NOVELSUncategorized

KWAI CIKIN KAYA 3

        Kamar kullum na dawo da ga makaranta a gajiye yauma, dan dukda tazarar nisan da ke tsakanin makarantarmu da gidanmu kullum a ƙafa nake zuwa na dawo, idan kinga na hau napep sai dai idan baba ko innata sun sami rarar kuɗi a cikin sana’arsu, to shine za’a ɗan bani talatin na break, maimakon naci wani abun sai na maƙale kuɗin idan an tashi na hau napep, shima da ƙyar ake ɗakkoni, wataranma bana samun maimun alfarmar sai dai na taho a ƙafar dai dana saba. To yanzu ma tun bayan rasuwar innata sai komai ya sake taɓarbarewa, dan baba baya da isashshiyar lafiya, wataranma ko ƙofar gidan bai iya fita wajen sana’ar tasa sai baban firdausi ya takura masa.
      Tunda na shawo kwanar anguwarmu gabana ya ƙara ƙarfin faɗuwa, dama tun daren jiya nakejin girata ta haggu na rawa, ci gaba nai da takowa tamkar kazar da ke shirin sakin ƙwai zunɓutu a ƙasa, matasan anguwarmu da dattijai zagaye da wani abu a ƙofar gidanmu, ga jini faca-faca a gefen titin wajen, dan gidan mu nakan titine sosai, kuma titin irin wanda ake yawan bi ne saboda shine babban titin anguwar.
     Yanda wasu da ga mutanen suka zubomin idanune ya sakani sake komawa jan ƙafa, dan kallon yafi kama da na wadda ake tausaya mawa. Yayinda na iso daf da su sai naga an fara darewa ana bani hanya, mamaki ya sake kamani, dan kuwa basu tsaremin hanyar da zan shiga gidaba, suna da ga gefen jikin gidanne. Dubana nakai ga ƴar sirɗaɗen hanyar da suka ƙirkira sai karaf idanuna akan mahaifina kwance jikin jini. A hankali jina ya fara nisa, duhu ya mamaye ganina sai ga duniya na juyamin, kafin na gama fahimtar mike faruwa har na rasa komai da ga motsin jama’ar duniya, na koma wata duniya can daban mai nisan zango da ta mutane.
       
         Yau ake yinta gobe sai labari ne ya sake riskar rayuwata a karo na biyu, dan kuwa na sake rasa mahaifina da lilin bigesa da mai motar akori kura yayi yayinda yake ƙoƙarin tsallaka titi. Kowa ya shaida baiga fitowar baba ba balle ƙoƙarin ƙetara titin da ya yi, ƙararsa kawai sukaji tare da mugun jan birki da mai akori-kuran yayi. Hakan yasa kowa yayo kan baba, ganin hankalin mutane ya raja’a kansa ne ya bama mai akori-kuran ƙofar samun hanyar guduwa, baiko sakkoba balle ya ga halin da ya jefa mahaifina ciki da ni tilon ƴarsa. Bakin babana ni yaketa ambata har aka ɗakkosa aka maido gaban gidan, faɗi yake a kira masa Bilkisu, a kira masa ɗiyarsa dan ALLAH, sai dai abin tausayi da yankewar rabon sake haɗuwa numfashinsa na tsayawa ina isowa ƙofar gidan.
     A wannan karon nafi tsintar kaina a ruɗani fiyema da rasuwar innata, banbancin da aka samu zaman wasu a cikin dangin mahaifina tare dani har akai sadakar uku.
      Randa akai sadakar uku kowa ya kuma kama gabansa, babu wanda yay min tayin na bisa, sai abubuwan ɗakin masu amfani da suka tsince duk suka tafi dasu, aka barni da ga ni sai tarkacen matattun tsunmokaran iyayena da ƙwanƙwatsatstsun kwanikan cin abincinmu……………✍????






        Turƙashi, lallai bilkisu kin cancanci shinfiɗa dogon bayani a farkon labarinki kafin mu masu binki mu fahimceki, ko wace rayuwa kuma zata riski gobanki tunda gashi a yau ɗinki dukkan ginshiƙanki sun janye da ga rayuwarki, rayuwa kenan, lokacin da wani jin dadinta ke ruɗarsa yana baza shirme, wani rakuɓe yake a cikinta domin alfarmar mafaka kawai koda bazata buɗa masa wani filin yin rawar banjo ba????, ALLAH ya fimu kusanci dake, ya fimu kuma sanin wace rayuwa ta dace dake, wane tanadi yay miki a gobenki harma da jibinki da zata iya zama amfanuwa da wasunki a dangi ko abokan zama, bamu saniba ko kece zaki zama ƙwai cikin ƙaya!! ɗin watan watarana.☹️????????‍♀️






https://www.youtube.com/channel/UCWiytn-_Bo_l8P5pZrYub8A/


ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button