Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Sha Da Kyar A Harin ’Yan Bindiga
Sai dai mataimakin gwamnan, wanda shi ne shugaban kwamitin aiki da cikawa kan tsaro na Jihar Kebbi ya musanta rade-radin da ke yawo cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da shi.
“Wannan babban abin dariya ne, ko a mafarki ban taba tunanin a ’yan bindiga sun yi garkuwa da ni ba; Yanzu dai ga ni kuna gani na a gidana ina walwala kamar tsuntsu,” inji Yombe.
Ya bayyana cewa, “A jiya (Talata), a Kanya an yi wani mummunan fada, saboda yadda ’yan bindiga suka cakude da mazaunan garin, da wuya sojoji su yi yaki da su saboda tsoron barnar da za a yi musu Aminiya ta rawaito.
“An yi kazamin fada a garin tsakanin sojoji da ’yan bindiga, amma sojojin sun gaza karya lagonsu saboda ’yan bindigar sun saje da mazauna garin.
“Don haka ba ni da hurumin bayar da adadin wadanda suka rasu a sanadin ba-ta-kashin.”
Rahotanni sun ce daga cikin mutum 19 da suka mutu a musayar wutar har da sojoji da ’yan sada da ke cikin ayarin motocin mataimakin gwamnan.
Harin na zuwa ne kwana guda bayan wani da aka kai yankin Anene, inda ’yan bindiga suka hallaka ’yan sa-kai sama da 60.
Yombe, ya shaida wa Aminiya cewa shi ne ya yi jagorancin tawagar dakarun sojin da suka fafata da ’yan bindigar a musayar wuta da aka yi.
Jihar Kebbi na ci gaba da fuskantar munanan hare-haren ’yan bindiga wadanda ke hallaka jama’a ba tare da kaukautawa ba.
[ad_2]