MIJIN KANWATA COMPLETE NOVELNOVELS

MIJIN KANWATA COMPLETE NOVEL

Follow this link to join my WhatsApp grou

MIJIN KANWATA..!
(k’addarata)

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI SALATI,GAFARA DA RAHMA SU TABBATA GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD SALLALAHU ALAIHI WASALLAM DA IYALANSA DA SAHABBANSA

Warning:
Using Any part of This book or making Audio without the permission of the Author is prohibited

SADAUKARWA: Gareku yan Amana MASOYANA masu bibiyar Labaraina Da Masoyana masu Siyan Labarai na Musamman Masoyana da suka Taru wajen nuna min kauna da soyayyah wajen siyan Littafin Imu da Intee YAN GIDANMU Wannan labarin gabadaya Sadaukarwa ne gareku gabadayanku

Page 1

KADUNA..
Area:Anguwan Dosa da misalin Karfe bakwai da Rabi 7:30am na Safiyar Ranar Talata

Safiya ce sosai ta yadda gilmamar ababen Hawa suka yawaita akan Shararriyar Titin kwaltan na anguwan Dosa kama Daga yan makaranta,Dake saman abun hawa Adaidaita zuwa kan wadanda ke tafiya akasa Da kuma wadanda iyayensu suka Daukosu Domin ijiyesu a mkaranta kafin su wuce wajen aiki Harda ma wadanda Direbobin Gidansu ya”yan masu Hali suma ana ta Kiciniyar kai su makaranta da kuma ma”aikata masu zuwa aiki harda masu dawowa sai Titin ya cika Glowslow yadan karu Fiye da in Rana ta Daga Kowa ya tafi Sagban gabansa.
Acikin masu Dawowa Daga wajen aiki Cikinsu Harda SUNAIMA ABDU DATTI ma”aikaciyar Lafiya ce Nurse Datake aiki a Asibittin Barau Dukku Dake nan kaduna Kusan Shekaru biyu da suka gabata.
Tana Cikin adaidaita wace ta Hayo Daga Bakin asibitin Tun bayan Fitowarta Tun jiya da Daddare tatafi aikin Dare gareta ma”ana Call sai yau da  safe da Masu aikin Safe suka zo suka Mika musu aikin kana su kuma suka yi sallama dasu suka nufo Gida acikin yan”uwan aikinta Mata dukkansu Matan aure ne da ya”yansu ita kadai ce bata taba aure ba Wasu mazajensu ke zuwa Daukansu Wasu kuma kannensu ko kuma Direban mazajen nasu Daga ita sai Sister Aneesa kadai Masu adaidaitan Kofar asibitin suka Haddace Yanayinsu Saboda Tsabar iya kwarewa ahawan adaidaitan Sister Aneesa matar aure ce itama Sai dai mijinta bamai Hali bane sai Rufin asiri ko Keke bai da ita Itace ma Take Tallafe da gidan da aikin Datake yi.
Sunaima bazata ta Kira kanta Budurwa ba Domin itama wai matar aure ce da aka Daura mata aure Wattani Biyar da suka gabata abaya kafin hakan ta Faru ta Daina kallon kanta a mtsayin Budurwa Eh mana ta wuce wannan Lokacin Shekararta Talatin aduniya Har ta gama Cire rai da aure kwatsam K’ADDARARTA ta shigo Rayuwarta Kaddaran da har yau har gobe ta Kasa yarda da Hakan ya Zama Kaddaranta gani take yi komai ba Daidai yake Tafiya ba in har Daidai ne ina ita ina Auran MIJIN KANWARTA..?
Wanda suke gogayar shekarun juna dashi..?mijin kanwarta masu soyuwa Gareta fa Meyasa Mutuwa ta Dauke SUNAIRA..?Meyasa Kaddararta ta ratso Da Mijin kanwarta..?wanda yake ganin Girmata nake ganinsa kamar kanina wanda yake auran kanwata da na bama Shekaru biyar aduniya..!
