NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 15&16

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO…*
*N@DI@*
1⃣5⃣&1⃣6⃣


Wayyo Allah,,yau Naga ta kaina yanzu mezan Gaya iyayen yarinyarnan,,zagaye titi Bello ya riqayi Yana kallan Motan har Saida suka bacewa ganinsa kafin ya daga qafa yaname danasanin amincewa da rakiyan nijlah..
Yanzu mezan Gaya Kaka,,wanne dalili nake dashi Wanda ze tabbatar musu da maganata gaskiya ce,,sosai ya zurfafa cikin tunani Yana tafiya Yana hada hanya a haka harya Kai kauyen kankan,Yana zuwa dakin Nasir ya Shiga nan ya Samu Nasir ya zuba tagumi Yana tinanin rayuwar kadaicin dazeyi a wannan kauye Shi Daya ba abokinsa..
Ko sallama Bello beba yafara da masifa,,Kai Ashe wannan abokin naka bashida kunya,,miskilancin banza yakewa mutane”” dagowa Nasir  yayi Yana kallan Bello da jajayen idanunsa yace” lafiya Bello,,Naganka anan?
To a ina zaka ganni Saida muka Shiga mota abokinka ya hankadoni waje,,yace wai ba inda Zan bishi daga Shi sai matarsa zasu tafi,,yanzu me kake tsammanin yakumbo ya dauka,,ni wallahi harna Fara tinanin mashkur Dan yankan Kaine..
Tinda Bello yafara magana Nasir yake dariya harya Kai Aya Nasir be dena dariya ba yanayi Yana kallan Bello,,haushine yakama Bello nan ya Fara hararan Nasir Yana cewa,,Ara ta kanni indai Yanke Kan nijlah zakuyi kaima bamu barinka Ka fita lafiya a wannan kauye..
Nasir be kulaba Saida yagama dariya kafin ya kama hannun Bello Yana cewa,, cool down abokina,,kaga niban iya yaran arna ba,,idan zaka gayamin da Hausa ko fulatanci Ka gayamin..
To shikenan zauna muyi magana,,wacce magana zamuyi alhalin an tafi da nijlah bamusan inda suke ba,,yanzu idan kaima kabi dare Ka gudu ina muka kama..
Haba Bello Ka kwantar da hankalinka nagayama babu wata matsala,,kuma ninasan abinda yasa mashkur yayi haka,,yanzu idan Kaine Ka tafi kiwan shanu sai Ka dawo gida da Mata,,wanne dalili zaka Gaya iyayenka” shiru Bello yayi Yana nazari kafin yace,,Zan gayamusu tsintota nayi a hanya,,to kagani kaima karya zaka Gaya iyayenka,,to tayaya kake tinanin mashkur ze tafi dakai ga kuma nijlah Wanda ya aure batare da Sanin iyayensa ko danginsaba..
Shiyasa akace yabarta anan yafara zuwa ya sanar da iyayensa kafin yakai musu ita,,yanzu ya zeyi Kenan,,Nima bansani ba cewan Nasir Yana qara cigaba da magana..
Inaga wani tinani yayi shiyasa yace Ka dawo shize tafi da nijlah,,Dan haka nakeso kace Kaine kafasa zuwa birni kace su tafi kawai sabida gani kuna ganina,,duk ranar dazan tafi saimu rankaya daku kuje can birni Kuga inda nijlah take,,koya kake gani za’ayi??
Amma Nasir tayaya kake tinanin yakumbo da Malam zasu yadda da wannan karyan,,zasu yadda sai kaqara da cewa dare ne yayi Baku samu mota ba,,dakyar aka samu guda shima gurin mutum dayane,,shine mashkur ya zauna ya Dora nijlah akan cinyensa suka tafi..
Eh to gwara wannan shawaran Amma bazan fita a dakin nan ba sai dare,,hakan yayi,,nan dai suka cigaba da tattaunawa Nasir Yana qara kwamtarwa sa Bello hankali…….

