NOVELSUncategorized

TARAYYA 15-16

Page 15
  
Shiru sultan yayi yana sauraren bayanin Jakadiya ya lumshe idanuwansa ya bude, +
Allah yataimaki sultan sarkin dayafi sarakunan qarninsa

Haryanxu baiwa rumanah bata zama cikakkiyar baiwa ga yarima ba””””””
Sune abinda Jakadiya tafada yasaka kallonta kafin cikin 6ayyanarda ikonsa yace,
Asanarwa yarima na sauke zaraah daga yau nabawa adama sultana kuma na dakatarda ita daga matsayinta na matar sultan harsai ranarda ya hada shimfida da baiwar.
Wani irin yawu Jakadiya ta hadiye cikeda rawar murya da girmamawa tace,
Angama da yardar Allah.
Tana fita aka isarda saqon ga yarima.
Aje cup ‘din hannunsa yayi tareda rintse idanuwansa dasuka canza lokaci ‘daya yabudesu yakalli ammynsa dake zaune taredashi a dining din palonta sunacin abinci.
Lumshe idanuwa sultana tayi ahankali tareda daukesu daga maheer daya qura mata sbd karya gano halinda tashiga ta miqe ahankali ta nufi hanyar bedroom dinta ya riqo hannunta tareda dawo da ita ya rungume ahankali.
Zamewa tayi takallesa tareda sakin murmushin dole cikin kulawa tace,
Karka takura kanka kayi abinda bakada ra’ayin so zan iya qarasa rayuwata akan wannan hukuncin nasa matuqar baka cikin takura maheer…..
Ahankali yabude baki cikeda kulawa yace,
It’s okay ammy zanyi abinda yace ba buqatar ki damu da idan inaso ko banaso.
Bazaka kallesa ka gano 6acin ransa sbd kyakkyawar fuskarsa koyaushe bata nuna 6acin ransa amma Tsananin 6acin ran dayake ciki ayau yafi na kullum sbd sultan nason ganin iyakarsa koyaushe da mahaifiyarsa yake amfani Dan cimma buqatarsa garesa Dan yasan aduniyarsa babu kamar mahaifiyarsa agurinsa.
Yau wani irin sabon turare Jakadiya tasa aka kawo daga gidan turaren dake qasar Wanda yafi kowane turare dadin qamshi da hanawa duk namijin daya shiga hancinsa nutsuwa.
Farar rigar bacci yau aka zabo mata daga closet tasaka akaro na farko da aka hanata saka bra jakadiya dakanta ta bita koina da turaren ta feshe kafin suka fito.
Kamar koyaushe tana shiga Jakadiya ta juya ta fice daga part din.
Ahankali ta nufi gurin kwananta.
Hasken blue and red bulb ya gauraye dakin.
Cak ta tsaya tsakiyar dakin bugun zuciyarta na canxawa har kirjinta yana dagowa amma takasa juyowa.
Akaro na farko daya qurawa wata mace daba matarsaba lazy eyes dinsa,
Dogon wandon kayan baccine kawai ajikinsa fari qal mai matuqar santsi da laushi,
Wani irin murdadden namijine maji qarfi da kyawun gabbai sbd yawan yin geam ya bude duk wani qarfi na jikinsa.
Abayanta taji tsayuwarsa numfashinta ya tsananta fita hannuwanta da qafafunta suka fara rawa ta rintse ido.
Bayanta dayake fari qal yaqurawa ido da gashinta daya rufe wuyanta yanaji qamshinta na shigarsa yanason ta6o wani  bangaren na sha’awarsa akaro na farko dataji muryarsa cikin wani irin taushi da aji yace,
Juyo.
Juyowa tayi ahankali  tareda sunkuyar dakai tanajin wata irin muzanta na shigarta sbd tanajin kallon dayake bin jikinta dashi na qyama.