Ita daman ai kaddara bata shawara da Kowa in ta tashi Faadamaka Wani Lokacin Bawa yakan ga kamar Allah baya son shi in ya Bashi wata kaddaran ammh kuma Hakuri da Juruya suna saka in ka Rumgumi kaddaranka Hannun Bibbiyu Watan Watarana Kai ne zakayi Dariya da wannan Kaddaran Domin yawancin Mutunne kaddaransu ne Alherinsu Duniya da Lahira.
Gidansu yana kan Titi ne gidan Data shafe Shekaru Talatin Tana Rayuwa acikinsu anan mai adaidaitan tace ya ijiyeta kafin ta Fito ta Bude karamar jakar Dake hannunta ta Dauko mai Kudinsa ta basa kana ta Fita Daga Cikin Adaidaitan lokaci Daya Tana kara gyara Zaman Dogon Hijabin Dake Jikinta Pick colour Wanda saboda Zama yadan Tattare ta kasa.
Dogon Hijabi ne har Kasa Domin hatta Dika dikinta suna Rufe ne,sai dai ka hango Kafarta Cikin wani Rufaffan Takalmin Fata baki mai kyau irin na mata zamani,da safa akafar naata wacce ta Rufe kafar ba’a iya ganin komai.
Doguwar Macece in nace Doguwa Ina Nufun Sunaima Tana da Tsawo sosai,bata da Kiba jikinta Siriri ne wanda in ka Lura ma kamar Hijabin Jikinta ne ya karamata Kauri,Fuskarta ne kadai a waje domin Hijabin na Zamani ne yana da Hannu ta kuma Sanyo duka hannuwanta waje Ammh Ta saka bakar Safar hannu,Hijabin irin mai Daurewa ta saman kai ne jalbab Shiyasa ta Daureshi ta baya Fuskarta ta Fito Tar cikin dan Hasken Ranan Daya Fara Fitowa.
Ba fara bace sosai sai dai Tana da Haskenta na kalan Chaculate,Tana Dauke da Doguwar Fuska ne mai Dauke da Dogon Hancinta har baka Bata da manyan Idanuwa sun dan Shige Ciki kalan bakinta dan karami wanda ya bada Shape din saman Leben yafi kasan Lefen Tudu sai ya bada wani Shape daga wajen Bakin nata Tana da yalwar gashin gira dana Ido,har dama na da sumar kai saboda yadda Daga goshinta kananan gashi suka kwanta luf.
Akallo Farko in kayi mata zaka Hango Tarin natsuwa da kalama atare da ita,Kwata kwata Fuskarta bata bayyana Shekarunta ba sai ma ka kara Kallonta in akace maka takai wadanan Shekarun saboda yadda ta Mori karamin Jikinta da karamar Fuskarta Data boye shekarunta..
Sunaima ba kyakyawa bace ta azo agani ammh kuma Tana Cikin jerin matan da Kyansu ba lokaci daya ake ganinsa ba sai ka Zauna dasu na wani Lokaci a hankali Tasirin kyansu da nasabarsu zai fara Fizgan Hankalin Mutum baka sani ba..!
Cikin Takunta na koyaushe Cikin Natsuwarta kamar ko yaushe kanta na kasa,ta Nufi Kofar Gidansu mai Dauke da Dakali guda Biyu,Gidan ginin da ne ammh kuma ya samu Gyara da Facin zamani yasa sai yayi kama dana Zamani gidan yana Shafe da Fenti ne gaba da bayansa kalan Green Dark mai Kurzukurzuni.
Gidan dan madaidacine bai da wani Girma,sosai yana Dauke da Kofa mai kyau ta zamani wanda zai sadaka da Zauran Gidan kafin ka isa Cikin Gidan
Kanta na kasa ta kariso Kofar Gida nasu Mashin din Data gani akofar Gidan nasu ya Tabbatar mata da Baba yana Gida bai kai fita ba.
Mirmishi ta saki acikin Ranta ita kadai akallah yau kila Baba zai Ceceta Daga Fada Inna na Fama da bata gajiya dashi aduk Lokaci irin haka Data ke dawowa Daga wajen aiki Bata wuce Gidanta ba..Gidanta kuma..?
