Labarai

zan tare a dajin Sambisa inna gaji Buhari Manjo Hamza Al Mustapha

Najeriya ta kara samun dan takarar shugaban kasa, ya kuma bayyana munufofinsa masu karfi a zaben 2023.

Hamza Al-Mustapha ya bayyana maunfofinsa, inda yace abu ne mai sauki a gare shi ya magance matsalar tsaro.

Ya kuma ce, dama kawai yake jira, da zarar ya zama shugaban kasa zai koma Sambisa domin gano matsalolin Boko Haram da kuma dakile su.

Tsohon soja mai jini a jika, kuma tsohon dogarin shugaban mulkin soja marigayi Janar Sani Abacha ya bayyana abu na farko da zai fara yi idan ya zama shugaban kasar Najeriya bayan zaban 2023 da ‘yan kasar ke shirin yi nan kusa.

Manjo Hamza Al-Mustapha, ya ci alwashin karar da ‘yan ta’addan Boko Haram, inda yace cikin watanni shida zai yi hakan, domin kuwa dajin Sambisa na jihar Borno zai tare bayan gaje kujerar Buhari domin gane wa kansa hanyar da zai bullowa lamarin.

Al-Mustapha ya bayyana hakan ne bayan bayyana aniyarsa ta zama shugaban kasa a karkashin inuwa jam’iyyar Action Alliance (AA), kamar yadda kafar labarai ta BBC ta tattaro.

A bayanansa, ya ce zai shafe mako guda a dajin na Sambisa domin gano wasu lamurra da suka cancanta ya mayar da hankali a kai domin tabbatar da Najeriya ta yi sallama da matsalar Boko Haram.

Daga Hausa Legit 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button