NOVELSUncategorized

KUNGIYAR ASIRI 9-10

REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)

MUGIRAT marubuciyar”LAHANI”,ban san da wani irin kalma zan yi amfani wurin nuna matuƙar godiyata a gare ki ba!,haƙiƙa kin nuna mun ƙauna da soyayya,sharhin ki a kan wanan littafin na matuƙar ƙara mun ƙwarin gwiwa. Har kullum ina maki fatar alheri a duk inda kike ALLAH ƙara maki basira da daukaka,Allah yasa ki zarce haka a duniyar marubuta amin❤ 




????7-8


     Ba zata iya buɗe baki ta furta mashi bata son kusantar ahalin shi baa,haka bata jin zata iya zuwa gidan nan.

Zuciya cike da sake sake ta girka ruwan shayi kawai sai bredi ta ɗaura saman tebur sanan ta mashi magana ta kammala…

Wai irin breakfast ne haka ko minti  talatin ba ayi cikakke ba har an gama?.

Haushi ne ya kamata,ta luka kwata kwata muhammad  baya ganin ƙoƙarin ta a gidan nan. Shayi ne idan ba zaku sha ba ai babu dole!,”ta juya fuuuu ta koma ɗaki”.

Murmushi yayi a bayyane,sarai yasan neman dalili take da safen nan kawai don kada taje gidan iyayen shi,amma yasan inda zai ɓollu mata.

Mami dake buga vedio game ya kala,wai kin gama gyaran ɗakin da naji tana maki magana ne?,daddy ni ba zan wani iya gyaran ɗaki ba kullum safe tunda ba fitsarin kwance nake yi baa.

Jinjina maganar ta yayi yna nazarin yanyin ta…,watau a gidan kowa shegen kanshi ne,ba wanda ke ragawa wani domin wata rana sai ka rasa gane tsakanin mami dasu waya haifi wa!.

Tashi yayi ya nufi kitchen inda yaji motsin zainab…,koda ya isa kamshi ya maye ko ina tana soya ƙwai ne.

Sannu da aiki uwargida me zan taya ki dashi?, a daƙile ta amshi shi”babu,ka jira na kusa gamawa zan fito yanzu”.

Jingina yayi da bango yana ta binta da kallo,a iya zaman da sukayi na shekaru biyar kafin haihuwar mami basu taɓa samun matsalar da zai kai su ga hayaniya ba bare har ya kai mata hannu. Zainab mace ce mai hakuri matuƙa da gudun zuciya,sai dai fa nan da nan ne ta haye wanda idan baka fahinta baka taɓa sanin ta shiga ɓacin rai.

Babu rayuwar auren da zaa ce baa fuskantar ƙalubale a wanan lokaci,amma idan ka samu abokin/abokiyar rayuwa mai haƙuri sai yazo da sauƙi. A iya sanin shi tunda aka haifi mami babu ranar da ba zasu samun saɓani,bashi da kaƙuri ko kaɗan!,zainab ta rikiɗe ta koma wat irin mafaɗaciya,bashi da halin nuna ɓacin ranshi zata haye ta rinƙa jinini kenan bata gajiya har zuws yau ɗin nan da mami keda shekaru goma tana neman na sha ɗaya ya rasa gane inda matsalar su take.

Kwasan kayan tayi bayan ta kashe gas ta nufi hanyar teburin cin abinci…,shauran plate da yaga ta aje zata dawo ta ɗauka y kwashe tare da binta a baya.

Ruwan zafin da ya ji kayan ƙamshi ta tsiyayawa kanta a ƙaramin kofi sanan ta haɗa dai dai yadda take so ta tura mashi flask ɗin gaban shi.

Bredi ta ɗiba tana shafa bota yana kallonta har ta gama tayi bismillah ta fara ci….,mami!.

Na’am daddy!,taso muci abinci.

Babu musu ta aje game ɗin ta nufo inda suke…,tea ya haɗa masu a cup ɗaya sanan ya sama soyayyaen ƙwan tsakiyar slice bread ya rufe da ɗaya ya miƙa mata nata,ya haɗa nashi.

