A GIDANA 44
Always Turn your wounds into wisdom.
*Congrats SURRYHAMS Barka da kammala littafi, Allah ya kara basira da zakin hannu, will miss Khal and Bahi our cute love birds????*
{44}
Tana kokarin fita daga motarta wayarta tai kara, a hankali ta sa hannu ta dauketa, sunan Swt Sis ne ya bayyana a alan wayar tata, a hankali ta rufe idanunta cikin wani yanayi sannan ta dauka.
Nabila daga can tace “Aunty? Muna ta jiranki.”
Cikin wani yanayi mai sanyi tace “Nabila kuyi hakuri bazan samu zuwa ba wlh.”
Da sauri Nabila tace “wani abin ya faru ne?”
Tace “bakomai meeting zan shiga yanzu ne, in na fito zan kira Dady.”
Jiki a sanyaye Nabila tace “shikenan mu zamu wuce, in kin fito mayi waya.”
Kai ta daga kamar tana ganinta tace “shikenan, akwai jakata a daki na ajiye muku kudin skul ki daukar muku.”
Mundoge, Aunty dan Allah ki kula da kanki.
Cikin jin dadi tace “to Nabila nagode.”
Kashe wayar tai sannan ta zubawa Tv Station din ido tana kara tuno farkon zuwanta da yawan canjin da aka samu daga fara aikinta zuwa yanzu.
Bude kofar motar tai sannan ta fito.
Komawa yai ya xauna a karo na biyu kenan yana zuwa nemanta batanan, haka kawai jikinshi yake bashi ba daidai ba kallan Afreey yai wacce ke zaune tana dane dane a waya, Nazifi ne ya shigo yana cewa “Manya zasu shiga emergency meeting yanzu.”
Kallansa Khalid yai, wani daga cikinsu yace “na meye meeting din?”
Nazifi yace “shi ke damuna.”
Ramatu ce tace “akan Hajiyar gadara ne ka sani.”
Kallanta Khalid yai, juyawa tai ta koma ta zauna cikin jin dadi.
Zainab ce ta tura kofar dakin taron sannan ta shiga.
Duk suna zaune wanda hakan yasa tasan sun gama tattauna abinda zasu ce mata kafin tazo.
Shiga tai ta gaishesu sannan taja kujerarta ta zauna.
Director Kabir ne ya kalleta sannan yace “Zainab munaso mu miki tambayoyi kuma muna fatan jin amsoshi gamsassu daga gareki.”
Kallansa tai batace komai ba.
Takarda ya mika mata yace “wanene ya saka law din nan akan duk wanda ya bari harkar personal life dinsa ta shiga cikin aikinsa za’a dau mataki a kansa?”
“Nice” abinda tace kenan ba tare da tai karin bayyani ba.
Yace “yanzu abinda ke faruwa fa menene?”
Tace “banida hadi da abinda kefaruwa, banga dalilin da zaisa a dinga hada rayuwata da wanda banda alaka dashi ba.”
Kallan juna sukai, Kabir yace “kenan kina san cemana wannan abin bai shafeki ba?”
Wai akan me za’a dinga jan abinda ba wani abu ba ya zama wani abu? Sau nawa wasu na samu matsalar zaman takewa? Akanta aka fara ko a kanta za’a kare?
Kallansa tai sosai tace “me Adam yai? Me nai? Dan wani ya dau hoton mu ya daura a instagram da facebook ni na daura? Sannan ba aure tsakanina dashi dan ya kama gabansa laifi na ne kenan?”
Murmushi yai yace “hakane, to wani hukunci kike tunanin zakima wanda ya fitarda tambayoyin jarabawarmu yaba wanda yake so yaci?”
Kallansa tai tace “hukuncinsa korar wata shida.”
Yace “wanda kuma ya ke da alaka wace bata aure ba tsakanin sa da dan uwan aikinsa fa? Alaka wacce take dauke da ayar tambaya mai karfi fa?”
Kai tsaye tace “korar sa za’ai”
Cikin jinjina kai da gamsuwa ya kalleta batare da ya dauke idanunsa akanta ba yace “menene tsakaninku da saban ma’aikacin da kika dauka Khalid?”
