NOVELSUncategorized

KWARATA RETURN 10

         Ai wannan auren ko auren da aka daura a coci bai kaishi ƙarko da aminci ba. Yaci uwar auren coci ya zarta na kotu kuma. Yadda bakya tunani auren ya wuce inda kwalwarki bata iya hasasowa saboda ya linka auren zobe dan auren Yazeedu auren kabari ne. Kuma haka gidana yake idan an shigo ba’a tafiya saidai idan za’a tafi kabari , nunawa yayi da hannunsa yana ci gaba da cewa wannan nasan zahiri ne tafiya ɗaya ba dawowa. A bakin tarihin rayuwarki waye kikaji ya shiga cikin ramin kabari ya fito ? Tou ba’a fita sai ranar da ƙiyama ta tsaya , wato ranar yauma tubalasra’il. Ranar girbe abinda ka shuka , ranar da uwa bata gane ɗanta miji idan yaga matarshi zaisha kwana. Tou gidan nan maƙabartarki ne a nan kabarinki yake idan kinga kin fita a gidan nan mutuwa kikayi dan ƙaniyar iskanci. Ya ƙarasa maganar yana shaƙe wuyan Jiddah tare da cewa biyamin kwai na….

      Yana shaƙe da ita yaci gaba da cewa shin bana faɗa miki abincin gidana adon idon duniya ne ba ? Dakel tace e , Yazeed yace amma kika ce kinji kin yadda ko ba haka nayi dake ba ? Cikin jin zafi shaƙa tace haka ne. Riƙe wuyanta yayi da hannu ɗaya yace duk kwai ɗaya dubu ɗaya na siyo abuna. Kuɗin mota da kuɗin kunna gas a gidana ba ranar sanwa ba. Bakina dana ɓata wurin ciniki , kin yanka albasa ba’a kan ƙa’idar ma’ikata ba. Zagin miji wanda babu shi a kundun tarihin musulci zunubi ne mai girma , domin wanke kai daga wutar Allah neman gafara da biyan kuɗin diyya dubu ɗari. Cin zarafin miji kin daƙile min guyuwa akan ƙalubantar ciyarwa kince gidanku akwai abinci. Domin samun sassauci kwanciyar kabari cikin salama zaki biya dubu hamsin domin wanke kai daga bugun mala’eku. Naira budu tamanin na neman yafiya ne domin kiyi kwanciyar kabari cikin salama. Da hannun da bai riƙe wuyanta ba ya fara lissafun kuɗin a wayarshi.

      Yana lissafa kuɗin yake cewa yau kuma anyi buking ina a wasan danbe ki biya kuɗinki da wuri ki yanki tikiti tun kafin ƙarfina ya ƙare. Ki bada budu goma tunda ke ta gida ce , zan siyar miki dashi ne akan farashi mai sauƙi amma ba haka ake siyarwa ba dan kada jibi ince miki dubu talatin ki fara wallahi² , cikin wahalalliyar murya tace bana so. Basai kinyi muradi ba kuɗin gado da katifa na yafe miki tunda ke matar gida ce. Kuɗin kwai naira dubu talatin. Cikin kakari Jiddah tace ai ba duka naci ba , damuwarki ne wannan inji Yazeed yaci gaba da cewa + naira dubu biyar ta-ra akan kin tari numfashin miji yana magana kina sako mishi baki….. Duka abinda kuɗinki suka kama dubu ɗari biyu da tis’in da biyar , amma ɗari 3 zaki bayar hada ladar lissafi dubu biyar , ya ƙarasa maganar yana sakin wuyarta ya turata can baya. Riƙe wurin daya shaƙa tayi tana ta tari , ƙuhul² kamar sakin mayu.

       Wai wannan wane irin zalinci ne ? A fusace ya nufi wurinta ya ɗaga hannu yace zan……. Da sauri ta duƙe. Wayarta ya ɗauka ya miƙa mata tare da cewa maza inji alart. Jiddah na kuka tayi ma Yazeed transfer. Dariya yayi bayan yaga tabbacin kwanciyarsu a asusun bankinshi ya rumgumeta yana sumbatar ta. Ina sanki haɗaɗiyar matata abun alfahirina bugun zuciyata , gaskiya yafa kamata azo a ƙulla hanyar neman wasu kuɗin kafin asusunki yayi shiru , ya faɗa yana fita daga kicin in sweetheart kisha shagalinki lafiya , lambar lokacin ki shine. 0 3 4 9 am. Wato yana nufin lokacinta da zai bata na katin danbe da ta siya shine 03:49am ya yada mata katin yayi gabanshi……. Kuka Jiddaah tai tayi tana Allah ya isa. Saida tasha kukanta har ta gode Allah ta kira Nabeela ta rattafa mata komai tayi ƙari akan abinda yayi mata ta kulle da cewa kuma yace baya sakinta. Abunka da ɗan uwa Nabeela taita kuka ta kira Rabiya ta faɗa mata. Rabiya ma taita tsinewa Yazeed wai zata faɗawa Dikko wallahi sai an kaso auren nan , yasan ashe Yazeed tsinannen Allah ne yasa aka haɗa auren saboda cuta irin nashi kaza² , taya Yazeed zai kulle yarinya a gida ba abinci yana bata gwale² sai duka ? A yinin ranar haka sukai ta yaɗa magana tsakanin su “yan ɗakinsu.