Kodai Gidan kanwarta inda tayi Rayuwar Shekaru biyar har da wasu Wattani sannan ita kuma a wattanin baya Kaddara itama takai ta Cikin Gidan a matsayin Matar gidan kamar yadda ashekarun baya takai Sunaira Cikin Gidan,Duk da alokacin ba awannan Gidan suka Fara zama ba Daga baya ne ya gina wannan Katon Gidan suka dawo.
Kanta na kasa tana Shirin Tura Kofar gidan ta shiga ta tsinkayo Murya Daga Gefenta Tana Fadin”Ah..ANTYNMU barka da dawowa..?
Ina kwana..?
Aka fada cikin Girmama Tun kafin ta Juyo tasan ko waye Hashimu ne mai Shagon Saida provision nan bakin Titi kusa da Gidansu
Makocine sosai Domin yafi Shekara Goma anan wajen yana Sana”arsa tun Farko Mahaifinsa ne keda Shagon yana Zama mai har Allah yamai Rasuwa da Farko shagon ya Mutu sai daga baya Shi Hashimun ya Dawo ya Tada Shagon kila da yan kudin Daya samu na Raban gadonsu ko kuma wasu kudaden ya Tada shagon da yanzu ya zama mallakinsa.
Matashi ne mai neman na kansa yana da matukar girmama na gaba Dashi,Sunaima bata da Sakewa kamar Sunaira shiyasa sun fi sabawa da Marigayiya Sunaira Lokacin Tana Raye ita haka Allah yayi ta Tana da Kiyayewa da kamewa sau da Dadama Mutane suna mata kallon mai Girman kai da kuma son Girma.
Juyowa Tayi Cikin dan Sakin Fuska Tana Fadin”Eh Hashimu Lafiya lau ya kasuwa..!
Yana Daga Kofar shagonsa zuwansa kenan baima kai ga Bude shagon ba yace”Lafiya lau mun godema Allah..Kin dawo Daga wajen aiki kenan..!?
Batayi mgana ba shima bai Damu ba Sanin Halinta yasa ya cigaba da Fadin”Ina su Wasim Fatan suna Lafiya..?
Yafada yana kallonta jin sunan Daya ambata yasata sakin Mirmishi har Fararan Kananan Hakoranta suka Bayyana a waje kafin ta kada kai Tana Fadin”Yanzu suna makaranta..Lafiyarsu Kalau Hashimu..!
Shima kan ya kada kafin yace”Allah ya Jikan SUNAIRA..Allah ya kyautata makwancinta..!
Sanda ya fadi haka kamar ya Famo mata da Tarin nauyin Dake Cikin Kirjinta ne wanda ta Binnesa Wattanin baya,Idanuwanta suka Cikoda kwallah kafin ta juya kawai acikin Ranta take amsa addu”arsa da Ameen ya Allah..
Har ta shige gidan bai Daina kallomta ba Kai ya kada kafin ya karisa Bude Shagonsa Allah ya gani Rayuwar Sunaima Tana bashi Tsausayi Lokaci Daya Kaddara ta zo mata Lokacin da bata Shiryama hakan ba.
Tana sawo Kafarta Tsakar Gidan nasu Wanda ke Shimfide da Siminti Ko”ina da Siririyar Sallamarta Ta fara Lekowa kamar wata Barauniya Tsakar Gidan tsit ba alamun Motsin kowa Madafi ta Leke Nan bataji Motsi ba Kallonta ta maida Kofar Dakin Baba Ta hango Takalmin Inna Ajiyar Zuciya ta sauke kafin tace afili..!
“Akallah dai yau Inna bazata fara Dani ba..!
Daga haka ta shigo Tsakar gidan Tana Sanda Lokaci Daya tana kallon yadda Inna ta Shareshi Tas kamar ka kwanta a wajen Saboda tsabta.
Sanda take yi a hankali Ta Nufi Hanyar Dakinta wanda ya Zame mata tamkar inda zata kalla ta Tuna da yar”uwanta Dakin da suka yi Rayuwa Tun Lokacin Kuruciyarsu har zuwa Girmansu har bayan auran Sunaira din bata da wajen Rayuwa sai wannan Dakin sau Tari Inna in taji Korafinta Ta dinga Mitan ita bata ko Fitowa ta shaki iskan Duniya alokacin Sunaima baki takan Tura tace”Ni Inna ki kyaleni..Banda Fadan ki na Fama ina ne iskan Allah baya zuwa..!
