NOVELSUncategorized

A GIDANA 43

You have come a long way and have won many battles. Whenever you’re faced with a difficult or challenging situation, you’ll overcome it. Yes, you can.

{43}


Kallanta yai yace “Saboda ni kike aiki anan?”

 Kallansa tai itama tace “korata zakai in saboda hakan ne?”

 Shiru yai yana dan tuno kadan daga cikin abinda ya faru a Buk yace “Sai yaushe ne zaki nutsu ki kula da rayuwarki? Meyasa bakya tunanin rayuwarki ta nan gaba?”

 Zuciyarta cikin kuna tace “Sai yaushe zaka dawo gareni?” Tai maganar idanunta na cicikowa suna neman kawo ruwa.

 Wani takaici ne ya kamashi yace “abinda kikeso kenan?”

Hawayenta ta shiga kokarin maidawa tace “bazai yiwu ba?”

Yana kallanta yace “badai ni kike jira na fad’a da kaina ba?”

 Wani takaici ne ya kara kamata dauke da wani zafin kishi tace “indai har ni bazan sameka ba to sai dai ka zauna haka, in har bazaka dawo gareniba ba wacce ta isa ta sameka.”

 Wani mugun kallo ya mata yace “Safiyya wai meke cikin kanki ne?”

 Kallansa tai tana hucin kishi, yace “can you please stop? Banasan kisani yimiki kiyayyar da baxata taba gogewa ba.”

 Ranta a bace ta kauda kanta, kallanta yai sannan cikin takaici ya juya.

 Harya isa gida hankalinsa gaba daya ya kasa kwanciya, ya tabbatar Afreey akwai abinda take amma daga gun wa? Taya zaiyi ya taimaki Zainab? Dan baisan me zai ce mata ba in ya ganta a wani hali.


Yana kwance shiru a cikin dakinsa, yana nazarin mafita, abincin daya shigo dashi daga cikin gida ya kalla, yunwar dake damunsa ce yasa ya zauna tare da sa hannu dan cin tuwon dawa miyar kubewa da Umma tai.

 Loma d’aya yakai ya fito da idanunsa da sauri, mikewa yai ya saki murmushi yana cewa ya akai banyi wannan tunanin ba?

 Da sauri ya tsame hannunsa sannan ya dauko wayarsa, number Zainab ya kira.

 Tana kwance a falo, Nabila da Nusaiba nata hada kayan tafiya, laptop dinta ce a gabanta tana dadannawa da alama wani abu take dubawa a ciki.

 Kallan wayarta tai dake kara sannan a fili tace “sai yanzu?”

 Hararar wayar tai wanda ni kaina harna dauka bazata dauka ba sai kuma naga ta daga da alama ringing din karshe ne kafin kiran ya katse.

 Daga can yace “Hello!”

 Shiru tai batace komai ba wanda hakan yasa ya kalli wayarsa dan ya dauka ba’a daga ba, ganin alamar ta daga yasa yace “naga kamar bacci kike in kin tashi na kira.”

 Sauke wayar yai yana jira yaji tayi magana jin takiyi yasa ya kara cewa “hello!”

 Murmushi tai sannan tace “na riga na saba da bakar maganarka sannan na gane kanafadan ta ne dan na maida murtani.”

 “Ummmmmm””

 Hade fuska tai tace “ya akai?”

 Mikewa tsaye yai yace “ya kike gani in kika amshi aikinki?”

 Da sauri tace “you mean?”

Yace “eh, duk abinda suke shirin miki basu isa su miki ba in har kina program dinki, saboda ganin bakya nan zai sa mutane tambayar abinda ke faruwa, waccen karan ance kin yi tafiya ne wanna fa? Hakan zai sa a shiga nemanki, ba hujja garesu ba sannan basu da ikon shiga rayuwarki, tunda sun san hakan, sannan a cikin shirin ki bayyana mutuwar auranki da kanki,  kin riga kin tsoshe abinda zasuyi amfani dashi.”

 Cikin gamsuwa da abinda yace da jin dadi yasa tace “nima yanzu nake tunanin sauke website dinmu da duk wani program da na saka a youtube”

Shima cikin gamsuwa yace “hakan yayi”

 Dan gyara kwanciyar ta tai tace “hmmm”
“Nagode”ta fada a hankali.
Sarai ya jita hakan neya bayyanar da murmushi a fuskarsa.
Can yace “ya zakiyi da Adam?”

