NOVELSUncategorized

KWARATA RETURN 3

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* ????
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
               *KWARATA RETURN…*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_Rubutawa…
            *JAMILA MUSA…*       *SAI NA AURI D ‘ K*


Naki ne “yar uwata ????????
*ASMA’U ZAYYANA*
 {{ Asmeenat Xeyyan }} alfaharina bugun zuciyar *JAMILA MUSA…*???? —— 3

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


      Bani kaɗai ba , mafiya yawan mata haka muke. Duk lokacin da muka shiga cikin wata ni’ima ta daban sai kanmu ya fara rawa mu riƙa yin wani hange na daban , wasu matan basa fara gilu² da kansu sai sun ƙoshi nan zasu ɓalle ƙofar iskanci da rashin kunya. Kamar dai ni yadda na kasance. Gani na tsaya a jikin madubi ina ta kallon kaina yayin da wani sashe na zuciyata ke nunamin in kalli kyauna ! Ashe haka na haɗu ? Haka nake kyakkyawa ? Aiko yadda nake mai kyan nan baima kamata ace ni ina aure a katsina ba , kamata yayi ace ina irin su Abujar nan idan ba Abuja ba ina can wasu ƙasashen duniya mijina ya ɗaukeni yabar nigeria dani , abun ba haka yake ba kuma ba’a kyau take ba. Jin daɗi da arziƙi duk kyanki da iya haɗuwarki sai Allah yaso zakiji. Ba’a kyau , asali ko nagarta yake ba. Arziƙi da hutuwa baiwa ce daga Allah idan yaso sai ya baka ya kuma sa kaji , ni’imar aure daban ce. Allah ya darata ta haka kuma ya martaba ma’aurata. Idan kina ƙarƙashin inuwar aure kinfi ƙima daraja da kuma martaba duk kuwa irin talaucin da mijinki yake fama dashi , kiyi haƙuri kiyi zamanki a gidan aurenki arziƙi na Allahna , kuma wannan ɗin dai shine hatimin tsirarki. Yayin da kika kalli kanki a madubi kika ga ke kin kai ƙarshe wurin haɗuwa ko kyau tou albarkacin martabar aure kika ci , daga zaran inda kikayi yarinta irin tawa kika zuge auren nan kin tashi aiki.

      Saboda kiyi duba da wani abu. Gidanku da gidan miji akwai ƙaton banbance² , karki kalli gidanku ana kashe kaji goma duk rana , ana yanka rago duk sati , kina da ɗakin sama ƙaton gado da a c ba’a ɗauke wuta ga wata ɓarkekiyar talabijin ta cinye rabin bango. Kuna cin shagali shayi da biredi duk safiya a haɗa da wani lafiyayen kayan cikin rago , dankali doya kwai da rana a samu wani lafiyayen abinci aci ku kulle na dare da wasu kayan marmari , idan zaki fita a baki driver ko ke ki tuƙa kanki , idan buƙatar shiga bayan gida yazo zaki sauko ne kawai daga saman gado ki shiga toilet hmmmm. Gidan miji kuma koko , tou wallahi wannan kokon ya fiye miki mutunci da kuma kwanciyar hankali , idan kuma kina ganin kin haɗu bara ki kashe auren kiyi gaba , tou budurwar bana tafi ta bara , duk haɗuwarki duk nasabarki duk mutunci duk yadda kike jin kina da nagarta siga ko kyau duk haɗuwarki duk kuɗin gidanku duk iyakar gogewarki da haɗuwarki idan wasu matan na (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); wure tou wallahi ke mayino ce , da kika kalli madubi kika ganki ke kyakkyawa ce ko kin haɗu tou darajar aure ne yasa kika zama haɗaɗɗar idan har tsautsayi ya kaiki kika cire auren nan kina tunanin zaki auri sarki tou fa lallai ko dogari ba naki bane ba danma karki ji ƙamshin masarauta. Ku kiyayi rashin kunya wa mazajenku , kar kuyi irin nawa kuga zagin miji ko rashin kunya ƙauracewa shinfiɗarshi ko rashin mishi sannu da zuwa hanashi abinci da rashin yi mishi magana shine mafita , a , a , wannan babban zunibi ne ga kuma ke mai aikatawa kina kashe kanki ne , kuma kina rage ma kanki mutunci , duk duniya babu abinda yafi mutunci haƙuri da kuma biyayya , zaman lafiya yafi komai karki kuskura ki zama mai tashin fitina a gidan aurenki , ki zaɓi zaman lafiya yafi komai ki kuma kiyayi kanki da haƙƙi……. Karki ce irin halina ya burgeki uhum a , a kar kiyi….
     