Alokacin Innan Dakuwa zata aika mata Tana Fadin”Yana zuwa ko”ina ammh ba kamar Waje duk inda ka Ratsa Iska na Hura ka..!
Har yau har gobe dakin nan a yadda yake ita kanta Innan ta kasa amfani Dashi duk da kuwa kaddara ta Dauketa Daga gabansu ta kai ta inda bata Shiryama hakan ba.
Ta isa kofar Dakin Ta Tura kenan Murnanta Daya Dakin yana Bude ne Ba sai tayi wahalan Budewa ba bata da mtsala dan makullin yana saman Window dakin inda ta saba ijiyeshi Tun a shekarun baya.
Ta zura Kafarta Kenan guda Daya tana Shirin Daga Dayan ta shige taji Salatin Inna da kwakwazonta.
Ido ta Runtse aranta tace”Shikenan ta riga ta ganni..!
Dawowa tayi Da baya ta Fasa Shiga Dakin dan Muskutawa tayi kafin tace”Inna mun tashi Lafiya..?na shigo ina ta sallama naji shuru na Dauka ma kina Makewayi ne..?
Tafada Tana Kifta kananan idonta Daga gani bata da gaskiya.
Hararanta Yar Dattajiuwan data Kira da Inna Takeyi Wacce akallah Shekarunta na Haihu bazai gaza 48 ba,Ammh akallon Farko in kayi mata Zaka Shaida mahaifiyar Sunaima ce Saboda Kamarsu kamar an Tsaga kara an yanka,Jikin da Fuskar gabadaya na Inna ne Sunaima ta Dauko,Hatta da yanayin Tsarin Fuskarsu sai dai bambamcin Ita Inna Tana da Haske sosai Domin zamu sakata Layin Farare,Duk da ta kwana Biyu a duniya da kuma Rayuwa ammh Farinta na nan atare da ita.
Inna Rukayyah kenan wanda ya”yanta Harda Mijinta suke kiranta Inna Kowa inna Daga ya”yan Makota har ya”yan yan”uwanta da Dangi Inna Rukayya ya Bace sai dai Inna Kuma Sunaima ce ta Fara yanka mata sunan nan tun Tana karama ta Fara Bude baki da Inna Shiyasa har sunan ya Bita kowa yasanta dashi ba wai domin Tsufanta yakai a Kirata da Inna ba.
Tana Hararanta Tana Tafa Hannu Lokaci Daya Tana Fadin”Sunaima Yaushe zaki hankali ne..?
Sai yaushe zaki fahimci Annabi ya Faku ne ki shiga Taitayinki..?
Tafada Cikin bacin rai Daga ganin Lamarin na Sunaima ya Fara isarta.
Girarta ta sosa Cikin Boye Laifinta Take Fadin”Kai Inna daga zuwa na ni kuma me nayi..!?
“Kaniyarki kikayi..?nace kaniyarki kikayi Mutuniyar banza da Wofi..!
Kullum kina Girma ammh kina kara Cin kasa Sunaima..?Yaushe zaki Zauna Kiyi Tunanin Rayuwar da Allah ya Zaba Miki itace Daidai ki daina Guje Gujen Daga Gidan Mijinki..?Wlh ba domin yaron nan SULAIMAN mai Hakuri ne ba da kuma Darajan Malam da Tuni Wani Labarin akeyi ba wannan ba..!
Tafada Cikin Fada,Fadan da ya riga ya Zama Jikinta Sumaina na kasa bata kara mgana ba sanin ko ta kara cewa wanu abu bazata iya Dakatar da Fadan Inna ba na yau da Safe kaf sai ta juye mata tayi bakan ne Tana Jira mai Ceton nata ya Fito ya kareta ta Samu ta Sulale.