      Daga baya suka bawa Jiddah haƙuri tare da tura mata kuɗi ta siya abinci kafin a samu mafita saifa Yazeed ya sakota ɗan iska mara mutunci anyi masa rana zai yiwa mutane dare. Rabiya da kanta tazo har gida taba Dikko labari , mugu yaji mugunta yasha dariya harta zarce musali. Saida yasha dariyarshi sannan ya turawa Sultana saƙo tazo palonshi , bayan naje yace Rabiya ta maido labari baya. Ran Rabiya kuwa ya hayaƙa taita zagin Dikko , waishi wane irin ɗan iska ne ? Ta faɗa mishi ciwo yana ta wata dariyar iskanci ? Cikin dariya yace bakinki ko nawa ? Fuuu Rabiya tai zuciya ta ɗauki jakarta , Dikko yace Hajjaju tsaya da Allah , naƙi in tsaya tunda kai ɗan iska ne. Allah ya baki haƙuri karki tafi. Tsoki tayi ta tsaya a bakin ƙofa , daga ni harshi duk fita mukayi , jingina yayi da ƙarfen bene ya ɗora hannuwanshi ta baya ya rakuɓe kamar mijin ɗiyar soja da yayi dukawa ita a barek kuma itace da gaskiya , haɗe rai yayi yana kallon Rabiya nima kusa dashi naje na tsaya ina kallonshi. Gyara bakinshi yayi shima ya kalleni. Murmushi nayi shi kuma ya sake gaggaɓewa da dariya…..

    Rungumeshi nayi nima ina dariya , safko hannunwan shi yayi ya riƙeni. Wai anci ƙaniyar iskanci mata na buking in mijinta , ita da haƙƙinta a nuna mata fin ƙarfi , kam balasti nan taff ya jinjina kanshi da mamaki cewa “yan iska duniya basa ƙarewa ko kunyar faɗa ma baiji ba tirrr. Dariya itama Rabiya tayi amma badan ranta yaso ba , haka dai da damuwa , ciki muka koma duk a palo muka zauna. Dikko yasa aka sake karanto labarin ni da bana nan naji da kaina.

      Shi kam Yazeed ma baida mutunci ko tsoron Allah bayayi ? Taya matarshi zata siyeshi dan yayi kwanciyar aure da ita ? Duk a raina nayi magana , tun daga wannan bansan inda zance su yaci gaba da tafiya ba , hankalina da tunanina kuma ya koma karatun rayuwa ta , ta baya. A gajiye na kwanta jikin Dikko ina ƙara hasko rayuwa da yadda ita kanta rayuwar tayi min hajijiya.

      Maganganun Dikko da kuma dalilinshi na sawa a karanto min rayuwar gidan Jiddah. Shima wannan duk hikima ce , yana so inyi gyara ne a inda nake da matsalolin zamantakewar aure. Sai zan tukan Inna , taƙaitacciyar jiyar zuciya na sauke dakel a hankali na furta Allah ya jiƙanku iyayena yasa kun dace da kyakkyawar makoma. Saukeni Dikko yayi daga saman jikinshi zaije ma Rabiya rakiya. Nidai ban bisu ba nace ta gaida gida ina daga kwance….. Duk inda kake ka godewa Allah kuma ka nuna haƙuri da jajircewa. Bazafa a gane matsalar ba sai tafiya tai nisa. Allah ka rufamin asiri ka ƙarawa mijina haƙuri da halina , Allah kasa in daina mishi abinda baya so.

      Tun daga wannan rana kamar anmin allurar natsuwa haka na zama wata baiwar Allah , har abun ya dami Dikko danshi a tunaninshi ko banji daɗin maganarshi akan “yan gidanmu shiyasa nake fushi ? Me yake damuna ne ? Ko banda lafiya ? Idan yayi min wani abu banji daɗi ba inyi haƙuri kuma in faɗa masa miye bazai sake ba. Nace masa babu komai amma hankalinshi ya gagara kwanciya.

         Ko yau a makaranta burus² nake kamar garin kwaki bai jiƙu ba. Shima daya kawoni makaranta dai ranshi bai mishi daɗi ba , wai shi baya san wannan fushin da nakeyi , dan Allah in saki raina mana , ya zanta haɗe mishi rai shi bayajin daɗin gani na a irin wannan yanayin , ko na gaji da ganinshi yaje hutu idan naso ganinshi saiya dawo ? Nace ba komai , tou kiyi murmushi mana An matana…… Yayi maganar yanayin murmushi mai tafe da yaudararren kallonshi. Kaɗan na yaƙe bakina tare da kwantar da kaina gefe kaɗan nayi mishi ɓarawon kallo kamar liman yaga wawan zama , so kike dai in koma gida da baƙin ciki ko ? A , a , tou wai meke damunki ne ? Ba komai , cike da ƙunar zuciya yace An mata wai yaushe kika zama munafuka ne ? In banda munafurci ni zaki riƙa munafurta ? Me nayi miki ne iye ? A kwana biyun nan kina ta ƙoƙarin riguzamin farin cikina laifin me na aikata ? Gaskiya ce na faɗa bayan nan miye aibu na iye…? Babu , hmmm yayi tare da gyara zamanshi yace jeki……. Fuuuuu na fita ban rufe motar ba. Bin bayanta yayi da kallo. Banyi tafiya mai tazara ba na dawo raina a duƙunƙune nayi ma motar shigar bulet nima. Da sauri yaɗan ja kanshi baya. Kusa dashi na tsallaka na dafa hannuna a jikin gilas in murfin motar da yake zaune ɗayan hannuna kuma a saman kujerar da yake , na sakashi tsakiyata kenan , wasa nayi da girarena sannan na kakkaɓa mishi ido da logo mai ibar yanayi muuuuuu muah nayi masa a bakinshi. Wahalallen murmushi yayi tare da fitar da sautin numfashi a gajiye yana ƙoƙarin riƙoni na sauka a wurin na zauna saman kujerar mai zaman banza sannan na fice daga motar….. Murmushi yayi tare da rufe murfin motar yaja yai tafiyarshi.

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button