NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 26

*_NO. 26_*
…………Rayuwa ta cigaba da shuɗawa, yau da gobe kayan ALLAH, tun ana ƙirgen kwanaki har aka koma sati, aka koma wattanin da suka ƙulla shekara, kafin wani dogon zango saigasu
Ummukulsoom da shekaru huɗu a makaranta, karatu yayi nisa sosai, yayinda nasarori da ƙalubale ke ƙaruwa, to dama rayuwa ta gaji haka, dolene wataran ayi kuka wataran takaici wataran al’ajabi wataran kuma dariya, abinda kawai ke saka nutsuwa a zuciyar bawa shine haƙuri da karɓar ƙadda ta nasara ko faɗuwa, godiya ga ALLAH alokacin daya baka koda kaɗanne, rintse ido daga hangen nasama ka kula da wanda bai kaikaba, karɓar da hannu biyu daga nasarar sa’a ko faɗuwa, dan duk wanda yashigo duniya yasa a ransa makarantace ita, lokacin da wancan ke zuwa aji na gaba sannan wani ke dawowa baya maimaita ajin kokuma barin makarantar baki ɗaya.
       Ummukulsoom tayi imani da waɗannan ƙalubalen a rayuwarta shiyyasa ta kwantar da hankalinta wajen maida hankali ga karatunta na boko dana islamiyya da Dad yazo da kansa ya sama musu. dan masu iya magana kance komai iliminka idan baka neman wani to lallai zaka rasa gaba ɗaya, kokuma kazama a jerin masu kafa tasu gidauniyar ta ɓata bisaga bigiren yarda da kai.
     Ƙwarai da gaske Ummu ta canja a shekarunnan, danta sake girma da cika, a wanda ya santama ya ganta a yanzu idan ba faɗa maka akaiba bazaka shaidata ba, ga wata nustuwa da hankali data ƙara, tareda aji irinnan manyan yara masu aiki da tarbiyyar addinin islama.
     Duk da kasan cewarsu acikin mafi rinjayen waɗanda ba musulmiba hakan baisa sun zubar da kimarsu da daraja ta ƴaƴan musulmaiba, basa shigar banza balle ballagazanci da sunan wayewa, akoda yaushe cikin taka tsantsan suke wajen girmama addininsu da al’adarsu, sun riƙe abinda yake nasu da hannu biyu, yayinda suka rintse idanu daga wanda bai dace dasuba ko bai zama mallakinsuba komai daɗinsa ko samun farin ciki daga garesa.
     Wannan rayuwar tasu saita fara tasiri a zuciyar Peace, tana mamakin dama haka musulmai keda ƙyaƙykyawar mu’amula ashe? Gasu mutane masu gaskiya da ƙarfafa kai, aduk lokacinda wata ƴar matsala ta shigo a karatunsu takan damu, amma saita su Ummukulsoom suna faɗin haka ALLAH ya ƙaddara, maybe wani tushen nasarace yasaka ubangiji jarabtarsu danyaga imaninsu, mai makon taga rauni tattare dasu sai taga tarin tawakkali da ƙarfin gwiwa.
       A ɓangaren ibada ko a ina suke lokacin salla yayi saisun sami wajen daya dace sunyita, ɓangaren mu’amularsu da maza akwai tsari, babu sakin fuska babu cuɗanya ta jiki sai dai da kuskure, Dakubo yayantane a gida ɗaya suke kwana suke tashi amma ko zama kusadasu basa bashi fuska balle taɓasu, sannan dukkan wani nau’in abinci ko nama da addininsu ya hanesu ci basa cinsa a gidan koda an girka, duk wani taro na shagala dasu jama’ar gidan zasuje su Bily basa  binsu, tasha roƙonsu su rakata Choch dan kawai jan ra’ayinsu amma saisu sami hanya mai sauki su waske mata, samari da yawa sukan nufesu da kalmar so ko ƙawance amma basu taɓa tozartasu ko cin zarafinsu ba, ta hanya mai sauƙi suke fahimtar dasu karatune yakawosu port ba soyayya ba, duk yanda wani shaiɗani yaso mu’amulantarsu sukan nemi tsarin  ALLAH da sharrinsa da gujema dukkan abinda zai ruɗesu da faɗawa tarkonsa.
       Rayuwarsu a wajen bata hanasu saka hijjab ba, bakuma ta ruɗesu saka farce a hannayensu ba ko ƙara gashin doki a kansu, daduk abinda addinin islam ya hanesu dashi, ako ina kuma basajin shakkar nuna su musulmaine bare jin kunya.
     Sunyi ƙawaye sosai yare daban-daban, sukan nema sani akan karatunsu ga wanda sukasan ya fisu, hakama wanda sukafi idan ya nemi taimakonsu sukan masa.
     Waɗannan kaɗanne daga nasarori dasu Ummukulsoom suka samu da cigaban rayuwa.
      A duk sanda suka sami sukuni kuma sakanzo gida suyi kwanaki su koma, hakama su Ummi sukanje su ziyarcesu aduk sanda suka sami ƙyaƙyƙyawar dama, kullum cikin musu nasiha suke da ƙara musu ƙwarin gwiwa tareda tsoratar dasu bijirema ALLAH da gangan saboda ruɗin duniya da tunanin ALLAH bazai kamaka ba wataran.
        Haka rayuwar taci gaba da matsawa har suka kusa shefe wata shekarar, a yanzu haka watanni ƙalilanne suka rage musu kammala karatunsu, musamman ma Ummukulsoom, dan ita bily ma tana gab kasancewar ba tsarinsu ɗaya baneba.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

