NOVELSUncategorized

KWAI CIKIN KAYA 2

*_Typing????_*
   
          *_????ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_          
                  *_Bilyn Abdull ce????????_*

*_Ban yarda wani yaymin amfani da littafin nanba ta kowacce hanya, komin ƙanƙantarta, inkuwa hakan ta kasance ban yafe ba☹️._*


_Na sadaukar da wannan littafi a gareku auntys ɗina, dan kune taurarin da Bilyn Abdull ke kallo a duniyar rubutunta, da ku kuma zan cigaba da alfahari *Aunty Fareeda Ado gachi & Aunty Rahama Abdul-Majeed (writer mace mutum)*, alkairin ALLAH ya kai muku a duk duniyar da kuke har gadon barci._????????????????

*Wattpad* ➖ _BilynAbdull_????


*______________________________________* 
                *_BOOK ONE_* 
                    _Shafi na biyu_
*______________________________________*


…………Motsin ruwan wankansa ne ya farkar da Shahudah, tunda ta yaye bargon da ga fuskarta nake tsarkake sunan ALLAH buwayi gagara misali da ya halicci wannan ƙyaƙyƙyawar baiwa tasa. Lallai Shahudah ƙyaƙyƙyawace wadda zamu iya sakata a jerin farko na ƙyawawan mutane, gata fara tas tamkar wata aljana.
       Har lokacin bata yaye bargon da ga jikinta ba, kamar yanda alamu suka nuna bata da niyyar tashi ma. 
    Kusan mintuna arba’in da shigarsa bayin sai gashi ya fito ɗaure da tawul ruwan sararin samaniya, yayinda ya rataya ƙarami fari a wuyansa, ya kama can ƙarshen tawul ɗin yana goge gefen kumatunsa. 
        Shahuda da har yanzu take kwanci ta a hankali ta buɗe ƙyawawan idanunta ta sauke akansa, hakan yayi dai-dai da kai nasa duban gareta shima. Kuma tamke fuska yay yana kauda idonsa a kanta tare da nufar mirror kansa tsaye. Kamar yanda baiyi magana ba itama sai bata ce uffanba sai binsa da kallo da takeyi. 
     Duk da Jawaad naji a jikinsa kallonsa takeyi bai juyoba, amma yana kallonta ta cikin mirror, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Kinyi salla?”.
       Ɓata fuska tayi tana kuma narketa alamar son yin shagwaɓa, “Haba bb, kamun laifi maimakon ka lallasheni da ban haƙuri saika wani faramin tambaya”.
     Duk da ya jita sarai sai ya share tamkar bai jiba, ya cigaba da shafa mansa yana lullumshe ido saboda ciwon da har yanzu ya keyi, sauƙinsa ma ruwannan da ya sakarma kan ya ji daɗinsa sosai gaskiya.
     Ba ƙaramin ƙunar zuciya ta kama Shahudah ba jin Jawaad ya shareta, ta turo baki gaba tana yaye bargon da take ciki. 
     Masha ALLAH na sake ambata ganin haɗaɗɗun kayan barcin da take sanye a ciki, sun mugun mannewa da farar fatarta, tare da zama ɗam jikin surarta tamkar dan ita aka halicci figigiyar rigar barcin da kaɗan ta gota mazaunanta, siririyace sai dai jikinta a murje yake alamar hutu, ba kowa ne zai ga Shahuda ya yarda ta haɗa jini da HAUSA FULANI ba, dan komai nata yafi kama da na masu jajayen kunnuwa…..
       Saurin janyeta yay da ga jikinsa jin ta rungumesa ta baya yana kuma ɓata fuska, a matuƙar harzuƙe ya juyo yana sanya jajayen idanunsa cikin fararen nata masu cikar gashi da gira baƙa wulik a sama. Sam bazata iya jurar kallon cikin idonsa ba, dan haka ta wani yi farr da nata cikin salo irin na manyan yara da ke taƙama da wayewa.
     Hanya kawai ya nuna mata ba tare da yace uffanba.
      Yanzu kam ranta yakai maƙura da haushin wulaƙancin Jawaad, dan haka ta yamutse fuska cikin tsiwa ta taka gaban gadon ta saka silifas ɗinta masu taushi ta nufi hanyar fita.
     Sai da ta kama hannun ƙofar ne ta tsinkayo Jarumar muryarsa na faɗin, “Saura idan kinje canma ki sake kwanciya kar kiyi sallar”.
      Harara ta watsa ma bayansa da ya juya mata ta fice tana ƙunƙunin da ita tasan mi take faɗa.
    
