NOVELSUncategorized

KWARATA RETURN 9

               *KWARATA RETURN…*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

Rubutawa…
            *JAMILA MUSA…*
       *SAI NA AURI D ‘ K*

???? —— 9

        A palo na sameshi zaune saman kujera. Ci gaba nayi da kuka na nufeshi. Hankalinshi yana saman wayanshi yace so kike dai in zaneki ko ? Kusa dashi na zauna nace baka san ya nakeji ba. Riƙoni yayi da hannun da wayar take riƙe cikin tausasassar murya yace baki so in zaneki ne ? Yayi tambayar yana kwantar da firgitaccin idanuwanshi masu saukar da kasala. Kaɗan na kalleshi a kasalance na ɗaga mishi kaina alamar ey. Yace to shikenan jeki ciki ki kwanta ina zuwa. Miƙewa nayi na riƙo hannunshi ina janshi , ba tare daya kalleni ba yace ya wai meye kuma ? Ban bashi amsa ba naci gaba da jan hannunshi , taƙaitaccen kallo yayi min sannan ya tashi muka shiga ciki tare.

        Cike da farin ciki Yazeed ya isa gidan Rabiya. Yau ciki aka shiga kasancewar ita matar gida bata nan. Yazeed kuwa tun a waje ya ɓalle botiran gaban rigarshi yana nuna yanayin haɗama. Kai tsaye ɗakin da aka bawa ita Jiddah a ɗakin ta wuce da Yazeed , suna shiga ya rumgumeta suuuu suka sulale saman gado gaba ɗayansu sunayin farin ciki tare da nunawa junansu kowa yayi maraicin kowa.

       A gaggauce dai aka shiga gabatar da wasa. Ya nemi yaddar gado da kuma sa’ar makoma sai addu’a na gaba ya samu nasara mai girma. Danshi a tunanin shi a filin wasa ake. Wasan yau yafi ko wane wasa martaba da mutumci a wurin Jiddah , kasancewar an samu wadatuwar fili da tsaftatuwar muhallin da akeyin wasan. Yazeedu kuwa ya ɓata manyan awowi kuma ko wace awa minti da seconds ya bada lafiyayyen naushi mai zama a zuciya har abada. Jiddah ma ta mayar da martani domin ita dama tuni Yayanta ya gogar da ita kuma ta ɗauki karatu.

     Rabiya kuwa tunda Yazeed da Jiddah suka shiga ita ta iso gidan , biyosu tayi tana lafiya ? Ina ne zataje da namiji ? Duk babu wanda yaji bare kuma yasan tana magana , suna shiga suka turo ƙofa garam har aka bige ma “yar sa idon banza goshi. Ai bawai Jiddah taji kunya ba ita Rabiya itace taji kunya dan haka ta koma ɗakinta tana neman mafita.

Taya zata iya furtawa Momy wannan zance ? Shedar zina wahala gareshi. Shin wai waye ma yace mata suna aikata saɓo ? Kuma ita bata kamasu sunayi ba , tou dan kawai sun shiga ɗaki ? Ta yuwu wani abu ya faru , sai saƙawa takeyi tana warwarewa lokaci² kuma tana kallon agogo kamar mara aikin yi har Yazeed ya fito , sai yanzu ta gane Yazeed. Shi ɗaya ya fito Jiddah bata biyoshi ba , tou meya faru ? Me sukeyi a ɗaki tsawon awowi 2 har zuwa 3… Ta shiga 3 zafa a samu matsala…..

       Saida Yazeed ya wuce itama ta fito ta nufi ɗakin Jiddah. Kwance ta sameta riƙe da wayarta tana ta latse². Da hannunta ta nuna da yanayin karta shiga haƙƙinta cikin warwarewar haruffa tace am Ji-dd- , ah Jiddah am dama nace lafiya naga Yazeed ya fita ? Ba tare da Jiddah ta kalli Rabiya ba tace lafiya qalau kawai kaina ne yake min ciwo ta ƙarasa maganar tana nuna kanta. Ɗan yatsina fuska tayi tare da ajiye wayar ta taci gaba da cewa gashi gida ba kowa kawai sai nayi ma Yaya D ‘ K waya ina buƙatar magani , shine fa ya aiko abokinshi ta ƙarasa maganar tana watsa hannunta….

      A ɗan tsorace Rabiya tace Dikkkkkkkkkko ? Ta kira sunanshi da mamaki cikin jan kalmomi wurin faɗar sunan tare da warware kaf ilahirin gininta. Ummm Jiddah ta faɗa tana jinjina kanta alamar gasgatawa. Rabiya tace taf Dikkon ? Jiddah tace shifa. Fuuu Rabiya ta fita , murmushi Jiddah tayi tare da cewa ai nasan idan na shigo dashi a tafiyar dole zai fito yayi masifa ya tilassa ayi auren , ba jiya naje muyi magana ba shine ya basar dani yana waani dariyar banza , An mata rigima , rigimo. Dariya ta sakeyi kaɗan tare da nunawa da “yan yatsunta sati biyu cif zanyi nayo waje. Wata 3 idda a cikin wata na huɗu zamu tare a sabon gida. {{ G R A }} a wata na biyar kuwa Caca zata kama gabanta , Pa-Pi zai zama nawa , wama ya sani ko jinina ne aka kai can…..? Da yanayin tunani tace babu shakka Pa-Pi nine uwarshi shine yake ƙwaƙwata , oho dai hakan ma bazai hana in kasheshi ba…….

     A tsagin Rabiya kuwa tunani takeyi , meye tsakanin Dikko da Jiddah ? Wane irin magani ne ya bada a kawo ma Jiddah ? Ciwon kan ƙaniyarta ? Karfa su maida ita wata gwanjon bisa titi , tana can tana huɗɗoɗinta suyi ta wucewa ba tare da tasan so adadin da ake wucewa ba. Anya Dikko yana da gaskiya ? Kardai zagayewa yakeyi idan bata nan…..? Har zata kira Momy ta fasa kawai ta kira Dikko. Babu daɗewa ya ɗauka ko gaisuwa babu tace yazo yanzu²n nan tana nemanshi. Magana yayi sannan ta bashi amsa da cewa kawai kazo nace idan kuma ni inzo tou… Magana ya sakeyi ita kuma tace shikenan kayi sauri ina jiranka.