Kusan atare suka rintse ido suka bude sai acikin idanuwan junansu ta mayarda nata ta rufe da sauri tareda sunkuyar dakai.
‘Dauke idonsa yayi tareda juya mata baya.
STORY CONTINUES BELOW
‘Daga qafa tayi duk ilahirin jikinta rawa yakeyi zata wuce yariqo hannunta.
Barin jikinta numfashinta ke qoqarin yi tayi saurin Jan boyayyan numfashi yadawo jikinta saidai tuni qafafunta suka kasa riqeta ta zube qasa kan gwiwoyinta tana dafe qirjinta dake bugawa da qarfi haryana mata zafi.
Tattara numfashi tayi ta dafa table din dake tsakar dakin ta miqe har lokacin numfashinta bai daina fita da sauriba jikinta bai daina rawaba ta fuskacesa kanta na sunkuye.
Sake kafeta yayi akaro na biyu.
Hannu ya daga yamatso da ita sosai har kirjinsu na haduwa musamman idan numfashinta ya taso sosai qirjinsu ke haduwa.
Ahankali yadauke fararen idanuwansa daga fuskarta zuwa qirjinta dake gugar nasa.
Hannu yadaga ya dora akafadunta yana kallon idanuwanta dake rintse hawaye na qoqarin fitowa cikinsu.
Ahankali ya zame siririn hannun fingilalliyar rigar dake jikinta data gama bayyana komai na surar jikinta.
Zamewa rigar tayi tafadi qasa
Rintse idanuwansa yayi tareda ja baya ya juya tareda kallon jikinsa ganin tsikar jikar jikinsa ta tashi abinda baitaba yiba kenan tun tashinsa.
Bakin gadonsa ya isa ya zauna tareda zamewa ya kwanta rigingine ya rufe idanuwansa batareda yasake kallon sashen datake ba.
Daukar rigarta tayi tamayar jiki amatuqar sanayaye ta matsa inda take rabewa ta lafe hawaye suka gangaro mata ta goge ahankali tareda rufe ido.
Har asuba tayi babu Wanda yayi bacci acikinsu tanajin anyi kiran farko ta miqe ta nufi qofa tana fita Jakadiya na isowa taqare mata kallo bataga alamar komaiba tasaki ajiyar zuciya afili kafin tamiqa mata doguwar rigar tasa suka wuce.
Yau ko palon farko bai iya fitaba sbd bayason magana ko ‘daya yau sultana ma saidai yayi mata massage
Fruits ‘dinda ke cikin small fridge 
Din bedroom din kawai ya iyasha Sam yau ko apatite bayada.
Yau rashin sukuninta yafi na kullum sbd har dare yasakeyi jikinta bai koma daidaiba ko cup tariqe hannunta rawa yakeyi data duba taga dare yakusa yi sai gabanta yafadi saidai tana bawa kanta hkr da qwarin gwiwa
Babu abinda takeson gani yanxu kamar nuratu,
Tana tsananin buqatar Wanda zatai magana dashi koda so dayane ayini.
Da daddare tun gurin kaita Jakadiya ta lurada yanda take cikin tsananin damuwa tashareta suna isa tashige itakuma tadawo.
Zaune yake akan cauch ‘din datake lafewa gefen yana aiki da apple laptop,
Fararen kayan baccine ajikinsa as usual ya miqe qafarsa akan glass center table dake gaban couch din.
Ba haske adakin sosai saidai tana iya ganinsa yana iya ganinta.
Tsayawa tayi takasa qarasawa kujerar sbd ganinsa agurin.
Aikinsa yakeyi hankali kwance batareda yanuna yasan da alamar wani mutum adakinba bayan kansa.,
Saida yagama ya ajiye laptop din tareda miqewa ya nufi lafiyayyan royal bed dinsa ya kwanta Kansa na sarawa.
Saida yakashe wuta yana kalli ta qarasa ta kwanta qasa ahankali.