Daddy shike nan breakfast din?,yau mummyn ki bata da lafiya shi yasa bata soya komi baa,kici da sauri ku shirya zamu babban gida(gidan iyayen shi)

Daɗi sosai ya kamata domin idan akwai inda take son zuwa a garin abuja bayan school sai babban gida,saboda akwai yara da yawa zata yi cin zali yau.

Saboda tsabar murna bata wani ci abincin sosai ba ta miƙe…,ina kuma zaki?

Wanka zanyi daddy idan mun isa zan ci abinci wurin su granny.

Duk abunda suke yi tana kallon su ta wutsiyar idanu kiris take jira a sako ta cikin hirar tayi cin mutunci,amma sun shareta kamar ma bata wurin.

Ganin tara na safe ta gota yasa ta hanye ruwan tea kawai ya mike,muje ki taimaka mun da wanka darling.

Wani harara ta watsa mashi kamar manyan idanunta zasu faɗa tare da jab dogon tsaki tana cigaba da kurɓan tea a yangance domin ta ƙudiri niyyr sai tayi abunda zai hana tafiyar da ita.

Dariya yayi sosai tsaf ya gano inda ta dosa ya kaɗa kai ya wuce ɗaki zuciyar shi fal soyayyar matar shi.

Har ya gama ɓata lokaci wurin wanka,ya shirya cikin yaddi brown mai ɗaukar ido ya fito tana zaune inda ya barta,ɗakin mami ya tura a hankali tana zaune saman gado ta baje kayan kwalliya birjiƙ tana fentin fuska!.

Dariya ya mata domin tun tana da shekaru uku haka tare da son kwalliya sai ta taka stool na ɗakin mummyna ta haye saman dressing mirror ta zauna sai tayi kache kache da komi.


MAMI kwalliyar ya isa haka nan rana nayi,idan mun tafi a nan zan barku saboda zan shiga suleja sai da yamma zan dawo mu saboda bana son barin mummynki ita ɗaya a gidan nan.

Tau daddy na. Kayan ta shiga haɗa wa already  ta saka doguwar rigar lace ɗinkin bubu pink,abunka da dogowar mace ya mata kyau duk da siririya ce sosai bata da kauri.

Fitowa suka yi a jere kamar wasu masoya yana kwasar dariyar shirmen taa…,turus yayi ganin har lokacin zainab na wurin tana wasa da kofin da ke hanunta!

Kallon juna suka shiga yi da mami,raɗa mashi tayi ƙasa ƙasa”ba tare da mummy zamu bane naga bata shirya baa?”.

Cikin ɗaga murya yadda zata ji ya fara magana,kyale mummyn nan taki ummu yanga kenan amma kada ki damu shawarar da kika bani shi zan ɗauka kawai aure zan ƙara tunda bata son mu!

Kuma bata son zuwa gurin su granny daddy.

An ƙi aje din munafukan banza,wallahi ai anyi lusarin namiji a nan wai duk girmanka baka da abokiyar shawara sai yar mitsitsiyar yarinya!,ba zan tafi gidan naku ba ai ba sona suke yi baa,ka ƙarata can da yan uwanka munafukai irinka.

Ranshi ya ɓaci ainum amma baya so yana biye mata suna samun saɓani a gaban mami gudun sake afkuwar wsni abu makamancin na jiya!

Mami kwashe kayan ki kai kitchen kinji?,tsaki taja tana harhaɗa kayan idan akwai abunda tafi tsana a duniya  bai wuce ɓacin ran daddynta ba duk a takan kasance cikin shauƙi idan taga suna tashin hankali haka,bata ƙaunar ganinsu cikin kwanciyar hankali kawa burinta su rabu kowa ya kama gaban shi domin sun zame mata wani katanga a tsakaninta da cikar burinta.

