KWARATA RETURN 10

Misalin ƙarfe 10:19 na dare. Kai mai karatu ka tuno wacece ni tun farko dana fara baka labarin rayuwata. Na kira kaina da ma’abociya iya shafa turare tsantsar kyau da cikakken body. Da gudu turaren dake jikina ya fita daga jikina ya tafi……… Saida ya zagaye kaf ilahirin gidan sannan ya dawo mazauninshi. Ƙarar tafiyar takalmina da ƙaraurawar da jigidar keyi ya haɗu yake fitar da wani irin halakken sauti mai daskarar da zuciyar duk wanda yaji sautin. Na wanku daga jiki har kayan dana saka. Fili na iba na fara bada taku. Pa – Pi dake kwance yana kallona yace unguwa zakije….? Ƙaniyar anguwa. Dariya yayi tare da cewa kuma wayyayi baci cau ba. Kusa dashi na matsa nace niɗin ce banyi kyau ba ? Dariya yayi tare da rufe idanuwanshi yace waca nike wayyayi… Tsoki nayi cikin jin haushi na koma gefen gado na zauna. Buɗe idanuwanshi yayi tare da cewa baci zuwa ? Ka rufe min baki munafiki kuma bazan sake zuwa dakai ko ina zanje ba tunda kace banyi kyau. Ɓata fuska yayi ya fara kuka yace wayyayi waca ne. Cike da masifa nace ka rufemin baki kuma bana sanka. Shiru yayi ya tura ɗan yatsashi cikin hanci yana kallona. Ka daina kallona. Sauka yayi daga saman gado yana kuka , duk kiran da nake mishi tafiyarshi yayi yabar ɗakin.
Yaya wai Momy tace bata sona. Tsoki Dikko yayi yace ka wuce ka bani wuri. Gefen kujera ya raɓe yana kallonshi cikin kuka yace kaima baka can Pa – Pi cikin ɗaga murya yace fita ka bani wuri nace…. Fita yayi da gudu yana kuka kaima wayyayi na fata dakai , Daga ɗakin Dikko wurin Ashiru ya tafi kai ƙara…… Tashi nayi tsaye ina miƙewa naji jigidar nan tayi wata irin tsuwwa , cassssss……. Burgeni abin yayi na ƙara bada tako ina matsawa jikin madubi. Tana cossss casss. Dariya nayi na samu abin wasa kamar yaro sabon tafiya da takalmi mai tsuwwa.
A wannan yanayin Dikko ya sameni , shi kuma ya biyo Pa – Pi ya dakeshi daya ce wai ya ɓata dashi. Kamar wani gele ya kafeni da ido yana muzurai. Murmushi nayi danni ina cikin shauƙi ne , iska yaja ta baki sannan yace ina Pa – Pi….? Kaje can ka nemeshi mana. A fusace ya shigo ciki , gudun da nayi dan hawa saman gado yaba jidar nan damar yin ihu sosai , cacasss.. Cosss cisss² cuuu. Wahalallen dariya Dikko yayi dakel a gajiye yace menene ke ƙara……? Yayi maganar yana ƙoƙarin riƙo ƙafata. Da sauri na fizge nayi baya. Tsaya in gani mana. Yayi maganar yana fizgoni da ƙarfe. Da sauri ya hanakaɗe rigar jikina ya kunce zanin jikina. Na tsani jigida sai kin cireshi……… Wace karuwa ta baki ita…..? Ni zaki maida mahaukaci ki riƙa kaɗamin ƙaraurawa , da kokawa ya kamata yana ƙoƙarin tsinkawa. Karka tsinkamin abu , saina tsinka ni ɗan iska ne da zaki riƙa min alama iye ? Yayi maganar yana gauramin mari in sakar mishi hannunshi dana riƙe , cizon hannun nayi cike da ɓacin rai nace bazan saki ba , kai……………. Ni kika cizarma hannu. Saina kashe ki…. , a tsorace nace shikenan tsaya baka so ko ? Ey bana so An mata. Shikenan bara in ciro maka , nayi maganar idona cike da hawaye. A tausaye ya kalleni ni kuma na cire jigidar na miƙa mishi. Taro hannunshi yayi dan ansa yana kallona…………..
11/02/2020
*JAMILA MUSA…*