MATSAYINAH COMPLTE NOVELNOVELS

MATSAYINAH COMPLTE NOVEL

[5/16, 3:10 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR( UMMU FARHANAH)…
19…
Wayar rike hannuna ina tunano abubuwa da dama da suka gilma a tsakaninmu, Seemah ce kuwa? She sounds different, wata zuciyar ta raya mani cewa kila ta sauya ra’ayi ne, i cant trust her again, she’s up to something, kin gama kimtsawa? Muryar Madam Zarah ne da azamata na zari gyalen kayan jikina ina fadin am coming, ni har na sha’afa na ma manta cewa fita zamuyi, ta rufe gidan sannan muka shiga mota ta tayar muka dau hanya, yau kwanana daya amma nakan yi mamakin saukin da rayuwarta ke dashi,a yanda na santa a can baya ban zaci a muhallinta tafi kowa saukin kai da iya muamala ba, gidanta manssion with fleet of cars, living a glamarous life, komai nata is classic irin rayuwar da Seemah ke hange kenan na sani, Madam Zarah baturiyace, rayuwarya a tsare take, she works with time, duk da wadan nan abubuwan data mallaka bata da mai girki, sai dai mai shara saboda girman gidan sai mai gadi, kaya kam dry cleaner take kaiwa saboda yanayin aikinta, balle kuma yanzun naga kullum hutu take komai na duniya ya sire mata, wannan ya sanya har nake ganin cewa ni HAMEEDAH ashe bani da wata matsala sam, mecece rayuwar? Takance mani life is too short to grief over nothing, baby you are too young to worry like this, Na dau wa kaina alkawarin sakin jiki da ita muyi sabo don kawar mata da damuwa, abuja muka zazzaga tana nuna mani guraren da ban ta6a zuwa ba, mune har Ladi kwali art centre dayake ma’abociyar art works ce, dakinta ma haka naga shirgi da tarkacen art iri iri, ma’abociyar zane ce sosai, she finds happiness in creativity da makamantarsu, mun jima a gurin tana min bayanai kan abubuwan da suka zame mani sabo, mukaje shan ice cream a nan nayita tuna Muhsin yasan baby da lagonta sosai, har naji hakan na neman 6ata mani sabon rayuwar da na tsinci kaina ciki, har muka bar gurin zuciyata tana hasko min lokutan da muke zuwa irin guraren ya cikani da ice cream, lallai kam you would never miss the well until the water runs dry, muna tafe ta dan kalloni tana fadin wani school zaki yi ne anmata? Na danyi murmushi gami da cewa no idea, nan ma shi din ne ya fado mani, ko ina batun school dina ya kwana? Taci gaba da cewa kinga ni Brandise Jewish University nayi, a can na karanci harkan kasuwanci, ke kam you are smart Hammy anya ba ‘yar jarida ko lawyer za’ayi ba? Lawyana na tuna, na dan murmusa ina gyada kaina, ta soma bani tarihin ta a sch wani zubin inyi dariya wani lokacin in dan tayata jimami, shekaru 2 ta baiwa mummyna, kusan 33 take, yet she looks very elegant, a haka muka karasa gidan nan, dinma labarin ya tsawaita har banson ya kare, Hammy kar kiyi harin dukiya da burin arziki irin nawa a rayuwar nan, ba komai cikinsa sai wahala dora wa kai nauyi mai girma da tashin hankali mara misaltuwa, kiyi amfani da kuruciyarki wisely, ki rike mutuncinki baby a haka zaki samu miji daya tamkar da dubu, ni kinga na riga nayi uwar watsi da tawa rayuwar? Na zalunci kaina na zagi musulunci da dabi’iata, yanzun me hakan ya haifar?na dauka birgewace, wayewane ….ta fashe da kuka mai tsima rai nima ina tayata, i want a child i would call my own but….. Kuka ya kwace mata, nima na ci gaba da tayata, min day tsawon wani lokaci sannan taci gaba da cewa after my first baby i had my womb removed, jikina yayi sanyi sosai, zan so Seemah taji wannan hirar, may be it will change her view about life, daga baya dai muka hakura don kanmu na rarrasheta, na bata shawar wari har ta nuna jin dadinta garesu, a lokacin nayiwa Bilal text kan zakkah da adadin abin data mallaka ya turo mani da amsa cewa bai sani ba amma zai tambayo min, wucewar mintina 10 sakonsa suka shigo mana da amsar gamsashiya muka bazama gurin zakkah don tsarkake dukiyarta, wannan kenan ….
