MATSAYINAH COMPLTE NOVEL

[5/16, 2:48 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)….
2…
A haka labaran yau ya tashi,zuciyata ta gaza nutsuwa har barci ya gagari idanuna sai na bige da tashin dare na rasa dalili na tsiri gayawa Allah cewa ya taimaka babyn da ake rikici kanta ta dawo gareni,haka kawai tsabar son zuciya nakejin cewa dani ta dace mu zauna in kula da rayuwarta,ni ko biya na za’a rikayi ana daukata aikinta zan amince in zama God mother dinta… Yau kam kotun a cike take da Al-umma duk an hallara ana son a jin yanda zata kaya,ni da nake gaban tv na kara masa sauti yayin da kirjina ke bugawa,ana nan anata fafatawa,haj ni’ima tana nan kan bakanta yayin da madam Zarah itama ke kan bakanta dayansu bashi da niyar janyewa, madam Zara ta gaya wa wakilin daukan labarai cewa itama a asibitin dutsen ta haihu daidai da lokacin da haj Ni’ima tace ta haifi babyn da ake rikici kanta kenan,nima lokacin d same tym and date na haifi tawa diyar da Allah ya kar6i kyautarsa,ta ci gaba da cewa saidai ni sanda na tashi naga tawa babyn matacciya natada hankali har numfashina na Neman daukewa,wannan dalilin be ya sanya suka min allurar barci, ko da na tashi ban ga babyn tawa ba sai aka ce mani an birneta tunda bani da kowa, babu gawa babu alamun an rufetan kaman yanda aka gaya mani, na tsananta bincike kan wannan lamarin, nurse on duty Sister Kaulah ce na maka ta a kotu, satin gurfana a kotu daya zagayo sai aka nemeta aka rasa,har zuwa yau din nan da ake wannan muhawaran ba ita ba labarinta,to ke don me kike kyautata zaton babyn ki ce?Saboda duk mai hankali idan ya kalli Ni’ima zai fahimci cewa ta wuce haihuwa,ni a bani dama kawai muyi DNA, Alkali ya buga gudumarsa kotu ta tashi kara sai sati na sama, haka wannan shima ya tashi…
Yau babu wuta dalilin matsalar da nepa ta samu gashi generaton gidan katuwace ta samu matsala ana kan gyarata,wannan ne ma yasani shigewa gidan mummyn Yusra(daya daga cikin mai kawo min babies idn zasu aiki,a can aka dasa daga inda aka tsaya) yau fada sosai ta barke tsakanin mata 2, ita madam Zara na bukatan a bata baby tayi DNA haj Ni’ima kuma ta rike ‘ya gam wai bazata bayar ba,’yarta ba inda za’a kaita,sai da kotu ta tashi aka daga kara sannan na samu natsuwa,nayi mata godiya na koma gida…
Jaridar daily trust na the following day shi ya ci gaba daga inda aka tsaya a labaran jiya,sub heading din ya kasance KAKA kARA KAKA,’yar watanni shida da zaratan matayen nan 2 ke rikici kanta,na maida hankali gurin ganin yanda zata kaya,gwamnati ta shigo cikin wannan lamarin,da sauri na mike tamkar an tsikareni,….. Gwamnatin tarayya ta Abuja ta kar6i diyar nan da rayuwarta ke cikin rikici,daga rana irin ta yau zuwa ranar da zata binciko gaskiyar lamari babyn da ta rada wa suna Hameedah zata kasance karkashin kulawarta da ikonta har sai ranar da gaskiya ta bayyana kanta… A sanyaye na rufe shafin ina girgiza kai,cab da sauran aiki tamkar wasa karamar magana ta zama babba.
dani ta dace mu zauna in kula da rayuwarta,ni ko biya na za’a rikayi ana daukata aikinta zan amince in zama God mother dinta… Yau kam kotun a cike take da Al-umma duk an hallara ana son a jin yanda zata kaya,ni da nake gaban tv na kara masa sauti yayin da kirjina ke bugawa,ana nan anata fafatawa,haj ni’ima tana nan kan bakanta yayin da madam Zarah itama ke kan bakanta dayansu bashi da niyar janyewa,madam Zara ta gaya wa wakilin daukan labarai cewa itama a asibitin dutsen ta haihu daidai da lokacin da haj Ni’ima tace ta haifi babyn da ake rikici kanta kenan,nima lokacin d same tym and date na haifi tawa diyar da Allah ya kar6i kyautarsa,ta ci gaba da cewa saidai ni sanda na tashi naga tawa babyn matacciya natada hankali har numfashina na Neman daukewa,wannan dalilin be ya sanya suka min allurar barci,ko da na tashi ban ga babyn tawa ba sai aka ce mani an birneta tunda bani da kowa,babu gawa babu alamun an rufetan kaman yanda aka gaya mani,na tsananta bincike kan wannan lamarin,nurse on duty Sister Kaulah ce na maka ta a kotu,satin gurfana a kotu daya zagayo sai aka nemeta aka rasa,har zuwa yau din nan da ake wannan muhawaran ba ita ba labarinta,to ke don me kike kyautata zaton babyn ki ce?Saboda duk mai hankali idan ya kalli Ni’ima zai fahimci cewa ta wuce haihuwa,ni a bani dama kawai muyi DNA, Alkali ya buga gudumarsa kotu ta tashi kara sai sati na sama, haka wannan shima ya tashi…Yau tun da garin Allah ta’ala ya waye ayyuka suka rinca6e mani kasancewar litinin ne, a kullum kuma yaran da nake raino kara yawa suke tamkar ni kadai ce mai kula da su a gidan,tun da gwamnati ta kar6i case din ba’a kara wani hira kan batun ba,wannan nema ya sanyani fidda rai na mika wa Allah lamurana gaba daya,ya na iya? Fadan da yafi karfinka sai ka maidashi wasa ai,da yamma liss iyaye suna ta zuwa tafiya da yaran su, sa6anin Abduljabbar da har zuwa lokacin shiru babu mama Kulu babu labarinta, ni ma na kosa tazo ta tafi da shi kar yayi min barci tunda dare ya fara yi, nayita kiran layinta amma shiru, daga bisanni na dauro alwalla na tayar da sallar magaruba yaron nata wasan sa, ana ta kiran sallar isha na sa6ashi a kafadata sannan na kai daki na kwantar don yayi barci abinshi,har zan kulle gida sai ga amon muryarta tana ta kwararo sallama,nayi ajiyar zuciya don ba abin da zuciyata bata saka mani ba game da rashin zuwanta,muka gaisa ta shigo ta fada kan kujerar reception din gurin tana mayar da numfashi,yaya dai ummu Abdujabbar? Ta ja tsaki sannan ta soma fadin na gaji Rahma pls inda ruwa bani tukun in sha yanda zan yi tuki zuwa gida a wannan lokacin shine damuwata,na kawo ta shanye tas sannan ta ci gaba da cewa kinsan daddyn Abdul na cikin yan house of assembly?na daga kai ina fadinhakane,ita kuma minister ce na ilimi,naji tana fadin muna can muna tattauna batun baby Hameedah da yanda zamuyi da ita,na dafe kirji ina zaro idanu,na yarda da nagartanki don haka mun yanke shawarar zamanta a nan gidan marayun(da yake ta manyace)don ba’a yarda ta zauna gidan kowa ba,za’a kawota gareki ki kula da ita kafin mu san abin yi,nayi murmushi sannan na dauko boy dinta sai da na rakata naga fitansu daga harabar gidan cike da farin ciki mara misaltuwa, lallai Allah ba azalumin bawansa bane.Ranar Na kwana da doki mara misaltuwa,ina ta yiwa Allah godiya da ya dubi zuciyata ya bani Hameedah ba don wayona ko don isata ba sai don karfin Mulkinsa,na jima zaune ina kallon agogo cike da zulumi,duk na kosa gari ya waye,har ban san sanda barci ya dauke ni ba… Yusra nake gyara wa diper sanda na tsinkayi jiniya da isowan ayarin motocin kusoshin kasa cikin gidan marayun,na tsinci kaina da lekan tagata don ganin ko su waye suka shigo don tunda na fara aiki a gurin ban ta6a ji ko ganin irin haka ba,mama kulu ce a gaba(ummu Abdujabbar) sai wata ‘yar gayu mai dauke da kwandon da nake zaton babies ake sawa a ciki kasancewar na hango kayan sanyin jarirai a ciki da alama babyn na ciki,daya bayan daya naga suna saukowa tamkar zasu cika mana gida,na koma na zauna ina saka abubuwa da dama cikin raina,wayanda ban ta6a gani a zahiri ba sai a tv ranar sanadin babyna Hameedah ‘yar albarka nayi tozali dasu,ba jimawa na ji ana kwankwasa mani kofa,da sasarfa na karasa na bude Abdujabbar da ke wasa ya tafi da saurinsa ya rungume ummansa,suka karaso ciki ba dukansuba,a yanda naga yawansu sauran suna waje,aka mikomin kwandon babyn gami da cewa daga yau hammy ta dawo karkasin kulawarki Rahma,na karkata kai don ganin mai wannan lafazin,gogagiyar ‘yar boko zan iya kiranta,daya daga cikin masu kananan shekaru a gwamnati,ta gyara zaman glass dinta daya taimaka gurin kawaita adonta sannan ta ci gaba da cewa bama bukatan wani yasan da zamanta sai mun 6illo wa lamarin tukun(mata ce ga ministan defence)idan da abin da kike bukata na kulawarta u let me know cewar mijinta,na gyada kai kawai don na gaza furta wata kalma,shigowan lawyan su ne ya sanyamu yin shiru yayin da kallo ya koma kansa,akwai kaya a boot zamu sauke sai ki fadi inda zasu zuba maki,basu wani jima ba bayan direbobin sun loda su nan,diper,da dai sauran tarkacen hameedah a store kwali kwali sannan suka soma tafiya,a takaice wannan shine mafarin haduwarmu dake, bazan taba mance wannan ranar ba,kuma bana kaunar abin da zai shiga tsakanin mu, tun daga ranar na daukaka kuma kece sila,ina dawainiya da ke tamkar ni na haifeki,haka nan nakanji kaunarki tana ratsa mani jiki,jijiya ,jini da bargo,har bana fatan rabuwarmu tazo tunda duk randa gaskiya ta tabbatar da dayan su a matsayin mahaifiyarki dole ta kwace mani ke,kin taso cikin gata,kulawa da tattali masu dama daga hannun gwamnati kuma ba’a kuma jin duriyan zaratan matayen nan ba,ana zaton ma ita madan Zara bata da miji a yawon shan iskanta ta samo cikin da take ikirarin ke ta haifo,da sauri na kalli fatata mai haske da kyalli saboda zargin furucin mummyna,na fashe da kuka mai tsanani,its ok yanzun me na kuka? Kila fa itace mamata kuma bata da miji na tabbata shegiya kenan dama ga kalat irin ta halfcast ni na ma san hakan ne bani da…. Da sauri ta rufen baki tana girgiza kai,ta sharen hawaye sannan ta ci gaba da fadin shakuwa da sabo mai yawa ta wanzu tsakanina da ke,tare muke kwana mu tashi tare,cikin yaran da na yi rainonsu ke din special ce,har kika yi wayon da za’a saki a makaranta,ita kanta sch din da kikayi ta kudi ce, direban ki kuma security ne tare muke kaiki in bishi kuma mu daukoki tare,lokaci lokaci ‘yan house kan zo dubaki a matsayin amana da aka bani…
Kina da shekaru 5 a duniya gwamnati ta kira zaratan matayen nan don tattaunawa wa da su,Wannan karan yanda kikasan jarida jira take har an rattaba hotunan su da jawabi dalla dalla,amma babu naki sai dai komai kyaji ance baby hameedah,ba wanda yake da labarin inda aka maidaki amma an san dai govt ce ta kar6eki aka maki lakani da ‘yar govt,ba dama a samu hotonki saidai yan bani na iya har sun kididige yawan shekarunki da duk wani bayani daya shafeki,har asibitin akaje akayi bincike ranar ma’aikatan sun sha wahala,duk wayanda suka haihu ranar da aka haifeki saida aka fito da files dinsu,gaskiya ta nuna cewa dukaninsu 2 sun haihu d same tym sai dai tsiran ‘yan mintina kadan,sannan har da Weight din babies da komai gasu nan ba karya,basira ta kare wa lauyan,sai aka koma kan likitoci da nurses on duty,Doctor Mu’azam Azumi ke da dutyn ranar da yake yamma ce kuma shekaransa daya da cikawa,ko da aka gangaro kan nurses su uku ne ranar a 6angaren haihuwa,kuma dutyn yamma,sister Kaulah kam ba’a kuma ganinta ko jin labarintaba(ta gudu bata kasar)Sister Mariyah ta samu transfer zuwa delta don aiki ya kai mijinta can,sai aka dauki adress dinta,sai na ukunsu sister Jane ce ita kuma girma ya kamata ta bar aiki har ta koma garinsu(Ekete ekpene), haka wahalhalun suka kasance,Kaulah ce dai bata bar aiki ba bata yi transfer ba bata mutu ba amma ba mai labarinta,sauran 2 aka tura mai bincikosu babu wani labarin da ya danganceki,an bincika Kaulah ma kafin daga baya aka samu labari gurin makociyarta wai ta bar kasan saidai bata san wace kasa taje ba,itama a bakin yaran ta taji wai zasu turai…
[5/16, 2:48 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
3…
Mummy to D N A fa? Na fadi ina kallonta,ta sada kai kasa sannan ta ci gaba da cewa bani da iko a kanki sai abin da aka shardanta mani,ko da na daukeki nima ai ba haka aka bar ni ba,suna sane da duk abin da na maki,aka kara daga case zuwa wani lokaci don an baza masu nemo Sis Kaulah saboda tabbatar da gaskiyan alamari ita kadai ke iya warware wannan dabaibayin da aka maki,gudun da tayi ya tabbatar da cewa akwai sa hannunta cikin lamarin, gashi an kasa kawo karshen wannan rikicin sai kace dada rura wutan ake, duk ran da suka hadu sai sun raba hali,bazan mance ranar da suka tashi hankulansu a kotu ba alkali ya daga karar,hajiya ni’ima ta bigi kirji tana fadin ko ba komai govt na kula da babyna cewan , babyn ki kuma,a gidan uban wa ta zama babyn naki? wannan shina furucin madam Zarah, Suka soma cece kuce,guri ya hargitse da hayaniya,audience nayi suma, alkali ya buga gudumarsa sanan ya tashi karan ta hanyar cewa kara bazata daukaka ba sai Kaulah ta bayyana,in kuma mutuwarta kenan hakan yana nufin dukanin ku 2 kun rasa babyn ,jama’a suka firfita ana ta yada labaran ni da nake gida na jinjina kaina,wannan yana nufin ba’a san ranar da rikicin zai kare ba,tirkashi…
An yi hutu mai nisan zango ni da ke muka bar kasar daga sch aka turaki (turkish), ni ma aka biyamin kujera don kula dake daga govt kenan,a can muka kasance har saida kuka koma sch sannan muka dawo naija,da an shawarci ministan tsaro ko za’a barki a kasar waje ne,amma ya ce gara ki zauna cikin kasar tunda ba’a ganeki,kin zama ‘yar gata mai ‘yanci kamar kowa.
Last week da misalin karfe hudu na idar da la’asar ina azkar, na tsinkayi diran motar mama kulu,da yake bata cika zama ba,yanzun mijinta na rike mukamin ambassador na naija a US,a kagauce ta zo min da batun Kaulah tana gari, dauki ya sanya har ban san sanda na mike zunbur ba,ta kasa zama sai labarta min take,lokacin kin fita saloon,wai a border aka kamata ta dawo daga ghana, danta ne ya rasu da gawarsa ta dawo don birneshi, na jinjina kai,tab abin duniya baya 6uya,to shine fa har matayen nan suka hada kai wai za’a ci gaba daga inda aka tsaya, Kaulah kam bata cikin hayyacinta sam abin duniya ya sanyata gaba, babu yayi mata yawa,duk ta lalace ni dana ganta sai da na tuna lokacin haihuwata ita ta kula dani,sai ranar na san ashe itace Kaulahan… Jaridu kam da suka baza gari na labarin an shigar da kara ne wannan karan gvt ne suka nemi a sanya hotanki don gaskata lamarin, ba karya bane,ba kage bane ba mafarki kikeyi ba babyna daz d truth,na rike hannayenta 2 ina zubar da kwallah kimin alfarma plssss zan samu? Tayi yake da hausawa kance yafi kuka ciwo sannan ta soma fadin fadi In Shaa Allahu kin wuce tsammaninki a nan ta fadi tana nuna zuciyarta,ke na za6a ki zame mani uwa,don Allah ki shigo kema kice ni babynki ce,ta waro idanu tana zarosu,hameeeeeedah! Wallahi kinji na rantse ba wace zan bi cikinsu, karfin hali 6arawo da sallama,hw does it sound for d past 15yrs ake rikicin nan ni nayi rainon ki duk ban ce ‘yata ce ba sai yau rana daya in bigi kirji ince baby na ce? Waye zai yarda da hakan? impossible dear,mummy amma dai kinsan ina sonki ko? nayi mata tambayar ina karya wuya yayin da idanuna suka kawo kwalla,ta tsira Mani idanu cikin nazarin abin da bazance gashi ba,I luv u more baby cewarta tana murmushin karfafa Mani gwiwa.
Na dan ja jikina sannan na koma nayi lamo a cinyarta ina kiyasta ragowan kwanakin da suka rage a koma kotun kila nan da wata daya kawai suka rage mani tare da ita(mummy Rahma), naji an dafa mani baya sannan ta ci gaba da cewa babyna u need 2 understand bamu ke zaban iyayenmu da ‘ya’yanmu ba,Allah ke da ikon za6a mana wayanda zamu haifa da wayanda suka haifemu,na share majinan da ke min yawo tamkar fanfo sannan na soma fadin daga yau na gama karatun,what? Haba mummy ya zan yi kinga fa idan na fita sai ayita nunani ana jefa maganganu kaina,hakan na jefa zuciyata cikin rudani,mummy ke kadai na sani all dis while ban ta6a tunanin hakan zata kasance gareni ba,kinga idan shari’a ta ki ci taki cinyewa sai Alkali ya sanya huka ya rabani 2 daidai kowa ya dauki rabonsa tunda haka suka za6i su susutani, wasu ma har suna cewa ni shegiyace tuna mata ke fada kaina babu namijin daya fito yace ni diyarsa ce(mijin matayen) ,na tabbata najasa ‘yar gaba da fatiha,na rushe da kuka mai raunana zukatan masu sauraro,shi kenan dalilan naki? Na gyada kaina ina ajiyar zuciya, kamal ma yace baya yi dani ba zai yi wa ‘ya’yansa shegiyar uwa ba,Junaid kam inda nake ya daina dosa sam bai kaunar ganina, dama ba sonki suke ba sharesu, kuma sch yanzun kika fara zuwa, zaki rika 6adakama yayin fita don masu kallonki baza su ganeki ba,dukanin su babu sa’an aurenki cikinsu,ta sumbaci goshina gami da cewa Allah yayi maki albarka babyna, har zata mike, da sauri na riko gefan rigarta, ta zuba mani idanu tana kallona, kiyi mani alkawarin ba zaki ta6a rabuwa dani ba sai mutuwa,ta murmusa sannan naji tana cewa udan nayi zaki saki ranki? Na gyada kaina, Ok naji na dauka,da sauri na rungumeta, na dauka baby,muna tare in shaa Allah har abada kinji?nayi murmushin daya nuna gamsuwata,Sannan ta karasa ta kwaso mani abincin tana fadin zo to ki dan ta6a kar ki zauna da yunwa, dadinta ma gobe zaku fara Waec kema ki dan huta kafin jami’a ko? Na yi sakototo ina kallonta amma ban tanka ba, zuciya ta a hargitse na tsinceta,wayarta dake ringing ta daga Ok gani nan itace furucincin da naji sannan ta katse layin tana kallona, kar ki bari su fahimci cewa kinsan komai game da asalinki ba a ce in gaya maki ba, na gyada kai sannan ta mike ta fice,ina nan zaune ina wasa da abincin,sai juya cokalin nake a plate din garnished spaghetti mai yalwan sinadari ga kulan farfesun kayan ciki, gefe guda pizza ce sai coslow ga drinks hadin gida,amma duk wannan bai dauki hankalina ba,na ja dan guntun tsaki gami da mikewa kai tsaye toilet na nufa na dauro alwalla don jin kiran sallar dake tashi cikin masallacin unguwar…
Kafafu sun dauke yayin da zukatan jama’a ke hutawa kasancewar dare ne amma na kasa runtsawa sai kosawa da nayi inga gari ya waye,a hankali aka turo kofan gami dayin sallama, na daga kaina ina kallonta, ta karaso ta kunna wutan dakin da yake dim light na bari a kunne,sannan tayi ma kanta mazauni a gefan katifata, kina zafafa lamarin nan baby why? Bari in baki labari ko? Na jinjina kai sannan na kafeta da idanu ina sauraronta, labarin shirmena ina yariya tare da na babies din data yi raino har bansan sanda na rika dariya ina rike ciki ba,ban son dariya irin haka kar ta illataki, na cusa handkerchief a baki ina fadin na daina, rigimata da Abdujabbar da take fadi ya sanyani dada fashewa da dariya, da sauri naga ta mike zata fita na bita da gudu ina fadin Allah na daina, no yi barci sai gobe sai in karasa maki ko? Ta sanyani na kwanta sannan ta lulu6eni tana tofeni da addu’ar da ta saba kaman ko yaushe ,sai da ta ga na runtse idanu sannan ta kashe fitilar ta fice, zuciyata cike da annashuwa har bansan sanda barcin yayi gaba dani ba…
Na idar da sallar asuba madadin in mike don shirya wa sch sai na 6ige da dauko album dina ina kallon hotunan mu tun yarintata zuwa sanda na dan tasa tare da mummy Rahma,komai na dawo mani cikin kwanyata tamkar yanzun akeyi, nakanji tamkar ni kadai ce nayi sa’ar uwa a duniya, amma duka wannan ace acting mummy ce? Na ja tsaki gami da cewa Allah basu isa ba, sahunta da naji ya sanyani saurin turashi karkashin pilo sannan nayi lamo tamkar mai barci,ta ja kafata tana min cakulkuli, ina kyalkyala dariya na mike oya maza ki shiga na tara maki ruwan wanka a jakuzi, kamin in fito har ta shirya min uniform dina, na tsaya gyara gashina ta kuma shigowa tana fadin shiriritar ki tayi yawa,ta miko min cup mai dauke da tea sai tray din wainar kwai da chips,maza cinye,ina kiciniyar sanya safa ta kar6e tana sanya min sannan na soma cin abincin, ta sanya min sandal tana kallon agogo,kinyi latti yau ni na rasa irinki sai shagwaban tsiya,kalli tym fa? Ina jiyo horn a kofar gida muka mike gaba daya tana rike da jakar makaranta ta a haka muka fice, direba na ne tare da wani dan taxi ,ta daura min nikab tanai min bayanin su, daga yau shi zai rika kaiki tunda an gane direbanki, ba ruwanki da furucin mutane ki kama kanki baby nasan ki da daukan magana kin ji ko? Na gyada kai ina goya jakata, tana tsaye har na 6ace wa ganinta,shin idan muka rabu wa zai min haka? Rayuwata sai da ke mummy na ayyana hakan a raina daidai sanda muka karasa bakin gate, na cire niqab din sannan na shige da sauri kamin a ankara da ni a gurin…
Mun fio daga chemistry praticals na wuce sch shop a can na sayi malt da crackers ina danci duk sai naji babu dadi don ban saba ba yau latti ya hanani tahowa da abinci, ashe ke shegiyace,da sauri na daga idanu don ganin mai wannan furucin, Maidah ce itama maiji da kanta, nayi murmushin keta sannan na ce oh yes har yanzun ubanki da yayi cikina be san darajata ba,a harzuke ta yi niyar yafito ni da sauri na kauce ina dariya, kika sake wannan kazamin hannun naki ya ta6ani sai na dai daitaki na fadi sannan nayi gaba na barta nan tana min kallon tsana, jama’a har sun dan soma taruwa a gurin magulmata anzo jin ba’asi, na 6ace gudun kar in tsaya fada zancen ya koma kunnan mummyna tunda ta riga ta nuna bata son hakan, a class ma zancen bai sauya zani ba, saidai ba kasafai nake biye masu ba, ni kam bani da shakikiya komai nawa mummy nake gaya mawa ni da ‘yan ajinmu sai kallo ko gaisuwa kawai, shi yasa ake mini kallon mai dagawa da takamar tsiya, wannan ne ya haifar da tsana har ya sanya suke yi dani,ina nan zaune har lokacin tashi ya kusa sai ga matar ministan tsaro da lauyanta sun iso, bayanta mijintane da security mai take masu baya, daga gefe kuma shugaban makarantarmu ne da alama ni suke nema, ai kuwa sai gashi yana kiran Hameedah Abdullah (da yake da sunan mijin mummy nake using, Abdullahi Buba), na mike na same su a waje, muka dan ke6e bayan mun gaisa ne ta dan dafa kafadata sannan naji tana fadin kiyi hakuri da halin da kika tsinci kanki kinji preety gal? Na gyada kai ina murmushi, Barista Muhsin gata nan, na maida kallona kan lawyern daidai sanda ya zare glass din idanun sa yana kare mini kallo , sannan ya kada kai gami da kallon agogon hannunsa, mijin ta me fadin ko dai DNA za’a yi ne? Lawyern ya amsa da cewa tukunna dai ni nafi son a tsare Kaulah har sai ta fadi yanda akayi mataye 2 ke fada kan baby daya, idan da saka hannunta kaga gaba masu irin halinta sai su kiyaye, because i would use her as an escape goat cewar ministan tsaro ,muna nan tsaye suna tattaunawa sai ga isowan mama Kulu tare da Abdujabbar ya zama big boy abinshi, tamkar ba tare mukayi yarintar mu ba,ya tsaya a jijkin mota yana jiran ta yayin da ta karaso garemu, kai Fareedah baki da kyau madadin ku jirani, ta tsoma baki cikin maganar nima naso ayi DNA din tun farko amma hakan bazai kawo karshen rikici ba ina suspecting da makarkashiya cikin lamarin, wannan dalilin ne kawai zai karfafa mana gwiwan neman kaulah ta gaya mana yaushe ta fara wannan aikin kuma mutane nawa ta aikata mawa? Hakane kuma, cewar barista Muhsin din, hammy u can go back 2 class cewan matar da naji an kira fareedah, ni kam a sanyaye naji ni ko me dalili? Na juya ga Abduljabbar din dake daga mani hannu fuskarsa dauke da fara’a, nima na daga masa sannan na koma class yayin da abubuwa da dama ke mani yawo a ka, yan aji suka watso mani idanu tamkar zasu cinye ni, ni kam ko a jikina naji wata tana fadin har gata yayi mata yawa, kai dama nice inji wata, dole ai ta rika tsula tsiyarta yarinya sai izzar jaraba, na kwashe da dariya amma ban tanka ba.
Ko da aka tashi ban tsaya bata lokaci ba na karasa inda sabon direbana ke jirana, duk na kosa in karasa gida saboda kewan mummy ya dameni, da niqab dina a fuska muka dau hanya…
Hira mukayi sosai, na labarta mata yanda mukayi a sch tana tayani fira tamkar kawata, idan kika gani da mummy muna harkokin mu zaki yi zaton ya da kanwa ne, mummy iron matayen nan be yan dagwas masu karamin jiki, kyayawa ce ba karya kuma tasan sirrin gayu ga iya daukan wanka, yqnzun haka tana da shekaru 31 amma Idan kika ganta bazaki kawo hakan ba,tare muke yin komai namu, na tsira mata idanu ina murmushi, wannan kallon fa? ta mani tambayar tana murguda min baki,na girgiza kai ina kunshe dariyar dake cina,oya talk,kin min kyau ne, like seriously cewarta tana daga min gira, na rufe bakina da tafin hannu ina dariya, ai kam ta hau min cakulkuli tana fadin sai kin fada,mummy wait, ta dakatar tana tsareni da idanu, mummy ke fa karama ce,ta zaro idanu tana girgiza kai,sannan ta soma fadin shi yasa abokan mijin su mama kulu da hajiya farida suka matsa min ko? na bata rai gami da gyara zama na ina turo baki, me kuma? Ni fa samudawan nan haushi suke bani, baby zaurawan nawa kike kira haka? nayi raurau da idanu yayin da nake fadin i cn feel it within me that some days he will be with u again,i will see him and cherish those moments, a sanyaye tasaki dariyar yake,hmmm hameedah,dnt give me hopes don Allah,zo nan ki gaya min dawa za’a yi baby? Abdujabbar din ne? Kai! Mummy ya min yaro ni dai na karasa maganar ina juyi, iyyyyye ‘yar caras dagwas to wani multi biloniyan ne ya samu wannan matsayin, kai mummy kina bani kunya na karasa ina rufe fuskata, ni dai bazan auri mai kudi ba mai rufin asiri nakeso wanda yasan darajata, naji tana tafi tamkar a filin muhawara, waya karanta maki wannan har kika yi hadda? Bani da kawa sai ke kila a bakin ki naji ko hakan nan kurun suka zo min, gud ,Allah ya nuna min wannan rana babyna, cikin tsigar tsokana ta fadi ina dariya da gudu na fada dakinta na barta a gurin ta ci gaba da kallon film din da ake haskawa a zee aflam…
Jin shiru mummy bata fito bane ya bani daman nokin office din dentist din(likitan hakori), come in cewar ta na tura kofa na shige dauke da jakar hannunta, sorry baby kin kosa ko? Ta fadi tana kallona daidai sanda ake kokarin wanke mata hakorin, zauna nan cewar matar,naja kujera nayi wa kaina mazauni,lokaci lokaci takan dan kalleni sannan inga ta maida hankali kan aikinta da yake dana shiga na daga niqab dina, mun mike zamu tafi mummy na gyaran dankunnena da zai fadi naji tana fadin madam pls is she ur younger sister? No, inji mummy,wounderful i just admire u,a daughter i guess? mummy dai murmushi kawai take ba amsa, she looks like a sister, muka dau hanyar fita muna hira a hanya, mummy kinji ba? Mutane suyi ta cewa wai ni kanwarki ce ko kafin fitowan jaridun nan ran da kika rakani sch ina ss 1 haka magulmatan sukaita son sanin ko ke wacece dina, wata har cewa tayi kila yayatace dake aure nake zaune a gurinta, shiru ya biyo bayan wannan furucin, wucewar mintina 2 na tsinkayi muryarta tana fadin nayi auren wuri shi yasa, ina da shekaru 12 aka aurar dani, shekaruna 16 na haifi babyna da take daidai da ke,yau gashi har shekaru goma sha biyar da rasuwanta,Allah ya jikanta na fadi duk sai naji babu dadi,dama nice babyn ina zan kai murna?
[5/16, 2:48 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
4…
Yau muke last paper zuwa wannan lokacin babu batun kotu an daga wa Kaulah kafa kasancewanr ta samu kanta cikin tsanani na rayuwa, tun dawowarta naija ba’a samu kanta ba, yau daban gobe kuma sai matsalar tafi ta ko yaushe tsanani, bayan birne danta aka bata gado jikin yayi tsanani ba wasa ba,fatan jama’a ta warke a dasa daga inda aka tsaya, ni kam har kullum idan nayi sallah fatana Allah yasa ta zarce gudun kar a rabani da mummyna, na gama paper ina kokarin fitowa daga class don karasawa sch shop inda na ga bashi da yawan mutane, na sayi malt ina dan sha, na nan zaune ganin lokacin dana deban ma mai taxi dina bai cika ba gashi yau mun fito da wuri, sai ga karasowan Mai’dah,Seemah da Jalila(yara masu ji da kansu, wayanda suke tashe sunyi suna a sch), na kau da kaina daga ganinsu don ni ban barin ko ta kwana gashi mummy ta yi min gargadi, har suka zauna ban kulasuba, ni dama ba kawaye gareni ba,sai dai su Yusra, Saima,Siyama ,Abduljabar da muka yi sabo dasu ,hakan ma don dai childhood friends dina be, sai suka sanyani a tsakiya ,Jalila ce ta kunna samsung galaxy dinta tana kokarin saita waka, na maida hankali gurin dadanna wayata (note 3), dukaninsu sukayi shiru ta kara masa volume cikin yanayi na neman jan hanklina, (i think my mum is amazing) shine wakar data kunna tana bi a hankali, wakar da wata marainiya ta rera cikin zazakar muryarta, ya dau hankalina sosai naji raunin zuciyata tamkar don ni akayi, amma ban bari sun fahimceni ba, wasu ma basu san matsayinsu ba cewan Seemah, ai gara ma marainiyar tasan bata da su amma su wa’e don an samu daurin gindi sai kankanban tsiya inji Mai’dah, Jalila ta sheke da dariya tana fadin kai rashin uwa ta asali kun san gur6ata tarbiya yake, ke dai bari Swanky wayasan tushen abin kila ma a juji aka kwaso gayar tsiyar, takaici da ya kwasheni har ban san sanda na ware yatsuna na kifa mata mari ba, duk naga sun mimike suna kokarin hademin kai,da azamata na mike ina ware idanu sannan na jefar da ragowar malt din gami da cire baret dina na wular ina jiran mai kawo duka, sai naga sun dan tsaya, ta shafi kuncinta tana fadin ni kika mara? Ask me again nace sannan nayi nufin juyawa in bar gurin, wani irin shaka naji ta bayan rigana wanda ya sanyani waigawa da dubara na sanya kafafu na kifeta wanda ya sanyata sakina, Seemah ce mai karfin halin fadin M’aidahar kikayi wa haka, bata tsaya jiran amsataba ta cakumoni fada ya barke, ita da Jalila suna kokarin kadani amma ba hali, jin suna kokarin kifani be ya sanyani saurin cakuma gashin Seemah da yake a daure,ta saki kara cikin karaji tana fadin kasheni zakiyi? na warware gashin gami da nanadoshi a tsinysiyar hannuna, duk sai tayi laushi, hakan ne yaba Jalila damar damko gashin kaina zata rama wa ‘yar uwarta, nayi saurin take mata yatsun kafa da takalmina itama ta saki razananniyar kara, horn din motarda mukaji shi ya tabbatar mana da cewar kanmu akayo, cikani Hameedah cewar Seemah idanunta cike da kwallah,na tabe baki gami da dauke kai, Seemah ai shege bai jin magana balle yayi mutunci kai! Itace furucinsa na farko cikin daga murya, da sauri ya karaso yana kiciniyar rabamu, zuciya ta kwasheni ni ban iya fushi ba,da ya raba sai na kuma komawa sai da naji muryar shugaban makarantar sannan ne aka fincikeni da karfin tsiya sauran kiris in kife kasa, nayi taga taga zan fadi aka tarboni ,idanuna suna juyawa na daga kai don ganin shin waye? Matashine mai ji da kansa, wankar tarwada mai Dan tsayi, ma’abocin fara’a, yana da kyau mai daukar hankali, yauma fuskar sa na manne da glass, shigarsa cikin Suit bakake wayanda suka dace dashi,duk kanshin sa ya cika gurin, Muhsin ne, lawyern govt da aka dauka don kare 6angarena, har zuwa wannan lokacin hannayensa na rike dani, cikin minti daya jal na karanto shi a tsanake,matshi mai ji da gayu da kuruciyarsa daya daga cikin wayanda kwazonsu da jajircewa kan abin da suka sanya gaba ke sanyasu daukaka cikin izinin Ubangaiji, mai kyau ne na nuna wa tsara ban ta6a ganin zatinsa da kamala ba irin na yau, ya kasa cikani ni kam na kau da kai ina kallon sashin da baret dina yake kasancewan ba dankwali a kaina, ga gashina da mummy ta gyara min da safen nan ya gama hargitsewa, na ja dan guntun tsaki ina tsima, Hameedah dambe fa? yayi wannan furucin yana kallon sashin da Seemah take, Na watsa masa idanu sannan na kalli hannayena da ya rike, shima sai lokacin ya ankare da sauri ya saki hannayen sannan ne na juya na tafi na dauko hulan ina karkadewa, Mr Johnson ke fadin me ya hadaku cikin tsarariyar turancinsa tamkar mutumin amurka, na yi biris dashi ina cika da sun barni na ruguza bakin gaba za suyi shakkan ta6a irina, Muhsin ne yayi masa magana dama yazone ya tafi dani bisa wani bincike, Mr Johnson ya jijiga kai yayin da yake fadin ba matsala, kuje tunda ai ta gama jarabawar, nayi tsit ina kallon su Jalila da ido ya raina fata,Semmah na daure gashin dana 6ata mata, ya kallo mu gami da cewa who is Hameedah? ban tanka ba na soma karkade jikina da yayi budu budu, Ma’idah dake gefe guda ta nunani ta hanyar cinno baki, ya kallo ni yana girgiza kai, Mr Johnson yace ma su Seemah follow me yayin da ya juya office dinsa,ni kam muna nan a tsaye ya dan kalleni sannan ya ce muje ko? na rakasa da harara har ya kai gurin mortar ban motsa ba,ya waiwayo gami da kafeni da idanu, yana nazarin abin da bazance gashi ba, taho mana cewarsa yana kokarin bude motar, na tsinci kaina da fadin ina zan bika? ba tare da ya juyo ba ya dakata sannan naji yace gidan yankan kai zamu, hmmm na fadi sannan na kara da cewa akwai mai zuwa daukata idan babu damuwa ka jira muga isowansa toh? Sorry ma’am ,ba haka kawai na yo nan ba, mummynki ta amince da hakan so ba zai zo ba yau, na jinjina kai sannan na wuce jikin motar kirar zamani gayen yana haskawa, ina niyan bude gidan baya naji ya bude gaba gami da cewa pls shigo nan kar ki maidani direba kanwata, na tsinci kaina da kasa yi masa gardama,gidan gaban na shige gami da rufe kofar bayan na zauna ya ja muka bar gurin, shiru ya ratsa tsakani na wasu dakiku, dukaninmu da abin da zuciyarmu ke rayawa, na maida kallona kan tsarin ginin Abj da muke ta wucewa, me ya hadaku kika biye masu? ya mani wannan tambayar ba tare da ya waiwayo ba, hankalinsa na ga tukin da yake, yana murza sityari cikin kwarewa, bai bani damar amsawa ba ya ci gaba da fadin kina da zubin nutsatsu masu kamun kai why? na tsinci kaina da cewa tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka na fadi sannan na tsuke bakina ban san tuna lamarin su, dayan can mai gashi fara da kukayi daben karshe da ita wacece? Faduwar gaba mai tsanani naji na rasa dalili, Seemah sunanta class dinmu daya mu duka, an ta6a ce maki kina kama da ita sosai kuwa? Na basar tamkar ba zan amsa ba amma Muhsin ya san kan sana’ar sa da dubaru ya sa na sake da shi muna hira, mutane kance muna kama amma jinin mu bai hadu ba, mun tsani juna sosai, me dalilin ku? Ita ta fara nuna min wariyan nima na bi da ita a haka, yanda mutum yazo min nake kar6ansa, a duk yanda nazo maki zaki kar6eni? Na dan yi jim, yanayina ya nuna alamun rudani? ya katsen shiru ta hanyar cewa come on a hakan ne zan samu kwarin gwiwan case din, ina nufin kar kiga tamkar na shiga rayuwarki daidai lokacin yayi parking a gaban inda nake zaton asibiti ne, ya kashe motar sannan ya ci gaba da cewa I was confused at first, kasa gane ki nayi, shi yasa na tambayi cikin ku wace ce Hameedah ,ya tayar ya gyara parking sannan ya waiwayo gareni gami da cewa duk kin canza yau idan mummynki ta ganki akwai rigima kam, na dan ta6e baki sannan na soma fadin rufani ka saya in mutu maza su kaini pls kar ka sanar da ita, ya gyada kai gami da sauka ,muje ko? Na rufa masa baya kai tsaye ciki muka nufa har muka bi ta wata hanya da ta sadamu da dakin da naga ya shiga, wata datijuwa muka samu kwance da alama barci take , da alama tana jin jiki, fatarta ta yamutse duk idanun sun zurma, na tsira mata idanu ina kallo tamkar talabijin, cikin yanayin rada na tsinci muryarsa yana fadin Kaulah ce ,na jinjina kai cikin takaici, ya ci gaba da cewa ta dan ciko fiye da can baya, she is recovering, very soon everything will fall into the right place,ya karasa yana murmushi sannan ya janyo min stool yana fadin zauna a nan zan dan je in dawo,na gyada masa kai kawai ni kam fitarsa na samu daman gyara jikina, cikin jakata na samu comb na dada kilace gashina sannan na tusashi cikin baret,powder kadan na mitsika a fuskar sai wetlips duk don kar inje gida a hargitse ina jin kunyar irin amsar da zan ba mummy, sallamarsa gami da turo koface ta sanyani natsuwa sosai daidai lokacin naga marar lafiyar tana alamun son mikewa,na taimaka mata ta dan kishingide tana cizan la66a,sannunku ta fadi a sanyaye sannan ta kafeni da idanu cikin nazari inaga son ganeni take, gata nan yau na kawo gabanki cewarsa sannan zanso kiyi wa batuna kyakyawar fahimta, duk wata hujja da zan kafa na samu a hannu juma’ah ta sama za’a ci gaba, fatana kar ki 6ata wa kanki lokaci ki ba lauya wahala, muryarta da rauni naji tana fadin na san mahaifiyarta, bata kai ga karasawa ba da sauri na dago kaina ina kallonta, tayi yake sannan ta ci gaba da cewa amma inaga…na katse mata hanzari yi shiru plsss karki fadi ko wacece ban son sani, a fusace na mike nayi waje gudun kar ta karasa furucinta a gabana saitin zuciyata ta tsananta bugawa da sauri na jingina da motarsa ina rasgarkuka sosai, wucewan mintina 5 sai gashi ya fito hannunsa rike da leda ya bude muka shiga, come on yaushe zaki fuskanci gaskiya? In dai wannan itace gaskiyar ban son ji ta rike abinta, alfarma nake nema gurinka Lawyerner zan samu? Fadi bukatarki ‘yar gata, na cigaba da cewa ka taimakeni ka janye wannan karar ba don na isa ba, yayi murmushi sannan ya juyo 6arina yana fuskantata, ya sasauta muryarsa tamkar mai neman gafara,’yancinki zan kwato maki kuma In Shaa Allahu akwai nasara, Hameedah wannan babba lamarine ya wuce tunanin duk wani mahaluki, kiyi ta addu’a kinji? To me yasa sai yanzun za’a tada zaune tsaye? Calm down ki saurareni ki kar6eni mana a yanda nazo maki, daz ur principle ko kin manta? Na zuba masa idanu tamkar wata shashasha sannan ya ci gaba da fadin sirri ne hammy akwai wasu babies da ta wannan karar zaki zama silar kwato masu ‘yanci ,ban da ke har da grown ups ma dat dont know their real identity i guess,cab ashe muna da yawa na ayyana a raina sannan na share kwallan da suke min yawo a fuska.