Mami na shiga kitchen din ya sungumi zainab wacce ke zille zille har cikin ban ɗaki ya sauke ta tare da surin sakar mata shawa sanan ya fice da sauri yaja mata ƙofa!,idan kinga dama kiyi wankar ko ki cigaba da zama ciki har wani abun ya sake faruwa dake kuma.

Jin haka tayi saurin cire kayan ta fara wanka a tsorace tana waige waige har ta gama,towel taja daga inda suke ajewa ta ɗauro ta fito…,baya cikin ɗakin gidn ma gaba ɗaya ya mata shiru nan take gabanta ya faɗi ta shiga tunanin ko sun wuce ne?.


Leƙwa tayi a window,motar shi na nan tayi hamdallah ba wani dogon shafe shafe tayi ba kawai itama ta zura doguwar riga na atamfa sai sarka da yan kunne data saka ta fesa turarai,handbag kalar mayafin da takalmi ta sunguma ta fito…,suna zaune palo hankalin su na kan game din da mami ke bugawa da wayar shi suka ji taku ɗas ɗas ɗas!.

Eyeeee kaga uwargida sarautar matador,takawar ki lafiya uwargida sarautar matador..,”uwargida sarautar banza dai taja tsaki”,idan an fasa tafiyar ne ka bani car key zani gwarimfa gidan yusrah(aminiyar ta kuma matar abokin shi).

Key ya wurga matador,zaki gwarinpa wurin gulma da tsegumi dai saboda ance zaa maki kishiya zaki tafi a tsegunta mata Amebo’s kawai.

Tana amsan key tayi gaba abunta…,basu wani ɓata lokaci ba ya kashe kayan wuta uka fito tare da mami wacce hankalinta ke kan game na(zombie highway) da take bugawa.
Rufe ƙofar shga ciki yayi ta waje suka nufi mota gimbiya zainab na gaba hakimce,mami ta buɗe gidan baya ta shige,shimaya shiga gaba tayi bismillah tare da ba motar wuta.


Sai da suka hau titi sosai ya tabbatar gwarinpa zata da gaske,bai ce komi ba ya ƙyale ta har suka isa layin sanan yace”juya kan motar zuwa kubwa!”.

Kallon shi tayi da kyau taga babu alamar wasa a fuskar shi,itama tayi kichin da rai;ai na faɗa maka ban zuwa kawai ga motar ka zan ƙarasa gidan a ƙasa!.

Allah zainab idan kika fita daga cikin motar nan zan ɓata maki rai tunda na lura bakya son zaman lafiya.

Tsaki taja tana maganganu ƙasa ƙasa…,daga bisani ta ɗaga murya”ni ba zan iya jan mota daga gwarinpa xuwa kubwa ba gaskiya ya mun nisa”.

Dama waya saka ki?, fito ki bani wuri
amma inda zuwa kazaure ne zaki iya ja ai shashasha kawai!

Cikeda ɓacin rai ta koma gidan baya saboda tasan baya son zama shi ɗaya gaba,haka baya son zaman mami a gaba saboda mugun bakin taa.

Gudun tashin hankali yasa bai mata magana ba yaja motar shiru babu mai magana har suka isa babban gida wanda yake a kubwa..,mai gadi ya buɗe nasu gate ya shige da motar tare da neman gefe ɗaya ya aje motar.

Fitowa suka yi duka mami ta miƙa mai wayar shi ,suka fara tafiya…,kai nifa ba zan iya yawon bin ɗaki ɗaki gaisuwa ba tunda ko ba abunda kuka gada sai yawa kamar ƴaƴan geto area(lol).

Bai tanka ba ya riƙe hanun mami suka nufi hanyar da zai sada su da sashin hajiyar shi..
_tabbas babban gida ne da ya amsa sunan shi,aƙalla akwai sashi sashi kusan shida da boys quaters a cikin domin irin compound house ɗin nan ne,matan aure huɗu ke cikjn gidanko wacce da sashin ta,saura biyu na mai gida da sashin baƙi.  Gidan retire commisioner of police MU’AZU BARAU ke nan wanda ya bauta wa ƙasar shi cikin gaskiya da adalci   har ya aje aiki wanan dalili yasa har wana n lokaci ba’a manta dashi baa,yana samun ɗumbin alherai a wurin manyan mutane,yaran shi duksun kawo ƙarfi kowa nada abun hannu gwargwado yadda zai iya riƙe kan shi da iyalan shi sai yasran yan uwa birjik dake tare dashi a gidan da yan jikoki dake zuwa.