Tace “zan je gidan Gobe da rana.”

 Okay yace suka dan yi shiru, basu taba doguwar waya haka ba dan waya ma bayinta suke ba sai da dalili shiyasa duk suka samu yanayin wani banbarakwai.

 Khalid ne yace “shikenan, sai da safe.”

 Tace “Allah ya tashemu.” Tai saurin kashe wayar, shiru tai tana nazari, tabbas shawarar da Khalid ya bata sosai ta gamsu da ita.

Ai mikewa tai ta zauna ta fara harhada abubuwan da zata gabatar a gobe, waya tama daya daga cikin masu dauko rahoto tace “ya turo mata na gobe.” Ba musu ya tura mata dan dama sau da dama takan tambaya shiyasa bai kawo komai ba.

 Da safe ta shirya tana rufo kofar daki Nabila na fitowa daga nasu dakin hannunta dauke da robar ruwa.

 Zainab ta kalleta tace “Hajiyar bacci ya akai kika farka?”

 Nabila ta kalleta tace “Allah Aunty zan daina kwana kan gado da Nusaiba kullum da ciwon jiki nake tashi, ta dinga makamin kafa kenan.”

 Dariya Zainab tai tace “shikenan sai ki koma dakin Goggo.”

 Hade fuska Nabila tai tace “ni wlh sunansu ma bansan naji an kira.” Ta kalli Zainab tace “Aunty haryau bazaki fadan abinda suka miki ba?”

 Kusa da ita ta matso ta dafa kafadarta tace “zan wuce Mamman yace sai rana zaku wuce ko?”

 Tace “Hmmm kikace zaki kaimu gun Asiya.”

 Kallanta tai sam ta manta tacewa Umma zata kawosu, gashi har hutu ya kare, ga Dady tasan yanzu zai fara fada akan zamanta ita kadai, next term kuna dawowa zan kaiku.

Hannun Zainab ta kamo, juyowa Zainab tai ta kalleta, a hankli ta sakar mata murmushi.

 Nabila ta maida mata tace “jiya kin samu bacci?”

 Hmmm ta fada tare da daga mata kai.
Nabila ta saki hannunta tace “karki manta kizo kafin mu tafi.”

 Kai ta daga sannan ta fita.

 Mamman nata goge motoci biyun dake waje dan Dady ya sai mata mota a ciki ma suka dawo.
Kallan Mamman tai ta gaisheshi, da sauri ya karaso yana gaisheta, murmushi tai tace “zan wuce dakaina.”

 Yace “ki bari na ajiyeki”
“A’a inada inda xani ne daga can.”

 Ba musu ya mika mata key sannan ya tsaya ya bude mata motar ta shiga sannan ya rufe, jan motar tai ta fita.

******
 Khalid ya gama shan tea da Tsame ya dau kajarsa xai fita sai ga Umma.

 Kallansa tai tace “ungo wannan ka kaiwa Zainab.”

 Kallan flask din yai ya amsa tare da budewa, ganin tsame yasa ya rufe yace “Hajiya Umma.”

Tace “Allah yasa zata iya ci, sannan kace karta kuskura ta sa komai a kular.”

To Umma, jakarsa ya bude ya saka sannan ya shiga yama Abba sallama ya fita.


 Zainab na shiga ta wuce fitting room ta shirya sosai, ba tare da ta ma wanda ya amshe da shirin nata magana ba.

 Wucewa tai Direct dakin shirye shirye, kawai taja ta zauna.

 Nazifi wanda shi yake gabatar da shirin a maimakonta yana shiga ya ganta a hakkimce, yanda yaga alamun fuskarta ne yasa yasan ba wasa, kusa da ita yaje ba musu ya mikamata takardun hannunsa tare da mata barka da cigaba.
sannan ya juya zai tafi.
Nazifi!
Juyowa yai ya kalleta, alama tamai daya zauna, kallanta yai yace “naam?”

Tace “let’s do it together.”

Da sauri ya kalli gun masu cameras sannan ya kalleta, alama tamai daya zauna.

 Da sauri ya zauna tare da dan matse kafafunsa alamar rashin sakewa.

 Khalid dake tsaye a gun camera yana ganin abinda ke faruwa, har suka fara gabatar da shirin, sannan ya juya.

 Director Kabir dake ta faman hada kan manyan gun aikinsu dan suzo ayi meeting akan Zainab.