Gurin datake yaqurawa ido itama ahankali tabude idanuwanta ta qurawa gadonsa ido akaro na farko
Duk da akwai duhu adakin.
So kusan hudu yana gwada ta6ata kozai iya kwanciya da ita amma Sam zuciyarsa na qyanqyami da hakan Wanda hakan yayi matuqar tunxura sultan yayi wani irin fushi mai muni tareda yanke wani irin mummunan hukunci aransa yace adaren yau idan yarima bai keta budurcin baiwa rumanah ba  washe gari su saurari hukuncinsa.
Koda saqon yaje masa baidamuba matuqar hukuncin kona menene bazai shafi ammynsaba.
Jin sanarwar abinda sultan yafada ya tsananta damuwarta da quncinta saidai batada Wanda ko fira dashi bare Wanda zata tattauna damuwarta dashi shiyasa taqara rungumar qaddararta tana jiran hukuncin yanda za’a cigaba da yanda akaso da ita.
**
Sama sama Cikin bacci take jin kukan yara da manya,
Mazaje da mata tareda wata irin iska mai daukeda hayaniya na amsa kuwwa ako ina na cikin masarauta da wajenta koina na amsawa a fadin garin.
Bude ido tayi ahankali tareda kallon inda take tayi ido biyu da maheer duqe agabanta yana idanuwansa sunyi wani irin mummunan ja wata irin damuwa da tashin hankali tareda neman mafita take hangowa acikin idanuwansa.,
Da sauri ta sauko daga gadon taji qafafuwanta sun nitsa cikin ruwa ta sauke idanuwanta ta duba a firgice tayi baya jikinta na wata irin rawa ganin jini kwance yana gudana.
Kallon maheer tayi da sauri ya girgiza mata kai cikin wata irin murya mai ciwo da sanyi yace,
mineelik assultana the redblood Queen.
Zaro idanuwa tayi cikin tsananin tashin hankali jin abinda yace,
Rawa jikinta yadauka
Ihun datake ji tun farko yafara yawa cikin kunnenta yana neman gigitata ta fita da sauri tafara gudu cikin jinin daketa gudu kamar ruwa ako Ina na bangon masarautar stains ne na jini,
Tana fitowa babban filin harabar palace din taga gawarwaki harbabu gurin saka qafa su zaka taka dole ka wuce ga ruwan sama dake sauka sosai Wanda suke qarawa jinin dake zube koina gudu.
Wata irin busa taji anyi wadda ta amsa kuwwa koina
Nan take taga mutane nata taruwa kamar tururuwa sbd mugun yawansu,
Haka suka cigaba da taruwa suna kallon wata babbar qofa dake been sama inda sultan ke fitowa idan zai fito yayi magana inda kowa ke iya ganinsa.
Kutsawa tafarayi Cikin mutanen tana bin mutanen da kallo
Nan tafara girgixa kai ganin ba jama’ar daularsu bace kawai hardana wasu daulolin,
Wanda alamu suka nuna da qarfin mulki aka mallakesu ana mulkarsu harsu har sarakunansu.
Saida aka taru harbaka iya qwaqwaran motsi sbd taro da yawan jama’a aka sakeyin busa nan guri yayi tsit ko kukan tsunstu babu kowa yamaida kallonsa ga qofarda sultan zai fito itama tayi saurin kallon qofar daidai lokacinda aka wangale qofar wadda tafi kama data zinari sbd kyalli.
Cikin wata irin doguwar Riga maroon colour tana ja da qasa tafito daga cikin qofar ta bayyana
Gashinta azube yake har bayanta yaji adon sarkokin zinari nakai har zuwa kafadunta hakama wuyanta sarkace har saman cikinta ta zinari,
Wani irin kyau da kyalli take fitarwa daidai hannuwanta a lalace suke kaca kaca da jini har jikin rigartama haka
kujerar karagar mulkin mineelik Wanda keta tsiyayar jini wasu irin samudawan guards suka ajiye mata tasaki wani irin qayataccen murmushi zata zauna……
Cikin wani matsanancin ihu takira sunanta da qarfi tana cewa,
Rumanahhhhhh karki zauna a wannan kujerar……rumanahhhhh
Zama tayi cikin wani irin iko da mulki nan gari yadauki ihun sunanta.