            *************

Karfe 1 na Rana a garin Kano yama aunty lateefah,tinda ta Shiga gidan tafara Kiran mummy,,duk ta inda tabi ma’aikatane ke gaisheta sedai ba Wanda ta amsa tana tafiya tana Kiran mummy harta isa dakinta..
Kwance ta Sami mummy ta zuba tagumi tana Kiran layin mashkur,,mummy na ganin lateefah tayi cilli da wayan tana cewa,, shikenan mashkur,, shikenan tinda bayana kakesan gani,,da gudu lateefah ta qarasa kusa da mummy tana tambayanta?
Mummy meya faru da mashkur menene kuma,,ko haryanzu be dawo gida ba?
Ina ze dawo lateefah yafiso saina mutu ze dawo gidannan,, wannan wanne irin karatu yarannan take da Har yazabi bacin raina..
Hannu ladeefah tasa tana gogewa mummy hawaye,,kiyi hakuri Mummy kina kallo nabar aikina Na dawo Nigeria sabida abinda yarannan ya aikata,,duk Da yace Ke Kika amince Amma banji dadin yadda Kika Tashi Hankalinki ba,mummy mashkur ba yaro bane Duk inda yake Ze Iya Kula da kansa,,Kuma shikenan seya tafi cikin matsiyata masu yawo a Jeje wadanda Basu da Wani abinci Sai nono,, wallahi Bazan lamuntaba koya dawo Ko hankalin kowa ya Tashi a gidannan..
Kiyi hakuri Mummy nasan Duk inda mashkur yake Yana hanya”Koda yazo Baze shigomin gida ba Sai an kaishi hospital an Duba lafiyarsa,,nasan zuwa yanzu yaci abubuwa marasa kyau da zasu Iya taba lafiyarsa,,Kuma inaso kufara kaishi toilet Na Baya yayi wankan kafin ya shigomin Daki…
Shikenan mummy za’ayi yadda kikace,,Abu daya nakeso ki kwantar da Hankalinki,,haba lateefa tayaya hankali Ze kwanta Ina zaune cikin Jin Dadi auta Yana cikin wahala kinga lateefa Idan Baze zoba kuje ku daukomin Shi Dan wallahi Na tsani Zama da wadannan mutanan,,shiyasa kikaga Ko nono Bana sha..
Ajiyar zuciya lateefah ta safke tana kallan mummy tana girgiza kai tace,,Dan Allah mummy ki rage wannan damuwan kinsani Idan daddy yaji Baze tabajin Dadi ba,,cike da fada mummy tace.
To yaji man Idan yaji saime dukana zeyi,,Koshi yayi irin wannan rayuwar ne,,Amma mummy Amma me Dan ubanki,,karfa ki batamin Rai.
Kiyi hakuri Mummy Naga Dai daddy Shima bafulatani ne,,kidena nuna kyamarsu a Fili Hakan Ze riqa sosamasa Rai..
Badai kema kina Bayan wadannan mutanan ba mutanan da saisu shekara Goma basuci Nama ba,,mummy kinsan nafiki tsanar Zama a irin wannan guri kawai Dai banaso kina fada agaban daddy..
Sallama Yaya yayi suka amsa nan ya Samu guri kusa da mummy ya zauna Yana gaisheta,,dauke kai mummy tayi taqi amsawa dan a ganinta basuyiwa mashkur Magana ba shiyasa be dawo ba..
Lateefah ce tayiwa Yaya sannu da zuwa nan ya amsa Yana cewa Ina mashkur yake?
Yaya be dawo ba Nima tinda nazo nake zuba idansa gashi Har 4 Na yamma be qaraso ba,,Anya Ko ya taho?
Eh Yana hanya dazu munyi Magana dashi yace nan da 2 hours ze Iya qarasowa..
 lateefah meya Samu mummy Ko Bata da lafiya?
Bansani ba,,kaida Nace kagayamasa ya dawo da wuri shine harka samu damar zuwa shibe qarasoba,,kiyi hakuri Mummy kinsan yanayin haryarsu Sai ya hau Mota biyu kafin su zo,,Nace driver zeyi daukansa yace harya kama hanya” karyane wallahi kunsan Allah Idan be dawo Yau ba Saina Saba muku a cikin gidannan..
Tinda daddy ya shigo yafara Jin hayaniya harya shigo falo ya Samesu zaune sun sa mummy tsakiya Suna Bata hakuri..
Daya Bayan daya ya riqa kallansu Yana mamakin zuwansu,,sannu da zuwa sukayi masa ya amsa tare da neman guri ya zauna Yana Kallan mummy yace..

Yanzu abinda kikeyi ya dace Kenan agaban yaranki kina zauna kina koya musu dabi’a mara kyau ta rashin sanin darajar Dan Adam,,to Wallahi kisani kowa da Kika gani da baiwar da Allah yayi masa dan haka kibi Duniya a sannu” turo baki mummy tayi ta budeshi a hankali tace,,to Ni menayi kawai Dan Nace yarona ya dawo gareni Sai ka kama fada kana fishi Dani” 
Ki rufemin baki,,kosu Fulanin ba Allah ya haliccesu ba,kinsan bakisan Fulani Kika auri jininsu,,Maryam a gidana Kika Zama abinda Kika Zama shine yanzu Har Kika Iya …..” Daddy kayi hakuri Kasan halin mummy tinba yanzu ba,,kasani Ko kauyensu Inna wuro batasan zuwa Har Allah yamata rasuwa,,daddy Mun girma hadda yara bazamu so ganin haka Yana faruwa a tsakaninka da mummy ba,,munsani daddy kaima ka Sani,,baku taba yin fada da mummy Sai a Kan maganar zuwa ruga lokaci gudu kaika Kadena zuwa daganan bamu sake ganin bacin ranku ba Sai yanzu da mashkur Yaja..

