NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 7&8

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO…*
*HUSSAIN 80k*
7⃣&8⃣


Kujimin kaka da baqin ciki,baki Nima mijina ya riqa saimin kayan dadi iron na abu, nijlah ta fada cike da yarinta!.
Cikin kuka yakumbo tace!uhmn nijlah Kenan angayamiki kayan Dadi shine aure,,me Kika Sani game da Zaman takewar aure” 
Allah kaka Na Sani,,badai ruwa Ake zubawa a buta na alwala ba,Sai kuma ka zauna Idan anyi tuwo a cikin gida ka dauka Langa a zuba masa tuwo..

Nijlah Kenan babu abinda Kika sani”Allah kaka Na Sani Niki Dena kirana yarinya Kuma Naga Abu tayi zamanta a gidan Musa Ai Dai Nima Zan zauna” Allah ya kyauta cewan kaka tana Jin quna cikin zuciyanta..

Tana nan zaune Har Malam ya dawo dauke da Leda a hannunsa,,
Wai haryanzu kina zaune kina tunani Akan abinda bashida mafita Sai wacce na fada” uhmn uhmn fa Malam wallahi nijlah bazata Iya Zaman aure ba,,ka Duba qanqantar shekarunta?

Yakumbo Kenan tin yaushe muke neman mafita bamu samu ba,,se yanzu Dana samu Zaki kawo matsala,,kiyi tinani Dan Allah.

Shiru yakumbo tayi tana nazari kafin tayi iya Bude baki tace” yanzu Malam Idan muka auran da ita akazo haihuwa ta kamu da jajjan fitsari ya zamuyi,, murmushi Malam yayi Dan ya gano abinda yakumbo Ke tsoro..

Indai wannan ne ki kwantar da Hankalinki,na tabbata nijlah bazata samu wannan matsalan ba,,to Malam kasan Wanda Ze aureta??

Kinga yakumbo Idan bakisan ayi aurennan kawai ki fada ni Kuma Zan zuba Miki Ido Naga yadda Zaki Iya Kula da ci da Shan nijlah,, yakumbo kinfi kowa sanin halin nijlah,,yinwa kawai Idan Taji ta riqa surfafa Miki kuka Ke Akan kudin dandali Sai nijlah ta kusan kwana tana ihu,,Ina Sai yanzu da Allah ya kawo mashkur wannan kauye nijlah ta Dan samu gata,,Idan ba haka bane Sai gayamin..

Matsowa nijlah tayi jikin Malam tana murna tace,,Malam kawai kayimin aure ka kyale kaka tayi ta abunta,,Nima Na riqa Cin tsire da kosai irin Na birni Ko,,dungurinta Malam yayi Yana cewa eh Zan Miki aure Amma sekin Dena yiwa mutane kukan dare” 
Dasauri nijlah tace Allah nadena,,kaka aidai Na Dade banayi Ko?

Shiru kaka tayi tana sauraran shirme nijlah kafin tayi qoqarin cewa,,Hakane Malam Nima Na yadda Na Kuma amince da auren nijlah sedai inaso ka zaba Mata mijin daze Iya Kula da ita!

Haba yakumbo muda zamu Bada sadakanta mune zamu zaba Wanda zamu aura Mata” to ai abin ne’ kinga kedai kawai kiyiwa yarinya addu’a.

Kinga dauki wannan kanzon ki jiqamana Musa a cikinmu” Ni Allah gari kwaki nakeso ba kanzo ba nijlah ta fada cike da shagwaba,,rarrashinta Malam yayi yayinda yakumbo ta tafara jiqa qanzon,,bako Mai haka ta zuba kuli suka ci.

Suna gamawa Malam ya tafi gidan kakannin nijlah Na wurin uwa,,anan ya samesu da magana nan,Basu Bada matsala ba Dan kowa ya amince,nan ya dawo gida cike da farin ciki Na samun nasara Dan a ganinsa auran da nijlah shine Abu mafi sauqi daze Bata farin cikin dasuka kasa Sama Mata Shi a matsayinta Na marainiya Kuma jika a gurin su..


*******

Zaune take ta hannu biyu Akan kumatu da alama tayi zurfi cikin tinanin,,a hankali ta cire hannu ta dauko wayanta dake Kan center table ta qara Danna Kiran layinsa.
Abu daya Ake gayamata Dan haka tayi cilli da wayan tana Tashi tsaye,,Saida Nace karkayi tafiyan nan Amma ka dage Saida kayi gashinan wayama ya gagaremu sedai kayi kasamu lokaci ka Kira,,Anya kuwa mashkur be samu matsala ba..

Girgiza kai daddy yayi Yana qarasowa kusa da mummy, nan ya zauna kusa da ita Yana kallanta cike da kulawa yace,,

Haba Khadija Se yaushe Zan gayamiki kidena sa damuwa a ranki,girma fa ya kamaki,,Karki sa ciwo yamiki illah Akan abinda bashida Wani illah..

Haba Alhaji Taya kake tinanin hankalina Ze kwanta Akan tafiyan mashkur,kako je kauyen kaga inda yake zaune,, toyaya kikeso ayimasa, mashkur Dai ba yarone qarami ba,da inyaji wahala Baze dawo gida ba,Kuma kina kallo nasama masa admission a UK Amma fur yaran nan yace bayaso ga idda yake muradi Toba seki barshi yaje yayi ba..

Cikin kuka mummy tace haba Alhaji kana nufin haka zamu zuba ido mashkur ya zauna cikin matsiyatan mutane dako Nama Sai su shekara Basu Ciba,,to wallahi Bazan taba yadda ba gwara tin farko kasan yadda zakayi da danka..

Girgiza kai daddy yayi Yana Kallan mummy yace” yanzu Ke Khadija Harkin isa ki aibata Fulani kokin manta Nima bafulatani ne,, dasauri mummy tace Amma Dai ba irinsu ba.

Cikin fishi daddy yace,Koma Dai menene jinin fulani kike aure Dan haka ki kyale yaro ya qarasa karatunsa Koma menene saikiyi Daga Baya,,

Turo baki mummy tayi ta Tashi dasauri ta Koma daki tana Kiran babban danta..

Hello mummyna barka da yamma,,yauwa Ibrahim,,mummy lafiya Naji muryanki haka,, mummy Ko baki da lafiya ne,,kuka mummy tasa tana cewa..

Ibrahim ka Kira wannan yaran ka gayamasa ya dawo gida, mashkur Yana neman doramin hawan jini.

Eyyah Mummy meya Samu mashkur din,, mummy Ko jiya munyi waya dashi yace Yana zaune lafiya a garin dayake” toka gayamasa ya dawo gida banasan zamansa cikin wadannan mutanan indai yanasan zamana dashi lafiya.

Shikenan mummy kiyi hakuri zanyi Magana dashi,,eh ka gayamasa yayi saurin neman transfer yadawo cikin gari,,to mummy kiyi hakuri insha Allahu Ze dawo,,kashe wayan mummy tayi tare da sakin tsaki..

*******

Tinda Malam ya Tashi yasa a ransa Yau Ze Bada auren nijlah gako wanne irin mutum ne indai yanada  kamala Kuma Ze Iya riqe nijlah..

Yakumbo ya Samu da maganan yayi sa’a Bata bashi matsala ba ta Kuma amince tare da Tarin adduointa ga auren jikar Tata.Comments &share

*Momn sultan ce*✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button