NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 41-42

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO…*
*MMN FAREESAH….*
4⃣1⃣&4⃣2⃣


Yayi Baya luuuuuuuu,, dasauri sauran likitocin dake tsaye sukayi nasaran tare sa Suna salati..
Taimakon gaggawa suka Shiga bashi,,cikin Ikon Allah suka Sami damar dawa masa da numfashinsa,,sedai Yana farkawa ya dafe kai Yana hawaye..
Ruwan da aka dauramasa ya fizge tare da Tashi tsaye cikin tashin hankali,,jiyake Shima kama Ze Mutu sabida ya tsara yadda rayuwarsu zata kasance da irin soyayya da zasu gudanar a Duk lokacin da komai ya daidaita..

Daddy ne ya shigo ransa a bace,,Yana tafiya cikin sauri harya qaraso inda mashkur Ke tsaye” mashkur besan da zuwan daddy ba sabida yadda yake acikin tashin hankali.
Motsin dayaji a bayansa ne yasashi saurin zabura a gigice jikinsa Har tsuma yake tsabar tashin hankali Hade da Dana Sani mara musaltuwa ya Bude baki zeyi Magana daddy ya katseshi…

Bakin daddy Na rawa kama ze kifa sabida tashin hankali yace”mezaka gayamin auta,,Ashe Baka da hankali” yanzu mezamu Gaya iyayen yarinyarnan”Yama za’ayi ka dauki ‘yar mutane ka kaita wannan gidan,,Bayan kasan halin mahaifin Yasmeen da Kishin tsiya,,gashi Shi bedauka mataki ba Yasmeen ta dauka,,sun kashe marainiyar Allah wanda bataji ba Bata gani ba..

Kuka me ciwo mashkur ya saki,,da gudu yafada jikin daddy,,cike da matsanancin tashin hankali  mashkur yace” daddy Dan Allah kada ta Mutu wallahi banshirya rabuwa da itaba,,daddy inasanta Dan Allah daddy kace ta Tashi..
Ganin da daddy yayi ba’a cikin hayyacinsa yaje ba shiyasa ya rungumeshi Yana shafa bayansa..

Sedai yadau lokaci jikin daddy Yana kuka kafin yafara safke ajiyar zuciya” ganin haka yasa daddy fara Magana a hankali..
Garin Yaya ka tafi da yarinyar mutane Har akayimata irin wannan illar,,kana Ina Hakan ta faru daddy ya jera masa wadannan tambayayoyin?

Bakin mashkur Na rawa yace,,daddy kayi hakuri Nima bansan haka zata faru ba,,kasani cewar daddy tare da tsaresa da Ido” wallahi daddy bansani ba,,Dana sanina Hakan tafaru ba,,nayi nayi tabari Amma Duk da haka Saida ta kashemini ita mashkur yaqare maganar cikin gunjin kuka..
Wallahi inasanta banaso Na rasata,, kuskuren ne Yasmeen ta Riga ta aikata mana,,daddy bansan yazanyi da itaba..


Mama na zaune a falo tana kallo Taji fadowar Abu akanta” dasauri ta dago tana kallan yasmeen,, cike da tashin hankali tafara jera Mata tambayoyi”
Yasmeen meya sameki” accident kukayi,,Ko Yan bindiga dadine suka tareku,, Yasmeen Bata Iya amsa mama ba, Saima kukanta data qara saki tana qara shiga jikin mama..
Tureta mama tayi tana cewa” Dan gidanku ki gayamin,,gaba daya kin Tashi hankali to kodai Yan garkuwane suka tareku a hanya..
Qin Magana Yasmeen tayi sabida batajin zata Iya furta Koda Kalma dayane sabida bakin Kishin dake Cin zuciyarta,,jitake inama ta Mutu kota Dena Jin abinda takeji a jikin zuciyarta..
Ganin tayi Shiru taqi Magana yasa mama Tashi tsaye tana cewa to Ina Shi mashkur din yake?
Ni ‘yan nan inazansa kaina,,ya Allah ka kawomin dauki” Ke Yasmeen kodai kurma Kika Zama mama ta fada tana kai Mata Duk..
Yasmeen ki Duba jikinki yadda Duk ya baci da jini indai wannan jinin mutum ne to Babu shakka hadari kuka Samu,,da yaushe kuka fita a gidannan baki gayamin ba,,Ina kukaje?