Kallansa tai cikin rashin fahimta tace “wani Khalid din?”
Director Kabir yai wani murmushin jin dadi yana tuno takardar da aka ajiye kai akan kai amfani da Khalid in taki saduda, tabbas akwai abu tsakaninsu, yayi kata driver, a gidansu ma ta xauna da auranta ya mutu sannan yanxu kusan kullum tare suke tafiya.”
Menene tsakaninku?
Tace “meye tsakanin mu kuwa?”
Kallansu yai yace “ba abu a tsakaninku ku kika zauna a gidansu?”
Kallansa tai da sauri.
Kallanta ya sakeyi cikin jin dadi yace “Binciken mu ya nuna karatun degree na Maths yai ba yanda za’ai ya rubuta amsoshi masu zafi akan karatun da bai da alaka dashi, in har ba bashi akai ba.
Abu na biyu yaran nan kin nuna baki da alaka dashi kuma mutane uku na tambaya sun nuna kin sanshi, sai a lokacin ma na tuna abinda kikamin akan nayi rejecting din takardarsa ta neman aiki.”
Me tama akanshi?
Murmushi yai yace “nan tazo tacimin mutunci akan nacuceshi taya zan hanashi aiki bayan yaci? Har takardar ajiye aikinta ta rubutamun saboda shi.”
Kallansa kawai take gaba daya ma tama rasa me ma zatace mai saboda gaba daya bata taba kawo jin abu makamancun haka bama, bata kawo abin nasu har yakai haka ba.
Kabir yace “mu kirashi mu tambayeshi alakarku da sanda kika turamai tambayoyin jarabawar? In har sharri muke miki?”
Kasa magana tai kawai sai kallanshi da take.
Can ya dauke kansa daga kanta yce “ance ma akanshi kika rabu da mijinki.”
Idanunta na kansa ita kadai tasan abinda take ji a cikin ranta.
kallansa tai kafin ta saki wani murmushi, kallanta yai yace “in har ba abu tsakaninku kina san wanke laifinki yanzu a kirashi ki koreshi daga aiki da kanki, wannan zai nuna mana tabbas ba abu a tsakaninku.”
Farcenta kawai take karzawa yanzu kam ta ma dauke ido daga kansa, kanta na jikin desk din dake gabanta.
Yanzu ne CEO din su yai gyaran murya sannan yace “Zainab ke muke sauraro.”
Dagowa tai ta kalleshi idanunta sunyi jaaa, tunowa take da sanda Khalid ya samu aiki Umma ta kirata cikin doki tana fada mata, cikin xuciyarta tace “Ya Allah!”
Samun kanta tai dayin murmushi tace “Duk da nasan kuna san korata ban taba tunanin zaku kaskantar da kanku ku je wannan matakin ba, duk cikinku na san yanda kuke jin haushin ni kadai ce mace a cikinku, na san ynda kuke jin haushin komai ta hanuna akeyi.”
Kallan Kabir tai tace “Weldone da kokari, nasan duk wannan abinda kake dan na baka plan din danai wata uku ina shiryawa ne, ba sai kunje wannan matakin ma lalata min mutunci na da shi kansa ba, i will live.”
Kallanta sukai da sauri, ta hadiyi wani abu tace “sai dai.”
Ta dago ta kallesu daya bayan daya tace “Inaso kusan wani abu, na muku alkawari a wannan indai har inada rai da lafiya a daidai wannan lokacin nan da shekara biyu sai kunyi zaman meeting na neman mafitar yanda zaku gyara matsalar dake faruwa a tv station din nan, na muku alkawari nan da shekara biyu in dai ina da rai inda zan koma aiki sai ya wuce wannan gidan naku daraja da daukaka, zan gani in hakkina da kuka ci zai barku, ko baku ceba banaji zan iya cigaba da aiki daku.”