Har ya tada motar muna tafe amma ya kuma maido da hirar Seemah,anya babu dabaibayi cikin lamuranku kuwa? Su wa kenan? Na mayar masa da amsa da tambaya, Seemah nake nufi dazun kasa ganeki nayi saboda shigarku iri daya ta uniform, kalar fata,gashi da yanayin fuska,hali da dan abin da ba’a rasa ba shi ya dan banban taku,inaga gaba ma zakace itace hameedahar na fadi ina 6ata rai,ni dai ta min kiyi hakuri ku zama frenz kinji? Bazai yuwu ba,why? Ban shirya wa hakan ba yarinyar da banda fitsara ,gadara da nuna isa ba abin data iya,sai girmankan tsiya,naga ya girgiza kai yana dariya sosai to sannu babba,ba laifina bane zuciya tana son mai kyautata mata a haka aka ginata kan kin mai munana mata,tun farkon shigarmu sch din bani da makiya sama da ita da click dinta,har ta tsani ace muna kama,da farko ba’a ganemu har sai da muka dan kwana biyu a sch din,zagi kam na sha iri iri,ya kada kai daidai sanda muka isa kofar gidanmu yana kokarin parking, leda ya miko min yana fadin gashi ki tafi dashi sakon mummy ne,na karba ina kokarin sauka ya kara da cewa sai wani lokacin ko? Ina murmushi na daga masa hannu sannan na juya na shige ciki lokacin na iske mummy tana Sallah, nima alwalar na dauro cikin sauri na canza kayana zuwa na gida sannan na tayar da tawa a gefanta,mun idar ta bincika ledar da Muhsin ya bani tana murmushi, ke kuma baby a ice cream zaki kare? Dana kar6o ban duba ba sai yanzun na fahimci nawa ne gudun kar in ki kar6a ne yasanyashi fadin na mummyne, muhsin akwai wayon tsiya, ta mikomin ledar ice cream din tana fadin Allah ya bashi lada yayi alheri ko baby? sarai na fahimci inda ta dosa na kya6e baki gami da fadin kai mummy ni fa ban roka ba kuma, Na dakata jin tana fadin to me nace ai murna nake tayaki ko nai laifi? Na sinne kai ina dariya kasa kasa, ta dauke kai daga gareni tana fadin oya zo ki dauki gift dinki, its so special ko baby? Irin wannan kyauta haka tashin farko an fara da favourite dinki, na dan shagwa6e fuska ina murmushin, ni dai mummy nace maki bazan auri mai kudi ba, ok ai yayi kyau sai ki dauko mallam Jatau ko lantana? Na sheke da dariya ina kyakyatawa duk sanda nake tare da mummy nakan jini sakayau tamkar bani da wata matsala sam, ta mike tana fadin na kula rowa ake min yau ko da yake hameedah aka siyawa ba Rahama ba, kafin in mayar mata da martani tuni har ta 6ace wa ganina, sashin matar gwamna ta nufa,na tisa ledar a gaba ina kwasan dadi, ina jin tahowarsu ita da matar gwamna da alama abu mai muhimmanci suke tattaunawa wannan ne ya sanyani mikewa na koma sashina don basu sarari….
Baba Labaran nan ma ya isa na furta sannan na soma gyara zaman rigata,saida na dada gyara fuskata sannan na bude kofar na fita,a nutse nake takawa don isa kayatacen shopin centre din,siyayyan graduation zanyi ba wasa, daga dan nesa kadan na hango shi, shigarsa cikin blue jeans da top mahadinsa, kafafunsa sanye da simple shoe na bakar fata, idanun manne da glass yana kallon agogon hannunsa, tamkar na sanshi amma gudun kar ya dagoni kuma ba shi din bane sai na basar kawai, na jima ina zagaya gurin ina tsintar abubuwan da nake bukata, daga gefena na tsinkayi muryar da bazan taba mance mallakinta ba, da alama waya ake amsawa wucewan mintina 3 sannan naji yanai min sallama, na dai amsa ba tare da na damu inga ko waye ba,hameedah masu gari har yanzun ba’a gama ba? Lallai daga jin wannan na gidane, na dan juya fuskata a sake ina kallon saitinsa, ganinsa ya sanyani dada sakin fuskata, wounderful dama kana nan? Talaka na nan hammy case ya 6oyeshi, wannan siyayyan fa tamkar na aure? Hmmm Lawyernah bari dai na karasa furucina yayin da nake kokarin cire glass din fuskata,yau ma shigata na din din din nayi(doguwar riga already made yar saudi), heel na sanya masu saukin nauyi,graduation things on point zaka zo? Na yi tambayar ina kallon idanunsa yes if am invited, gud kazo da wife, fiance ko gal friend, ance kowa yayi inviting mutane ‘yan uwansa ni bani da kowa sai mummy kuma ban son inga ita kadaice, na karasa maganar ina jin dacin yanayin dana tsinci kaina ciki, In dai ana raba kaza a gurin i will honor it Allaah’s willing, nayi ‘yar dariya ina kare bakina da hannun damata yayin da hagun me rike da basket, wayarsa ce ta kuma kara, wannan karan bai daga ba yayi hanyar waje da sauri yana fadin excuse me,har na gama yawona na nufi hanyar waje da ledoji niki niki na hango shi tafe yana amsa waya, ya katse layin daidai sanda ya karaso gareni, zan wuce na fadi ina nufar mota, ke da waye wai? Driver na ne wani abu ne? No tambaya kawai, ko kafin in karasa har ya rigani shigewa motarsa agogo sarkin aiki ba zakice kin sameshi cikin sauki ba ganinsa sai an shirya, kullum chikin programs yake ,kila ma shi ya biya min kudin siyayyata,wta zuciyar ta ce waya sani? don har ta gama zubamin a jaka banga ta lissafa ba,nawane kudinku? An biya maki ai ta fadi sannan ta koma sauraron wasu na yi kasake ina jira tamkar so nake inji mai wannan kankanban amma ba hali, a sanyaye na bi hanyar fita na dan waiwaiga amma ban ga alaman Muhsin din ba, ya tafi kenan sai wani lokacin,a haka na zuba kayan a boot sannan na shiga ya ja muka bar gurin,ni din Allah yayi min baiwar fahimtar mutum da inda yasanya gaba cikin lokaci kankani,haka nan nayita saka abubuwa da dama a raina har muka isa gida,marhaba da zuwan ‘yan graduation,hmmm baby za’a shiga sahun ‘yan jami’a,na murmusa sannan na ajiye kayan masu nauyin jaraba ina fadin wash, tab dubu nawa kika kaso haka? Nima ban sani ba,kaman ya? Ance an biya min na rasa dalili,a ina kikayi shopping din?Shop rite, na fadi ba tare da damuwa ba ta yi murmushi sannan ta ci gaba da cewa Allah ya jishe mu alheri, amin kawai na ce don ban san dalilin wannan addu’ar ba,mummy muje ki za6i outfit dinki ingani kafin jibi,ah aha! A dai bar wa jibin ko? Gaskiya mummy wayo zaki min nasanki ok muje to, dakinta muka nufa na bude wordrobe dinta ina ware idanu har sai da naga wayanda suka kwanta min,ta kar6a tana fadin wannan ai sai kisa a ce min granny ,haka nakeso ba gara ba mummy ni dai ban san gardawan nan suna shishige maki, Allaah’s willing, my daddy will be with us soon, mummy ki daure plsssssssssss.
CANADA
Zamu iya kiranshi da matshi tunda yana ganiyar cin lokacinsa, mai yalwan arziki da wadata, mutum mai shekaru arba’in a duniya, ya tara komai da duk wani mahaluki zai yi zalaman samu cikin wannan yanayin bakin ciki ke addabarsa ko me dalilinsa? Alhaji Abdullahi Buba kenan daya daga cikin jigajigan ‘yan kasuwan naija da ganinsu kanyi wuya kwarai, harkokinsa sunfi ci a kasashen duniya, shi kansa yakanji dama Allah ya misanya masa dukiyan da farin ciki madauwamiya, ingarimin namijin da jin dadi,kulawa da kudi suka 6oye yawan shekarunsa, yana da 40 amma zakiyi zaton dan 35 ne,yau din ma kaman kullum a hanyan ganin likitansa yake don gwada BP dinsa tunda cutarsa ta hawan jini ta sanyashi gaba, lokacin baya can tamkar ba zai yi rai ba, tsabar damuwa, sanyawa rai burin samun matsayinsa na can baya wanda sune ummul abaisin halin daya tsinci kansa a ciki, Alhaji A.Buba da yayi farin jini gun ma’abota kasuwanci shine tafe yana wassafa abubuwa cikin rainsa, cikin shigar girma na suit ruwan toka, mutum ne fari sosai da za’a iya fasaltashi da balarabe don yanayin fatansa, ya tura kofan yana neman izini likitan ya bashi daman shiga, Dr Matins ya bashi hannu suka gaisa sannan ya ja kujera ya zauna, bayan ‘yan gaishe gaishe Dr ke tambayarsa yanayin da yake ji sannan ya yi ‘yan gwaje gwajensa, Dr matins kwararen likitan da yasan aikinsa ya yi wasu aune aune sannan ya fuskanci patient din yayin da ya soma fadin, baka samun isashen hutu kuma magunguna baza suyi tasirin da ake bukata ba, Magani bai aiki sai da nutsuwar mai amfani da su go and try dis,sun jima yana masa lecture kan yanda zai kula da kansa don shawo kan matsalar sa, sannan ya mika mika masa wasu magunguna sukayi sallama, kai tsaye motarsa ya nufa yayin da abubuwa da dama me masa yawo a kwanya, tamkar jira ake wayoyinsa suka soma ringing, ya ja tsaki gami da kunna motar ba tare da ya damu da dagasu ba, zuciyarsa na kuna, a ra’ayinsa yanzun yana isa gida kawai ya samu ya huta, amma a zahiri ba hutun jiki kawai yake bukata ba har da na zuciya, shin ya za ayi zuciyarsa ta samu hakan? wayoyinsa suka ci gaba da ringing alamace na hutu bai gansa ba,ya ja tsaki cike da takaici kai tsaye yayi parking guri guda sannan ya dauki ta tsakiyar gami da karawa a kunne don amsawa, Ramadan ne daga Johannasburg yake sanar dashi isowan italian products dinsa a sea ports,ya yi masa godiya yana katse kayin dayar ta dau tsuwa, Mr Ray daga Washinton District ke neman ganinsa duk a gobe ya bi shi da to, na ukun Alhaji Dikko ne daga Saudi matsalarsa ta custom ce, Alhaji buba ina da kaya daga cameroon an tsaresu an hana ni,yau gani a saudi fatana zuwa jibi ka yi masu magana nasan da ka sanya baki zasu daga mini kafa,an gama ya fadi sannan ya ajiye cike da damuwa shi kenan bawa bashi da hutu,matsaloli gasu nan ne ba sauki,da wannan ya karasa gidan masu yi masa hidima suna masa barka da zuwa,tsabar rikicin da ya tsinci kansa ciki kasa amsawa yayi,a palo ya tarar da baki suna jiransa a bisa dalilai barkatai,ya dafe kai bayan ya zauna yana karanto addu’oin samun sasauci cikin kwanyansa,ya furzar da iska mai tattare da huci daga bakinsa har idanunsa sun rine don gajiya,saida ya sha ruwan da ya sanya aka kawo masa don samun salama gami da rage suit din jikinsa sannan ya kali abokan kasuwancinsa dake zazaune ya basu hannu suka gagaisa,Mr Ralph da Mr Brown sai secetary dinsu wayanda suke da hannun jari tare,wasu kudade ya basu abin da suke bukata kenan cikin lokaci kadan ya sallamesu yana hamdala,tafiyan
su da mintina talatin har yayi nufin wucewa masters bedroom dinsa , wayar landline dake kafe a sitroom ta soma ringing ya karasa ya karata a kunne,daga dayan 6angaren Ibrahim ne ke magana cikin sautin kuka, uncle ka taimaka yau kwana uku suka rage a shiga karar daddyna, sai a lokacin ya tina da wannan batun ashe fa yana da zuwa naija kwana kusa, IB na bukatan taimako marayan Allah, daddyn ne kawai abin tinkahonsa gashi an tsareshi a abuja airport sun makashi a federal high court wai ana tuhumansa da laifin safaran kwayoyi,shi kadai zai tsaya masa a matsayin dan uwa, ka shirya gobe mu wuce ko? da dariya a muryarsa yake fadin THANK YOU UNCLE, ya kife layin sannan ya haura sama, madadin ya huta don cika sharudan Dr Martins, sai ya 6ige da harhada kaya, sannan ya kira PA dinsa yana mai sanar dashi cewa gone zai yi tafiya, ya danna wa secretary dinsa kira gami da bashi umarnin yayi cancelling din appointments da meetings din gobe, wannan kenan.
[5/16, 2:48 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
5…
Tun jiya ban huta ba saboda shiri nake na kece raini,haka nan kawai nake jin farin ciki mara tushe,yinin jiyan nan cur a gidan kunshi nayi shi hanu da kafafu an zane tas ja da baki lallen alura sak ta larabawa,ga gyaran gashi da aka min stiming shima das abuna,tun da na fito daga wanka nake ta shirin tafiya graduation ground,daga palo nake jiyo muryar mummy da alama ta kosa in fito ne,na dan leka ta window ina fadin mummy 2 munites pls,au har yanzun baki kai ga sa kayan ba? Oh kwaliya fa nake tsarawa yau dabance,oh ni dai naga ta kaina mijinki ya samu aiki baby an fi awa daya ana abu guda naga dai ba zabiya kike son zama ba? Wannan hasken fatan ai ya isa,na koma sai a lokacin na zaro pakistan dina dinkin waje ta kasashen Asia, yau abin da nake ra’ayi kenan,na shirya cikin pink shar sannan na debo sarka na sanya wani a goshi na zuba awarwaro da sarka tamkar indiya na sanya wani dan karfe tamkar dan kunne a kan hancina,kwaliyata mai sanyi nayi don kar in dauko kamanin aljanu, sai juyi nake a gaban madubi ina yaba kaina, masha Allah naji ta fadi tana hangoni ta window fito to kar lokacin ya kure,mummy takalmana pls gasunan a shoe rak kar in tsuguna kwaliyata ta 6aci, na sanya su heel ne dai kaman kullum masu kalan tufafina,sitirata su ba sari ba kuma su ba pakistan zalla ba,a gidan baya muka zauna driver ya ja muka dau hanya, wayarsa ce ta katsen kokarin neman layinsu Yusra da nake,na daga ina fadin don’t tell me u are nt coming? yayi ‘yar dariyarsa gami da cewa no na isa, zan zo ai,kuma hanya ko? yeah mun kusa ma,OK later cewarsa yana katse wayar, sai ga wayar su Saima suna fadin ina nake? am on my way, zumudin na me ? naga dai its my grad nt yours ,mummy na jin my tana dariya, tun muna yara haka alakarmu take, min girma halayyen mu na nan, abduljabbar ba zai samu zuwa ba, yana US inda yake karantar business abin shi ,amma ya turon greeting da CONGRATULATIONS tun ran dana gama final paper.
GRADUATION ARENA
Saima ta katse wayar tana murmushi, Siyama dake gefanta ta soma fadin Allah yasa kar ta dade, jaira ta sa muka doka sammako ,I just wnt us to give her the present kafin a fara ceremony, hirar suka ci gaba dayi wanda suka lula kan abin da ko waccensu ke sha’awar karantawa, dai dai lokacin shu’umar ta Sanyo kafar ta cikin hall din, fatabarakallahu ahsanal kalikin cewar siyama data mike baki sake hankalinta kacokan gurin wace suke muradin gani, Saima na zaune ta tsira ma kofar idanu fuskar nan dauke da fara’a tana fadin WOW, baby bazata kasheni da salon ta ba, ita kuma madadin ta karaso sai tayi tsaye tana murmushin ganin ta dau hankulan jama’a, duk sukayi gurinta da doki kowa na son ya fara isa gareta, ta Dan daga doguwar rigar lace din jikinta kalar pink ,yayin da heel dinta ya bayyana, sannan ta soma takunta na isa, tana barin bakin kofar ma’idah ce a bayanta ,sai jalila daga hagunta suna shigowa,Yusra ta shigo daga damarta ta wuce ciki suka kusan karo da Saima, murmushi suka sakar wa juna suna fadin we thought you are not coming? I have been around na tsaya siyan mata present ne, hyyyyy ta fadi sanda ta karasa garesu, warmly suka karbeta ta hanyar rungumeta suna mata CONGRATULATIONS, fuskarta ba yabo ba fallasa ta karbesu, Yusra ce ta mintsineta cike da tsokana take fadin stop pretending, I know deep inside you this is your happiest moment, ta yamutsa fuska don Sam ba mai son surutu bace, burgeta sukayi a matsayinta na mai son associating with classy chicks ta je su gaisa, baby bakiyi kunshin ba jiya? how comes? tambayar da yusra tayi mata kenan tana nazarin ta, Ma’idah da Jalila suka yi intruding aka soma gagaisawa, kowa na mamakin abubuwan dake dankare a rai, suka tsaya hira jefi jefi suna nazarin babyn data sauya masu tashi daya, Saima ce ta matsa mata da tambayoyin hey why are you cool? me aka maki? ke ina kika baro mummy? bata magana sai dai ta girgiza kai, Yusra tayi shiru tana kallon ta cike da tuhuma, sannan a sanyaye tace Who are u pleas……. maganar ta katse dai dai sanda mummy da Hameedah suka sanyo kai cikin hall din, da sauri suka nufe su cike da doki Yusra ta rungumeta suna juyi, kallo ya koma Kansu, Saima ta daka mata duka suna dariya, baby kin bamu wahala, like seriously? nayi tambayar ina daga masu gira , Siyama ta shigo tsakani ta rungumeni tana fadin fabulous, gal you look muah, ta karasa tana min Peck a goshi, anga Hameedah dole in zama statue cewar mummy sounding happy, su 3 suka tafi gareta suka rungumeta tamkar zasu kaita kasa, hey kar su kar da mummynah please, mummyn ki ko mummyn mu? I can’t believe my eyes cewar Yusra, sannan ta fincikoni tana fadin come and see your double ganger, Sam ban fahimcetaba ,binta nake tamkar rakumi da akala, Seemah muna nufa kai tsaye,zaune take cikin kujerar plastic a hakimce, Yusra wait, the ceremony is getting started ,I known her, she’s my classmate, opening prayers ya sanyamu samun gurin zama duk muka nutsuwa, sit muka zauna ni da mummyna da friends dina, naji daban kasancewar banga Muhsin ba, ga iyaye da’yanuwa sun cika gurin sai naji kwalla ta cika mani idanu daidai lokacin aka umarci graduants su koma 6angaren da aka ke6e masu, na mika wa mummy hand bag dina dan shafal dan gayu kawai na daukoshi daga waya sai purse a ciki, muna tafe muka hade da clik din su seemah itama uwar gayan ta dau wankan pink, cikin rashin Sa’a kuma sai kujerar mu ta kasance a jere gani ga Seemah sai wani shan kamshi take, ni kam basu isheni kallo ba kuma a shirye nake in cin uban duk wace ta kuma shiga gonata, kaman ance kalli can hankalina ya koma ga kofan shigowa dai dai lokacin da Muhsin gentle man ke takunsa cikin shigar alfarma gefansa wata kyakyawar matashiya na gani sun jero tana yanga, ashe na taka wannan matsayin da zan nemi alfarma in samu? Hawayen farinciki ne suka zubomin na sanya hannu na daukesu ina sauraron jawabin guest of honor, ya dago min hannu fuskarsa dauke da fara’a nima na daga masa, naji salama a raina na juya don gyara zamana idanuna suka kai kan Seemah dake kallon su Muhsin din, sai na dauke kai na share kawai…
SEEMAH ABDULHALIM KUSADA ‘ya ce ga Dr Abdulhalim Kusada, Dan bokon da keda matsayin masters a administration, da PhD in politics, gagarumin dan kasuwan da siyasa ne da duniyarsa ke gara masa, matarsa daya jal uwa ga Seemah da Rihab, yaran sun taso cikin gata da sangarta, duk abin da sukeso ake masu, wannan dalilin be ya sanya ‘yarsu Seemah ke jin ta isa da kowa a fadin duniyar nan, toh abu ne da aka dade ana nema ba’a samu ba(haihuwa), shi yasa suke ma yaran wani irin so beyoun expectation…
Deep inside her bakin ciki ke cinta, Seemah yarinyace mai tsanin son Kanta, tana da izza da takama, tana son ace komai ita, komai nata ya zamana stay clear no go area, ta tsani wani yayi competition da ita balle kuma a sha gabanta ,tana da jin kan da zuciyarta ke yaudaranta har ta ke ganin ba ya ita, hatta kyau Seemah bata yarda akwai Wanda ya kama kafarta ba, shi yasa a duniya bata da rival/ makiya sama da hameedah, komai hameedah, why is she standing in my way? kyawun da nake ji dashi kuma ace we look alike, I will do all it takes to see your downfall, ta ayyana a ranta tana jin tamkar ta shakota ta huta, da labarin case din hameedah ya fito tamkar da zuba ruwa a kasa ta sha don murna, sai ta samu zuciyarta na rage tsanar da takewa her so called rival saboda tana ci mata mutunci son rai, abin haushin shine bata taba jin irin hakan ga kowa ba sai hameedah, ita kanta takan rasa dalili, Idan su 2 suna guri hameedah tafita tafiya da hankulan jama’a , wannan abin na ci mata tuwo a kwarya, haka hot guys da hameedah sukeyi, d most handsome a school mq hameedah ce crush din shi, best in academics ma hameedah, am sick and tired of all this tayi murmuring angrily. An yi abubuwa da dama sannan aka koma kan prizes wanda mafi akasarinsa ni na yi meriting, sai Seemah data samu itama, ina da 7 yayin da ta samu 5,sai wasu abokan karatun mu da suma suka samu 2-3, ni da Seemah ne dai muka kwashesu, yau kam kasa yi min magana suikayi ko me dalili? Taro yayi kyau ana ta rabon souvenir, abinci, drink, snacks da saurinsu, ganin hakan ne ya sanya ni karasawa gurin ‘yan uwana, mummyna da fara’a ta rungumeni tana ta murna, ashe dai ban sha wahalar banza ba ta fadi tana jinjina min, nagode da kayi honorin invitation din, na soma fadi daidai sanda na karasa gabansa yayin da idanuna ke kan wace suka taho tare, never mind cewarsa, muka gagaisa itama nai mata godiya tadan murmusa tana fadin muke da godiya, waccan ‘yaruwarkice ko? Na kai idanuna inda naga tana nuna dan yatsanta manuni, Seemah take nufi,na dan yamutsa fusa gami da girgiza kaina mummy ta kar6i zancen da fadin kira frenz din naki mana baby, wannan ne ya sanyani jin tamkar inyi ihu don takai ci, na juya gareshi yayi min alaman aikata hakan da idanu Ya na iya? Allah ya gani ina jin Seemah a raina, farkon shigata school na so abota da ita don haka kawai take burgeni amma na sauya tunani ganin alkibilarta, a sanyaye na juya lokacin suna ta daukan hotuna, ina karasawa Jalila ke fadin yauwa Hammy zo muyi hotan tarihi plss duk sai suka maido da hankalinsu gareni, muje gurin yan uwana sai muyi hoton a can kawai na fadi sannan muka juya tare, na dan waiwaya bayana Seemah na hango tsaye tamkar an dasa ta wannan ne ya sanyani komawa gareta fatana a rabu lafiya wa ya san gobe? Mummyna na son ganinki na fadi ina kallon idanunta, wayancan ‘yan uwankine? Na gyada kai ina nufin eh, gud sun kyauta a rana irin ta yau kin fi bukatan yan kara saboda kar kadici ta karasa ki, wasu ma sun san darajar kalan dangi saboda neman suna ,amma dai haya kika daukesu ko? saboda kin…. Zazzafan marin dana kifa mata ne ya maido da hankulan jama’a garemu, gurin ya dauki shiru tsit kikeji duk sai naji kunya ta kamani ina iya hangyan takaici kwance a fuskar mummy, su Maidah da ke tare da mummyn ne suka karaso garemu da sauri ina ce mun bar magananan a kan zaki nemi sulhu da Hameedah cewan Jalila, yau ake yayemu galz mun fa girma, na ja tsaki sannan muka karasa inda ake jiranmu, tsabar 6acin rai har ban ganin gabana ban ankareba na taka abu mai tsantsi har na kusan kifewa naji an rikoni ta bayana, na waiwaya a hankali Seemah ce mai rikenin mamaki ya cikani, na basar duk muka wayance, mummy ga Jalila,Mai’dah da Seemah, ku kuma ga mamana farin cikin raina na karashe ina kallonta (mummy), idanun ta fes akan Seemah tana jansu da hira, ke mai kama da hameedah ina dai fatan baki da rigima, sonkai da shagwa6a irinta wa’e? Duk muka sa dariya, Barister Muhsin ga class mates dina, congratulations galz gaba ta fi baya yawa ina fatan zaku zama abin koyi ga Al-ummah? In Shaa Allah suka fadi gaba daya, gud ga Sa’adah nan ya fadi yana nuna wace suka taho tare ina fata zaku zama frenz? Da fara’a suka rika gagaisawa, mummy jefi jefi ta kan auno min harara, a raina nace baki san makirai bane shi yasa, kamin mu bar gurin nan saida aka dasa hira ,wasa da dariya sosai mummy da kanta taje boot ta kwaso masu souvenirs, duk sai naji babu dadi bata ta6a nuna min fushinta ba irin yau, shi kansa Muhsin ya dago inda ta sa gaba, muka yi ex changing contacts cikin dadin rai sannan ana ta kida da raye raye na music din zamani masu tashe, daga bisani aka koma hotuna, munyi muduka, sai na mu ‘yan sch (mu hudu kenan da graduation gown),munyi mu uku,mummy a tsakiya sai ni da Seemah muka sanyata a tsakiyan, na karshe Muhsin ne a tsakiyan mu ni da Sa’adah, sannan muka shirya tafiya inda muka fito, ni da shi ne muka fara yin gaba yayin da sauran ke can gurin su Seemah, ni na rasa me ke jan hankalin mutane gareta haka, takaici ya rufeni har ban san sanda naja tsaki ba, yaya dai ya fadi yana kallona? Ba tare da ya jira amsa ba ya ci gaba da cewa ki koyi danne fushinki ba a ko ina ake reactin ba, yau ranar farin ciki ne amma kalli yanda duk kika daure fuska me yayi zafi? Ai da burgewa mutum ya ga mai kama da shi, wa ya san gobe shin ko kina da yakinin an rabu kenan? Na girgiza masa kai yayin da idanuna suke a kasa hawaye fal, yayi ajiyar zuciya sannan ya kara da cewa ita rayuwa a sannu ake binta jibi In Shaa Allahu zamu soma shiga kotu da fatan kina addu’a? Na gyada kaina kawai ina wasa da yatsuna ,daz great kuma ina bukatarki a gurin, da sauri na daga idanuna ina kallonsa, kar kice komai kema da amfaninki a gurin ki zama eyez witness, sahun su ne ya sanyashi saurin cewa ki lallami mummy ki bata hakuri kin sa6a mata nagode, itace furicina ta karshe sannan na wuce gurin motarmu har muka bar gurin ni da Sa’dah muna daga wa junanmu hannu, yayi sa’ar mace na ayyana a raina,har muka isa gida bata kulani ba, Saukar mu keda wuya, na yi nufin kar6an kayan hannunta, da sauri ta daga min hannu gami da cewa matsa cikin daga murya, da sauri nayi gefe har ta wuceni ban daina kallonta ba, na rufa mata baya ashe mummy na fushi? Na shiga uku na furta a hankali, Seemah ce mai wannan laifin makira mai siffar kamilal, na wuce dakina har na cire kaya na yi wanka na sauya wasu ban ji duriyar ta ba, cikin sanda na leka dakinta caraf idanunmu suka hadu me kike nema? Tambayar da ta zo min tamkar saukar aradu, na ja jiki a sanyaye na koma palo tv na kunna amma hankalina baya kai sam, me mummy take nufi? Semmah ta fini matsayi kenan? Muguwar yarinya burinta ya cika na san ta maye gurbina ma, har wayewan garin babu shiri tsakaninmu, abin na ci min tuwo a kwarya, amma na rasa yanda zan shawo kan lamarin, daren ranar da kyar na runtsa duk na kosa gari ya waye ayi wace za’ayi…
Da addu’ar tashi daga barci na sauka daga kayataciyar katifata , kai tsaye toilet na nufa na dauro alwalla gami da gabatar da nafila zuwa sallar asuba, sannan na sauna azkar, da kyar na karanta shafikan Al- Qur’an 2 na mike ina salati, a kitchen na isketa tana hada mana breakfast, kallo daya tayi mani ta dauke kanta daga inda nake tsaye,nan na raku6e a bakin kofa ina kallonta har ta gama ta zuba a plate zata fita dining area na bita da spoon dina a hannu , ganin bata kulani bane ya sanyani zama opposite dinta kamar dai ko yaushe,na kai spoon zan diba ta zaren idanu gami da fadin ke waya gayyaceki? na janye hannun idanuna suka kawo kwalla, mummynah! whose your mummy? ta yi Mani tambayar tamkar wace taga abin kyama, hakan ne ya tunzuran zuciya matuka , mummy please, what cewarta tana kai tumbler baki, bafa laifi na bane, am not your mum ,da na isa mummynki you will not disobey me, hawayen da suka cika Mani idanu suka samu daman silalowa…
[5/16, 2:48 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
6…
Mummy yunwa fa nakeji, kuma ni zan debo maki? haka baki San hanyar kitchen din ba? shin ke bakuwar gidan ce? Hawayen suka ci gaba da silalowa daidai sanda wayarta ta soma ringing naga ta karata a kunne,voh my baby ya gajiyar graduation din? Na zuba mata idanu ina kallonta, ehen gata nan ma tana ta min rikicin, ya kawayen naku? Ok Seemah ki gaida mutan gidan ko? Ta kalli inda nake zaune sannan ta ajiye wayar, haba mummy kinsan fa tare muke cin abinci kuma yau… bata bani damar karasa wa ba ta tari numfashi na, ah ah ha in baki ci ai babu tilas cikin harkan nan, na sanya kuka ina fadin kiyi hakuri bazan kara ba na daina, hakurin me kike bayarwa ne? Na ririke kafafunta ina magiya, cikani kar ki katsen hanzari, mummy kar ki tilastani in soma kokwanto kanki ki gafarce ni Seemah ce ta shigo tsakani baki san yanda mukayi da su ba kuma baki tambayeni ba, bana son sani ai ba tun yau nake kwadaitar da ke ribar hakuri da kawaici ba, aure zakiyi shin idan kanwar mijinki tayi kuskure sai ki shara mata mari? Ko an gaya maki duka muka taru muka zama daya? Ke ce mai ikirarin zaki auri talaka mafi akasari suna kuma basu shagwa6a matansu idan kikaje da wannan hali ya zaki kare? Ko ance maki kowani namiji ne ke aikata adalci dari bisa dari a harkan gidansa? Wani kan fifita yan uwansa akan matar ta yanda bai damu da jin dalili ba baki da tarbiya kawai zai rike kin 6ata masu zumunci, ko kuma don kin aureshi sai ya zubar da yan uwansa? Na girgiza kai ina kuka sosai,to me laifin Seemah fisabilillah? Idan aka sa6a maka ai sulhu akeyi ko ke kin fi karfin kuskure? Dole zanso Seemah mana tunda ta talafi baby kar ta fadi a bainar jama’a, kuma kaso wanda ya soka kukan nan ya isa haka ta dagoni ta rungume tana dan jijigani, wannan ya zama na karshe kin ji ko? Ina murmushi na ce to sannan ta sani naje na wanko fuskata na dawo muka zauna cin abincin kaman ko yaushe.
CANADA*
Kokarinsa na son isowa Nigeria a takaitaciyar lokacine ya kai shi ga dora Secretary dinsa kan wasu harkokin da ba zai gaza tafiyar dasu ba yanda ya dace, sannan ya yi masu visa tare da hada ‘yan kayayyakin da yake son wucewa dasu, yinin ranar duk bai huta ba, sun yi waya da IB shima a shirye yake, abu daya ke masa yawo a zuciya, duk tsawon shekarun nan da yayi a kasashen ketare bai taka rawa gurin kawar da wannan shaukin da ke tattare da shi ba, ya Mike tsaye cikin tsananin damuwa yana Jan tsaki, banda wannan karar babu abin da zai kai shi wannan kasar, ya furta cikin kunan rai yayin da yake fesar da hucin bakin sa idanun a rintse, ruwa ya debo cikin shanpe flute ya sha yayin da yake rage kayan jikin sa, kwakwalwarsa na taryo masa shudaden lamari, ya salam ya furta cikin radadi sannan ya mika hannu daga Inda yake yana laluban magungunan da Dr Martins ya bashi cikin drawers, a dadafe ya kwankwade sannan ya kishingide hannunsa dafe da saitin zuciyar sa, idan da abin daya tsani tozali dashi a yanzun ya biyo bayan kasar da yayi wa bankwana(Nigeria), saboda tarin kalubalen da rayuwa ta karanta masa, amma bashi da zabi dole ya soke komai ya je, bai san tsawon lokacin daya dauka yana wannan tunanin ba har barci barawo ya sace shi….
Karan alarm ne ya katse masa barcin da yake cikin nutsuwa ,ya yamutsa fuska gami da jan tsaki, da alama yana jin dadin yanayin daya tsinci kansa a wannan lokacin, sannan ya mike yana mamakin irin lokacin daya dauka yana barcin daya jima bai irinsa ba, alwala ya dauro yana shirin tada sallah door bell ya katse masa hanzari, da azamarsa ya karasa ya bude kofar IB ya bayyana, shigarsa cikin track suit army green din da suka karbe shi, kafafun kunshe cikin trainners yayin daya goya katuwar jaka a baya, hey Uncle cewarsa cikin zumudi ,daga muryar sa zaki karanci farin ciki tsantsa, ya rungumesa yana fadin i wana pray son , sannan suka shige ciki, IB yayi hanyar bedroom inda yayi wanka ya sauya kaya sannan yayi sallar shima, ba tare da bata lokaci ba suka wuce filin jirgi.
Zuciyarsa ta gaza natsuwa sam sai abubuwa take saka masa, jefi jefi yakan ja tsaki sannan ya gyara zama, IB na kula da shi har ya danganta hakan da gajiyace kawai, a haka har barci IB din yayi don jigin ya lula.
ABUJA
A yau ni da mummy muka bar gidan mai girma govenor Niger inda muka koma dakwa (flat, daya daga cikin gidajen mijin mama kulu) da zama , saboda mai gidan da iyalinsa zasu vacation England, wannan dalilin ne ya sanya aka hadamu da securities, a yau din ne kuma zamu za’a fara sauraron kara a kotu, ni hameedah da mummy muka hero don karasawa cikin kotun, gefe guda su hajiya ni’ima ne da tawagarsu, daga bayanmu mukajiyo muryan lawyana yana amsa waya, na tabe Baku cike da tunanin shi wannan bai hutawa ne? Sun sauka lafiya inda ya samu yayi masu booking hotel room, da alamun gajiya tattare dasu ,har gara IB yayi barci cikin jirgi, shi kam har yanzun bai runtsa ba, wanka sukayi gami da sauya kaya sannan suka yi ordering abinci, coffee suka sha da kayan cikin rago, shi kam tunda suka shigo kasar yake kale kale, komai ya sauya ,tsarin ginin ikko da zamantakewar mutane ,ke har da ci gaban da aka samu, lallai ya jima rabonsa da kasar sa, har zuwa wannan lokacin da suke hutawa a hostel room, damuwa bata sakes shi ba, IB kam TV ya kunna yana searching stations, komai daban ne a gurinshi, tsawon shekarunsa a turai ya yisu, wannan ne zuwansa Lagos na farko a rayuwarsa, ya nemi Layin Lawyern don jin abin da yake ciki amma bata Shiga ba, sai da suka rama salolin da ake binsu sannan suka sake ficewa booking flight din abuja, sun dan jima kafin su koma dakinsu, IB kam ya kosa a je abujan nan saboda koba komai zai yi yawo, tarkon zuwansa naija sun je Dolphin da wounderland, fatansa Allah yasa a gama case din daddynsa lafiya,da wannan zulumin suka kwanta, a wannan tsakanin barci kan gagareshi, ya waiwaya gami da tsira ma IB fake barcinsa peacefully idanu, tunaninsa na can garin Kaduna, ya dafe goshi cike da damuwa, ji yake dama ya gansa yanzun a Dan bushiya, dole in koma again ya furta cikin yanayin rashin madafa…
Washegari sammako suka doka zuwa abuja, flight din safe suka bi kai tsaye, saukansu ke da wuya ,suka yi shatan abin hawa zuwa hotel kuma, daga shi har Son dinshi suka zama tamkar wasu kauyawa, sai kale kale suke, key kawai ya karba a reception sannan suka wuce daki, suna isa ya ajiya kaya sannan ya umarci IB daya zauna cikin room din kar ya fita, yayin da shi kuma ya nufi Court ,lokaci ya ja kuma bashi da yakinin za’a fara shari’ar nan yau, don 10am akace kuma karfe 11am ya iso masauki.
Na waiwaya ina kallonsa, sannan na mayar da hankalina ga kotun, muka shige kai tsaye, sallamarsa ce ta dakatar damu, har ya karaso inda muke yana fadin ok ka shigo to mu gain, sannan ya katse layin , na juya ina kallonsa gami da cewa kai baka hutawa ne? Ya mayar da wayar aljihu yana fadin hameedah kenan, na waiwaya ga mummy amma naga wayam mummy ta wuceni ta shige ciki, ni dashi muka juya don shiga ciki,muryar da tayi mana sallamace ta dakatar damu, ba tare da waiwaya ba na dai amsa sallamar sannan na shige abuna, shi ya tsaya sauraron bakonsa. Sun gaisa a takaice sannan ya gabatar da kansa, am Abdullahi Buba by name, dan uwa ga Alhaji muntari da ake zargi , barr Muhsin yayi murmushi gami da cewa Allah sarki, amma ka makara don yanzun haka akwai karar da zamu saurara, sai dai a sake new arrangement amma banda yau, muna line up activities ,ok kawai ya iya fadi cikin damuwa, sannan suka yi sallama cikin girmamawa, akwai wani babban almari tattare da bakon nan, amma bazai ce ga dalilin wannan zargin nashi ba, ya nufi cikin hall din da sauri.