        Dan Allah kaje tare dani. Cikin faɗa yace wai ina ne zanje dake ? Saida nayi kalar ban tausayi da marainiyan murya nace dan Allah. Baimin magana ba ya ɗauki wayoyinshi , shikenan tunda bara ka fita dani ba Allah yasa ka dawo ban….. Bakiyi me ba ? Gyara bakina nayi ina kallon ƙasa , bai sake kallona ba yace zo muje. Da sauri na wuceshi na tafi ɗakina , hijabi kaɗai na ɗauka ko wayana ban tafi da , nayi waje. Pa-Pi shima biyoni yayi yana kuka jaije…. Kafe kai yayi shi bazaije da Pa-Pi ba , shi kuma Pa-Pi riƙeni yayi idan ba’a zuwa dashi nima babu inda zanje. Dikko yace ka sakarmin mata kaji ? Yayi maganar yana zaro mishi ido. Da ita zanje kaine bazan tafi dakai ba. Riƙeni yayi Momy karci tafi ci barni. Dikko yace kai so nawa ka tafi ka barta ɗan rainin hankali sakarta nace maka. Kamar an matsi bakinshi yace kaicuwa jakuje….? Ya faɗa da yanayin tsoro ! Yaci gaba da cewa kuma fa’a cuwa da Pa-Pi ya ƙarasa maganar yana ma Dikko wani irin kallo haɗe da murmushi. Kete Momy ce cinyi kuka , jinjina kanshi yayi sannan yace cima Yaya ce yayi kuka ya ƙarasa yana dariya. Nuna kanshi yayi sannan na nunamu yace ni kuma can muku dayiya wayyayi. 

     Yadda yayi abun ne yaba Dikko dariya , yace ni kuma wallahi in zaneka. Dariya Pa-Pi yayi cewa kowa ce yayi kuka wayyayi. Yana ƙara yawan dariyar wai zaiga Yaya yanayin kuka. Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji lokaci guda wata irin zufa ta ketomin , murya a sanyaye nace ma Dikko nidai na fasa zuwa. Dariya Pa-Pi yayi tare da cewa wayyayi Momy taji tsoyo. Dikko yace keda Allah manta dashi taho muje yayi maganar yana jan hannu na , kinga sai kirana takeyi zo muje kinji….? Ƙwacewa nayi nidai kawai kai kaje , cikin rarrashi yace ke An mata haukan Pa-Pi zai tsorataki ? Da Allah zo muje yana ci gaba da jana. Fizgewa nayi nidai na fasa , cikin ɗaga murya yace kada Allah yasa kije kuma tunda har kika ce zaki kika fasa , idan na fita sai 2n dare zan dawo.

       Jiki a sanyaye na kalleshi. Ɗagamin gira yayi tare da kwantar da idonshi na haggu , a hankali ya fidda sautin sumba cikin natsuwa da salo mai tada hankali yana ƙara riƙe ganin idanuwanshi , duk iya masifar sa idonka bara ka gane abinda yayi ba , wannan karatun daga ni saishi kaɗai muka fahimci yaren juna. Ajiyar zuciya nayi kaɗan cikin ƙarfin hali , shi kuma ya ɗagamin hannu ya wuce. Tunda na fasa zuwa ya tafi da Ashiru….

      Dariya Pa-Pi yaci gaba dayi yana riƙe da hannuna har muka shiga ciki. Saida muka zauna na tambayeshi wai waye yace mishi zamuyi kuka ? Zama yayi kusa dani yace wai a cikin wayar Yaya ya gani , cike da ɓacin rai nace dan ubanka a wayar aka ce zamuyi kuka ? Kallona yayi ya ɗaure fuska shima da yanayin fushi yana hararata wai saiya faɗawa Yaya nayi zagi ya zaneni , shima ai jiya Yaya ya dakeshi da yayi zagi wa kare…. Tsoki nayi sannan nace ya tashi ya bani wuri. Ƙin sauka yayi saidai ya juyamin baya wai yama fata dani. Kaje ka ɓatan. Ba’a ciyyawa dake…. A palo na barshi na koma ciki , kasancewar zufar da naji inayi dole tasa naje nayi wanka. Ina fitowa kuma masassara tace gata nan zuwa , dakel na iya shafa mai kaɗan sannan naɗan kashe masƙin man da fauda , kayana na saka na kwanta.

        Dikko jin kiran waya yayi yawa , ya fara faɗa wai ita Rabiya bata da haƙuri gashi yana tafiya zuwa wurinta amma ta dameshi da kira. Wannan ɗan abun harya hasalar dashi danshi baida wahalar fushi amma yana saurin sauka. Cike da ɓacin rai ya ɗauki wayar a inda take ajiye amma sai yaga Inna ce take kiranshi. Ɗauka yayi da sallama ba Inna ce ta ansa sallamar ba mijinta ne ya ansa dakel yace kana ina ne ? Saida Dikko ya kalli hanya sannan ya faɗa masa ta inda yake. Tou wai kazo gidan Kaka dakai da Sultana. Lafiya Dikko ya tambaya ? Umm ai na tura maka saƙo ka duba , a , a , wai meye ne….? Baiyi magana ba ya ajiye waya.