A hankali suke taka wa duk inda suka  gifta  harabar gidan sai ya tsaya an kwashi gaisuwa,itakam  ko a jikinta har suka nufi ƙofar da zai sada su da palon hajia lanti da sallama ya tura..,aka amsa masu daga ciki domin sashin kullum a cike yake da yan uwa,ɗiya da jikoki.

Hajia AMINA(wacce aka fi sani da lanti )na zaune saman kujera mai zaman mutum ɗaya sanye cikn lafaya kure shar abunka da baƙar mace doguwa sosai mai jiki sai ya amshi jikinta ainun,baka gane yanayin fuskar ta domin ba kasafai ta faya fara’a ba haka ba zaka kirata miskila ba ita dai haka yanayin fuskarta yake kuma bata cika shiga tsabgar dabe shafe taba musamman sha’anin yara,amma idan ka sake ta buɗe baki tayi magana akan ka!,taka ta ƙare ba zaku taɓa shan inuwa ɗaya ba wanan dalili yasa baa jinta da abokan zamanta har  yanzu da girma ya kama.

Itace matar aure ta biyu a gidan,Allah ya albarkace ta da haihuwar yara shida duka maza(shafi’u,jafar,hamza,umar,muhammad sai usman). Ko wane na zaune lafiya da iyalan shi cikin rufin asiri suna nan nan da ita kullum burin su faranta zuciyar taal,musamman a wanan lokaci da  mahaifin su ƙarfi ya ƙare sai yan uban ci ya tashi a gidan kowa nashi ya sani dalikin da yasa basa nisa da ita sosai kenan,idan aiki ya fitar dasu matan su da yara na tare da ita ko wace n ƙoƙarin faranta mata banda zainab wacce suka samu matsala tun lokacin da taga an kwashi shekaru da auren su bata haihu ba har matar usman da tazo daga baya haihuwar ta uku a yanzu.

Wanan yanayi na fuskar hajia lanti ke saka zainab shiga taitayinta duk lokacin da suka yi ido huɗu koda me tazo gidan sai tayi sanyi laƙwas.

Abunka da dangin miji doctor faiza ta faɗa wa hajia ai matsalar rashin haihuwar daga zainab ne shine dalilin da yasa ta tsane ta uwa uba tun bayan haihuwar mami da abubuwa ke faruwa da zainab ta tashi hanklin kowa lokacin hajia lanti ta tsaurara tsana a gare ta,a nata hasashe haihuwar ce zainab bata so da ɗan ta.

Lura da zainab tayi kowa gidan yi da itayake musamman matan yan uwn mijinta sun samu fuska wurin uwar mijin nasu ko wane lokaci suka haɗu ƙoƙarin gasa mata baƙar magana yake a gaban hajia har shi muhammad  din amma ba mai ƙwaɓar su.

Tun daga nan ta fara ja baya baya da lamarin su cikin ikon ALLAH ma a samu gurbin karatu a nan abuja tana masters  ɗinta wanda ana kamalla wa zata zama cikakkiyar barrister.

Wanan ya ƙara tunzura hajia gani take zainab tafi ƙarfin ɗan nata,tun aga haihuwa ɗaya ƙalau ƙalau yarinya na ƙoƙarin shga shekara sha ɗaya shiru babu wani labari!

Zube wa tayi ƙasa tana kwasar gaisuwa…,sai dai ko kallo bata ishi kowa a wurin ba.

Hasali ma hankalin su na kan muhammad  suka gaisawa duka…,mami ta tsallake su ta haye jikin hajia.