Hall din yayi tsit ,kowa ya nutsu yana jiran a fara, alkali ya shigo aka mike saida ya zauna sannan kowa ya zauna, aka gabatar da kara gami da umartan lauloyi 2 masu kare bangaroroin su fito, kai na naji ya sara min da sauri na rike mummy cike da fargaba, daga rana irin ta yau zan iya rasa ta, wannan tunanin ne ya sanyani tsira mata idanu, da ina da iko da na kori karar nan, lauyana ne ya fara bayyana kansa da matsayinsa dannan barister Bala Sumaila ya gabatar da kansa a matsayin mai kare bangaren Kaulah wace tayi tsit tana wa jama’a kallon fes, yau naga mace mai kekashashiyar zuciya ,kyace rakiya ta yo don ba alaman damuwa ko tashin hankali a tattare da ita, na tsuke bakina gudun kar hankula su dawo kaina, idan nayi wasa damuwa sai su taru su karasani, na mayar da kai na kwantar kan cinyar mummy don zaune nake dab da ita, yaya dai? Ta fadi tana shafa wuyana,akwai matsala ko baby, na dan girgiza mata kai,to ya jikinki yayi zafi? Mummy kiyi hakuri, ok na bar tambayar, in ban son ta kureni hakan na kan fadi kalman hakuri in ta raitsani da tambayoyinta, to ma tukunna ince mata me? muryasa naji Wanda ya tabbatar da cewa an fara case, malama zaki iya shaida wa kotu ko ke wacece? Furucin lauyanane daya taimaka gurin bankadoni daga birnin tunani, kaulah yake ma wannan tambayan yayin da ya tsaya kusa da ita, ta dan kalli inda nake zaune sannan naji ta soma fadin sunana Kaulatu Muhammad Anas tsohuwar ma’aikaciyar asibitin dutse ta jihar kaduna, nayi aiki karkashin marigayi doctor Azumi tare da Sis Jane da dai sauransu, ya gayada kai yana fadin baki gaya mana bangaren aikin ki ba, haihuwa nake kar6a idan ina duty, gud banda shi babu wata sana’a da kike yi? babu, kin tabbata, mai girma Muhsin bashi da ikwon wuce gona da iri cewan Bala Sumaila mai kareta, Alkali mai sauraron kara ya daga masa hannu alaman yayi shiru, na gode tsawon wani lokaci kika dauka kina aikin? Shekaru talatin nayi a services, zaki iya ce min tsawon wannan lokacin baki ta6a wata sana’a ba? Ta girgiza kai, ko kuskure ba’a ta6a samu ba daga gareki? Kin kyauta, shekaru 15 da watanni 6 baya zaki iya tuna yanda rayuwarki ta kasance? Tayi jim cikin tunani bai bata daman magana ba yaci gaba da cewa ina mijinki da labarin sa? ina da shekaru 25 a aiki ya cika ya bar ni da yara uku, kana na ne? A a maidaidaicin shekaru garesu, dawainiyarsu fa? Ni na dauka, why? Danginsa sun ki mu, a lissafe salary dinki ba zai dauki nauyin komai nasu ba ina kika samu tallafi? Tunda kince ita kadai ce sana’ar, objection my lord cewan Sumaila mai kareta amma ba’a bashi daman magana ba…
[5/16, 2:48 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
Masoyana sakon ku na isowa gareni, barakallahufeekum, nagode da kulawan ku, Allaah ya bar min ku, ina kaunarku a duk inda kuke…
taku har kullum… Ummu Farhanah
7…
Ban dai ta6a sata ba ta fadi gami da jan tsaki, ya nuna gurin su hajiya Ni’ima Garba da Madam Zarah gami da cewa kin san wadancan? Ta kallesu a kaikaice gami da girgiza kai sannan ta kara da cewa sana’ata ba irin mutanan da ba zan iya cin karo dasu ba kuma ba lallai bane in rike fuskokinsu ko abin daya dangancesu ba, ya bata izinin ta je ta zauna tukun yayin da hajiya Ni’ima ta maye gurbinta, mace ce kosashiya mai takama da abin data mallaka, shigarta kadai ya isa mai kallonta fahimtar cewa matar manyace , sunana Ni’ima mata ga Alhaji Abdulhalim Kusada mai tireloli, ta dan gyara zaman rigarta tana fadin ko tsinke ban kaudarwa (tana nufin ita ‘yar hutu ce), ya gyada kai kawai sannan ya ci gaba da cewa kafin haihuwa shin ina kike zuwa awo? A gida ake min,why? Saboda hutu kawai, shin waye ya dauki nauyin ki tunda shari’ar shekaru 15 baya ya nuna cewa shi Alhaji Abdulhalim din bai amince da cikin naki ba, ni na dau nauyin kaina mana, kuna da family doctor kenan? Ah ah Kaulah na dauka nake biyanta hakinta karshen ko wani wata, har dakina take zuwa ta dubani kullum, kina da kaulah a hannu me ya sa da kika tashi haihuwa baki kirata gida ba kika je asibitin? Da kika tashi zuwa ma ba private ba irin na manya, ta dan yi jim sannan ta dora da cewa ra’ayi? Yayin nakudan wa ya kaiki kina labour ko zamu iya magana da shi direban naki? Ah ah ni na tuka kaina kasancewar ba kowa a gidan, kotun ta dau hayaniya sama sama, an dan tsahirta aka ci gaba, a asibitin kuma waye ya kar6eki? Kaulah ce, kince ita ke maki awo amma a bayananta ta nuna cewa bata san abin daya danganceki ba, karya takeyi barister, bayan haihuwarki da idanunki kinga abin da kika samu? Eh mace mai koshin lafiya, a dakin haihuwan kuma ke kadai suka saka ko kina da makociya? Ni kadai ce, dalili? Na kudine kawai zai iya zama hakan, sai dai idan ranar ba’a samu masu haihuwa da yasa ba, nan ma tsit tayi, inaga matsayina suka duba ta fadi cikin jin kai, aka bata izinin zama sannan aka umarci madam Zarah da ta karasa gurin tuhuman da Kaulah ta bari, Kasaitaciyar mace mai cikan zati da haiba wace kallo daya za kiyi mata ki fahimci cewan taci kuruciyarat, irinsu a zamanin ‘yan matancin su ,sun ci duniyarsu da tsinke, da takun takama ta karasa inda ake nemanta, idanuna akan muhsin naga yayi murmushi yana girgiza kai, ko me dalilinsa? idanunta manne da glass na gayu kawai sai gum da take taunawa yayin da take kallon ilahirin mutanan hall din, zaki iya shaida wa kotu ko ke wacece? Ni ce Madam Zarah mace mai zaman kanta, ta karasa fadi tana ciro glass din idanun nata, na gaji arziki daga iyayena kowa ai yasan daura tavel and tours? Hayaniya ya dan kaure shima da kyar aka tsahirata sannan ta ci gaba, a nan nake samun halal dina, a maganar ki baki shaida mana kina da aure ko kin ta6a yi ba amma gaki a rikicin baby hameedah, shin zaki iya gaya mana kotu waye mahaifinta? Ras Naji gabana ya fadi ,Allah ya isa indai kika tabbata uwata na ayyana a raina, ta soma fadin eh wanda yayi cikin ya rasu ,likitanane doctor Nataniel ,ina da cikinta ban kai ga haihuwan ba ma ya mutu, ok a takaice dai shegiya kika haifa? Objection my lord, Mushin watch ur tounge cewan bala sumaila, ya amshi kuskurensa sannan ya ci gaba da cewa kafin haihuwa fa ina kika fara awo? Ta dan juya gum din bakin tamkar kilaki sannan ta ci gaba da fadin na soma awo ne a Trinidad, daya daga cikin kashashen da nayi rayuwata, da tafiya ta kamani na koma Germany can ma nayi awo sannan na kai wa wata kawata ziyara a Kd inda nayi sati 2 a nursing home na dan yi awon kasancewar tana kusa ne da gurin, da nakuda ta kamani munje babu gado suka turamu dutse hospital din, a can Kaulah ta kar6eni na haihu ta hanyar CS har na samu tsawon kwanaki ina barcin wahala, da kika farka fa? Wani jinsi kika tarar na babyn ki? Ni ban ma samu wannan damar ba,why? Na tarar da babyn babu rai wai kuma an cirota a gawa aka birne min tunda ban farka ba, naga gawar cikin tashin hankali, din haka ban kula da jinsin ba, wani irin mataki kika dauka a can baya? Kotu na mika karar kaulah ta gudu, objection my lord uzuri ne ya sanyata ketare kasan, kaulah na da dangi a can don haka zumunci taje yi, ya kada kai kawai sannan ya bata daman komawa gurin zamanta. Bala Sumaila ya umarci Kaulah da tashi ,ta karasa inda wanda ake tuhuma ke tsayawa , ya soma fadin kotu tana san Sanin dalilin zuwanki Ghana, ta karasa ta numfasa gami da gyara tsayuwa sannan ta fara da cewa kakata a can gahana take, dalilin zuwa kuwa ba wata mai tsauri bace ila canza ra’ayin zamantakewar da zuciyata ta samu, saboda samun ci gaban yarana su saba da can tunda wanda ya zama dolensu(mahaifi)ya rasu, a can na ci gaba da aikin midwifery dina don dogaro da kai, objection my lord cewar lauyana, Kaulah bata bi due processes na Neman izinin Baron aiki ba, My lord muhsin bashi da daman kure client dina wannan dalilin ne ya sanya alkali buga gudumarsa ya tashi kara akan sai sati na sama(sati 2 masu zuwa kenan), na mike hannuna cikin na mummy duk yanayina ya sauya wannan dalilin ne ya sanyata rikoni muna takawa a hankali, tamkar jira ake a tashi karar sai ga ‘yan jaridu sun rufemu dole tasa muka koma ciki sai flash ke tashi suna daukanmu hotuna, daga bayana naji muryarta tana fadin wounderful, my baby is all grown up, Na watsa mata idanu sannan na kai idanuna kan mummy tare da fashewa da kuka, ban son ganinta ta 6ata min suna, muhsin ne ya karaso yanai mata bayani, madam Zarah its matter of tym, kwantar da hankalinki gaskiya zatayi halinta, ku mike in fitar daku ya umarcemu, mummy ta dauramin Niqab sannan ta gyara nata mayafin ya dan rufe mata fuska,a motarsa muka bar harabar kotu, daga nesa kadan yana iya hango mutumin daya kira kansa Abdullah Buba jingine da wata shegiyar mota ubansu yana lalatsa waya fuskarsa babu walwala,ya kalli mummy a fakaice, hankalinta Sam bai he gurin ba ,hirar batun kotu take ita da muhsin da alama bata kula da abin da ya hango ba, toh Anya ba sharrin zuciya bane ke kunsa masa zargin mutumin ba? Kar fa in tada zaune tsaye,wata zuciyar ke raya masa, Baby kin yi shiru watsapp? ta yi mani tambayar tana leken fuskata, da kyar na tattaro jarumta na yi yake ina yamutsa fuska sannan a shagwa6e na ke fadin mummy kinai min addu’a? Ta fashe da dariya don kawar da damuwata, come on honey, my sweet sweet chochomilo, my angel idan ban maki ba wa zan ma daya rage mani? Daddynah, mummy shi din ma yana bukatar du’a, yanayinta naga ya sauya sannan a sanyaye ta furta never baby daz d most wounderful abin da na rasa a rayuwata, nan da nan idanunta suka kawo kwallah, na tsira mata idanu cikin tunani mai rikitarwa, mummyyyyyyyy, na ja sunan cikin alamun rarrashi, ta gaza amsawa da gani na tabo abin da take dannewa, mummy Allaah’s willing it would come 2 pass, na rike mata hannaye 2 ina lallashi, mummy chill, smile, hmmm kali fa lauyana na kallonmu, duk muka fashe da dariya, na gyara zamana a rashin sa’a muka hada idanu da shi ta madubin gaba yana kallona, ya daga mani gira yana murmushi, daga gani shi kam nishadi yakeji, nayi saurin kau da kaina ina kallon motocin gefan titin, muna is a gida mummy ta five abinta, ina niyan sauka naji yana fadin hameedah can we talk? Na tsaya cak mummy ce ta shige cikin gidan ya fito ya karaso gareni gami da bude mani kofar,na sauka a nutse amma zuciyata fal take da damuwa, shi din ma yau sai naga duk ya sauya mani, kina takura kanki da yawa why? bai bani damar amsawa ba ya ci gaba da cewa zo ki zauna baby, ya fadi daidai sanda ya budemin mota gidan gaba, na Dan kalleshi da niyyar magana na dai share gami da bin umarninsa, zaunawa shima ya zagaya ya zauna sannan ya umarceni da rufe kofar, ba tsammani naga ya ja motan ya fita sai na bi shi da idanu, a wani hotel ya saukemu sannan ya budemin kofan muka karasa haraban gurin, me muke yi a nan lauyana? Zauna yace min gami da janyo min data daga cikin kujerun da aka zuba a gurin, sannan ya je ya kar6o mana drinks,ni kam ice cream ya lodo min, murmushi nayi cike da mamakin inda ya samo labarin ni mayan ice cream ce, tank u, na fadi ina dan sha, Hameedah Abdullahi Buba! Furucinsa kenan, na daga idanuna ina kallonsa,In Shaa Allah u a d fruit of d innocent souls(Rahma da buba ya ayyana a ransa),na daga gira cikin rashin fahimta, kai kwanyanka bata tsahirtawa sam, kullum aiki, ina zaka aiki, me kake ? Aiki, daga ina kake? Aiki…. Ya katseni yana murmushi, funny you hammy, mummynki bata ta6a nuna maki hotan dadyn naki ba? Na girgiza kaina ina juya cokalin ice a hannuna, bakisan looks dinsa ba? Nahi na fadi ina dariya(to ashwariya), hmm ina son mu zama team zai yuwu? why not? in dai zan rika shan ice cream zan complying, yayi dariya gami da cewa toh ai ba a bani kazar grad ba ma, is too late dear na fadi ina goge bakina da tissue, no campaign after election, yayi murmushi yana girgiza kai sannan yaci gaba da cewa, Gud, keep close watch kan mummy, kuma ki ja seemah a jiki zan samu lokaci inji feed back din,ok? Na gyada gira ina shan ice abuna, oh hammy baki da matsala yau, haka dai kace , yace exactly haka na gani, muje in maidaki gida ko? Ya saukeni yana daga min hannu yayin da yake fadin ki daure kinji? Kar Seemah ta firgitaki dole ki samo wani abu game da ita, na gyada masa kai sannan na shige cikin gidan, mummy nata kallon taurarin dan adam, mummyna na fadi bayan gaisawa a tsaitsaye ta bini da idanu tana dariya, baby yau ma ice din aka sha? Nima dariyar nake ina isa na dasa barci don hutawa zuciyata cike da tunanin dalilin da ya sanyani cusa kaina ga Seemah, na dan ja tsaki ina kada kai, ban da so makaho ne me lauyan zai yi da Seemah, kyan dan maciji sam bata da hali, na gyara kwanciya har ban san sanda barci ya daukeni ba…
Daga nan hotel room din ya nufa(sheraton)inda sukayi zasu hadu da Abdullahi Buba don tattauna case din data sanyashi gaba, shi kansa bai ta6a handiling case mai tsaurin wannan ba, at times yakanji tamkar ba zai yi nasara ba, sai dai kafiya da naci da suke dada tunzurashi, gani nan a reception ya fadi sannan ya katse layin, ba jimawa mutumin ya bayyana, sosai kamanin ke dada bayyana kansa, mummy Rahma choculate colour ce, Abdullahi Buba fari ne sosai, yayin da baby can be classified as a half cast, why is all these crossing my mind? tabbas akwai serious resemblance tsakanin mummy and baby, yeah daz Truth but… sallamarsa ce ta katse masa tunani,suka yi musabiha sannan ya jashi zuwa inda akwai karancin mutane,seemah kuma fa? wata zuciyar ta ayyana mass, Me dangartakarsu? Alhaji Buba yayi gyaran murya gami da cewa kana da alkawari ,da sauri ya daga idanu ya kalleshi yayin da buban ya daga gira yana murmushi, Subhanallah, she smiles just like him, sakin baki yayi yana nazarin da har ya wuce gona da iri bai ankare ba saida ya dan bige masa kafada, what if its coincident ? cewan wani 6ari na zuciyarsa, ya Dan tattara nutsuwarsa yana murmushi, ina son muyi wata magana amma its confidencial ok ,bismillah lauyana,wannan ma irin furucin hammy ne, ya kake ganin zamuyi ne? Duk matsalar daga gareka take Alhaji, an shaida maka ranar zuwa ka mance ne hala? Lauyana hmmm harkokina ba masu sauki bane, gani mai karancin lafiya, tun yana hawan jini yanzun na koma treating din zuciya, da ka sanar da iyalinka zata tuna maka ai, yayi yake gami da cewa ba iyalin ai, what? Yes hakan nake nufi, am single, ya tsira masa idanu na tsawon wani lokaci cike da mamaki to ko me dalilinsa,Shin me makoman Seemah? where does she belong? Why do they shear characteristics with hameedah? su waye iyayensu? madam Zarah is light in complexion, the 2 gals hv same skin colour with her, what about resemblance? furucin Alhaji Buba be ya katse masa tunani, kana mamakine? Yes of course ko dai baka da lafiya ne? Yayi murmushi mai ciwo sannan ya kara da cewa ko daya, yanzun haka ma da izainin Ubangiji akwai gudan jinji na a doron kasa, ban gane ba, na ta6a aure a shekarun baya, inaga if am not mistaken, kusan 19yrs back kenan, to rabuwa kukayi ko mutuwa tayi? Wata kaddara ce mai karfi ta gilma tsakani, ban saki matata ba lauyana, tafiya nayi da yake tun can baya ni mafataucine, nayi karatu har diploma amma babu aikin dogaro da kai kawai nakeyi, wata tafiya da nayi 6arayi suka taremu a hanya mu, dan abin da muka rike na kudi da guzuri suka kwace, ganin bai gamsar dasu bane ya sanyasu yi mana dukan mutuwa, tsawon sati 2 muna cikin wannan halin, ni kam kwana bai cika ba da tsawon rai gaba, wani attajiri ya tsincemu a dajin nan, an fidda ranmu, shima yace motarsace ta lalace aka tsaya gyara shine ya shiga dagin fitsari, sauran 2 tuni sun cika sai ni din ma bana numfashi, sai a asibiti aka tabbatar ina da rai, aka bani taimakon gagawa, tsawon sati 2 aka dauka ana bani kulawa , Professor Isah Bawa babban attajiri ne da ya mallaki dukiya na ban mamaki, asalinshi dan Jihar kano ne, amma yana zaune a lagos, Yaransa 2 ,amma ni guda 1 na sani, dayan ya rasu tuni, matarsa ma da sukayi auren buduruwa da saurayi ta rasu tuni, ance gurin haihuwa ta cika, bayan shekaru da rasuwarta ya auri mataye 2 amma Allah bai yi zasu samu rabo ba, bai yi dace ba duk ya sallamesu, arzikinsa suke kwadayi ba don Allah suka aureshi ba, cikinsu har da mai shirin hallakashi taci gado, a Lagos na zauna da shi( doctor Isa Bawa)dan boko ne na garari, dansa ne muntarin da kuke tuhuma, ya hadamu bayan na warke amma hankalina na ga matata da na bari da tsohon ciki, bayan na warke sumul na koma kaduna don ganinta amma hakan bai yuwu ba, ba kowa a cikin sashin da muka zauna, na samu labarin mahaifinta da yayi mana saura cikin yanuwa ya rasu bisa wannan dalilin ita kuma ta bar garin, na yi yawo cikin naija ko zan dace har na gaji na koma, lokaci lokaci nakan dan dawo in bincika amma shiru kake ji, yayi ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da cewa to ina labarin cikin da ka bari? Ko a can gidan da baba ya zauna da ba mai labarin hakan? Babu saboda ba wanda yayi mani wannan zancen, tun ina sanya rai har na sare, akwai taimakon da zan iya yi maka amma tukuna dai kafin nan zan so ka zama currrent a labaran kasa, in kuma ba dama ka saurari radio ko yawan duba daily trust In Shaa Allahu za’a dace, wayarasa ce tayi ringing ya dauka gami da karata a kunne, tsawon seconds 40 amma ba zai ce ga abin da mai kiran ke cewa ba, ya katse wayar yana fadin akwai aiki a gaba na Alhaji ka min hakuri gashi sai nemana ake tayi, matsalar ntwk ne, ban jin abin da mai kiran ke fadi, ya dan ja tsaki gami da katewa yayin da ya soma cewa amma wani hanzari ba gudu ba,misali yanzun Rahma ta bayyana zaka maidata ? Yayi murmushinsa gami da cewa why not? Idan ka samu tayi aure fa? lauyana bar wannan zancen, ita alkhairi ce a gareni kuma Allaah’s willing zata koma gareni, ina son yara sosai amma…. Kwallan da ya dade yana dannewa suka kawo ,wannan dalilin ne ya sanyashi yin shiru yana mayar da numfashi sama sama tamkar za’a zare masa rai, a kidime Barr Muhsin ke fadin lafiya ? Lauyana, ya fadi cikin radadi yana waro idanu cikin yanayin ciwo, am fyn barni kawai kayi tafiyarka is nt a new thing, I have to go and I can’t leave you like this, what is your room number? ya fadi yana rintse idanu, Barr Muhsin ya taimaka masa, a daddafe suka karasa dakin India IB ke kallon kungfu movie, ganinsu ya sanyashi saurin mikewa gami da lalubo mass magunguna, saida ya tabbar ya dan lafa mass sannan ya fice IB nayi masa godiya…
[5/16, 2:48 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
8…
Nutsuwa yayi cikin motarsa yayin da abubuwa da yawa me masa yawo a ka, madadin ya tayar ya wuce sai ya bige da warware wa zucuyarsa yanda zai tafiyar da wannan lamarin, ga alamu sun nuna kuru kuru amma yana neman evidence da zai kama don tabbatar da wannan labarin a kotu, ya ciro recorder ya kasheta ko ba komai wannan ma zai dan fito da batun, kai tsaye office ya nufa inda zasu hadu da wasu client dinsa…..
Kwaliyar na share lokaci mai tsawo inayi, baby !muryar mummy ce mai wannan kiran, bata bani damar amswa ba ta ci gaba da fadin naji shiru ko dai kin fasa fitan ne? Gani nan na fadi ina gyara zaman takalmina mai tudu da kyan daukan hankali, na karasa inda take zaune tana kallon hanyar da zata sada mutum da sashina, ta nan na bullo ina takun daukar hankali, marvelous amma shi wannan mayafin ba haka zaki masa ba ai, zo in gyara maki, sai ina? Ta fadi tanai min kallon tuhuma, cikin Kubwa fa zan shiga, OK dear wajan wa kenan? Na cinno baki gami da cewa Seemah, gud yaushe kika koyi kau da kai? Mummy Allah zan fasa, sorry na daina to, dauko purse da waya in ba zaki dauki jakar ba, ban son kina fita babu ko sisi kar abin kunya ya faru a hanya, na dauka fuskata sanye da niqab ,tare muka fito inda take dada jadada mani cewa an canza min driver, ta sallami baba ilya saboda tsaro,muka karsa inda mortar take,wannan karan ba taxi bace, motace ta gida ‘yar karama , amma driven asali dan taxi ne aka dauki hayarsa na tsawon wani lokaci, har sai an gama case don tabbatar da lafiyta, mun gaisa sannan ya tayar muka bar gurin ina daga ma mummy hannu, shiru ya ratsa sakaninmu, ya mayar da hankalinsa kan tukin yayin da na lalace gurin lalatsa wayata, lokaci lokaci nakan daga idanu don ganin inda muke, Bilal pls drop me for this place na fadi yayin da nake nuna masa addres din, small madam u luk gud dis morning o, thanks kawai na fadi ina jin dadin yanda ya yabi kwalliyata, zuciyata tana kaunar a yaba kwalliyata,a haka muka karasa gidan, wani dankarere gini ne ni da Bilal din muka kalli juna sannan na kau da kaina cike da tunanin ko in fasa shiga ne? Mamaki ya hanamu karasawa ciki, na tuno kalaman Muhsin”hammy mai jin zafin ciwo shine mai rai, mai jin zafin ciwon wani shine mutum”,ki kokarta ki zama daga masu ceto rayuwar wasu daga hatsari ko 6arna plsss, Seemah is blind ke ce fitilarta understood? Ya fadi yana kallona, na gyada masa kai don kawai a wuce gurin ba don na gane ba, me nawa ? Don tani ta mutu a makance mana, small madam make i go inside? Tambayar ce ta katsen tunani, yes proceed, yaja muka karasa bakin gate yana horn, wani dan tsamurmuri ya leko da uniform yana fadin can i help u? Bilal ya sauka yanai masa bayani ina zaune ina jiransa, sai gashi ya dawo a sanyaye, small madam den asay make u call am, takaici tamkar zuciyata zata buga, Seemahan ce sai da izininta zan shiga? Kiran Muhsin ya shigo wayata, na daga ina fadin lauyana ni fa na gaji awan mu kusan daya mai gadi ya hanamu shiga wai masu gidan basu san da zuwan mu ba, ok chill baby cewarsa, plsss kirata ba don na isa ba, haka dai na katse wayarsa na kira ta Seemah itama wucewan mintina ashirin no answer.
Na dan yi jugum ina nazari daidai sanda wata kayataciyar mota ta kunno kai gidan cikin rawar jiki mutumin da wulakancinsa ta 6atamin rai ya wangale gate din, nima da gadara na sauka a kafa na shige gidan, ina ji yana fadin hajiya ashe kece? Ban tanka ba, inaga ya zaci Seemah ce ,motar naga an bude da sauri ‘yar yarinya mai kimanin shekaru 6 ta taho da gudu ta rungumeni tana fadin Aunty See nah ce, nayi turus ina kallonta,ta rike min hannu mukayi cikin gidan ni dai kallonta kawai nake sai binta nake don na rasa ta cewa, a haka muka 6illa ta wani palo na gidan, ta kuma sanya kai cikin wani sashi na gidan mai girman gaske, muna ta ratsa dakuna masu kyan tsari sannan daga baya naga ta tura wata kofa tana kyalkyala dariya, yau na kawoki sashinki aunty See ta kuma doka tsalle sanna ta karasa tura kofan tana ‘yan surutan da sam hankalina da tunanina bai kansu, dakine na kece raini, tarkacen da za’a iya dangantasu da na ‘yan mata sune cikin hadadan dakin, sai wata hadadiyar gado mai girma da kyan tsari mai yanayi da italian bed amma kuma ba shi bane, na natsu ina kallon wace ke kwance tsakiyar makekyan gadon lulu6e da bargo, yarinyar mai karadin tsiya ke fadin ina zuwa sannan ta fice da gudu ta rufe kofan ya bada sauti mai kara sosai ji kike garam, firgice naga ta farka tana fadin who is that idiot? Tana mitsitsike idanunta, karaf idanunta a kaina, ke kam baki da zuciya kin hanani barci salon ki karar mani da charji? Na dan yamutsa fuska sannan na ja tsaki, ta mimike a kan gadon tana ta masifa, haka nan kurum an hana mutum rintsawa, ni kam ina nan na ki tankawa gudun kar mu tara ‘yan kallo, ta sauko na matsa daga hanya ta fice, ba jimawa sai gata ta shigo lokacin karfe tara na safe kenan, ina kallo ta shimfida sallaya jikinta kayan barcine a haka ta dora hijab iya tsintsiyar hannunta har ban san sanda na saki jiki kan gadon ba, mamaki ya kasheni a gurin,wannan wace iriyar rayuwa ce? kafafunta a waje ba abin da hijabin ya rufe mata , riga da wando ne jikinta ,cotton iyakan wandon gwiwarta, Sallar ma ba ta wani bashi hakinsa ba, dama ta kosa ta sallame ta kwa6a min abin da ya samu na bakar magana, ai kuwa tana idarwa ba addu’a, ta ci gaba daga inda ta tsaya, ke uban wa ya baki izinin shigowa ne? uwarki bata koya maki cewa ba’a asubanci zuwa gidan wasu ba?Na tsira mata idanu ina kallon iya gudun ruwanta, bakin ciki tamkar ya kasheni, ta ci gaba da fadin magana nakeyi, na danne bacin raina gami da cewa to Uwata, kya bari ai in kin haifa sai ki yi mata wannan tambayar, na fashe da dariya sannan na dora da cewa barcin wahala kike don bazan dangantashi da hutu ba, banko kofa akyai daidai sanda ta wurgo mani wayar hannunta nayi maza na tsugunna ya daki mirror, yarinyar dazu ce, a tsorace naji ta saki kara, ba karamin razana tayi ba tana kwala ihu, mumsy ga aljanar aunty See tana fasa mana gida, wayyo Allah na, na kuma kecewa da wata wawiyar dariya, na kula dariyace abar dake kunna ta,wannan karan mikewa tayi cikin zafin rai ta karaso gareni, sannan ta fizo hannun damata tana ja tamkar zata rabashi da gangar jikina, naki kulata sam, sai ma mahaukaciyar dariyar dana ci gaba dayi tamkar sabuwar kamu, sai kin fita wallahi tunda ba gidan govt bane, sai na hankadaki waje ,ai ba gidan marayu bane da zaki zo ki baje kina haukanki, daidai lokacin matar gidan ta bayyana, mace mai yalwan jiki da kosashiyar ce, ga tsawo daidai burgewa tayi shiga na fari da jan leshi wayanda suka kawaita halitarta, princess! Me naji Rihab na fadi? Bata kai ga bata amsa bama naji ta dora da fadin oh shet! What d hell is this? Na shiga uku, na mike gami da tureta ina tattara ya nawa ya nawa, takalma na ma a hannu na debo su, wayata na ringing, na dan duba kiran driver na ne(Bilal), young lady, who are u? wannan itace tambayar da tayi min,Na zaro niqab dina daga purse ina wuri wuri da idanu, her guest,na fadi cike da fargaba, ita kam wace aka kira da princess tayi biris ta ki tanka mana, u are welcome, cewarta cikin fara’a ,mumsy she broke my phone,mirrow and….ta fadi tana wani narkewa, sweethrt (mijinta)will soon be home zan kirashi ya taho maki da su, lallai yarinya yau naga inda ta samu tarbiyar banzanta, na daga wayar gami da cewa 2 min, don dama nace masa bazan dade ba, matar nan ba yanda bata yi in dan huta ba naki, duk na kosa in koma gida kawai,wannan dalilin ne ya sanyata rakani, muna fita bakin gate muka ci karo da Kaulah, hajiya Ni’ima in fita zakiyi ki jira akwai magana mu yita da dumi dumi kafin next week(ranar komawa kotu),ta dan yi mata alama da idanu sannan ta kara da cewa guest din princess zan raka, sai a lokacin tayi arba dani, Subhanallah naji ta fadi a kidime, sannan ta wayance tana fadin oh hakane fa, ni kam na sha jinin jikina da 2 lauyana ya turoni, muhsin is too smart na ayyana a raina, sannan ta jani muka karasa inda Bilal ke jirana, na hau muka bar gurin sai mayar da batun gidan muke,madam i dey worry i tink say dey don komot ur head,ni kam abin sai ya bani dariya ma, mutumin yaci gaba da cewa, Buba ka dauka taka kaddarar kenan, idan Rahma tana raye zaka ganta , ta sha wahala sosai bayan tafiyarka, mama ta gaya min cewa ka zo sau 2 amma Allah bai yi zamu hadu ba, lokacin na samu scholarship zuwa Malaysia inda nayi degree dina ,am happy for u dude cewarsa yana dan bubuga kafadar abokinsa Abu (Abubakar), Wanda suka taso tare tun kuruciya, lallai ka zama bature Buba, har turancin ma da komai, harshenka irin nasu, zo mu zaga kaga guri, hayin Dan bushiya da kadaure sun sauya, gwamnatin Kaduna na shekarun baya sun mana aiki, I’m nt in d mood cewarsa yana yamutsa fuska, IB dake bakin ruwa(rafi) yana selfie ya soma fading Uncleeeeee cikin tsabar farin ciki, yayi dariya gami da cewa that little brat have no worries, suka tsintsire da dariya suna kyakyatawa, amma Buba baka taba ajiye min contact dinka ba, am sorry, I never thought of it, yanzun ma ba don na ce ina neman gidan mai garin kadaure ba da na bace a hanya, IB ,ya kwalawa yaron kira cikin daga murya, sannan ya ci gaba da fadin let’s get going its getting late, sukayi musabiha da Abu bayan sun exchanging contacts, ya bi ta malali don ficewa daga layin India zasu bi hanyar abuja,a bakin gadan Abu ya samu adaidaita ya wuce gida cike da murnar ganin abokin nasa, ga kudaden daya cika shi da su, fatansa Allah yasa yaga Rahamar daya fito nema…
Hotel room service din ne ya shigo ya ajiye jaridu na week din gaba daya bugun daily trust sannan ya fice,fitowar Alhaji Buba daga wanka kenan , jikinsa sanye da white bathrobe yana tsane jikinsa don kammalawa yaje yaga likita, IB miko minsu pls zuciyata tana bani akwai alheri a wannan zuwan namu, cewarsa yana kallon inda papers din suke, ya kwso duka ya ajiyesu a gabansa asannan ya tura masa table ya dorasu a kai, a hankali yake dudubawa yayin da shayinsa mai tiriri ke gefanasa yana dan kur6a, ya ja dan guntun tsaki ganin har lokacin ba wani labari da ya shafeshi, ya saki cup din shayin ta tarwatse daidai sanda ya kalli sub headin din, sannan ya mike zunbur ganin hotunan da ake zuba bayanai kansu, zuciyarsa ce ta hau harbawa da sauri ya jefar yana ta safa da marwa, Rahma Rahma Rahma ya rinka furtawa yana rintsa idanu, Rahmarsa ce kuwa? dama a kullum ya tsananta tunani da bincike kanta sai ta rika yi masa gizo ,IB ya mike a firgice yana fading Uncle are you OK? am fine cewarsa yana tattaro nutsuwarsa.
IB ne ya dafeshi da kyar ya samu ya zauna yana jero masa tambayoyi, Uncle lafiya? Uncle you are hiding something, Ya jijiga shi yana dada fadin uncle ko ka ganta ne? Tsabar yanda rayuwarsa ta canza har IB dan da ke shekaru 13 a duniya ya san matsalarsa, jin ya ki bashi amsane tsabar kidima ya sanyashi tattaro newspapern yana fadin uncle to me ya firgitaka haka? Ya zuba idanu shima yana dudu bawa, can ya karanto shafin da uncle din nasa ya gani ,ya natsu sosai jikin shi nabashi cewan akwai labarin rahaman a ciki tunda gashi ya damu sosai har yana danganta yanayin da na can baya, Rahama Abdullahi Buba shima ya gani 6aro6aro rubuce a shafin da tayi bayani kan yanda baby hameedah tazo gareta, kasan hotantane wannan ne ya sanyashi mayar da hankalinsa ga bayanan da suke dayan shafin inda ake fadin sati na gaba za’a ci gaba da karar, uncle kaje ranar juma’a zaka ganta In Shaa Allah, ya dan muskata cike da zakuwa yake fadin ina da yakinin na bar da a doron kasa, ya mike zumbur tamkar wanda aka tsikra gami da cewa babyna ne, uncle baka nan fa ya zakace naka ne? Ya dafa kan yaron yana girgiza kai, manta kawai IB bazaka gane ba, amma shari’a yanzun aka fara,ya karasa fadin maganar yayin da yake ficewa, Uncle! Uncle!! Uncle!!! Amma bai tsaya sauraronsa ba ya fice abinsa, Yaron da ya gaji sai yayi shiru abinsa…
Motarsa ya shige don a irin wannan yanayin, yafi son kadaicewa, zuciyarsa tana kuna, fatansa Allah yasa ba karyar data saba karanta masa bane, ya daki sitiyari yana fitar da huci daga bakinsa, so yake ya tabbar da abin da idanunsa suka gani, yana son jin muryar da zata ce masa it’s true, it’s real, everything will fall into their places,amma all these are illusions, its impossible wani sashi na zuciyarsa ke raya masa,Ya kife kansa a kan sitiyarin yayin daya zurfafa tunaninsa,idan akayi la’akari da kididigan babyn dalokacin barin gidana zuwa yau da shekarun hameedhar u would arrive at da same answer, why? Ina son ganin yarinyar ,i wnt to see her ,ya furta a sanyaye,ya sanya hannu ya goge hawayen dadin dake silalo masa a fuska, lallai sanu sanu bata hana zuwa saidai a dade ba’a je ba,wata zuciyar tace to idan an samu akasi fa? Never, cewarsa ya kuma mikewa zunbur yana muzurai shi kadai, sannan ya sanya kai ya koma dakin da suka sauka…
Hmmmmmmmmmmmmmm kaka kara kaka…
[5/16, 3:10 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
9…
A hankali sautin wakar ke tashi, shigata cikin bakar doguwar riga mai kwaliyyar fararen stones, na kewaye fuskata da dankwalin yayin da fuskata ke dauke da light make up, na karasa gaban spearkan gami da kara volume Ina juyi, a nan na lalace Ina rawar I LOVE YOU MAMA , shogowar su yusrah ne ya hautsina Palon ,abinka da ‘yan mata muka soma shewa da rungume juna kasancewar an jima ba’a hadu ba, Sweet sweet mummy bazan barki ba sam, na karasa furucina daidai sanda na rungumeta ina dariya, hhmmm naji to kya tashi muje ko? Allah mummy kin min sutura, naji zaki wuce ko in cici6eki? Na daga kafa ina murmushi duk mukayi waje, Allah na gaji da wannan shari’ar gara ayita ta kare, baby yau me kikaci ne haka? cewar Saima tana dariya,Sai surutan tsiya kya saurara ko? inji mummy tana miko mani black skin slippers dina, Muka shige mota yau karar da ‘yan govt house za’a saurareta, ga mama kulu da abdujabbar da mijinta, ministan tsaro dana ilimi da dr fareedah ‘yar kwalisa, ga kadan daga cikin gwamnonin jihaho duk sun hallara, na ware idanu so nake inga muhsin amma bai karaso ba don sammako muka doka, duk sai naji ni a takure, inda hali so nake in masa wata tambaya ,a hankali kotun ke cika ba jimawa sai ga isowan hajiya ni’ima,madam zarah daga gefe guda kaulah ce, na sada kaina kasa zuciyata tana kuna, wayarsa ce ta shigo mani na karata a kunne, are you around? tambayarsa kenan ,na mike ina fadin mummy lawyerna na nemana a waje, ta kalki agogin wayarta gami da cewa be carefull, na fice da dan saurina don isa inda yace in sameshin, a jikin motarsa yake yana dadanna way a ,a raina na ayyana haka dai kullum, aikin kenan, gaisawa muka tsaya yi daidai sands wata mota kirar da ban taba gani ba tayi parking daga nesa kadan, hankalinsa na kaina ya soma fadin I wnt to hear every detail, hankalina na ga mortar da naga an bude gidan gaba gami da zuro kafa, wani yaro mai yanayin black Americans ya sauko ,shigarsa cikin jeans blue da jacket, da take grain da dn sanyi, ya juya din ganin abin daya dauken hankali, labarin yanda mukayi da Seemah name bashi kafin cikar lokacin case dina, hankulanmu na ga tattaunawar muka tsinkayi among muryarsa yana mana sallama cikin kamala, wannan ne ya katse hirar, suka soma gaisawa ni kam juyawa nayi zan bar gurin mukayi karo, na Dan dakata gami da waiwayawa, black American din dazun ne, tare suke da mutumin, I’m…. I’m… so sorry cewarsa yana kokarin dauko Mani wayar dana jefar, sorry hameedah cewar Barr muhsin, IB walk with focus cewar mutumin sannan ya kara da fadin baby are you OK? wannan furucin be ya sanyani waiwaya gareshi ina fadin am fine, IB go and wait in the… maganar ta makale daidai sanda ya daura idanu kan yarinyar, ya saki baki yana kallon halittar da ko a mafarki yasan asalinta, kamewa yayi a gurin yana wassafo yanayin Rahma da wannan , kafin yayi wani yunkuri tuni ta bace masa, Hameedah Abdullahi Buba? ya tambayi kansa yana bin inda yaga tabi da kallo, ni kam ina gurin mummy muna jiran cikar lokaci, mutumin na min yawo a ka,kila ma ba ‘yan naija bane na furta a hankali,may be kasarsu zasu koma cewan wani sashi na zuciyata, na dan ja tsaki cike da damuwa,baby! Ta fadi tana dan bubuga mani baya, lafiyanki kuwa? Kwala suka kawo idanuna yayin na ba gaira ba dalili, wat is it? na tsinci kaina da cewa ban ga Muhsin din ba, sai naga tana murmushi daidai sanda alkali mai sauraron karan ya shigo duk aka mike, a lokacin na hangi shigowan lauyana na 6ata rai ina harararsa,ai kuwa nayi sa’a ya waigo muka hada idanu sai naga yana girgiza kansa fuskar dauke da fara’a ya karasa inda suke zama, Sai naga ya dan sha mur, Kai muhsin yasan makamin aikinsa, too smart, gashi da foresight, aka soma gabatar da karar na yi jugum ina kallon sa, haka nan kurum naji ina bala’in sha’awar karanatar law, ko me dalili? bayan wasu ‘yan gabatarwa da akayi ,aka cigaba daga inda aka tsaya, Kaulah ce akae wa tambayoyi, me ya sanya kuka birne mata baby ba tare da amincewarta ba? Ta yi karaf tana fadin babu wani nata a kusa kuma gudun kar a barta dashi tana cikin wani hali, kuna da mutuwary a Kaduna wannan ma ai ba dalili bane, objection my lord cewan bala sumaila, alkali ya daga masa hannu ya ci gaba da cewa suwaye shaidun ki gurin birnewa? Shiru ba amsa, mai girma ya kamata ka fahimci cewa kage ne wannan shirya labarin akayi, kotu ya dan dau hayaniya aka lafa sannan naji yana fadin madam zarah tace daki daya kuka sata da Rahma actin mummy din baby hameedah, eh cewarta, to me dalili? Tayi tsiru tsiru sannan naji tace bamu da wata manufa, gud, tunda kika zargi kanki akwai manufar kenan, kaman yanda acting mummyn ta shaida wa jama’a cewar madam zarah tana barci kuka kai ta uku dakin masu haihuwar, itama lokacin tana dakin tare dasu kafin ta samu sallama, shin zaki iya gaya wa kotu ko wacece ta ukun su? Haj binta ce, tana sauka ta tura masa haji Bintar don amsa wasu tambayoyi itama, zaki iya gaya wa kotu ko ke wacece? Mace ‘yar takama da fadin rai mai kalar hutu ta soma fadin sunana Binta Idris, mata ga dr Mahmud,ko zaki sanar damu dangartakarki da kaulah? Eh kaulah aminiyace a gurina, ya akayi kawancenku ta samo asali? Tare mukayi karatu a jami’ar bayero, lokacin ina karanta fanin harshe(english) ita kuma tana karanta aikin data rayu akansa,’ya’yan ku nawa? 1 kawai Allah ya bamu ( Hameedah), ko kuna da family doctor? Eh ada can akwai asibitin da muke zuwa amma tunda kaulah ta kama aiki muka mayar da kusancinmu, gud cewarsa,mijin ki fa? Baya kasar,dalili? Ya tafi special assignment egypt,ok kina iya sauka, ya nemi mummyna ta karasa gurin don shaida abin data sani itama, ta gyara zaman gyalanta tana sauraronsa, ya sunan malamar? Rahmah Abdullahi Buba, me alakarki da ‘year da ake rikici kanta? no na raineta, shin zaki iya sanar da kotu yanda akayi kika haifi ‘yarki, na raini cikina na tsawon watanni 9,da nakuda ta kamani abin yazo da gardama aka kaini asibiti cikin matsanacin hali, a haka na haihu ba cikin hayacina ba, ina zaton cikin alluran da akayi mani akwai na barci, don barci mai nauyi ne ya daukeni sanda na farka na sami jaririyata a gefena an lulu6eta da dankwalin taufafin jikina, kaulah da kanta ta ce maki ‘yar da kika haifa kewnan? Eh, mijin ki fa? “gashi nan” itace furucin da akayi cikin daga murya, kallo ya koma sama, na saki baki ina kallon hanyar shigowan, faduwar da naji ya sanyani saurin waiwayawa, mummyna ce na gani a kasa warwas, da sauri jiki na rawa na karasa gurinta ina jijigata, kotun ya hautsine da surutu lauyana ke fadin Alhaji Abdullahi Buba ba’a zo kan karar ku ba ai, yes, nazo claiming diyata da Rahma ne cewarsa, ya karasa fadi yana dukan kirjinsa, wannan ya sanya dukanin mutanan cikin gurin mikewa da sauri yayin da hayaniyar ta fi ta baya, na maida idanuna kansa ina kallo ba tare da na fahimci matsayin da zuciyata ke ciki ba, wata sabuwa ,ni naga ta kaina, tawace ta sameni, dama duk wanda bai san asalinsa ba haka yake kasancewa? Kullum sababin iyaye yake samu?Duk yanda naso dagata abin yaci tura, na tattaro duka karfina a sannu na hada hannayena 2 na dago ta ina nishi, nauyinta ya rinjayeni wanda hakan ne ya sanyani tafiya luuuuuuu zan kifa, tuni kafafuna suka durkushe dai dai sanda naji hannaye 4 a kewaye damu, aka karbe mummy ina gani za’a raba ni da ita, na rakashi da kallo sanda ya juya da ita sannan naji an daga ni nima ,wasu taurari ne suka rufan idanu, akali ya buga gudumarsa yana fadin kooooooot,ya tashi kara till further notice, da sauri IB ya bude ma Uncle din nasa gidan baya suka sanya mummy Rahma, yan jarida sai daukan hotuna suke ,amma wannan karan ba wanda yabi ta kansu, kai tsaye asibiti suka nufa, Barr Muhsin da Madam Zarah ne suka jero da gudu, motar madam zara ce a kusa, don haka ita aka bude ya shige bayan motar da ita, Madam Zarah ce ke jan motar cikin tukin Sauri, saida ya tabbatar an Shiga da mummy emergency sannan ya samu guri ya tsaya kirjinsa na bugawa, yayi ajiyar zuciya yana kai komo duk sai IB din ya tsaya kallonsa.
