawanci idan sun zo gidan hankalinta na kan yara ne ashe tana hankalce dasu.

Hajia lanti ta yafutu ta da hannu,zo nan ki zauna kusa dani mai suna na,wanan ba maganar yara bane kar ki sake cewa komi kinji?,tana lafe gefen hajia tace saboda bakwa son gaskiya baa!

Kallon matan dake tsaye suna zirya tayi,idan zaku gyara halin su ko wacce ta kwantar da hankalin ta babu abunda zai faru da yaran kurt,amma idan ku ka sake zagin mummy na sai dai ku haifi wasu yaran!.

aƙalla sun jima zugum har aka kira sallah kowa ya nufi wurin sallah,mami ta tayar da mummyta tayi sallah.
Tsam ta miƙe kanta na ciwo amma ta rasa me ya fau da ita near,ta kasa tuna komi haka ta nufi hanyar ɗakin da take sallah idan tazo…

Tun suna sallah wayar hajia keta ruri har aka idar ta miƙa hannu,lamban uncle jafar ta gani.

sallama hajia tayi,sai suka ji ta furta alhamdulillah ina suke?,masha Alah sai kun iso lafiya ALLAH kawo ku cikin aminci.

Tunda ta fara wayar hankalin su na kanta har ta kamalla sanan ta dube su;sai ku gode wa ALLAH yaran ku suna cikin ƙoshin lafiya gasu nan dawo wa gida.

Ko wacce ta shiga washe baki suna gode wa ALLAH…

Zainab na ɗakin baƙi bayan ta idar da sallah ciwon kai ya matsa mata bata ko iya ɗaga kan,kishingiɗe wa tayi saman sallaya sai bacci.

Isowar su gida yasa aka sake dawo wa palo ana jirar shigowar suasion,mami da sauran yaran suna kusa da hajia har iyayen su maza suka shigo da sauran yan uwn sumul kamar ma ba abunda ya faru.

Ko wane cikin yaran ya koma wurin iyayen shi mata suka rungume yaran cike da so da ƙauna,sai lokacin muham ya lura zainab bata wurin ya yiwa mami alama da hannu taje wurin shi,”ina mummyn ki?”,tana bacci kanta na ciwo ne.

Babban yayan su ya yi bayani an duba kowa a asibiti babu wani matsala sai yan magunguna da aka basu kawai.

Godiya suka yiwa Allah dukan su hajia tace ya kamata a fito da abinci kowa yaci tunda hankali ya kwanta….,masu aikin suka shiga shirya masu abincin saman babban kafet na cin abinci.

muhammad  ya riƙe hanun mami suka nufi ɗakin da zainab take bacci…,tashinta ya shiga yi su tafi wurin cin abinci!,cikin bacci tace ba zata iya fita ba kanta na bala’in sarawa ne.

Hankalin shi bai kwanta yace kawai ta tashi su tafi gida,da kyar ta miƙe hanunta dafe da goshi hannun shi zagaye a ƙugunta suka fito….,kallo ya dawo kan su ,haushi kamar ya kashe sauran matan domin mazajen su ba masu yawan zama bane basa samun kulawa sosai irin haka.

Hajia tace menene kuma?,bana son tashin hankali fa!,hajia kanta ke ciwo zamu wuce gida.

Allah kai ku lafiya kawai tace!,sauran yan uwan shi maza suka mata fatan samun lafiya,matan kuwa babu bakin magana.

Sai da suka isa wurin mota yace ina jakarta  da takalmi?,ta nuna hanyar sashin hajia mariya.
Sai da ya zaunar ta ita,mami ma ta shiga sanan ya nufin sashin ya kwaso kayan hajia mariya tayi masu Allah tsare gaba suka nufi gida.

Har suka isa tana cije leɓe ya kwantar da ita a daƙi tare da samo mata magana da kyar tasha,ya nufi kitchen tare da mami suka girka taliya a sauƙaƙe.
Bata wani ciba  ta koma bacci…,yinin ranar bacci kawai take har dare sanan ta warware tayi wanka da taimakon mijinta suka baje a palo yana tambayar ta abunda ya faru a babban gida bayan tafiyar shi?.

Ni ban san komi ba kawai ta bashi amsa,ya maganar tafiya kazaure?.

Mami tace wai har yanzu baki haƙura da tafiyar bane mmumy?,harara ta watsa mata kawai domin babu abunda zai hanata zuwa kazaure tare dasu a gobetween,sai dai idan ta tuna da maganar mami na sai dai gawarta sai tsoro ya ziyarci zuciyar ta!.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button