CAPTAIN RASHEED COMPLETE HAUSA NOVEL
CAPTAIN RASHEED COMPLETE HAUSA NOVEL

CAPTAIN RASHEED
☄???? 1⃣〰5⃣
Na ???? Jeeddah ja’o????
Tsaye yake ,tsayuwa irin na jaruman sojoji ,ya hard’e hannayen shi ta bayanshi ,kai a k’asa yana sauraron mutumin. Wanda ya cigaba da cewa ” Ashe in bana nan bazaku iya kula da komai ba ? Am very disappointed in you !! Wannan ai zancen banza ne!!!! A lokaci guda yayi wurgi da jaridar da ke hannun shi a fuskar jarumin gami da cewa ” take a look at these!!! Jaridar ta bugi fuskar shi sannan ta fad’i k’asa amma abunka da namiji ko motsawa bai yi ba!!! Dattijon da ke maganar yace ” na baka nan da sati daya a san yadda akayi aka nemo min kayayyakin nan in kuma ba haka ba I will held you responsible!!! Kaji na gaya maka! Yana kai wannan ya kwashi wayoyin sa ya fice wasu sojoji suka bi bayan shi , aka bud’e masa k’ofar mota ya shiga suka bar gidan..
Mutumin da ke tsaye kuwa wanda da ka ganshi kaga mai yi masa fadan ya tab’e baki ya nemi kujera ya zauna zuciyan shi na tafarfasa gaba d’aya tunanin shi ya dagule ,ya maida duban shi ga jaridar da ke jefe a k’asa ya sake kauda kai. Wata mata ce sanye da bak’in leshi yasha silver stones idonta da farin gilashi ke sauk’owa daga bene ,har ta zauna kusa dashi bai ma sani ba ,ta d’aura hannun ta akan nashi ta rike ,ya juyo ya dubeta ,tare da k’arfin halin yin murmushi ,itama murmushin tayi sannan tace” My son! Kayi hakuri ,Abban ka fa ya rasa a kan waye zai yi quenching fushin shi ne ,nima saida yayi min saikace ni din ma soja ce ,balle kai kuma da jiya ma sai bayan abun ya faru ka iso garin???? ranshi ne kawai a 6ace. Dan nata ya dubeta yace ” but mom ai……,.” Kafin ya k’arasa tace ” shhhhh!!! ” don’t stress your self !!, breakfast is ready! Naji kace kana da meeting ko? Ka tashi Kaje ka ci abinci ka shirya ka fita, bana kuma so in sake gani kana had’e rai!! Babu musu ya tashi ya nufi dining section don yin breakfast yayin da ita kuwa Hajiyar ta koma stairs abunta…….
☄☄ asalin labarin☄☄
Major General Abubakar Rasheed babba ne a Cikin Nigerian Military kuma wanda aka dama aka shanye dasu a Army!! Matarshi Fad’imatu bafulatana ce daga Gombe state fara kyakkyawa doguwa amma kasantuwar sunan kakarta aka sa mata kuma suna k’iran kakar da inna sai ita ma suke kiranta da INNA FETEL (INNA K’ARAMA), Dansu guda d’aya tilo mai suna RASHEED sunan baban mahaifin shi aka sa mishi , suna zaune a Abuja army barracks ,Rasheed har ya girma burinshi ya zama soja irin baban shi ,sun bashi ilimin addini da na boko ,karfi kuwa ba’a magana domin tare yake workout da mahaifin shi ,balle ma Yaron da ya tashi cikin sojoji sannan kuma ya kasance mai himma haka kuma suke tafiyar da rayuwar su cikin jin dadi ,family ne mai cike da soyayya, duk da kankancin familyn akwai abokanan Rasheed da suke tare da shi a gidan su biyu Muhammed wanda suke ce mishi Al’amin da kuma Abubakar Sadiq wanda zaman su a gidan ya maida familyn tamkar babba ne domin Inna da Abba sun d’auke su tamkar yayan cikin su ne , Al’amin air force ne while Sadiq ma captain ne a takaice dai familyn duk taron military ranks akayi????. Wannan kenan.
☄
Rasheed na gama breakfast ya nufi side nashi don shiryawa ,already ya kusa yin latti ma haka ya shirya cikin gaggawa ya fito ,direct sai d’akin Inna. Tana zaune sai faman rubuce rubuce takeyi yayi sallama, ta amsa fuska cike da fara’a tace ” har ka shirya kenan!” Murmushi shima yayi yace ” yes mom” tayi masa adduoi da ta saba in zai fita, ya amsa da Ameen sannan ya fice ya nufi motarshi????