Fitowar likitane ya dauki hankulansu, ta farfado, amma tana bukatar hutu, but zaku iya ganinta sai dai…. ai bai tsaya jin bayanan ba ya shige ward din da gudu, IB yayi dariya yana fadin thank you doctor … Tsaye yake a saitin fuskarta yana kallon shiga da fitar numfashinta, shes so cute ya ayyana a ransa, yarinyar nada kyau na ban mamaki, ta dan motsa tana fadin mummy cikin gunjin kuka, ya karasa daf da ita daidai sanda madam zarah ta shigo da ledojin kayan eatry, cikin fara’a ta me kallonsu ,baby nah kin tashi? ta yamutsa fuska gami da kau da kai, treat everyone nice ta ji ya fadi cikin rada, wannan ne ya sanyata yin yake, ta karaso ta rungumeta tana ajiyar rai, abincin ta mika mata tana murmushi ,eat dear, na girgiza mata kai idanuna suna kawo kwalla, ina mummy? sallamarsa ce ta katse mu, dogon namijine fari mai tsiffan idanians zance ko larabawa, shigarsa cikin suit ruwan toka masu duhu, kan ba hula sai hakan ya fito da zahirin kyawunsa, giran cinkus da gashi, ga gemu ya tara ,gashin kan baki wuluk sai sheki suke, ya duko yana min kallon kurilla ,nima na kafeshi da idanu ina kankantasu, wannan dalilin ne ya sanyashi murmushin sa mai kyau ,sannan na hada dogon hancinsa da nawa yana kallon idanuna, baby ya furta in a cool voice, wani iri naji cikin jikina ,ya karasa hade goshin mu yayin da hannunsu na dama me dan bubuga bayan, wt I feel for you is beyond words, all I knw is am right here for mah kid , Price less jewel ,ya rungumeni na tsawon mintuna, dakin ya dau shiru nima na kasa motsi, mummy na furta idanuna na fitar da kwalla, ya janye jikinsa gami da min light kiss a goshi, your mum is fine, go see her dear cewarsa yana daga mani gira, na dan waiwaiya ina neman slipass dina, lawyerna ya fita ban ganshi ba, har na mike mutunin dana kasa kama sunan shi yana sanya mani takalma, can sai ga isowan lauyana yana murmushi naga sun tafa hannu suna gaisawa, thank u Barr muhsin ka cancanci yabo, nagode Alhaji Abdullahi Buba ni ka takaitawa, don akwai aiki a gabana, inada zuwa asibitin da mummy Rahma ta haihu in lalubo file dinta don ganin sunayen alluran da aka mata, ina hameedhar? naji ya fadi sanda ya soma waiwaye a kokarinsa na hangyan inda nake, na fito data bayan Wanda name zaton mijin mummy ne, idanuna suka sauka a nasa, ya daga min kai da idanu yayi Mani signal, na fahimci its true, lost daddynah ne, shi ya haifeki? cewar wani sashi na zuciyata, ko da yake ai mijin mama baba ne, cikin murnar Dana rasa ko na miye na jingina da bayansa ina fadin alhamdulillah, ya tallaboni ya rike ta gefensa yana kallona, ina ta sakin numfashi tamkar wace aka biyo da gudu, sai jinsa nayi yana magana, baby! Da sauri na daga idanu ina kallonsa na tsinci kaina da sakar masa murmushi, ya gyara mana tsayuwa gami da rungumeni da kyau,na dan yi jim ina tsoron wannan katobarar , idan ba mahaifina bane haramun nefa wannan alakar, na dan janye jikina ,ya riko mani hannu yana fadin muje ki ga mummynki, tamkar ‘yar shekaru 2 haka ya rika jana sai kace za’a sace ni, ya tura kofan muka shiga har lokacin barci take sosai hankali kwance, dr yace she was unconcious,amma yanzun barci take,ya fadi yana kallona na jinjina kai kawai don am speechless, muhsin lawyarna ya turo kofan yana fadin na barku lfy akwai sauran gashi, bai tsaya jiran amsa ba ya saki kofan ya fice, har kullum lamuransa kan dore mani kai,kullum lokacinsa a kayyade suke…
Can kotu jama’a suna ta mayar da magana kan karar da ta zama abin al’ajabi ga mutane, ba ma su kadai ba ita kanta kaulahan ta sare, madam zaran da zuwan dady ya koreta ne ke ta mita tana muzurai ita ta gaji da jan rai,asan wace za’a ,a haka dai dole taro ya watse kenan kowa ya kama gabansa… Ya tura mani stool gami da cewa zauna baby kar ki gaji da tsayuwa, na zauna babu musu sannan yayiwa Abu waya yanai mass albishir ,daidai lokacin naga mummy tana motsi sannan ta dago kanta tana kallonmu da azamarsa ya rigani karasawa gareta yana tambayanta me take bukata a kidime, sai na lalace gurin kallonsa ma,ta rike mani hannu tana kallonsa ko me dalili? Ta dan mari fuskarata da dayan hannun da sauri ya dafe hannun yana fadin haba dear me na marin kanki? Ta saukar da fuskarta kasa cikin yanayin sanyi da natsuwa tana fadin na dauka mafarki nakeyi ne, kallanni da kyau dear am real ni Abdullah Buba na dawo,a karo na 2 ina kwadayin aurenki, mummy naga ta fashe da kuka na durkusa a gurin gami da tsira mata idanu ni kam kwakwalwatace ta cunkushe,ga aminiyar tawa tana cikin wani hali(mummy), ringing din wayace ta katsesu mummy ta dauka, sanda ta katse wayar ta kalleni gami da cewa jeki baby bilal na jira ya maidaki gida,mummy! Na fadi ina kallon yatsun kafata, jeki kar ki damu zan kula da ita cewarsa, na kalli kwayar idanunta tayi min alaman in wuce din, a nan na barta ni kam cike da jimamin yanda zata kaya, wani sashi na zuciyata murna nakeyi mummy zatayi aure, mijinta ya tattraki ya kora inji wani 6arin, da sauri na kawar da wannan wawan tunanin nawa,small madam hope say no problem? Nothing nace masa sannan na kara da cewa mijin mummyna ne ya dawo, sai naji yana salati wai shi nan tayani murna yakeyi, bilal akwai barkwanci yana sanyani nishadi ga raha da kamun kai,a haka muka karasa gidan, lamuransa kan dauki hankalina kwarai, cikin taxi drivers din ma shi daban ne, dan gayu ya iya ado ga natsuwa da sanin ya kamata, ba ma wannan kadai ba, lokuta da dama nakan yi mamakin yanayinsa, anya taxi driver din gaskya ne? Akwai tsafta da tsarin kula da tufafi, wanda ya sha banban da sauran yan taxi din dana sani,yau kam a sabuwar taxi dal ya zo daukana,a tsanake na kare wa cikinsa kallo mai kyau komai na ciki ya fita daban da wayanda nake gani, bilal! Yes small madam, ba hausa shi ya sanya yake dan gwari gwarin turancinsa, ina ka samo wannan kuma? Ya yi murmushi gami da cewa kar ki manta a karkashin gvt nake tunda ke din ta gaban goshinsu ce, hmmm? yes na them give me, na jinjina kai ina kare masa kallo, u no gree? No ba haka bane daidai lokacin wayar muhsin ta shigo na karata a kunnena ina fara’a, lauyana! Ok gani nan tafe, na katse wayar gami da yin ajiyar zuciya, daidai sanda ya saukeni yana fadin sai gobe, har nayi gaba ya dakatar da ni, come now, na koma ina tambayansa dalili, wen u dey comot 2moro? Nayi dan jim cikin tunani sannan na soma fadin i dnt know bt i will call u, na juya kai tsaye inda yayi parking na nufa, yana tsaye a jikin motarsa hannayen sa rungume kan kirjinsa, ran lauya shi dade na fadi ina dan rusunawa, dariya ma abin ya bashi sai da ya dan dara sannan muka koma kan kujeru hannayensa dauke da files, na kai dubana garesu ina yamutsa fuska, ya kuma bushewa da dariya yana girgiza kai, hammy mai rai bai hutawa sai ran da ajali ta kira, na daga kai kawai ina jinjina lamarin, akwai deal baby gal ya zamuyi kenan? Na gyara zamana ina fadin daz serious, ba wani mai wahalarwa bane, ko? Ya gyada kai yana danne dariyarsa, gidansu Seemah zaki koma, when? Na fadi a rikice, cool down mana ai ba cire kan mutane suke ba dai, uhum! Gobe In Shaa Allahu akwai fitar da zatayi ke sai ki maye gurbinta, bari zan wuce goben mu hadu 10am daidai, ok? To amma… ya katsen hanzari ta hanyar fadin natsu ba matsala zan kula da takunki kinji ko? Nayi murmushi sannan muka mike tare don yi masa rakiya, na fita da sauri ya koma gefan gadon yana fadin Rahma please, ta saki kuka mai cin rai tana shasheka , ai bai San sanda ya rungumeta ba yana shafa mata kai, shiiiiii it’s OK am here, am sorry, did you just say you are sorry? all these years , why? ta karasa tana bubugeshi, ya matseta gam din ta daina buge bugen, hakan ya sanyata yin luf ,tamakar babyn daya samu mama ,mine kisan dai ina sonki ko? tayi dariya cikin kuka tunowa da irin maganar babyn ta hameedah Kennan, takance mummy kin San dai ina sonki ko? I hope my dreams come true ,ta fadi cikin hawaye, amin cewarsa yana bubuga mata baya ,who called you? tayi tambayar cikin tsabar damuwa, you did dear, kaddarku ce ta dawo dani Nigeria, ta janye jikinta tana watsa masa harara, yayi dariya yana girgiza kai, ta tsira masa idanu tana kallo ,you will never change cewarsa yana tuno rayuwarsu a baya, idan Rahamarsa ta harareshi yana nufin ta sauko, yasan lagon abarsa kam, na dauka ka mutu, nasan mijina will never turn his back on me, what have I done wrong? listen cewarsa yana gyara tsayuwarsa, I will be back, ya fice, madara ya dauko cikin mota ,ya tsiyaya mata cikin cup ta sha sannan suka zauna labarin bayan rabuwa.
Ranar cike da tarin damuwa mara misaltuwa na kwana a haka kuma na tashi, kadaici, jimami da rashin sanin madafa sune suka sanyani gaba, ina gaban dressing mirrow sai ga wayarsa, baby kina ina? Shiryawa nake, ok ki sa black abaya plane da nadi na dankwalinsa, look plane kar ki yi wani kwaliyya mai yawa ko? in fact no make ups ,your face should look as nude as possible, Ok na fadi cike da mamakin wannan order din, yana gefan gidansu Seemah saga nesa kadan, daidai lokacin motar su seemah ta gilma ta gefan motarsa dauke da irin shigar, da yake a bakin gate ta shiga motar, daga inda yake yana hango komai, ya jinjina kai yana murmushi sannan ya bi bayansu, shoprite ta wuce siyayya, hakan ne ya bashi damar komawa ta gidan don daukota…
Flat takalma na sanya sannan na fito don kar bilal ya kosa amma sai na hangi har muhsin din ma ya iso, na sallami bilal na karasa gurin lauyana muka gaisa, ya budemin gidan gaba na fada sannan ya tayar muka bar gidan, muna tafe ya dan yi parkin a gefan titi yana kallona, muga bag dinki nasan ba ki rasa sweets, bai jira na mikamasa ba ya amshe da gaske lalubawa yayi ya rufe ya miko mani yana fadin take care kar kiyi sakaci da ita, na jin jina kaina kawai muka wuce ya ci gaba da cewa kar kiyi wa kowa magana idan kin shiga gidan don ki saje da Seemah sosai, keep a grimy face, na gyada kai kawai ya saukeni yana dada jadada mani cewa kar ina dade kuma in kasance kusa da wayata, kaulah na nan cikin gidan naga shigarta, to kawai na ce sannan na wuce cikin gidan da takun takama irin yanda naga Seemah nayi, ta inda nabi farkon zuwana na maida hankali na wuce don kar in 6ace a gidan mutane, na fada kan gadonta ina tunanin yanda zanyi in shiga gurin haji Ni’ima, kofa naji an turo da sauri na ja blanket na rufe kaina ina ajiyar zuciya, ta shafan kafafu tana cewa yau ana fashin shopping din ne? Na kasa magana kawai nayi luf, tare suke da kaulah ni kam nayi lamo tamkar ina barci, yi zamanki mu tattauna a nan ita wannan nauyin barci ne da ita, gidan baya rabo da baki tunda sweethrt ya dawo ma yan siyasan nan sai zarya suke, sashina kuma akwai Rihab da masu aiki magulmatane kar su kaini gaba, kaulah lamarin nan ya wuce tsammanin mu fa, tun da wannan mutumin ya bayyana na san sai munga tozarci ba kadan ba, mai kudi ne kuma akwai kamanni a zahiri , ni nasan duk ran da gaskiya ta fito yan siyasa sun samu abin fada a kanmu, sweethrt bazai samu kujerar next year ba, kaulah ya kike ganin zamu yi? Na fi jin Rihab ma sun shaku da Seemah ya zanyi idan gaskiya tayi halinta? Wannan tsagerin yaron mara ta idanu zai iya yin komai kan samun seemah da hameerdah su koma ga uwarsu actin mummy, ni da nake a la6e sai da na zabura da na ankare ashefa a 6oye nake sai na kuma yin luf kar su harbo jirgina,ci gaba da cewa ni da nasan hakan ce zata kasance da ban yi wannan aikin ba cewan kaulah, Rihab mafa kwanakin nan mamarta ta mutu a moto accident, wannan da sauki ba mai tuhumarmu game da ita cewar haj Ni’ima, ni ina gudun kar Alhaji na ya samu labarin rashin haihuwarsa ne in shiga uku, gadon nan na kwallafa wa rai, danginsa mugayen gaskya ne,yanzun din ma sun ki sakan mani mara sam sai sanya idanun jaraba, ga sin ‘ya ‘ya tamkar su suke raba haihuwar, ban son kishiya balle tazo ta hayayyafa a gidana da mijina never, kaulah say something kin yi shiru, wai ni me ya dawo dake ne ma? Bayan munyi dake duk bukatunki zan tura maki can kasar, haj a bar tone tone abin da yawuce ya riga ya wuce sai mu fuskanci gaba ko? Hakane amma duk kece sila kaulah, ahaye nanaye cewar Kaulah a kufule, in ce ke kika dai ijaza min, ina zawne kalau kika jaza mani,ina zaman zamana ke da hajiya Binta (aminiyarta) kuka sanyani gaba har saida na aikata tsiya ,kuka sanyani na cuci bayin Allah, hakama zakice? Kwarai kuwa ai gaskiyar kenan, gashi nan kin 6ata mata tarbiyan ‘ya ai (seemah) ,Kaulah saurara, ba fada zamu tsaya yi ba mu fahimci juna shine maslaha sannan mu san yanda mukayi muka kwaci kanmu, ta yaya haj ?bayan aikin gama ya gama? Kwantar da hankalinki ni nakeda Gosha a hannuna ,waye kuma hakan haj Ni’ima? Wani yaro nane mai basirar jaraba, bari zan nemeshi mu sanda abin yi, inaga tunda cin hanci bai biya ba gara a kau dashi a doron kasa, kidima ta sanyani yin atishawar karfi da yaji, nayi dan juyi ina gyara duvet din dana tatar bisa gadon, princess ta fadi tana dan bubga mani baya, na shareta gami da rintse idanuna ina fitar da numfashin karfi da yaji, yauwa kaulah as i was saying, muryar mijintane ya katsesu, honey! Ta dan gyara murya sannan ta fice na dada lafewa ina jiran shigowarta, dakin ya dau shiru banda ashar din da Kaulah ke kutuntumawa, shegiya kambun shedanu cewar kaulah, ta sanya rayuka cikin hatsari mtssssss ta ja tsaki sannan naji karan kofa ta shigo, wayata ta hau ringing
Na daga kaina ina kallon inda na ajiye handa bag din kusan a karkashin gado take dab da su amma ba halin dauka, shiru ya ratsa dakin in kika dauke wayar daketa kara sai kirjina ya tsananta bugawa, shin me abin yi? Haka kawai za’a yi kin kawo shawara haj Ni’ima, bari in je ga haj Binta inji daga gareta ko? Hakan ma yayi daidai ki gaisheta da kyau, uhum ta fadi sannan naji zasu fice, au ita wannan wayar bazata daina ringing bane? Ah ah ta tashi dai ta dauka haj, no princess in har tana hutawa ba mai shiga gonarta, bar ta kawai ta gaji ta daina don kanta, naji sun ja kofar sama sama nake jin sautun hirar su, na karasa da sanda na dauko wayar, sakon lauyanane yana mai sanar dani isowar Seemah, gata nan a bakin gate ya karashe da kifito ina jira a gefan gidan, ras! Naji faduwar gaba mai tsanani lokaci guda duk na rude, har gumi ya tsatsafo mani, ilahirin jikina na rawa naji batun mutuwa, a jaka na tura takalmana, na sa6ata ina saka abin yi, shin ina mafita? Ta ina zan bi ? gashi hanya 1 kawai na sani, Rihab ce naji tana fadin aunty see me kika siyo mani? Da azamata na fada wordrobe a raku6e sannan na janyo a hankali naji an turo kofan dakin ana amsa waya, gud Ma’idah ok, zan biya wa jalila sai mu karasa mu daukoki ko? Madalla bari zan kiraki anjima, ta katse layin sannan ta kwala wa mai aikin gidan kira, Mari! Cikin sautinta na daga murya, stupid kawai ko uban wa take zaton zai gyara mani dakin? Idiot, do i have to always tell her what to do? Sake wordrobe kawai ma zanyi this month bari mumsyn ta shigo na gaji da sanya kayan nan, ta kuma jan tsaki tana canza kayan jikinta kalli fa ina saka irin na ‘yan matan gari, gara dai one in town kawai, Rihab jeki kice wa mumsy idan matar ta tafi zamuyi magana, yarinyar ta fice da gudu (Rihab), magulmata kawai ko me ake shukawa kuma? cewar Seemah, Oho dai ta bama kanta amsa, Sai ga shigowan mai aikin cikin kamilaliyar mury ta soma gaisuwa, hold it cewar Seemah ,daga muryarata na fahimci babba ce kila ma sa’ar kakarta, dakin kuma uban wa zai gyara shi? Ayi hakuri uwar dakina ina gyara bangaran ALHAJI NE, kutumar uba cewrata sannan a yi cikin toilet yayin da take cewa kar ki bari raina ya baci, an gama cewar matar bari in dauko kayan aikina ,naji ta ja tsaki sai karar kofar ya biyo baya, ba jimawa itama ta fice zuwa cikin gidan tana banbamin her riom is filthy, a hankali na zuro kaina ina leke sannan da sanda na fito ina ware idanu don ganin ta inda wani zai ganni, na tura kofar palon shiru babu motsin kowa, ko takalmi na kasa cirowa in sanyasu a haka na kai karshen palon, murayar magidanci naji daga bayana, kila maigidan ne na ayyana a raina ,wannan ne ya sanyani daga kafata don kar ya hangoni, a haka na karasa bakin kofan gidan inda mukaci karo da mai wankinsu hannayensa dauke da gogagun kaya, kayan suka zubo sanda mukayi karo, a hargitse cikin tsananin rudani nake fadin so so sorry, na arce ko waiwaye sai bakin gate inda na hango muhsin a jikin motarsa fuskar tattare da damuwa, lokaci lokaci yakan kalli agogon hannunsa sannan ya maida hankalinsa ga gate dain gidan, da sauri nayi niyyar tsallakawa titi don samunsa a dayan tsallakyan,wata mota ta taho daga nesa kadan da gudunta, ban ankareba na jini a kife bayan karar motar da ta cikan dodon kunne, daga ni har shi watse a gefan titin, da sauri ya mike yana karkade jikinsa, nima ya tsince mani abubuwan handbag dina da suka watse ya zubasu a ciki, me ke damunkine har zaki tsallake titi baki wani tsaya dubawa ba? Na yi ajiyar zuciya ina fadin Alhmdlh, lauyana na fadi ina in ina, oya tashi mu bar gurin nan, na mike muka shige motar ,sai a lokacin na fahimci da motar ta taho zata bugeni shi yayi saurin hankadeni wannan ne ya sanyamu zubewa kasa gaba daya…
[5/16, 3:10 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
10…
Sannu dear ya fadi cikin kulawa, na dan yi yake saboda har zuwa yanzun bani da wata nutsuwa, Seemah twin dina ce? na tambayi kaina ina gyara jakata data sukurkuce, tunanin me kikeyi? yayi tambayar yana bude motar, na tsaya sororo ina kallon sa don sam bana fahimtar abin da yake cewa, maganganunsu ne ke mani yawo a kwanya, muhsin zasu kashe kenan, why? ya danna horn yana tsareni da idanu ,sannan ya buden gefan driver na zauna ya mayar ya rufe shima ya zaga ya shiga Ya tayar muka bar gurin , lokaci lokaci yakan dan waiwayo ya kalleni, na kasa magana sai zancen zuci, baby cewarsa yana murza sitiyari cikin kwarewa, kar ki damu it shall be well, na jinjina masa kai yayin da nake kokarin mayar da kwallayar da suka cika mani idanu, saida mukayi nisa sosai har mun kusan karasawa asibiti don nan yace zai saukeni inga mummy, naga yayi parkin gefen titi sannan ya karbi hand bag dina yana fadin da fatan dai ajiyata tana nan? Ni kam binsa nayi da idanu ya hau laluba jakar yana fadin daz great, recorder naga ya dauko wace ban san da zamanta ba, ina na samo wannan? Dazun na sanya shi ciki sanda na tambayi sweet kafin ki shiga, na gyada kai kawai ina kallon inda muke, ina ne nan? Gidan mu cewarsa yana kashe motar sannan ya kara da cewa sauko muje ki rakani in adana wannan ya fadi yana nuna recordern, ba musu na sauka a sannu muka jera zuwa cikin gidan, lallai su din ma wasu ne a kasar amma bashi da takama ko girmankai, baza ki fahimci MATSAYINSA a yanayinsa ba har sai kin je muhalinsa, a palon gidan muka tarar da mutan gidan suna kallo, ,’ yan mata uku na gani zaune kan data saga cikin hadadun kujerun da suka kawaita fankaceciyar palon, cikin su Sa’adah kawai na sani, ta karaso da murnarta muka rungume juna, gefe guda hamshakiyar, mace ce zaune tana amsa waya, ba sai an gaya maki ba zaki fahimci mamansu ce, na karasa na gaidata wani irin kallo ta watso min sannan ta amsa a dakile tana yamutsa fuska, a daddare na zauna tamkar a ce kule in arce a guje, ina ganin fitowarsa nayi saurin mikewa na rigashi ma fita ko me ya kawo hakan? Ina iya jiyota tana tambayarsa,vwa cece wancan babayo? Client dina ce cewarsa yana kokarin faita, da kyau , ai kasan dai ruwa baya tsami banza, client har gida? Ban ji me yace mata ba ni kam a mota ya sameni nayi da na sanin binsa gidan, daga ni har shi babu mai magana muka bar gidan zuciyata sam babu dadi, me laifina? Motar ta dau shiru in kika dauke karar motoci da ababen hawa dake gilmawa, ya kau da shirun ta hanyar cewa kinga mahaifiyata ko? Na gyada kaina don a halin da nake bazan iya magana ba, kannena fa? Na gansu, Ku dika kuna kama, dukanku masu kyau ne, yayi murmushi gami da cewa haka mutane ke cewa, Sa’adah ce mai bina, sai ummu salama, asma’u muna ce mata hushan autar mu kuma kenan, bamu gaisa ba suna kallo lokacin basu kula da shigowata ba, na yi mamakin jin Sa’adah kanwace a gurinsa, kiyi hakuri haka mama take min ko don ni kadai ne da namiji kuma first born? Na yi ajiyar zuciya gami da cewa ta damu son dinta yayi aure ne ko? kuma bata da laifi ai duk wata uwa burinta taga jika ko jikoki ,ya yi murmushi yana shafa kansa, hmmm hammy kenan baby manya, ah to kaine ina zaka aiki, daga ina kake? aiki, me kakeyi? aiki, me zakayi,? aiki, dariya yayi sosai gami da cewa nagode, sai abin ya bani dariya nima, kaga laifinka ya shafeni ko? Sowie oya sauko muje,ya fadi daidai sanda yayi parking, na sauka muka shige asibitin, mutumin nan zaune kan kujera yana gyangyadi yayin da mummyna kea barci, sai naji tausayinsa ta kamani, kila bai yi barci ba daren jiya, na tsira masu idanu sannan na kalli muhsin cikin rashin Sa’a muka hada idanu, na yi saurin kawar da kaina gefe guda ina fadin kaje kawai ni ba yanzun zan tafi ba nan zan wuni, ok kawai yace naga ya fice ,gefan sa na karasa ina kare masa kallo, zuciyata dauke da wani lamari mai girma, ni dai ina jin kaunarsa sosai a tattare dani, ko zan iya kiransa daddynah? na dan jima durkushe ina tufka da warwara, ba jimawa wayarsa ta hau kara naga ya dan bude idanunsa yana kokarin tashi ya lalubo wayar, na kai idanuna kan watyar dake karkashin kujerarsa ina murmushi, sannan na sanya hannuna na dauko gami da mika masa, fuskarsa dauke da fara’a ya karba don amsawa, karata yayi a kunne na kafesa da idanu na rasa me nake ji a game dashi ,ni dai nasan yana da kyau sosai ga shi dan boko , turai tayi molding dinshi sosai, ya kalloni fuskar dauke da fara’a sannan ya kai dayan hannunsa yana shafa mani kai, har ya gama wayar muka gaisa sannan yayi waje don ganin mai nemansa, na san lauyanane na zauna a inda ya tashi yayin da na sanya hannuna cikin na mummy ina kallon fita da shigar numfashinta, u are a great woman na furta daidai sanda hawaye suka sirnano mani nayi mata kiss a goshi sai naga ta bude idanunta tar a kaina, yaushe kikazo sarkin kuka? na yamutsa fuska gami da fashewa da kukan sosai ina jin daci a raina Oh no cewarta tana girgiza mani kai, yaushe zaki girma ne wai? naci gaba da kukana ,ta rungumeni tana Dan shafa mani baya, waya taba mani ke? ba ke bace ba, me nayi kuma? kina ta rashin lafiya kika barni ni kadai a gida, sorry dear ai na warke, wannan ne kawai matsalar? yeah na fadi ina share hawayena ,are you sure? tayi tambayar tana kallon kwayar idanuna, baby you are hiding something, Muhsin ne ? na kuma fashewa da wani sabon kukan, sorry toh na daina tambayar, oya sauko muyi breakfast,muka dan zauna muka soma hirar mu jefi jefi yayin da muke karyawa, mummy pls ki dawo ni nasan kin warke, ah ah ha, ni da jikina wani da jimin zafin ciwo, kadaici zatai min illa fa ,na fadi ina turo baki, dai dai lokacin ya shigo yana mata sannu, don Allah ka nema min sallama na warke, likitan ma yace sai yamma zai sallameki sai ku shirya, ni zan dan leka gida, ok godiya muke na fadi daidai sanda ya fita,na matsa kunanta ina mata rada, ta kafeni da idanu tana murmushi yayin da idanunta suka kawo kwalla , why not? yariga yace me ‘yarsa ce ,he’s ready for the challenges ahead, call him daddy kinji? feel free ta karasa tana min murmushi ,mummy, yes baby, kinsan dai ina sonki ko? ta tsintsire da dariya hawaye na zarya a kuncinta , ina sonki nima, mummy ya kai haka? na fadi ina nuna karmin yatsa na, beyound that dear cewarta tana kafeni da idanu, ta rasa abin dayasa bata tana kula da wasu halayen hameedah irin na mijinta bane sai yanzunA asibitin na wuni ni da mummy muna makale da juna, ji nake tamkar za’a kwace mani ita, Bilal na kira ya zo maidani don mummy tace inje kawai tana nan tafe kar in kosa, yau dinma cikin daukan wankan yake, na dubeshi a kaikaice muka gaisa, eatry zamu wuce nace masa don bansan lokacin dawowan mummy ba bazan iya girki ba ni kam don a gajiye nake ba kadan ba, zuciyata babu dadi sam, ya tayar muna tafe a hankali muna hira, small madam yau duk ban ganki ba, nayi dan murmushi gami da cewa hakane ya gida? Gida ba lafiya, me ya faru? Mamana bata da lafiya ya fadi cikin yanayin damuwa kuma bani da kudin magani, na dan yi jim ina duban sa, to me ya hanaka zuwa ka gaya mana? Small madam ur madam no well hw i go worry am? Na gyada kaina ina jimami, muje gidan naku to na fadi ina tunanin taimaka masa, ehn? ya furata irin na mass bazata din nan, Eh nace muje can din duk cikin turanci muke maganar, ya karya kwana muka dau hanyar layinsu, cikin kauyen Abj suke ga tafiya har na kosa, sanda muka karasa gidan makocinsu ke shaida mana cewa an kaita asibiti, na kallesi sannan na kau da kaina yayin da nake fadin kayi hakuri gida zan koma, am too tired amma don Allah ka sanar damu kudin da ake bukata in da rabo zanje watarana in ganta, sai godiya yake da haka muka juya ya maidani gida, ni da nake neman abinci sai gani ban ma bi takansa ba don gajiya,a haka na fada gado ko sashin mummy ban duba ba balle in san ko ta dawo…
Wata sabuwar rayuwa mukeyi tunda mutumin ya bayyana cikin rayuwarmu kukan mummy ya kare, ina kula farincikinta yafi na baya nima hakan ya kawo wanzuwar kwanciyar hankali tsakaninmu, duk wasu alhazai masu neman aurenta sun kau tunda tayi za6i na har abada…
Yau kam mijin mummy kudade ya zuba mani duk a kokarinsa na son jana a jiki, na kwasa ban san adadinsu ba don ba kirgawa nayi ba, murna ta isheni kai tsaye waje nayi na ko ci sa’a bilal na shirin fita, da sauri na karasa gareshi ina daga masa hannu, ya dan dakata yana kallona, small madam na wetin? Murna ta cikani yau zan taimakeshi, ya jikin mummy? Da sauki ya fadi yana jiran jin abinda ya sanyani murna haka, na kwashi kudin na mika masa ina fadin gashi ka kula da ita, ya hangame baki yana zaro idanu, take it bilal, ka kar6a hannun na karkarwa sannan na juya da sauri ina jinsa yana ta godiya amma ban tanka ba, na wuce cikin gidan abuna,
cikin satin naso zuwa ganin marar lafiyan amma ba hali, bai cika zuwa ba ni kuma dama ban fita sai da uzuri mai tsauri, ina nan muna break na samu wayar muhsin ya zo, na tsame hannuna gami da mikewa mummy baki bude tana kallona, baby! Ba sai ya jira ki gama ba, ah ah ban son ya gaji da jira, uhum sarkin tsurfa ina murmushi na dau tissue na goge bakina dama da hijab a jikina na fice, yau kam cikin motarsa yake zaune, ya zuro kafa daya waje daya daga ciki, na kwankwasa masa glass sannan ya juyo gareni, ka 6uya, na fadi ina kallonsa,h mmm shigo ki zauna akwai deal, na zagaya ya bude mani sannan ya maida hankalinsa kaina yana fadin bansan da bakin dazan maki godiya ba, amma one more thing, inda hali ina bukatar kusancin ki da haj Binta,eh na fadi a kidime, Yes zai taimaka, kar fa su kamani? Na yarda da basirarki tunda wadancan basu fahimci wani abu ba itama mai toshashiyar kwanya ce, na kyalkyace da dariya sannan na tsagaita ina fadin how possible is it? Ke mace ce ki yi amfani da basirarki, wannan karan nima inda da uzuri akwai tafiya a gabana, a sanyaye nace kai ke karfafa mani gwiwa kai bazan iya ba, haba ya zaki ce hakan?m? Sabodake na saki jiki basirata bata yi wani tasiri ba a nan, don me saida tafiya tayi nisa zaki dauke kafa? Matar nan mai kwadayin samunki a matsayin ‘ya ce ki natsu ki kalli abubuwan nan da idon basira, kar fa ina yabonki sallah ki kasa alwalla, ya za’ayi ki 6ata rawarki da tsalle? Just do this for me don Allah wannan ya zama na karshe i promise, na jinjina kaina a sanyaye shi kansa yau a sanyaye ya zo mani, me ke damunsa ne? yaushe zaka tafi? gobe nake son wucewa ,wani aiki ne me jirana a can din, na saurari recorder din , ba sai na gaya maki ba ,by now i believe yiu already know everything , na jinjina masa kai ina ajiyar rai, but take care of yourself, we can’t trust because we don’t know who is hunting us, OK? na gyada masa kai kawai…
[5/16, 3:10 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR. (UMMU FARHANAH)…
11…
Gurin yayi tsit ni din ma na rasa ta cewa, ya katse shirun ta hanyar cewa Sa’adah na son ganinki tace in sanar da ke, me zan ce mata? Na yi ajiyar zuciya gami da sada kaina kasa yayin da nake wasa da yatsuna , sannan na soma fadin she is welcome amma yaushe zata zo? Bata tsai da lokaci ba tukun, ina sonta bata da matsala, hakane cewarsa, ya dan gyara zamansa sannan ya kara da cewa zan samu? In Shaa Allahu zan duba insan abin yi, ki kula da kanki fa,kuma zamu rika waya don jin yanda ta kaya ki yi min wannan kokarin kiji? Na gyada kaina kawai ina shirin sauka, muga wayarki cewarsa yana duba agogon rolex dake daure a tsintsiyar hannunsa, na mika masa, naga yana danne danne, ban kawo komai a raina ba na dai zuba masa na mujiya, ya gama ya miko min gami da cewa always stay close 2 ur phone, okey kawai na iya fadi, zan yi tafiya na ce maki, ya fadi don dakatar da ni,Allah ya dawo da kai lafiya bring all d eatables kaji? Sai a lokacin naga ya dan yi murmushi yana fadin amin, ki gaida mummy sauri nake yau bamu gaisa ba, uhum kawai na fadi nayi cikin gidan, ganina ne ya sanyata kallon agogo tana duban inda nake, mummy yace in gaisheki, ya kyauta ai ga breakfast din can na bari ki cinye, na koshi ni kam ,me kikaci? Babu, shi yasa ai naso ki karasa kafin ki fita gashi nan ai ya fita a rainki hankalin ki ya kwanta ko? Kai mummy, hmmm baby, na zauna gefanta muna hirar shari’ar da ta zama shiririta, a haka har lokacin sallar azahar tayi, bilal nayi ma waya ya zo ya saukeni ina da gurin zuwa,sannan na soma shiri har na kamala zuciyata ta gaza shiryamin abin da zan gaya wa mummyna,ban son zargi gashi ba zai yuwu in fadi gaskiya ba,ba ma wannan ba ban son ta hanani wannan fitar, ina kwadayin cikawa muhsin alkawarin dana dauka,ina sa6a jakata na tsinkayi muryarta a bayan garden, mummy zani siyan kayan dadi, na fadi ina sauri kar taga har kaya na canza, kar ki dade fa cewarta, ina fita bilal na isowa na fada ciki ina fadin gwarinpa, ya dau hanya da kwatancen muhsin muka gane gidan, sai da muka isa inda zan sauka sannan ido ya raina fata, shin me zance ya kawoni? Na dan leka ina hangyan ayarin motocin da ke parkin sapace, sai ga idanun maigadi cikin nawa, wat do u want? Tamkar in arta a guje amma wannan ba shawara bace, na dake zuciyata sai lugude takeyi tamkar ana daka, en…uh… Hmmm i wnt 2 see hajiya, na fadi cike da alamun rashin gaskiya, sai naga ya juya baya yana yes ma, ras gabana ya fadi wannan karan na kusa dani tsaf zai ji karan bugun zuciyata, bayanina yake mata naji sautin sahunta tana nufomu, are u sure yace mani? Na gyada kai kawai ina jiran inga abin da zai wakana,
na zuba wa saitin gate din idanu ina kallon ta inda zata 6illo, mace ce doguwa baka ,dirariya mai kyawun sura, tabarkallah na furta ina kallon takunta a fakaice, matayen dake fada kaina dukaninsu manya ne masu fada aji, shigarta cikin atamfa light purple da peach mai koriyar design, ta nufomu cikin takun dake nuna isashiya ce,tana karasowa na kago fara’a tamkar wata mumu nake fadin hajiya ina kwana? Wow kece yau a gidana? Lah wrong number ne ma wata Rukayya nake tambaya tare muka gama sch, ayya kinga kuwa nan babu Rukky, sai dai ko nan makwabta suna da Rukky, na gyada kaina ina godiya har zan wuce naji tana fadin Musa pls follow her, security din ya bini muka shige makota, shi yayi masu bayani aka kawo min ‘yar goye ita kadai ce rukkyn sai dai akwai wayanda suka tashi a nan muma mai gidan aka wa appointment last month muka dawo, cikin su akwai rukky buduruwa ce ma bata dade da gama sch ba, da sauri nace eh hakane ashe an sake postin din babansu, eh cewarta kinsan aikin soja, na jinjina kai sai a lokacin hankalina ya kwanta ganin ba’a harbo jirgina ba, na tsallake na daya na fadi a raina ina murna, musan ya tisa ni gaba muka koma ga haji Bintar don yi mata sallama, tana nan bakin gate din tana jiran isowanmu, na kalleta ina yake, mum zan tafi, ta yashare baki jin na ambaci mum, ko ruwa ba sai ki tsaya ki sha ba, jirana akeyi kar bilal ya kosa , Shi din ma ba sai ya shigo ba? Na ko yi masa magana gami da cewa kar ya bari mu dade ya azalzala sai mun tafi don kar ta rikeni, ok small madam ya fadi sannan muka shige ita tayi mana jagora zuwa tsatsaran palon gidan, ta dau waya tana dadannwa ,can naji tana fadin ummi kawo abun ta6awa reception inada baki, ba jimawa aka shigo da tray 2 sheke da kayan kwalama, sai jugs na ruwan sanyi dana juice, ta rika janmu da hira, ni da dama abin da nakeso kenan na biye mata muna tayi, bilal ya duba agogonsa yana yamitsa fuska, madam zamu wuce ya fadi kai tsaye, ana jiranmu a gida, wannan ne ya bamu daman mikewa, daga gani ba haka taso ba amma babu halin tsaidamu, muka shige tana fadin sai yaushe ? Nayi murmushi hakata soma cima ruwa, zan zo In Shaa Allahu, gobe? Ah ah cikin satin nan,ok sai na ganki, muka dau hanya zuciyata tai mani dadi,na tsaya na kwashi kayan dadin don wuce tuhumar mummyna, katuwar leda ta sanya aka loda min na wuce da abuna, babu iron ‘yar kunyar nan, ah to, ance raba Arne da makami ibada, nakan yi mamakin dalilan da suka sanya su 6ata lokacinsu kan fada a kaina, why me? ga yara nan bila adadi dole sai ni? me na tsare masu?..
