Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
MATSAYINAH COMPLTE NOVELNOVELS

MATSAYINAH COMPLTE NOVEL

Ad

_____

Compiled by Unar Dalha Funtua.

Copies by Safiyya Abdurahman Abubakar.

Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuhu…

_Tabbas labarin nan ya taba faruwa, zamu iya kiransa true life don Ina shekaruna na primary ya faru da wata yarinya a Lagos, a news na samu updates din, sai da na mallaki hankali na, sannan na zabi in yi rubutu kansa, nayi kwaskwarima da ‘yan gyare gyare, na true life din ba twins bace, na kara dai abubuwa don Sanya masu karatu Nishadi, but the lesson I want to pass across remains the same…

Idan yayi kama da rayuwarki kiyi hakuri, its just a fiction☺, don’t pick offense please🙏🏼.

Asha karatu lafiya

MATSAYINAH

NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR
(UMMU FARHANAH)…

1…

Rayuwa takanzo wa bawa cikin yanda mai kowa da komai ya tsara abinsa, duk yanda kaso da kiyaye kanka abu ne mawuyaci, yanda na tsinci kaina cikin rayuwata ni kaina na san babu yace zanyi, ni din bani da wani gata sai yanda akayi da ni, uwa uba bani da wani tushe da zan danganta kaina dashi, irin haihuwar da uwata tayi mani ya sanyani zama “celebrity” yanda ba dama in ratsa guri yanzun zakiga ana nunani mutane suna fadin gata nan, aibatani kam har ya zame mani jiki tunda ba yau aka fara ba, abin da kan sosa mani zuciya har zuwa wannan ranar babu tsayayyar magana game da asalina, Allah yasa ni ba ‘yar gaba da fatiha bace, na fadi ina share hawayena babyna ta fadi cikin yanayin daga murya tana dan duduba inda zata hangoni,ta dan 6ata rai sannan naji tana fadin ke kuma ba’a isa a taka maki burki ba ko? Na girgiza kaina gami da mikewa ina gyara zaman takalmana, biyoni, ta fadi sannan ta yi gaba ni ma na rufa mata baya, mummy Rahmah kenan matar da nayi wayo da ita a matsayin uwa, duniyar nan bani da sama da ita, palon gidan muka zauna nida uwar gidan gwamnar jihar da aka maidani don tabbatar da lafiyata kafin a gama case a high court,me zakici? Tayi mani wannan tambayar tana kallona, na koshi na fadi kai tsaye, Rahma kuje please naga kece acting mummyn ta zatafi sakewa da ke, muka koma dakin da aka cika mani da abin duniya a matsayin muhallina, na zauna dab da kofar dakin ina razgar kuka mai tsima rai, a hankali ta karaso ta kama hannayena 2 gami da cewa its ok babyna me haka? kina girma kina cin kasa haka na koya maki? Na girgiza kaina amma na kasa tsayar da kukan da yaci karfina, muryarta naji tayi rauni karo na farko a rayuwata kenan da zanga raunin mummyna Rahmah, ta janyoni jikinta tana shafaDA mani kai sannan ta soma fadin zuciyata ta kan damu da yanayin da nake ganin ki a ciki babyna, ban son damuwarki sam amma ya na iya? Wannan itace kalmar data zame mata abin fadi a duk sanda na rikice mata,ta fice yayin da narakata da idanu zuciyata cike da abubuwan da suka min karan tsaye cikin raina, ni MATSAYINAH kawai nake son sani, ba jimawa ta shigo da plates kala kala mai dauke da nau’in abinci, tana dan yi murmushi daidai lokacin da take fadin come to me my child, na karasa na fada jikinta ina gunji, me ke shirin faruwa dake ne Hameedah? Mummy ban sani ba jiya a sch wasu ‘yan class dinmu suka bani newspapers na karanta mai dauke da hotounana da labarai kala kala, mummy pls kice mani karyane Allah ke na sani ke nake mafarkin samu a matsayin uwa, bani da kowa mummy ki taimaka mu kasance tare sai dai mutuwa ta raba mu, mummy ke fa ina ‘yan uwanki? Ta dan jima kafin tayi magana har nayi zaton bazan samu wannan amsar ba naji tana fadin nima bani da kowa sai ke, kaman ya? Kawayena suna hiran yayyensu, daddyn