Sai dai kuma yana ciki yana jinsu bai Fito ba karyawa yake yi yana Saurin ya fita yau ya makara Indai Fadan Rukayya ne kan Sunaima sai takai Gobe Tanayi bata gaji ba Shiyasa yayi bakam sai ya gama Shiryan in ya Fito sai ya Shiga mganar domin yasan Fitowarsa kadai Sunaima Take jira.
Mita Inna ta Cigaba da yayi bata gaji ba Ta inda take Shiga bata nan take Fita ba Sunaima ta gaji da Tsayuwa ga Zafi ya isheta yasa ta ijiye jakarta nan kasa ta Kwabe Hijabin Jikinta Fararan Uniform dinta suka bayyana Riga da wando da karamin Hijabi Kan igiyan Dake Tsakar gidan ta karisa ta Rataye Hijabin Kitchen ta Shiga ta Debo Ruwa Daga sanyayyar Randan Inna Ta sha Ruwa sosai ta Sauke Numfashi
Kafin ta Fito tana Sauke ajiyar Zuciya Ta gefen ido ta kalli Inna Dake ta Jifanta da Harara aranta Tayi Dariya tace”Inna..innata inna Sunaira Inna Ahmad..!
Tafada Daidai Lokacin da wani yaro dan kamanin shekara 18,ya shigo Gidan yana sanye da Rigar makaranta Wando kuma na gida ne sai dai Wandon Dake hannunsa na makaranta ne,kana ganinsa kaga Fuskar Sunaima Sai dai shi Yana da dan Jiki kuma bai kaita Haske ba baki ne shi.
Yana shigowa ko Sallama bai yi ba yace”Haba Inna wai don Allah ke da wa kike ta Fada da Sassafan nan..?mutane sai wucewa suke salon ki ja arika cewa Innansu Amadun nan ta Cika Fada ko..?
Yafada Yana Tura bakinsa Inna ta Kallesa ta karkace kai tace”An Dade ba”a ce..Nace an dade ba”a ce ba..Ai kowa ya sani Kan gaskiyata nake..!
Ahmad ya Daga baki yace”Inna ni fa ba Damuwa zan yi ba..kawai Problem din sai an ce Inna su Amadu..Kiduba ki gani da sunana ..!
Bai gama Rufe baki ta Fara neman abun Duka ganin haka yasa ya kwashi Gudu zuwa bayan Sunaima Dake faman Danne Dariyanta Ganin Diramar Inna da Autatanta.
Ganin Inda ya Labe yana leko dakai yasa Inna tace”Baka samu mafaka ba..In ba Hada da yayar taka na Muku Ribiti acikin Gidan ba ku ce ba sunana Rukayyah ba..!
Ahmad ya Daga hannu da Sauri yana Fadin”Wa yace ba sunan ki Rukayyah ba Inna..?wlh sunanki Rukayyah suna mai Dadin sunan Diyar ma”aikacin Allah Annabi muhamnadu Sallalahu Alaiwasallam..!
Suka Karishe mai Hatta Inna Sai da Ta Murmusa Ahmad sai Allah ya Shirrya ya maidata kamar kakarsa.
Sunaima na Danne Dariyan tace”Ka fa makara Ahmad..!
Wandon Hannunsa ya Daga mata yana Fadin”Kinga abunda ya Tsaidani..Sai da nazo sakawa naga ya warware shine na Fita shagon su Auwalu ya takemin na kuma shigo Naji Inna ta Fara Sauke Fadanta na Safe dake..Aini Tun asuba Take neman Saukemin ni da Baba mukayi mata Bakam..!
Yafada yana Dariya Sunaima itama Dariyam tayi batayi mgana ba Ganin Inna ta Kada kai ta koma Cikin Dakin Baba,yasa ta kalli Ahmed Tana Fadin”Kai dai fadi gaskiya ko Dai Mashin din Baba kake son ka hau ya Rage maka Hanya..!
Yana sosa kansa yace”To Antynmu Baba fa sai ya wuce makarantar mu fa zai isa tasu..Shikenan kamar wani Dan Riko sai arika bani kudin adaidaita ai wlh karin girma ne akaga Baba ya Ketoni cikin makaranta ina bayansa ina kara Hura Hanci Dan Headmester guda ai na wuce Raini Antynmu..!
