NOVELSUncategorized

KWAI CIKIN KAYA 3

 
Bilyn Abdull ce????????SADAUKARWA:
Aunty Fareeda Gachi
Aunty Rahma A-Majeed
                BOOK ONE 
                    Shafi na uku 
______________


……….Zaman duniya da kayan cikinta buƙatar kowacce, amma waɗanda duniya ke buƙata da amfanuwa da kayan cikinta mutanene ƙalilan. A lokacin da wasu mutane ke bushasha da wani yanki na jin daɗin cikinta wasunsu kuka suke da kwankwaɗar ɗacin cikinta.
        Yayinda idanun wasu ya bushe da ga kwaranyar ruwa mai amsa sunan hawaye, a lokacinne ijiyar wasu ke ambaliyar zubarwa da buƙatar abin gogewa koda ace ruwan hawayen bazai dakata daga malala ba.

      Zuciyoyi duk iri ɗayane a suna, amma a aiyuka kowa da irin tasa. In dai zuciya zata kasance mabanbanta a ƙirazan mutane, to lallai dolene launin halayya da ɗabi’unsu ma ya banbanta. Sai dai wanda ya halicci duniyar da kayan cikinta, ya fika sanin miyasa ya banbanta ma’abota mu’amulantar ta da shawagi a cikinta harma da gudun zukatansu. 
        Kamar yanda duk ilimin ɗan adam bai isa ƙayyade numfashin da ke fita daga huhunsa zuwa maƙogwaro ya fita ta hanci ba, to lallai babu mai ilimin ƙa’idance ko banbance yawan jinsin ƙabilu da mutanen dake danƙare da duniyar nan sai wanda ya halicceta. A lokacin da fankama da tinƙahonka ke kwarzanta abincin tukunyar gidanka, da zaka leƙa ta gidan wani sai kaga ta fita abin kallo da kayan alfarma masu armashi.
      Sai dai duk wannan ba shi bane tushen zancen, ba kuma shi bane abin dubi da hange ko burin riska, tsarin shine waiwaya can bayan bayanka ka hango waɗanda ko tukunyar ɗorawar basu da ita balle tunanin hura wutar da zata dafa musu.
       Wani tun haihuwarsa ALLAH ya azurta tushensa ko zuri’arsa da rahamar fitowa cikin gingimemen hasken da ko baka mallaki komai ba a duniya sai shi to lallai ya gama maka komai, domin ya baka abinda ya fi komai tsadar tsada a cikin alfarmarsa. Sai dai abin mamaki da al’ajabi sai ka samu mafi yawan masu wannan damar sunyi wasarere da ita tare da mata riƙon sakainar kashi suna hange da gudun kamo wasu al’adu da ke da alaƙa da kishiyar nasu.
     Zancen nawa a bayyane yake, sai dai fa fahimtarsa ba kowace kwanyace hasashenta zai kai canba, ba kuma toshewar basira ce zata kawo rashin fahimtar ba, sam ko kusa ba hakan bane, ɗunbin abin tarawa ne kawai kema ƙwaƙwalen jama’a yawa su gaza warware wani ƙullun igiyar a jikin gugar da takai kimanin dogon zamani ana cuɗanya da ita a rijiyar mai bakandamiyar alfarmar ruwa buƙatar kowa.
    Shi wancan dama ya samu, amma rashin fahimtar hanyar da yake jefa ƙafa ta sakashi gaza fahimtar akwai waninsa da ke da buƙatar koda kwatankwacin tasa damarce shima ya shigo a dama dashi.
      Gashi dai a cikin duniyar irinta wadda ke da damar a tafin hannu, ga kuma gangar jiki da fitar numfashi duk ALLAH ya haliccesa da ita shima, sai dai sam ba ƙofa ɗaya ya ke shiga da fita tsakaninsa da mai damar a cikin duniyar ba. Hakan yasa yake kallon tasa duniyar da ban a cikin duniya, ba dan baya ci ko sha ba kamar kai, hatta barci da kake domin hutu da dariyar farin ciki duk ALLAH shima ya azurtashi dasu, abin lurar shine kai duniyar rungumeta kayi tsam, itama ta tallafeka tare da sake cusaka jikinta kuna kwasar ɗumin juna saboda tsantsar buƙatarka da takeyi, Shiko waninka rakaɓe yake a jikinta tamkar hawainiyar da ke ɗauke da ciki ta ke jiran ranar haihuwa.