      Har dare haka na samu aiki jikin madubi. Saidai inyi sallah in dawo inci gaba da kallon kaina , saida aka kira isha’e nabar jikin madubi naje nayi wanka tare da ɗauro alwallah dan gabatar da sallah , ina gama sallah na fito dancin abinci. Zama na kenan ban fara cin abincin ba akace min wai Umar yana jirana a palon ƙasa ,

     Cewa nayi aje ace masa banda lokacinshi , tunda dai na gano makircinshi nasan yadda zan zauna dashi. Ai ni lokacin nida Dikko zai aureni shine yaje ya faɗawa Jiddah , amma ni za’amin bazai faɗa ba , shima Dikkon zai dawo ya sameni sai ya sakeni tunda ba tare aka haifeni dashi ba….

      Momy kuwa idan hankalinta yayi dubu ya tashi ɗaya bayan ɗaya , Aunty Bilki baƙar muguwar munafuka ne ta bugawa a jikin mujalla , Umar yazo ya faɗawa Momy Mai gida fa yayi tafiya da Sharifa , wai duk girman Dikko ita Momy bata daina fargaba akanshi ba , ga kuma Papi data matsa mishi tace dole sai yaje dashi tunda hada su Ashiru zai tafi. Saida aka kai ruwa rana ya yadda yayi tafiya da Papi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
    Dikko kuma koda yaga saƙonni Sultana baima da lokacinta bare kuma yasa ran zaiyi tunanin bata amsa , mafiya yawan mata suna da cusashshiyar ƙwalwa , ƙalilin ɗinsu ne zasuji zancen ƙarin aure suyi abu na hankali da tunani , ita An mata bai ɗauketa mai hankali ba. Amma insha Allah idan yaga wanda zai auri mai ƙaramar shekaru irin An mata saiya bashi shawara kar ya aura yaje ya auri macen da tasan abinda takeyi , shidai yau gashi har An mata tace mishi karuwa wai shi…. Shine karuwa kamar An mata ta zauna ta rubuto mishi zagi na rashin mutunci , haka Jiddah itama tayi lokacin da zai auri An mata tayita hauka tana zaginshi. Jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai yace aure ba fashi sai nayi idan kin gune ki gyara hali. Kallon Papi yayi dake kwance jikinshi yana bacci duk ya rirriƙeshi saboda gajiya , a bayyane yace idan An mata batayi hankali yanzu ba yaushe zatayi hankali ?  Shi kuma yana ganinshi babba duk ya wuce irin wa’anan shirmen , da kuma anyi rashin sa’a suna wuri ɗaya tayi wannan maganganun zai ɗauki zafi shima ya yaɓa mata magana mai zafi ita kuma ta kasa riƙewa ta tattaro nata ɓacin ran da yarinta ta kwaɓa mishi rashin wayau.

     Daga nan sai duka , ita kuma a kunne take sai fuuu ta tafi gida tayi yaji. Yadda Mamarta bata sanshi bata ko ƙaunar ganinshi itama sai ta tafasashe ta fara turo doguwar wasiƙa a saki “yarta , ƙalilin matsala ta fito amma ƙaliliyar magana bata iya kashe wutar dake ƙoƙarin ruruwa. Yana ta ƙoƙari wurin ganin ya farka da ita daga baccin rashin wayan data tafi amma baida lokaci kuma shi a ganinshi abinda yasa An mata ta rainashi girmanshi tun farko daya buɗe a gabanta. Yana gani shekarunshi yakai na ita ta girmamashi tasan matsayinshi da ƙimarshi ta kuma riƙa kiyaye wasu kalaman akanshi bata gani kuma bata dainawa. 