      Wai Allahna , Inna ta tafi itama….. Lahaula walaƙuwat illabillah shine abinda ya furta. Dakel ya nunawa Ashiru ya koma gida , taya Ashiru yaci suka dawo gida , dawowarsu ne shi Dikko ya shigo ya samu Sultana tana wanka , ɗakinshi ya koma yana tunanin ta wace hanya shi zai iya furtawa Sultana wannan saƙo….? Ita ya zata kalleshi ? Saƙon mutuwa baƙin saƙo ne , har abadan duniya baraka manta da wanda yazo maka da wannan aike ba. Ya juya ya rasa yadda zaiyi , ko Ashiru bai faɗawa ba. Wane hali An mata zata shiga ? Zatayi kuka kamar zata cinye ranta ya sani , shima kuma za shiga tashin hankali , duk duniya a wannan rayuwa idan akwai abinda ke tada mishi hankali yake firgita mishi tunani yake sashi ɗimuwar rayuwa da manta shi ɗin ko waye wallahi bai wuce tashin hankalin Sultana ba. Shi kaɗai ya isa yayi mata amma idan wani ya taɓota bayan shi ? Tou fa lallai zaici gari da yaƙi….. 

         Kira ne yake ta shigowa a wayata babu ƙaƙƙautawa. A wahalce na miƙa hannu na dakel dan ɗauko wayar dake saman bedsite. Kafin in ɗaukota a hannuna tuni ta tsinke har wani kiran ya sake shigowa ya fita. Saƙo ne ya shigo dan haka ban fara duba rashin kiran dana samu ba na fara da saƙon.

        _Ke Sultana an faɗa miki uwarki ta mutu baki tahowa ? Tou ta mutu can wurin siya ma ɗanki abun wasa , mota tayi ƙoli² ta dakota da ƙasa sannan tabi ta kanta ta wuce. Ba wata tsiya nake kiranki ki bani ba bare kijamin aji ke surukar gwamna…_

      Yayar Inna ce surukar Sultan wanda zan aura da farko tasa aka fasa auren ya auri “yar ta. Duk me ya kawo wannan dogon bayani tou ? Salati nayi na sanar da mahalicci na daya isa da rayuwata. Dakel na iya gano number Dikko a wayata na fara kiranshi komai bana iya gani kasancewar inaji na a cikin wata irin baƙuwar rayuwa. Shikenan na zama marainiya gaba da baya , babu uwa ba uba , Allahu Akbar , tabbas ubangiji shine mai iko akan komai da kowa.

     _Kema ɗayar mara zuciyar_ 

      Itace kalmar data fara dawomin a cikin kaina , ina hango Inna palonta a daren jiya……

      _Me yasa shi ba’asan kawoshi ne wai ? Har sai wannan lokacin ? Kubar shi bana so tunda ba zaizomin yini ba._

       Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un , wani irin ihu na kurma , na fara magangu na sakin layi , kai… Wai Allahna , innalillahi wa’inna ilaihir raji’un , nayi kuka sau adadin yadda naji ciwon mutuwar Inna a zuciyata , haba Inna sai kuma kema ki tafi ki barni ? Shikenan ? Tou wai mema yasa kika je siyen wani abun wasa ? Waye ya aikeki ? Haba Innata meya sa²….. ? Kema shine dai kika tafi kika barni ? Gaskiya nadai zauce nayi maganganu marasa daɗin rubutawa. Dikko yayi maganar shi banama jinsa dan gaskiya bana iya gane abinda yake cewa. Kukan da nakeyi ne shine ya tayar mishi da hankali shima yaita kuka kamar ƙaramin yaro wai zai mutu. Shi baya so yaga inayin damuwa , in rufa mishi asiri nasan bashi da lafiya , shima yaji ɓarin maganganu kamar aradu ta faɗo. 

        Ko a gidan rasuwa haka naita bori ina ihu mai tayar da hankali duk wani imani , babu wanda ya damu dani bare yace ke daƙiƙiya ki gyara kalamanki ko kiyi ma mutane shiru , Kaka ce kaɗai take rarrashi na , sai Pa-Pi daya riƙeni yana ta ihu wai waye ya dakeni. Yayar Inna ni bansan abinda yasa bata ƙaunana ba , bansan me nayi mata ba ta tsaneni da zafi haka. Ko waye ya rasa yayi kuka , nidai a duniyar rayuwata banga abinda yafi rashin iyaye raɗaɗi da ciwo ba. Inajin yadda aketa faɗar yadda mutuwar Inna ta kasance. Wai bayan tayi waya dani a yadda shi mijinta ya basu labari.

        Baiwar Allah ashe abinda tayi mana jiya ya dameta. Ta faɗawa mijinta cewa gaskiya Dikko jajirtaccen namiji ne , kaifi ɗaya ne ita a yadda ta fahimta , tsaye yake babu munafurci a lamarinshi. Idan zaiyi kawai zaiyi idan bayayi ko za’a mutu zai tsaya a wurin. Wai tace masa idan yaji fushi ya sakar mata “ya , shine yace bai gaji ba , wai me yake nufi ? Ta ɗauki biro da takadda tayi rubutu akai , bayan ta gama sukazo gidan Kaka dashi da ita. Yace shi baisan abinda ya kawota ba , haka kuma baiji firarsu ba. Yau kuma tace a kawo mata Pa-Pi , wai shine taje ta sissiyo mishi abun wasa wai tasan Dikko zaiyi farin ciki dan ta goge damuwar data saka mishi a daren jiya. To shine fa ta gama sissiye²n tana zuwa wurin motar ta mota yabi ta kanta ya wuce…..

       Ni ɗaya a wurin Inna , banda Ya banda ƙani haka nake ni ziƙau ina , ba uwa ba uba ba Yaya ba ƙani. Ga “yan uwan Inna ni basa so na , ahalin Babana kuma gasu dai ga yadda suke , “yan uwan Dikko sune suketa bani haƙuri , bawan Allah shi kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye sai turowa Rabiya saƙo yakeyi wai An mata tayi haƙuri ta daina kuka , bayan wani lokaci kuma ya rubuto cewa wai shi yana nan bazai tafi ya barni ba insha Allah , hmmm haka dai yaita rubuce² har akaje aka rufo Inna aka dawo.