 Ramlatu ta kirashi ta sanar dashi abimda ke faruwa, ba karamin tashin hankali ya shiga ba.

Cikin hanzari ya juyo tare da sanar dasu su iso suma.

 Zuciyarsa fal take da takaici, tare da kara shan alwashin korar Zainab koda zai rasa komai nashi ne kuwa.

 Yana isa tana kammala shirinta, daga karshe ne ta mikawa Nazifi takarda bayan an dan tafi nuna rahoto.
Kallanta yai da sauri, tasani sarai mamakin abinda ke jiki yakeyi hakan yasa ta daga mai kai alamar eh.

 Ana dawowa daga rahotanni, Nazifi yace “ga shirin namu ya kawo karshe, akwai abinda ke yawan damuna.”

Yadanyi dariya ya kalli Zainab yace “gaba daya yanzu zamanin na rasa meke faruwa a ciki, sai kaga mace da namiji anyi auran soyayya mai karfi amma wata uku sai kaji aure ya mutu, me kike tunani yana kawo wannan matsalar?”

 Dariya Zainab tai tace “ai ku maza ku za’a tambaya, dan kune masu sakin kaga kune kuka san menene ya ke sa kuke yinsa.”

 Ta kalleshi tace “ni kaina watan ni hudu da suka gabata nawa auran ya mutu, kaga kuwa kai ne zaka amsa wannan tambayar.”

 Nazifi yace “Inalilahi bamuda labari, ba dai hutun da kika dauk……


Dariya tai tare da daga kai sannan tace “shi dan adam kowane da nashi kaddarar da Allah yake dauramai shi yasa a koda yaushe muke rokon Allah ya bamu ikon cin jarabawarmu.”

 Nazifi ya jinjina kai…….. nan suka kara tattaunawa akan matsalar aure sannan sukai sallama.

 Director Kabir ta kalla wanda ke tsaye a jikin kofa ransa a matukar bace.
itama kallansa tai sannan ta shiga yima Nazifi magana ba tare da ta tanka mai ba.

 A zuciya  ya juya.

 Yana shiga yaga envelop doguwa akan desk dinsa, budeta yai ransa duk ba dadi, dan ya gama sadaukarwa Zainab ta riga tayi winning ba abinda ya isa yayi.

 Abinda ya gani a ciki ne yasa ya zauna akan kujera da sauri yana kara karantawa.

Zainab ta kalli Khalid wanda ke printing, sannan ta wuce.

 Tana shiga office dinta ta saki murmushi tare da yin ajiyar zuciya, xama tai ta jawo flask dinta tana kurbar tea tare da duba abubuwan data sauke.

Wayar cikin office dince tai kara hakan yasa ta daga.

 Director Zainab ki shigo akwai Emergency meeting nan after lunch .

 Okay kawai tace ta ajiye wayar, nazari ta shigayi tana tunanin me za’a tattauna.


Mikewa tai ta dauko key din motarta, ta fito.

Mota ta shiga ta wuce gidan su Adam.

Goggo na zaune tana kallo, yau kamar nela sun san farin cikin da take ciki suka kawo mata wuta, gefe dankali da kwai da suka ci suka koshi ne harda ragewa a gefe, ga kofin shayi nan a gefenta tana kallo tana sha.

 Adam ne ya kalleta yace “wai Goggo idanki baya zafi?”

 Zafin me?
Kallo mana.

Tsaki tai tace “ni wannan tv din ma ai a dole nake kallo da ita, yo meza’ai da wannan yar fucikar tv din? In na tuno ta gidan Zainab sai maji raina ya baci, duk kai……..”

 Kallan ta yai sai ta wayance tace “yaushe zaka bank ka tattalo mana kudin?”

 Dariya yasa yace “yanzu ma.”

 Lalitarta ta bude tace “kai inaji tare zamu tsoron baka kudi nake.”

Shikenan sai ki shirya.

Zatai magana akai sallama, taran Asabe ne ta bude labule tace “A’a d’an nan ya akai? Ta fada tana dan toshe tv dinta da labule ta dauka abinda yazo kenan.

 Yace “ana sallama da Adam ne.”

 Goggo ta kalli Adam tace “kaji!”

 Wata dariya yasa yace “wato Allah yamin farin jini ta ko ina wlh.”

 Mikewa yai yana kade riga cikin isa da takama.

 Yana fita ya ga motar Zainab, idanu ya zaro da sauri ya nufi motar.