su, kaka, da sauran ‘yan uwa amma ni sai dai ayita ra6ani anai min kara na rasa na asali, yau naji abin daya daga mani hankali mummy pls kice kage ne? Da ban damuwa idan ana aibata ni amma yanzun na fahimci gaskiyace kuma daci gareta, mummy baki ta6a haihuwa bane? Hawayene na gani sun cika mata idanu sannan ta soma fadin da ace ‘yata tana nan kididigan shekarunku daya ne exactly, a sanyaye sautin kukanta ke fita ta ci gaba da cewa bayan 7 miscarriages ita kadai na haifa ta mutu ban samu daman ganinta da rai ba, amma Hameedah kin dinken wannan 6arakar,mijinki fa? Ni ban ta6a ganinsa ba,ta dan yi gyaran murya sannan ta ci gaba da cewa Allah ya jikansa, nayi auren soyayya da Buba namijin gaske tun zamanin kuruciyata muka hadu, alal hakika yayi mani halarci har iyayena suka amince a wancan lokacin bamu da wasu dangi masu yawa, shi da kansa ya dogara dama babu wani nasa don maraya ne tun da kuruciyarsa, ni kam ‘yar gatan iyaye ce, ni kadai suka haifa mukayi auren so sai dai matsalar 6arin cikin da na rika samu shi ya hana wanzuwar farin cikin mu gaba daya, nama fishi damuwa saboda inada son yara ba wasa ba, shi kam sai yayita riritani, ina da ciki na uku labarin mutuwan innata ya riskeni, wannan firgicin daya haddasa mani faduwa shi yayi sanadin fitar cikina, na wahala a asibiti akace mahaifata tana da tsantsi, na dogara da Allah kula da Baba ya dawo kaina don shi akwai shekarun girma da tsufa datijo ne mai tawakali, a haka har saida nayi sau 7, ana takwas din ne Allah ya kaddara zamu samu sanyin idaniya, lokacin har na fidda rai, cikina ya dan tasa Buba yayi wata tafiya da bazance ga dalilin kin dawowarsa ba, mafataucine dan gaske mai kamala da sanin darajar na gaba da shi, daga ni sai baba mai kokarin kwantar mani da hankalina, har ciki ya kai minzalin haihuwa a gida nakuda ta kamani da wahala na kasa haihuwa saida makota suka taimaka aka kaini asibiti, a can na haifi babyn da har gobe kamaninta bazasu 6ace wa idanuna ba, ina cikin wani hali aka wanketa aka nadota a dankwalin atamfar jikina, na farka daga barci na sameta a gefena farin ciki tamkar in zuba ruwa a kasa in sha, sai dai kash, murna ta koma ciki sanda na fahimci Allah ya kar6i kyautar da ya mani, kuka sosai nayi aka yi mata komai aka rufeta angulu ta koma gidanta na tsamiya, na koma aikin bauta a gidan jama’a tunda babu mai dawainiyarmu, a haka na samu tayin aiki a gidan marayu dake Abuja lokacin watanni 2 kenan da haihuwar babyna, ina kula da Baba ina taimakon kaina, ranar wata alhamis na wayi gari da labarin data daki zuciyata ba wasa ba, baba ya rasu a hanyar dawowarsa daga masallaci mota ta kade manishi, nafi jin rashin Baba don a wancan lokacin shi kadai ya rage mani abokin shawara bango majingini, ban dogara da shawarta wa kaina komai ba sai abin da Baba ya gaya mani nake aiki dashi, nayi kukan nayi kewa mai yawa kamin daga bay a na zama jarumar gaske… Haduwarmu dake ya samo asaline da tarin kulaliyar da rayuwarki ta afka a ciki, ni Rahma ina da karancin ilimin boko amma na addni Alhamdulillah, hakan ne ya hanani samun aiki mai tsoka, son yara da Allah ya dora mani shi ya dawama dani a gidan marayu,ina yawan bin labarai ko jaridu don dai kawai inda hali in samu labarin Buba, sai dai yanzun har na sare na fidda ran sa, wannan nema ya hanani