Yau ma bani da wata dubara sai na 6ige da zuwa duba jikin maman bilal, ni nasan in ba haka nayi ba bani da wata mafita, da kanta ta kirashi tanai masa sanu da kokari, ta umarceni da daukan kayan abinci a kitchen in tafin mata dasu, mummy ta 6atan budjet, na dan tsagaita ina lissafawa a raina, ko da yake bilal mutuminane, na karasa taxi din daidai sanda yake zuba kayan a boot yana fara’a, small madam u too gud oh! ,na yi murmushi kawai zuciyata cike da zulumin yanda zata kaya, mun dau hanya na samu kiran muhsin, ina missin din sa kam,da azamata na daga ina fadin lauyan govt ina ka shige ne? Daga dayan 6angaren na saurara yayin da ya soma cewa baby ya kke? Kalau,me lbr? Ina office din abokina a lagos so ya rayuwa? Takaici ne ya kamani, gud kawai na ce, hello kin yi shiru, uhum kai nake sauraro, ok ya deal dinmu? Na gama 6angarena kai fa? No baki gama ba ,tun da ka tafi kayi waya kaji yanda mukayi, yi hakuri na amshi laifina, amma ke da kikaji shiru kin nemeni? Na yi tsit, baki san uzurin daya rikeni ba, well ya wuce dai ya kikayi da haj Bintar? A nutse na labarta masa komai, muryarsa da yanayi na nishadi naji yace daz great, ni kam me zan baki a rayuwr nan? Kana da abin da zaka bani, ok naji dadi zan fi kowa murna in har ina da abin da zai burgeki har ki amince ki kar6a, idan Allah yasa na dawo ajali bata kira ba zan sameki sai mu tattauna ko? Ok, uhum abu na gaba shine saka unkown camera a gidan, zaki iya? Zan kokarta, gud ki biya gidanmu zanwa Sa’adah waya sai ta baki ko? Da naji ya ambaci gidansu saida gabana ya fadi, na dake na basar ya kara da cewa recorda kuma kar kiyi sakaci da ita kin gane ko? Yes sir na karasa da salon tsokana, smart gal kina burgeni da haka muka katse wayar na daga idanuna ina kallon bilal dake kokarin parking, har mun iso? Yes ma cewarsa na sauka muka shige dan karamin gidan daya nuna min wani dan daki karami naga ya dosa da alama a nan mamansa take da zama, akwai kayan mace ciki amma yau din ma bata nan na dan zauna kadan ina jiran ta wucewan mintina 20 babu ita na kalleshi gami da cewa ni zan tafi Bilal akwai tafiya a gabana, sorry small madam i no give you water ya kara da cewa su na rijiya suke sha, wannan ne ya bani daman kallonsa, skin dinsa luwai luwai in kuwa hakan ne lallai yana da kyan yanayi don bazaki kalleshi a yanda yake kice daga gidan talauci ya fito ba, muje to ni dama a koshe nake ai, muka fice inai masa kwatancen inda zamu wuce..Ban samu matsalar shiga gidan ba kasancewan ba shine zuwana na farko ba, yau kam ba kowa a palon ina ta sallama sai can naji shigowan wata buduruwa ‘yar kimanin shekaru 24 cikin shigar da bazaki tantance matsayin addininta
ba, shigarta cikin jeans din daya dameta sosai, hakan ne ya sanya ko wani taku daya sai koina na jikinta ya amsa, rigar ‘yar karama ce sosai, shigar blue tayi , tana da kyawun da nake zaton shi ke rudata, takalmanta flat masu saukin yanayi, ta riko goggle dinta a hannu tana taunar chew gum, wani iron kallo ta watso Mani ,na raka hat din data rufa a ka a matsayin hijab ko mayafi da idanu, sallamar ma ta gagareta kila ba musulma bace cewan wani sashi na zuciyata, Sa’adah ce suka shigo tare da ‘yan uwanta masu kama ba sai an fada ba zaki fahimci cewa kannenta ne,da fara’arta ta tarbeni, sorry yaya yayi mani waya shi yasa muka dawo da wuri munje bikin ‘yar kanwar mamane a wuse, na jinjina kai kawai, wow Suhaila ke ce yau a gidan? Cewar auta Husnah suka soma hira da bakuwarsu, nima mun gagaisa suna dan jana cikin hirar amma ban wani basu kai ba hankalina na ga Sa’adah ta sallameni da wuri kar mamansu ta dawo daga gidan bikin ta sameni, wace suka kira da Suhaila ba dama in kalli sashinta sai mun hada idanu tana hararata ko me na tsare mata? Wayar ta soma ringing na daga ta ina murmushi, lauyana, eh gashi nan sis Sa’adah ta dauko, uhum, kai sai yaushe? Ok sai na jika, na katse gami da mikewa daidai sanda ta mikomin jaka tana fadin ke dai ya maidaki lauyan karfi da yaji, gaskiya kam ai yana yaba kokarinki cewan auta Husnah, mai bin Sa’adan ce ta ciko mani leda da kayan biki tana fadin ga naki rabon, Hameedar kenan ko?Cewar Suhaila, na daga girata ina kallonta, karkade kunnuwanki kiji da kyau…ko kamin ta karasa fadin manufarta tuni Sa’adahan ta ja hannuna mukayi waje, manta da wannan ba lafiya gareta ba, an fada maki ina son ganinki ko? Eh,to zan nemeki ba yanzun ba tukun, nayi mata godiya sannan na hau Billal ya ja muka bar… Tamakar in shaida mata alakarmu ta jini amma ya na iya? Kar in 6ata hikimar aikin lauyana, gara shi ya fada kar ta zargi wani abu, kin yi shiru, na’am! Dazun yake maganar karatunki na jami’a, wa? Oh na gane mummy tun yanzun? Uhum ki fitar da za6inki don yasan inda zai sanyaki ko? Na jinjina kaina daidai lokacin dana mike tsaye ina fadin sai na keta hazo nikam a kasashen wadancan zanyi university, ke dai kika sani, na sanya dariya sannan na fada daki…
Ban kai ga karasawa palon
ba hannuna dauke da mayafi mahadin suturan jikin mummy zan kai mata na tsinkayi furucin karshe a wayarta, ok sai kazo ina jira, wannan ya bani tabbacin fitan zatayi, don haka ina mika mata nayi dakina da sauri na soma shirin barin gidan, yau ko ta halin kaka sai na je gidan haj Binta na cika alkawarina, tuni Bilal ya karaso yana jirana in kammala shiri, na leka ta taga ina ganin dadyna ya bude mata gidan gaba ta fada, sannan ya zagaya ya bude nasa ya ja suka bar gidan, na kafa uban tagumi zuciyata fal farin ciki,hmmm soyayya manya, Seemah ki gama hauanki ki dawo mu zauna karkashin inuwa daya na ayyana a raina daidai sanda na mike don samunsa a waje, Jirani awa 2 kawai zanyi na fadi sannan na karasa cikin gidan, yau kuma da wanne zan sameta? Muryata ta karade inda ta kira da reception (dankareren falo)da sautin sallama sannan na dan ja na tsaye ina jiran umarni, ilai kuwa sai gata ta fito daga cikin gidan hannunta rike da glass cup mai dauke da ruwa tar tana dan sipping dinsa, oyoyo baby kece tafe cikin wannan kwaleliyar ranar? Na yi murmushi yayin da nake rausayar da kaina, mum ya na iya? Bayan zuciyata na kewarki, ban jira izini ba na saki jikina kan daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun da suka dada fito da kyau da tsarin palon, gud kin cika ‘yar halak, ko zamu karasa sit room? Na mike na rufa mata baya tana fadin ya kika je gidan wancan ranar? Lafiya Alhmdlh, duk muka zauna wannan karan da kanta ta tarbeni da kayan kwalam da makulashe sai abinci da rabinsa kayan gina jikine, na rasa ma wanda zanci, zuciyata ke rada mini maza saki jiki kiciyo wa kanki matsala a rasa inda kika shige, wani na zuciyata ke fadin ai akwai Bilal a waje yana jiranki, in kikayi nawan fita ma yasan da dalili, wannan ya dada karfafa mini gwiwa na dada bajewa, ta mike ta kuna mani kallo tana dan yi mani bayanin film din na dan biye mata ta saki jiki totally, wai ina bilal ne? Yana jirana in gama mu wuce,ai ya kyauta hala dashi za’a yi? Eh kawai nace, gaskiya kin mori miji gashi yana kashe uzurinsa don kaiki unguwa, na yi murmushi tamkar wata sokuwa sannan na mike ina fadin zan dan zaga bayan gida, ok bari in bude maki can 6angaren ,ta mike kamin ta dawo na dauki camerar na samu guri na cusata inda ba mai gani sai dai dan kwakwa bayan nayi setting dinsa na koma na zauna ina dadana wayata kaman da gaske,sai gata ta fito tana fadin muje to, ba abin da nayi a bayin na yi flushing na fito na sameta a zaune, to ni zan wuce,ah haba dai? To mum sirikinki na shanya ba gara in hanzarta ba? Ya na iya? Baby sai yaushe? Kila gobe In Shaa Allahu idan na dawo daga computer studies, to ina fa jira kar ki manta, ta rakoni har gurin motar na shiga gidan gaba na zauna tanai wa Bilal tsiya ya tsya yana kallona cikin rashin fahimta nima sai na basar,har ta gama surutanta murmushi kawai naga yana yi, maganarta na karshe shine ka kulan mani da ita ya kada kai sannan ya ja muka dau hanya, na kalli shashinsa ina fadin no mind her, har muka karasa gidan babu mai magana, ina shirin sauka jakata ta fadi ni nama manta na dorashi a kan cinyata, da sauri ya daukemin yana fadi sorry eh? Da ka barshi ma na dauka da kaina, no dat haj say make i take care of u, ban tanka masa ba yau am not in the mood, na ja jiki na shige dakina, da sanda na leka dakinta bata dawo ba, nayi ajiyar zuciya sannan na samu guri na zauna ina tunanin rayuwata ni daya,m
me ke shirin faruwa dani ne? Na ja tsaki daidai sanda ringin din wayar ta azalzala mani, ya na iya? Dole na dauka ina fadin lauyana ya dai? Eh na saka saura recordern, ok, kai da baka gari ya zaka san lokacin zuwanta gidan hajiyar? Sanu mai idanu, ok zan kokarta, na katse layin ina mamakin hikimarsa, wucewan awa daya sai ga wayarata ta shigo, mummy ki mika gaisuwata, to da kayan dadi kuma, uhum, na tsintsire da dariya sannan na shiga kitchen don dora girki yanda zan gama kafin ta dawo gida, shi ya kuma shigowa da sallama, small madam zan iya tafiya? Eh jeka kawai sai gobe kuma, na fadi ina kokarin ajiye abinci a dining table.
Ki zama ready kaulah 12 daidai zata gidan haji Binta, na mike da azamata ina fadin ok, kana gari ne? Ah ah tukunna dai, to idan na gama fa ya zanyi dasu? Kar ki damu gama dai tukun, ki kula fa akwai hatsari inda hali ki karasa kafin kaulhan don kar ta ganki a gidan, to shikenan na fadi sannan na ajiye wayar ina ta safa da marwa,ya zanyi ne yau? Na suri jaka mai dauke da recordern na wuce dakinta, sai ina? Tayi mani tambayar idanunta fes a kaina, Seemah zan duba fa, na fadi ina rausayar da kaina fatana Allah yasa ta gamsu don tana da saurin dagoni, ok kar ki dade dai, nayi mata kiss a goshi da murnata na fice yayin data bini da kallo, yau shi kansa Bilal idanu ya zuba mani, farin ciki na yau ya zama over ko me dalili? Misalin karfe 11 da rabi na karasa kofar gidan daidai sanda mai gadi ke rufe gate da alama wani ne ya fita, na wuce ciki yau matar gidan a kitchen na sameta tana hada delicacies, na zauna a reception din inda nafi zargin bakinta na zama, cincin da kayan flawa ta fara gabatar mani sai drinks mai dan sanyi tana fadin dan ta6a kafin in gama girkin, sannan ta koma kan aikinta tana dan mani hira da yake muna hango juna kitchen din yana bangon 6arin hagun recption din ne, wannan ya bani daman sake settin din cameran dana makala, sannan na cusa recorder a tsakanin manya manyan kujerunta, sha 2 saura na mike gami da cewa bari in shiga sitroom, ok kya ma fi sakewa a can cewarta, na koma can ina dan kallon tv dana samu a kunne
12 :15pm sai ga muryar kaulah ita da haj Bintan ina jiyo sautinsu daga reception din suna hirarrakinsu irin ta hamshakan mata, sosai nake jiyo hirarsu kasancewar gidan shiru ne sai na rage volume din plasma don zan fi jin gulmar, da magana ta dauko hanya sai naji tsit da alama rada sukeyi, Allah yasa dai recorderta ta dauka, abin dana ayyana a raina kenan, wucewan awa 1 ban ji duriyarsu ba sai dai karan kwanuka a kitchen da sahun tafiya jefi jefi, duk sai naji raina ya sosu kar dai sun harbo jirgina? Na yi lamo har naji komai ma ya fitar mani a raina, hajiyar da kanta ta shigo ta kawo mani abinci tana fadin ki ci ban son filako, na dan murmusa tamkar in bita da zata koma inga ko kaulah ta tafi ne, amma ba hali kar ta zargi dalilan zuwan nawa kenan, abincin ma cakalkala shi nayi aikin 6arna don kar ta ce na raina na soma shirin tafiya, saida nayi sallah sannan na koma palon lokacin nayi zaton ta tafi, ai kuwa na tarar ta dawo kenan daga rakiyarta nima na dan dakata ina fadin zan wuce, kai haba? Sai kace wata bakuwa ke da gidanku, bilal fa yana jirana, ba sai ya tafi ba driver ya maidaki, uhm uhm na fadi ina noke kafada, shi kenan ‘yar daru bari ina zuwa,na dakata ina jiran shigowarta,da sauri na dauke su na cusa a jakata sannan na natsu, ta nufoni da leda madaidaicin, jikinsa mai tambarin store tana fadin gashi kya shafa na so in ki kar6a ta kallameni da fadin baki yarda da ni ba kenan, ya na iya? Dole tasa na kar6a wannan karan ma rakiyar har mota tana fadin in law sorry ta shanyaka ko? Da fara’a sosai yace ba matsala in dai akan small madam ne zai yi komai, ni kam na basar na shige ta rufo mani tana daga mana hannu … Ni da nayi karyar zuwa gidansu Seemah banje ba, muna barin unguwarsu haji Binta motarmu ta hadu da su mummy a hanya zamu shiga hannun da suke su kuma zasu fito, na kau da kaina Bilal na fadin see madam na yi tamkar ban ji ba, Allah ya taimaka mani bansan abin daya dauke mata hankali ba ni dai nasan bata kula damu ba, gabana ya tsananta faduwa daidai sanda motar ta wuce juna na kau da fuskata, sannan suna shigewa nayi ajiyar zuciya, small madam wetin? Headache kawai nace masa duk na kosa mu karasa gida in duba records din dana kwaso, Allah yasa kar naji kunya dai, ranar duk na sauya small madam u sure say no trouble? Yayi mani wannan tambayar bayan na sauka, na girgiza masa kai kawai don na kasa magana hankalina na ga jakar hannuna da abinda ya kunsa, shi kam ya zuba mata idanu har ta bace sannan ya fesar da huci daga bakinsa yana dan shafa kansa, son yarinyar yake tamkar ransa, soyayyarta zata illatashi hmmm ruwa ba sa’an kwando bane ko zai dawama yanai mata bauta bazai gaji ba, ya ja ya bar gidan yana tunanin yanda zai shawo kan lamuran…
Muhsin ya dai? Wai kai me ke damunkane? Tun da ka zo lag nake ji a jikina cewa matsalace ta koro ka, haka nan kurun ba zaka kwaso kanka kazo mani ba ana tsakar aiki, natsuwarka, lamuranka, forcus dinka da abubuwa da dama sun ta6u, ya zakayi da sababin client din daka sanya gaba idan ka rasa wadannan abubuwan dana lissafo? Yau kuma da wannan salon ka tashi? Pls ka daure mu fita uni lag na festac akwai wani justice a law department da zan dan gani, Muhammad kyaleni kawai kayi tafiyarka am not in the mood shi yasa kaga na nisanci gida gaba daya, why? Duk hijirar da zakayi sai ka koma inda ka fito, ba gara ka tsaya ka daidaita lamuranka ba? Lets be serious ya fadi yana janyo stool din zama mene ne matsalarka Muhsin?
[5/16, 3:10 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
12…
Ya dan ja tsaki har idanunsa sun kada tsabar damuwa, kwanakin nan ya warke daga damuwar data sanya aka bashi gado, ka yi shiru Muhsin? Ya zan maka da kwakwan ka na tsiya? Ikon Allah naga namiji mai zurfin ciki to ma tukunna dai in ka kasa gaya wa Sa’adah ai ka sanar dani ko? Muhammad its complicated abin da kamar wuya, hmmm dan boko agogo sarkin aiki tunda naga ka takura first tym in ur lyf da ka kauce wa boko saboda damuwa nasan ba karamar matsalace ta tunkaro ka ba, dan fesa mani mana, kasan ai Suhaila ko? Marar kunya nan mai kalar karuwai ko? Sorry ‘yar uwar kace amma ba zan fasa fadin gaskiya ba, me tayi? Ita hajiya takeson na aura all this while gashi ni ba za6i bace ko mata sun kare a duniya ban jin zan iya zama da ita, ya sheke da dariya har da bubuga kafa, hmmm angon Suhaila uwar feleke, kaga her rank go high ko ba komai ta samu namiji daya tamkar da dubu a hannu, ya rankwashi kan yana cizan la66a, shegyan sama Sa’adah zata kwashi ciwon surutu a gurinka kam, kai dama wannan ne ya kwantar da kai? Tsaya mana aku ai ban gama ba, ok ja muje ragon namiji, ban ta6a soyayya ba kai shaidane ban yardama akwaita ba, hakane fa book warmer, sanda na saki jiki ina harkokina kwatsam Allah ya jehota cikin rayuwata, da farko na dauka shakuwace, abota na kirata, sabo na kalli lamarin wannan ne ya sanyani basarwa, amma a kullum yanayin dada bunkasa yakeyi, na kasa gaskata hakan sai da na bar garin gaba daya nakejin ba karya cikin lamuran, hahahaha ya fashe da wata wawiyar dariya, af sorry na manta fa ya kuma kwashewa da dariya wannan ya sanya Muhsin din mikewa ya bar masa dakin, tsaya mana abokina, Ya rufa masa baya yana kiran haba Muhsin ya fadi yana kokarin shanye dariyarsa, kai ne ai wani bahagon mutum mai fadin love is a ferry tail, yau gaka a tatsuniyar gizo da koki ai, yanzun ya kakeji a zuciyarka, kaga Muhammad zo ka fice ka barni inji da damuwata, abin bai kai nan ba ya tsaya daf dashi yana fadin wacece wannan mai sa’ar da sarkin aiki mai ka’idah ke mutuwar so? Yarinyace fa! Na sani amma ai tana da suna ko? Hameedah sunanta the worst part shine mama bata sonta, ran da na ta6a kai ta gida sai da ta kidima ‘yar mutane, sai ka ganta zaka fahimci inda na dosa, i see kuma kace yarinyace? Eh just 16 ‘yar mutunci mai hankali ce, bari in kira Sa’adah taji yau bro dinta na yaba wa mace, tirkashi, kai kasan wannan all i know is mama zata hallakani in ta matsu in auri diyar dan uwanta mai halin kafirai kuma ta hanani auren wace nake so, Allah zaku iya rasani, ya isa abin bai kai haka ba ,ni kam kayi mata biyayya mana inyaso ka auri zabinka daga baya, hmm ba sauki haduwarsu ma matsalace babba, nan sa’adah tayi mani waya ranar da na sa hameedah taje gida kar6an camera, tace ita da Suhailan sun hadu ta tareta zatai mata tijara da isgilanci ita ta jata sukai waje, Allah yaso mama bata nan, ga babyn itama bata daukan wargi na san hali sai dai su daku, wow kace restlers zaka hada, Allah ya tsareni da hada mata babu natsuwa a gidana, da alama hakan ma zata kasance, um haka dai kace amma babyn ma karatu zata yi inji mummynta, book na dukan boko kenan, Allah ya nuna mani ranar da wannan bakin zai mutu cewan Muhsin, kaga matsalarka da izinin Allah zamu shawo kanta tashi muje kar ya shiga karantarwa mu tsaya jiransa, basu wani jima ba suka fito tare da Justice Madu din da yake mai karamci ne, a nan suka samu ganawa da Muhsin shima ya samu shiga daga nan gida suka wuce kai tsaye, nagode muhammad da ka hadani da Justice Madu inaji a jikina wannan haduwar alkhairi ne hulda da irinsu akwai karuwa, hakane fa mai first love at 30,ya isheka kai abu bai wuce maka ne? Hmmm bar ni in fada mana kana son ‘yar 16 kaga 14yrs interval kenan, ya dan jingina da jikin kujerar yana mayar da numfashi, haka soyayya take Muhammad? Na wahala fa, uhm wannan yanzun ka fara ma da dadi idan kayi sa’a, kaga kamar ni da Sa’adah ‘yar albarka mun dace ko? Kai kasan wannan aku sarkin surutu, ko me ka kirani na dai yi maka zarra da nayi sa’ar fara soyayya, ni in ma tambayeka, tasan kana sonta ? No,why? Bani da courage din sanar da itane, i seeee, amma kana da courage din tara litattafai da surutai a kotu? Ya sheke da dariya yana girgiza kai, wannan ne ma ya sanya Muhsin din yi masa banza, ya dan tsagaita yayin da yake fadin its good Muhsin am so jelous, nasan zata soka don tun muna yara kai mai sa’a ne a duk abubuwan daka sanya gaba, zaku ji dadin zama kuma yanda kake maganarta da kuma yanayin shekarun aurenku zaka sha nishadi, akwai banbanci mai yawa a irin shekarunku da tsakanin ni da Sa’adah, ka gane? Bai jira ya bashi amsa ba yaci gaba da cewa ko da yake yanzun na san zakaga kamar na damekane da surutai, amma nan gaba da zarar kun yi auren zaka fahimci manufata, haka Uncle dina a kansa na ga wannan experience din lokacin muna Secondary school,a nice couple and a lucky man, ka gama ? Cewar Muhsin din, shima Muhammad din banza yayi masa ya kunna radion motar don kau da shirun, da haka suka karasa gidan, wata zuciyar ta raya masa kiranta ya ji ya take,amma sai yaji abin banbarakwai.
ABUJA
Ina isa daki na rufe kofata sannan na ja labulan na koma kan gado, a nan na baje kolin kayan cikin jakar don jin bayanai dala dala, na saki jiki sosai ina bubudewa, camera tayi aikinta ba laifi akwai hotunan kafa hujja cikinta, tunda ya dauki su tare(haj binta da kaulah), na dauki recordern zan duba kenan ringing din wayata ta katseni, ina murmushi na karata a kunnena, lauyana na fadi inai masa wasa da salo na tsokana, yar tsigar jikinsa ta tashi, har kullum yakanji wani yanayi a duk sanda yaji tana fadin lauyana, watan ya samu wannan matsayin shi din nata ne, yayi ajiyar zuciya gami da cewa kin bani wahala fa baby, da nayi me? Ya basar ta hanyara cewa ko ki kirani ki gayan feed back, afuwan to yanzun ai gashi zan fada maka ko? Gud ya kikayi? Na karkace ina labarta masa komai, ina ji kira ta shigo wayar na duba sunan Bilal ne ya bayyana a screen din,1 min pls ga kiran Bilal nan bari zan nemeka, ban jira amsarsa ba na katse wayar sannan na daga ta ina fadin ya akayi ne mutumina? Ciwon kan ya sauka? Itace tambayar da yayi mani, eh, dama magani na kawo maki kuma ban gan ki ba, na sha ai na ce masa yayi mani sannu sannan ya katse wayar, nayi dan jim ina nazarinsa, yana da kirki yaji dadinsa, ya mike tsaye cike da takaici, me yasa za tai masa haka? Ta katse masa waya saboda Bilal, ya fika matsayi kenan cewan wani sashi na zuciyarsa, it cant be, da azamarsa ya kuma neman layinta, bugu daya ta shiga, wayarce ta katsen tunanin Bilal, na dagata ina ajiyar zuciya, kin gama wayar? Abin daya fada kenan, eh na amsa masa ina mamakin lauyana, mutum ne wanda duk kwakwanki ba zaki canki mood dinsaba, ya san kansa ya iya controling fushinsa, ji yake tamkar ya fizgota ta cikin wayar, ya lumshe idanunsa yana cizan la66ansa, so ya kike? Ya furta muryarsa so cool, lfy ina ‘yar dariyata na bashi amsa, ina son hakan, me kikeyi? Ina duba sakonkane, me ka gani? Ji nayi yau nishadi tai maki yawa why? Nima ban sani ba ,haka kawai? Eh, kinji dadinki, Mun dan yi hira ba laifi cikin salo na shagwa6a nake ce masa barci, Ok toh have a nice sleep zan nemeki an jima, na gode ka gaida abokinka, na katse wayar sannan na yi juyi a kan katifata ni daya sai ayyana abubuwa barkata nake a raina, na soma karanto azkar kin yamma, a haka barcin yayi gaba dani ba tsammani, knocking din mummyna ne ya tadani da sauri na bude gami da fadawa kanta, lfy Kika kule kanki ? Lau barci, gajiya da son hutu ne, matsa don Allah sai lalacin tsiya tamkar wata sarauniya, ga daddynki can a palo yana neman ‘yar shiririta, kai mummy ni din? Ta yi dan murmushi sannan ta wuce sashinta tana taku daidai ba abin da ya sha mata kai, na juya nan na iskeshi yana dadana laptop, business manya, muna ta hira mutumin bai gajiya dani sam ya bani ledoji yana fadin ban mantakiba, kinga namafi mummynki damuwa da ke ko? Ya iya tsokona kam, ya kara da cewa ko pencil bata tuna dake ba a siyayyarta, na jinjina masa kai ina dariya, maza to kije kiyi sallar magaruba nima masallaci zani,ok nace inai masa godiya daga nan dakina na nufa,ni kam nayi sa’ar iyaye ina zan sanya kaina don murna? Abinci muke ci a dining table muna hirar mu, baby ga shi na kalleta,card ta mikomin sannan ta kau da kanta, na budeshi cike da doki da sauri na rungumeta ina shewa, cikani karki 6allani ki sanya mijina a uku, mummy ni me yasa tuntuni baki sanar dani auren ba? Kece ai waliyi na kya tsareni ai da tambayoyi, na daina yauwa anko, special outfit, uhum grand entry, mummyna zan fito da ke wow, na fadi ina doka uban tsalle a kan kushin, ta saki baki tana kallona na rufe idanuna ina dariya itama dariyar na bata, ta tsintsire da dariya tana girgiza kai.
Shirye shiryen biki ya kan kama kwana kusa aka sanya don angon ya matsu ayi a wuce gurin, mummy ta sanyani na kai ma Seemah IV, yau ma da naje shiga gidan ban sha wahala ba amma na sha kallo gurin mutan gidan, duk wanda na wuce sai na gaisar ina ga zatonsu seemah ce gata yau tana gaida jama’a ko a ina ta kwana? Na tsaya a tsakiyan gidan ina kwala sallama, yau kam princess din ce da kanta ta fito ta sameni cikin shiga mai tsada da gani fita take shirin yi, ta leko ganin ni ce ya sanyata fadin yau kuma da wanne kika zo?ke nifa ban ma yarda da wannan zaryan da kike mana kwanan nan ba, ko na tuwo ake nema? na San a nan akafi auki, talaka ko kajaga? Tana wani yamutsa fuska, alkhairi na fadi sannan na kau da kaina, gashi na mika mata katin ina fadin gayyatar biki ne, ta sanya dariya oh kin samu mai kwasar rashin asalin ne? bakin ya mutu sanda ta soma karantawa, na bar ta tsaye ina iya jiyota tana kwala mani kira, Hameedah na basar da sauri ta biyo bayana tana fadin kinaji inai maki magana kika yi banza da ni ko? ,ke me yasa baki da mutunci ne? Har kurace zatace da kare maye? Na mayar da wannan kalmomin yayin dana juya gareta lafiya? Me zan maki? Kiketa kwala kirana a sarari, ta ja tsaki tana fadin alfarma zan maki kizo mu fita store tare kila ma in ta kama muyi sayayyya iri daya, ko? Na fadi sannan na ta6e fuska, am busy kin gane? Na barta nan tsaye bilal ya ja muka bar masu gidan, naga alama abin yayi mata ciwo, small madam who be that? Kawatace na fadi sannan na bar maganar.
Mummy taso muyi siyayya amma daddy ya hana cewarsa da an gama karar kotu zamu tattara mu bar kasar CANADA zamu koma yace a can yake da zama, harkokinsa sun fi ci a can, ina zaune a palon gidan ina dan duba ovation don za6an kwaliyar da zata dace da mummyna ni zan mata ado ko ta ki ko taso, gefena lemone ina dan sha ina duduba magazine din,turo kofar da akayine ya dau hankalina da yake na dan turata na saki labulan ta ciki, itace kamar ko yaushe cikin takun takama ba ko sallama, na kau da kaina ina yin abin da na sanya gaba, ina mutan gidan? cewarta tana dadanna waya, yanda kika San Allah bai hallici wata a gurin ba haka nayi mata, Bakiji ne ina magana ta fadi cikin daga sauti, ke dakata nan gidanmune don haka duk wanda ya shigo cikinsa dole ya bi tsarin musulunci, mai hankali bai Shiva guru said ya nemi izini, kin fado ba sallama bare gaisuwa, mu musulmai ne munsan darajar mutane mai aiki ma mutum ne cikake kaman ki, ta katsen hanzari ta hanyar cewa ya isheki kar ki kuma zagina don na zo gidanku baya nufin zan dauki cin kashi ya kamata ki fahimci cewan ba gurinki na zo ba, Allah ma ya rufa maki asiri ba don govt ta tallafa maki ba ke kin ma isa ki taka inda Princess Seemah ta taka? Na mari bakin ina huci ta saki kara cikin radadi ta cakumi wuyan rigana, daga ni har ita ba wanda ya san sanda ya iso sai ganinsa mukayi ya shigo tsakanin mu yana rabamu, na natsu ita kuma ta ci gaba da cewa ni din nan da kika raina sai na gyara maki zama, enough of that nonsense cewan daddy, me ya hadaku? Ya kame a tsaye sannan ya zuba mana idanu sanda ya kalli Seemah, sai inga ya juyo kuma ya kalleni na juya na wuce dakina ban san ya suka kare ba…
Yau yinin lalle akayi a gidan mun sha kunshi hankalin mummy na gareni kar in mata nisa, an min an mata da yamma Seemah tazo tayi sha’awa mummy ta sanya akayi mata itama, jama’a sai bata hameedah suke don ni a dakin mummy na zauna ita kuma ganina a dakin ya sanyata komawa palonmu bata kaunar muyi shearin gurin zama, balle mu hada wani abu, shi kansa lallen daban ta sanya akayi mata, no kuma irin na mummy aka zana mani, a haka aka soma shagulgulan biki mai kayatarwa, ba’ayi gayyata da yawa ba amma mutane sun cika mana gida da yake mummy mai jama’a ce, muhsin bai zo ba ko me nayi masa? Seemah ta kawo Haji Ni’ima, haj Binta kuma ni tazo ma, madam Zarah kam gift ta kawo mana na kece raini don bata samu daman zuwa ba, ba’a maganar ma govt, sha tara ta arziki mummyna ta samu, fareedah, ummu Abdujabbar(mama kulu), ministoci,da iyayen yaran da tayi rainon su irin su Yusrah, Siyama da Seemah ‘yan mata sa’annina wayanda muka kula kawance dasu, ni na zauna a sit din aminiyar amarya, na kame abuna tamkar gaske, nayi kwalliya na fito sosai ban damu ba sai dai ba wani abu mai yawa akayi ba aka saki kida alaman taro ya soma watsewa, sai rabon abubuwa akeyi harkar girma da hutu aka yi komai cikin wadata, kaman ance daga kanki na hango shigowarsa cikin kyakyawan shiga, ya dan fada amma shi din mai kyau ne, sai naga tamkar an kara masa kyau, shigarsa cikin jallabiya coffe brown, ya kara hula ‘yar karama fara sol wanda gashinsa kawai ta rufe, hannun dauke da links , gayen nan yayi ne ba karya, ko don taba ganinsa a haka bane sai cikin suit? a ko wani yanayi kyau gareshi, nayi nufin saukane shima naga gurinmu ya nufo yana daga mani hannun jinjina, na gyara zaman gwagwarona gami da dan tattare rigata yayin da nake ratsawa cikin jama’a gudun kar a takamani in fadi da yake doguwar gown ce wace ta dace da ni, baby kin ganki kuwa? Ya sanyani tsayawa ina kallon kaina sannan na matsa gareshi ina fadin ka ganka kuwa? 2 min pls bari inga Bilal, kar ki dade ya fadi ni kuma na wuceshi, makulan gidan dana mota na bashi ina fadin ya debo drinks a fridge mu sallami baki, small madam u look muah(kiss) yayi da bakinsa a iska, ni kam dariya ya bani, Bilal baka rabuwa da raha kai kam, ya fice ni kam na juya gareshi ina fadin yaushe a gari? Shigowata kenan ko ki sanar dani abin arzikin daya samemu? na marairaice ina fadin Ayya ni nasan mummy bazata barka ba shi yasa ban damu da sai kaji daga gareni ba, me zan baka? Komai ma, me kakeso? Ke, na dan yi far idanu ina fadin ka dawo kenan ka zan dai ni ba abinci bace ko da yake akwai shawarma in kawo maka? Yayi ‘yar dariya ita wannan a kayan dadi kawai tafi auki zatonta kowa ma ra’ayinta gareshi, kayi shiru, kawo to, na tafi na shirya masa da ice-cream na kawo inda nai masa mazauni, ka sha hutu abinka sai ka yi tsawo naga kaman an rage maka ki6a, me zai yi in ba dariya ba? Waton an rage mani kiba ko? Eh mana gaka nan ka zama kwalancukwe (slang din dake nufin Dan siriri),baka cin abinci ne ko? ina zuwa na ce masa, sakwara da miyar agushi ga nama da ganda, sai drinks dana kwaso ina tafe ina hardewa a hanya, na dire a gaban sa, kaci kila ka samu ka koma kaman da, ya tsira mani idanu ko me yake kallo haka? Ai kuma ba rana daya ake kiba ba baby ,shi kenan zan gaya wa Sa’adah ta rika baka abinci da yawa, ya jinjina kai gami da cewa zauna to ki tayani hira in ci abincin naki, mu na nan zaune Seemah da hajiyarta sukazo wucewa, da harara muka rabu, hajiyar ce ma ta dan daga mana hannu…
[5/16, 3:10 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
13…
Muna nan a zaune naji wayar mummy ta shigo, kina ina? Muna tare ne da Muhsin, ok mu fa zamu wuce ya kenan? Mummy bari in taho to, kar ki dade ya maidoki kafin 12 kin ji ko? Na kalli agogon hannuna daya nuna 11-30pm, Na katse wayar daidai sanda Bilal ya iso garemu yana fadin Small madam nyt don reach o, ban kai ga cewa wani abu ba naji yana ce masa ya je kawai zai maidani gidan da kansa, na madam say make i carry her, Muhsin din bai kara magana ba miskilin namiji kenan, ni nai masa alaman ya je kawai sai goben, naga yanayi na rashin jin dadin hakan a idanunsa ni din ma ba haka naso ba, amma hakan ya dace inyi, na rasa dalili haka nan kurum nakeji a raina ban kyauta ma Bilal ba, ka yi shiru? Hmmm sai yaushe zaki koma wa driver ki rabu da taxi? Ba rana amma kila idan kara ta tashi da gaskiyarta, daddy yace CANADA zamu koma, a can zakiyi ilimi kenan? Na jinjina masa kai kawai,kin zama so cool lfy? Kai zan tambaya yau ka canza mani, baby ni aikinane kan sanyani gaba,ke fa? Oho! Na fadi ina daga kafadata,yayi dan murmushi yana nunani da dan yatsansa manuni, ke fa sai dai a barki, wayar seemah ce ta shigo mani, hameedah taimaka kizo please, wayarsa naji tayi ringing ya karata a kunne, lafiya seemah? Rabin hankalina na gareshi ,na gaza concentrating, wannan dalilin ne yasa na dauki cup din juice dina na fice, a harabar hotel din na hangota ,na katse wayar gami da daga mata hannu, ta nufoni tana murmushi, Baby am sorry cewarta tana goge kwalla, duk said na rikice ,me ya faru? nothing, just feeling the guilt of my arrogance , na ja kujera na zauna gami da ajiye cup din juice dina a gefe na ina kallonta, Seemah! na kirata a sanyaye ina jin abin da nakan ji yana mani yawo a jiki idan nayi tozali da ita, wannan dalilin ne ya sanya naso muyi kawance ta watsan kasa a idanu, ashe kaunace ta ‘yan uwan taka, dear bani da riko, idan kika karanceni sha yanzun warkewa yanzun CE, ta jinjina kai tana matsar kwalla, clean your tears na fadi ina murmushi hankali kwance, waya CE ta shigo Mani na daga gami da Baron gurinta ina fadin kazo muna entrance fa, OK, na koma gurin zamana ina jin dadin mun dinke 6arakar mu, can we be friends? ta Mani tambayar tana langa6ar da kai, we are more than that, our relationship is beyond just been friends,ta rungumeni tana shasheka, its okay nace ina rocking dinmu, tafin da mukaji tamkar filing muhawara be ya sanyani janye jikina daga nata, na mayar masa da murmushinsa ina fadin are we gud to go? ya daga Mani gira yana daga kafadu gami da ware hannaye, wannan be ya sanyamu mikewa gaba daya, na kwankwade sauran juice dina sannan muka bar gurin,saida mortar su Seemah ta wuce sannan muka nufi motar Muhsin, baby! na’am, watch your steps please, ba kowa zaki rika welcoming ba ,mind the way you accept people, especially those that have hurt you before, give them more time to repent, be sure they are real, Seemah is my unknown twin, na sani cewarsa yana laluban makulin motar, amma ka dawo kenan ko? I think so cewarsa yana kokarin bude bangaran driver, lauyana na ambace shi ina jin jiri yana dibana, na karasa na dafa motar da sauri ina layi, da sauri ya dawo inda nake yana anbaton lafiya a rikice? da in ina nake fadin am not O…. o…. o…OK, da sauri na rungumoshi ina shinshina ko wani sashi na jikinsa, ba karamin jarumta yayi ba gurin hankadeta yana tattaro nutsuwarsa, baby me haka? kar ka gujeni please ta fadin cikin kuka sosai tana shasheka yayin da jikinta he rawa, zaro idanu yayi yana karanto Duk wata addu’ar data zo masa, Allah yasa ba gadar zare Seemah ta hada masu ba ,ya furta cikin damuwa mai yawa, kafin ya ankare har ta fizge madaidaicin mayafin data yane kanta dashi tana kokarin zuge zip din rigar, da sauri yayi nufin riko hannayenta yana fadin it can’t be, ta rukunkumeshi tana dariya, ni zaka ma kwalele? suka soma kokawa, daya riko ta sai ta fizge, da kyar ya samu ya daure hannayenta 2 da nayafin data jefar, ta turo baki tana lasan labbanta da harshe tamkar mayyar data shekara bata samu na lashewa ba, ya bude motar sannan ya dorata kan sit din baya yana haki, dabara CE ta kare masa, ya zai yi? da yasan hakan ce zata kasance da bai zo dinner nan ba, ya Dora hannaye 2 a ka yana hangyan yanda mummy zata yi idan ta gansu haka… Murna fal cikinta, fatanta hakarta ta cima ruwa, Hameedah this is your down fall, you are ruined ,ta furta tana gyara zamanta a began hadadiyar gadonta, I would have play smart and calk your so called mummy taga babynta a wannan halin, but not so fast, idan sha’awar ta ci ubanki sai ya dura maki ciki, slow poison is the best, the world will see the fruit of lawyer and client, ta tsintsure da dariya tana rike ciki, yayin da hawaye ke gangaro mata,this is just the beginning, ta furta gami da kashe bedside lamp tana shirin kwanciya barci…
NO doubts, ya fahimci abu ta sanya mata cikin juice, how comes? Seemah whyyyyy? ya harde hannayensa 2 cikin summar kansa yana jin wani yanayi a tattare dashi, ya ma akayi suna magana ta fita bai kula ba? dam it ! ya furta yana buga hannunsa a jikin motar, Sa’adah ce ta fado masa ,amma kuma dare yayi ga mama tana gidan, shi yasan ko giyan wake yasha ba zai soma kiran iyayen yarinyar ba cikin wannan halin, da sauri ya nufi motar don ganin halin da take ciki, wayarta na gefe guda tana ta faman ringing, kiran mummy Rahmah ne, yayin da babyn keta kiciniyar kunce mayafin daya daureta dashi, Allah ya isa ta furta idanunta na fitar da kwalla, I know it all, ni kake gudu ko? a sanyaye ya danna mata silent, toh, me zai ce mata? wallahi sai na raba kaina da wannan din,ta fadi tana zuburo bakin dake nuna igiyar, ya dafe goshinsa gami da janyewa gudun abin dake fizgarsa gareta, da azamarsa ya soma lalubo lambarta yana fatan samun salama a wannan yanayin, ya kalli agogon daya nuna 12:30am, duk yan biki sun watse ,abinka da hotel ba Wanda ya damu da wanzuwarsa a gurin, ko INA tsit idan kika dauke bakin da sukayi booking hotel rooms dake gilmawa jefi jefi, toh wa zai kira ? trust no 1, ya dada jarraba layinta hat tswaon wani lokaci no answer, cikin barci ta lalubi wayar ta danna mata silent tana kunkuni ba tare da ta duba mai kiran ba, haka sai yaci gaba da kira ,wayar taci gaba da haskaka mata fuska alamun mai kiran ya nace, ta ja tsaki gami da danna ta a speaker tana fadin waye? Muryarsa ce ta sanyata watsakewa, Broooo! ta mike a hanzarce tana tunkude duvet , sannan ta sanya takalma tana binciko kayan sakawa cikin wordrobe, a hanzare ta hau sauya wasu Dana baccin jikinta yayin da wayar me makale a kunnantatana sauraron sa, amma kasan dai ban isa in ja daya daga cikin motocin parking lots ba ko? I know ya fadi daga day an bangaran, Nima ai banson mama ta fahimci wani abu, ta cigaba da harhada first aid box da duk wash abubuwan da take ganin tana bukata, what do we do? find your way out of the house first, bari zan kira Anas ( abokinsa da suke makota, yanada da mata da ‘yan yaransa 2 gwanin sha’awa)ya bamu Aron mota, ta katse wayar tana hararan schedules dinta na gobe, I planned 2 sleep and rest my brain ta fadi cikin takaici tana hura hanci, I will be on call as early as 7am ta karasa tana fincikar Jakarta, yaushe na dawo daga aiki gaba daya yau? ta ja tsaki gami da kashe wutar dakin, sannan ta jera pillow kan gadon gami da rufewa da duvet tamkar itace kwance, Allah ka doramu kan mama ta furta sannan tayi hanyar waje… wucewar mintina 30 shiru ,no answar ,ya katse wayar cikin tashin hankali yaje fadin Allah kaga zuciyata, this is my only hope, Anas pick cewarsa yana kokarin neman Layin, ya kuma kallon agogo dake nuna 2am, ko in kaita asibiti ne? toh wani asibitin tukunna ma ? da hanzari ya soma laluban ID card cike da kwarin gwiwan ya samu relief, to his greatest surprise bai duko ba, tana cikin aljihun suit din daya cire, kiran Anas din ne ya katse shi, da sauri ya daga yana fadin shegen sama, ina tare da iyalina ne, Muhsin jekayi aure please ka daina kiran masu aure at late hour, Anas ka wahalar ni, Sa’adah na gaban gidanku for an hour, lafiya? chill guy, mota zaka bamu ,tawa ta Dan samu matsala kuma na rasa yanda za’ayi in koma guda,it’s urgent pls, mace ce fa, I know, toh, Allah ya kare, amin cewarsa, suka yi sallama sannan ya katse wayar,yana kokarin turata aljihu ta kai masa damka cikin zafin nama tana fadin wa na kama? ta sammace shi, wuyansa ta matse da hannayenta 2 tana fadin an gaya maka bazan iya bane? jini me diga daga hannayenta duk ya bata Mayan jikinta, amma ko zafin ciwukan data juwa kanta garin fada glass din mota ta fito ta window bata ji, hankali da zuluminta na ga cikar burinta.