       Bai sake bi ta kanta ba ya kammala abinda zaiyi a gaban madubin ya nufi Wadrobe ɗinsa ya saka boxer kawai ya fito falo. Kayan tea da ke ajiye saman D/table ya nufa, ya ɗauki kofi ya haɗa komai kafin yaje ga disfensa ya matso ruwan zafi dai-dai buƙatarsa. A haka ya koma bedroom ɗinsa yana juya cokali cikin kofin shayin da keta tururi.
        Zama yay bakin gadon yana shan shayin a hankali, ko zafinsa baya ma damuwa da shi. A da can sam baya shan shayi sosai, ya kan sha amma ba ko yaushe ba saboda baya cikin abinda ya damesa, amma tun bayan auren sa da Shahudah suka ƙulla abota da tea, a yanzu baya da abincin da ya bama muhimmanci a rayuwarsa irin shayi, tun yana sha akan dole harya fara zame masa jiki, inma bai sha ba sam baya jinsa dai-dai, a baki sunan kawai yana da matane, amma a aikace ita da hotiho babu banbanci, dan babu wani abu na matan kirki masu daraja da Shahudah ta iya, banda tsagwaron son jiki da son hutu babu abinda ta tara, a ɓangaren gyaran jiki dai kam gwana ce, dan ƴar gayuce ta gani kasheni, sai dai sam babu tarbiyya mai birgewa da akasan ƴaƴan musulmai da ita, komai nata kwaikwayone daga jinin yahudu da nasara, salla wannan sai yayi mata jan ido take yinta, daga lokacin da yay nisan kiwo kuwa a aikinsa baisan wace wainar take toyawa ba a ɓangaren bautar ALLAH….
      A hankali ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yana ajiye kofin hannunsa saman durowan gefen gadon, magani ya ciro a ciki ya sha kafin ya haye gadon da ke manne da ƙamshin turarensu ya kwanta yana jan bargon ya lulluɓe har kansa.

           Koda Shahuda ta koma ɗakinta sam bataji gargaɗin Jawaad ba akan tayi salla, sai ma gado da ta faɗa tana ƙunƙuni wai baza tayin ba, a haukanta da gajeren tunani tunda Jawaad ya ɓata mata rai to itama saita ƙuntata zuciyarsa da ƙinyin sallar da yace tayi, dan haka tai kwanciyarta barci ya sake kwasheta saboda sanyin garin na ruwa da aka maka a daren jiya.

      
ALLAH ya ƙyauta to, saikace kabari ɗaya za’a saki da Jawaad ɗin Shahuda????? kokuma shike bada sakamako idan anyi sallar????????‍♀️?, ALLAH ka rabamu da wayewa mara amfani⛹????‍♀️.


                  ★★★★★★★

       Ring ɗin wayarsa ne ya farkar da shi da ga nannauyan barcin da yay nisa a ciki, ya janye bargon da ga kansa da ƙyar tare da miƙa hannu saman dirowan gefen gadon ya ɗauki ƙaramar wayarsa da ke vibration. Ba tare da ya duba wanene ba ya ɗaga kawai ya saka a kunne yana sake maida idanunsa ya lumshe. Tsawon seconds arba’in yana sauraren mai maganar da ga can, kafin ya furta “Ok sir” cikin nutsatstsiyar muryarsa da ke gauraye da barci. Ƙarƙashin filon ya tura wayar yana sake juya kwanciyarsa hankali kwance, sai faman ɓata fuska yake na jin takaicin katse masa barci da akayi. Sai da yaja kusan mintuna uku sannan ya ture bargon yana jan dogon tsaki, ƙaramin agogon dake gefen dirowan gadon ya kalla, ⏰11:29am, numfashi ya sauke a hankali dan sam baiyi tunanin barcin nasa yayi dogon zango haka ba, tashi yay ya sauka daga gadon gaba ɗaya.
    Sosai ƙyanƙyamin bayin nan yakeyi, dan yakai kusan kwana huɗu kenan babu wanki, tun randa Batool tazo bai sake ganin gyara ba saboda tsabagen lalacin matar gidan.
     A ɗarare yay abinda zaiyi ya fito ba tare da ya sake wanka ba, baƙar jallabiyarsa mai dogon hannu ya ɗauka ya zura kawai da silifas ya fice zuwa ƙasa.

     Sai sha ɗaya saura Shahudah ta tashi a sabon barcin da ta sake komawa, sai faman ɓata fuska take tamkar ance   ta tashi dole ne, rigar barcinta ta zame tare da sakinta a tsakkiyar ɗakin tai tsaye tsirara da ga ita sai pant wanda shi da babu duk ɗaya, hankalinta kwance ko tunanin bayan jinsinta akwai na aljanu da ido baya ganinsu a ɗakin batai ba, a haka ta nufi bathroom.
    Tsawon lokaci ta ɗauka a ciki kafin ta fito ɗaure da wani mitsitsin tawul kalar ruwan hoda, shima tana zuwa gaban mirror ta sakeshi ƙasa, a haka ta shafa mai kafin ta buɗe Wadrobe ta ɗauki doguwar riga ɓaƙa ta saka, tare da naɗa ɗankwalin rigar ta ɗau abin salla ta shinfiɗa.

