NOVELSUncategorized

DIYAM 8

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Eight : The Numbers

Ta jima a kwance a gurin, har Judith ta dawo ta shiga kitchen ta fara hada
musu dinner, sannan ta tashi ta shiga daki tayi sallar magrib ta kwanta, ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba tana ta saka da warwara. Allah ya gani bata son wannan zuwan nashi dan tasan ba zasu kare da dadi ba, zuwa zaiyi suyi ta rigima kuma rigimar da babu inda zata kai su. A nesa nesa dai sai sunfi samun kwanciyar hankali, wannan shi yasa ta zabi tahowa karatu nan kasar dan tayi baya dashi har abubuwa su warware. She don’t want to keep hurting herself and she don’t want to hurt others. Bassam ne ya fado mata a rai. Poor innocent Bassam, daga ganinsa tasan is from a wealthy family amma duk da haka bata son involving dinsa a wannan drama din, kuma she is afraid that he is already involved saboda irin kallon da yake mata kwana biyun nan. Kar dai ace ya fara son tane. She will have to put a stop to their relationship.

Har daki Judith ta kawo mata dinner kuma ta matsa mata sai data ci, tana ta tambayar ta abinda yake damunta amma sai tace mata family issue ne kawai. 

Washegari tana shiga class ta hango Bassam a seat din kusa da inda take zama, sai tayi sauri ta dauke kanta ta samu front seat ta zauna. Bata jima da zama ba taji kamshin turarensa a kusa da ita, bata dago kai ba yace “Are we changing seat?” Still bata kalle shi ba tace “I am” ya koma baya, ana jimawa sai gashi ya dawo da takardun sa ya zauna a seat din kusa da ita. Bata ce masa komai ba ta dauko littafi tana karantawa, shima ya dauko nasa yana flipping through the pages, can ya ajiye yace “can we go and eat? Ni fa yunwa nake ji” bata kalle shi ba tace “you can. Am okay” yace “me kika ci?” Sai ta mike zumbur ta rataya jakarta, yace “ina kuma zakije?” Tace “somewhere quiet” ya bita da kallo baki bude har ta fice daga ajin. Ya ajiye littafin hannunsa yana tunanin a inda yayi laifi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Har aka fara lecture bata dawo ba. Sai a lokacin yayi realizing cewa bashi da number dinta, dan haka hankalinsa gaba-daya yana gurinta har akayi lecture din aka gama. She never misses her lectures tunda ya santa sai yau. Ya fara tunanin ko bata da lafiya ne? Lecturer din yana fita shima ya fita ya fara nemanta, duk inda suke zuwa tare sai daya je amma bata nan har lokacin wata lecture din yayi sannan ya dawo wai ko zata zo wannan amma itama shiru har aka gama. Ana gama wa ya tafi department din su Murjanatu ya tarar yau sam basu da lecture ma dan haka bata zo ba. Yana futowa ya tare cab sai block dinsu. Ya hau lift har apartment dinsu yayi ringing bell, daga ciki ya jiyo muryar Diyam ta amsa “who is there?” yace “thank God. Bassam ne, Diyam?” shiru tayi bata bude ba, har yayi kamar zai sake danna bell din kuma sai ta bude, fuskarta a hade ta tsaya tana kallonsa kawai bata ce komai ba, ya tsafa kansa yace “You skipped your class and I was worried and thought ko baki da lfy ne” direct tace masa “lfy ta kalau as you can see” tana ganin yadda expression din fuskarsa ya chanja, daga gani tasan bai ji dadin abinda tayi masa ba amma sai kawai ta juya zata koma ciki ba tare data kara cewa komai ba, yace “Diyam?” ta dakata amma bata juyo ba, yace “in kina so in daina kula ki ne just say so ba sai kin tsaya kwana kwana ba, but please don’t skip your classes because of me” daga haka taji motsin tafiyarsa. Ta juyo tana kallon kofar duk ranta babu dadi, sam bata ji dadin bata wa Bassam rai da tayi ba but wani abun ya zama dole ne, laifin tane tun farko data fara zama involved with him amma ai a lokacin bata yi tunanin zai yi attaching wasu strings a relationship din nasu ba. Ta dawo ta rufe kofar sannan takoma ta kwanta a doguwar kujera ta rufe idonta tana lissafin yadda next weekend din zai kasance. Haka ta ringa jera tsaki ita kadai a kwance har taji motsi a hanyar corridor din dakunansu, ta daga kai taga Murjanatu a tsaye tana kallonta, nan take ta kara bata rai ta juya bayanta. Murjanatu ta karaso ta zauna a gefenta tace a hankali “Diyam” Diyam ta mike ta dauki wayarta ta shige ciki ta barta a zaune.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Bassam tunda ya bar gidan su Diyam ya saka hannayensa a cikin aljihunsa ya fara tafiya, wani irin zafi yake ji a ransa yana jin zuciyarsa tana kara karyewa, tambayar da yake ta maimaitawa kansa itace me yayi mata? Duk iya tunanin sa in ya dawo da hirarrakinsu baya sai yaga babu inda yagaya mata ko da kuwa wata magana ce marar dadi. Shi akwai wanda ya samu power over him a rayuwarsa irin Diyam? Tun farkon haduwar su baya iya mayar mata da magana, to me ya faru? Babu abinda ya kai ayi maka hukunci ba tare da kasan laifin me kayi ba ciwo. Yana isa kofar hotel dinsa sako ya shigo cikin wayarsa. Ya dauko yana dubawa, for the first time in weeks ya samu sako daga gida, daga brother dinsa, yaji heart dinsa tana racing kafin ya bude amma yana bude wa sai ya tarar babu ko kalma daya a cikin sakon sai hoto, hoton flight ticket.