     Bara dai mu ajiye duk wani dogon zance mu tsunduma cikin labarin ko mai karatu zaifi fahimtar gonar audigar da nake masa nuni da ita mai ɗauke da buɗaɗɗiyar kaɗa da gwaiduwarta ta fashe sumfut a filin gona.
    
           Ni dai sunana Bilkeesu ɗiya ga malam Ado makaho, ƙwarai mahafina makahone da ko tafiya baya iya yi sai da ɗan jagora, Sai mahaifiyata Asiya.
       A shekarun baya can mahaifina yana ɗan gani da ido ɗaya, amma da ga baya wahalhalun rayuwa suka ida rufe ɗayan idon yazam gaba ɗaya, mahaifiyata ma tana da nakasar ƙafa, dan kuwa gurguwace bata ma iya tafiya sai dai jan jiki.
         A matsayin da iyayena suke kawai zai nuna muku ni ba kowan kowa bace ba, dan kuwa muɗin talakawane irin tiɓis ɗinan da a kullum sai an nemo za’aci. Abin da zai matuƙar birgeka a rayuwar iyayena shine sam mahaifina baya bara balle aje kan mahaifiyata,  duk da baba baya gani bai yarda zama maroƙi ba, dan a ganinsa UBANGIJI ya masa dukkan gata da ya bashi rai da lafiya, idaniyar ganice kawai bashi da ita.
        Sana’ar mahaifina itace sai da kayan ɗinki irinsu zare, allura, almakashi da dai sauran kayan nau’in ɗinki tsiraru dai-dai arziƙinsa, a gaba ɗaya jarin idan zaka dinƙuleshi waje ɗaya bazai wuce na naira dubu goma sha biyarba, wataƙil ma na zurma da yawa. Dalilin kamewarsa na janye kansa da ga ƙasƙancin bara ne ya ja hankalin mafi yawan telolin anguwarmu zuwa sayayyar kayan ɗinki a wajensa.
       Sai mahaifiyata da ke saida kayan kuka, kuɓewa busashshe, kayan ƙamshi harda daddawa domin kare mana mutunci itama.
       Gidan da muke gidan hayane mai ɗauke da ɗakuna kusan arba’in, dan irin dogon gidannan ne da akan jeranta ɗakuna reras da ga farkon baranda zuwa ƙarshe tamkar gidan karuwai, ba wani faɗine da gidan ba, amma kowa iyakar mu’amularsa a ƙofar ɗakinsa ne da bazata gaza taku goma ba, babban kicinne guda ɗaya a gidanmu dake a farkon shigowa gidan wanda ya gama cuɗewar baƙi saboda mafi yawancinmu girkin icce mukeyi, masu arziƙin cikinmu ne keda lasisin dahuwar abinci saman gawayi, can da ga ƙarshen gidan kuwa banɗakine guda biyu, na kashi da wanka, wanda suka ɗaine duk yawan mutanen gidan ke shiga, shiyyasa mafi yawanmu zaki samu kowa da fo ɗinsa na kashi a ɗaki ko ƙaramin botikin fenti, da safe idan bakai azamar tashi kai wanka ba to fa ka tabbata ƙila sai dare ko goshin magriba zaka samu damar yinsa, shiyyasa da yawanmu mukan jera kwana biyu babu wanka.
        Tunda na taso a gidan na ganmu, hakama mafi yawan waɗanda suke gidan haka na tashi na gansu, dan haka zuwa yanzu mun wuce ƴan zaman haya sai dai ƴan uwa.