Mikewa tsaye tai tace “Zaman da mukai a wannan wuri yasa na fara tausayin kaina, mijin dana rabu dashi da mahaifina, na yanda na sadaukar da komai akanku na sadaukar da duk wani lokaci na ina faman ganin na daukaka wannan guri, abinci wannan sai nayi da gaske nake ci, sai na tashi tsakar dare na hau aiki duk saboda neman ci gaban mu, bansan sakkayar dazan samu ba kenan.”
Director Kabir ne yace “ke mutane nawa kika kora ba tare da hakkinsu ya kamaki ba?”
Kallansa tai ranta a matukar bace tace “duk wadanda na kora fadamin wanda bai aikata babban laifi ba? Sannan cire gurbatatu danai ba shine yasa muka samu ci gaba ba?”
Yace “Kema ai babban laifin kikai.”
Kai ta daga cikin takaici tace “hakane ashe babban laifi nai.”
Sallama ta musu ta juya, gaba daya shiru sukai, har taje jikin kofa ta dawo tadau maker mai makon tai rubutu a whiteboard din dake meeting room din ta wuce jikin kofa ta rubuta musu resignation letter ta cila maker din ta fita.
Office dinta ta wuce gaba daya ji take kamar zata fadi saboda jirin da takeji.
Hannunta rawa yakeyi sam ta kasa bude kofar, makulin ma ta kasa sashi a jikin kofar.
Khalid daya taho dan ganin ko sun gama ne ya karaso, ganin abinda ke faruwa yasa ya karasa da sauri ya amshi key din.
Kallansa tai idanunta basa gani sosai, yana budewa ta shiga ciki, bayanta yabi da sauri shima yace “Are you okay?”
Juyowa tai ta kalleshi sannan ta kara rufe ido ta bude, murmushi ta kakaro tace “yeah, can you help me?”
Da me?
I need to pack.
Cikin rashin fahimta yace “pack?”
Kai ta daga tace “in an tashi please.”
Shiru yai tare da zuba mata ido, tabbas akwai babban abinda ke faruwa da ita kuma tana neman kadaicewa, hakan yasa ya sauke jakarsa ya ciro flask din ya ajiye yace “inji Umma, in an tashi na dawo.”
Juyawa yai har yaje kofa ya juyo ya kalleta, tana tsaye haryanzu.
Tana ji ya rufe kofa alamar ya fita ta zube a kasa, gaba daya jikinta ne ya shiga karkarwa, zuciyarta na wani irin kuna.
Wasu zafaffan hawaye ne suka zubo mata, kawai ta fashe da kuka.
Tayi koka har ta gaji.
******
Khalid kam sam ya kasa maida hankali akan aiki, tabbas akwai abinda ke faruwa, menene?
Ramatu ce ta shigo tana dariya, kallan Su tai tace “Hajiyar gadara dai an ajiye aiki.”
Da sauri Khalid ya kalleta, yace “aiki?”
Yanda damuwarsa ta fito karara ne yasa Ramatu tace “eh yanzu, ahhh masamu hutu haba kullum cikin takura”
Idanunsa ne suka sauka akan Afreey wacce yaga tana murmushi ta kasa, Nazifi ne yace “ban gane ba? Waya isa ya sata ta ajiye aikinta?”
Ramatu tace “ina na sani?”
Shiru Khalid yai yana tunanin meke faruwa? Adam
Ne? Raziyya ce? Ba shiri ya hau bincike a facebook da instagram sai dai baiga wani sabon posting daya shafeta ba.
Har aka tashi zuciyarsa ta kasa nutsuwa.
******
Jiki a sanyaye Adam ya shigo gida, zama yai a falo akan yar katifarsu yai shiru ya baxa uban tagumi.
Goggo data fito daga bandaki ne ta kalleshi tace “kai kuma fa?”
Kallanta yai ya sauke wata ajiyar zuciya.
Zama tai tare da jawo mai tana shafawa tace “kai fa kayan haushinka yama yawa, meye hakan?”
Kallanta yai yace “Goggo yanzu Zainab ta tafi.”
Da sauri tace “Zainab?”
Kai ya daga alamar eh yace ” Goggo yaune karo na farko dana taba ji Zainab ta rokeni abu.”