      Duk ahalin Dikko sun tayani zaman makoki har Momy. Mai gilashi da zugar ƙawayenta “yan tasha amma banda Halima tayomin gayyarsu zuga guda. Akayi ta gulma na wai ni na tara karuwai a wurin rasuwar Mamana , Nabeela ma tazo kuma tayi kuka kamar yadda taga inayi itama , ta tausayamin sosai , tamin sannu da rashi. Sati ɗaya nayi a gidan Kaka nan nake kwana , Dikko kuma idan yazo sai dare sosai yake tafiya dashi da Pa-Pi.

       “Yan uwan Inna kuwa bawai ta mutuwarta suke ba , abinda ta bari kawai suke ta lissafi. Babu kunya bare tsoron Allah suke farfaɗo suturunta kowa yana cewa ya kamasu , ita surukar Sultan itace take maganar kayan ɗaki wai dama wallahi ita kafinta yayi mata ha’inci kullum tana fama da “yan ƙwanƙwashe² gado ba kirki , kujerun ma duk sun rubza kaza². Shin aisai ta kwashe ita da zata tsaya tsaron duniya.

      Ranar da akayi addu’ar 7 a ranar na bar gidan saboda wulaƙancin da sukemin. Da zan tafi ne Kaka ta bani wata takkada cewa Maryam gashi mahaifiyarki tace a baki. Meye a ciki ? Nima bansan ko ta miye ba , tadai cemin zata turoki ki ansa , amma itama kanta gaskiya batayi tunanin zaki anshi takardar bata a raye ba. Ansa nayi nabar palon. Dikko da kanshi ya ɗaukeni muka koma gida.

      Nidai babu wanda a cikinsu yayi min magana game da duk wani abu daya shafi Inna. Basa gabana dan ni basu ne damuwata rashinta shine ƙaton ciwon dake damuna. Suke san abun duniya wanda har ya gusar da imani daga zukatansu , ana kukan mutuwa suna lissafin abinda zasu gada. Tun a mota Dikko kemin nasiha har muka je gida. Da kanshi yayi ma Pa-Pi wanka ya kwantar dashi. Duk inda na juya Pa-Pi sai yayi ta kallona sai kuma ya kalli Dikko.

       Har bacci ya fara fizgarshi ya buɗe idonshi yace cinci abinci ? Murmushi nayi kaɗan tare da nuna mishi da kaina alamar eh. Shima murmushi yayi ba tare daya sake magana ba ya rufe idanuwanshi yaci gaba da bacci. Nima saida nayi wanka sannan naɗan taɓa fura. Saman gado na koma na warware takaddar da Inna ta bayar a bani , Dikko kuma yana tacan gefen Pa-Pi yana latse² a wayarshi…… Ga abinda Inna ta rubuta a takadarta.

     _Aminci Allah , yaddar Allah wadatar zuci zaman lafiya da kwanciyar hankali su ƙara tabbata a gareki ɗiyata…._

_Sultana ki gafarceni a rayuwa. Nasan bakyajin daɗin abinda nake miki… ? Ni wallahi duk abubuwan da nakeyi ma Dikko dake banyi da nufi ba. Saidai ina hasko miki rayuwar gaba. Ke ɗaya na haifa a duniya baki da Baba haka kuma baki da “yan uwa da kika fita ciki ɗaya dasu. “Yan uwana kuma bakya gabansu , daga ni saike muka rage a duniyarmu , ina neman yafiyarki dan Allah , ki yafemin kuma insha Allah bazan sake ba…_

             _Amma ki san wani abu a rayuwa. Nifa ba san Dikko ne banayi ba , a , a ni iskancin shi ne gaskiya bana so. Idonshi ya waye da yawa. Ni gaskiya a tsarin rayuwata bana sha’awa ko muradin namiji mai buɗewar ido da gogewar rayuwar irin na Dikko , amma ya za’ayi tunda haka Allah ya rubuto ? Nidai ina neman yafiyarki karki ɗaukeni a matsayin uwar data fi san kanta akan “yarta. Ban hanaki zaman aure ba haka kuma ban tilasta ki kashe ba. Saboda aure dai sunna ne mai ƙarfi daga cikin sunnonin Manza Allah S. A. W , kamar yadda ayoyi da dama suka nuna mana:•_

       _Allah {{ S W T }} yana faɗa a suratul rum cikin alqur’ani mai girma. “Kuma daga ayarSa ne ya halitta daga garemu mataye domin mu samu natsuwa daga garesu. Kuma ya sanya tsakaninmu ƙauna da tausayi , haƙiƙa wannan aya ce ga ma’abota hankali. “Wannan aya ta tattara duk wani ma’ana na aure a cikinta. Saura namu farfasawa mu auna mugani , shin ma’anar aure da abinda yake cikinsa kuwa kamar yadda Allah ya nuna mana hakan mukeyi. Da farko Allah ya ambaci ma’aurata da ababen samun natsuwa duk anan ya kawo jinsin mata ne. To amma ai mun sani idan har macen bata samu natsuwa ba ? Shi kanshi namijin natsuwarshi ragaggiya ne. Tambaya anan ta ina ma’aurata zasu sami kwanciyar hankali…….?_

   Hah. Ci.. Nayi tare da yin murmushi mai ciwo na goge hawayen dake bin idona. Ina ci gaba da kuka. Naci gaba da karatun takardar Inna…..

_Na farko:• a samun natsuwar aure shine hadafin yinsa. Bai taɓa yiwuwa aure ya kasance an ginashi kan wani hadafi sannan ya zamo ɗorarre. Wannan shi yasa Annabi {{ S  A W }} bayan ya zayyano kaso na matan da ake aure. Ƙarshe yace “na hore ku da ma’abociyar addini. To haƙiƙa abun nufi anan shine ba wni hadafin da zai haifar maka da cikakkiyar kwanciyar hankalin aure sai hadafin tarayya domin Allah…_