   Shidai da shine mace mijinshi ya tashi ƙara aure ba zagin mijin zaiyi ba , zagin miji , rashin kunya , ƙauracewa shinfiɗarshi da zance yaji ko tambayar sakin aure bashi ne mafita ba. Haka kuma bazai daina dafawa miji abinci ba , sannu da zuwa da Allah ya kiyaye hanya duk sai yayi , da farko dai abinda zaiyi shine , zai duba wace ce mijin nashi zai aura , shi kuma ɗin waye shi , ita wacce za’a auron ya take ? Shima ɗin ya yake ne ? Me yafi ta me tafishi ? Me gareta wanda shi bai kai ba ? Duk namijin da zai ƙara aure dole yana da wani dalili nashi na daban tunda kowa da ra’ayinshi kuma ba a bayyane yake ba a ɓoye yake. Gyara dai kawai shi yafi a gareki , bawai sai auren yazo ba kullum ki kasance a gyara da kiyayewa tsafta biyayya iya lafazi da girmama shi. Kuma duk hakan bazai hanashi ƙara auren ba idan Allah ya rubuto da wani rabon. Kije kiyi duk abinda kikaji kina iyawa danni banda  lokacin da zan zauna na koyar dake zaman takewar rayuwa na yau da kullum ƙaramar yarinya dake.

    Duk kyan mace idan ba gyara zero. Duk nagartarki da sigarki idan babu biyayyar aure zero. Duk kuɗin gidanku idan kinajin ke wata shegiya ce idan baki bi mijinki kuka zauna lafiya ba baki haɗu ba. Duk kuma yadda namiji yake sanki a zuciyarshi rashin kunya da rashin mutuntashi ke ƙaton zero ce mai ido da kunnuwa a wurinshi dan rashin biyayya wa namiji ba ƙarami rage miki martaba yake ba. Amma duk rashin kyanki idan dai kina da ɗa’a da biyayya haƙuri tsafta iya girki kauda kai akan duk girman abu bawai dan ba’a ɓata miki ba , a , a haƙuri dai kikayi kika bashi baya tou kinyi a haka idan kika haɗa da iya gyara tsakiyar filin wasa. Misali duk kyau ko (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); haɗuwar abinci. Yaji manya tsokokin nama yasha mai idan dai babu kayan masarufi da aka sarrafashi dasu duk wannan manya namomin idan kaci sai ka tofar saboda ba’a ƙawatashi da abinda zaisa ya ciwu ba , wasu zasu nemi magi yaji da ɗan gishiri su gyarashi dan su samu damar ci a sauƙaƙe amma bazaiyi daɗi ba a hakan ma tunda ba’a dafo dasu a tare ba , ɗan ɗanon dai zai bada wani iri daban kawai dai babu daɗi , tou haka kyakkyawar mace take idan babu abinda na lissafa a sama ko an zauna da ita sai an tofar. Ku gyara domin zamani ya canja akala fa……

      Daga Abuja Sharifa tayi sallama da Dikko ta juyo bayan ya ajiye mata manyan kuɗi a account ya kuma bata wasu a zahirance , danshi mutum ne mai bala’en san yaga kana girmamashi ka kuma yi mishi ladabi. Haka kuma Dikko yake san godiya idan yayi maka abu kuma wannan halin shine tuni yake ƙoƙarin ganin ya koyawa Sultana , tunda ko dukanta yayi zaice ta gode masa.

      Tunda Sharifa ta dawo katsina taci gaba da halba hotunan da ta ɗauko ita da Dikko , da yake ta iya kwanciyar aska har Papi ta jawoshi jikinta yana kwakwarta. Dan da zata tafi shine Papi yaita kuka yana cewa Yaya mu tafi da ita , shine abun ya bawa Dikko mamaki tunda Papi yake bai taɓa kuka idan An mata bata nan ba , ko idan zata fita. Sai yaga zama ɗaya duk rashin yadda na Papi yana kuka dan Sharifa zata tafi. Wannan abu ya ɗaga hankalin Dikko anya An mata tasan abinda take ….?Tsakaninta da Papi duka ne idan kuma yayi mata magana sai tace ai shima haka yake dukanta kamar wata jaka saboda haka wurin ɗanshi zata rama duk dukan da yasan yayi mata a duniya.