Amatuqar  gigice sultana ta zabura daga baccinta tana tareda lalubar bedside lamp takunna da sauri jikinta na muguwar karkarwa tafara karanta innalillahi tana hada wani mugun gumi.,
Wannan mafarkin nata babu alkhairi acikinsa,
Meya hadata da wannan mummunan mafarkin?
Tsoro da fargaba taji yana shigarta tayi saurin saukowa tafada toilet tayo alwala tazo tafara jera nafiloli kafin asuba tayi.
Har gari ya waye bata sake ko kwanciyaba bare rintsawa,
Abinda tagani amafarki tamkar wani gargadine ga abinda suke shirin  yiwa rumanah bata fatar ko acikin bacci tasake irin wannan mafarkin bare ya tabbata.
Dan haka ta yanke shawara komai zai faru shirye takeda daukar  hukuncin sultan.
Qarfe goma sha ‘daya na rana saqon kiran sultan yazo gareta babu bata lokaci ta miqe cikin shirinta da adonta ta nufi part dinsa kuyanginta na biyeda ita,
Duk inda ta gifta kafin ta qaraso anrabe anxube qasa ana gaidata cikin matuqar girmamawa harta isa tun a qofar palon farko suka dakata itada Jakadiya data fito tarbonta suka qarasa.
Tana isa jikinta yayi mugun sanyi sbd ganin yanda kowa ya dauke wuta sai mizurai akeyi sbd ran sultan ya baci kuma kowa yasan hukuncinsa ba sauqi ba kyau haka itama ta isa kujerar dake matsayin tata tazauna bayan ta kwashi gaisuwa.
Maheer ransa amatuqar bace yake sbd baisan hukuncinda sultan zai yankeba akan ammynsa.
Cikin kakkaisar murya yakalli Jakadiya yace,
Inason jin dalili qwaya ‘daya daya daga yarima Wanda ya hanasa cika umarnin sultan dinsa.
Cikin rawar murya Jakadiya takalli yarima zata maimaita masa abinda sultan ya tambaya batareda yakalli ko dayansuba kai tsaye yace,
Banada sha’awar kowace mace bayan wadda igiyoyin aurena suke kanta.
Wani numfashin bacin rai sultan yafitar yana kallon yarima sbd yasan daga yau hukuncinda zai yanke akansa yagama da rayuwarsa gaba daya cikin isa da mulki yabude baki yace,
Jakadiya atambayesa yana buqatar qarin lokaci kokuwa shikenan……
Cikin tsananin dauriya da danne fargabarta da fargabar abinda zai biyo bayan abinda zatayi tabude baki tace,
Ina neman afuwar sultan amma baiwa rumanah ta haramta garesa daga yau sbd na ‘yantata daga wannan lokacin harzuwa qarshen rayuwarta,
Daga yanxu ita ba baiwa bace sbd haka ta haramta ga kowane namiji idan ba mijin aurentaba.
Cikin wani irin mugun mamaki da 6acin rai dabai taba yiba yake kallonta jin abinda tafada,
Ta ‘yanta baiwarda yabada umarnin yarima ya kwana da ita kenan ‘danta takare daga aikata abinda baiso
Tabbas zasu ‘dandani hukuncin sultan daga ita har ‘danta.