Yau kam duk mun tashi da nishadi zuciyoyinmu wasai, wannan dalilin nema ya sanya muka shirya tafiya don jindadi kawai, tayi mana booking a airport dinta onlyn washegari sai lagos, can dinma guess wat? Muna sauka na tuna da Muhsin zuciyata tana raya mani hirar lagos da Muhammad Sultan, why is he always crossing my mind? na rika kawarwa ina son in ganni tamkar Hameedahar can baya kafin shigowarsa cikin rayuwata, a haka muka nufi gidan wata kawarta , itama ‘yar kasuwace mai harkar gwalagwalai, da fara’a ta karbemu, tana shirin fita don a bakin kofa muka sameta zata rufe gidan, da kamar mu jirata a gidan tace dadewa zatayi, wannan ne ma ya sanya Madam Zarah cewa mu shiga motar kawai taje damu, i want mah baby to explore the city, nayi murmushi, dauko gwala gwalai zatayi a golden enterprises,motar ma abar kalloce, ta shige gidan gaba muna tafe suna hira ni a gidan baya nake ina sauraronsu sama sama nafi mayar da hankali kan game din wayata da nake bugawa candy crush, can ta mikomi shany da tarkacan kayan dadi, baby ci wannan kafin mukoma gidan, na kar6a ina godiya, mu uku muka shiga kampanin ni kallo naje su kam kaya suke sara sai shigya shige nake ina ta6eta6e, a very big place with charming looks, har mukazo tafiya na kar6i trolley basket daya ina tayasu turawa, dab da zamu bar cashier unit motar ta ratso cikin harabar gurin, ba jimawa na ciki ya bayyana kansa cikin takun kasaita, sai mai “G” cewar l
Aunty Laura(kawar Madam), ina ka shige ne haka muna ta neman kaya ance ba’a dauko ba? Wace wannan kaman Zarah? Goodness ina kika shige all this years? Cewarsa cikin American accent yayin da yake zare white glass dinsa, tayi murmushi kawai gami da cewa ya bayan school? Abdulwaheed life have really change you, yeah, fyn ‘yar manya so wannan daughtar mu ce kenan? Ya fadi yana kare mani kallo, na kau da kaina ina dadanna waya don banson kallo, baby ga class mate dina Waheed el-Mustapha, na dan yi yake sannan na gyada kai alaman gaisuwa ina daga masu hannu, naga alama dan gayu ne bai bukatar a tsugunna gaidashi, sannan na bar masu gurin kai tsaye mota na nufa ina fadin na gaji da yawa, ok gamu nan muma cewan Aunty Laura, sun dan jima suna hira dashi sannan sukazo zamu tafi, Baby ga naki ta fadi daidai sanda ta jeho min ledoji masu tambarin gurin G enterprise ,ina alajabi su wadannan kudi baya masu wuyan kissa har na rasa abin cewa, yana nan tsaye a inda muka barshi yana aikin daga mana hannu, taja mukayi waje, oh na manta Waheed ne ya ce a baki yaga baki dauki komai ba, aunty kuma….shiiiiii ya isa kyautace kawai ai ko Zarah? Suka kyalkyale da dariya sannan duka suka shareni suna hirar wasu kayayyaki, Laurah kwanaki uku zamu maki mu dan ga lag tukun saboda daga nan zamu leka Kaduna sannan mu koma inda muka fito, kai Zarah ko da yake na gode kin kyauta tunda kin raya zumunci, nayi lamo a bayan sit ina kallonsu, Aunty Zarah tah! Uhm babyna mai manyan hali ya akayi? Zamu beach ko? Ba matsala zan kaiki, nayi dan murmushi tana da kirki abinta, na dan bude ledojin ina kallon abin mamaki ina zan kai wannan? Kai wa twinny mana cewar madam Zarah, kutumar na furta a razane bakina na rawa wanda ya haddasa mani rudewa da gaza furta wata kalmar, na shiga uku auzubillahi, a sanyaye na ke fadin me zance wa Seemah? Duk suka zuba mani idanu daidai lokacin tayi parking a farfajiyar gidanta, zo nan Hammy me yasa kike haka ne? A hankai na sauko hannuna cikin nata muna takawa zuwa cikin gidan, nice silar 6acin ran Seemah takance ta tsaneni komai Hameedah, tun muna yara,
Litsen, kaddarar kice ko ta Allah? Ke like janyo mutanan da tsiya ko su suke manner maki? me na damun kanki? Itama ta koyi dabiunki ta gani idan bata zama abarso ga kowa ba, oya muje ciki ki huta anjima akwai outing ok? Abincin ma yafita na danyi sama sama don a koshe nake ba jimawa barcin gajiya ta saukarmin, sai yamma lis muka kimtsa mun dan zazaga muka dawo da kayan kwalam (mummy kance a nan nafi auki)…
Kirikiri mama ta maidashi bawan Suhaila, da yamma ta samu sallama Mama ma cewa tayi gida za’a maidata sai ta warke sumul zata tare, bakin ciki kamar ya shakota, don kuwa wahalar bata yanke masa ba sai ta tare tunda Mama zata kasa ta tsare sai ya aikata sa6anin ra’ayinsa ne, ita kuwa Suhailar ta samu yanda takeso sai wani nanarkewa take tana zuba tsiyarta, ba dama ko masallaci yaje yanzun nan zata ce tana bukatar kaza Mama tace me yasa ya fita shi mai iyali, yana gyara tie ta leko tana fadin amma kasan dai ban warkeba ko? Yayi mata banza yau za’a yita don sun riga sun kureshi kiris yake jira tunda daga ita har Maman matsalarsu kawai suke dubawa, ta sahidawa Mama yana kokarin fita ta sawo kai tana fadin ban isa da kai ba kenan? Kasan dai yau ya kamata taje ganin likita ko? Na sani ya fadi kai tsaye fuskar nan babu walwala, haba Mama ki rika adalci a tsakaninmu don Allah, kali fa bamu tare ba amma yarinyar nan ta gama rainani, sai kace kaina aka fara ajiye iyali?a matsayina na namiji bani da iko kanta? An danne nawa hakin an takurani sai kace ni na rako maza duniya? Ta kalleshi shekeke tana jinjina lamuran, haka kace? Ya sada kansa kasa yana sauraronta, h
Hameedah ce dai ko? Ga fili ga maidoki zanga yace za’ayi ka sameta ina raye, ni na tafi, ya fadi ya sanya kai ya fice tana rakashi da harara, ya taxa mota kai tsaye gurin baby ya nufa, da ita yaci karo a lanbun gidan tana jin music da alama nishadi takeji ita kadai, handsome ta furta gami da tsira masa idanu, shigarta cikin english gown iya cinya , coffee brown mai tsantsi ,ta yi many an braids guda biyu aka jera masu ribbons manya ,ko wanne a barin kafadarta, she looks very pretty, hannun rike da juice tana sipping, ganinsa ne ya sanyata saurin mikewa cikin farin ciki ta karasa gareshi, shi kam ya tsaya gami da tsira mata idanu, ta tsaya dab dashi tana fadin nice meeting you, its a pleasure Seemah where is she? Who? Baby mana, duk da ya fahimci cewa seemah ce amma yaji dadin ganinta sak baby amma shi a kowani yanayi ya sameta yana tantance su don ya san banbancinsu, kina hutawa ina mutan gidan ne? Mama taje clinic daddy ne dai a sit roomromm muje in rakaka, no yi zamanki kar in takuraki, yayi mamaki kwarai da bata aibata baby ba, shi kam itace silar zuwansa gidan, sun gaisa daddy kam a fakaice yake kare masa kallo to rashin lfy yayi ko me? Mushin kaine haka? Nine daddy, dakin yayi tsit kowa da abin da yake sakawa a rainsa, can dai ya daure yace ina baby da mummyne? Babynka ta kaura gidan madam Zarah.. muryar mummy ce ta katse su tana sallama, ah ah muhsin! Ka daina neman mu laifi mukayi? Yayi murmushi yana fadin uzurine mummy Rahma, to Allah ya kiyaye gaba, be wani jima ba ya bar gidan zuciyarsa da tunaninsa naga baby, kai tsaye gidanta ya nufa amma kash! Bata nan ya zauna a bakin gate dinta yana tunanin abin yi… Toh, ‘Yan uwa ku bashi shawara.