    Mai gilashi kuwa tana ganin status in Sharifa kuma tabi duk ta yaɗa a kafafen sada zumunta na nahiyar yanar gizo. Hankinta fa ya tashi , kuma tayi alƙawari da rayuwarta ko zata mutu yadda Sharifa ta lalata mata aurenta wallahi babu gudu ba ja da baya itama sai ta lalata nata da Dikko. Addu’arta ɗaya shine Sultana ta bata haɗin kai a dai² lokacin da Sultana ta ɗauki waya. Mai gilashi barka da dare. Yawwa matar D ‘ K ya gda ? Lafiya qalau ya Papi ? Wallahi baya nan yayi tafiya da Babanshi. Zuwa ina haka ? Kinga ni wallahi bansan ina suka tafi ba , kai ƙawata ƙaddarorinki har biyu basa nan kuma baki san ina ne suka je ba ? Ey bai faɗamin ba nima ban damu da sanin can inda zaije ba , kai Sultana ? Tou me yasa haka ? Ke kindai san halina sabgar gabata ma ta isheni…… Lallai sai wata “yar iskar banza da bata aurar miki miji ba tasan ina zaije. Gaskiya ke Sultana jakace , nice jaka Mai gilashi ? Cikin kwantar da murya Mai gilashi ta fashe da kuka tace Sultana kiyi haƙuri idan ranki ya ɓaci matsala ce na hango miki ina ta ƙoƙarin gyara miki amma kin gagara fahimta ta  , wata maƙiyata mijinki zai aura , idan har kika kuskura ya aureta wallahi׳ ƙaryarki ta ƙare……..!!! Tana faɗin haka ta tsinke wayarta.

    Mai gislashi na fita a wayar Sultana kiran Momy yana shigowa , irin zagin da take ma “ya “yanta irinshi tayi min , kuma tayi min rantsuwa da Allah idan har ban raba Dikko da Sharifa ba idan tazo gidan abin bazai min kyau ba , kuji wani irin ɗanyen hukunci. Momy wace Sharifa ce ? Kamar dai yadda Nabeela ta faɗamin haka Momy itama taimin bayani. Sannan ita ma ta kulle da cewa , idan har kika kuskura Dikko ya auro Sharifa wallahi׳ kashinki ya bushe , Dikko tsabar tantirin kwallon ɗan iska ne shi. Duk yadda baki zato ko tunani ya wuce. Idan kika bari ta shigo tou tabbas kece a waje………. Tana faɗin haka ta kashe wayarta. Abin duba anan shine , da Dikko manemin mata ne idan har Sharifa ta dafeshi sai ta Allah saboda sabon halin da nazo mishi dashi , kunga dai nice da kaina na ƙirƙiri matsala a gidana saboda ɗaukar shawara marar makama , idan kuma an samu namiji mai surutu daya je wurin mace zai kwace ɗimi kamar ya lashi wuta matarshi kaza². Tou macen bariki bata bashi haƙuri saidai tace rabu da banza taje can ta ƙunshe har yayi wari , duk lokacin da kaji kana (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); buƙata kazo in baka. Kinga daga nan kin zama ruwan kwance , haka take faruwa ne yanzu. Kina zaune da mijinki lami lafiya hankalinku kwance baki nemi komai a wurinshi kin rasa ba , haka kawai sai kiga ya tsiro miki da wasu sabbin ɗabi’u yana cin ubanki babu gyara babu dalili. Duk yabi ya ƙuntata miki ki rasa abinda kikayi mishi ya fito da wasu manyan miyagun halaye wanda kuma ke ada sam baki sanshi dasu ba , hmmm bance mijinki ba kila ya samu wata mace can ta riƙe mishi wuya an barki da ciwon damuwa. Haka suke matan bariki su ba aure suke ba mazajen wawayen mata suke mayar wa jarinsu , sune zasuyi ta karta suna ƙwalƙwale musu aljihu. Su riƙesu da bariki suyi ta gabatar da wasan danbe kina gida kwance kamar asara kinci kinsha sai neman fitina da hana ma miji zaman lafiya , ɗari biyar tayi miki wahalar gani dubu ɗarin shi tana wurin mata. Wanda kuma ya faɗa miki gaskiya ya zama abokin gabarki rai ba haƙuri sai a tattara kaya ayi gaba…. Kudaiyi nazari sai ku gano inda damuwar take mune ko su ?…… 

    Bayan Momy ta kashe waya taci gaba da faɗa , waime ma Sharifa take dashi baƙar banza , me Dikko ya gani a jikinta ? Ga matarshi kamar balarabiya ta fara haifo mishi kyakkyawan ɗa dan Papi yana da kyau sosai masha Allah , ita ko Momy tana ma mamakin yadda Dikko lokaci guda ya zama mara kunya , saboda a da ta mishi maganar Sharifa da farko kenan dai yace mata ta kwantar da hankali komai zaizo a sauƙaƙe , jiya kuma da zaiyi tafiya tai mishi maganar Sharifa ce mata yayi ci gaba ake san samu. Dogon nazari Momy tayi tou wane ci gaba zai sama wanda matarshi bata bashi ba ?Tayi maganar a bayyane tare da rufe idanuwanta tana wasa da wayarta a saman goshi.