Wani irin karfine da ita , wannan dalilin ne ya sanya sa jin azabar data me gana masa, tari yake yana kiciniyar kwatar Kansas don ta matse masa makoshi, baby please cewarsa cikin raunaniyar murya idanun sun yi ja zir, na San baka sona ai ta fadi tana Dada cakumar wuyar , who said so? ina tsananin sonki ,kaunarki tana wahalar dani ,ta saki dariya tana kyakyatawa, really? amma ban ga alama ba, da dabara ya banbare mata hannaye yana fadin come to me in nuna maki kalar son da nake maki, cikin zakuwa ta rike rigar zata yaga da sauri ya riko hannayen yana fadin tsaya cikin rawar baki, ta galla masa harara tana Jan kwafa , yayi murmushi yana kallon ta ,sannan ya riko hannayen yana mai cewa why did you do this? bai ankare ba ta kai masa runguma tana kokarin dannesa, yayi namijin kokari gurin matseta gam, ta saki karat data karade harabar gurin tana fadin kafata, da sauri ya cikata cike da tunanin wani abin ne ya harbi kafar, yana cikata ta keta rigar, karar yagewarta ce ta dau hankalinsa, da hanzari ya mike daga durkushen dayayi yana duban kafar datake wa kwarmato, daga it a sai bra da under skirt, ta sanya hannu zata cire skirt din na ya kau da kai sannan kifar da ita da kafarsa ta fadi ,ba tare da bacin lokaci ba ya lulunbeta da rigar yana nannade ta da shi tamkar goro, Allah ya isa macuci, ta furta cikin jin zafin kifewar, ko ina na jikinta ciwo take mata, musamman yanda ya had a dukanin jikinta cikin riga, ganin bata da mafita ne ya sanyata harbinsa da kafarta tana yi tana kukan ya zalunceta, cikin huci yake furta ,Allah ya tsareni tsawon rayuwata ban tana aikata zina ba, In Shaa Allah bazan soma ba akanki, tayi dariya cikin sautinta na bakin cikin yayin data ci gaba da cewa let me go, dai dai lokacin hasken mortar data shigo hotel din ta dallare masu idanu..
Ta daga labulan palon tana kallon gate tamkar tana expecting wani, mine I believe she’s fine, muje ki kwanta, I trust d guy,I do too cewarta amma diya mace sai da sanya idanu, besides, wannan mafarkin danayi kanta is a bad one, gashi daga ita har shi babu mai daga mana waya, he ki canza kaya mu koma hotel din toh, let’s check and see if anything is wrong, shi din ma yana dai karfafa mata gwiwa ne amma deep inside him hankalinsa ya ki kwanciya, wucewar mintina 2 ta karaso gareshi cikin hanzari ya tayar da motar suka bar gidan.
Da saurinta tayi parking ganin abin ya wuci zatonta , toh me ya kawo hakan? a iya sanin ta dai Hameedah kamila ce, ta karasa inda suke tana fadin what exactly happened here? no time for explanations, me zaki iya mata? ruwan lemon tsamin data matse tun a gida ta hada da ruwan dumi daga flask sannan ta umarci ya danne hannayen ,sun sha wahala kafin su samu ta sha ,don fesar wa ta dinga yi tana yatsina fuska, hancin Muhsin ya danne ta kasa shakar numfashi hakan ne ya sanyata sha ba don ta so ba, wahalar data sha shi ya sanyata yin lamo tana raba idanu, allura Sa’adah ta mata sannan ta natsu, muhsin ya sanyata cikin motar suka tayar ta Anas da Sa’adah ke ja na gaba yayin daya rufa mata baya, suna fita motar su mummy ta sanya kai cikin harabar hotel din ,ai bata tsaya jiran yayi parking ba ta bude motar da gudu ta fice sannan tayi cikin event hall din, ba kowa sai ma’aikatan daketa kai komo, ta fice zuwa harabar gurin tana dube duben guraren da motoci suke ,karar wayar muhsin ne ya katse Alhaji Buba dake fadin taho muje gidansu mana muji shi din Ina yake, mummy ta tsura masa idanu ba don ta fahimci inda ya sanya gaba ba, toh yaushe ma ta San gidansu? ko babynta bata jin tasan gidansu lawyern nata(mummy kenan, ‘yarki mai wayo ce), ya karata a kunne cikin doki gami da cewa ,Subhanallah, how manage? yanzun kuna Ina? a sanyaye ya kara da cewa toh Alhamdulillah, Allah ya kiyaye gaba ,kuna Ina ne ? ya katse wayar yana kallon mummy data cukwikwiyeshi tana son jin batun, hatsari sukayi cewarsa yana Dan bubuga mata baya ,bt she’s fine, yace suna asibiti doctor ta bata kulawar gagawa har tayi barci, taja ajiyar rai tana fadin no wounder, amma nothing serious except injuries, muje please cewarta tana kokarin raba jikinta da nasa, not now, muje kici abinci tunda kin samu labarin ta ko? first thing tomorrow morning zamu je mu taho da ita gida, ba musu ta juya tana jin hankalinta na kwanciya…
Ya kalli Sa’adah data kafesa da idanu yana murmushi kwallar farin ciki na silalowa daga idanunsa , Alhamdulillah for passing this test ya furta a sanyaye yana kallon babyn dake barci sosai, poor girl ya fadi yana kokarin tayar da motar,
don isa gida, Sa’adah ta shige gaba suka bar wurin don tsayawa sukayi kiran su mummy dama, saida ta mika ma Anas motarsa sannan suka yi parking nesa kadan da gidan, a kafada ya sabo ta yana fadin Sa’adah be fast din Allah, cikin sanda ta shige Palo don dole ta nan zaki wuce ki shiga duk wani bangare na gidan, kofar kitchen din da aka turo ne ya sanyata labewa jikin labulai tana zaro eyes, auta husnah ce hannunta rike da cup tana sipping ruwa ,wannan ne ya bata Damar leka dakin mama cike da fatan da cewa, ta yi murmushi gami da ficewa da sauri ta sameshi a bakin Palon ,she’s fast asleep ta furta cikin rada, ya shige ciki ta rufa masa baya, kai tsaye dakinta ya nufa ya ajiyeta kan gadonta yana fadin take care of her don Allah, me kuke bukata? kaji mutum ni da aikina kuma ,yayi murmushi yana fadin YOU ARE A LIFE SAVER , Alhamdulillah I have you as a sister, da azamarta ta soma dressing ciwukan hameedahan sannan ta gyarata fes ta sauya mata kayan jikinta zuwa Riga da wando ‘yan kanti, zuciyarta cike da tunanin wannan lamari , ba Jimawa ta bingire gefanta sukayi barcin tare, tamkar cikin mafarki ta ji hannayenta a kunshe, a hankali ta bude idanun ta tar kan Sa’adah dake sanya farar rigar likitoci cikin sauri , idanunta suka kawo kwalla tana kokarin gyara zama da sauri ta karasa gefan gadon tana murmushi, ya jikin? ta fashe da kuka tana shasheka , me nakeyi a nan? daran jiya ne ya fado mata , duk abin da suka rika faruwa tar cikin idanunta, nooooo ta furta cikin tashin hankali, ta rungumeta cikin rarrashi , dama tasan za’ayi hakan, ta tsura wa boobs dinta idanu tana ayyana yaga wadannan a ranta, ta kuma fashewa da kuka tana rintse idanu, no hameedah bar wanan kukan, tashi in tayaki kiyi wanka ki shirya muje asibiti ayi checking dinki, tana jin Kalmar checking ta dada rudewa ,da sauri ta saki wandon jikinta tana son tabbatar da abin da take zato bai faru ba, wannan ne ya sanya Sa’dah dariya tana kyakyatawa ,ke ba fa abin da ya faru, taja mata hannu zuwa toilet gami da tara mata ruwan zafi da yawa a jakuzi, be careful please kar ki jika hannunki, ta barta don tayi wankan sannan ta koma daki ta hada mata kayan sawa tana karasa shirinta.
Ta hada kai da gwiwa tana jin tsanar kanta mai tsanani, a hankali ta saki kukan takaici da dana sanin tsayawa dashi a hotel daran jiya bata bi iyayenta ba, shiru ba Hameedah ba labarinta, ta kwankwasa mata toilet din tana fadin kin gama? shirun data Jine ya sanyata tura kofar tana fatan lafiya , yanda ta barata haka ta sameta, baby am late tashi don Allah, ta dago jajayen idanunta tana fadin ni ban iyawa cikin shagwaba, OK bro kazo ka taya ta wankan cewar Sa’adah cikin daga sauti ,ai da sauri ta mike garin shiga jakuzin har zata kifa ,ta kunshe dariyarta tana son zama serious, bari in hada mana breakfast mu wuce dashi cewarta tana kokarin ficewa daga bayin, Sis ta furta Wanda ya sanya ta dakatawa, ya dai baby? mummynah … ta tari numfashinta ta hanyar cewa she’s aware cewa accident kukayi daran jiya, shi yasa nace we should be fast ,don suna hanyar zuwa inda nake aiki dubaki, cikin mintina goma suka kammala shiru tsaf, ta kira Muhsin a waya tana fadin Bro we are ready, ta zazaro idanu tana fadin shi zai kaimu? no zai je dakin mama ne don mu fita ba tare da tasan kina nan ba, ta ja ajiyar rai tana jin hankalin ta ya Dan kwanta don Sam bata kaunar tozali dashi, ya wuce sashin maman don tsareta da surutai karta samu daman fita kitchen da wuri, auta da ummu salma ne suka shirya breakfast yau, da azamarta ta yi gaba dauke da kwandon breakfast da dauran tarkacen asibiti yayin da Hameedahar ta rufa mata baya, sai da ta tabbatar sun fita daga gidan sannan ta kira ta sanar dashi suna waje, shima ya sallami mama dake banbamin yana bata mata lokaci kan batun Suhaila, da sauri ya koma dakinsa don daukan car key ya wuce chambers inda ake jiransa.
Da saurinta ta karasa gareta tana kare mata kalli sannan ta rungumeta tana fadin Alhamdulillah you are sound ,mummynah cewarta hawaye na gangaro mata, shhhhh its OK , ya abin ya faru ne wai cewar daddy dake kare mata kallo ,ya karasa gareta yana shafa mata kai, a hannayenki kawai kikaji ciwon? ta girgiza kai tana tunanin karyar da zata hada, hakan nan kawai ta tsinci kanta da cewa I don’t know how it happened, kawai ina answer call din Seemah ne naga motarmu tana tangal tangal ,tsoron mutuwa ce ta sani buga glass da takalmina ya fashe sannan na fita ta window,he struggled hard kafin motar ta tsaya, ni a gurin na suma dana tashi na ganni a nan, kwalla suka cicika idanunta tana jin radadin wannan abu, how can she tell them it’s Seemah? how will the story sound? Iran kuma ta fadi gaskiya ta karyta lawyernta kenan, ta soma yarfe hannayen cikin tarin damuwa take fadin I hv bruises on my Tommy too, Subhannallah cewar mummy tana daga mata blouse, da yanka gashi nan a gefan cikin har an mata dinki, sallamarsa ce ta sanyata cusa kanta cikin jikin mummy, tayi luf tana sauraron muryarsa dake cike da kamala, wani irin kunyarsa takeji a yau, thank you cewar mummy tana shafa kan baby, daddy da muhsin din suna tattaunawa, baby gida zamu koma ki karsa warkewa a can, nima haka nakeso mummynah ta furta tana jin hakan yafi a ranta, muryar Doc Sa’adah dake shigowace ta katse hirar, mummy gara dai ta gama receiving treatment din a nan, though nothing serious is remaining amma she needs to rest, ko zuwa gobe ne sai ta koma gida, da mamaki mummy ke kallon ta sannan ta riko hannunta tana fadin Sa’adah surprisingly, ashe kece? yeah medical personnel ce ai cewar Muhsin, ba komai she will stay yanda kikace, ba haka ‘yartata taso ba, hakan ne ya sanyata dago kai tana cunno baki, yinin ranar tare da mummy and Daddy sukayi shi a asibitin, Muhsin ne dai tuni ya koma bakin aikinsa saboda rana ce da yake busy sosai.
Da murnarta ta kamala shiru tana son sanin halin da Hameedah ke ciki, ba karamar murna tayi ba da ta kira mummy taji suna gurin Hameedah, zanje in gan ta ,buri na ya cika ta fadi tana tsalle da juyi…
[5/16, 3:10 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
14 – 15
14…
Sa’adah bata wani zauna dasu ba saboda kula da sauran patients dinta da suka dauke hankalinta, iyayen nata ne dai a kusa suna riritata, daddy ne ya fita da taimakon kwatancen mummy ya siyo masu abubuwan ciye ciye iri iri, mummy ce ke feeding dinta yayin da tayi kwanciyarta jikin daddyn tana ci yana bata labarin Queen’s university dake Canada, I want mah gal to be a professor of great repute ya fadi yana ja mata hanci, wannan ne ya sanyasu dariya gaba daya dai dai sanda aka turo kofar, mummy ta mike da doki take fadin daughter dama kina hanya? ganin Seemah ce ya sanya Hameedah ta cuno baki tana fadin Ouch! what cewarsu har suna hada baki, ai mummy bata San sanda ta nufi gefan su tana duduba hannayen ba, mine ka taba mata ciwon ko? bata jira amsa ba ta tsintsire da dariya tana fadin am joking mummy, haka nan kawai nake son Ku kusa dani, sai abin ya ba daddyn dariya, Seemah ta tsira masa idanu tana kallon sa, the man is gorgeous ta ayyana a ranta, from his speeches and introduction that dinner night ta fahimci multi billionaire ne, a successful business tycoon at that, Canada ta ayyana a ranta, where will I be when she will fly abroad for studies? hy cewar daddy Wanda hakan ne ya katse mata tunani, tayi yake gami da karasawa ciki mummy ta bata White chair suka gaisa , daddy sarkin sin ‘ya’ya ke fadin come over here yana nuna mata gefansa, Hameedah ta runtse idanu tana karanto duk addu’ar data zo mata gudun kar ta shako wuyar Shegiya, I like you because you look very much alike ya karasa yana nuna baby, tell me more about your self cewarsa cikin fara’a, ta soma introducing kanta a nutse tana wasa da yatsunta, ya nutsu yana karantar duk wani motsinta yayin da abubuwa barkatai ke masa yawo a kwanta, ciki Kuwa, har da kwadayin bin didigin asalin Seemah Abdulhalim Kusada, haka nan kawai yake jin there is a mystery behind this resemblance, ko dai balain son yara ne ke ingizasa? ta mike cikin takaici don zuciyarta na kaunar barin inda Seemah take, ya riko hannunta yana fadin ina zaki? strolling kawai ta iya furtawa, OK let’s walk you out baby, shi da mummy suka sanyata a tsakiya daga dayan gefansa kuma Seemah ce tana bashi labarin school daya sukayi da baby, deep inside her tana kwadayin ya kasance mahaifinta saboda matsayinsa, dukiyarsa, kyawunsa,kirkinsa da yanda ya iya gayu, Seemah fa duk inda harkar girma yake tana kaunar cusa kai, ko ba komai zata yagi rabonta, tana da kwadayi da buri mai tsanani, ta Dan jima har su mummy suka zo tafiya don Sa’adah a barta ta karasa ladanta, gobe suzo su dauketa , daddy da kansa yace ta bari zasu sauketa gida kafin su wuce ,farin ciki fal ranta sai dai Hameedah na hana ruwa gudu ta fadi tana cizon dan yatsa, hirar ta mika itama ta saki jiki tana warware masa zare da abawa har suka karasa inda zai sauketa gaban gate din gidansu, tana daga masu hannu suka wuce ,wani kululun abu ne taji ya tokare mata makoshi tunawa da ance fa hatsari sukayi, nothing happened kenan ta raya a ranta tana jin takaicin bata lokacinta da tayi gurin shirya plan din, idanunta suka kawo kwalla ,ta buga hannayenta a gado tana duka gami da cewa why is that idiot always ahead of me? kuka ya kwace mata tana jin zata iya kasheta ta huta, kowa na mata kaunar da ita ta rasa, even if she had no biological parents, am sure those couple are what any child will pray to have as parents, riches and wealth, ta saki jiki kan gadon ta tana raina MATSAYIN nata iyayen, walllahi sai naje abroad karatu na furta cikin daga sauti tana hararar dakin ,abi kadan Hameedah, daga cewa Ouch duk sun wani rude ta fadi gami da Jan tsaki, baby up ,baby down, katuwa da ita sai sangarci take suna ingizata, ranar dai Seemah kasa barci tayi ,ta raba daran tana zulumin Alhaji Abdullahi Buba da komai NASA…
Sis, na’am baby, kin San me? sai kin fada, I like you , tayi murmushi tana gyara mata zaman pillown kanta sannan ta janyo kujera ta zauna dai dai saitin fuskarta suna hira don dare ne, ni dai ban iya jiran har sai sun zo daukata ki maidani please am missing home, amma din Allah kar ki bari ya kuma zuwa gurina ,why? ya gama ganin jikina fa ta karasa tana sharce kwallar fuskarta, is that the only problem? ta daga mata kai tana kallon ta, can you pretend like nothing ever happened? tayi Jim din ta gaza bada wannan amsar, taxi gaba da cewa dama fa Seemah so take ta rabaki da makusantan ki, wannan dama ce a ganina ki manta komai kar ki bar space din da zata yi yanda takeso, ni nasan mah Bro is handsome and he’s a crushe……tayi dariyar daya katse Sa’adah ,kai Sis ba kyau yabon kai fa,kuma nifa ba komai tsakanin mu, OK toh, kings Seemah ta kar dake two zero, ga ciwon jiki ga rashin lawyernki, kuma su mummy zasu gane akwai Matsala if you can’t pretend, kina da amsar da zaki basu Iran suka tsareki da tambayoyi? no, manta da wannan tukunna ma, is mah Bro not a hot cake? kice min bai hadu ba zan gane tayi tambayar tana daga mata gira, da sauri babyn ta rufa idanu tana dariya, nifa Sis barci nakeyi cewar ta don ta rasa ta cewa, ashe dai muna da kyawun tunda an kasa karyatawa hmmmmm sis kenan, baby kenan, Sis farkon ganinki nayi zaton mate dina ce ke ,kuma na dauka ke zai aura, no, mijina yana Lag, kin San abokin sa Muhammad? nayi dan Jim sannan na girgiza mata kai ina murmushi, though akwai tazarar shekaru masu yawa tsakanina da Bro, ya kammala primary kafin a haifeni, kuma na gama school very early, kin gane? ta karsa furucinta tana daga gira ,yeah na gane ,yi barci zan mai daki gida gobe kinji? thanks na fadi ina karanto addu’ar barci…
Kin San dai ba yanda za’ayi ya ki binmu gidanku bayan he’s free today, tattaro nutsuwarki ki bude wata chapter daban ,abin daya faru ya wuce ,act normal kinji? in nice ke nunawa zanyi tamkar ban fahimci abin daya faru a daran ba, ita kuma Seemah barta kawai, iska na wahalar da mai kayan kara, zan iya kuwa? nayi tambayar ina zazaro idanu, yeah zakiyi fin haka ma,daidai lokacin ya nufomu cikin shigarsa na kullum (suit bakake), hannunsa daya cikin aljihu day an rike da car key, na dauke kaina ina gaskata hirar mu na daran jiya, THIS GUY IS HANDSOME ,anya ya San irin halitta da baiwar da Allah ya masa kuwa? amma baida lokacin komai sai na LAW, hmmm, wayaga agogo sarkin aiki, har ya bude suka shige bayan ya buden bangaran baya ban kula ba na Lula birnin tunani, karar wayata ce ta ankarar dani, daddy ne mai kiran, ba sai kunzo ba ni fa na taho muna hanya, OK miss u too, na katse layin ina murmushi, Lawyernah! na’am baby ya jikin? nifa na warke na fadi ina kallon hanya, sarkin kulaficin Mummy ko don ita ai kya ce kin warke, Sa’adah ke fadin mummy’s pet ce fa, daga nan shiru ya ratsa idan kika dauke karar ababen hawa dake gilmawa, kowa shiru yayi har muka isa gida babu mai ma dan uwansa magana, ni waya nake dannawa Sa’adah na nazarin ilmin Nafs dake hannun ta, shi kuma ya maida hankalin sa kan tukin, yayi parking muka shiga ciki, a harabar gidan muka tarar da Bilal zaune gefe guda, ganina ne ya sanyashi saurin mikewa yana fadin small madam cikin fara’a, how your body? Big Madam say you dey sick , a tsaitsaye muka gaisa ya min ya jiki na shige ciki, mummy na zaune a palo ta dan waiga ta kalleni gami da mikewa cike da murna na tafi na rungumeta, ta rungume Sa’adah tana ta godiya, ranar ita da daddy suka matsa dole mukayi breakfast gaba daya sannan suka tafi…
Rayuwarmu ta inganta tunda iyayena suka hade kansu bani da wannan matsalar ta saniyar ware matsalata yanzun ta nauyin da kirjina ke min sai kuma yawan tunani wanda mafi akasari na Bilal ne ko me dalili? Sannan gefe guda akwai shakuwa da fahimtar juna mai girma tsakanina da Lawyernah, duk da dai wasu lokutan nakan gaza kau da daran dinner daga raina, amma hakan bai hana ruwa gudu, a wannan halin aka soma daukaka karar a yita ta kare, shiryawa nakeyi sanda na samu wayarsa yana mai sanar dani cewa gashi nan a farfajiyar gidanmu, na dauki jakata mai kunshe da sakonsa yau zan mikasu ga wanda yafi kowa sanin muhimmancin su, yana nan a tsaye yakan burgeni bashi da hayaniya mai kamewa ne yau ma shigarsa cikin suit baki daga ganinsa zaki san kinga lauya agogo sarkin aiki, na karasa gefansa ina fadin yau asubanci zakayi? Yana murmushi ya soma fadin ya na iya? Muje mu zauna ki min bayanan yanda akayi kika dauki wadan nan, kai lauyana? Eh mana ba kya son in saci basira ne? Basira? Ni kam har wata aba ce da zan amfane ka? Ya dan kashen idanu yana fadin naji muje dai, muna nan zaune na bashi labarin yanda mukayi da hajiya a gidan ta, hankalin sa na kaina har na diga aya, Yayi ajiyar zuciya gami da cewa toh me zan baki? Baka mance ba kenan? Bani da mantuwa ni, kaji dadin ka? Abu daya nakeso in samu daga gareka
Ya dan numfasa gami da cewa ok zan iya baki kome kika nema, lokacin ka nake bukata ka bani in har zan samu saboda nasan bukatata idan ma mai yuwa ce to zan dauki abin da yafi komai muhimmanci a gurinka (lokaci), yarda da aminci shi ya sanyi neman wannan alfarmar daga gareka, taimaka mani zakayi don Allah ka bincika mani makarantar data san kanta a fannin law inda za’a horani, dalili? So nake in zama kai, a rainsa yake ayyana zaki zama ni idan kika aureni, sai ka gaya ma daddyna ya agaza in taka wannan matsayin, shi kenan? Eh na fadi ina kallonsa, in Shaa Allahu zan cika maki alkawarin ki, duk muka mike tsaye yana fadin bari in wuce to kar in makara ko? Na gode lauyana, ina nan tsaye naga fitarsa sannan na juya na koma cikin gidan inda na tarar da Bilal din zaune shi daya a jikin karfen AC ya zabga uban tagumi, duk sai naji na shiga damuwa sosai na tsaya a gurinsa ina tambayar matsalarsa, duk yanda na dage sai ya fadi tun ina wasa har na gaji fir yaki gaya mani, nima na wuce cikin fushi da sauri ya riko gefan gyalena yana fadin sorry na u curse am, na juya ina kallonsa da yanayin tuhuma, u dey make me waste my tym if i come wk i go just sit down, i no go home, na saki baki ina kallonsa, idan kinsan zamana bashi da amfani ba sai in tafi ba, na soma fadin ba haka bane kayi hakuri, yayi dan jim cikin nazari kaga mummy ce ta daukeka bani ba, bani da daman sallamanka
an san ka tafi ka barni ni kadai ina fita na fadi gami da wucewa abuna, ya zuba mani danu ni kam nayi cikin gidan ina sake sake a raina, mummyna a kitchen tana hada wa mijinta delicacies, ta daga murya tana mai cewa Muhsin din ya tafi kenan? Eh kawai na ce sannan na dauki remote ina kokarin kamo tashar da ake hasko film mai dadi, yaushe zaki yiwa Seemah ban gajiya? ta yi mani tambayar tana sauraron amsa, Oh mummy ita wannan Seemahar baki manta ta ne? Ah ah ha! Kun jini da neman dalili, in baki zuwa ai sai ki sanar dani tunda alfarma na nema ba dole zan maki ba, sorry nadaina amma….na dai yi shiru na kula Seemah ta samu fada a zuciyar uwarta idan nayi wasa sai tayi waje dani ta kwace nawa matsayin ta hada da nata ma, kin yi shiru? A shagua6e nake fadin idan na huta zanje, to uwata ni din ma fita zanyi sai ki kar6i mukullan a gurin mai gadi in zaku shigo ko? Na gyada kaina ina limshe idanu, hankalina nakan TV ina kallon Bahubali ta kammala girkinta, sashinta ta fito ba jimawa ta dawo gareni hannunta dauke da ledoji tana fadin gasunan ki bata daidai sanda ta diresu a gabana….
Na kintsa tsaf zuciyata cike da tunanin yanda zata kaya dani da mutuniyar tawa ‘yar daru, ina jin haushin abin data aikata mani amma hakan bai sauya yanda nake jinta a raina ba, na samu Bilal muka wuce gurinta, muna tafe muna sauraron tashan radion da ya kamo mana don kau da shirun da yayi yawa, a haka muka isa gidan zai je ya dawo ya maidani ya fadi sannan ya juya, yayin da na sanya kai cikin gidan, daidai lokacin mota tayi horn a bayana na matsa gefe guda ta karasa shigowa ciki, ‘yar izza ce ta shigo ba tare da bata lokaci ba ta sauko ta sameni ina tafe a nutse, keee! Kiran raini tayi mani wannan nema ya sanyani dan dakatawa bakinta dauke da gum tana taunawa irin na rashin mutunci,wai ke me yasa baki da zuciyane? Ina da labarin kin zama kadangaruwan bakin tulu, munafukar lauyoyi ko? Gaya min mana, na maida hankalina gareta yayin dana kafeta da idanu, hala kanki kika bashi don jan hankalin sa? ji nayi tamkar ta watsa mani garwashi, ke karya dakata kiji! Idan banyi kima a idanun jama’a ba kema kinyi asara don abin da yayini shi yayiki, Muhsin ba bawan mace bane get dat in 2 ur empty brain ke ake taimakawa kina cikin duhu, idan aka kare mana kallo ke ce ma mai ruwan karuwan, na ja tsaki mtssssss gami dayin gaba abuna da sauri ta rufa min baya zuciyar nan cike da damuwa tamkar zata kifa.
Fuskar sa babu walwala, a haka ya harbata kwalta muka dau hanya, na kula da yanayin bilal bai kaunar ganinmu tare da Muhsin sai inga yana wani shan mur, muna tafe yana fadin kin yi kyau yau nayi murmushi kawai….
Tana katse wayar Hameedah tayiwa yaronta waya, Gosha jeka kawai ba matsala yanzun ya fito daga gidan yana hanyar Shoprite tare da wata buduruwa zaka ganta sak Seemah, uhun hajiya an gama, kayi aikin ka da kyau fa? Kuma ka kiyaye kasan babban guri zasu ko? Toh naji just dnt let them get you don gayen shegyan kwaro ne yasan kan aikinsa, tana murna an kusan kau dashi daga doron kasa ta kira hajiya Binta tana mai shaida mata abin da ake ciki sai shewa mata biyun sukeyi tamkar an masu wahayi da aljannah, gara hakan cewar Ni’iman in kuwa ba haka ba zai 6allo mana ruwa babu shiri…
Madam Zarah mace mai ji da kanta amma lamuran sun sanyata fita cikin tsarin rayuwarta, damuwa da zulumin shari’ar sun sanyata gaba, duk yanda taso samun gudan jininta abin ya ci tura ,likitoci da dama sun ce mahaifar ta bazata iya daukan ciki ba, zaune take kan stool gurin shan iska a gefan lanbun gidanta tana ayyana abubuwa da dama a rainta Nataniel ban so ka mutu ka barni ba, ta fashe da kuka zuciyata nai mata radadi, babynka na cikin wani hali ta fadi a sanyaye tamkar mai rada, dama ita rayuwar haka take juyi juyi, ta kalli mansion dinta mai dauke da kawa na zamani tana ayyana wa dana mutu ba mai gado a banza kenan…
Na dan zazaga bangarori daban daban na tsinci abubuwan da nake so, ban wani jima ba na fito daga cikin gurin na iske shi a mota ina mai fadin muje to kar mummy taji shiru zan rakata asibiti ne, ya jinjina kai muka bar gurin, na janyo wayata gami da karawa a kunne ina fadin lauyana ka isa gurin? To nima dai gamu a hanyar gida na siyo maka eh, ina kallon bilal na hararata na basar, kar ka damu In Shaa Allahu na fadi ina murmushi …..ban kai ga karasa maganar ba komai nawa ya tsaya cak daidai sanda naji harbin bindiga tamkar daga sama, Inalillahi na tsinci bakina na furtawa a kidime, baby lafiya? Muhsin ka yafemin ni nasan mutuwace, harbi har jeri uku a kirjin bilal wannan ne ya sanyashi sakin sitiyarin na tallaboshi ina kwala ihu motar tayi ciki damu da duk wace ta nufomu,tuni na saki wayar ina fadin sai a lahira, na rika jijigashi ina kiran sunansa amma shiru, tamkar ba shine kyakyawan saurayin nan ba dana sani a baya, na kece da kuka daidai sanda motar ta karasa inda zata tsaya, sai da tayi tumbling sannan ta dakata ni kam daga wannan lokacin ban kuma sanin abin da ke faruwa ba, abin da nasani dai ba karamar 6arna mukayi wa jama’a ba…
Haka ta bar shi da wayar a hannu yana ta 6a6atu cikin tashin hankali to amma ya ya iya? Dolensa ya mike jin tace suna hanyar gida daga shopright ne ya sanyashi daukan mota don zuwa garesu, dawowarsa kenan amma bai ga ta zama ba, hanyar ya bi cikin sauri tamkar zai tashi sama ji yake ma baya wani sauri sam, a haka ya karasa gurin inda ya iske dandazon jama’a sun kewaye abin da bai san ko menene ba, haka nan kurin yaji gaban shi na faduwa, ya soma jero adduo’i iri iri, da kyar ya zare makuli daga jikin motar gami da tattaro nutsuwarsa yana fatan Allah yasa ba ita bace aka wa wannan runfar, a nutse ya sauka sannan ya kutsa cikin jama’a yana waware idanu don ganin ta inda abin da yake nema yake, lokacin an soma daukan mutane da anbulance don da yawansu ma basu san inda kansu yake ba, bilal kam ba kanta, ya sanya aka taimaka masa suka sanya shi da Hameedah a motarsa, bilal din ne ma abin tausayi ita kam sarauniyar ko kwarzane bata ji ba amma bata cikin hayyacinta sam, dadyn yayiwa waya kai tsaye don su hadu a can asibitin yanda abin zai zo mada da sauki ,ba jimawa ya karasa asibiti inda aka shiga tuhumar sa kan abinda bashi da hannu ciki, tamkar yayi kuka babu mai fidda shi in har sai an taimaka masa gurin basu agajin gagawa to dole sai ya taho da dan sanda, itace dai asibitin…
… (UMMU FARHANAH)…
15…
Har ya sare yana kokarin fito da Hameedhar ya sa a mota in yaso sai a wuce private kawai sai ga daddy da dan sanda sun bayyana ba tare da 6ata lokaci ba aka shiga basu kulawa na gaggawa, hameedah kam ance ta bugu sosai ta yanda duk jikinta zai mata tsami yayin da bilal ke bukatar aiki don sai an fitar masa da bullet din da suke jikinsa, cikin dankankanin lokaci likitocin suka dukufa wannan dalilin ne ya sanya daddy da muhsin din suka shiga zarya a kofan dakin kowa cikin damuwa, mummy kam bata da labari sam…
Yaya dai? Ta saki dariyar keta tana shewa ni nasan Gosha karshene, ka kyauta bari in dauko balance din naka, ta dauko wrapper din dubu daya ta cila masa, yana fito ya ca6e yayin da yake fara’a, daidai ficewar sa ta kira hajiya Binta tana tsegunta mata, Seemah dake la6e tana ji tsaki taja daga shi har hameedahan basu da amfani, matsiyata kawai ta fadi tana yamutsa fuska, a tsarinta talaka bashi da amfani sam, me za’ayi da matsiyaci? Kai ko aure zanyi sai dai wanda ya tada kai da arziki ko ta tsiya in mori shege, sai gidan hutu wallahi ta ayyana a ranta tana kallon kanta a mirror, dama ba kowani tsami nake kulawa ba, har yau banga Mr Right dina ba, I want to marry a man that will worship me, tayi murmushi tana zaban kayan sawa son zuwa birthday party din Jalila , wata muguwar gown ta dauko iya gwiwa duk yasha stones ta ko ina ,ga nauyi amma saman a bude yake, hannun shimi gareshi ta ajiye kan gado tana kintsa kanta, that Muhsin would have been a choice amma bai da Naira ,he’s dam cute and breath taking ta furta, ko ina sonshi bazan ji haushin mutuwarsa ba because that bitch (Hameedah) need it, I hope this will be your end ,ta mike gami da zura short gown din da dad ya siyo mata daga Italy, da takalmi da purse mai tsinin kusa komai silver mai kyan gaske, kan ba dankwali sai wata hula ubansu data dora mai dauri tamkar canopy, ta ratso palon uwar tana kan phone gulma yayi dadi, baba Sule dake bakin gata ke fadin hajiya kiji tsoron Allah kije ki sauya wannan shiga, a ranta ta ayyana nifa ba a kanka nake ba, na gaji da wannan shishigin ,yau zan maganin Allah yace Annabi yace, dama a masallaci uwarka ta haifeka, a zahiri tayi murmushi gami da cewa na gode mallam, har zata koma ciki ta kuma dawowa tana fadin dama maman Suhaila tazo dazun (matarsa), tace mai gidanku yace yagji da zaman hayanku kusan shekara 1 babu biya, karfe 4 yana nan zuwa da dansanda a kama mashi kai, wallahi gara ma ka tattara ka zille, Idan kuran ta lafa ka dawo, da azamarsa ya mike jiki na kyarma yake zazaro idanu, nagode hajiya, bani da abin basu Idan suka tsareni, saida ta tabbatar ya fara hada komatsansa sannan ta shige cikin Palo da gudu tana ihu, ai hajiya bata San sanda ta saki wayar tana tambayar lafiya ba, ta soma birgima tana kuka, mum shine ya danneni yana taba min nan, ta karasa tana nuna kirjinta , kutumar uba cewar hajiyar, hallarcin dana wa matarsa da safen nan data kawo koken kudin haya na watanni 10 na bayar irin sakayar da zai min kenen, sorry princess tashi ta fadi tana dagata cikin tsigar rarrashi, muje in ga urban daya tsaya masa, suna isa farfajiyar gidan ta hango sa ya sabi jakarsa ta buhu yana Jan keke, ta soma tafa hannaye yana salalami, dan buhun uba toh wallahi kar ka dawo min gida, ta fadi cikin daga murya, da damuwa yake fadin hajiya ayi hakuri so nake sai komai ya nutsa sai in dawo, a’a wallahi zamanka nan gidan ya kare, Idan ka dawo hukumace zata raba mu na gayamaka, jeki gyara fuskarki kizo ki tafi ta furta tana shafa mata kai, jibeshi kaman mutumin arziki, don’t worry ban kara daukar mai aiki sai mutumun kirki, ta shige sashinta tana jin farin ciki mara misaltuwa, l luv riches, wannan kudurin nema ya sanyata mike kafafu tana ayyana yanda zata auri mai kudi bana wasa ba, kai ko ya yi aure sai nayi sanadin mutuwar auren, idan ma ana shirin yi ne sai dai a fasa, ta dan yi murmushi gami da mikewa don kammalawa ta fice..
Sanda aka basu umarnin shiga su duba marar lafiyar, da sauri suka shige daidai sanda likitan ya wuce office dinsa, Muhsin ya zauna a gefan gadonta bayan ya duba bilal din gami da kafeta da idanu, daddy kam tsayawa yayi cak mamaki ta kashesi a tsaye, me BAM keyi a nan? Ko da yake zai bi lamuran a sannu idan ya warke su sasanta kansu, kar dai shine bilal din da mummy and hameedah ke yawan fadi? Ya dan dafe kansa sosai yake taryo inda suke haduwa, jarumi a fagyan aikinsa (custom), mai kwazo da basira gashi nan shame shame tamkar bazai kuma motsawa ba, baya manta taimakon sa gareshi a MATSAYINSA na dan kasuwa a bodar nigeria to cameroon inda akayi masa shifting daga baya ya koma wani gurin karshen haduwar su kenan, motsin da hameedahar tayi ne ya katse masa tunani ko kafin ya karasa tuni abin kunya ya faru, Muhsin din dake kusa ta kai wa cafka tana girgiza shi, sama sama nake jin kuwa a kunnuwa na tamkar yanzun abin ke faruwa, idanuna a lumshe suke amma ina iya taryo accident dinan tsaf na rintse idanun gam da sauri na mike zaune sannan jin motsi a kusa danine ya sanyani saurin rungume na gefen nawa, na shiga firgici, kwakwalwata ta dau rudu yayin da dukanin jikina ke amsawa tsabar buguwa, kuka nake sosai ina surutai cikin barci barci gashi nan dai a farke nake amma ni kaina ban san MATSAYIN da nake ba, na shiga uku ni naga mutuwa, nayi ta yi tamkar wace junu suka shigeta sabuwar kamu, ana iya kwatantani da ‘yar giya, ya tsaya sororo don bai san abin yi ba, shi kansa daddy daya karaso garesu kallo ya tsaya yi, ta dad tamke hannayenta a jikinsa tamau yanda ba zai iya fincikewa ba, mummy naga lahira sosai bilal na sanya kuka, da sauri daddy ya tafi kiran doctor, har sanda suka shigo tana nan makale dashi, its normal cewarsa firgicine ya shigeta wannan nema ya sanya aka zurkuda mani alluran barci, nayi luf a jikinsa ina sharar barci, saida yayi nauyi sannan aka samu daman gyarani na koma kan gadon sosai.
Ni kam na dau tsawon kwanaki uku ina barci wanda ya taimaka gurin watsakewata saidai dan abin da ba’a rasa ba, tafiya kam likita yace sai na rika zagawa kafafuna zasu saki, cikin wannan yanayin bilal yake babu ranar mikewarsa, yana da rai amma har zuwa rana irin ta yau bazai ce ga wanda ke kansa ba, daddy da Muhsin ke zarya kanmu, zuwan mummy uku sai kuka da yake mai tausayi ce wannan ya sanya daddy ya bata red card game da asibitin, sai dai tayi girki daddy ya dauko, shi da muhsin ke shiftin din kwana, lokuta da dama kannansa kan zo tayani hira musamman Sa’adah a nan wata kalar shakuwa ta shiga tsakaninmu dika, hakan ta haifar da wani yanayi a tsakanin mu har ya kaishi ga sakin jiki dani sosai miskilin namiji amma ya sauya takunsa game dani, koma me hakan ke nufi ni kam na san cewa shi mai halin girma ne kwarai…
Na mike da sanu ina fadin wash a dole sai nayi wa su Husnah rakiya, Sa’adah dauke da kwandon abincin da suka kawo mani yayin da auta husnah ta dau tarkacan da suka wuni dashi, Muhsin ne ya turo mani karfen da nake dan dafawa don sabawa da taku in samu lafiyar kafafuna, yau din ma shine a gefena muna tafe yana dan biye mani don kar in fadi, a haka muka karasa bakin motarsu ina bada sakon su gaida mama, akwai labari cewan Sa’adah amma sai kin warke, na jinjina mata kai sannan ya taimaka mani muka koma ciki, a haka na warke sarai amma sai naji na kasa komawa gida saboda bilal dake kwance ba ranar warkewansa, hakan kan karya mani zuciya musammam idan na kalli yanda ya koma duk sai inji rayuwata ta kuntata, har nake ganin cewa likitocin basu san kan aikin su ba tunda gashi sun gaza bashi tallafin gagawa da zata sanyashi warkewa, Yau satina 2 normal nake jina na mike garas ina jin karfi tamkar doki har ana kokarin sallamata, naga farin ciki a gurin muhsin da na rasa dalilinsa ,ya fita tare da daddy ina zaton office din likita suka nufa, ni kam na karasa gaban gadon bilal idanuna har sun kawo kwallah, sai yaushe zaka tashi ne? Na fadi cikin sarkewar murya, ina kokarin durkusawa don kafafuna sun gaza rikeni nayi rauni sosai, har ban san sanda suka shigo ba daddy naji yana fadin Allah zai duba lamuransa kiyita yi masa addu’a, na ja jiki na bar gurin ina harhada hanya, muhsin ya cillo mani tissue na goge fuskata hannunsa sa6e da jakar aikinsa yana fadin oya muje yau zanyi resumin aiki, nayi wa daddy sallama muka bar gurin,a motar kam hira muke cikin hikima da basira yake cusa mani kalamansa masu kama da bugun ciki, kai tsaye dai bazance ga manufarsu ba amma shi yasan me yake son fahimta ,na ga dai kin warke ya karfin jikin? Alhmdlh, yayi kyau cewarsa amma naga kin sauya yanayi ko dai kwanciyar bata isheki bane? Uhm uhm ban gajiya da zaman dakin ,kin kyauta ya fadi yana kokarin shan kwana ,ko dai mummy ta tattarokine ki koma can da zama? Haba dai shi din ma na wani lokaci ne in kuwa ba haka ba wakeson zaman jinya? Ni kam ina so, hmmm why? nayi tambayar ina zaro idanu, Saboda nishadi yake sawa amma Allah ya riga ya yanke mani tunda marar lafiyar ta mike ,na gyada kaina ina kallonsa, akwai aiki a gabanmu fa, na me? Recorder din nan na dada sauraronsa na fahimci aikin su Ni’ima da binta ne ni suka so su hallaka don kar labarin miyagun aikinsu ya fito a ji, nayi dan jim ina tuna sanda naji tana fadin Gosha yarona is smart kawai a kawar dashi, sannan na jinjina kai ina gaskatawa, wannan dalilin ya sanya aka dad mayar da karan mai tsawo, ba karshen sa kenan ba sai an kara tattaro bayanai don fallasa su, hakane kuma na fadi cikin alamu na nuna ina tare dashi, lauyana wai bilal bashi da kowa ne? Shi zaki tambaya ai, naga tunda ya shiga wannan halin ba wanda yazo daga 6angaran sa shi yasa na shiga damuwa, kiris ya rage ya saki sitiyarin saboda yanda ya kafeni da idanu, nayi kara gami da cewa accident wanda ya taimaka gurin karkato da hankalin sa ga tukin, yi hakuri please kar ka karasa ni, na bude da sauri na sauka, ni kam daga yau na daina hawa mota haka kawai, last 2 weeks naga ajali a 6agas mutuwar mutane 6 kan idanuna nice dai lokacina bai yi ba, bilal da sauran sa amma ba kanta, ya sauka ya iskeni har na soma takawa, baby sorry zo in maidaki mana, naki din na fadi ina noke kafada ta, sannan na saki hawayen da suka cika mani idanu, muje to in saki a mota ki koma gida ko? Nayi dan jim sannan na kara da cewa ni fa motar ce bana so, ok na fahimta, muje to tunda babu nisa daga nan in dan taka maki, a haka kam muka wuce har cikin gida sannan ya tafi… hmmm kwalkwalwata akwai tarin rikici cikinsa ga damuwa da jimamin makomar bilal.