       Shekarar su yaa Amaan huɗu cikin ta biyar suka dawo ƙasarsu ta haihuwa, dukda kasancewar yaƙine ya kaisu akwai cigaba tattare da tafiyar tasu mai yawa.
     Ƴan uwa da abokan arziƙi sunyi farin ciki matuƙa da ganinsu, tareda godiya ga ubangijin daya basu ƙwarin gwiwa da nasara.
          
          Lokacin da Attahir sukaje dubasu Ummu shida maman Ahmad ba ƙaramin mamaki ya shaba da ganin Ummukulsoom gaba ɗayanta ta canja, sai jinjina kai yake da sake girmama sunan ALLAH, wlhy koshi da ace a hanya yagamu da ita bazai taɓa shaidata ba, komanta ya canja tazama big girl ta gaske.
     Baisan wata dariyar shaƙiyanci ta kufce masaba lokacin da Amaan ya faɗo masa a rai.
         Lallai yana tausayin ƴan maza, ashe lokacin wasan yayi, dan angama gyara filin ga ƙwallo ga ƴan kallon wasa harma da alƙalan wasa a gefe.

      Cike da zolaya ya kalli Ummu yana faɗin “Ummukulsoom baki tambayeni ina mutuminba?”.
       Fararen idanunta ta ɗago ta kallesa, cikin muryarta mai sanyi da tarin nutsuwa tace, “Yaya Attahir wanene mutumin kuma?”.
       Murmushinsa ya faɗaɗa sosai yana kuma kallon ƙyakykyawar fuskarta, “Lallai na kuma yarda ƙanwata ta girma, to tundama kin mantashi bara na tuna miki, abokina Ajiwa”.
      Cikin halin ko in kula tace, “Yaya kenan, shida ba sallah ba yaza ai nai saving nashi a memory na dan gudun kiyayewa, shiba azumiba balle yazama cikin rubutattun ayukana na wajibi, mai riƙewa da adalci shike riƙe zuciya, mai ƙyautatawa da nasibi shike zane a dutse tamkar ruwa mai yaɗuwa a ƙorama, duk wanda kura ta koroshi a tafiya to ka tabbata bazai sake bin hanyarba, idan kaga an riƙe to ɗayan biyune, mosoyin na gaskiya, ko malami mafi kulawa akan ɗalibi, dan ba a taɓa mantawa da abubuwa uku, mutuwa, hisabi, makoma, tsoron ALLAH kesa a tuna mutuwa, Imani kesa a tuna makoma, ƙyaƙyƙyawan buri kesa a tuna alajanna, shikuma baya jerin ko ɗaya aciki, mizaisa yazama abin tunawata”.
        Kai Attahir ya jinjina cikin fadaɗa murmushin fuskarsa, lallai duk bulalar daka raina itake zanar ciki da bayanka kaji zafi har ƙarkashin zuciyarka, Ajiwa lokacin yayifa, ga wuri ga kuma waina, ƴan kallo saiku ƙara shiri.