     Babban gidan daya sha ado da ciyayi , sai mamallakin gidan ya fara samun matsala. Misali , tsakar dare sai yaji ana dukanshi sai ya tashi dan ganin mai dukan nashi , amma saiya duba ya duba baiga kowa ba. Ya sake komawa ya kwanta a tsorace ya kasa bacci sai yaji haniniyar doki da ƙarar takonshi yana tun karo shi. A firgice sai ka tashi , kana tashi saika sake ganin ba kowa. Amma sai aka gaggaɓe maka da dariya , me zaka fahimta ? Da farko dai idan zamanka ne na farko a gidan zakace iska ne , idan kuma ka daɗe a gidan baka taɓa jin irin haka ba zakace jifa ce { asiri } daga nan sai ka samu ayi maka addu’a dan kawar da wannan matsalar. Amma sai abun yaci gaba maimakon a samu sauƙi sai damuwar taci uwar ta farko , bayan wani lokaci sai kaji ana cewa idan baka tashi ba a gidan nan zamu kashe ka , ko zamu nakasa ka , sai kaƙiji baka tashi ba. Bayan wani lokaci sai a nakasa maka ɗa ɗaya ko kai. daga haka kai mai gidan zaka fara nazarin canja muhalli ƙarshe kana iya samun ƙaramin gida wanda baikai ƙwatar wanda kake ciki ba. Ba shakka ci gaban da Dikko yake nema matsalar tana nan ta tare a wurin Sultana. Wata zuciyar tace a , a matsalar tana wurin Dikko , wani sashe na zuciyarta kuma yace wallahi Sultana ce mai matsalar amma abinda za’ayi ki fara zama da ita ki gano ina damuwar take , idan ta gyara zakiji zance aure ya mutu , idan kuma Dikko yayi aure tabbas matsalar tana nan wurinshi……

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
   Duk da bazai yuwu mace ta hana mijinta aure ba idan Allah ya rubutu hakan. Wayonki ko dabararki hikima da iya tattalin miji duk kissarki duk kwarkwasarki duk feleƙenki da iya duniyancinki idan Allah ya rubutu da rabon wata a cikinshi sai tazo , idan kuma kika taso da hauka sai ajalin rabo yazo yayi gaba dake. Ita bawai ta hana Dikko yayi aure bane ba a , a iskancin ita Sharifa ya girmi tunanin duk inda mai tunani baya tunani , musulmin karuwanci takeyi gata da kisan mummuƙe kuma haka ta kware wurin iya kwanciyar kwantar ɓauna. Ba Sultana ba har ita idan har Dikko yayi gigin aurar Sharifa tou fa lallai itama kanta Dikko ba nata bane ba.

     Wata irin dariya suka gaggaɓe da ita gaba ɗaya duk karuwar dake wurin , ƙarar kiɗa ta karaɗe kaf ilahirin girman gidan karuwan dake can wurin Sitirolin , sanye ta shigo cikin wata irin zureriyar hijabi tasha niƙaf da safa , tana shigowo aka canja sabuwar waƙa ta matan bariki , da rawa Sharifa ta shiga tana shiga tsakiyar wurin da ake gabatar da shagalin ta cire hijabinta daga ita sai fant da bra , *KWARATA* n ta kuwa sukace gasu nan , a tsakiyar fili suka fara ɓarin kuɗi….

      Mai gilashi kuwa tana gama waya da Sultana ta fara kiran wani kwartonta , babu wani daɗewa da ɓata lokaci ya ɗauka , ba ko gaisuwa tace kana ta ina ne haka ? Ina gidan “yanci ya faɗa a taƙaice , na wace anguwa ? Ya faɗa mata ko wane yake , kaga Sharifa ne ? Bana tare da ita tana can babban gida. Lafiya ne dai a wurin ? Ey tanayin shagali ne , wanda zata aura yaje egypt daga can zai wuce yayi umara yana dawowa za’ayi musu baiko…. Waye zata aura ne ? D ‘ K mana. Shima ya zama ɗan hannu kenan ? A , a , to me yasa zai aureta ? Nima dai ban sani ba , shiru Mai gilashi tayi tana nazari bayan wani lokaci tace sai anjima ta kashe wayarta….