A bakin mummy na tsinci labarin mutuwar Alhji miji ga hajiya Binta shima a hatsarin da ita da aminiyarata suka jaza mana tashi ta sameshi, murna kamar in yi yaya? Mummy da yake an barta a duhu sai ta shiga yi mani fada duka mai rai mamaci ne, idan ma murnar ya mutu nake nima tawa tana tafe, na basar don kar ta zargi wani abu, kar wani ya gani yayi zaton da sa hannun mu ciki…
Na gaza zaman gidan sai zaryan zuwa asibiti in ga lafiyarsa dana dora wa kaina damuwa na ba gayra babu dalil, har na gama zaman asibiti gashi shi kansa bilal ya samu sauki babu laifi ba idanun Seemah, shin ya zaman mu a karkashin inuwa daya zai kasance?…
Takun karshe na sanyawa karar mu ta yau don nasan ko ta halin kaka yau sirrin 6oye zai bayyana, an yi walkiya kuma mun gani, tsawon wannan lokacin basu da labarin Muhsin na nan tunda shima tun faruwar lamarin ya rage zirga zirga, wannan ya haifar masu da kwarin gwiwar zuwa kotu cikin shigar girma da takun takama, ko ba komai dole shari’ar ta watse tunda su hameedahar basu da madafa cewar haji Ni’ima, hakane cewar haj Binta da mutuwar mijinta bai sanyata sauya taku ba, su 2 suka shigo ba jimawa sai ga lemosine din data dauko madam Zarah, kan idanuna ta sauko yau a nutse sosai duk sai naji tausayinta ya cikani, tana da gaskiyarta amma su haji Ni’ima sun sanyata gaba, daga can kusoshin govt ne zaune sun kame guri daya suna jiran tsanmani, kara dai ina fatan karshensa kenan, ni kam ‘yar ganin kwakwaf ina nan tsaye daga jikin kofar da zata sadaki da cikin dakin taron, Kaulah ce shigowar karshe tana neman tawagarta, daidai lokacin dana juya zan shiga ciki lauyana ya karaso yana gyara necktie, baby manya cewarsa ,nayi murmushi kawai ina girgiza kai tare muka shige ciki ya wuce na koma gefan mummyna, shari’a ta soma gudana cikin hikimar masu aikinsu, na natsu ina son inga Seemah taga makomar ta kwarai da gaske, nifa hukuncin azaluman da suka raba ‘ya da uwa bai daman ba kamar yanda na matsu in ga family REUNION dinmu, Kaulah ta karasa inda wanda ake tuhuma ke tsayawa yayin da Muhsin ke fadin ko zaki gaya wa kotu yanda akayi Rahma Abdullah Buba ta haifi nata babyn ? Ta zaro idanu cike da kidima ta kara da cewa ni na gyara babies din su dai, good, ya kikayi da su? Objection my lord cewar barister bala sumaila mai kare 6angaran su, amma bai samu daman magana ba, go on Kaulah sai akayi yaya? Ni fa…..ni to….hmmm sis Jane ce ta fara kar6an haihuwar ta aka kirata a emergency unit shine ta sakar mani, me ta haifa? Dan mutum mana, yayi kyau ya fadi yana zaro file daga karkashin takardun hannunsa, ga file din da Jane din ta cike nan na lalubo da tsiya na samoshi,
ya mika wa alkali mai sauraron shari’a yayin da yake fadin ya mai girma ka duba wannan lamarin da kyau zaka fahimci shirin da wa’yan nan suka rikayi a baya zuwa yau, ya fadi yana nuna su(kaulah ,da haj Ni’ima da haj Binta), dakin ya dau hayaniya kuma ya dan lafa, ya kikayi da madam Zarah a baya? Ta dan yamutsa fuska gami da cewa ya ko zanyi da ita? Iyaka an bata abinda ta cancanta, ya gyada kai yana murmushi, kin kyauta, bala sumaila ya nemi mummy ta amsa tambayoyin sa, shin me ya hanaki fadin alakarki da su tun farkon shari’ar? Saboda a ganina bani da dangartaka da su wannan ba muhalina bane, mai girma ya kamata ka duba lamuranta da kunnan basira tace ba muhalinta bane shin me take nema kuma, ta sauka ta koma matsayinta ni kam na kosa a gama, karshen tika tika tik…
Hajiya Ni’ima shin ko zaki sanar da kotu inda kika samo ‘ya’yan ki? Objection my lord! Barister ina ake samun ‘ya ‘ya dama? Yayi masa banza cike da kulewa yana sauraronta, ina da miji shin naga ai ba daga sama suke fadowa ba ko? I see, ya ce yana shafa kwantaciyar sumar sa da tasha gyara, na mijinkine kenan? Ta gyada kai kawai alaman hakan take nufi, bayan bashi da kwayoyin haihuwa wa yayi cikin da kika bashi? Wannan ba abin da shafe ka bane……Objection my lord, barrister ka daina 6atawa client dina suna, hmmm ci gaba, me ya samo asalin haduwarku da kawancanku da ta rikede ta shi daya ta zama ta aminai tsakaninki da hajiya Binta? A asibiti dakin haihuwa muka hadu, uhum, kenan muna iya cewa a gurin haihuwa kawancen ta kullu? Eh kusan hakane, ya jinjina kai alaman gamsuwa, mai girma ka bani dama kotu ta saurari wannan recordern, ga hotuna kuma, ya fadi yayin da yake mikawa alkali mai sauraron kara, alkalin ya soma karantowa bayan ya tsagaita da rubuce rubucensa, file dai rubutun da sahannun na Jane ne wace a yanzun tayi ritaya, identical twins ta rubuta baby girls, on friday morning by 12:30am, sunan mai haihuwar Rahma Basiru mata ga Abdullahi Buba ,Sauran kuma rubutun Kaulah ne, hotuna kuma tabbas ba karya ga su nan a zahiri kamannin ne a jikin hoton kowa ya natsu don jin ya zata kaya, aka sanyata a loud speaker, maganar na fitowa tiryan tiryan hajiya binta ta mike zata fice masu tsaro suka cafketa( itace ta kawo shawara Satan babies a asibiti gurin haihuwa, ita ta nemo wa haj Ni’ima Kaulah, sannan da aikin yayi kyau ta nemi a sato mata daya itama), hajiya Ni’ima da fitsarin zaune, kaulah tayi wuri wuri da idanu duk ido ya raina fata, mummy kam sanda zancan yazo karshe sumewa tayi daddy ya talla6o ta yana girgizawa, da sauri na dauko swan a mota na masa yana tsiyaya mata, sanda ta farfado ta rungumoni tsam tana sumbatan goshina, shari’a taci gaba daga inda ta tsaya, ko zakice mana bakisan Gosha ba? Hajiya Bintan ta zaro idanu tana karkada kai yayin da bakin barister bala sumaila ya mutu sai dai idanu, mai girma bari in kawo shaidana cewar lawyerna, ya kallo cikin audience yana masa alaman kira, sai ga mai gadin gidanta muhsin ya shigo dashi witness box, ya sunan malamin? Adamu Zakariyya, ko zaka gawa kotu aikinka? nine mai gadin haj Ni’ima, tun farkon aurenta muke tare, yayi kyau cewar muhsin, kai ba bako bane, shin ko zaka iya sanar da kotu yanda akayi ta samu Rihab (autarta), eh toh, tana da shekaru 2 hajiya ta sanya yaronta Gosha ya sato ta a kofar gidansu tana wasa har an nema an hakura, waye gosha kuma? Yaron ta ne wanda take aike idan bukatarta ta taso, ya jinjina kai yana fadin a ina za’a samo shi? wannan ita ta sani don ni kam ganin sa kawai nakeyi ban san daga inda yake fitowa ba amma abin da na sani shine babban dan daba ne bana wasa ba, ina tsammanin a nan Abuja yake rayuwar sa…
Mallam Adamu amanar gidan da na baka kenan zakazo bainar jama’a kana tozartani? Ta fashe da kuka na gode kana iya tafiya, cewar lawyerna, ya fice wanda kai tsaye ake haska wannan shari’ar a gidan talabijin na kasa don nuna wa duniya kudurin wadan nan mata, Kaulah aka kuma nema don rufe zancen, ya akayi da babyn wancan matar? Madam zarah take nufi, tayi Dan jim, jikinta tsamo tsamo duk ta jike da gumi tamkar 6erar daya fada a ruwa, tana raba idanu tamkar shege a rabon gado, ta kalli madam Zarah da ta matsu taji abin da zata ce sannan a raunane ta soma fadin ba yin kaina bane su suka tirsasani, ina goyon ma’aruf 3rd born dina lamuran suka fara gudana lokacin mijina yana raye, har asibiti hajiya binta ta sameni da batun zan rika binta gida awo wanda a lokacin ban fahimci cewan bata da komai jikinta ba, nema dai take ruwa a jallo, zumudin samun kudi daga gareta ne ya rufe mani idanu don a can baya ba wani aikin da zai rikemu mijina kedashi ba, kamar yanda muka shirya ranar wata talata da safe na ziyarceta don cika alkawari na, a lokacin take shaida mani cewa ita ba don ciki ta kirani ba sai don neman baby, kuma aminiyarta Ni’ima zamu taimaka wa, batun ya bani mamaki sam ban fahimta ba, ta labarta mani plan din da ya razana ni,ta ce hakan nake nufi ki saurareni, mijina ta bashi da kwayoyin haihuwa kuma dole ta samu yara gudun kar ya mutu ta yi 2 zero ba yara babu gado, danginsa kafafu ne basu barinta ta wala bare kuma idan babu shi ai dama don shi suke raga mata, hajiya ya kike son inyi? Gud yanzun kike zance, ke nurse ce na samu labarin a fannin haihuwa kike ko? nace eh cikin zakuwa, haka nakeso dama, musanyan yara zakiyi ta yanda zata samu rabonta, yay kenan? Ina nufin zata yi cikin karya idan an samu maijegon da zaki saci diyar ta sai ki mani waya in shirya ta muzo haihuwar karya ,idan plan din yayi kyau nima zan hau network, mu hade dasu yafi saukin sata ai, ba sani za’a yi ba hanklin mu kwance kin gani, kai hajiya ban iyawa dan mutum fa? Ah to sai me? Ai ba dan shila nace zanyi da shi ba rikewa zanyi in ririta tamkar gudan jinina
Idan aka kamani fa? Bai yuwa mune fa govt, ko kin manta mijina na da matsayi a can? Ni’ima ma fa babban dan siyasa take aure, har na tafi tausar zuciyata takeyi in amince da kudurin ta inyi tunani a kai, na koma gida bukatu suka matsoni, ga miji ba lafiya, ga yara da dawainiyar su, ga ‘yan uwana kowa da nashi da mu suka dogara, duk da albashina na da tsoka amma bai isa sam, wannan ne ya sanyani komawa gareta muka tsara yanda abu zai yuwu…
Ranar juma’a bayan watanni 7 kenan da wannan batun na samu cikan burina kudade zasu iso hannuna inyi yanda nakeso dasu, na tsinci kaina a dakin haihuwa dumudumu, sista Jane ta saki aikinta ta wuce emergency unit, wannan ne ya bani damar kiran hajiya bintar, Ni’ima tazo ranga ranga da tirtsetsen cikin ta tamkar gaske, aka garota a gadon majinyata, na kar6eta lokacin nayi ma Rahma allurar barci mai nauyi, zarah kuma cs akayi mata bata farfado ba, ta cire cikin na dauki babyn Rahma guda daya na nada a dankwalin hajiya binta na bata, sai ga shigowar hajiya binta itama bukatar, na dau dayar twin din na nada na baiwa hajiya Binta a nata dankwalin, na dauki gawar diyar zarah da tazo babu rai na nada a dankwalin Rahman na bar mata don naga yarinya ce a lokacin tana da shekaru 16 duniya, a haka muka tashi na kar6i kudadena masu tsoka wadanda suka jefani cikin rudani a yau, Rahma muka fara sallama taci kuka ta gode wa Allah, tafiyar ta da amincewar babyn nata ya mutu ya bamu damar karfafa zukatan mu, hajiya binta da ni’ima suka wuce daga ni sai zarah data farka ta ci kwalata dole sai taga gawar ‘yarta don cikckiyar yar bariki ce, idon a bude yake….
[5/16, 3:10 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
16…
Shakar daya hanani numfashi Zarah tayi mani,da kyar doctor ya kwaceni daga gareta,aka hadu ana rarrashinta, data samu sauki aka sallameta kawai sai naji sammaci daga kotu, har gidana akaje aka kai mani takardar kara, wannan ya sanyani neman su hajiya Binta da Ni’ima na sanar masu, abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, da kanta take zuwa tana zargin babyn Bintan diyartace, suka soma rigimar da taki yankewa, a haka kafin zagayowar ranar tsayawa a kotun suka hadamani guzuri da kudin rikewa na bar kasar gaba daya, lokacin na gaba takabar mijina, a can din ma muna waya suna sanar dani irin rigimar da akeyi da Zarah taki hakura bayan ance mata danta na kasa, a can rayuwa ta sauya komai nawa ya kare daidai lokacin da 1st born dina ya mutu dole ta sanyani shirin dawowa gida(Nigeria)idan baka san inda zaka ba ai kasan daga inda ka fito, garin shigowane aka kamani a border,a lokacin ma sun cizi yatsa game da bayyanar da nayi, shin me yasa zan dawo bayan sun dau nauyina? Ya na iya? Ta fashe da kuka ni kam kallonta kawai nakeyi abin alajabi a gabana, na dafa kafadar mummy ina kakane ido, menene? Ni ki goyani barci nakeji, ta dan yi murmushi tana shafa mani kai har gobe kuruciya bazata barki ba, sai rigimar tsiya, idan na goyaki inyi yaya da babyn cikina? Kooooooot cewar alkali yana buga gudumarsa, an tashi kara sai sati na sama lokacin an samo Gosha, daddyne ya riko hannuna muka fito yanai mata batun Seemah, na yi tamkar ban ji su ba, a wayance na zare kaina na nufi mota ina jiran isowarsu don su a hankali suke takunsu tamkar ba za su iso ba, na shiga dadana wayata a zuciyata ina jinjina ma Muhsin bisa namijin kokarinsa na fito da gaskiyar lamari ba wasa ba, gefe daya kuma jimamin rashin zuwana asibiti duba Bilal a yau nake, ko ya jikinsa? Mun dau hanya har lokacin hirar suke basu ko sakoni cikin zancensu sam, a haka muka isa gidan…
Cikin tashin hankali suka fito suna jifan juna da maganganu masu zafi,banda Batman basira wake fifita kawance kan ‘yan uwantaka? ke da kika rasa mijinki a hanyar neman duniya, naji ai gara ni rasa mijin nawa nayi da sauki am sure he is in his grave, ke fa? wani irin asiri ne baki bankada wa mijinki ba? Har kurace zatace da Kare maye? Uban ways ya koya mani, daga taimako sai cibi ya zama kari? Toh gaya wa duniya halinki, boka dai yace ranar da asiri ya Tonu auranki ya kara, said a koma kauye a kwana kuma a gadon kara, Wannan shi zai zama sanadin mutuwar auranki jahila, ke akwai wanda ya kaiki jahilci? Ke da kikayi shirka kika dora ni kan hanya? Ubanki dan banga matsiyacin kauye, ji kike tassssss, ta kai mata mari da duka a kirji, ni kika daka? Baki daki banza ba wallahi, dambe ya so kacamewa jama’a suka raba su, kowa ya kama gabansa kaulah kam hankalinta yayi masifar tashi don da kyar ta koma gida… Hajiya Binta tamkar zuciyarta zata yi bumb haka ta rikaji a haka ta isa gidan, shigarta ke da wuya ta tarar da mai gidan nata a bakin kofa yana jiran shigowarta, ta marairaice tana fadin sweetyna! Ya daga mata hannu yana fadin ke da wa? Sweety my foot, na sakeki saki uku, ya furta ba tare da ya tsaya jin abin da zatace ba, waje yayi yana kokarin tada motarsa ta rufa masa baya, amma kafin ta karasa tuni har ya tada ya bar ta da hayakin inji, ta dafe kai a gurin tana rusa kuka mai tsima rai a haka Seemah ta sameta, hannayenta 2 a kugunta take fadin bazan zauna ba nima gaban iyayenan zan koma, ba kunya bale kara ta tsallaketa, Seeeeeeemah! Ta kwala mata kira wanda ya sanyata dakatawa, ki sani,ba’a canza wa tuwo suna,ta girgiza kafada alama na halin ko in kula sannan ta shige cikin gidan.
Ta dade zaune a gurin babu mai rarrashinta wannan ne ya sanyata mikewa zuciyarta cike da tunanin yanda zata kaya, tun da ta aureshi ta watsar da zumunci ba wanda ta ta6a tallafa ma balle ya kai ga kai masu ziyara, anya kuwa zama ta iya gane hanyar kauyensu? Ta fesar da numfashi mai zafi tana goge hawayen fuskarta yayin da zuciyarta ke kuna, a dayan 6angaren Seemah ce raku6e a jikin hamshakin gadon bedroom dinta tana tunanin makomarta, ni ban damu cewa bashi ya haifeni ba,zan iya zama da shi in har zai amince ya dauki nauyina zuwa Oxford Uni inda na ci burin yin ilimina, ta watsar da pilalikan kan gadon cikin karaji tana huci,stupid kawai Allah ya isa idan na bar wannan gidan bazan yafe maki ba Hameedah kece sila, don nace ke shegiyace shine zaki tozartani? So kike komai muyi shearin a rayuwa? Namiji daya da nake burin mallaka saboda iliminsa ga tsara ado (muhsin)na san idan na sameshi nayi zarra har abada, ki kayi masa kane kane a zuciya, dan ubanki mummyn namu ma taki ce abu kadan mummyna mummyna, school dole ta sanyani zama in gama ta saboda in gyara maki zama shegiyar yarinya amma hakana bai cima ruwa ba, sai yaushe zaki bar rayuwatane? Ta bige kwalaban designer turarrikanta suka tarwatse sannan ta yi zaman dirshan tana rasgar kuka sosai, yanzun kuma a naki toshashiyar basirar karkashin inuwa daya zamu zauna ko? Never! Wallahi in ko na amince na zauna sai ki yaba wa aya zakinta, ni hameedah kika ruguza wa shiri ko? Tayi kwafa sannan ta mike da zamarta ta dauko wayarta tana neman layin gogagun kawayen da suka hadu a club sati biyun da suka wuce, ji take tamkar ta kashe kanta, hada dangartaka da hameedah ai mugun ci baya ne… Ya dan gyara zamansa nikam na tura masa pilo a baya don ya ji dadin jingina ina masa sannu sannan na hada masa tea, zuwa yanzun plasta ce kawai da ba’a gama cirewa ba, amma jiki kam Alhmdlh,yana ta kallona na hada masa tea din mai kauri da farfesun kayan ciki a kan tray na jerasu na mika masa, na kula yana jin dadin hakan, daddy ne ya shigo yana amsa waya da sauri na mike na kar6i jakar hannunsa inai masa barka da zuwa, ya kalleni gami da cewa kije muhsin zai maidaki gida tare muke, na jinjina kai sannan na dau jakata na fice inai ma Bilal sai gobe, lauyana gwarzon namiji ya yau? Yayi murmushi kawai ba tare da yace komai ba ya tada motar muka wuce, jefi jefi nake kallonsa da alama yau damuwa tayi masa yawa, sai yaushe zaka huta? Ya dan girgiza kansa yana fadin kin san ban gama shari’ar Aa abokin dady ba ko? Hakane amma ni ban son inga mutum cikin damuwa always, kai kam ban cika fahintar mood dinka ba,ya aiki? Sorry na dameka da surutu ko? Matarka tana da aiki a gabanta, wannan ya sanyashi sakin dariya yana murza sitiyarin a slow yake fadin baby manya, kowa da kike ganinsa da abin daya dameshi, dazun ake sanar dani fitowar WAEC dinku, na dan muskuta ina ajiyar rai, yeah! ina alkawarina? An gama amma ban gaya ma daddynki ba, ni dai na ki wayon kai a nan kayi karatun? No,to tsabar wayo da iya tsara zance sai ka wani linkeni ta baibai, nifa ba zan zauna karatu nan ba binsu zan yi Canada, Dama ku lauyoyin nan kun iya lauye mutane kar ka manta nace kai nake son zama kaga dole in bi sahunka fakat,mafi mishkila cewarsa zan sanar masa sauran abin da zai biyo baya sai ki jure ko? Wannan hirar muke har muka isa gidan yayi parking muka sauka gaba daya palo muka wuce, inda muka tarar da mummy tana shirya table IB da daddy ya kawo mana da safe kuma yana kallon ball, said ihun goal yake yana rawa, muhsin ya bashi hannu suka gaisa sannan shima ya zauna suka ci gaba da kallon tare, ni kam mummy na shigewa ina taimaka mata da aikin, Mummy tace kazo ka daukanmaku abinci, na fadi idanuna a kan IB sannan na juya, ina iya juyo sa yana kokarin tafiya mummy ke fadin yi hakuri ban sa guba ba ai ka dai ci ko yaya ne, kai kenan kullum fulako, da wannan ban kuma jin furucinsa ba, ni da ita mukaci a dinning din bangaranta yayin da sukayi amfani dana palon gidan, akwai abin da kika cewa Seemah? Na girgiza kai daidai sanda na ajiye kofin juice gami da cewa ah ah wani abu ne? No na dai damu in san halin da take ciki ne, lah mummy ki nemi alfarmar Muhsin ko Bilal dayansu dai aje a sanar da mutan gidan, ni ban ma tsayar da shawara ba, bari dai daddynku ya san matakin dauka kan diyarsa ban son hawan jini, na mike ina tattare kwanuka sannan nayi kitchen don wankesu, a raina nake ayyana Bilal kam ya wuce raini a gurinki Seemah duk da taxi driver ne amma ba ya daukan raini, ko ni bai kyale ba,wannan da yana da arziki ban san ya zai kare ba, muhsin kuma miskilin kansa akwai tsare gida, shi kam ya san yanda zai kwaso ki ja’ira, ko wanne mummy ta tura maki tayi daidai, mazan sun san yanda ake handling din irinki…..
Yana gama cin abinci sukayi sallama sannan da azamarsa ya nufi gida bukatarsa kawai ya samu ya huta don samun nutsuwar zuciyarsa a sannu ya warware matsalar data durfafo shi, yau kam da alama baki akayi a gidan, kasancewarsa ba mai son hayaniya mai yawa bane balle kuma yau ba’a mood din yake ba wannan ne ya sanyashi wucewa sashin sa kai tsaye, har ya soma barci sama sama ya tsinci zantukanta tamkar almara, lallai ma ka haifi da baka haifi halinsa ba, albasa bata yi halin ruwa ba, kai da na rika kiran wayarka ka mani banza, shine duk wahalar danake sha kanka baka gani, da ka shigo kuma kayi kwanciyarka, anya muhsin lafiyarka kuwa? Ta sanya kuka tana fadin ni na san kunyata ni kake kokarin yi a bainar jama’a, to wallahi kayi kadan sati 2 na sama bikin ku da Suhaila, in ka isa sai ka nuna mani cewa kai dan zamani ne, dazun su auntynka halimah suka kai kaya nan suka wuni ana taya ni murna, tuwona maina muhsin shine daidai kai, wa zai zauna da kai miskili kafi mahaukaci ban haushi? ita din ma taimaka maka zatayi, ya sada kai kasa har ta kai karshen maganarta tana kallonsa, tun da ta shigo sai yanzun ya furta kalmomin nan 2 zuciyarsa tamkar zata tarwatse, yi hakuri sannan ya dan yin shiru, dama ita mama ‘yar daru ce ba na kadan ba, ga daukan abu da muhimmanci, in kuwa ba haka ba me hadina da Suhaila? Har ta fice bai daina nazarin yanda abubuwa suke zuwan masa ba, ya dan ja tsaki gami da mikewa a sanyaye ya dauko wayarsa, Muhammad ya kira don shaida masa kangin da mama ke neman jefashi, ya kake? mutan abj! Ya dan ta6e baki cike da damuwa yake fadin Sultan wannan abu fa ya kusan faruwa, ko? Cewarsa to sai me kai ba mijin mata 4 bane? To don me zaka damu kanka tun baka kai ko ina ba da kuruciyarka ka hallaka kanka ka bar mu da tashin hankali, see yarinyar nan fa bance ina sonta ba tukun gashi mama ta 6ata mani show, ni nasan baza ta auri mai mata ba wannan uwar kishin da twin dinta Seemah ma yi take bare wata Suhaila, ya isa man, ba abin daya fi karfinn addu’a ka dukufa nima zan tayaka, kuma sannan kar ka watsa ma mama katsa a idanu Allaah’s willing ta debo ruwan dafa kanta ai, irin su Suhaila ai maganin uwar miji ce sosai, idan bata samu ragon namiji ba sai ayi kaikayi koma kan mashekiya, ni dai bazan gaji da gaya maka ba, ka nuna hakurinka mama ta cancanci koma menene tun rasuwar Baba muna jss3 itace uwa itace uban, wani irin zagine bata sha ba gurin danginku amma ta jure saboda ku ta sha kuka ta manta, yau lokacin rama wacan ranar da ta yi maku ne, kaji man? Yayi ajiyar rai gami da cewa ok zan kwatanta amma zuciyata bazata dauka ba kirjina na min nauyi anya bazan halaka ba, maza to in kaga kana iyawa kilan ta wannan hanyar ta saki ra’ayinta in taga dan mama zai margaya ya karasa batun da wawiyar dariya, sukayi sallama ya kife layin yana dafe kansa dake sara masa, wai me ke shirin faruwa da shi ne? Matsalolin rankwacakam na yau daban na gobe daban.
Ya mike a kan gadonsa yayin da idanun ke kallon cilin yana ayyana abubuwa da dama a rainsa, a hankali akayi sallama gami da turo kofa sannan ta kafeshi da idanu yana nan kwance tamkar mai kirga cilin, ta dan shuri kafafun a sanyaye ta kara da cewa Bro ka rika raga wa kanka mana, ya muskuta sannan yayi mata umarnin zama a gefan gadon, Sa’adah me hikimar kin fadin sakona ga Hameedah? Ke fa shaidace kan wahalar da nake sha haba Sa’adah, Bro gaya mata kunna sabon wutan da zai rura wannan ne, kali fa kowa a dangi na son wannan hadin mama ta tsani baiwar Allahan nan ba kadan ba, har mai sunanta bata kaunar ji, ga Suhaila jahilace ta fannin zamantakewar jama’a kanta kawai ta sani,in har ta samu uban kowa ma ya rasa, yarinyar is happy bayyanar wannan maganar cutanta za’a yi ka duba wannan lamarin, in da rabo zakaga you end up with her amma gaya mata bai taso ba muma kasan muna sonta bata da matsala saboda ra’ayinkace amma kuma… Its ok Sa’adah tashi ki fice, Bro….. Fice nace shashasha i cnt count on u me amfanin kasancewa da ke? Ba laifinki bane zama da Muhammad Sultan ne ya koya maki shegyan surutu da keta, ya dan jingina kansa da bango yana ajiyar zuciya cikin yanayi na rashin madafa,daidai lokacin ta banko kofan shigarta cikin jeans designer kan nan ya sha attachment cikin wani irin yanayi take taku ita ga ‘yar gata, faratinan sun yi zako zako, wuya da yatsu sun sha daham masu daukan ido,wandon ya kamata irin fitina nun matan nan ce tana taunan gum, rigar ‘yar karama wanda ya bayyana tsarin jikinta fara kal ta karkata wuyan gefe daya yana zamowa, burst din kina hangoshi duk a cikin wayewa ne, Suhaila ‘yan mata masu azababan kyau sai kamshi ke tashi, da sasarfa ta karasa dab da shi zata zauna ya matsa yana nuna mata gurin zama,no kai nazo dubawa mama tace you are sick ko? Ke likitace? Yes yes yes nawan luv doctor,ya ja tsaki gami da mikewa kwanyansa a cushe shi ya ma rasa inda zai sanya kansa, da husnah auta suka ci karo tana fadin sowie yaya wata ke nemanka a waje, wacece? Muryar bayansu ta tanbaya da sauri, suhailace mai wannan tambayar, kafin ya ankare ta rigasu fita da shirin ci mata mutunci, Allah yasa dai ba Hameedah bace mai nemansa ya ayyana a ransa don baya kaunar abu ya hadasu da Suhaila gudun kar mama tace hasashenta daidai ne, Seemah ce cikin kasaitaciyar shiga wace ta dada fito da zatinta, kyawu kam nan gani nan bari yarinyar ta isa a kalleta a kuma kallo ko makiyi sai ya kyasa, wannan karan english wears ta zuba designers masu tsadan farashi sai wasu mahaukatan chain manya da suka cika mata wuya, vandana ta daura ta dan kewaye gashin kanta data saki a baya, Big gal ake gaya maki ita da kanta ta tuko motar takalman masu tudun gaske wayanda suka dace da skirt din jikinta, tana nan zaune tana jiran fitowarsa sai karkada makulan hannunta takeyi. (tana mamakin dukiyarsu Muhsin, Ashe masu arzikine take rainashi, ai kan yanzun tana yinshi),daidai nan Suhaila ta fito da dan gudunta tana haki shi ne a bayanata ya tsaya jikin bango gami da jingina dashi yayin da ya harde hannayensa yana kare masu kallo,a sanin da yayi masu ya fahimci ba hameedah bace babynsa mai class ce, Hy mai kyau ta fadi tana kwantar da kai, keeeee cewar Suhaila, ke jakar inace? A tsanake ta kare mata kallo tana yamutsa fuska sannan ta kara da jan tsaki mtsss tana fadin daga gani u missed road don ba Chinyere a gidan nan, muhsin gurinka nazo fa, dan ubanki kin yi kadan ki zagyan in kyale kan uba, hey hang am ko nayi maki kama da kashi ne? Irinku karuwan nan ne masu kama tasha so dole ayi kyaman ta6aku kar mutum ya kwaso wa kansa cuta, ba don haka ba da ko hakora uku na cire a wannan kazamin bakin banyi asara ba, ta cakumi kwalar rigarta tana fadin ke har kin isa hameedah kike ko wa?karaf a kunnan mama dake karasowa gurin ta amshe tana mai cewa Hameedah! Mara kunya wace bata gaji arziki ba, me ya kawota nan? Tayi masa tambayar yayin data zuba masa idanu, ya sada kai kasa gami da cewa ba ita bace, da kyau dan zamani, cikani karya cewan Seemah,da kyar ta kwaci kanta tana fadin an dai yi asarar haihuwa , Mama ta kame a tsaye ita kam ta mayar da eye glass dinta dinta sannan ta tayar da motar ta bata wuta ta taga ta leko tana mai ce masa sai wani lokacin, ta badesu da iska tayi gaba,mama ta shiga tafi tana salallami, shi kam a nan ya barsu ya shige dakinsa don in ya biye mata yanzun za’a fara rigima sabuwa ya san halin abarsa…
Shirye shiryen biki kam ba abin da aka fasa, angon da akeyi dominsa harkokin gabansa ma kawai yakeyi bai damu da lamuransuba… Cikin wannan satin Bilal ya samu sallama jiki yayi kyau har ya koma bakin aikinsa(direban Hameedah), daddy kam ya rasa dalili amma sai ya birne abin a ransa don ganin iya gudun ruwansa… Yayi parkin daga dan nesa kadan sannan ya kira wayarta ai kuwa abin so ya samu ba jimawa sai gata ta fito fuskarta dauke da murmushi tana kallon kwayar idanunsa, shiga muje yayi mata wannan umarnin, ta bude dayan 6angaran ta zauna bata damu da jin inda yake niyar kaitaba, ya tayar idanunta kur a kansa ji take burintane ya cika, eatry ya kaisu ba jiran umarni ta sauka tana gyaara zaman rigarta, ba ja this is our 1st date ta ayyana a ranta tana fara’a, bismillah ya fadi bayan ya gyara parkin suka rankaya ciki, ita ta fara zama a sit na 2 bai tanka ba ya dai zauna ya bita a hakan,kalan abin da za’a kawo ma list din na isowa ita ta amshe tayi tikin sai ya bita da idanu, aka cika gurin da ordernta ta soma kai shawarma tana fadin ya baka cin komai? Ya girgiza kai gami da cewa lallai kama da wane bata wane,what? Cewarta, ki saurareni da kyau,ta dada natsuwa taga fuskarsa babu alamun wasa, Alhaji tsohon dadynki yana US forever ya tafi kenan, ki tattara ki koma ga iyayenki,wat? Ta fadi cikin kidima ,yes ai kin jini,gidan da kike ciki kawai ya rage masa a naija,amma ya kwashe komai nasa,ta yi tsit tana ajiyar zuciya,daddynki mai kudi ne dake zaune a Canada,can zaku koma suna sonki Seemah mummynki ta damu dake, comeon cheerup yaushe zaki koma? Ki fada zan maidaki what a nice family reunion, tayi smiling sai ta rikide masa tamkar babynsa, gabanta ya fadi sanda ta tuna da Hameedah, Hameedah fa? Manta da ita kece ‘yar yayi ai, ta fashe dadariya, oya tashi muje to, suka mike gaba daya.
MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
17…
Sanda ta shiga gidan diban kayanta ta tarar da hajiya Ni’ima nata safa da marwa a palonta duk halitarta ta canza, damuwa da fargaba sun canzata taga diyar na diban kaya, ina zaki ki barni ni kadai? Inda kika daukoni zan koma? Haba princess, kar ki ta6ani yau zaman takaici ya kau, zama da annoba irinku ta yanke, ta tsaya sororo baki a hangame tana kallonta, shi kam ya zuba mata kayan a mota a cike taf sannan suka dau hanya, tana planning abubuwan da zatayi a ranta, daula, gidan arziki ba talauci,harkar girma zata bar naija, sai ji tayi yana parking da azamarta ta sauko Hameedah ce ta fara lekowa ta tagan dakinta sannan ta fito dan gaisawa da lauyanta, yau kam ya cika mata burinta tunda ya dauko Seemah ya cika alkawari kenan, Seemah! Ta fadi tana mai nuna alaman barka da zuwa, uhum hy cewan seemah fuskar a gimtse yayin da ta daga mata hannun dama sannan ta kau da kanta daga gareta, ina mummyna? Tayi mata banza da ita tana fadin lauyana shigo pls ko ruwane ka dan sha, duka suka barta a gurin tana cizan yatsa Bilal dake tsaye yana kallonsu shi ya karasa ya taya ta kai kayan ciki, sannu fa direba ta fadi tana taku daidai, ya bita da idanu fuskarsa cike da takaici, albarkacin Hameedah taci dai, a sit room ta samesu suna hira rabinta dariya ce gashi bata san abinda suke cewa ba, don Allah lauyana? Allah kuwa you made it ai dama ban jinki nasan wannan brain din za’ayi abin arziki, zan ba daddy result din hakan ya miki? Yes yes yes! Am proud zan taka matakina na farko da zata sadani da tsanin kujerar barister Muhsin, ranka ya dade mai girma lauya Allah ya ja da rainka, tare da naki cewarsa, zan gudu idan masu gidan sun dawo kar ki manta da sakona, na rakashi har sai da naga motar ta fita sannan na dawo cikin gidan inda na tarar tana ta dube dube, dakunan gidan take dudubawa ko me take nema? Na kau da kaina don karma ta 6ata mani rai, ina wake wakena na bi 6arin da dakina yake ina iya jiyo zazzakar muryarta tana mani masifa na basar, laptop na dauka ina dan buga game, kamar daga sama naji bugun kofar dakina an turoshi, a firgice na waiga itace ta shigo hannunta a kugu tana karewa salon dakin nawa kallo, na zuba mata na mujiya tana karkada kafadat, can ta ta6e baki sannan ta doka wani uban tsaki, ya kamata fa a san ni Seemah bazan iya hada daki da kowa ba, na kau da kaina ina yamutsa fuska sai yaushe zata daidaita sahuntane? Ba jimawa ta dauko kit dinta nikam abar kallo na maidata, sai wani takun takama da gadara take, kayana da Billal ya kawo daga laundry dazun na dan jerasu a gadon da yake tana da fadi katifar, su ta watsa kan rug tana fadin haba gida sai kace babu house help? Ita kadi dai can ta dau towel dina ta shiga wanka tana ta waka a bayin sannan aka fito ba jimawa ta sakar mana speaker cikin music din zamani ita kanta ginin gidan amsawa take, hakurina ya kare yarinyar ta soma kureni, alwallar la’asar nayo zanyi sallah a dakin nawa amma babu dama, na kai hannu zan kashe ta bige hannun tana lakace lakacen kayan ado a kwabata, me haka? Mele ta mayar mani tana rangwada, hankadata nayi waje na sanya kwado sai bige bige take na yi sallata, sannan na kwanta barci, muryar mummynah ce ta tayar dani ina iya jiyo amon daddy yana fadin baby bude kofar mana ku kwana yau daya jal kinji? Ba haka naso ba amma na share, ina budewa na fada jikinta ina fadin nayi kewarki da yawa sugar, sweet sweet mummy, ta dan bige bakin cikin tsigar wasa take fadin you still can’t accommodate babby haka na koya maki? Na dan sha mur ina girgiza kai, a gefan dady na hangota farinciki fal raina tunda na san na fita matsayi nesa ba kusa ba, ko me ta gaya masu? Kishi karara a kwayar idanunta na gunshe dariyata ina sinna kai, ta shige dakin tana fadin mummy yunwa nakeji fa, banda rashin tunani matar data dawo daga anguwace zata samar maki abinci? zo baby cewar sa, na karasa gareshi ina ‘yar dariya, ‘yar daru kawai karfa ku kona ma government gida, na riko ipad din hannunsa ina kallon hotunan bikin da sukaje da mummy a yau, ki yi hakuri gobe Allaah’s willing dakinta Zai kammalu kinji? Na gyada kai ina fadin ba komai ai Kamar kullum mun dade a palo muna hirar da muka saba, daddy ke bamu labarin 6arayin da suka kamasu da abokan tafiyarsa, wani fannin musha dariya yayin da da yawansa bakinciki ne, hakimar ta kame kan daya daga cikin kujerun palon tana dadanna remote, na kula ita a gareta dukiya tafi mutum muhimmanci, abincin ma sai ta za6i wanda zata ci ga wulakanci ba wanda ta kyale, har lokacin kwanciyar mu yayi bata da alaman tashi, mummy ta juya halshe da larabci take ce mani banda hayaniya baby ki zama wace zan yarda da ita, ok? Na jinjina mata kai kawai idanuna fal barci, a nan na barta inaji mummy na ce mata in kin gama kai kashe kayan kallon, ni kam ban kuma bi takansu ba na nufi gadona ina sake sake cikin raina, na rungume ‘yar pillow na mai siffar zuciya ina mayar da numfashi daidai sanda na kashe wutar dakin…
Tun ina jurewa har na kasa sosai nake jiyo hirarta a waya tamkar mai jinnu sai surutai take har barcin ya fitar mani a idanu, na mike na bar mata dakin palo na koma da bargona, ga wuta ta kunna mana tar, nan dinma har na fara barcin tamkar cikin mafarki naji tana sheka dariya yayin da take kokarin bude frige hannun hagun manne da waya a kunnanta, ji nake tamkar in shakota, na hakura na koma nayo alwalla na soma jero nafilfili, ina kan sallayar har goshin asuba a lokacin sarauniyar ke kokarin kwanciya barci, ana sallar asuba barcinta yayi nauyi tuni n.i kam ina idarwa kitchen na nufa don kama wa mummy aiki, da misalin karfe 12 na safe ta fito tana wani shan kamshi, tuni dakinta ya kammalu ni kaina na kosa tayi parking don daren jiya banji da kyau ba ta barni da rama barci, daddy ke kallon aljazeera ni kam ina goge undies dina rashin aikin yi kawai, mummy ta sanyani gaba tanai mani tsiya, takuntane ya dakatar da kowa ta dau pillow daya ta zauna kan kujera gami da dorashi kan cinyarta tana wani kale kale, ya kwanan bakunta? Cewar mummy lau ta fadi tana kallon screen din plasma, zan dan kalli wani programm ta fadi tana kallon daddy alamane na son kar6an remote daga gareshi, ya kalleta sannan ya mayar da idanunsa kan mummy ta kau da kanta, batare da yace komai ba ya basar kawai, dakinki is ready cewarsa, na gani ta fadi gami da mikewa ko tayi sallar asuba? Abinda ban sani ba kenan sakin baki nayi yayin da na bita da kallo, lallai kunyanga ta haifi uwargijiyarta,tirkashi! Anya kuwa diyatace Rahma wannan babu mix up? Mummy naga ta zuba masa idanu tana nazarin abin fadi, kin yi shiru? To me zan ce maka? Baby jeki dakinki kawai ki bamu guri, na shige a sanyaye me hakan yake nufi? Annoba zata kassara mana jin dadi na ayyana a raina, sanda na tura kofar da sallama da sauri na runtse idanuna saboda mugun gamon da sukayi, tsaye take haihuwar uwarta tana shafa, kunnan na manne da head phone anayi ana rawa a gaban dreesing mirrow, da alama bata san da wanzuwata a gurin ba, towel dina da tayi amfani dashi a yashe kan gadon duk ya jika gurin, zuciyata tayi fam kiris nake jira tayi wani abu in shako shegiya, i trust mummy ba don haka ba nima ina bayan daddy, fatana kar sa in san da suke yayi tsayi dai, nima ina kokwanton hakan ina ka samo kwan da ka sanya mani? Ta yi tambayar cikin damuwa, Yayi kwafa yana jijiga kafa, ah to ashe babu dadi duk kabi ka isheni da batun, zan je muyi DNA kawai, daka kyauta ai nima in huta da kallon hadarin kajin nan da kake mani, ta mike ta bar masa gurin, sanda na fito palon babu kowa don haka da sanda na nufi, sashinta, mummy manya aminiyata ta kaina, na dafe bayanta ina tsokananta, wanda ya sanyata ajiyar zuciya sannan na ji tana fadin duba kigani idan yana nan, na leka dakinsa wayam, ya fita na fadi cike da fargaba, zauna to zamuyi magana, yau duk ta hade rai nima sai ya sanyani shiga taitayina don kar in dada ruru wutar, kina da idea baby matso ki sanar dani wani abu game da ita tunda tun kuruciya kuke tare kunyi school daya, mummy Seemah fa sai addu’a na fadi raina a jagule, ta kafe ni da idanu tana fadin lallai kame da wani bata wani, badon ni na haifeku ba na sanki baby da bazan ke tantance ku ba, yarinya ‘yar firit irin wannan ta gallabi jama’a? A raina nace yes da haihuwarta gara 6arinta born by mistake ce, ta rufe batun gami da cewa any way, daddynku yace aurar daku zai yi gaba daya don samun saukin lamuransa, ajiye irin Seemah a gida hatsarine, irinta she’s up to anything ba macen da za’a yarda da ita bace, mummy laifinta ya shafeni kenan? Nq fadi ina dafe kirjin na dake mugun bugawa, ah ah ba haka ake nufi ba, bai yuwa ayi auran mutum daya kinsan hakan, gashi da same age, na sharce kwallar daya tarun mani a idanu ina hango Bilal ta windo shi kadai nake burin aure, ya zanyi da batun karatuna da muke da Muhsin? Shi kenan bazan ci gaba da ilimi ba? No baby wa ya gaya maki hakan? Ko mijinki bazai dau nauyinki ba daddynki na da wannan niyar so kwantar da hankalinki,a sanyaye na mike ina hada hanya zuciyata tai rauni ba kadan ba, Seemah why? Na banko kofar dakina ina shashekan kuka, ta kalleni sannan ta ja tsaki tana taunar gum, kin cikawa mutane kunne cewarta sannan ta kara sautin wakarta tana harhada kayanta don komawa dakinta, ke ba taya mutum zakiyai ba sai shegyan iyayi da kankanban jaraba, nonsense kawai, nayi mata banza ina jimamin lamurana…
Ya dan dubi agogwansa cike da takaicin lamuransa, yaushe ya zama direban mace ne? Duk aikin mama ne banda hakan yaushe zai tsaya biye wa mace kamar Suhaila? Sai kuwa gata ta 6ilo ta 6angaren mama tana wani karkade karkade tamkar wata dancing girl, ya sada kansa kasa yana karkada makulan motar hannunsa, sannan ya bude ya shiga zuciyarsa na kuna, har ta zauna ya tayar ta dakatar dashi ta hanyar fadin oh na manta da color 2 dina(attachment), ya buga uban tsaki sannan ya bigi sitiyarin yana muzurai, wai ke wa kika ajiye ne? Kai ta fadi tana cin magani, kar ka daga mani hankali fa don kaga ina sonka? Ta sakar masa kofar ji kike gwaram har ya dan razana sannan ta shige ciki har ta hadashi da mama, da yake gyaran gashi zai kaita kasancewar auran nasu dada matsowa yakeyi, yayin da tashin hankalinsa ke dada karuwa, jimamin rabuwa da sahibarsa ita kam bata san irin wainar da ake toyawa ba(HameedahA nutse na karasa gefansa nayiwa kaina matsugunni kan kujerar da yakan dan zauna idan ya gaji da wankin, wannan ne ya saanyashi waiwayowa yana murmushi small madam hw now? Sannu da aiki nazo maka, i dey happy cewarsa, na kar6i jaket din da yake niyyar shanyawa ina fadin zan taimaka maka, ya rike baki yana kada kai leave am i no fit face oga and madam, na tsintsire da dariya ina kallon kofar palo daidai sanda Seemah ta fito da boxers sai wata fitinaniyar vest tana sharce gashinta, Bilal! Ta kwada masa uwar kira tana karkada comb din hannunta, ina nan zaune naga ya karasa da dan saurinsa yana fadin ma! Ta watsa masa takalmanta tanafadin maza goge mani shi zani outing, nayi tsit don kar mummy ta yi dani, muka ci gaba da hirar mu ni kam sama sama nake jinsa don Seemah ta jagula mani lissafi ba kadan ba, ina nan zaune na jiyo hargowarta a kitchen sai ga IB ya fito da remote yana fadin baki isa ba matsiyaciya, ta biyoshi ina jinta tana fadin kar ka kuma shigowa gidan nan useless kawai, ni da mutumin nawa muka kame garin kallo, na mike tsam cikin gidan na nufa ina kiran sunanta, me ya hadaki da dan amana? Ban son shishigi ina ruwanki? Kama kanki kar or else zan yi maganinki hammy, na kada kai sannan na kara da cewa ke fa baki san darajar kanki ba bare kisan na mutane, hold it! Akwai wanda ya rasa darajarsa irinki mai yake wa kowa hakora? Lack of class soyayya da direbanki kaskantace mafi karanta ga….ji kike kau na kwada mata mari ina fadin enough karuwa, ta shako mani wuyar riga da kokawa, IB ne ya shigo da saurinsa ya nufi sashin mummy yana fadin kizo zasu kashe kansu, wannan ne ya sanyani kwatan kaina da sauri na shige daki, sannan na kule kaina a ciki ina haki, hankalina a tashe tunda ya sanar da mummy na kilace kaina na ma kasa fita daga dakin, tsoron fushinta nake, can sai ga horn din motar daddy wanda ya sanyani samun kwarin gwiwan bude kofan na fito, ya shigo cikin palon fuskar babu walwala, ku fito zamu asibiti, ya fadi kai tsaye sannan naga ya fice, mummy ta dan kalloni cikin harara sannan ta kara da cewa sai ku bishi ai, Seemahhhhhhhh! ta kwala mata kira cikin damuwa, ‘yar takamar ta fito tana taku daidai da shimi iya cinya a jikinta, jeki sauya shiga ku raka daddynku asibiti, bata jira amsa ba ta bar mana gurin tana ‘yan surutan dake nuna alamun mun kaita bango, na ja na fice da mayafin kayana a hannu, shi kansa daddyn a tsorace na karasa gareshi don babu sasauci a bangarori biyun, wucewar mintina 20 ba Seemah ba alamun ta ,daddy ya yi ta horn yana jan tsaki can sai gata tana gyara zaman gogles a idanunta, wai uban me take takama dashi ne? Zuciyarta a bushe sai fitinar tsiya ni ban taba ganin mai hali irin wannan ba, ta bude ta shige ya tayar motar shiru itace ma naji ta zama business call wayar a busy take tana ta amsa kira tamkar ‘yar kasuwa har muka karasa asibitin, kuje ciki ina zuwa cewarsa, kai tasye muka nufi ciki, bq jimawa ya tufa mana baya muka shige office din likita, jinin mu aka dauka yayi mana umarnin jiransa a mota yayin da muka barshi a ciki ko me suke tattaunawa da likitan? Ta bugo kofar gam tana fadin aikin banza kawai, ai ba claiming iyaye nayi ba da za’a ke tozartani, banda son kai ai ni ‘yarsa ce ta halak, ta doka kujerar da nake zaune gami da cewa kina ji munafuka kin shareni, nayi dariyar keta ina cewa its a pity zaman gidanku na neman gagararki saboda babu nan, na fadi ina nuna kwakwalwar ta, a futsace ta bige mani hannu tana muzurai, kika sake hannunki ya ta6ani yau sai nayi maganinki a doron kasa, kar ki sanya wa iyayena high Blood Pressure, sahun daddyne ya nutsar damu, har a lokacin surutanta take bata damu da yaji ko kar yaji ba, Shima bai bi ta kanta ba don zuwa yanzun sun san halin abarsu already, a sannu yaja muka dau hanyar gida…
Jama’a sun cika unguwar don taya amaren murnar wannan rana, agon da kanasa yaje airport dauko amininsa Muhammad Sultan baki abin magana, a motar ma bai kyale shi ba sai tsokanarsa yake kamar dai yanda ya saba, Allah zaka sha mamaki sultan kaga na hanaka Sa’adah, ya dan sosa keya yana fadin afwan na hannun daman, ehen ya batun baby ‘yar gata? Ya dan saki fuskarsa yana fadin tana nan, ba haka na ke nufi ba, ta sani? Ah ah ! no need, da kyau jarumi, inda hali zan ganta kafin in koma Lag, why? Wannan ni na sani cewarsa, zan gani ai, dama ai ban fatan ka makance gara ka gani din, gobe akwai baki daga 6angarena man ya kenan? Sanin kankane cewan gobe Allaah’s willing zamu zauna shari’ar karshe, shari’a tafi auran naka muhimmanci kenan, yes of course tafi amaryar daraja, i seeeeee, to ka jira ai goben a daura tukun kafin kayi gaban kanka ko? To babana, ba batun iskanci a nan Muhsin daz da truth, me akeyine a layinku haka? Wai mothers day jibi duk sun tara mutane ana ta hayaniya, hmmm mata da bidiri suke bari na kira sahibar, ya daga wayarsa yana kokarin samu Sa’adah tun kan suyi parkin…
Allaah’s willing daga yau an gama zaman kotu, na ayyana a raina zuciyata kal, zan ga lauyana inji makomar karatun nawa, ke baki san kina 6atawa mutane lokaci ba? Tayi mani wannan tambayar bayan ta hankado mani kofar daki tana tsaye a kaina sai karkada kugu take, wai ke yaushe zaki hankaltune? Bayan kece mai wannan sifofin don yau daya nayi kuskure sai ki sanyani gaba? Tafice tana fadin ki samemu a mota, don kar in barsu suna jira na hanzarta na samu duk sun shiga motar daddy ne ya tukamu, daga nan sai kotu.
MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
18…
Wayewar garin ya tashi da niyar barin gidan, wannan dalilin nema ya sanyashi shiryawa tsaf yayin da ya zuba uniform dinsa cikin briefcase, Muhammad Sultan na bayi yana wanka agon ya fice ba tare da mutan gidan sun farga ba, kai tsaye gurin aikinsa ya nufa a motar abokinsa da suka fakata a kofar gidan, gudun kar ya ja ta gida mama ta dagoshi tunda yasan hali…
Na kafe kofar kotun da idanu ina jiran isowarsa amma har tsawon wani lokaci bai iso ba, yau ko lfy? Na tambayi zuciyata ina kokwanto, wannan ne ya bani daman kiran layinsa don jin abin dake faruwa, Sultan dake ta faman shiryawa ya dan ja tsaki ganin kiran taki tsinkewa, ko ina Muhsin ya shiga har ya bar waya haka? Ya dan tsagaita sannan ya karasa ya dauka yana tunanin wannan marar hakurin tunda ankira sau barkatai ba’a daukaba ai sai ayi hakuri, na dan yi gyaran murya yayin da naji an daga wayar sannan na soma fadin lauyana lfy? Ina alkawarin mu? Ya har yanzun baka iso ba? Yayi tsit yana tunain wacece, kwakwalwar sa ce ta cushe ganin ya gaza fahimtar MATSAYINTA , baby! Hmmm waye? Na fahimci ban raba jin wannan voice din ba, na dau murya don shi din ba bakona bane da wani zai dau wayarsa in kasa ganewa, aminin sa ne, Ya Muhammad! har yanzun bai iso ba fa, ya bar wayar a gida ina tsammanin nan gurinku ya nufo, na yi ajiyar zuciya gami da cewa uhum Shukran, hmmm baby mai babban matsayi ya fadi daidai sanda ya katse wayar, ko me hakan ke nufi? Tsokanace cewan wani sashi na zuciyata, ina dire wannan tunanin kaman ance daga kanki mukayi ido hudu dashi, gwarzon namiji wanda in har zai keta taro sai ya zama abin kallo, irinsa mata ke rubibin samu, na sakar masa murmushi yayin da nake daga masa hannu yayi mani alamun zamu hadu anjima, na gyada kaina kawai cikin gamsuwa, Seemah kaman zata fashe…
Ma Shaa Allah cewar mama daidai sanda tajiyo marokin dake sanar da daurin auren a bakin masallaci wanda yake nuna alaman an daura kenan, ta daga kanta tanai wa Allah godiya, daya nuna mata wannan ranar, daga yau dan fari (dan da tafi so) ya zama babba shima, shewa ‘yan matan amarya Suhaila suka dumame gidan dashi, ire irenta ta kwaso kalar ta kenan su suka dace da ajinta, har kullum suke gareta tasu ce ta zo daya, daga mai karin gashi sai wace ta gaji da bilicin ga shigar banza da rashin fahimta addini, cikinsu harda kafirai wayanda ba musulmai ba kuma ba Christian ba ,tunda ba za’a dangarta su da hakan ba, ita kanta amaryar ba wan ba kanin, rabon data kai sallolinta cikaku kan lokacinsu har ta mance, lokuta da dama daga sallar asuba shikenan…
Al-amin ne ya shigo da azamarsa yana fadin MAN ka zama ango, baya nan cewan Muhammad Sultan, ya dan dakata yana fadin ina ya shige ne? Ya dan fita cewarsa, oh ba haka naso ba yau ga manyan baki na kawo su ganshi, muje mu gagaisa, sanda yayi arba da personalities din saida yaji takaicin tafiyar da Muhsin yayi, mutanan da yake burin son hulda dasu don samun ci gaban rayuwarsa su Alamin ya kawo su, shi kam ya dan tsaya suka gagaisa, ya dai kar6i numbarsu don isar da sakon zuwansu ga aminin nasa.
Sanda kotun ta idar da shari’ar yau wanda ya kasance na yanke hukunci ga masu laifin sai naji zuciyata ta karye, musamman da naga hajiya binta ta durkushe tana razgar kuka, madam zarah kam bata da laifi sam dole akace su biyata wasu kudade da kwakwalwata ta gaza sarrafa adadinsu cikin sauki, kaulah sumewa tayi sanda taji an yanke mata zaman birsin na tsawo shekaru rayuwarta, hajiya Ni’ima natar fitar da kwallah ta gaza motsawa daga inda take, daddy kam yace ya yafe nashi taran dake kansu amma they can’t go unpurnished, lalli duk nisan jifa kasa zata fado, madam Zarah ta karaso gareni da sasarfa tana kokarin fadin wani abu, na daskare a gurin na matsu inji furucinta, ina da rauni zuciyata bata daukan damuwa, har kwalla sun zubo mani, ina sonki hammy ta fadi tana shafa mani kai, zaki rika kawo mani ziyara? Na daga idanu ina kallonta har na rasa abin cewa sam, kin yi shiru? Na dan goge mata kwallan dake zubo mata gami da cewa Allaah’s willing I will pay visit from time to time ,ta yi murmushi sannan cikin yanayin murna mai gawraye da kuka take fadin zan iya zuwa in ganki? Why not? Tnx hammy ki rika sanyani cikin addu’ar ki kinji? Na gyada kai ina dan murmushi, kan mu ankare tuni ‘yan jarida sun sanyamu a tsakiya, Aunty kema kin yafe masu taran ko? Nayi tambayar cikin kulawa, Eh ta fadi tana kallon Seemah da ta iso inda muke da rikicin tsiya, taho muje dan ubanki, ta fadi tana jan hannuna da karfin tsiya, sai ga sautin muryarsa yana kokarin kawar da mutane don ya cima inda nake tsaye, baby fito cewarsa, na daga kai ina kallon jama’an dake gabana, sai da Seemah tasan yanda tayi ta jani muka bar gurin da masifarta, na yakice kaina daga gareta bayan mun bar gurin ina fadin wannan wani irin wulakanci ne ke baki ganin magana muke da madam Zarah? Komai ke hammy? To wallahi na gaji ina nan bazaki ke yaduwa ba labarinki na kaiwa inda ban zato, ina kika shige ne ina ta nemanki? Na dan murmusa gami da juya mata baya yayin da na fuskanceshi, more grease to your elbow lawyana, murmushi yayi sannan na soma fadin bani kayan pls zanyi hoto dasu, kai baby sarkin buri, kar fa ki mutu da buri, uhm uhm bari fadin hakan sai na baurge ka, yes yes yes oya gyara wig din, ya daukeni a wayar sa yayin da yake fadin yau ga justice Hameedah yayin da yake dariya, aikin banza cewarta sannan ta wuce fuuu nikam dariya na saki saboda yanzun ba komai tayi yake bani haushi ba, ke bakisan wanda ya mutu da buri kabarin sa kumbura yake ba? Na waro idanu ina fadin inji wa? Kai mutane dai suka tsara abinsu ko? Yayi murmushi ba tare da ya bani amsa ba, yayi to bari in kara maki daya ko? Ok muje chamber ka daukan ,muka wuce muna tafe muna hira abin mu, baby mu tafi ne, muryar daddy ne daga mota, no ina zuwa mummy afwan bazan dade ba ,ki kwana ma cewar Seemah, zan kar6a fa in wankesu, i luv the looks kin bani dama in wanko in cire copies dina nima? Ok sai ka ajiye min copies dina ko? Yes muje, ya bude mani kofa na shiga ya rufe daddy nai masa jinjina kan kokarin da yayi zuwa yau, a haka yaja muka bar gurin, Saida motar ta 6ace masa sannan ya soma tunanin wucewa gida, daidai lokacin dayake shirin tada mota wayar Muhammd Sultan ta shigo, ya daga yana fadin ya dai? Kai fa dan Iska ne baka iya abu ba don tsiya sai ka bar lamuran gabanka kaje kayi zamanka? Ban son damuwa please, i seee wallahi ka kiyayi 6acin ran mama don tsira da mutuncin ka, again dazun nan Chief Justic din Nigeria Dr Alfa da tawagarsa suka tafi karkashin jagorancin Alamin, Subhanallah! Ya fadi yana dukan sitiyari, ina fatan dai gida ka yo don shirin dinner? Am speech less Sultan bari dai gani nan tafe, anyi mugun mutum ko ya sanar mani in koma gida da wuri cewarsa yana murza sityarin motar…
Yayi parkin a kofar gidan daidai sanda ya sawo kai zaya shiga amarya Suhaila da tawagara ta suka fito da niyar shan iska, shi kam baima ganta ba ya dan dakata yana gagaisawa da abokansa da suka zuba kujeru a harabar gidan suna fira, ga ango cewar abatula aminiyar amarya, wannan ne ya bata daman karasawa with full confidence tana rausayawa a hanya, wow kace yau kayi tozali da justice? Tsaya nan ka zaci karya na shara maka? Well ya muke ciki? Manta kawai MAN shi din ma yana son ganin ka, good dude Alhamdulillah burina zai….maganar ta katse masa dai dai sanda yaji hannu an rungumoshi ta baya, Sultan ya dan kau da kai yana fadin Ango Ango, harkar manya kenan, honey nayi kewanki sosi ashe ka dawo? Ya yakice ta yana fadin kai kuma sai kaci gaba da zigata, sannan ya juya yayi cikin gida zuciyarsa tana raya masa abubuwa game da hakan, yarinya karama irin Suhaila tasan ta makale wa namiji me hakan ke nufi? Gashi ta zubar da girman sa a gaban mutane , a bainar jama’a, Sultan ma yana rura wutan rikici tsakanin su, yayi kwafa sannan ya soma rage kayan jikinsa don shan iska, can ya shirya shiga wanka da zulumin fitowa ya shirya ya ziyarci gidan government don ganin wayanda suka bashi kwangilan case din data kula kulaliyar da ta haifar da abu mafi girma cikin zuciyarsa game da Hameedah, wanda har gobe bai jin akwai wanda yafishi dacewa da samunta a matsayin uwar ‘ya’yansa, bai wani jima ba ya dan watsa ruwa kawai ya fito don kar ya 6ata lokaci, kugunsa daure da towel yayin da ‘yar karama ke hannun sa yana tsane sumarsa dashi, a nutse ya karasa gaban dreesing mirrow da yake dan gayune bakin sa dauke da fito mai amon kidan kuchi kuchi hotahe, duk da dai tsohuwar film ce shi kam har gobe yana son ta sosai, takan sanyashi nishadi, tunda ta shigo tayiwa kanta mazauni kan gadon sa tana jiran fitowar sa, ta madubi ya ganta hakan ya sanyashi juyawa da sauri, cike da takaicinta ya soma fadin me ya kawoki? Ta dan yaye skirt dinta cinyoyinta santala santala suka bayyana yayin da take fadin laifine don na zo neman lada? Ta laso lebanta tana shafa hips dinta a slow gami da langabe kai, da iya taku irin na mata ‘yan bariki masu jan ra’ayin mutum ta mike tana dan sa6ile hannun rigarta a kokarin ta na son bayyana surorin tada sha’awa, me yasa kanka kawai ka sani? Ta fadi a shagawabe tana nufoshi, haba mijina kar ka yi haka please, ya shareta yana sanya kayansa bai ankara ba ya ji saukan numfashin ta a wuyan sa kanta na manne da bayan sa, ya tureta ta fada kan gado gami da nuna ta da dan yatsa, wai ke wace iriyar mutum ce marar kunya?ah ah ha ! ai ba kunya a musulunci, to kunyar wa zanji tunda kowa ya shaida kai mijinane, ya ja uban tsaki gami da cewa kin yi asara tunda kika kasa hakuri har sai an kaiki dakinki, haka kace ko? Ke ce ai kika rako mata duniya, haka ka gani? Bai kuma bi ta kanta ba ya dau brief case ya fice da sauri ta rufa masa baya, ko kamin ta cimashi har ya tayar da mota kan idanunta ya fice tamkar ta kwala ihu don takaici, bazan jure wulakancin ka ba ta ayyana hakan a rainta, wannan fitar har dare bai dawo ba, gashi babu wanda yasan inda ya shiga sai hada hadan zuwa dinner akeyi amma angon shiru tamkar shaho yaci shirwa, har aka soma kai mutane abjuja garden don gabatar da taron shiru babu Muhsin, rai 6ace Muhammad Sultan ya soma laluban wayarta (Hameedah), ko baya gurinta ita ke sarrafa zuciyarsa, zata san yanda zata shawo masa kansa, kira daya ta daga da yake tana wasa da wayar ya kira, an mata adon gari ya fadi da salon tsokana don son janta a jiki, Muhammad Sultan ne, uhummmm! kai baka neman mutane kullum lawyana yana min hirar ka, so sorry baby aikine amma yanzun ina gurinsu Muhsin , yau ban ganshi ba ,OK ko zamu gana? Dare fa yayi? Amma zan fadi idan an barni shi kenan, thanks cewar sa sannan ya katse wayar yana nazarin kaifin basira da hankalin ta, shi kam Ango wayarsa ya sanya tuni a silent don kar a dame shi ya shiga tsabgar gabansa, har muka gama shiryawa ni da Seemah ina dan kokarin samun wayarsa amma bai dauka, ko me ya ke yi haka ? Haka dai na basar dama so nake inji ko yana gida, yau nayi mamakin yanda akayi a gida suka bari in fito a daren nan, Seemah da kanta ta amince zata rakani, daddy ke janmu muna tafe muna ‘yar hirarmu…
Ya fito kenan bayan sun sallameshi ya dau hanyar gidan yana tuki ya zaro wayar sa don ganin agogo ko karfe nawa, missed calls rututu, ita ya fara kira, na dau wayar ina murmushi, na’am, kana ina? Na dan Shiga busy ne, where are u? Hanyar gidanku tare da Seemah daddy zai kaimu, ji yayi kansa ya sara har bai san sanda yace mata no abuja garden dai ba, gudun kar suje can mama ta wulakanta su, sai kuma me? Au ashe tsabgarsa ake yi a can? Yau duk rufa rufa zata kau, baby da idanun ta zata ga yau ya zama ango, ya dan yi jim yana nazari, shin me abin yi?
Na mayar da wayar na ajiye ina kallon Seemah data kafeni da idanu tana fadin casu akeyi gurin hala? Na dan girgiza kai gami da cewa ke kuma kwakwalwarki bata daukan abin arziki sai party, casu da clubbing, ta dan yamutsa fuska da alama ba nice a gabanta ba, Seemah tun sanda Sultan yayi mani waya naga tayi sanyi ko me ya dameta haka ne? Daddy ya dan yi murmushi gami da cewa ni kam cikin ku na rasa ko waye babba, da gaske abuja garden din muka nufa duk na kosa inji dalilin kiran da Sultan ke mani, tayi banza damu har muka karasa gurin ba bakinta cikin hirarmu, ya dan gyara parkin muka sauka duka, Seemah tayi gaba abinta bata tsaya jiranmu ba, baby! Na dan dakata ya cimani yana fadin me mukazo yi? Ni ma daddy i have no idea inaga batun lawyana zai gaya mani, akwai damuwa ko? Na dan yi yake ina girgiza kaina, come on gaya mani mecece damuwarki? Ban sani ba nima daddy muje kawai my heart is beating Seemah ta 6ace mana, ya riko hannuna muka nufi inda mukaga mutane sunata harkokin gabansu, ga securities ga haduwa da gurin yayi yasha gyara ba na wasa ba, zuciyata na jita wasai ni kam ina kaunar inga an kawaita abu, muna nan tsaye wani gaye ya nufomu da fara’ar sa yana fadin gud ‘yar halak kin cika alkawari, sai a lokacin na ganeshi, daddy meet Muhanmad Sultan, Ya Muhammad ga daddynah, suka gaisa ya dada yi masa bayanin ko shi waye da MATSAYINSA a gurin sultan din, yayi mana sit duk muka zauna ni kam ina dan waiwaigawa don ganin inda zan ganshi, amma ai yace in same shi a nan, daga inda muke zaune ina hango abubuwan da ke dada tabbatar da zargina, Suhaila na ganeta itace wace Sa’adah ta mani rakiya da naje gidansu ta gayan magana gudun kar in mayar, to wa ye angwon nata? Seemah na hanga daga dan nesa kadan tana amsa waya (business centre manya), na kau da kaina ina kallon agogo sai ga sallamar sa ya dawo yana fadin daddy ka bani aronta please, ba matsala cewarsa na mike na rufa masa baya, muka dan bar gurin inaji MC na fadin a daga wa ango kafa uzuri ne ya tsai da shi, to ko Muhammad Sultan ne? Muka tsaya a gefan wata mota inda ke da karancin jama’a, Hameedah me tsakaninki da Muhsin? Muhsin kuma? Na yi masa tambayar banbarakwai, kwa
kwalwata tana kokarin hada sentence don am speechless, na soma stammering, ban….hmmm…fahimceka ba! Natsu kinga ba tara zaki biya ba, na dan yi dariya ina fadin to ai kune kun iya kure mutum da tambayoyi, lawyer
na ne, hmmm! ai nasan nakine bance nawa ne ba, wannan alakar ba ta har abada bace watarana zaki daina furta hakan gareshi idan na karfan ya bayyana, hakane amma ni nasan kaunarmu daga Allah ne bazan iya fassara maka alakarmu ba ka gane? Ban jira ya bada amsa ba naci gaba da cewa shi din yanada girma, kima, da darajar da har kasa ta rufen idanu bazan mance halarcin sa gareni ba, ko bayan nayi aure i would try 2 keep contact with his family, aure baby? Sai a yanzun ya samu abin cewa, aure? Zan yi amintaka da future wife dinshi ina ganin……enough ya fadi yana daga mani hannu yarinyar da dan karan wayo take, duk ta gama tsarashi, idan har kina tunanin two different families shin ina kaunarku da kike ikirari? Nayi ajiyar rai gami da cewa its natural amma…..hasken motar da aka dallaro mana ya katsen hanzari, duk muka tsaya tamkar wayanda aka dasa, amon muryarsa wanda ko a ina na ji nasan mamallakinsa shi ya katse shirun, ya kashe motar ya fito kai tsaye gurinmu yake nufowa, baby ya fadi a sanyaye daga dan nesa kadan yana kare mani kallo, lawyernah! Hmmm! Me ya sameka? Me kika gani? Ka canza agogo sarkin aiki baka hutawa ne ko? Yanzun ma nasan daga aikin ka fito ko? Ya dan yi tattaki ya karaso garemu yana ajiyar rai, duk sai naji na damu ban ta6a ganinsa haka ba, na tsira masa idanu ina tuna can baya, shima ni yake kallo Say something kaga tafiya zamuyi nayi mamakin da aka amincewa zuwana gurin nan ma a wannan lokacin,ya zuba hannayensa 2 a aljihun sa yana son cewa wani abu daidai sanda wayar daddy ta shigo mani, ki zo ina jira,to kawai nace na kife wayar sannan najuya ina fadin bari inzo…
Ya dafa masa kafada yana kokarin kwantar masa da hankali, yarinyar tana sonka MAN, haka tace maka? Yayi tambayar da zakuwa, no relax amma na fahimci batasan alkibilarta bane fakat, ya fesar da huci daga bakinsa yana fadin ban da hope Sultan ni nasan gawata mama take bukata, cool ka duba kaga yanda ta nuna damuwarta don kawai ka sukurkuce, wannan ma matsayi ka taka wanda ya sanya nake ganin kana da rabo ko a nan gaba ne zakace na gaya maka, daddy daya taho da kaya niki niki ke fadin kai masa, me wannan? Kai masa nace ban son surutu, na sunkuci katuwar kwalin da bazance ga abin dake cikinsaba mai adon gift ya sha kyalkyale ba kadan ba, kan motarsa na ajiye Sultan ya bude boot ya sanyata ciki, ko baka da lafiya ne? Ya girgiza mani kai gami da cewa muje in gaida daddyn naki, duk muka bar gurin Sultan yayi gaba ni dashi muka jero inai masa magiyar ya fadi matsalarsa, ta cikin taron muka ratso tamkar daga sama naji tana magana da kakausar murya wanda ya razana kusan kowa na gurin, karamar ‘yar iska bazaki bar min mijina ba Hameedah? na dan dubeshi a razane furucinta ya tarwatsa mini lissafi, hakane Muhsin yau ne aurenka? yayi tsit nikam na bar masa gurin fuuu inajinsa yana kwalamani kira sannan ya rufa mani baya, naje na jingina da motarmu ina haki tamkar wace taci gudu ta koshi, baby listen zan miki bayani, ni ba abin da zaka ce min tunda baka daukeni da muhimmanci ba kake 6oye mani abin daya shafeka, kar kimin kuka don Allah kinga zaki tara mana jama’a a…
Razanan nan kara mukaji ya gauraye gurin, duk muka waiwaya Seemah ce tsaye tana huci amarya Suhaila kuma yashe a kasa kan tarwatsatsan kwalabe a kasa taji rauni a kafarta yana fitar da jini, ke har kin isa don albarkacin mijinki anzo auranki sai ki nemi ki cutar damu? Seemah! Me haka? Gata nan ‘yar kwaya kwalba ta fasa ta taho zata caka maki, matsiyaciya me kike ji dashi? Suhaila ke fadin Muhsin kana kallo bazaka dau mataki ba ko? Nikam da sauri na kira wayar daddy yazo mu tafi gida abin ya isheni ga mutane har sun soma yayata batun, nice ajinki ta fadi tana kokarin tashi duk jini ya 6ata jikinta, na janye Seemah tana ruwan bala’i muka bar gurin a haka taron ya watse, karo na 2 kenan da Seemah zata taimaka mini a bainar jama’a, wannan yasa naji sanyi a raina dan’uwa dadi gareshi ,da azama muka shige mota har daddy ya ja muka soma fita daga gurin Seemah na bala’i, ni aka ta6o ya isa hakan nan kalli fa yanda jama’a suke kokarin bin bayanmu? Na fadi ina kallon glass din baya daidai inda muka baro dandazon mutane sun kewaye amaryar ana ririketa, munafuka ‘yar hana ruwa gudu da kin barni na fasa bakin nan da bashi da manners sam ta fadi tana hararata, abin na ci mata rai daddy kam idanu ya zuba mana, kun dai 6ata masu shiri ko? Have you ever seen a fighting bride? Daddy we are sorry na fadi a sanyaye, am not the victim here so I don’t deserve it cewarsa yana kokarin shan kwana, ita kam Seemah tunaninta naga Muhsin, bai yuwa inyi competing da balagaza he will be mine ta ayyana a rainta, i will do anything to get you, samun opportunity nayi nayi amfani dashi naci ubanta, ya za’ayi ta auri wanda na kallafa raina kansa kuma ta zauna lafiya? Ina zan samo high personality wanda ya jiku da qualities dinsa especially kudi? MAI “G” WILL BE A CHOICE, tayi murmuring tana smiling, Daddy dama kasan zai yi aure? ta jefa masa wannan tambayar ni kam na mayar da hankali don jin amsarsa, Seemah me naki a ciki? Daddy gaya min, ta fadi tana kallonsa ta madubin driver, daddy ina ‘yarka zaka 6oye mani? He didn’t even send IV, Its ok na fadi ina kokarin kawar da batun, yaushe Bilal zai dawo na tambayesa cike da damuwa ina goge hawayen fuskata,Seemah ta fashe da dariya irin na keta tanayi tana bubuga kafa tamkar mugyanbo, sannan ta kara da cewa mai aikinki hammy? Hahaha, yes yes yes baki san ciwon kanki ba, ni kam yanzun sai mai G (mamallakin Golding enterprises kamfanin da tayi suna da reshe kala kala a fadin duniya) mai G shine Waheed El-Mustapha dan naija da tawraruwarsa ke haskawa, na kalleta shekeke ina jimamin lafuzanta, ganin dariyar tayi yawa ya sanyani bibigeta ina fadin ke lafiyar ki kuwa?daddy diyarka tayi gamo, ke ras nake, ko? A gidan uban wa kika san mai G? mutumin da bashi da lokacin kansa bale na Seemah, exactly ba irin Bilal bane so cheap and downgraded,
Seemah always aims higher kin gane? Ai dama tun ba yau ba nasan kina da jinnu kuma you are not balanced Seemah, kutumar uba! Repeat what that…
Cikin bacin rai daddy ke fadin kar in kara jin muryar dayanku ya bada umarni kai tsaye yana nuna alamun mun kai shi bango, don zai yi aure sai ya nemi izininki? Rainin hankali kai, daidai lokacin muka sauka gaba dayanmu Seemah ta fashe da dariya yayin da ta bi hanyar dakinta tana kwasar dariya, na zuba kan kujera ina ajiyar zuciya kwanyata tana haskomin mummunar daren yau, ni kai wa haka? Yarda da amana laifine? Me yasa nayi sabo da kai? Ina kallon wayarsa ta shigo mani har ta tsinke ban da niyyar dagawa, hmmm uban ango ko aminin ango? Cewar mummy, ya dai? Rahma yaranki zasu haukata mutum, tayi ‘yar dariyar kissa tana sinne kai to wa suka kwaso? Yaja ‘yar guntuwar tsaki sannan ya wuceta kai tsaye dakinsa ya nufa, ina nan zaune ina jinsu ta dan waiwayo gareni gami da cewa baby ya dai? Mummy kaina ciwo, ta ware hannayenta tana kallona, na karasa na rungumeta ta dan dafa wuyana sannan ta kwala wa Seemah kira,tana can har ta kwanta barci cikin short nighty dinta, ta wani zun6uro baki gami da cewa gani, oya dauko magani a kitchen yana nan dazun na ajiyeshi kan dish washer, wai ke hammy me na ki na sha ma wani panadol a ciwon kan daba naki ba? Muhsin ne ko? Cikin rauni nace mummy please, OK sorry na daina tambayar, Mummy ba wani gulmane cewar Seemah dake tsaye, Zaki dauko ko surutu zaki tsaya? ta wuce simi simi shakar mummy a gurinta tamkar taga mutuwarta, na sha maganin sannan ta gyara mani kwanciya kan 3 sitter tana dan yi min hirar jan hankali, nace yanzun ina ne ke maki ciwo? kwalla suka zubo min da sauri na rungumeta ina jin kadaici cikin raina, mummy dakin nan yayi mani girma pls ki kwana a nan, zuciyata tana min yaji, mummy pls ki kira min Bilal inji yaushe zai dawo, na sanya kuka mai rauni bata hanani ba, sai da nayi mai isata ta dago ha6ata tana nazarina, idanunta kaina kur tana tunani can naji tace kinason Bilal ko? Na gyada mata kai alamun eh, amma zuciyarki ta damu da Muhsin ko? Hakane mummy ki min addu’a kinji aminiyata kice Allah ya yaye mani,a haka daddy ya samemu, ya kunna TV dakin ya dan sauya jefi jefi yake dan kallona da alama hakan na ta6a zuciyarsa amma bai ce komai ba, daren ranar kwanan zaune mukayi gaba daya sai tsakar dare gaba daya har Seemah mummy ta taso mukayi tahajjud sannan muka ci gaba da harkokin mu, Seemah ce ma ta koma barcin ni kam kan cinyar mummy na dora kaina ita da daddy suna hira ni kam hankalina baya tare dani, ko me nawa? Lalli Seemah tayi daidai da tace hawayenta mai tsada ne bazata 6ata lokacinta kan da namiji ba, da asubane daddy ya barmu a nan mukayi sallar mu, yaje masallaci sai da gari yayi haske sannan ya samemu muna dan harkokinmu, baby ki bar damuwa kinji? Na dan kalleshi ina murmushi da gefan kumatu daya tamkar dole, kin rame ‘yar gidan madam Zarah, tashi muje kiyi break ban son ana maida hannun agogo baya Ok? Na dan gyada kaina ina yake, daddy kamin izini in bar gidan nan, mummy ta kalleshi ta gyada masa kai kawai alamun ya amince min, ina zaki baby ke ba ‘yan uwa ba? Gurin madam Zarah daddy inajin kewa mai yawa zan bar gida kila in daidaita kaina, mummy me yasa nakejin haka? Sabone with time zaki ware kinji? Na gyada mata kai gami da mikewa ba jimawa mummy da kanta ta shigo ta dan shishirya mani kayana cikin ‘yar karamar trolley bag dina, yaushe zaki dawo? Bani da za6i na fadi ina sanya takalmana, ita da kanta tayi wa matar waya tana can tana zuba idon ganina, Seemah na raka6e a jikin taga tana daga mani hannu, dan zaman da mukayi mun soma fahimtar juna duk da dai ba abin daya sauya a zamantakewar mu, nima na daga mata daddyna ne ya kaini gidan, she’s dam rich cewar daddy yana karewa mansion dinta kallo, yeah , she’s an empress in her empire, come here cewarsa yana bude mani hannayensa, na karasa da sauri muka rungume juna, peck ya mani a goshi gami da cewa I will miss you, yaushe zaki dawo? Na langabe kai ina murmushi yayin da kwalla suka cika mani idanu, it will take a while, love you daddy, love you too baby, ya rakani har cikin gidan, ai kam taji dadin ganina, sun dan taba hira sannan ya wuce , ina daga masa hannu, sai na dan ji daban dama burina in nisanci gida…
Wajan ya cika da jama’a sun sanyasu a tsakiya ga Suhailar nata dura ashar jama’a sun soma watsewa duk wanda yasan mutuncin kansa yana neman hanyar gidansu, ko kamin ya ankare har Mama ta bayyana tana zazaga masa fada wai shi ya kawo Hameedah ance mata tun safe yake tare da ita, ni zakawa haka dan nan? Anya kuwa kana neman gamawa da duniya lafiya? Yi hakuri Mama cewar Muhammad Sultan duk wannan bai taso ba, muji da marainiya ‘yar gata tukunna wannan jinin dake zuba ayi masa ayah, uhum dan albarka baka yi sa’an aboki ba sam wannan son ransa kawai ya sani, ya taimaka masa aka tafi kaita asibiti gudun jarabar Mama dole ya bisu ita bata raina abin fada, a can din ma bai tsira ba ana mata dreesing sai raki take tana cakumo tie dinsa duk sai yaji duniyar ma ta isheshi, ko da baby taki daga masa waya sai damuwar tafi ta baya yawa, Sa’adah na tare dashi tana karfafa masa gwiwa yayin da Sultan ya kasance mai zirga zirga kan lafiyar Suhailar, shi kam yama rasa abin dake masa dadi,
ranar sai da aka bata gado suka 6ige da kwanan zaune, amarya tayi barci cike da annashuwa, sanda gari ya waye ma da shi ta soma yin tozali fuskarta dauke da murmushi take kallonsa yayin da zuciyarta ke kitsima mata tuggun da zatai masa, manufarta ta rabashi da kowa, tasamu kansa, ta mori dukiyarsa sannan daga baya ta mallake duk wani abin daya mallaka, dole in fara da shegiya Hameedah yarinya karama mai kwanyan tsiya, Mama ce ta turo kofa da sallama, fuskarta wasai sanda taga ta a farka, burinta Muhsin ya riketa da amana, ya kyautata mata su rike juna su hayaiyafa don debe mata kewan maraicin dake tattare da ita, da yake ‘yar danuwanta ne kuma ita kenan iyayen sun rasu sun barta a hannun Mama, shi ya sanya take kokarin ganin an hada zumunci na har abada don tabbatar da lafiyar Suhaila da farin cikinta, kai! Ta daka masa tsawa tana fadin tashi maza kaje gida ka debo mata kayan sakawa dana amfani, Mama anjima fa za’a sallame ta, na sani dole dai ta kimtsa daga nan ko dan nema? Ba yanda ya iya haka ya mike ya bar gurin zuciyarsa tana suya Suhaila ba irin macen da ake shagwa6awa bace yaushe Mama zata fahiminci hakan? Kwakwalwar sa ta cunkushe tamkar ya kashe kansa don takaici, ga rashin barci, damuwa, zulumi, jimami kai komai ma ya dameshi…
Ta mike tana kewaye gurin duk a kokarinta na son warware kulaiyar da take shiryawa kanta, dole in yi wani abu ta furta a hankali, kai ta wani hanya zan hadu da mai “G”(mai golden enterprises)? Ta kalli kanta da kyau tana fadin ni matar babban mutum ce sam ban dace da gajari gajari ba, wata zuciyar tace janyo Hammy a jiki tana da farin jini da saurin shiga rai, bazata rasa abin yi kan hakan ba, ta mike tamkar an tsikareta wayarta ta lalubo ta kira mutuniyar tata, twinny ta fadi cikin yanayin damuwa, kin tafi kin barni cikin kewa mai yawa, shine koki gayyace ni muje tare? Ok see you soon cike da nishadi suke hira tamkar ba sune masu dambe ba a lokutan can baya…