☄????Jeeddah ja’o????☄
[4/9, 11:32 AM] Jeeddah ja’o????: ????☄CAPTAIN
RASHEED☄???? 6⃣〰1⃣0⃣
Na ????Jeeddah ja’o????
Ya d’auki hanya bai zame ko ina ba sai No 7 Garki road ,inda military defence headquarters yake ,isarsa gate din aka bude mar ya shige ya yi parking, yana fitowa wayar sa tayi kara saida ya gama kwashe files din da ke motan sannan ya d’aga wayar ,daga d’ayan 6angaren wanda ya kirashi yace ” ina hanya fa dude !! Na jika shiru tun jiya baka min emailing wannan article d’in ba” Rasheed ya d’an shafa kanshi yace ” Oooh !! Am sorry I was totally carried away by circumstances around here wallahy ni na k’osa ma ka dawo ko zan huta ” daga d’aya ‘bangaren yace babu wani nan !! Wato so kake in dawo a had’a dani a fad’an ko?” Rasheed yace hmm kana jin dad’i fa lallai mom tana yi da kai!! Wato har ta fad’a maka abunda ya faru ? ” yana maganan ne a lokaci guda yana kallon agogon hannun shi ,ya zaro ido waje:oops: sannan yace ” look dude!! We’ll talk later am already late for the meeting !! Dad is going to finish me up today,” Sadiq ya bushe da dariya yace ” OK ltr :D:D”
Sauri yake ta zubawa a hallway din nan yana wuce offices na manyan soji har ya kai meeting room sannan ya tsaya ya gama kimtsawa ya bud’e k’ofar a hankali yana shiga sukayi ido hud’u da Abba ,ya kafse kamar bai ma san da shi ba ,ya nemi guri zama ,bai zauna ba saida yayi apologising for lattin da ya maka ,don ya lura wasu har sun k’osa ma. Ba tare da ya kalle she ba Abba yace ” you may start presenting how the operation is going to be ” ya kwashi files din aka kashe wuta sannan aka kunna projector wato majigi sannan ya fara presentation din nashi hankali Kwance ya kammala duk Kowa kuma ya yaba da hakan. Minti talatin ne kachal dama meeting d’in Kowa ya fice banda Rasheed da Abban shi ,shi Abba kawai bai ga daman tashi bane amma Rasheed files d’in yake tattare wa , har ya gama zai fita Abba yace ” a office d’ina akwai wasu files guda biyu red colour an rubuta operation red I want you to go through them ,Kaje ka d’auka yanzu!!” Rasheed yace “SIR!!!???????????????? ya fice ya barshi cikin room d’in….,…….
K’arfe biyar na yamma Sadiq ya k’ira Rasheed ,yana dagawa yace ” dude na iso fa amma kuma I can’t drive anymore jikina ba k’arfi sosai wlhy ,Kazo ka d’auke ni plssss!! ” Rasheed yace OK kana ina yanzu?Suleja road ! OK ganinan zuwa” ya kashe wayar ya tashi ya saka wata Yar shirt nashi blue armless gashi button din a bud’e hakan yayi displaying twelve packs nashi ,bai saka buttons din ba har saida ya iso inda Sadiq yake ,shima yayi hakan ne saboda tarin y’an mata da ya gani a chan gefe ,saboda mutum ne mai kunya when it comes to issue na mata saboda haka ne ko a barrack bai cika shiga sabgarsu ba sai na mutum d’aya ,wato childhood friend nashi wanda ban ambace ta tun farko ba ,sunan ta Imtihaal ya fita da wajen shekara biyar amma sun shaqu sosai, saidai yanzu bata k’asar ,taje karatu a Malaysia… Sadiq ya d’an lallaba ya k’araso inda motar yake ,shi kuma Rasheed ya bud’e masa ya shiga sannan ya zagayo shima ya shigo gami da rufe k’ofar, har zai sa key ya kunna ya juya ya dubi Sadiq da sai yamutsa fuska yake yi yace ” ya dai dude! Me ke damunka ne? ” wlhy ina fada maka na tsaya ne na ci fast food a wani restaurant cikina ya birkice sau wajen bakwai ina tsayawa a hanya sai na nemi gurin juyewa???? lol. Rasheed ya bushe da wata irin dariya ta mugunta wanda har saida yasa Sadiq razana ???????????? ” yanzu kai dan Allah meye abin dariya ???? ni shiyasa bana son fad’a maka wallahy nasan dama abunda zaka min kenan???? ” Rasheed ya ci gaba da dariyarsa haka suka isa gida tun Sadiq na fushi har shima ya biye masa suka ci gaba da dariyar????.