Yayi ajjiyar zuciya ya jingina da bango, wato babu wata magana kenan a tsakanin su sai yaje gida. Abinda suke bukata dashi shine ya kai kansa gida ya karbi laifinsa. Yayi ajjiyar zuciya ya mayar da wayar aljihu a ransa yace “not now brother” dan bayajin zai bar kasar har sai yayi straightening tsakanin sa da Diyam. Ya tuno da shawarar da Diyam ta bashi na cewa ya je gurin Aunty Hafsat ya bata hakuri sannan ya tafi gida ya kai kanshi. Wani tunani ya fado masa a game da Diyam, anya ba wannan ne dalilin da yasa ta juya masa baya ba?

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Washegari Friday, da sassafe Diyam taje school dan ko breakfast bata tsaya tayi ba saboda bata ma son abinda zai hada ta magana da Murjanatu har sai tayi deciding inda zatayi placing dinta. Ta jima a class tana duba takardunta amma a can kasan zuciyarta tana duba ta inda Bassam zai bullo. Tana nan a zaune har aka zo aka sanar cewa lecturer din ba zai samu zuwa ba, a dai dai nan Bassam ya shigo, suna hada ido tayi saurin dauke kanta amma ta kasan idonta ta hango shi straight ya taho gurinta, ta fara kokarin harhada takardunta pretending to be busy har yazo daf da seat dinta ya tsaya, da dan karfi yace “why? Menene dalilinki na cutting dina off? Laifin me nayi?” Bata ce komai ba amma sai taji wani abu ya rike a tsakiyar cikinta kamar mai jin yunwa, nan take jikinta ya kama karkarwa har takardun hannunta suka zame suka zube a kasa, ta sunkuya tana kwashewa shima ya sunkuyo yana taya ta, sunkuyon da tayi yasa rolling din veil dinta ya kunce gashinta ya zubo ya rufe mata fuska ya sauka akan hannayensa. Still yayi yana kallon tsaho, baki da santsin gashin, ya daga hannunsa ya mayar mata da gashin bayanta tare da bude mata fuskarta, a lokacin ya lura da how red fuskarta da idonta sukayi, sai kawai yaji tashi zuciyar tayi melting, yaji kamar bai kyauta ba da ya daga mata murya har ya bata mata rai. Ta mike ta warce papers din hannunsa ta ajiye a gefe tana gyara veil dinta yace “am sorry Diyam but dan Allah ki gaya min abinda nayi miki” ta dauki takardun ta ta zagaye shi zata wuce ya rike jakarta yace “saboda na fada miki am in trouble da family na shine zaki juya min baya?” Da sauri ta juyo tana sauke manyan idanuwanta da suka yi ja a kansa, she looked shocked, bata taba zaton zai yi linking wannan abin da labarin sa ba, ta warce jakarta tace “is that what you are thinking? tunanin da kake yi a kaina kenan?” Ya daga kafada yace “then tell me otherwise, me nayi miki” tace “babu abinda kayi min Bassam” ta danyi shiru kamar mai tunani sannan cikin karyayyiyar murya tace “am just not who you think I am. Am sorry” ta juya da sauri saboda hawayen da taji yana taho mata. Kafin ta kai kofa ya kuma rike jakarta, ta juyo ta zuba masa jajayen idanuwanta yace shima da raunanniyar murya “ko ba zaki cigaba da kulani ba, at least give me your number yadda zan ke jin halin da kike ciki ko a waya ne, ko physically ba zamuyi magana ba at least…..” 

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
“Number?” Ta katse shi “wacce number zan baka Bassam? Ohhh I have so many numbers a cikin wannan kan nawa” ta fara lissafa masa da yatsun hannunta “kaga na farko 24 itace number din shekaru na, 3 itace number adadin yayan dana haifa a duniya, 2 itace number of times I was divorced, 8 itace shekarun yar karamar yarinya ta, infinity shine number of times my heart was broken and 0 is the tolerance I have for other hear breaks. So tell me, wacce number zan baka a cikin wadannan?” 

A hankali jakarta ta zame daga hannunsa saboda yadda gaba-daya jikinsa ya saki, tamkar numfashin sa aka zare gaba daya. Ta tako zuwa dai dai fuskarsa tace “like I said, am not who you think I am”. 

Har ta fita daga ajin bai motsa daga inda yake ba.

You did not see that coming, did you?

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button