       ⛹????‍♀lallai zamusha kallo na haƙiƙa????????


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

           “Fodio kana jinafa amma kaimin shiru ko?”.
      Manyan idanunsa daya gada a wajenta ya buɗe a kanta, cikin muryar nan tasa mai amo da izza yace, “Momcy bansan mizan cemiki ba nikam, danni ban shirya auren ƴar kowaba”.
     Harara ta zabga masa tareda watsa masa daƙƙuwa, “kaci gidanku Fodio, mikake nufi? Ba zakayi aureba a rayuwarka komi?”
     Numfashi ya firzar tareda lumshe idanunsa ya buɗe a kanta, sai dai yaƙi cewa komai.
      “Wai miye ka tsuramin waɗannan idanun?”.
    Karan farko da ya saki murmushin gefen baki wanda na tabbata da wata macen yaymawa saita kuma sumewa, bayi yakeba shiyyasa idan yayi saiya kasance na musamman, ita kanta Momcy da ta haifesa saida ta hangame baki, “O ALLAH, Fodio dan ALLAH karinga koda murmushi ne a rayuwarka, ba ƙaramin ƙyau yake makaba wlhy, amma ina daɗi ko yaushe fuska ɗinke kamar wanda aka haifa mala’ikun rahama basa kusa”.
     Kansa kawai yaɗan dafe amma baice mata komaiba, yakuma maida fuskar ya ƙara haɗewa.
    Dad dake bayansu tuni, yaɗan girgiza kansa kafin ya ida shigowa falon da sallama ciki-ciki kamar yanda ya saba.
     Duk amsawa sukai, Hajiya Jamila dake kallonsa a ranta ayyanawa take “Oh ni jamila, wannan wane irin mutane ALLAH ya haɗani dasu, nikam nama ƙagara Bassam ya kammala karatunnan yadawo ko haƙoransa na rinƙa gani naji daɗi, amma kana tare da waɗannan ai dole ka zata kullum wani nasu ke mutuwa”.
    Sudai basu san tanaiba, dan Amaan ma tashi yay yafice abinsa, dama abinci yazo ci, bayan yagamane yaɗan kwanta a falon yana hutawa kasancewar yanzu gidan nasu babu hayaniyar kowa, daga Momcy sai Dad, saiko idan ƴaƴan aunty Ummy su zo, yarinyar Ameer ma ba kawota akeba sai dai idan uwarta tazo gidan, hakama Ummayya yaronta sai tazo take zuwa dashi, Aneesa kam yanzune take da cikin, itakuma Aunty Nurse tana abuja abinta da ƴaƴanta tagwaye itama data haifa duk maza, inba zuwa taiba ba ganinsu akeba. Sai ƴan aiki wanda kuma dokace shigowarsu sashen musamman da ayanzu Yaa Amaan ɗin yana a gidan.