Yadda ya karishe mganar yana Hura Hanci yasa Sunaima yin karamar Dariya Daidai Lokacin da Inna ta Sake Fitowa Bayanta Baba ne ke Biye da ita,Ahmad na ganin Baba ya Fito ya Ruga zuwa Daki yana Fadin”Don Allah Baba ka jirani..Na yau kawai ka Ragemin Hanya..plz..!
Yafada yana shigewa Dakinsa Dake gabda Zauran gidan.
Dukkansu da kallo suka Bisa sanin Halinsa in da Ahmas ya samu Dama Mashin din Baba zai Hamdame ta zama nashi yadda yake son Mashin din ko Baba albarka.
Sunaima na ganin Fitowar Baba ta Sauke Numfashi Rankwafa yayi Tana Fadin”Ina kwana Baba..!
Tafada kanta na kasa Cikin Ladabinta yana gyara zaman Hulan kansa yana kallonta Lokaci Daya yana Fadin”Lafiya kalau Sunaimatu..Uwar Aliyu da zabba”u.Ina fatan kina cikin Koshin Lafiya..?
Yafada yana Cigaba da kallonta Dagowa Tayi tana kallon Fuskar Mahaifin nasu da basu Daukosa ba ko kadan Shi baki ne,sannan yana da Jiki kadan wajensa Ahmed ya gaji Kiba,sai dai yalwar suma awajensa suka Dauko ammh bayan haka komai na Inna suka Dauko.
Dattijone mai Dattako da sanin ya kamata ashekarunsa bai fi Shekara 55 a duniya ba kuma Jikinsa bai wani bayyana Wahala ba shi headmaster ne a wata fimarin gwannati Dake Hayin dan Mani Baba Mutum ne nagari mai yalwata iyalansa Shiyasa ba wanda zai gansu ya Kira musu Wahala.
Sunaima ta amsa ma Baba da cewa”Lafiya kalau baba..!
Inna na gefe batace komai ba wai don bata da abun Fada ba ba”a kawo gabar da Zatayi mganar bane.
Cikin Nazarinta Malam Abdullahi Datti wanda kowa yafi sani da Abdu Datti ya kalli Tilon yarsa yace”Madallah naga Daga wajen aiki kike.ko..?ya wajen shi megidan naki da Ya”yan naki kuma..?fatan duk suna Lafiya..!?
Sunaima kanta na kasa ta maimata Megidanki..!?
Itafa har yanzu gani take komai kamar mafarki tun sanda aka Tabbatar da Daurin auranta ita da Sulaiman gani take kamar Za”a ce mata karya ne ba gaskiya bane.
Kanta na kasa ta amsa mai da Lafiyalau,Kafin ta nemi Gafaran Allah din karya tayimai batasan Halin Dayake Ciki ba ko yana Lafiya ko akasinsa Rabonta da ganinsa kuwa in batayi karya ba tafi Sati Tun Ranar da Wasim bai da Lafiya yana Zazzabin Cikin Dare taje ta Buga Kofar Dakinsa ya Fiti ta shaidamai bata ita ma aka kaisa asibitin ba shi kadai ya Tafi ita Tana Gida Tare da Wafiyya.
Ya’yanta kuwa suna Lafiya domin jiyan da zata fito sai da Magajiya yar aikin da Mahaifiyar Sulaiman Hajiya Zabba”u ta samo musu Daga garinsu KARGI tun Sunaira Tana da Rai ta Musu wayau ta jasu Dakinsu ta Dauke musu hankali da Cartoon kana ta samu Damar tafiya wajen aikinta Saboda tasani Rigima ce kwance in suka ga Tafiyarta Domim Tun Sunaira nada Rai Wasim da Wafiya ya”yanta ne Dukkansu ita ta yayesui sun saba Da ita Fiye da kima kamar kaddara ta sanar dasu Watarana ita Zata zama makwafin Mahaifiyarsu Wajen mahaifinsu dasu kansu din.
Inna ce ta tabe baki kafin tace”Mallam ka Tambayeta da izinin Mijin nata ta Baro asibiti ta biyo nan gidan.?