Kallan yaya daddy yayi yace meya dawo dakai kasar nan yanzu,,bakinsa Na rawa yace daddy Wani aiki nazo Yi,,Ke Kuma fa daddy yafada Yana nuna lateefah da cikinta ya duru ruwa harta fara karkarwa..
Ba tambayanki nayi ba,,Ina Kika Baro mijinki?
Nina kirata,,Shima Sadiq Nina kirashi tinda kai bazaka Sashi ya dawo gidaba su zasu Sashi yadawo,,to ai shikenan Idan ya dawo saiki jiqashi ki yanshe Ko,,be jira amsar mummy ba ya fita a falon..
Hira suka cigaba dayi ita Dai mummy jinsu kawai take tana Kalle kalle tare da.neman ta hanyar da mashkur Ze shigo,,Har akafara Kiran Sallar magrib Basu qaraso ba haka Dai kowanne su ya daura alwala sukayi sallah,,Suna cigaba da Zaman jiransa…

Tinda nijlah Taji warin Mai zuciyanta yafara Tashi nan ta fara toshe hanci tana kallan mashkur,,a hankali yake Mata Magana Yana Kallan yadda idanunta sukayi zuru zuru,,
Menene Naga kina toshe baki da hanci,,
Banasan warin Mai ka saukeni cikina juyawa yake tafada tana yinqurin Amai,,kafin motan ta tsaya tafara Kwara Amai a jikin mashkur Har Saida ta Bata gaban rigarsa,,be damu da Hakan ba Saima shafa bayanta ya riqayi Yana Mata sannu,,Seda ta gama me motan ya Basu ruwa a jarka suka wanke jikinsu,,nan suka cigaba da tafiya hancinta a toshe ,,karfe 7 Na dare Suka sauka a cikin garin Kano,,me napep ya tare suka Shiga nan yayi masa kwantancen gidansu kasancewar mashkur be taba Hawa nape ba,,dariya me nape yayi Yana cewa Malam haka kai bakone,,mu ba address Ake bamu ba,unguwa kawai Zaka fada Idan mukaje saika nuna gidanka,,ok kawia mashkur yace yacigaba da jera nijlah sannu,,tinda suka Hau napep bacci ya dauketa Har suka kai gidansu mashkur Bata Sani ba.
Bayan ya sallami me napep ya tsaya tinanin ta yadda zefara tashinta Sai kawai ya dauketa ya kwankwasa get..
Waye ne Ze balle mana kofa qara bugawa mashkur yayi Yana cewa nine baba zoka Bude..
DA gudu baba me Gadi ya Bude kofan Yana yiwa mashkur sannu da zuwa..
Ahankali mashkur yace,,baba ga kayana Dan Allah ka temaka ashigomin dasu,,to ranka ya Dade,,nan baba yafara rufe qofan,,qaran qofa yasa nijlah Bude Ido tana Kalle kalle..
Ahankali mashkur ya safketa Yana jera Mata sannu,,Ina kayana nijlah tafada cike da sanyin kuka.
Kingansu can Karki faramin halin naki,,dasauri ta dauko kullin dankwalinta ta Dora akai tana Kalle kallen gidan..
Hannunta ya kama Yana cewa ‘yar kauye Sai Wani Kalle kalle kike,,lah kado kaga wannan abun da Ake nunawa,,lah kado Kalli kaza haka nijlah ta riqa fada Har suka isa qofan falon..
Da sallama mashkur ya Shiga zuciyarsa na harbawa tare da  matsanancin faduwar gaba..
Mummy dake zaune tasa abinci agaba Taji sallamar mashkur,,dasauri ta dago ido Aiko tayi sa’a idanta be safka Kan Na mashkur ba saiya sauka Akan santaleliyar surukarta..
Zabura tayi ta Tashi tana nuna nijlah da yatsa bakinta yakasa magana…
Aunty lateefah ce tayi qoqarin Bude baki tace mashkur Kaine haka,,ita Kuma wannan Daga ina,,Ina Zaka kaita..
Mashkur be Iya Magana ba illah zuba musu shanyenyun idanunsa dayayi Yana cigaba da tafiya,,,har Saida yakai jikin kujera Ze zauna hannunsa riqe Dana nijlah yaji muryar mummy tana Magana..
Karka fara Zama min Kan kujera ka Kuma ficemin da wannan aljanar yarinyar”waima a gidan ubanwa ka samota Sai kuma tasa kuka tana cewa.
Kunga irin jajibe jajiben nasa,,ya kamomin wannan qazantar Har gida…

Mashkur wacece wannan Daga ina ka daukota??

Kafin mashkur yayi Magana yaji tsincin muryar nijlah..

Sunana nijlah kawu Daga garin kankan ya daukoni Kuma ni matarsace Ko kado?????????????????????*Kuyi hakuri wayana ya Samu matsala ba lallai ku qara Jina a ‘yan kwanakinan ba,,sedai kuyi fatan Allah yasa ta gyaru da wuri,,Nima ba haka naso ba,,zanyi missig zafafan comments dinku????????????*
*Comments & share* 
*momn sultan ce*✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button