         “Abban Fodio wai kana ganin haka zamu cigaba da zubama Fodio ido bazai yi aureba kenan? Ga ƴan uwansa kowanne har da ɗansa ko ƴarsa a gabansa, ko Buhayyah akaima aure yanzu haihuwa zatayi itama”.
     Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, bai tankaba baikuma sake kallontaba.
     Jigum tai tana kallonsa, ranta duk a jagule, a tsawon shekaru huɗunan gaba ɗaya Alhaji Mahmud ya canja mata, ya daina hira da ita, abinci ma saiya gadama yake ci, baya shawarar komai da ita, komai saidai taga yayisa batareda yace da ita uffanba, ko dawowar Fodio dukda yasani ƙin sanar mata yayi, sai dai kawai ta gansa, hakama tafiyar Buhayyah makaranta, lamarin na matuƙar damunta sosai, ta bashi haƙuri yace ya haƙura amma yaƙi sake mata kamar da, ga kaɗaici da take fama dashi a gidan, haka take yini kamar wata mayya, dawowar Fodio ma bawani rage mata kaɗaici tayiba, tunda ba zama yake suyi hiraba sai yaso. Garama idan su Ummayya ne sukazo, sukuma Dad ya kafa musu dokar sai da ƙwaƙwƙwaran abu zasu zo masa gida…….
     Ganin zai tashi tai saurin miƙewa itama tana marairaice murya, “Haba Abban Fodio dan ALLAH ka saurareni mana, wlhy rashin auren yaronnan yana damuna, kar muna nan sake da baki ya saka kansa a halin neman mata”.
      Bakinsa ya taɓe yana rabawa ta gefenta zai fice, “Ashe kina tsoron ya nemi matan kika sakashi rabuwa da wadda ALLAH ya halatta masa? Saiki dage ki masa aure na ƙwarya tabi ƙwarya ga ƴaƴan manyan mutane cike da gari, ai baikamata ma kizo guna neman shawara ba uwar ɗa”.
       Sosai zancensa ke tsitstsinka zuciyarta, wai har yanzu zancennan yana ransa kenan? Miyasa Abban Fodio keda riƙo irin haka? Abu kusan shekara biyar yakasa goguwa a ransa, yarinyarma ƙila yanzu tagama rakwaɓewa a ƙauye, yanzu hakama tayi haihuwa ƙila tafi huɗu. Jagwaf ta koma ta zauna a kujera yayinda zufa ta jiketa, kardai Abban Fodio yace ya cire hannunsa akan lamarinsa, hakan ba karamar masifa bace a gareta, dan bazata iya tanƙwara Fodio ba ita kaɗai sai da taimakonsa, musamman akan abinda bashi yace yana soba, shegen taurin kasa daya gada a gurinsa shine babbar damuwarta dashi. 
    Ta matuƙar daɗewa a wajen tana saƙawa da kwancewa, yayinda maganar mahaifiyarta ke kuma girgiza ranta, *“Jamila kinyi kuskuren saka Usman ya bijirema mahaifinsa akan aƙida mara amfani, to kisanifa wlhy wataran kezai bijiremawa, dan ƙofa kika nuna masa ta daina muku biyayya akan dukkan abinda kuka ɗorasa akai, kekanki kinsan shegen murɗin halin wannan yaron da taurin zuciya, ko bayan ba raina saikin tina wannan maganar a lokacin dakikaso tankwarasa akan umarninki ya kasa tankwaruwa”*.
     Ta taune leɓe da karfi tana faɗin “Ina hakanma bazai yuwuba mama, babu ɗan dazan haifa a cikina ya isa mijirema umarnina, sakin yarinya danasa yayi kuwa ai nafi mahaifinsa gaskiya, dan kowa yana bukatar cigaba a rayuwa baci bayaba, dolene na zaɓama Fodio matar aure da kaina a wannan karon inhar bashida zaɓin kansa”.
       Wani murmushi Dad dake jiyota daga bedroom ɗinsa yayi, ya jinjina kansa.

     Duk yanda Momcy taso Dad yabata haɗinkai a kan matsalar rashin auren Fodio ya watsar da ita yaƙi saurarenta, yakumaki yima Amaan ɗin maganar.
        Shima Yaa Amaan a satin yaje Ajiwa, kwanakinsa uku ya dawo, a ranar bai ƙwana a kd ba yanufi Lagos shida Attahir dan ana musu nema na gaggawa.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
   
            Haka rayuwar taci gaba da tafiya su Ummukulsoom suka fara jarabawar ƙarshe, gaba ɗaya ta gama tattara hankalinta can, fatanta nasara kawai daga ita har Bily.
          Yanzu hakama dukkan jama’ar gidan suna falo suna hira, sai dai banda Ummukulsoom dake zaune a ɗakinsu tana karatu, tana jiyo dariyarsu daga ɗakin har bily. Mafi yawan lokaci haka take batason yawan hayaniya yanzu, tafi bukatar kaɗaice kanta tai nazarin littatafansu na islamiyya kokuma na boko, wannan halayyar tata kansa mutane da yawa ɗaukarta mai tsananin ɗaukar kai, sam kuma ba haka bane, saika mu’amulanceta zaka fahimci halayyarta mai ƙyau.
          Haka kawai taji sha’awar kiran maman Ahmad su gaisa, tai dailing Number nata tare da sakawa a Hans free taci gaba da duba buk ɗin gabanta, sam Number taƙi shiga, hakanne yasata tunanin kiran Yaya Attahir maybe yana gida……