Mallam Kana sakaci da Halin yarinyar nan fa..Ka duba yau wata nawa da auranta da yaron nan..?ammh bata Taba Natsuwa na Sati Daya agidanta ba Kullum Tana Hanya zuwa nan Gidan Shin baka Sanar da ita nan ba Gidan ta bane Gidanta nachan Inda Akai kaita ba..!
Baba kansa na kasa Kafin ya Dago yana Fadin”Bi mata ahankali Innarsu..!
Inna ta saki baki kafin tace”Kamar Sunaima ce zan mata ahankali..?yarinya ce..?
Baba yace”Ki bar Fadanan hakanan Rukayyah zan mata fada..!
Inna tace”Wlh ka gayamata gaskiya..Ba Domin Mahaifin yaron nan da Maimatarba ba da yanzu Sunaima baki Taka martaban Zama Matar aure ba..Kina sane da yadda Mahaifiyar yaron nan take nuna kiyayyanta Kai tsaye akan yar”uwanki mai Rasuwa bama ke ba Dakewar Sulaiman da kuma Kirkin Sunaira ya jawo mata so cikin Danginsa Inda basu son Bare ya Rabesu,Yau bata agidan Duniya ke kuma kin maye Gurbinta,Domin ki samu Damar kula da ya”yan Data bari kada suyi maraici kinsani kinsan komai Sunaima yadda Mahaifiyar Sulaiman ta nuna adawarta da wannan auran ba Domin Mahaifimsa Dake Tsaye da Kafafunsa ba da Tuni Ta saka ya Sake ki..Ammh kin kasa natsuwa ki zauna ki Rungumi kaddaranki..?Mijin ki ne fa yanzu wanda duka Nauyi da Komai yana kanki ammh kanki Tsaye kike aikata abunda kikiga Dama Sunaima..?kamar ba mace ba kin Sakarma yan aiki Ragamar gidan ki data ya”yan yar”uwarki yanzu in Sunaira ta dawo Duniyar nan taga yadda Kikema Sulaiman da ya’yanta Rikon Sakainar kashi Zata yafe miki..?
Nace Zata kalleki da idon Rahama da Salama!?
Ko Kafin Inna Ta gama mganarta Gaban Rigar Sunaima ya gama Jikewa da Hawaye kuka take sosai wanda bai da Sauti Kukan Tunawa da abubuwa Dadama Cikin Rayuwarta.
Gabadaya su Inna sunki su gane abunda Take so ta ganar dasu ne,Kwata Kwata da ita da Sulaiman basu Dace da juna ba akwai Tarin Tazara mai yawa a tsakaninsu in Sunaira ta Dace dashi ai ko A Hallita suna da bambamci Sunaira mai Hakuri ce mai kawaici mai Rama Alheri da Sharri mai Raunin zuciya da Soyayyace Sunaira tana da Kirki da Budaddiyar zuciyar da ta saka Dangin Sulaiman suka Fara Ragamata saboda Darajan soyayyar Mijinta da Kirkinta da ya”yan da suka Fara Tarawa.
Sunaira da Sulaiman sun dace a mataayim ma”aurata ammah ita bata Dace dashi ba Zuciyarsu da Ra”ayinsu ba Daya bane
Tun yana auran Sunaira basu da wani Alaqa mai kyau ita dashi Tana masa kallon mai Baudewar Hali shima yana mata kallon mace mai Girman kai da Son Girma Su Inna wai sun manta ne Shekarunta kusan dayaa dashi?Taya ya ZAta Iya zama da wanda take mai kallon kamar kaninta amtsayin miji..?Mijin kanwarta masu soyuwa gareta da sukayi zaman soyayyah da ita kanta Shaida ce?ai ba karya Mahaifiyarsa Tayi ba da ta tako gidan nan anan wajen ta Kirata da Tsohuwa bayan Labarin Daurin auranta da Danta Sulaiman yaje mata ai batayi karya ba Ni din Tsohuwa ce ga Dan”ta Kamar akwai kwaruwa acikin Lamarin Bai dace ta zama matarsa ba ya Dace ace ya samu Daidai dashi itama ta samu Daidaita da ita Tsoho kamarta kamar yadda Mahaifiyarsa tace su kasa ganewa shi kanshi baya Bukatarta a Rayuwarsa kunya ce yake ji yasa bai Taba Daga ido ya Fada musu ba ammh bai Taba Damuwa da Wanzuwarta da Rashinta acikin Gidan nasa ba abu Daya ya sani Ya”yansa sune kadai abunda yake Damuwa dashi Bayan aikinsa ammh ita kanta ta sani bata Chanchanta ba,in Saboda su Wasim ne da su Baba basu yanke wannan Hukuncin ba sun barta Tayi Zamanta agida Allah barshi sai wasim din su dawo wajenta da Zama ta yarda ta amince Zata Rikesu har Karshen Rayuwarta bata gaji ba..!
