Labaran Kannywood

Masha’Allah Matar Ali Artwork ta Haifa Masa da Namiji, Yayi Masa Huduba da (Muhammad) Allah ya raya.

Masha’Allah Matar Ali Artwork ta Haifa Masa da Namiji, Yayi Masa Huduba da (Muhammad) Allah ya raya.

Fitaccen Jarumi a Masana’antar Kannywood Aliyu Muhammad da akafi sani Ali artwork ko madagwal ya samu Karuwar da Namiji Ya kuma yi masa huduba da Muhammad (Aryan )

Ali artwork shine wanda ya wallafa labarin a shafinsa na Instagram inda yayiwa Allah Godia akan wannan ni’ima da yayi mashi, ya bayyana a shafin nasa kamar haka.

 

Alhamdullilah Masha Allah Muna Godiya ga Allah subuhanahu wata alah daya nuna mana wannan Babbar kyauta wacce babu mai baka irinta sai ubangijin sammai da kassai

Allahu wahidil kahharu Allah mungode maka da wannan ni’ima daka mana, Allah ka bawa Matata Hauwa’u lafiya da karfin jiki Allah ka albarkaci wannan Yaro ka bashi kariya Allah kasa mahaddacin Al-Qur’ani ne Allah ka bashi ikon yin biyayya ga iyayensa Allah kabashi ikon rike gaskiya da Amana a duk inda yake Allah kabashi ikon riko da addinin Muslunci ka kuma bashi ikon bin koyarwar fiyayyan Halitta SHUGABAN mu Annabi Muhammadu S.A.W

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button