Bilal Ismail Kurfi wanda akafi sani da direban Hameedah asali dan jihar Katsina ne, babban custom din da ya zama zakaran gwajin dafi a fagyan aikinsa, da daya tamkar da dubu a gurin iyayensa, alamura da yawa sun faru, ciki har da ayyukan da kan hadashi da Alhaji Abdullahi Buba, mazaje biyun sun san junansu a matsayin custom da shahararan Dan kasuwa, yauma Bilal ne kan duty a bakin border sanda kayan Alhaji Abdullahi Buba suka iso kasar, ya kalli motar data wuce da sanfarin english gold yana jinjina kansa, sannan ya kira wayar daddy don tabbatar da cewa kayan sun iso kafin ya bar kasar, shi kansa ya gaji zuciyarsa da idaniyarsa na kwadayin ganin Hameedah, bugu daya daddyn ya daga wayar yana fadin Bilal naga aiki yayi kyau me ake ciki? Yayi ajiyar zuciya gami da cewa an gama Allaah’s willing gani ma a bakin boder amma gobe zan dawo Abj, Bilal kaine ko idanunane ke mani gizo? Yayi ‘yar dariya gami da cewa nine, but why? You are more than just been a driver, daddy akawi magana amma sai na iso, Ok na gode kwarai, sukayi sallama ya katse layin, burinsa yana isa kawai yayi ma daddy batun Hameedah daga nan ma zai hada lefansa kawai ya huta da hutun jaki da kaya…
Yanda ruwan beach din ke gudu da kyalli shi yafi daukan hankalina, sanye nake cikin riga da wando masu saukin nauyi amma basu kama min jiki ba, cotton amma sun kar6eni inji Madam Zarah, Royal blue masu stones, light make up nayi kawai don ban cika kwaliyya ba dama, aunty Laurace ta siya mani su jiya, na sanya hijab ‘yar karama daidai wuyana mai adon stones, mukayi zaman mu a nan tekun muna wasa da ruwa, wounderful indeed abin ya kayatar dani, Assalamualaikum muryar data kasance bakuwa a dodon kunnuwana shi naji dab damu, ban wani damu ba na tattare kafar wandona na doshi bakin beach din sosai ina fadin aunties please snapshot, ina can nishadi ya cikan zuciya har na gaji don kaina na mike ina karkade jikina, aikuwa waiwayowan da zanyi idanuna cikin nasa, hannunsa rike da camera yana ta daukana, na sha mur can na hangosu sun yi shimfida da alama picnic zamuyi aunty Laurah na aikin fiddo da kuloli a boot dinta Madam Zarah na tayata, Hameedah ko? Cewarsa yana kare mani kallo, yana sanye da designers na dolce and gabbana, na dauke kai cikin takaici, Ko kallonsa banyi ba nasan shine zai rura wutar data lafa tsakanina da Seemah, na karasa gurinsu ina fadin wash na gaji,Waheed bari muzo ka daukemu cewan Madam Zarah, haka kuwa akayi yayi mana kati 5 sannan aka rufe babin, ashe nan kukazo? Bari Waheed baby akwai son exploring, good ina fatan lag ya miki dadin zama? Ya jeho min tambaya yana murmushi, ba laifi itace amsar da na bashi kai tsaye, yes ai nasan tafi kauyanku kyau, har ban san sanda nace lag din shi yafi abj? Na tsira masa idanu ina bukatar amsa, kina da jane? Sosai ma, ok zan nuna maki evidence dina, yayi kyau ai, dariya sosai Madam Zarah keyi, waheed ba’a musu da baby fa, sai dai ka hakura ka janye wannan da kake gani akwai baki, kin manta shi hala cewan Laurah tana murmushi, Ya kalli aunty Zarah yana fadin yarinyar nan da na zaci bata magana ne amma ji fa don na tambayi kyauyansu ta sauya zani, duk suka tsintsire da dariya ni kam na ta6e baki ina kokarin zuba abinci a plate, kaganta nan bata da surutu sai zaro maganan tsiya, i seee ya ce yana kokarin juyawa, bari ina zuwa ya fadi sannan ya bar gurin, aunty kinga yanda ya rika daukata a hoto kuwa? Hmmmmm sarkin tsoro a hannuna ya kar6i camerar kina can bakin teku kina shirmanki baki sani ba, kwantar da hankalinki sai Muhsin ko? Na kya6e baki ni sam ban son ina tunashi sai inji duk wani farin ciki na ya yaye bakin ciki ya maye gurbinsa, Bilal dai, uhum yarinya fadi dai kike ko bashi dana tuwo? Na cusa kaina cikin cinyarta ina fadin daina fada yana da kokarin nema, tayi murmushi tana gyara mani hijab dina, oya to dago muci kar ya huce ko? Ga ice cream can na taho maki dasu, na dago kaina daidai lokacin na hangoshi kan doki mai kyan gaske yana jan linzami a hannu, dan hutu na ayyana a raina sannan na dau spoon, ita Seemah ina ta san Waheed? A branch dinsa na abj inda muke zuwa shoppin wasu lokutan, wani zuwa da mukayi suke rabon magazine dinsu muma aka bamu daya, a nan muka karanto abubuwan da bamu ta6aji ba game da rayuwarsa, tarihinsa, kasuwancinsa da dai sauransu,wai zai nuna mani proov ko? To me ban gani ba a lag din? Bari in kirashi ki tambayeshi mana, no na hakura, ranar tamkar bazamu koma gida ba haka mukayita bushasharmu…
Mummy a bakin gate tana kokarin bama mai gadi sallahu ta tsinkayi amon muryarsa yana kwararo sallama, hakan ne ya sanyata tsayawa har ya karaso gareta, sak dan kauye shigarsa cikin riga da wando farare ne na yadi amma daga gani zaki fahimci sunji wahala ne suka koma hakan, ga ba guga hannunsa dauke da buhu itama tasha ta6o tamkar an jehoshi, madam ya fadi yana dan risinawa, how i meet una? Tayi murmushi gami da cewa Bilal manya har an gama noman daminar? Ya nuna buhunsa gami da cewa gashi nan ma na kawo maku daga cikin abin da aka samu a gonata, mummy ta karba tana godiya,kayan marmari ne ciki.
MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
20…
Har yau mummy bata san matsayin Bilal da aikinsaba, a yanda ta daukeshi direban Hameedah ne, kuma yanzun da case ya kare zata sallameshi, in kuma yana son babynta da gaske tamkar yanda ta damu dashi toh ita da daddy zasu shawarta irin sana’ar da suke ganin zasu taimaka masa dashi, a haka take kallonsa yayin da shakuwa mai yawa da wani al’amari mara misaltuwa wanda zan iya danganta hakan da sabo ta kullu tsakaninsa da maigidan, ta dauka hakan ya farune saboda saukin kan mijinta…
Ya dade yana jaraba layinta amma da alama bata shiga ba, wucewan awanni da dama yana nan zaune har ya gaji don kansa ya mike yana zancan zuci, fatansa Allah yasa in ya kuma dawowa yayi sa’an ganinta, da wannan damuwar ya koma gida tamkar ya kifa haka yake jinsa, daga dan nesa kadan ya hangota a bakin gate da wani saurayi suna tsaye, Suhailace matar auransa da mutumin da bai shaidashi ba sai wangale masa baki take, abin ne ya daure masa kai shin wace iriyar rayuwa Mama ta za6a masane? Wucesu yayi ya barta gurin don bai ga amfanin tsayawa 6ata lokacinsa a gurinta ba, gidan babu kowa sai Mama itama tana dakinta don haka bata san wainar da ake toyawa ba, shi kam yasan aure tsakaninsa da Suhaila abu ne mai wuyan sha’ani, ga sa6anin ra’ayi wanda ya haifar da tazara mai yawa tsakanin su, they are not compatible kawai, bata kuma da natsuwar da zakayi mata magana ta saurareka, bata daukan gyara kuma ga jin kai da raini, sai hassada da izgilin tsiya, ya jefa rigarsa kan daya daga cikin kujerun dake tsakiyar katuwar palon yana jin zafi ga tarin damu, AC ya kunna yana tunain mafita, turo kofa tayi tana taunar gum wannan ne ya bashi daman kare mata kallo, ina kikaje? Ya tambayeta cikin 6acin rai, ina ka ganni dazun? Da izinin wa Suhaila? Wace ta san darajata(Mama), ta saki jiki kan kujerar gefansa tana waka, yunwa nakeji fa, ai kasan hanyar kitchen ni ban tambayeka inda kaje ba sai kai ka tsareni da tambayoyi, baka da adalci kan ka kawai ka sani macuci, ya dan kalleta tamkar ya mayar mata da martani ya dai shareta don bashi da wannan lokacin, kai tsaye kitchen ya nufa ya dafa ‘yar taliya tsabar yunwa da mai da yaji ya kwada garau garau hakan nan yaci tana kallonsa, ya nemi Sa’adah a waya sai jaraba yake masu ya za’ayi dukansu su bar gida babu abinci, naga dai Suhaila muka bari, ke kidaina lissafa wannan cikin mutane, tana jinsa ta ja uban tsaki ta fice, har ya ajiye wayar yana nazarinta, shi kam cikin mata bai san rukunin da zai ajiye Suhaila ba…
Yau kam da gaske mai “G” yake, karfe 10 na safe ya iso gidan, aunty ta sanyani shiryawa zamu fita tare, shi da kansa yake jan motar wata ‘yar madaidaiciya mai kyan gaske, morning, na fadi ina gyada kai don shi kam akeedar turawa gareshi, morning mah baby, Hameedah come in , turancinma tamkar wani baamurike, ya bude mani gidan gaba na fada,yau na yawo things pretty sai kin gaji don kanki kin amince cewa abj kauye ne, ok bismillah, na fadi babu shaku, ya tayar muka dau hanyar Festac daga nan sai victoria island, ke duk inda yayi tunanin haduwarsa a lag mun dan zazzaga, cikin nishadi ya waiwayo gareni yana fadin ya kika lag? Not bad either na fadi amma abj is ahead, musu preety naji, ya dau hanyar maidani gida holdup ta rikemu daidai sanda wata mota ta jera damu wace ta haifar mani ta faduwar gaba, Muhammad Sultan na gani shima ni yake kallo, na rasa dalilin jin faduwar gaba don na ganshi, yayi mani murmushi nima na mayar, la66ansa suka motsa na fahimci sannu yace, na kada kai kawai lokacin amininsa ne a raina, ko ina yake yanzun haka? Amaryarsa ta 6oyeshi, na fada kogin tunani har bansan an sakemu ba sai ji nayi yana fadin who was He? Na dan yi firgigit ina mayar da numfashi tattare da damuwa, your guy? Yes kawai na bashi amsa bazan iya dogon jawabi ba, daz nice amma baki ta6a gaya mani ba, daz my privacy, kin kyauta ai, da alama rainsa ya dan sosu amma ya zan masa? Mutum da nake fatan zumuncinmu ta kare a lag ina zan kai shi? What was he expecting? Daga ganin shi sai in soma zuba? Na sauka a sanyaye ina jan kafa zuciyata cike da jimamin rashin wayarsa, shi mutum ne wanda bana fatan zumuncin mu tayi rauni balle yankewa saboda abubuwa da dama, nayi mamakin yanda yayi saurin yakiceni daga cikin rayuwarsa, na daukeshi ne matsayin yaya babba don bamu dashi, Allah ya gina shakuwa da wani babban alamari a tsakanin zukatanmu, ina zan ganka in fada maka matsalolina ka ban shawara? Kai ne maganin kukana ka gaya mani ya zanyi da Bilal, ina sonsa ya soni shima, na fada cikin gidan da sauri ni nama manta da wani a wajan, ranar ganin Sultan ya tayar mani da abinda na birne cikin zuciyata, na soma neman wayata sai a lokacin ma na tuna cewa tana abj, na barta a can gidan aunty Zarah…Washegari da sassafe cikin ikon Allah damu jirgin safe ta daga zuwa Kd…