         Karku ɗauka ciranine ya kawomu garin har muka samu mafaka a wannan gidan haya mai kama da hotel, sam ba haka bane, mahaifina da mahaifiyata duk haifaffun garinne, kuma dukkan danginsu suna ciki suna rayuwa, hasalima akwai masu arziƙi a ciki. Sai dai kowa yasan halin zuciya irin ta wannan zamanin, inhar baka da shi to kaida banza duk ɗaya kuke, kai tsaye ma ake mantawa da kai a cikin dangi. To ballema irin iyayena da suka kasance naka sassu, inhar za’a iya mantawa da mai ƙafafu da hannu da idanu saboda talauci ya masa katutu ta yaya kuke tunanin ba za’a manta da musakan iyayena da bayan rauni da ALLAH ya jarabcesu da shi na halittar jiki harda talauci?.
         Ni kaɗai iyayena suka haifa a duniya, nima an jima ba’a sameninba, sai da ga baya ALLAH ya azurtasu da samuna matsayin ƴa ɗaya tilo a garesu, duk da talaucin iyayena da kasantuwarsu nakasassu ni ƴar gatace, dan gwargwadon iko iyayena tsaye suke a kan bani tarbiya, nakanje makarantar gwamnati kamar yanda sauran ƴaƴan gidanmu ke zuwa, hakama ina zuwa islamiyya. Sai dai aduk lokacin da aka buƙaci wani abu da ga makaranta da yafi ƙarfin ƙarfinmu hankalin iyayena kan tashi da ni kaina, wannan yasa da yawan lokuta karatun nawa ke kwan gaba kwan baya, dan kuwa ƴan ajinmu sunsha tsallakewa gaba su banni da maimaita aji saboda rashin kuɗin abu idan an buƙata tamkar ba makarantar gwamnati ba.
       Badan bani da ƙoƙaru bane, a wannan ɓangaren ma ina sahun farko na gwarzayen yara masu ƙwaƙwalwar karatu da fahimtarsa, sai dai rashin kuɗi ke daƙileni a kulum.
          A yanzu haka shekaruna sha takwas, amma har yanzu ss2 nake na makaranta, saboda matsalar komawa baya da naita fuskanta.
        Bani kaɗaice budurwa a gidanmu ba, a ƙalla zamu iya kaiwa fin mu ashirin kuma duk yawancin sa’oin juna, sai dai kowa da gwaninsa (inji masayin taliya ƴar murji????), dan kuwa kowaccenmu tanada abokiyar mu’amularta daga cikin ƴammatan gidan, dan haka muka kasance kusan nau’i uku zuwa huɗu a ɗaukar rayuwa. 
      A kwai sahun farko da suke ɗaukar kansu masu matuƙar aji da jin sunfi kowa hakama iyayensu sunfi na kowa arziƙi a gidan, a group ɗin sun tasarma su kusan bakwai, sai sahu na biyu da ajinsu bai kai waɗancan sahun farkon su sakasu a cikinsu ba, sai suma sukaja tasu zugar da zama abokan takarar waɗancan ta fuskar sumafa ba bayaba, sai kaso na uku da suka ɗau rayuwar saisa-saisa saboda ƙoƙari na tsawatarwar iyaye da gudun jefa kai a halaka, sai mu da ke karshe da muka kasance ba kowan kowa ba, hasalima mune akema kallon ƙarshen ƙasƙantattu marasa gata da galihu, ta kowacce fuska bamu da wani amfani sai tarbiyyar iyaye da ke jagorantar dukkan haƙurunmu da ɗaukar duniyar wajen maƙalewa kafin wa’adin barinta ya cika.
         Ba wani yawane da muba gayyar ƙarshen, dan kuwa da ga ni sai Firdausi ne da take ƙawata jallin jal a gidan, dan kuwa matsayin iyayenmu kusan ɗayane, itama mahaifanta suna fama da ciwon talauci tamkar mu, sai dai su sunma ɗan ɗaramu, dan babanta nada sana’ar saida kayan miya itama anan ƙofar gidan, shinema ke taimakawa babana a tashi sana’ar idan anzo saya da idan za’a danƙa masa kuɗi, kuma ita iyayenta duk lafiyayyune, sai yazam har kwancen kayan sawa itace mai bani, dan saka sabbin kaya a gareni sai sallah, suma kala ɗaya ne da ƙyar ake ƙulla kuɗinsu saboda ƙoƙarin iyayena nason ganin sun sharemin hawaye a cikin tsarata.