aure na rike kaina da daraja, nayi farin jini a fagyan kula da yara har manyan ma’aikata kan kawo mani yaransu nan idan zasu aiki in sun taso su biya su kar6esu, haka takan kasance kullum a nan ne nayi sabo da mutane da dama, ina da gogewa wanda ya sanya ake mani kallon ‘yar boko, safiyar wata juma’ah mummyn Saimah da Siyamah ce ta kawosu(‘yan 2), na kar6osu ina murna sun dan yi wayo don sun dan shekarunsu 2 suna takawa ko ina abinsu, yaran bul bul tabarkallah, na bita mota don kar6o jakar daipar da sauransu, jaridace a hannunta har na juya zan tafi naji tana salati, hankalina ya koma kanta lfy dai? Ta mikomin jaridar gami da cewa ingo mummyn yara nayi latti, ki duba ki ajiye mani, in nazo daukan babies sai in kar6a ko? Nayi godiya sannan na koma cikin gidan da yaran da suka zame Mani tamkar zuri’ata, hankalina yana kan jaridar, duk na kosa in San abin data kunsa, lokacin Ina da yara ‘yan dagwai dagwai sun kai goma a karkashin kulawata, a yi kokarin basu kulawa kamar kullum amma bani nasamu damar duba jaridar ba har Sai da yaran suka samu barci ni kaina na tabbata ayyuka sun min sauki sannan na soma dubawa,hoton babyn da aka kira ‘yar watanni shida,ganinta naji matsanacin faduwar gaba na ba gayra babu dalili,kyakyawa wace labarinta da sa in san da ake kanta ya sauya tunanina,naji ina kaunarta ina kwadayin riketa amma babu wannan damar,kamar yanda jaridar ta shaida wa mai karatu cewa akayi Hajiya Ni’ima Garba ce mahaifiyar wannan yarinya,wace aka haifa a asibitin dutse, nima a nan na haifi babyna a wancan lokacin cikin jihar Kd kenan, amma an samu sa6anin labari kan haihuwarta, don an ce ta manyata hajiya ni’ima bata cikin rukunin matan da suke ganiyar haihuwa, anyi hira mai gadin gidanta ma yace bata ta6a haihuwa ba sai kan wannan da shima yake kokwanto kansa, ana cikin wannan lamarin kuma wata hamshakiyar mai kudi itama ta taso tana fadin ‘yartace shine ta kai kara kotu, ana wata ga wata, har mummyn su twince ta dawo daukansu ban cikin nutsuwata, wannan ne ma ya sanyata cemin yarinyar tana da shiga rai, ki rika sauraron news karfe 9 na naija don sun daukaka kara kuma ba wasa tunda dukansu masu fadan babayn manyane, kinga sai inda karfi ya kare kenan? Na gyada mata kai kawai ina godiya har kosawa nakeyi 9 tayi don inji ya za’a kare… Yauma kaman kullum ina zaune a gaban tv saboda jin taken labaran kasa da za’a fara, na natsu sosai aka hasko kotun duk da dai ba wani bayanai sukeyi dala dala ba amma na kalli abin da nakeso, mataye 2 dake claiming babyn duk ba yara bane, an kira mijin ita haj Ni’imar waton Alhj Garba yayi yan bayanansa, cewa shi ba mazauni bane babban dan kasuwa ne da kan fita kasashe, wani hutu da ya dawo naija ya risketa da ciki, a wannan lokacin ga yawon shiga asibitoci data dorawa kanta damuwan sai ta haihu, shi din bai gamsu da asalin babyn ba saboda halin da mai dakinsa ta tsiro tunda tace tana da ciki ya ga bakin lamura sosai, ya dauko dairy dinta ya mikashi ga kotun tare da cewa gata nan duk hukuncin daya dace da ita ayi mata ba hannuna ciki, daga yanda labaran ya kasance said naji na kagu in ji yanda zata kaya, babyn abar tausayi ce, sun taru sun jefata cikin hatsari, an mata dabaibayin da idan ta girma a hakan rayuwa zatayi mata kunci, na jima zaune INA saka da warwara, duk da dai ba komai make fahimta ba saboda kalaman kan yi mani tsauri amma na fahimci Inda aka sanya gaba.

Ad

_____

1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button