Sultan ka 6uya, ina nan Muhsin aiki ya min yawa, you sound different baka da lfy ne? Komai ma ya dameni wallahi ga baby ta 6oye mani na rasa inda zan sanya kaina, kana ina yanzun? Kofar gidan Madam Zarah inda akace ta koma, yayi kyau amma ni kam na ganta a Lag yanzun nan a gaban motar AbdulWaheed El mustapha(mai golden enterprises wanda akafi sani da Waheed),ya fesar da huci daga bakinsa yana fadin i can’t believe this is happening to me, serously? wallahi babynkace gara kazo tun wuri ka tsareta ayita ta kare kar kazo kana cizon dan yatsa, ya mike da azamarsa ya tada mota yana fadin ka shirya tarbata friend zan taho bazan iya bari sai gobe ba, gida kuma fa? Kai dai ka saurari zuwana nagode, duka katse wayar kowannansu na tunani, yaushe ta hadu da Waheed? A ina ta san shi ita ba ‘yar lag ba? Lallai Muhsin ya rikito… Ranar bai rintsa ba ya dau hanyar lag ji yake tamkar yayi tsuntsuwa ya ganshi a gabanta, da kanzar kanzar dinsa ya isa lag cikin dare wanda hakan ya sanyashi bin Sultan din gida in yaso washegari yaje su dinke 6arakarsu Daren ranar ma basu da wata hira sai ta Hameedah, yanzun ina zan ganta? Ya fadi yana safa da marwa, kwantar da hankalinka jiya ban kyalesu ba bayan an sakemu saida nabi bayansu naga gidan daya shiga da ita, har fitansa saida na gani ba gidansa bane ina kyautata zatin lift yayi mata, don babu wani hirar da suka tsaya yi ta shige cikin gidan, yayi dan murmushi yana fadin nagode Sultan… Wayewan gari da sassafe suka baro gidan yau madai holdup ce ta kwafsa masu, duk ya kagara minti daya 2 sai kiga ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa, Sultan baka sauri fa? Ya shareshi a haka suka isa gidan, suna kokarin parkin din motarsu Laurah ta dawo itama cikin motarta tana parking wannan ne yabasu daman saukowa don yi mata magana, bayan gaisuwa Sultan ne yayi mata dan gajeran bayanin da zata fahimta, to yanzun me abinyi? Ta fadi tana kallonsu gaba daya,kamar ya? Inji Muhsin, dawowata kenan daga rakiya don saida jirginsu ya tashi sannan na dawo, duk sukayi shiru gaba daya suna kallon kallo, amma dai ga numbarta nan, ina nufin Zarah don hammy ‘yar daru tace yajin aiki take ma wayarta, sukayi mata godiya sannan suka kama hanyar gida, ba yanda ya iya, sanda ya kira lambar har sun sauka babyn ta kwanta barcin gajiya, dole ya hakura zuwa wani lokaci…
Zaune suke su 2 cikin garden din gidan suna hirar kasuwancinsu da abubuwan da suka shige masu gaba, daddy ya gaza hakuri har sai ya fadi bukatarsa na zuwa direbanci gidansa, wannan ne ma ya sanyashi tambayarsa dalili, ya sadda kan sa kasa yana fadin bani da wata manufa, kuma bansan iyalinka bane ka min afuwa in na 6ata maka, Alhaji Abdullah ina kaunar diyarka Hameedah fatana in sameta a matsayin mata ta, ina da dalilan 6oye asalina, cikinsu kuwa har da son shakuwa da gudan jininka, ita nakeso fisabillahi, naji cewan daddy amma bani da daman yi mata dole sai abin datace tunda ita ke zaman auren ba ni ba, amma ka sa a ranka cewa ba abin da zaka nema in har ina iko dashi in hanaka…
Kaduna kam ba wani dadewa zamuyi ba don wasu takardu Madam Zarah ta kar6a a can muka soma shirin tafiya abj tunda dama can ba zama ne ya kai mu ba, mun biyo ta asibitin da aka yi rikici kanmu ta nuna mani gami da cewa har gobe tabon nan na nan daram a raina, aunty to me zai hanaki sake aure gaki mai kyau? Ta dan yi murmushi gami da cewa zan so hakan amma na bar wa Allah komai, ko auran nayi nasan babu batun baby? Muna ta hirar mu cikin mota tamkar kar mu rabu, naji tana fadin Subhanallah kinga na manta sakon ki, dazun kina barci Muhsin ya kirani, lauyana? Na fadi ina dafe kirjina, me yace maki? Na yi tambayar cikin zakuwa, yana son magana dake, ya damu dake yanzun dai ga wayar ki kirashi, na girgiza kai ina fadin ina son ganin sa nima i missed him so much, gara dai mu karasa din zan nemeshi, da kin kyauta wanda ke gaisheka kaima ka gaidashi… Zuciyata ta na kewarshi, wannan nema ya sanya muna isa da gudu nayi cikin gidan na lalubo wayata a cikin dakinta na kunna, ko hutawa bamuyi ba na kira layinsa tamkar jira yake ya daga da saurin baki ya ambaci baby! Ina lag yanzun haka mun nufo hanyar abj, zuciyata tayi sanyi kalau, ok amma zaka zo yau? Why not? Ina son muyi wata magana, nima haka akwai labari lauyana, Allah ya kawoka lfy ina jiranka a gidanmu, na katse layin cike da dokin son ganinsa, ni da Madam Zarah muka