Kuka take sosai wannan karon har Sautinta na Fitowa Cikin Dashashiyar Muryanta Take Fadin”Mutuwa ce..Mutuwa ce ta jani Cikin Wannan kaddaran Inna..Kaddaran da ban Shiryamata ba..Ni zuciyata ba irin ta Sunaira bace mai afuwa da Ramgwame ina da Taurin Zuciyar da bazan iya Juran hakan ba..!
Kukanta yaci Karfinta da yasa ta Mike Ta Dauki Jakarta Zata shiga Dakin Baba ya saka baki ya Kira sunanta ta Juyo Idanuwanta na Zubar da kwallar Kwallar Tunawa da yadda Mutuwa ta Dauke Sunaira da yadda Kaddaranta ta fara daga Lokacin
Cikin Taushinsa yace”Yaushe zaki koma Gidanki Sunaima..!?
Kanta na kasa tace”In su Wasim sun tashi daga makaranta zan Biya na Dauke su dagachan zan wuce…bazan kara Dawowa Gidan nan ba Inna da Baba sai in har Bukatan hakan Tataso..Kiyi hakuri Inna..!
Daga haka ta juya ta shige Dakin da Gudu Tana sakin kukanta asarari.
Baba ya kalli Inna itama ta kallesa Gabadayansu Rauninsu ya bayyana Eh mana Har abada ba wanda zai manta da wannan Raunin Raunin Rasa Sunaira acikin wannan ahalin.
Wucewa kawai yayi yana Fadin”Sai na dawo..!
Inna daga saman lebe ta amsa mai Tana Kauda kanta kada yaga Taruwan Hawayenta Ahmad dake tsaye tun Dazu Shima Kwallar ya Dauke yana Fadin”Shikenan Inna itama Antyn tamu bazata kara zuwa ba sai an Dade kenan..?
Wani kallo Tayi mai dayasa ya saba Jakar makarantarsa ya fice yana Fadin”Bye Inna..Bye Antynmu Allah ya Huci Zuciyarki..!
Haka ya fice yana Fada jin Baba har ya Tada mashin dinsa ba karamin aikin Baba bane ya tafi ya barsa yasa ya Fice da Gudu Tsausayin Anty Sunaima Dankare acikin Ransa shi bai ga aibun Sulaiman ba Baisan wani Tunani Anty Sunaima take yi da zata Tuna Tarin kyautatawar Sulaiman garesu Tun Anty Sunaira nada rai har bayan kasa ta Rufe idonta da bata Tsaya Tana faman jeka ka dawo ba Ita da Allah ba yabama Dami a kala Tsuntsu sama Gashassshe.
Inna Garin kofar Dakin Baba ta Dafe Lokaci Daya tana kokuwa da Numfashinta har aka gama Zaman makokin Rasuwar Sunaira batayi kukan Sarari ba sai dai na zucci..Ammh Lokaci bayan Lokacin in abun ya Ciwota haka zata shige Daki Tayi ta kuka Allah Sarki Sunaira Allah ya kyautata makwannciki..Allah ya bama yar”uwarki zuciyar Daukan wannan Kaddaran nata Nasani akwai Watan watarana da Sunaima Zata Godema kaddaran data Ratso Sulaiman MIJIN KANWARTA cikin Rayuwarta Akwai Ranar na zuwa da Zata Gode musu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button