            Zaune suke da Attahir a Office suna tattaunawa akan maganar ƙarin girma da ake shirin musu, sai dai shi Amaan manyan nata masa zagon ƙasa saboda wani dalili nasu,  kiran Bily ne ya shigo wayar Attahir dan haka ya ɗaga yana faɗin “To autar Ummi ko accaunt yay ƙasane?”.
     Amaan dake zaune na saurarensa amma baice masa komaiba, har Attahir ya daga suka gaisa ya tambayeta ina bestie ɗinta?”.
      daga can bily tace, “Tana ɗaki yaya, kasanta ba gajiya da karatu takeba, ina aunty Hafsat da abokinka Yaa Amaan?”.
     “Ai haka akeso gara ku dage ku sami results masu kyau, Auntynku na gida, Ajiwa kam gamu a tare, zaiki gaidashi ne?”.
      “Wai yaya barshi, wanda a filima ko gaidashi kai bai amsawa da kyau inaga a waya, kace ina gaidashi dai”.
     “A’a ba ayi hakaba kedai gashi ku gaisa”.
    Kafin Bily tace wani abu Attahir ya mikama Amaan wayar yana mikewa da faɗin, “Autar Ummi ce zata gaisheka, bara naje toilet”.
       Uffan baicema Attahir ba, amma yakai wayar kunne da nufin amsawa, saboda bazai iya ƙin jinin Attahir ba, ballema Bily tanada hankali yarinyar.
      A lokacin da Yaa Amaan ke ƙokari kai wayar kunnensane Bily kuma daga can ta yanke saboda tsorata, dan harga ALLAH bazata iya yin waya dashiba.
    Jin wayar ta tsinke ne yasashi jan karamin tsaki yana niyyar ajewa kira ya shigo, screen ɗin ya tsurama ido, *_My Sister_* da ya gani, ya sashi tunanin ko bily ce ta sake kira, dan haka tana gab da tsinkewa ya ɗaga tareda saka wayar a kunnensa yakoma jikin kujera ya lafe yana lumshe idanu.
        daga can Ummu tai murmushi jin Attahir ya ɗaga, cike da nutsuwa tace, “Assalamu alaika yayana!”.
      Wani irin yarrr Amaan dake saurarenta yaji, babu shiri ya buɗe lumsassun idanunsa yana jawo numfashi da ƙarfi, karan farko a rayuwarsa da sautin muryar mace ta sashi jin wani yanayi, baki ya buɗe zai amsa daga can Ummu daduk ta ɗauka Attahir ne ta katseshi cikin shagwaɓa da faɗin, “Yayana yau ƴar shiruce abin, shikenan namayi fushi”.
      Yanzunkam da ƙarfi ya rumtse idon tareda haɗiye tsargawar da zuciyarsa ke nemanyi, sanin inhar tacigaba da magana zai iya cutuwa yasashi saurin katseta kar a samu matsala, can ƙasan maƙoshi yace, “Kina lafiya? Ya karatu?”.
     Gabantane ya faɗi itama, jin muryar dabata yaya Attahir ba, tace, “Ya ALLAH, bawan ALLAH ina mai wayar?”.
      Sosai ya buɗe idanunsa akan Attahir daya fito daga bayin dake cikin Office ɗin, batareda ya bata amsaba ya ajiye wayar yana faɗin, “Kai malam da wace uwar iyayi ka haɗani?”.
     “Uwar iyayi kuma?” Attahir ya faɗa yana karasowa ya ɗauki wayar, idanu ya waro ganin Ummukulsoom, baisan dariya tazo masaba, yay azamar danne bakinsa tareda ɗora wayar a kunne yana faɗin, “Sorry Autar Ummi bana kusane ykk?”.
        daga can Ummu tace, “ALLAH yaya Attahir harna fara tunanin faɗar baƙar magana, wanene wannan ya ɗaga wayar yanata mutane gwalli kamar wani mace?”.
     “Tofa anzo wajen, bar wancan batun, minene labari?”.
     “Babu komai, kira nai mu gaisa kawai dama ka kuma haɗani da Aunty Hafsat”.
      “Im yanzu dai kika faɗi gaskiya, kindai nema Number kawarki baki samuba kika kirani, to ina wajen aiki idan na koma zan kira”.
      “To yaya na gode, ammafa hasashenka ba gaskiya bane”.
    Bata jira cewarsaba ta yanke wayar cikeda takaicin wanda yafara ɗaga mata waya……..✍????

*_ALLAH ka gafartama iyayenmi????????????_*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button