shirya sai gidanmu, tun kan mu sauka nake waro idanu so nake inga ta inda Bilal din zai 6illo in masa surprise, da gudunta ta daneni tana murna, sannan ta sakeni ta dirma mani dundu tana fadin sai yau kika tuna gida? Na ririko hannayenta ina fara’a, kai twinny irin wannan dukan ai sai bayan ya birma, daidai sanda IB da wata ‘yar yarinya mai kyau suka fito, muka gagaisa na dan ta6o kanta ina fadin wats ur name? Rihab cewarta, na tsirawa Seemah idanu,twiny ina aka samota? ‘yar da haj Ni’ima barawniya ta satoce bamu san asalintaba, ta rungumeni gami da cewa kema aunty See ce ko? Duk muka kwashe da dariya, Seemah kawai kika sani Rihab? Eh injita muka shige ciki don gaida masu gidan, ai kam na taba ganin yarinyar sanda nake zuwa bincike gidan, daidai lokacin daddy da Billal dina suka shigo cikin gidan da alama fita sukayi tare, Daddy ya shigo ya zauna yayin da abokin tafiyar nasa ya fice, na karasa da gudu na rungumeshi ina ‘yar shagwa6a ta, ya tsira mani idanu yana nazarina, ko tunanin me yake? You look better dear, how is Zarah? She’s fine tana sitting room, Kafin mummy tafito na fice don bin bayansa, a boot na iskeshi yana daga wasu takardu wayanda sahuna ya sanyashi saurin turesu gefe guda, me kakeyi haka? Noting cewarsa ya siga karkade boot din, ka dade da yawa ya mutan kauyen? Yayi murmushi yana fadin dama ai cirani na dawo yi, ni ban ta6a ganin wanda yanayin kauye kan gyarashi ba irinka, na dan zuba masa idanu ina kallo har bansan muna hada idanu ba, sautin kiran sunana cikin muryar mummy ita ta fargar damu, na juya da sauri ina fadin ina zuwa, na isa da azamata na durkushe a gabanta, sannan na kwantar da kaina kan cinyarta, babby kece haka? Sati daya ba shekara ba? Kai mummy baki haihu ba har yanzun? Da ce maki akayi haihuwar ice cream ne? Shi kadai kika sani ko? Duk suka kwashe da dariya sunai wa Madam godiya har ta mike zata tafi da alkawarin ziyarar juna muka rakata bakin gate, lokaci lokaci nakan duba agogona zuwa yanzuin na kagu inga isowansa ko me ya tsaidashi haka? Wata zuciyar tace lag fa baby ba kusa bace…
Dakina na shige ina dan kinkinmtsawa Rihab ta shigo tana fadin daddy na kira, na fice ban kawo komai a raina ba, mummy na zaune a gefan kujerar sa na dama yayin da Bilal ke raka6e a can kofar palo, na sha jinin jiki na na rasa dalili naji ni ba kuzari, na karasa na dan rage tsawona ina kallon kwayar idanun ta amma hakan bai sanyani fahimtar komai ba, gyaran murya ya soma alamace ta seriousness na dada shiga taitayina sosai ina sauraronsa, dakin tsit sai amon muryar daddy ingarimin namiji da ya karade kunnuwar mu muna sauraron sa, na dai fahimci bayanai ya tsaya yi kaina wayanda kwakwalwa ta suka gaza fahimta ko me yasa? Shin ina ya dosa?
Abu daya kawai na tsinta cikin kalamomin sa da suka kasance na karshe su suka tsayi mani a rai, yana bukatar auranki kwana kusa, na yi tsit ina kallon yatsuna zuciyata da kwakwalwa ta sun kasa sarrafa amsar bayarwa, kin yi shiru? Ya fadi don hankulan su na kaina, nayi murmushi kawai ko me hakan? Daidai sanda Bilal din ya sauke nanawyar ajiyar zuciya, shi kenan abinda yafi alheri Allah ya tabbatar mana Bilal, wannan ya bashi damar mikewa ya fice, na kasa tashi daga tsugunnon da nayi, yana 6acewa mummy ta dan muskuta tana fadin haba nawan why? Da akayi me? Karfin sa nake dubawa amma zaka sama mashi wata sana’a ko? Yayi murmushi kawai sannan ya kallo inda nake jeki baby dama maganar kenan, na mike ina sisine kai nayi waje, ban kai ga isa inda na dosa ba wata mota ta sanyo kai cikin gidan na tsaya cak ina kallonta, a sannu ya ajiyeta ya fito, na zuba masa eyez cikin mamakin lamura da dama, lawyana ka sauya why? Me ya sameka haka? Ya dan murmusa sannan ya shige yana mai cewa bari in kwashi gaisuwa tukunna, na tsaya nan ina jiran fitowarsa, ina hangyan ficewar sa ta kofan baya, Bilal kenan sarkin kishi, nayi wa kaina mazauni a gefan garden har ya gama ya fito hannayen sa cikin aljihun sa gentle man yanda na sansa yana nan, nutsuwar ma sai abinda ya karu, baby ‘yar lag, ni ba ‘yar kauye bace ziyara mukaje, shine ko sanarwa haba baby na cancanci hakan daga gareki? Afwan mutumi na dama na baka first time in my lyf in yi abu ta gaban kaina kar inyi involving dinka ciki saboda lamuran da suka shude a wancan lokacin, nayi zaton ba mai shiga cikin kyakyawar alakar da muka gina tsakanin mu? Nima haka naso amma nayi babban kuskure, i know i screwed up, dalili? Saboda abubuwa da dama ko don fansar raina na fitar da wanan idea din, but Alhamdulilah am now better, ya dan jingina da motarsa yana wasa da makulan, kin kyauta kenan? Kwarai kuwa, ina kaunarmu baby? Ina alkawarinmu lawyana? Na zaci nine mutum na farko da zai ji damuwarki, kwalla suka cika mani idanu ko na me? Ina fadin a can baya nima haka na yi zato amma kuma sai naga akasin hakan, Suhailarka na iya kawar dani a doron kasa wannan bawani abu bane a gareta, tana da gaskiyar ta auren ta kake a shariance me nawa MATSAYIN da zan shiga rayuwar ku? Kar kiyi min haka babbyna, kina da babban matsayi kaso mafi girma a nan, ya fadi yana nuna zuciyar sa Suhailar ma bata kamo kafarki ba, haka dai kace ita ce matar auranka wace Mama keso duniya ta shaida MATSAYINTA gareka, ni kuwa fa? Aminci ne mai karfi ko? Haka kika fassara abin?…