      _A cikin aure mai kawo natsuwa kenan. Haƙiƙa a yau munyi sake tare da watsi da haƙƙin junanmu ta yanda takei har wasu abubuwan ma an shafesu daga rayuwar auren sai wajen mutane jefi² mun barwa turawa wanda kuma mu addininmu ne ya koyar damu su. Ina horonki da ki zama mai biyayya , ki zama mai kunya da juyawa abin duniya baya. Kiyi kara ki zama mai haƙuri. Rayuwar gaba ɗayanta haƙuri ce , ki guji yaɗa sirrin mijinki wa kowa da koma waye. Kar kiyi abinda bakiyi shawara da mijinki ba , ki kiyaye fushin shi ki guji ɓata masa rai da gudun duk abinda baya so idan har bai tsaɓawa Allah ba. Haƙuri׳ ki zama mai haƙuri da biyayyar aure kinji uwar masu gida. ?_

       _Ki kiyaye munanan kalamai. Karki kuskura ki jiyar da kunnuwan mijinki ɓatattar magana daga gareki. Magana mara daɗi ko muni kiyi ƙoƙarin kare kunnuwan mijinki dasu. Kar kiyi masa:• ƙarya. Ki kula dashi , ki zama mai tsafta , kar kici amanar shi , banda zargi ki guji abokai , karki raina masa iyaye. Ki kiyaye kuma kisan yadda zakiyu ma’amula da “yan uwansa._

    _Kinga wa’anan abubuwan da zan lissafo su ? To ki kiyayesu domin sune ke taka rawa wurin rusa aure matsawar ba’a kiyayesu ba._

       _Rashin ilimin zamantakewar aure , al’adu , rashin binken halin miji , rashin binciken halin mace , matsalar iyayen miji , rashin tsafta , matsalar dangin miji , rashin iya magana , rashin iya ciyarwa , rashin iya kwanciyar aure , rashin adalci , auren kisan wuta , cin amanar aure , ƙawaye , zafin kishi , sata , gulma , wayar miji {{ phone }} , rashin lafiyar miji wajen gamsar da iyali da itama rashin lafiyar macen wajen gamsar miji , sharrin boka. Ke kina tunanin ni bana sanki ? Taya ma zaki yadda ki fara wannan tunanin ? Tunda kike a duniya kin taɓa ganin uwar data haifa “yarta tace bata santa ne….? Ni ina so ne ki goge da rayuwa ke ɗaya , ki kuma iya haɗiyar baƙin ciki da magance damuwa dan ki zamar da kanki garkuwar rayuwarki. Domin idan yau ina nan gobe bana nan , yadda kike ke ɗayan nan babu abokin shawara ko na bar duniya barakiji wahalar rayuwa da kowa ba. Ina so ne kawai in auno iya girman soyayyarki a zuciyar mijinki. Na gani kuma ni nasan yana sanki dan nayi masa wani abu a abuja. Wallahi nayi tunanin yadda ake faɗar rashin mutunci zaizo ne kawai ya sakeki. Sai baiyi ba kuma nima baimin rashin kunya ko kallon banza ba kamar yadda nayi tunani… Wallahi inajin kunyarki ne , abun nan da nayi muku banyi da nufi ba , yayi ta damu nane banji daɗi ba , shi yasa na fara rubutun neman yafiya kafin mu haɗu dan mashala.Tou dake dashi duk ina san ganinku domin na nemi gafararku , sai kuma kema zamuyi zama na musamman…… sai mun haɗu kafin inyi tafiya_

         _Fatima Salis Abbakar {{ Inna }}_

      Wata irin ƙara nayi tare da cewa da yaushe ne zamu haɗu ? A ina me zaki ce man ne iye ? Cike da tashin hali ya kallo inda nake yace haba An mata wai meye kike haka ne ? Cikin muryar kuka na raunana murya tare da cewa ƙarshena yazo. Wannan kalma dana furta shine yasa Dikko kakkafawa , wani irin birkitaccen ihu na ƙarayi tare da matsawa inda yake , sautin ihun yasashi ɗaukewa gaba ɗayanshi. Da gudu na fita na gayyato Ashiru , cikin tashin hankali muka dawo tare dashi , shi ɗakin Dikko ya wuce sannan yazo ɗakina , haka yaita mishi shaƙe² harya dawo. Ɗan gajeren tsoki yayi tare da cewa insha Allahu saina mutu tunda dai baki bari in zauna lafiya. Fita Ashiru yayi ni kuma na matsa kusa dashi ina kuka , a gajiye ya jawoni jikinshi idonshi cike da hawaye yace wallahi bana san kina ihu , ki ƙyaleni in huta dan Allah. Kwanciya nayi a jikinshi nace na bari. Gefenshi ya nuna min in sauka daga jikinshi in kwanta , sauka nayi na kwanta ina kallonshi dakel ya lumshe idanuwanshi cikin yanayin jigatuwa kiyi bacci , rufe idanuwana nayi hannuna a saman gemunshi.

       Bayan wani lokaci mai nisa ya sauke ajiyar zuciya tare da sauke hannun Sultana daga jikinshi. Wayoyinshi ya ɗauka ya fita a ɗakin. A gefen gado ya ajiye wayoyinshi bayan yaje ɗakinshi sannan ya wuce toilet kai tsaye. Wanka yayo ya fito ɗaure da rigar wanka yana tunane² , shi kaɗai yasan yadda yakejin rayuwarshi da kuma yadda yakeyinta a daddafe. Taƙaitaccen tsoki yayi tare da zuwa wurin wayoyinshi dan ganin mai kiranshi , Sharifa ce. Ɗauka yayi ba tare daya bari tayi magana ba yace yana zuwa….

        Ajiye wayar yayi ya matsa wurin madubi. Kamar mace yaita ƙwasƙwarima , yana gamawa yabi kayan da zai saka ya bulbulesu da tulare shi zaije zance. Kallon kanshi yayi sosai a madubi shi kanshi yasan haɗaɗɗe ne shi ɗin. Murmushi yayi kaɗan tare da ɗan shafa gemunshi da bayan hannunshi na haggu sannan yayi kallonshi na gefen ido mai tabbatar da shi ɗin cikakken ɗan duniya ne. 