‘Dagowa yayi yakalli wazirinsa cikin wani irin yanayi na nuna rashin damuwa yace,
Ta ‘yanta baiwarta sbd ta rahamtata ga ‘danta sbd bayaso nikuma zan halasta masa ita ayau sbd umarnin sultan baya bin iska,
KUJE ABADA SANARWAR ‘DAURIN AUREN YARIMA MAHEER IBN ABDULSHAMS ABDALLAH DA ‘YANTACCIYAR BAIWA UMMU-RUMANAH BULAMA nanda awa biyar duk Wanda baizo ya shaida ‘daurin aurenba nakoresa daga qasata sai bayan shekara biyar yadawo.,, 3
SULTANA ZAARAH BAYAN ‘DAURIN AURE ZATA KOMA GURIN IYAYENTA BAZATA DAWOBA SAI MATAR YARIMA MAHEER RUMANAH TA HAIHU.
#mamuhgee
Page 16
Not edited.⚠ +
Wani irin kallo sultana ta ‘dago tayi masa cikeda mamaki da takaicin abinda yake shirin yi kafin ta bude baki tayi magana cikeda nuna isarsa da matsayinsa yace,
Lij(sadaukin kuma amintaccen mayaqin meneelik) duk wanda ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin sultan ko a fuskane ko wanene shi arabasa da abinda yafiso ajikinsa,
Idan nace ko wanene ina nufin kowanene,
Jakadiya kije ashirya sabuwar surukar sultan nanbada jimawaba zata zama uwar magajin meneelik. 2
Yana gama fada ya miqe yashige palonsa na hutawa tareda manyan masarauta dazasu tattauna wani abin,
Wasu majiya qarfin samudawa suka tsaya qofar Dan bata tsaro.
Kai tsaye ya miqe yabar palon batareda fuskarsa ta nuna meke cikin zuciyarsaba.
Sultana ma miqewa tayi jikinta amatuqar sanyaye zuciyarta cikeda takaici da tunanin rashin ganin amfanin ‘yantawarda tayiwa rumanah tunda hakan baisa ta tsirar da ita daga masifar datake gudar mataba ta haihuwar namiji a wannan masarauta ta mineelik. 1
Jakadiya kuwa wani irin zufa take yarfewa Tana qoqarin ganin ancika umarnin sultan saidai itama damuwarta da tsoronta yahana farincikinta wanxuwa musamman idan taduba yanayin tsoro da fargabar dake yawan samunsu idan sukayi tunanin rabon dazai shiga tsananin yarima da rumanah., 1
Wannan masarauta batada tarihi mai kyau,
Jinin mutanen da ake kashewa yananan yana bibiyar duk wani hakkinsa,
Masiface acikeda masarautar wadda babu Wanda yasanta saisu dasuka ginu acikinta
Har abada bazata ta6a yiwa rumanah fatar shiga cikin jerin wainda masifar zata cigaba da shigarsuba aqarshe tabasu qarshe mai matuqar tausayi da kokawa saidai tasan bawa baya wuce qaddararsa,
Duk dubararsu da qoqarin kubutarda ita idan Allah yace tana cikin masu wannan mummunan qaddarar saita shiga. 1
Zubewa sultana tayi kan daya daga cikin kujerun palonta na farko sbd bazata iya qarasawa na biyunba tareda ‘dagawa kuyanginta hannu nan suka watse cikin girmamawa.
Dafe goshinta dake daukeda adon sarqar zinari tayi tareda rufe ido tarasa wane irin hali zuciyarta take ciki sbd takasa riqe tunani ”daya dazatayi cikin biyu auren maheer da rumanah kokuwa korarda sultan yamata gefe ‘daya kuma tsoro ne fal yafi cika mata zuciya.
Ya Allah kadubi maraicin rumanah kazaba mata kyakkyawar rayuwa agaba.
Tana cikin wannan halin Jakadiya tashigo ‘yan mata biyar na bayanta ‘daukeda manyan trays suna qyalli kamar zinari suka jeru sanku sunkuye.
Kallo daya Jakadiya tayiwa sultana ‘din tasan tana cikin tension murya asanyaye tace,
Allah taimaki sultana anshirya zuwa gurin shirya sabuwar amaryar yarima maheer sa albarki akazo karba.