    ????tsantsar mamaki da al’ajab sun rufeni ganin sai yanzune Shahudah zatai sallar asuba, sha ɗaya da kusan ƙwata????????‍♀️. 
      
       Ina nan zaune ganin ikon ALLAH harta idar da sallar tata a cikin ƙanƙanin lokacin da bazai gaza mintuna uku ba. Rigar ta sake cirewa ta ajiye, ta ɗauki tawul ɗinta ta sake ɗaurawa tare da jan stool ta zauna aka fara tsara ƙwalliya ta garari.

          Kai tsaye ɗakin Shahudah Jawaad ya shiga, juyowa tai ta ɗan kallesa ta ɗauke ido ita a dole fushi takeyi da shi.
        Shima sai da ya fara ƙarema ɗakin kallo kafin ya kai dubansa gareta, kallon kusan seconds goma yay mata sannan ya cigaba da takowa cikin ɗakin, jikin bangon da mirror yake ya jingina tare da harɗe ƙafafunsa waje guda ya tura duka hannunsa a aljihun jallabiyar.
      Tsayuwar tasa sai ya  zam tamkar sun fuskanci junane shi da Shahudah, hakan yasa ta sake ƙwaɓe face ɗinta tana cigaba da zana kwalliyarta.
    Tsawon mintuna biyu suna a haka, babu wanda ya cema ɗan uwansa ci kanka, sai zuwa can Shahudah ta ɗago manyan idanunta da gashin ya sake jin maskara ya miƙe gazar-gazar fiye da da ta kallesa, “Nikam karka cinyeni dan ALLAH bb”.
      Idanunsa ya janye a kanta yana sakin guntun murmushi da ya saka kumatunsa loɓawa, itama Shahudah sai tayi murmushin. 
      “Breakfast fa?” yay maganar yana sake maido kallonsa gareta.
      Sosai ta sake zuba masa idanunta tana narke fuska, sai dai batace komaiba.
        Hannayensa ya zare daga aljihu ya maida a ƙirjinsa ya harɗe, “Yanzu nan Hudah kina ganin wannan rayuwar itace ta dace da matar aure ta hausa fulani? Wata bakwai kawai da aurenmu amma matsaloli sunzo sun mana ɗaurin goro a cikin gida, wanda duk kece sanadinsu, shin ke wai bazaki taɓa canjawa bane?!…..” ‘Ya ƙare maganar a tsawace’.
        Razana tayi matuƙa, dan haka ta zabura tana jan jikinta baya tare da waro manyan idanunta waje, “Wai ni bb ya kake so in maka ne? Kaifa nace a ɗakko kuku da wanda zaike mana gyara amma kace baka yarda ba, ta yaya kake tunanin zan iya aikin gyaran wannan ƙaton gidanne saboda ALLAH, kum….”
     Haɗiye sauran maganar tata tayi tana ƙunƙuni saboda wani ɗan iskan kallo da yake mata, wanda ta tabbata yafara harzuƙa, idan ko ta bari ya kai ƙarshe zai iya ɓarota a kujerar ya haɗa kanta da mirror. 
     “Shahudah baki kai matsayin sakani yin abinda ban niyyaba, dan bazan taɓa kawo wani ƙaton banza gidana ba da sunan ma’aikaci, ki kama kanki kafin na raba shi da wuyanki a gidannan wlhy, stupid girl kawai”. Ya ƙare maganar da juyawa zai fita.
      Cikin ƙunƙuni Shahudah ke faɗin, “Karka kawo ɗin, kata zama a gida tamkar tirken akuyiyin ƙauye kuwa, dan nikam ba ƴar wahala bace, kake wani cewa kamar ba matar hausa fulani ba, ALLAH ya rabani zama irinsu waɗannan kidahuman da basusan ko yanda zama su gyara jikinsu ba balle su san miye rayuwa, da ana canja yare ma da tuni na canja nawa anbar dangantani da wasu hausa fulani can mtsowww.

   ????tab, babbar magana, Shahudah anya kinada man kai kuwa? Matan hausawan ne bamusan abinda mukeba????????????‍♀️? Rigiji gabji☹️.

         Sarai Jawaad yaji abinda Shahudah ta faɗa, amma sai ya fice ko waiwayota baiyiba, bedroom ɗinsa ya koma ransa duk a jagule, ya ɗau babbar wayarsa da ke a kashe ya kunna, wata Number ya lalubo tare da danna mata kira, bugu biyu aka ɗauka.
       Sama-sama sukai gaisuwa da wadda ya ambaci sunanta da Hibba, kafin yace, “Cikin yarannan wace a gida?”.
    Bansan mi aka ce masa da ga canba, ya dai sake faɗin “turomin ita” kawai ya yanke wayar ya ajiye.
     Tsaki yaja yana jingina da fuskar gadon tare da lumshe idanunsa ya afka duniyar tunani…………✍????






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button