      Bayan sati 3…

Haka dai rayuwar take ta doka ƙaraurawa tsakanin rayuwarmu gaba ɗayanmu. Kwaɗo , ni su Amisty , Mai gilashi , Sharifa , mardiyya , Yusra Yazeed Jiddah Aunty Suwaiba Momy Aunty Bilki & Dikko…..

    Har yanzu Dikko bai nemeni ba nima na manta dashi , ina nan ina fama da girman kai , kuma kullum saina ganshi online. Bayamin magana nima bana mishi , dani dashi kowa yana huɗɗar gabanshi kawai , ko hotunan daya turomin nace masa basuyi kyau ba. Daya gani bai bani amsa ba , 

    Dikko kuma bawai yayi fushi bane ba , a , a ya dai zubawa Sultana ido yaga iya gudun ruwanta da hankalinta. Shin zata nemeshi ko kuwa ? Shima kullum yana ganinta online , idan ya ganta saidai yayi murmushi yace An mata kina ɗauwaniyar da yarinta , wai ni ? Nine kike ma haka ko ? Hmmm ai ya miki kyau….

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
    Kullum sai Momy ta kirani tace nayi waya da Dikko ? Sai ince mata nayi. Shine ya faɗa mata bana kiranshi koma dai miye nikam ban sani ba. Nabeela ma ta kirani tace matar Yaya kinyi waya dasu Papi ? Itama nace mata nayi Rabiya ma haka……

      Gaba ɗayanmu zaune muke a palo. Duk mu 6 ɗin babu wanda yake magana , palon yayi shiru irin yadda yara kecewa mutuwa ta ratsa da ba’ayi shiru ba data ɗauka. Mai gilashi kuwa ta tsareni da kallon takaici nima na ƙura mata ido naƙi na daina kallonta. Kowa yana kallon kowa bayan ta faɗamin cewa ta gaji da rashin zuwata makaranta kullum² da banayi kuma bana ɗaukar wayarta sai naga dama to tashawo ta dubu tazo. Murmushin takaici tayi tare da kauda kanta gefe tana girgiza kanta cikin yanayin damuwa……..

     Gabatar min da ƙawayenta tayi. Hadiza Fadeela Halimatu Zainab sai ita duk dani mun zama shidda kenan. Ƙawayena ne su dukansu kuma duk matan aurene. Wacce ta kira da Hadiza ta nunamin tana ci gaba da cewa kinga wannan ƙawata ce sosai Hadiza kenan , amma mu a cikin ƙawayenmu muna kiranta da ashana. Kallonta nayi sosai bayan wani lokaci nace ƙona gidan kowa na faɗa ina jinjina kaina. 

    Ita kuma mai gilashi taci gaba da cewa , su duk maƙota ne kansu a haɗe yake kowa bata ɓoye sirrin kowa. Nuna su tayi duka , tana nunasu tana tafiya da maganarta cewa kuma mu dukanmu a gidan wannan muke zaman majalisa ta nuna wacce ta nunamin a matsayin Halimatu. Idan kin yadda zaki shiga cikinmu kema kije majalisa ko azo gidanki ayi. Inji Hadiza kenan ta anshi maganar daga hannun Mai gilashi. Nace a , a , me yasa ne ? Saboda nan ɗin ba gidana bane ba. Tace ya raina ki kenan shi yasa kika ce haka ? Ummm gaskiya kam ko bai rainani ba ni har yanzu banfi ƙarfinshi ba saidai , zan bar gidanshi na faɗi barin gidan a zuciyata. Ita kuma Halimatu tace nikam nafi ƙarfin nawa domin ina amfani da kayan mata masu kyau shine yake bina bani (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); nake binshi ba dan yana tsoron yayi min laifi dare yayi in juya mishi baya….