       Taf yauma Sharifa ɗif take ta ibi wuta sosai. Har bata iya tafiya sai layi takeyi , ga wasu irin kaya data saka kuma ko breziya bata da , kaf halittar surar ƙirjinta babu wanda baka gani kawai kamar buɗe yake. Full light yayi a dai² lokacin da yayi parking. Dogon kallo yayi mata daga cikin mota inda sukayi zasu haɗu dan yau ba g r a aka haɗe ba. Wasa yayi da fitilar mota ta nufoshi tana rangwaɗa , tana isowa ta wani kama murfin mota ta inda yake ta buɗe , rufe ta da faɗa yayi wai ita wata irin jaka ce ? Haka ta ratso duniya ta taho kowa yana kallonta ? Irin barinkinta zata yi mishi wai Dikko zata runguma , ƙara ƙufulewa yayi dan duk duniya ya tsani ana taɓashi , turata yayi baya da ƙafarshi cike da ɓacin rai yace Dikkon zaki kaiwa hannu eye ? Cikin hayaniya yace kai…… Lallai kin isa yayi maganar yana buɗo duk girman idanuwanshi. Ƙara nufoshi tayi da sauri ta ƙara ƙaddabeshi , ta ɗauka shiru zaiyi ya fara aiko numfashi kamar yadda Mai gilashi ta faɗa , sai taji karatu yasha ban². Da tsiya² ya fitar da ita jikinshi dakel. Kafin ya fito mota ta ƙara komawa ta cakumeshi , kai……….. Da Allah ki daina riƙemin jiki , riƙo fuskarshi tayi tana matsar da nata kusa da nashi. Tureta ya ƙarayi da ƙarfi tayi baya. Da sauri yasa hannunshi aljihu ya ciro cingom kasancewar warin sigari da sauran wasu kayan mayen da yaji warinsu daga bakinta zuciyarshi ta tashi.

      Tsalle tayi ta anshe cingom in tasa a bakinta wai yaci daga bakinta , kakarin amai Dikko ya farayi yana matsawa gefe tare da riƙe bakinshi. Caɓoshi tayi ta baya , aiko kamar jira yakeyi ya kakkaɓota ya fara kwallo da ita , saida ya bata kashin bala’e ya shige motarshi yai tafiyarshi ya barta kwance a hanya tana kuka.

       Tsoki yayi tare da ɗaukar wayarshi dake wata ƙara zutt². Yusra ce , reject ya latsa yana gunguni. Cike da ɓacin rai ya koma gida duk saima yaci uwar matan nan dan ubansu , kawai ma dan ana magana dasu zasu ɗaukeshi wani daƙiƙi ? Bari har itama mai turo kanta tsirara zaici uwar ubanta ta sake zuba mishi banzayen hotunanta a waya saiya kasheta….. Ya faɗa yana kaiwa gado harbi da ƙafarshi. Dama su mata ma basu da wayau jira suke ayi musu magana su fara rainawa mutane wayau. Kamar shi ? Sai kace wani sa’ar wasansu ? Shi waccan jakar yarinyar ma zata wani daƙune ? Jinjina kanshi yayi da damuwa yace sai kace wani jaririn da yazo inda aka daɗe ana addu’ar samun shi , kai wallahi ya raina kanshi da har shi wata daƙiƙiya zata runguma. Tuno yadda Sharifa ta kasance a jikinshi da yadda harma ta samu damar tallabar mishi fuska , duk yana ina ? Aikin me yakeyi ina zamarshi ? Aiko wallahi da bai daketa ba har abadan duniya da baida kwanciyar hankali , tsoki yayi tare da cewa duk dai haka ta moremin wallahi…… Balgazar mace. Haka yaita masifa shi ɗaya a ɗaki dama tusa hali bare anci wake. Fushin mutum ɗaya ke sa idan yana fushi yake haɗawa kowa da kowa , wanda yasan anayi da wanda baiji bai gani ba , ai kuma kunsan laifin wani yake hucewa akan kowa. Yau duk wata macen dake cikin wayarshi Sharifa taja musu anyi blocking insu , anyi adding nasu zuwa blacklist. Wato shi harkarshi ba baƙin ciki bajin haushi sabgar Katsinawa.

       Dikko shine ya shiga yai ruwa yai tsaki aka ɗaura auren Jiddah da Yazeed. Rabiya ta labarta mishi komai tsakaninta da Yazeed iyakar abinda ta gani , hankalin Dikko kuwa ya ɗagu domin shi yasan waye Yazeed. Sadaki da lefe har kayan ɗaki shine yayi dan Yazeed yace bashi da kuɗi , Jiddah ta faɗawa Dikko ita ta bada kuɗin aure. Shine Yazeed yace ɓarayi suka sace kuɗin. Andai ɗaura aure amarya ta tare a gidan angonta…… Ita kuma tana lissafin kwanakin fitowarta da ko nawa ga wata zata koma gidan Dikko.

        Hafsa. Duk maganin da akayi ma Hafsa a asibiti hannu yaƙi ɗauka bare asa ran samun sauƙi har zuwa matakin warkewa. Bayan dogon bincike likita ya tabbatar Hafsa tana da ciwon shiga. Cire hannun shine maslaha inji malamin asibiti dan idan ba’a cire shi ba matsalar zatafi haka injisu. An cire mata hannu dai² gaɓa.

     Amisty kuwa kafin ta gama warwarewa Momyn Hafsa tasa aka cafketa. Bayan tasha shegen duka aka tambayeta kuɗi tace babu , a yadda su “yan sanda suka fahimta Amisty tana da damuwa a ƙwaƙwalwarta. Haka suka gogawa Momy bayani dole tasa suka saketa dan Amisty ta samu ɗimuwar tunani. Amma duk wannan bai ishi Momy ishara ba saida ta siyar da gidan iyayenta da gidan Amisty na Qerau. Amisty dai ga hauka ga kuma yawon haya…. Bariki kuma ta kama gabanta , sheɗan ya fita a kanta ya sake sheƙa. Duniyar yanzu ba Amisty take buƙata ba zamanin wasu ne. Haka takeyin juyin ɗan mangwaro ita duniya dawowa take daga rakiyarka da zaran ta raka ka sai ta dawo ta sake raka wani halakakken wanda sheɗan yayi ma tusa a zuciya.