       Haka rayuwa ta zaɓar mana, badan wanda ya haliccemu baya sonmu ba, badan mun kasance masu saɓa masa ba, sai dan kawai haka ya tsara son ganin bayinsa a cikin duniyarsa dan yazama ilimi ga jahilai, izna ga masu wauta, rahama ga masu haƙuri, sake girmama mulkin ALLAH ga masu mulki.
         Gidanmu wani irin gidane da bansan yanda zan fassara muku shi ku fahimta ba sam, dan duk wani mugun hali ya ƙunsa saboda jama’ar daya tara masu kalar hali iri-iri a zukata. A duk lokacin da kake barci to ka tabbata sai ka samu wanda ke maka munshari a gidan, hakama akwai masu kallo da ido ɗaya, akwai masu gani ta ƙeya kuma. Tsabar iya annamimancin gidanmu ko faɗa ba’a yawan yi, kasan kuwa duk zaman da ya haɗa jama’a irin na gidanmu kaga ba’a faɗa to lallai ka jinjina wannan zaman kuwa.
    Ɗakinmu shine a can ƙarshe sai na su firdausi, hakan yasa baban firdausi samun damar yimana ƙaramar baca ta katako a ɗan lungun da ke gaban ɗakinmu wanda dalilin ginin banɗakuna ya fita. wannan bacar ce ta zama ɗakinmu ni da firdausi, dan ɗakunan gidan duk falle ɗai-ɗai ne, hakan yasa mafi yawan ƴammatan gidan daina kwana a ciki sai dai suje maƙwafta kwana.
     Rana mafi muni da razani a rayuwata itace ranar da muka wayi gari mahaifiyata babu lafiya, tun a daren jiya amai da gudawa suka saukar mata, kafin safiya tayi ligif, lokacin da ɗaya daga cikin mazan gidanmu mai tuƙin a daidaita ke ƙoƙarin sakata a napep ɗin dan zuwa asibiti sai rai yayi halinsa.
     Tashin hankali ba’a sa maka rana, dan kuwa yanda na tsinci kaina a cikima ai ɓata lokacine, har aka kai gawar mahaifiyata makwancinta ban san ina hankalina ya ke ba, sai bayan komai ya dai-daita har rana ta doshi faɗuwa sannan na dawo hayyacina.
       Abinda ya daɗa harmutsa dukkan tunanina shine babu kowanne ɗan uwan mahaifana da ya zauna dan karɓar gaisuwa a gidan, tun bayan binneta da aka dawo sukai ɗan zaman awoyi uku zuwa huɗu sai kowa ya kama gabansa.
      Nayi kukan da yafi na rasuwar innata a wannan lokacin kam, hakama babana da ruɗani ya maidashi kurman gaske bai uhm baya uh-uhm, dama gashi babu ijiyar gani.
          Matan gidanmu sun ɗan tausaya mana a tsakanin nan, dan kuwa kullum sai an samu mai bamu abinci ni da baba, dama maman firdausi kullum saita bamu na rana da dare, dan mafi yawan jama’ar gidan basa abincin safe, kowa sai dai yaje ya siyo a waje, sai ƙalilan a ciki dake ɗanyi shima da risho a ɗaki gudun idanun masu ƙwalama.
         Bayan kwanaki uku na makokin mahaifiyata akai addu’ar uku, sai aranar ne naga wasu tsiraru a cikin dangin iyayena, harma sukaimin gaisuwa. Ko da aka kammala addu’a sai kowa ya sake kama gabansa aka barni da ga ni sai babana kawai.
       Rayuwa ta cigaba da shurawa duk muna fama da tabon rashin innata ni da mahaifina, dukda baba yana dannewa da aro jarumtar rashin inna a gabana har ya lallasheni, nasan shima yana a cikin wani hali. A haka kwanaki sukaita shuɗewa har inna ta cika watanni uku da rasuwa. Zuwa yanzu naɗan saki jikina, amma ba da kowa ba, dan dama can ni miskilace kamar yanda ake jifana da zagi a cikin gidanmu, (akance sai miskilancin tsiya tamkar ƴar wani da wata), idan naji hakan iyakata murmushi kawai, dan bani da abin faɗa.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button