Wanan na ɗaya daga cikin dalilin da yasa sauran matan basa ƙaunar zainab duk da cin kashin da ake nata amma hajia bata da kamar mami cikin jikokin taa! 

Yaran kuwa da sun gano mami kowa ke kama kanshi saboda cin zalin su taje bil haƙi kuma babu wanda ya isa ya kwabe taa.

Granny yunwa nake ji!,shafa kanta tayi.
Waya faɗa maki idan anyi kwalliya ana cin abinci?

Ehhh haka ne bana son ɓata kwalliya na,amma dai zan dha zoɓo irin mai daɗin nan da kike yi.
Ja’ira kawai buɗe firij ki ɗauko yadda zai ishe ki.

A guje ta sauka daga jikin ta tare da tattake ƙafafun sauran yarsn dake wasa a ƙasa ta haura wurin firij a…

Kausar matar babban ɗanta tayi magana”hajia tunda muka iso nake sha’awar zoɓon nan kin hana mun nida keda lalura ma(ta nuna ƙaramin cikin da take ɗauke da shi),sai ga mami ance ta sha yadda zai ishe ta”.

Banza tayi da ita domin ba kasafai ta cika mai da martani baa!,siyama matar umar ta amshe,kin san itace yar gwal cikin jikokin hajia saboda haka bata san babu ba kawai ki haɗiye ƙwaɗayin ki auntyna kya dha shauran ta anjima da yamma idan hajia ta yi buɗe baki.

Haka dai duka cigaba a yaɗa habaici akan zainab wacce ba ita ta hana aba su zoɓo baa…

Muhammad  kam hankalin shi na awurin hajia ko banza ba ya maida hankali akan ƙana nan maganganun mata.

Jug mami ta dawo dashi shaƙe da zoɓo sai cup ta nemi wuri saman kujera ta zauna kamar wata babbar mace sauran yaran suka zuba mata idanu wanda kusan biyu biyu ne a cikj ta girma,uku sa anta ne duka maza sai mata biyu da suka girme ta d namiji ɗaya wanda shine  babba cikin jikokin(abdul gafar) yana can cikin gida.

Ƙare masu kallo tayi duke,yana kallon ko zaku sha ne?,yan warinta da ƙana nan duka amsa da eh!.

Dariyata kece dashi na mugunta!,abu mai sauƙi kowa yaja layi zan baku ai.

Zainab sai zullumi take cikin zuciyarta kada mami taja mata wani tashin hankalin!,ai kuwa suka ja layi duka ta shiga auna zoɓo tana basu a cup suna sha cikin jin daɗi yau baa masu mugunta ba sai ƙyalƙyalar dariya take…,hajia kau abun ya mata daɗi yan jikokinta sun haɗa kan su nan suka shige daƙin baccinta tare da muhammad  dayace yana son magana da ita  mai muhimmanci.

Suna shiga ya nemi wuri a ƙasa ya zauna tareda zayyane mata duk abunda ya faru a daren jiya daga bisani ya nemi alfarma a sanarwa mahaifin su domin a duba lamarin a idon basira ya fara tsorata matuƙa.

Tsaki taja,me akayi akayi zainab?,ita ɗin banza har zaka yadda da makircin ta akan gudan jinin ka?,ina ce nan muka zauna a kai a ɗakin nan kayi mata gargaɗi mai ƙarfi akan aibata mami?,yau kai da kanka kaxo mun da wanan maganar banza haka?,yaushe kazama shashashan namiji ne moha!?.

Wallahi a hir ɗinka ta miƙe zuwa habyar waje tana bambamin faɗa…,ke zainab ki kiyaye ni fa!, bana son makirci da munafuncin banza.

Daidai inda zainab ke zaune ta tsaya,ɗana da jikata sun fi ƙarfin ki,ki koma ki faɗa wa bokan ki asiri ba zai taɓa tasiri a jikin shi ba kwaraki sake sabon shiri daidai nake dake dominnaga ina ɗaga maki ƙafa a dalilin wanan(ta nuna mami) amma bakya gani!,kwana nan zaki nufi gidan ku domin baki isa ki tayar mun da hankali ba oya tattara ta ku tafi bana buƙatar ta a nan,wa yan nan sun ishe ni(ta nuna sauran surukan taa).