[5/16, 3:10 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH*
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
21…
Eh, baby you got it wrong, everything happened so fast, ina sonki sosai, na dade ina son ki but I lack the courage to admit it, na San kema kina sona, tsoron yanda zaki dauki lamarin shi ya hanani gaya maki, jikinane yayi sanyi sosai, nifa ban taba kawo aure a tsakaninmu ba, na ayyana hakan a raina ina tattaro nutsuwata, I like him, he will make a good home, na soma fadin ni kam na san ban iya auna iyakar kaunar da nake maka, duk sanda wani abu ya sameni kai ke fara fado mani a rai fatana in sameka in sanar da kai, ban san iyakan damuwar da zuciyata kan yi akanka ba in har kana cikin damuwa, ban san alakar zukatanmu fatana muci gaba da zumuncinmu kar wani abun da bai kai ya kawo ba ya gilma a tsakani, na fahimci a kanka nakan shiga cikin wani yanayi amma soyayya na aure naga Bilal, kayi mani uzuri bakin alkalami ya riga ya bushe bani da ikon mayar da hannun agogo baya, ni alkawarinsace tuni anyi ruwa kasa ta tsotse, mu kaddara haka Allah ya tsaro mana tamu rayuwar, bani da wata mafita da……enough ya fadi gami da daga mani hannu, good tunda haka kika zartar muryarsa tayi rauni sosai, ko kamin in ankare har ya fizgi motarsa da gudu ya bar mana gidan, na mike da sauri amma ina har ya fice da yake gate a bude yake, iyayena suka fito a guje daddy na fadin lfy? Mummy ta rikoni tana nazarina, da sauri na kwantar da kaina kan kafadarta sannan na rusa kuka ina jijiga, menene? Na kasa magana kwakwalwata tayi charji zuciyata tayi rauni, tunanina ya gushe kukan kawai nakeson yi yayin da idanuna suka daina hangyan komai, ta rikomani hannu muka shige cikin gidan, ta zaunar dani gami da ta6a wuyana, kinga banso zafafa lamura gashi har jikin ki ya sauya, Subhanallah! Baby you’re burning up already cewar daddy da hannunsa ke wuyana, Rahma kira doctor please, dear wannan ba na doctor bane, barni da ita kawai…
Mama ta kalleta gami da cewa har yanzun bai kiraki ba? Tana sharar kwalla ta ci gaba da cewa Wallahi kuwa mama ko hannuna bai ta6a rikewa ba, zai sameni a gidan nan ai ta fadi cikin 6acin rai tana cika tamkar zata fashe…
A daddafe ya karasa gida tamkar motar zata tashi sama tsabar tashin sense, ya karasa palon yana jan kafa ya saki jikinsa kan sofa yana ajiyar rai, hannunsa daya na dafe a ka, ji yake tamkar ana sukuwa a kan nasa, Bro Muhsin, cewar Sa’adah cikin damuwa, me ya sameka? Kira min likita dear, auta Husnah kawo mani ruwa pls, a wahale ya daga idanunsa yana kallon Mama dake watsa masa harara tamkar ta wankeshi da mari, Allah idan ka kureni zan tsine maka ta fadi tana tsima, haba Mama inji kanwar Sa’adah(mai bi mata) ummu Salama kenan, yi mani shiru munafukai kawai ai duk bakinku daya, ta tsaya masa a ka hannayenta 2 a kwankwasonta tana jijiga, ni ka wulakanta ko Muhsin? Ya ma kasa dago idanu ya kalleta shi kadai yasan abin da yake ji a kokon ransa… Na sada kaina kasa ina labarta mata farkon haduwata da lawyana zuwa yau, Mummy ta zuba mani idanu tana nazarin yanayina, kina addu’a kuwa babynah? Na gyada kai wani kukan ke neman su6uce mani, inayi na bata amsa muryata a raunane kwarai, muje to kisha magani ki kwanta zan san abin yi ok? Kema ki natsu ki sanar dani damuwarki fisabilillah, har yanzun ina da matsayin aminiyarki babynah? Yes mummy, ok zan ga abin da zan iya kinji? Yinin ranar Muhsin ya 6ata mani mood ba yanda na iya, na shirya tafiya gidan Madam Zarah don debo kayana da na bari a can tsabar sauri inzo inga gida ban daukosuba, Bilal ne ya kaini da kansa nayi masa alaman zan jima ya tafi kawai, na shiga gidan da sallama ina son ganin ta inda zata fito, ta riko hannuna tana murna zauna ki huta tukunna kawata, na dan jingina da kujerar muna hira har yamma sannan ita da kanta ta maidoni gida wannan ya sanyani na dan ji sanyi a raina, a gidan ma dagewa nayi ina gwada lambarsa amma na kasa samu wayarsa ma a kashe take……..