‘Dago fuskarta datai ja tayi takalli jakadiya batareda tace komaiba ta miqe tashiga bedroom dinta tafito da wani madaidaicin akwati yana kyalli.
Zama tayi tareda aje akwatin batareda takalli jakadiya ba murya ba kuzari tace,
Allah yasawa aure albarka.
Amin jakadiya tace tareda kai hannu tabude akwatin.
Sarqoqin zinari ne masu nauyi da marasa nauyi nakai dana qafafu taredana wuya da awarwaro har kusan basa qirguwa.
Hannu Jakadiya tasa tana zarosu tana zubawa acikin tray dinda suka shigo dasu harsaida tray din yacika suka fice,
Sashen adama suka isa tana zaune cikin royal kushins din dasuka qayata palonta cikeda girmamawa aka iso mata da saqon zuwansu Jakadiya tace sushigo. 1
‘Yan matanda ke bayan Jakadiya ‘daukeda manyan trays din takalla cikeda mamaki sbd alamu na sakawa aure albarka zaka bayar.,
Wane zaiyi aure kuma ayau batareda tasaniba?
Lallai ana wasa da ita amma karsu damu da zarar ta ‘Dora mazaunanta akan kujerar mulkin mineelik tayi alqawarin bawa dabbobin dake zagaye da qasar naman wainda suke wasa da alamarinta.
STORY CONTINUES BELOW
Cikin girmamawa Jakadiya ta katseta da cewa,
Sultana zaarah ta ‘yanta baiwarta ummu-rumanah ayau kuma ayau sultan zai aurawa yarima maheer ita akan sadaki tiren zinari,
Sultana ta bada nata tiren saka albarkar aure saurake gimbiya adama ina fatar ba’a shiga cikin lokacin hutawarkiba.
Cikin wani irin yanayi na mamaki ta kalli Jakadiya tace,
Aure tsakanin yarima da baiwa?
Kozansan dalilin wannan auren na gaggawa?
Allah yataimakeki maganar dai ‘dayace.
Rintse ido tayi tareda Jan numfashi cikin takaici
Sam sultan bazai bari tashaqi numfashi mai dadi ba sbd wannan masifar tasa tason haihuwar magajin mineelik,
Meyasa koyaushe yake son 6ata mata aiki idan yayi nisa,
Tana qyalewane ta lafe sbd bokanta yace mata sa’arta ba yanxu takeba saizuwa gaba takwantarda hankali tajira sbd ba’a taba haihuwar namiji ba a masarautar yayi duba yaga tabbas mace ce zatayi mulkin mineelik bayan sultan takuma tabbatarda itace macenda zatayi mulki amma badan hakaba da tuni tasaka anbinne sultan da ransa takaiga cikar burinta. 1
Murmushi tasaki tana ‘dauke gira ‘daya tace,
Allah yayiwa aure albarka.
Sarkar jikinta data kanta taredata qafafunta tasa baiwarta nuratu ta cire ta daura akan tray din suka miqe suka fice.
Nuratu duk ilahirin jikinta rawa yakeyi gurin cire mata sbd tsananin farin cikin data shiga jin zancen,
Ta matsu tagama yiwa sarauniya adama yankan fruits taje tafadawa mamani sbd yau tun safe adama tasakata aikin abinci kusan kala biyar sbd ‘yarta meenah zata zo hutun makaranta daga Sydney.
Part dinsa ya isa cikin wani irin yanayi da babu mai iya gano maike zuciyarsa ya zauna kan sofa tareda rintse idanuwansa yana shafo sumar kansa.,
Miqewa yasakeyi ya nufi bathroom yashiga cikin bathtub bai tsaya bata lokaciba yayi wanka yafito ya zauna gaban mirror yana goge jikinsa,
Shiri yayi cikin Ethiopian royal kaftans black and golden wainda yasaka ranar daurin aurensa da suhailat.,
Turare yafesa tareda saka takalmi ya fesa turare tareda gyara gashinsa mai ‘Dan tsawo ya ‘daure tsakiyar kai yasaka hula batareda yakalli kansa a madubi ba ya nufi qofa ya fita inda guards kusan guda goma da fadawan sultan suke jiransa Dan masa rakiya har gurin daurin auren.