       Halima dai ba kowa bace wannan amarya sai ƙanwar Hadiza. Wata garɗamemiyar budurwa ce takai shekaru 27. An tura anyi ciniki amma bata samu shigewa ba , anyi addu’a an bada sadakar ƙuli da alawa amma abu ya gagara dan haka ta shiga ta fita har gidan uwayen mijin Halima ta basu labari irin uƙubar da take ba ɗansu. Nan fa dangin miji suka fara cacai² , akai ta faɗo baƙin halinta , raina dangin miji uwar miji raina miji da baƙar rowarta. Itama dai Hadiza ta kawo nata sharrin ta raɓa da “yar ta² barikin dai ta samu aka siyi kanwarta. Shima Abdul haka aka ɗaurashi kunsan maza basa wuce tayin mace kamar almajiri ne da sauran abinci… Cikin ikon Allah yaga yarinya kuma tayi mishi. Gata “yar kyakkyawa kamar Rabi’atu Aminu Maman Dee. Mai kunya da laushin magana kamar Asmeenat Zeeyan. Mai kyawun kallo da iya murmushi kamar Aunty Musa Qerau. Ga iya wanka mai ɗaukar hankali kamar Hauwa Musa Qerau. Ta iya adon lalle mai burge kamar Zainab Abbakar Matawalle haka ta iya gyaran kai kamar Fati M Ga magana da salon ɗaukar hankali bakinta kamar Ruƙayya Sharif Maulaya hassan. Kai tafa haɗu haɗuwar haɗewa , idan zatayi kallo tanayinshi ne da salon bugun zuciya kamar Rabi Musa Qerau. Bari dai in daina zugata haka nan karta kamo Halimatu Musa {{ Uwa }} haɗuwa.

    Abdul da yaga yarinya tayi mishi sosai dan haka suka antaya a duniyar munafukar soyayya. Ita kuma Hadiza kullum tana liƙe da gidan Halima tana ƙara kakkaɓowa “yar uwarta sirrin gida. Har daren ɗaurin aure duk suna tare da Halima sunajin hukuncin da zatayi wa amarya. Da taji saita dokawa “yar uwarta waya suyi shawara su san hanyar da zasu hudowa lamarin. Ina wanda ya raba faɗa bai kallo ba , sun haɗu sun haɗa ƙarfi da hikima duka ɗaya zasuyi su zare Halima a gidan miji idan tayi wasa saboda sunyi mata ƙofar raggo , ita bata sansu ba , su kuma suna tare da ita suna shirya mata gadar zare.

       A kusa da gidan Halima Abdul ya kama haya ya ajiye amaryarshi Amina. Tunda bai shirya aure ba hawoshi yayi kai tsaye. Anan fa akayi uwar watsi , Halima ta fara bori da wallahi² data tabbatar amarya ƙanwar aminyartar ce. Nanfa fitina ya ɓalle suka kashe santa aikata ruwan bala’e babu ƙaƙƙautawa , Hadiza ta biya kuɗi ta ibo hayar “yan daba tace duk matar data sake cewa tuf ko ta leƙo daga gidanta idan dai ba Allah sa alkairi ta fito ba aradu su yagewa koma waye baki. Dan su sunaso suyi hidimar biki cikin natsuwa , a gefe kuma ga masu DJ sunata wulakanci da waƙoƙi na habaici umarni daga Hadiza , c b n gidan kuɗi. Can naga sabbin kuɗi suna wali bisa iska. Shagali wanda ko a bikin Halima basuyi irinshi ba. Hadiza kuwa a yanzu zasuci na ƙurya da bakin gado. Ballagazar mace ga ƙarsheki.

    Tunda Mardiyya ta haura katangar maƙabarta ta ibi santa. Mota tahau ? Da ƙafa taje ? Oho , candai Yola ta yadda zango , hauka tuburan marar gane matsayin ido da ciki. A gidan mahaukata aka ajeta shine suka shiga neman “yan uwanta , bayan an samosu aka danƙata wa iyayenta , sai suyi ta magani har a dace , wa gari ya waya ? Ruwa ya ƙarewa ɗan kada bai gama wanka ba.

     Amarya Jiddah kuwa an wani saki baki aci kazar amarci. Ai a ranar ango bai kwana gida ba. Tou dama me zai tsaya yi ne ? Abinda za’a tsaya danshi ayi murna da ɗoki ai ansanshi tun a gida. Saboda shi dama za’aci kazar tou yabi ya wuce , anyi karatu an tusa feji , allonta kawai take wankewa gwargwadon yadda ta biya karatun. Sati ɗaya da “yan kwanaki ta fara zance tafiya , Yazeedu yace ina ? Ai yadda baya tare da D ‘ K a yanzu gara ma yayi ƙoƙarin riƙe auren “yar uwarshi yasan ya mishi sauƙin gani. Haya² ta taso da rashin kunya ya nannagawa banza duka na fitar misali. Wannan shine horonta duk idan ta sake zance saki….

     Duk wannan sa’a da Sharifa ta gwada na shawarar da mai gilashi ta bada taga ta faɗi ? Bata daddara ba. Dan haka ta faɗawa Mai gilashi Dikko ya rufeta a waya. Mai gilashi tace mafita na ƙarshe kizo makarantarmu ajinmu ɗaya da matarshi kashin bala’e zaki bata , daga nan idan kika daki matar zai nemeki danjin dalili , sai ki faɗamin ni kuma zan baki shawara na ƙarshe. Idan kika daketa zataje ta faɗawa mijinta , tana faɗa mishi shi kuma zai nemeki danjin ba’asi. Yana kiranki ke kuma ba ɗauka zakiyi ba sai ki kira ita Aunty Bilki ki farfaɗa mata maganar da zan faɗa miki idan kinyi dukan. Daga nan zatace kizo gidan gwamnati. Idan kikaje government house sai ki kira Dikko ki faɗa masa cewa kinga kiranshi bakya kusa ne sai yanzu. Zai ce me matata tayi miki kika daketa ne ? Sai kice ai ina nan gidanku ma. Fuuuu zai tako mota yazo , ai kinsan dai dama bawai wani can² yake santa ba suma nashi familyn basa santa. Ai nanfa za’a haɗu a bata rashin gaskiya duk idan kinyi dukan zan faɗa miki abinda zaki ce ya haɗaki da ita Sultanar.