Kallanshi tai ta matso tace “komawa takesan yi?”
Kai ya girgiza yace “Rokana tai na kyaleta haka nan.”
Hawaye ne ya zubomai ya kalli Goggo yace ” Goggo ya zanyi.”
Kallansa tai ta koma dabas ta zauna zuciyarta na kuna ta kasa magana itama.
Can tace “ka hakura kenan?” Ido ta kuramai tace “ko ukun kai da gaske?”
Dan kai ya kauda yace “ko ukun nai in na dage biyu nai ai ba yanda za’ai.”
Cikin takaici takai mai bugu, tace “kai dai wlh kaji asara, da alama ka fara hauka, ni anya ma kudin nan da aka baka a takarda na gaske ne?”
Kallanta yai yace “kema kina tunani haka ko?”
Tace “to akan me za’a baka uban kudi ba tare da kayi wani abu ba?”
Yace “nima abinda ke ban mamaki kenan, sannan Afreey fa dama can ba wai kyauta gareta ba.”
Afreey? Meye hakan suna kamar na aljanu?
Dariya yasa yace “ke ina kikasan sunan gayu?”
Tsaki tai tace duk kai kaja mana da kun haihu da Zainab ta isa ta koremu?
Haushine ya kamashi, tace ni tsinaniyar magen ma har yau banganta ba, ta ja mana bala’i tai gaba.
******
Kayanta kawai take ta hadawa, wayarta dake kara ta jawo ganin sunan Dady yasa ta dauka da sauri.
Dady bayan sun gaisa yace “ashe basu dade da tahowa ba?”
Tace “eh wlh ni suka tsaya jira kuma na shiga meeting.”
Yace “kinje gidan Auntyn naki?”
Tace “na kirata a waya tace zata samomin wace zata zauna, haryanzu batace komai ba.”
Shiru yai sannan yace ” komai dai lafiya ko?”
Hawaye ne suka zubo mata tace “Dady na ajiye aikina yanzu.”
Da sauri y mike tsaye yace “meya faru?”
Share kwallar ta tai tace “wani gun zai nema nan gaba daya abin nasu ya baci.”
Shiru yai dan yasan tabbas da wani abu, can yace “ki dawo gida, dan dama hankalina ba’a kwance yake da barinki ke kadai ba, in har ba aure kikai ba bazan bari ki cigaba da zama ke kadai ba, in ba so kike a fara miki fassara akan zaman kanki kike ba.”
Aure?
Yace “eh shi kadai ne zai sa na barki ki cigaba da zama a kano, tunda har kika ajiye aikinki to ki shirya wani satin zanzo daukanki.”
Dady amma……
Kashe wayar sa yai cikin mamaki tabi wayar da kalli, dady ne kuwa? Taya Dadynta zai mata fada haka? Ko ta bakinta bai nemi ji ba?
Aure? Tafiya? Ta ya zata koma bayan yanzu ne take da dalilin zama a kano?
Dady kam yana kashe wayar yai shiru, shikansa mamaki yake yanda yai maganar sai dai yasan dole ne yai haka in ba haka ba baxata taba yadda ta dawo ba shi kuma gaskiya bayasan barinta sam a can ita kadai.
Khalid ne yai knocking a hankali ya shigo.
Kallanta yai, itama kallansa tai.
Shiru yai baisan me zaice mata ba, itama shiru tai dan kanta a cike yake da tunani.
Duk ta hada kayan hakan yasa ta mike tadau box daya matsowa yai ya amsa daga hannunta ya kara dayan akai.
Kallanta yai yace “kofar.”
Karasowa tai ta bude mai kofar, ya fita.
Jakarta ta dauko da flask din Umma.
Kallan staffs din tai duk sun fito kasa suna jiranta.
Wasu harda hawaye wasu kuwa tasan na karya ne, kallan Tv Station din tai tace “in Allah ya yarda nan da shekara biyu sai kun nemi yafiyar abinda kuka min.”
Haka ta shiga musu sallama kafin ta wuce jikin motarta.