Shiru zainab take kanta na ƙasa ko a jikinta domin  idan da sabo ta saba da ire iren wanan cin mutunci daga hajia!,muhammad  sai hakuri yake bata domin da yasan haka zai aru da bai kawo maganar ba!.

yanzu duk sauran yan uwan shi sai ta faɗa madu ayi mahi zaman kanshi,abunda yafi tsana tsoguri tsoma.

Bai wani tsaya ba ganin hajia tayi shiru ya ce da ita zai shiga suleja wani aiki sai yamma zai dawo.

Allah tsare hanyata mashi ya wuce rai ɓace…,kamar jira suke ya fita ai kuwa aka mata chaaaa da ƙananan maganganu!

MAMI kam sai ɗura wa yan uwata zoɓo take tana dariya hankali kwance ko sha bata yi ba tun wanda tasha wurin firij.

Sai da zainab ta faki idanun shi ta miƙe zuwa sashin hajia mariya..
Itace babba a gidan mai faɗa a ji kuma tana da sauƙin kai da faram faram amma fa akwai son girma domin tana iya baki kyautar dubu ɗari kai tsaye domin ta sayi girma wurin kibbutz!,yaranta takwas amma huɗu ke raya biyu mata sune manya a gidan sai sauran mazan jafar ɗin haji lanti ya girme su.

Sashin  ba laifi shaƙe da ɗan mutum musamman mata yan maula duk da mahaifin su muhammad  ba wani shahararren kuɗi ne dashi baa,amma ya tara zuri a abun alfahari masu arziki matuƙa kowa da irin buɗin shi suke riƙe da gidan.

Cike da girmama wa aka amshita sai hidima masu aikin sashen suke da ita aka cika mata gava da ksan ciye ciye.

Bayan gaishe gaishe wuri ya ɗan natsa hankalinta na kan chat da suke da sisterta safiyyah akan abubuwan da suka faru jiya!.

Sai da hajia ta sallami yan maula suka ƙara gaisawa ta tambayeta babu wat matsala ko?.

Tace babu sun zo yini ne taga sashin can mutane sun yi yawa a wuto nan du gaisa.

Allah sarki ai ya shigo kafun ya wuce mun gaisa,ina mai sunan hajia?,tana can suna wasa.

Shiru ya biyo baya daga bisani tace bari ta ɗan kwanta kafin a kira sallah tunda baƙi sun rage. A fito lafiya tayi mata tare da kishingiɗe wa ƙasa chat yayi daɗi.

Dama duk zuwanta gidan sashin hajia mariya take yini,tayi yadda takeso har su tashi wuce wa,nan bacci ya fara ɗaukan ta inda take kwace…,cikin baccin ta hango mami cikin jajjayen kaya saman wani babban tsauni ƙasa kuma yarane wanda ba zasu wue sa ana ba suna kewaye ta tsaunin wuta na tashi a tsakanin su cikin dare ne sosai a dokar jeji!

Ta furta;GREAT ZUMBA!
sauran suka harɗe hannayen su a ƙirji tare da furta;GREAT(cikin tsigar girmamawa).
Ta sake faɗa cikin ɗaga murya;GREAT  YOUNG  FEARLESS!

Suka amshi da;GREAT!.
Gaba ɗaya suka haɗa baki:BLOOD FOR BLOOD,forever we remain loyal,we are pround to be ,we learn to be fearless,rouget and heartless,we are bound to provide security  for ourselves so help us GREAT ZUMBA!.

ZUMBA!ZUMBA!!ZUMBAAA!!!

Sai ga sauran yan yan mami data ba zoƁO an saka su tsakiya tare da kece wa da dariya mai ban mamaki suna ta kuka!!!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button