Duk tambayoyin da mama tayi babu Wanda ta Samu amsa,,ita kadai tayi burarinta ta gama,, ganin datayi Yasmeen taqi kulata yasata sakin kuka tare da fitowa waje da gudu tana cewa..
Me Gadi wakaga ya ajiye Yasmeen?
Cikin tashin hankali hankali baba me Gadi yace’ hajiya Ai Yasmeen ce ta kashe wata yarinya da wannan alhajin mashkur yazo da ita,,Nima ina nan inajin radio banji abun ba Sai Daga Baya..

Cike da matsanancin tashin hankali da fargaba mama ta dafe qirji tana cewa” kisa fa kace Malam Audu?

Kwarai kuwa Dan gaskiya yarinya ta Mutu sabida Nida kaina nadubata Kuma kinsan ninake sallar gawa a garinmu kafin Na Samu wannan aiki..

Mama taba idajiba ta Koma ciki da gudu ta dauka waya ta Kira Abba”
Tana kuka tace” Alhaji kayi sauri kazo gida ba lafiya”
What!!! 
Hajiya Karki gayamin Wani Abu ya faru da ‘yar Lele,,Dan Allah ba yadda zanyiba,,kowaye ya tabata Sai inda qarfina ya qare..

Mama batasan lokacin data saki tsaki ba,tana cewa”
To ai shikenan yanzu saika zo kaga abinda kudi da shagwabawa game da sanka suka jama”
Murmushi Abba yayi Yana cewa kedai kullum bakida abokin Kishi Sama da Yasmeen,,yanzu fisabilillahi Idan ban shagwaba lelena ba wazan shagwaba,,da Allah kidena yimin irin haka..

Hawaye masu zafi mama ta goge tana cewa” to ai gashinan abinda gata Yaja Mata” ta kashe “Yar mutane..
Cikin firgice Abba yace” ehhhh hajiya kinko San abinda kike fada,,kisa fa kikace”

A hasale mama tace eh,,abinda Kaji Shi nake fada,,Dan haka yanzu ka dawo gida musan halin da yarinya take ciki,,tana gama fada ta katse Kiran tana zagaye faloon…

Zuwa yanzu ita Kanta Yasmeen hankalinta yatara Tashi Amma Idan ta Tinan ta rabu da damuwanta Sai Taji hankalinta ya kwanta,,Babu abinda Ke Daga Mata hankali illah kukan mama data zauna Kan kujera tanayi tana salati tare da neman dauki gurin Allah.

Ahankali Yasmeen ta matso kusa da mama tana cewa,,pls mama kidena zubda hawayenki Akan wannan banzar,,hawayenki yadena zuba Akan ‘yar sadaka mara Gata..
Tasss tasss tasss mama ta dauke Yasmeen da Mari tana nunata da yatsa’
Yasmeen Karki Bari bakina ya fadi mummunar Kalma akanki” Kuda kuke da kudin ki Kuka ba kanku” to wallah ki Sani Idan Har wannan yarinya ta Mutu Bazan Bari ki zauna a gida kinajin dadiba,,wallahi kema Sai an daureki,,shashasha kawai..

Bani wayarki,,hannun Yasmeen na rawa taba mama wayar’ Cilla Mata wayar mama tayi tana cewa” ubankine Ze budemin day Zaki Bani ita ahaka,,wallahi kikayi wasa kema Saina lakada Miki Dukan mutuwa kinga Sai ayi biyu…

Hannun Yasmeen Na rawa ta dauka wayan ta cire password ta miqa mama”
Number mashkur mama ta Duba ta danne Kiran..

Mashkur dake kwance jikin daddy Yana kuka yaji wayarsa Na ringin kasa dauka yayi Sai daddyne ya amsa Kiran..

Assalamu alaikum,, daddy ya amsa yanasan sanin wacece,,Dan ba Suna yagani jiki ba,,

Bakin mama Na rawa tace,,nice mahaifiyar Yasmeen” Dan Allah a wanne asibiti kuke?

Seda daddy ya rintse Ido kafin yace,, muna standard hospital,,dan Allah yame jikin,,mama ta tambaya cike da Kunya..

Zuwa yanzu bamusan halin datake ciki ba,,dazu Dai harsun fito da ita Sai kuma aka Koma ciki,,Suna qara Duba lafiyanta..

Wani irin dadi mama Taji Dan harga Allah Idan nijlah ta rasu batasan inda zata sa kantaba..

Bata saurari Yasmeen Ko Abba ba ta dauka mayafi ta fita da saurin gaske Har tana hadawa da gudu..

Yau mama da Kanta tayi drive sabida tsabar zauri da yadda zuciyarta Ke azalzata.Comments & share

*Momn sultan ce*✍✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button