    Wata irin haramtacciyar batsa Mai gilashi ta liliyo ta watso , gaba ɗayanmu dariya mukayi na tsere Mai gilashi da ido danni dai Allah ya sani ɗan tasha yana burgeni sosai. Har kowa ya gama dariya ni ban daina ba , wayata na ɗauka na rubuta batsar ina dariya. Ban gama dariya ba ta fara bada labari dan kawar da zance ni na shiga madakatarsu ita tafi so tayi zama daga ita sai Sultana dan ganin Dikko bai auri Sharifa ba…

     Ita kuma idan ta faɗi zancen iskanci bata dariya sai ta ɗaure fuska taci gaba da bada wani labarin , kai da ake bawa labarin kaine abun zai daɗe yana zungurar zuciyarka kana dariya. Kuma ita bata munafurci akan iskancin da takeyi duk namijin data nema sai ta faɗa. Ci gaba tayi da cewa , wata rana naje asibiti banda lafiya dani da Hadiza mukaje , ta nunata , murmushi Hadizar tayi tana kallon Mai gilashi. Ita kuma bata kalli Hadiza ba taci gaba da cewa , ciwo ya isheni kamar zan mutu , sannan ban daɗe da aure ba. Kuma ban fara tararayya da Alhajin da muke gidanshi ba. Nadai ɗana masa tarko yana ta wani zuƙewa , ni kuma jin labarin zamu zauna a BQ in gidan wani attajiri yasa nasha uban gyara , ashe abun ba sauƙi ne dashi ba , wasu mazan tayi ɗaya kake musu su amsa wasu kuma sai ankai ruwa rana sai ka nuno musu maitarka fili , jin zanzo zama a BQ n gidan kuɗi yasa na ɗirki kayan mata kamar ba gobe. Mara ciwo ciki ciwo kamar zan mutu , shi kuma ango ya saki baki yana jiran a kawomishi Sa’aden banza yashani basilla. Auren da akayi da ganganɗe² sai kawai inzo in zauna ya sussukeni kamar ƙasar kasuwa yaita bi yana wuce babu wani gata. To banzo gidan ba saida naje aka sakamin allurar tazarar iyali na shekara biyar implant , abinda yasa nayi har na shekaru biyar shine.

    Na farko dai zan fita daga gidan wanda nake aure a yanzu zanje in samu matashi mai ƙarfi da wadatacciyar lafiyar gabatar min da wasan danbe ko ba abinci dan ina tara manyan kuɗi a asusun banki na , saboda idan nayi sabon aure ba maganar zina zan tuba ga Allah ne na nemi lahirar da gaske tunda dai mun samu mun ajiye tarihi a katsinar…. Duk gidan karuwan dake garin nan idan kikaje hotuna ne na farko a jikin album insu saboda nice karuwar data fara lalata namijin da bai taɓa karuwanci ba. Nice karuwar dana fara karuwanci da “yan (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); samarin yara wanda suke makarantar gaba da primary , wato secondery sch. Makarantar masu kuɗi nake bi ina zaliƙo “ya “yan wanda Babansu yafi kuɗi , nice nake ɓatasu in kuma sa suyomin satar kuɗi a gidajen iyayensu su kawomin ni kuma na ɗorasu a network sune sukaji yadda abun yake sai suke farautomin abokansu ina basu suna bani kuɗi. Tarihi ya nuna ni nice karuwar danayi iskanci da wani tsohon malami wanda yake wa’anzatarwa da tunatar da karuwai muji tsoron Allah mu daina zina , to nice naje na rufe bakin wa’azi dan shima malam ya zama kwarto , nice karuwa ta farko da tayi ma namiji fyaɗe kuma Baban ƙawata ne har a cikin ƙuryar ɗakinshi kuma a cikin gidanshi.