 Kallansa tai sannan ta budemai yai saurin bude kofar ya shiga cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa.

 Kallanta yai yace “Honey!”

 Kallansa tai ta zubamai ido wanda harya sa ya sosa sumar kansa tace “Bani wayarka.”

Da sauri ya mika mata, duk hotunan da sukai tare ta goge sannan ta mikamai.

 Kallanta yai yace “me kikai?”

Tace “hotunan mu na goge.”
Da sauri ya duba hotunan ko d’aya babu, kallanta yai yace “Honey!”

Da wa kake?

 Shiru yai kafin yace ” Honey dan Allah bazan yi maganar hoto ba amma dan Allah ki amince mu maida auran mu? Kinji?”

 Kallansa kawai take tama rasa me zata cemai, yace “Honey na tuba ki yafemin, Allah nayi laifi amma wlh abinda kike tunani bai faru ba, dan Allah Honey ki………”

 Wata irin dariya tasa wanda kana ji kasan ta bakin ciki ce dariya tai sosai dan ni kaina bantaba ganin Zainab na dariya haka ba, cikin dariyar tace “mu maida aure?”

Kai ya daga da sauri.

Kallansa tai sannan tace “yanzu nake nazari iya zaman danai dakai har yai baka taba nuna min jarabawarka ba, dauko takardunka ni da kaina zan samoma aiki.”

 Kallanta uai kabansa ya shiga faduwa yace “takardu?”

 Tace “eh dakosu.”

 “Zan dauko amma Honey ki am……..”

Shiru tai tana kallansa, can tace “Adam haka kake tun dama ko kuma yanzu ne na maidaka haka?”

Cikin rashin fahimta ya kalleta, zuciyarta na kuna tace “wad’an nan dabi’un naka sababbi da nake gani yasa na shiga tunani, dama can haka halayenka suke? Boyewa kai saboda ni ko kuma nice bayan aurena ka koma haka?”

 Kallanta yai yanayinsa duk ya canza.

 Idanunta ne suka ciciko tace “Wani irin rayuwa mukai nida kai har shekara 4? A kwanakin nan wannan amsar haryanzu na kasa samota.”

 Cikin sanyin murya yace “Honey!”

Tace “in har kanada imani da tunani ko cewa akai kamin abu zakamin? Bayan abinda ka aikata min? Har sai ka karamin da abinda zai sa na tsaneka har karshen rayuwa ta?”


 Kallanta yai hawaye ne suka gangaro mai, itama hawaye ne suka zubo mata tace “na rokeka da Allah Adam ka kyaleni, jiya da kyar nai bacci ina tunanin tambayar da akamin wacce banida amsarta, an tambayen dalilin daya sa duk wanda nake tare dashi baya zaune dani zuciya daya, na dade ina tunanin wani irin shiga hakkinka nai a zaman mu da zaka sakamin da haka.”

 Da sauri yace “ba abinda kikamin Honey, ni din ne bazan iya hakuri dake ba.”

 Yanayin kallan da takemai ne ya canza tace “da alama kanka ba daya ba Adam, na rokeka da Allah ka barni nai rayuwata, ka barni naji da abinda ke damuna plz.”

 Shiru yai baice komai ba, kallansa tai tace “zan wuce, inada meeting.”

 Kallanta yai jiki a sanyeye ya fito taja motarta ta tafi.


 Ganin time din ya kusa yasa ta kara gudun mota, tana isa ta shiga ciki, wucewa tai gun meeting din tana bude kofar taji gabanta yayi wani irin faduwa, da sauri ta shiga yin addu’a a ranta.

Khalid ne ya kalli Mai maganar, cikin gulma yace “sun shiga meeting da alama akan Director Zainab ne.”

 Nazifi ne yace “wai matsalar ta meye? Rayuwartace fa menene dan auranta ya mutu? Ita take da kanta? Ko ita ke san ta kashe auran nata?”

 Ramatu cikin fishi tace “ita mutanen data kora saboda rayuwarsu fa?”

Da sauri mutanen gun suka fara bin bayanta, Khalid wanda ke zaune ransa yafara baci matuka.

 Afreey ce ta kalleshi cikin kuluwa.

Nazifi yace “dukansu abinda sukai ya shafi aikinsu san kai kawai kuke yi da muna bakin ciki.”


Nima nace haka ne????plz ku bat Zee tasha ruwa ya tsirga mata????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button