Zaune take kan kujerar mirror ita kadai kamar koyaushe shiru tayi nisa cikin tunani tareda qurawa kanta ido.
Qura mata ido Jakadiya tayi kafin tayi gyaran murya tareda yiwa ‘yan matan alama da ido cikin nutsuwa suka zo gaban rumanah data miqe cikeda ladabi tana gaida Jakadiya suka Jere matansu.
Sam bata shiga ko saka kanta ga duk abinda tasan bai shafetaba shiyasa ko inda aka ajiye kayan bata kallaba ta sunkuyar dakanta tana jiran umarni daga jakadiya sbd tasan dole akwai abinda yakawota.
Fuskarta Jakadiya take kallo tace,
Ayau sultana zaarah matar sultan abdulshams sarkin masarautar mineelik ta ‘yantaki ummu-rumanah bulama sbd ki auri ‘danta ‘yarima maheer Wanda za’a daura miki aure dashi yanxu nanda mintuna qalilan.
Kallon Jakadiya tayi da kyau taga fuskarta babu wasa ko raini yasa tayi qasa da kanta sbd tasan babu abinda zaisa Jakadiya tafadi abinda bahakaba sbd dokace a masarautar duk Wanda yayi kuskuren qarya aka ganosa allurar dabazai qara maganaba ake masa shikenan yazama kurma shiyasa duk tsanani duk wuya ba’a qarya a mineelik. 1
Shiru kawai tayi sbd haryanxu batajin kanta amatsayi na an ‘yantata tunda za’ayi auren manufa da ita,
Aurenda tasan dalilinsa Dan haka babu abin murna a ‘yancinta.
Riqota sukayi zuwa toilet batai musuba jiki asake tabisu.
Wani irin gyara na musamman aka hau yimata idanuwanta arufe har aka gama suka fito nan aka zaunar da ita gaban madubi nan wasu mata suka shigo su hudu cikin wani irin ado irin na al’adarsu suka fara gyara mata fuska cikin qanqanin lokaci suka tsara wata irin kyakkyawar kwalliya a fuskarta,
Ana gamawa kallo ‘daya Jakadiya tayi mata taji numfashinta ya sarqe tayi saurin sakin tari tana dafe qirjinta.
Wata irin doguwar Riga fara qal mai adon wasu irin golden stones masu matuqar kyau da qyalli aka saka mata tareda daure dogon gashinta tsakiyar kanta kafin aka saka mata wata irin kyakkyawar doguwar sarqar zinari tareda awarwaronta sai wata irin kyakkyawar sarqar kai data qafafu kafin aka lullubeta da dogon mayafin daya fito daga hannun sultana.
 24
Suna gamawa Jakadiya tayi gyaran murya nan dukkaninsu suka miqe tareda miqarda rumanah data zauna sai yanda akayi da ita itadai tasan da dah da yanxu duk ‘dayane babu wani banbanci arayuwarta.
Kai tsaye part din sultana aka nufa da ita inda ana gama ‘daurin aure itace zata kaita ga sultan yasawa aure albarka.
Kamar yanda sultan yabada umarni bayan awanni biyar cif dubban jama’ar qasar da maqwaftanta sun shaida ‘daurin auren yarima maheer abdulshams da ummu-rumanah bulama akan sadaki silallan zinari guda hamsin.
Ana gama daurawa yarima sultan yafara kallo cikin wani irin yanayi na murmushi.
Yarima har lokacin baiyi magana ko daya da kowaba har aka watse.
#mamuhgee

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button