    Nice karuwar dai da karuwancin yasa na fita ƙasashen ƙetare , { wai kunsan ina take nufi ? Wasu states in fa take magana } na kafa manyan tarihi sosai nice karuwar da ƙasa ya kamata tayi alfahari dani amma har yanzu gwamnati bata nemeni ba duk yadda na jajirce wurin yima jahata hidima. Na bautata ma jahar katsina sosai wurin ganin na ciwo mata babbar lamba a cikin sahun manya karuwai duk a cikin shekaru 2 nayi wannan ɓarnar ina da shekaru 28 a duniya. Amma har yanzu ba’a haskoni a cikin talabijin ba , saidai dana kamo tasha dan ganin ko za’a hasko ni sai inga ana cewa wannan ce taje gasar karatu a wata ƙasa , sune sukaje fareti gaban gwamna , manyan “yan kwallo sune suka ceci wane daga kaza , an kamo manyan ɓarayin da sukayi sata a wuri kaza suka samu damar nasarar guduwa tou an kamosu , ko sune sukaje wurin musabaƙa , ɗan sanda kaza ya kamo “yan ƙwaya da dai² sauransu wannan itace ta zama kaza² amma an kifewa karuwai ciki duk babu su a cikin tv. Haba ai nayi ƙoƙari sosai shi yasa ko kinje gidan karuwan dake garin nan sai an baki hotuna na kin gani tare da bada ɗan taƙaitaccen tarihin rayuwata cewa kiyi koyi dani. Tarihi kuma dai har yanzu ya sake nunawa nice karuwa ta farko da nayi aure na koma makarantar boko. Kuma nice karuwan dana faɗi bayan na haɗu da abin harin nawa { haɗuwarta da Dikko kenan } , zan tuba amma sai nan bayan shekaru biyar. Idan kika mutu kafin lokacin fa ? Na tambayeta , kallabin kanta ta cire tana duƙomin da kanta daya yasha kitso da ƙarin gashin doki , furfura nawa kika gani a kaina ne ? Ba ko ɗaya na bata amsa , rufe kan tayi tana cewa sam mutuwa bama zata fara zuwa wurina ba a yanzu. Ke kina da matsala ana maganar arziƙi kizo ma mutane da wata maganar da bata dace ba. Ta ƙarasa maganar tana tsoki tare da gyara zaman gilashin dake manne a saman fuskarta cewa tunda ma kika kira mutuwa na fasa baki labarin. A haka dai ta tsaya bataci gaba ba ta tattara zugar ƙawayenta suka tafi tana cemin inyi ƙoƙari inzo makaranta…

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
        Duk mutanen dake cikin gidan sun kasa bacci a daren nan saboda wani irin kuka da Hafsa takeyi mai tada hankali. Sai burgima takeyi tana riƙe hannunta dake zubar da wani irin ruwa marasa kyan gani , da anzo warware hannun sai tace karku buɗemin hannu ku tafi ku barni , fita kowa yayi daga ɗakin aka barta ita da Amisty , tagumi Amisty tayi tana tunanin yadda sukayi da malamin. Tayi masa bayani kaf akan labarin rayuwar Hafsa da kuma yadda take san Dikko kamar ta kashe kanta , tace zata rako Hafsa idan tazo karya nuna yasanta suna zuwa yaja zare ya karanto mata komai kuma yace zai iya aikin yasa kuɗi masu yawa , ita zata ma Hafsa wayau ta saido gidajen Dady a kawo kuɗin sai ita da Malam su raba kuɗin , ya yadda ? Yace ya yadda da hakan…..

    Cike da yaudara Amisty ta fashe da kuka ta rumgume Hafsa sukaci gaba da kuka tare , saida suka sha kuka har suka gode Allah sannan Amisty tayi ma Hafsa labarin ta gano inda malamin Sultana yake ta kuma ƙara da cewa shine yayi ma Sultana aiki ta auri Dikko dan haka zasuje wurinshi idan Allah ya kaimu , Hafsa taji daɗi kuma tayi na’am da haka ta ƙara riƙe Amisty sosai a jikinta tana godiya.

       Ya Yazeed idan baraka damu ba ina so muyi auren sati ɗaya , sarai fa ya gane amma sai yace ya auren sati ɗaya yake ne ? Zaka aureni ne bayan sati ɗaya saika sakeni ina so zan koma ɗakina ne , kallon rainin wayau Yazeed yayi mata cewa gaskiya banayi , dan Allah Ya Yazeed , cike da duniyanci yace tou faɗi farashi ɗaya mai tsoka naji , wane irin farashi ne ? Jiddah ta tambaya , Yazeed yace kije ki fara tambayo yadda abun yake , yana faɗin haka ya wuce wurin motarshi ya shige yaja ya kama gabanshi cikin farin ciki. A ranshi kuma yanajin yakai wani babban ƙwaro shi zai auri matar da D ‘ K ya saki , farashin da yake magana kuma shine ita Jiddah nawa zata biya shi ya aureta , idan kuma ya aureta zataci ubanta sauran ƙudirin nashi kuma shine da zuciyarshi yabar ma ranshi……

       

       *JAMILA MUSA…*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button