      Sharifa tace amma kina ganin wannan ba matsala ? Mai gilashi tace haba Sharifa idan da matsala harna faɗa miki kiyi ? Matsalata ai taki ce. Dole mu haɗu muyi maganin matsala kodan ci gabanmu. Sharifa tace idan aka faɗi fa ? Mai gilashi tace shikenan sai ki sake ƙawar shawara. Sharifa tace tou shikenan. Batayi tunanin matsalar da hakan zai haifar ba……

          Hmmm su kuma zugar gidanmu duk abun nan wai sai yau suka zomin gaisuwa. Ƙwansu da ƙwarƙwata babba da yaro babu wanda aka rago har iyaye , jimillarsu dai su sattin da wani abu. Kacaniya kenan , gaskiya nayi farin cikin ganinsu sosai har farin ciki na yaƙi ɓoyuwa. Haka suka shigo wurjanjan kamar an ɓalle garken shanu. Kowa da irin siffarshi. Kai gaskiya Baba ɗan bala’e ne , wannan kwanyaman “ya “ya inama amfaninsu ba ɗaya na zaɓe. Haka suka shigo palo sukaita hayaniya , har bakajin maganar wani. Abinci nasa aka kawo musu. Ɗiff kowa ya ɗauke wuta suka fara caccaka. Gayam². Gurum² taunar nama. Abinci kuma nakai karo suka ci gaba da surutu……

           Da hada “yan gidan Baba ƙarami zamu zo sukace basu zuwa. Cacai² gardama ta buɗe , bafa haka sukace ba ku faɗi gaskiya ni nafi san abinda mutum ya faɗa ana faɗinshi. Daga maida magana sai faɗa , har ana neman bugawa. Haƙuri na basu dakel dai suka haƙura , duk lemunan da aka kawo musu kowa cikin jakarta tasa abunta wacce bata da jaka ta matse abunta a hannu. Tashi sukayi wai zasuje su zagaya gida dan kar suje wata rana anayin labari su kasa ƙarda komai. Kamar wata geliya haka nabisu babu inda basu shiga ba a gidan sai ɗakin mai gidan ne kaɗai basu shiga ba. A store kuwa buhun garin kwakin nan suka jawo , kalluba suka cire ba tare da izinina ba suka hau rabo , wai wannan ai kiran tsiya ne wai meya kawo fir’auna aljanna ga gidan wuta. Haka dai sukai ta zambaɗa iskanci suna maganganun irin nasu na “yan cikin lungu. Duk abinda suka gani yayi musu a store sukayi gaba dashi. A ɗakina kuwa cewa sukayi in basu zazzagar kayan sawa. Fa’iza kuwa cewa tayi saidai wasu a basu kaya wasu takalmi wasu jikkuna , kuma wai waye ma nake bawa kwance gasu ? Duk zasu sakamin numbobinsu idan zamu koma sabon gida a basu kayan tsohon gida , weldrop na buɗe na fiddo musu kaya sukai ta zaɓe. Ciki kuwa hada rigunan da Dikko ya kawomin tsaraba suka ɗauka. Nan dai suka yini sai dare suka tafi nayi musu hasafin kuɗi masu nauhi suka kama gabansu….

      Kwanan “yan gidan biyu da zuwa Dikko yana kallon hutana na a waya ya karkatomin waya wai insa mishi wannan rigar yau. So ɗaya na kalleta nace na bada ta. Sake zuƙo hoton yayi yace wannan kalli. Ba tare dana kalleshi ba nace wannan ɗin. Haba yarinya wasa kikeyi , wallahi da gaske na bayar da ita , cike da ɓacin rai yace waye yace kika bayarmin kayata………..?

         Kar kuji Dikko yana da kuɗi kuce ya tsaya akan wani banzar riga yana surutunshi. Duk iya kuɗin namiji ke mace yafa kamata da Allah ki riƙa abu da lissafi. Tunatarwa ne. Duk irin kuɗin mijinki baifa kamata haka ba gaskiya , ta yuwu kila a jikin wata ya gani tayi mishi kyau ya siyo shima kiyi mishi gayu. Bawai nace ba’ayin kyauta ko karki bayar a , a abunda dai ina nufi a ɗan riƙayinshi haka dai da lissafi.

       Domin shidai Dikko a saudiya yaga riga jikin wata “yar budurwar balarabiya. Shine ya hasko idan tashi matar ta shiga a irin rigar itama zata bada irin abinda waccan ta bayar , ina fatan dai kun ɗan fahimceni. Shine ya shiga shima ya samota kalarta da komai da komai dan ayi mishi ado a gidanshi shima. A ita ga matar mai kuɗin banza idan na bayar gobe ya siyo wani. Ita ya siyo domin ke…, bashi da tabbas idan ya koma siye ya samo irinta , ta yuwu a canja kala ko kuma a samu banbancin company. Shin ba’a shiga haƙƙi ba….? Saboda haka idan dai namiji ya siyo abu ya kawo miki lallai yana da dalilinshi……

          Ai na baka ya rabaka da abunka. Ni kike faɗama wannan maganar dan kin ɗaukeni abokin wasar ki ? Yayi maganar cikin fushi yana tashi zaune. Ni zan siyo miki abu ki bayar dashi ? Nayi miki magana zaki faɗamin na baki ya rabani da abuna….? Yayi maganar yana saukowa daga saman gado , miƙewa nayi da sauri. Cikin firgitacciyar murya yace idan kika fita sai nai miki shigar bulet………


       


      08/02/2020

*JAMILA MUSA…*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button