Ta shige cikin gidan fuuuu ita wai ya 6ata mata rai, Suhaila manya, tun Mama na masifa har ta gaji bata tsinke da lamuran ba saida ya zube a gurin ta rikice tana jijigashi, daidai sanda likitan nasa ya shigo dauke da kayan aikinsa, cikin lokaci kankani ya soma gabatar da aikinsa yana ta bincike da dai sauransu, Mama nata safa da marwa ta kwalawa Suhailan kira a matsayinta na matarsa amma shiru kikeji, tai kwanciyarta bata da matsala sam,
dakinsa aka kwantar dashi bayan ya sha treatment, barci yake sosai har wayewan gari bai farka ba Mama ta kasa barci wace ta kira kanta matarsa har 12 safe ba a ganta ba, ta shafa wa idanunta toka tana tsula tsiyarta, har Mama ta soma jin zafinta kuma, ta fito cikin yanayi na annashuwa tana fadin Mama zan dan leka gidansu Yusy (yusrah), ta zuba mata harara tana fadin ba inda zaki ga mijinka kwance ba’a san me ke damun saba, ta ta6e baki gami da cewa to ai gani nayi ko da ace na zauna hakan bashine zai sanyashi samun sauki ba, nifa ba likita bace, shifa bai damu dani ba Mama na tabbata idan nice nan kwance ban isheshi kallo ba, ta saki baki tana kallonta har ta idda maganarta ta fice Mama na mamakin lamuran, anya Sunailace? ko kamin ta mayar mata har ta tayar da mota sai dai fitarta ta gani ta tagar palon, abin ya daure mata kai sosai….
Ta zuba masa juice a kofin hannunsa tana fadin to me hikimar hadasu aure? Kasan yaran zamani akwai raini da dogon buri kar sai anyi auren ya kasa riketa fa? Kin cika naci kan batu guda Rahma, bari dai in sanar dake da surprise zamu maku daga ke har ita ranar daurin auren yazo a Bilal dinsa na usul, ban gane ba shi dama wannan da muke gani jabu ne? Kwarai kuwa babban mutum ne don kuwa ya tara arziki, dukiya da girma bana shekaru ba ina nufin ta fuskar daukaka, tsawon shekaru goma muna aiki tare dashi a kasashan duniya, mummy ta gyara zamanta tana mamakin kalaman mijinta, me yasa ya linkemu a baibai?saboda tarin matsalolin da ya fuskanta a baya ga kuma dalilai masu karfi, na gamsu amma ya zamuyi da Seemah kuma? Muhsin zamu bama in ya amince ko ya kika gani? Seemah dake jikin window tana sauraron hirarsu ji tayi tamkar kafafunta bazasu dauki nauyintaba, wall
ahi hammy baki isa ba ta fadi tana cizon yatsa, ta mike ta shige dakinta tana kai kawo duk cikin tunanin yanda zatayi, shin zata hakura ne har saitaci nasaran haduwa da mai G ko kuwa Bilal zata komawa? Muhsin din me ashe ma bashi da komai shi ba kowa bane na 6ata lokacina kansa, bari dai wannan banzar tazo insan inda na sanya gaba, ta leka waje daidai sanda motar daddy ta shigo, Bilal ke janta gefansa Hameedaharsa ce da alama unguwa sukaje tare, taji ranta ya dan sosu bai kyautu in tsaya garin kallon ruwa kwada yayi mani kafa ba, na karasa ciki da tarin ledojina gefe kuma Rihab ce da nata guzurin, zuciyata na raya mani inje inga Muhsin shirun yayi yawa hakan nan, yau kwanaki 3 ban ji shi ba, ban ganshi ba ko lafiya? Ji nayi an yafitoni na kusan fadowa don bazata akayi mani tayi saurin tallabo ni, matsoraciya kawai, zo kiji Hammy akwai gist, na kan yi mamakin yaushe mukayi wannan sabon? Kasancewar ta zame mani abokiyar fada sai ya zamana inai ma hakan kallon basaban ba, zauna mana kar ki kosa, na dan yi murmushi ina kallonta twinny ya akayine? Aure nakesoi Hameedah ki taimaka ki binciko yanda za’a yi ih hadu da mai G, gabana ne ya fadi har naso bayar da kaina, ya dai? Nothing ina dai tunanine na rasa abin da zan ce mata, ke! Ta fadi tana girgizani ko zaki tambayi wannan matar ne mai ruwan karuwai? A hanzarce na zuba mata idanu gami da sauya fuska, me na shan mur sai kace na zagi uwarki? Aunty Zarahan ce karuwa? Yes siffartace haka mai kwalliyar jaraba ko kage nayi mata? Ke kuma kilaki ba? Ko kwartuwa kya kirani ban damu ba fatana ki cikamin burina, na mike na barta a nan ta biyoni da gudu na rufe kofar dakina don kar ta damenima, haka na shareta don bani da lokacin aikata wannan bukatar nata. Rihab is staying until I finish my search for her biological parents cewarsa yana kallon mu, treat her as one of us, is that clear? Daddy I was sleeping fa cewar Seemah don ni ya sanya na taso ta kan wannan meeting din, banza yayi da ita, ni da mummy muka zuba masu idanu, ta wuce fuuuu tana gunaguni, zo nan cewar mummy cikin daga murya, hakan ne ya sanyata dakatawa tana Jan tsaki, cikin dacin rai ta karasa gareta gami da dauketa da mari, you don’t walk out of your elders, get lost kafin in inyi kulikuli da ke, na rufe baki da hannayena cike da mamaki sosai, wannan shine karo na farko da zanga mummy tayi duka, tsawon rayuwata bata taba marina ba, kai bani ba duka childhood friends dina da muka taso tare ban ga wanda mummy ta taba yi wa tsawa ba bare duka, ta wuce daki da gudu gami da banko mana kofar garam, did you have to descend on her like that? Don Allah mine barni in yi bakin kokarina kafin ta zama ikon wani, Allah ya isa Ni’ima cewarta tana kallon inda nake, idanun nan sun yi ja, na langabe kai gami da girgiza mata kai alaman kar ta bari hawayen su zubo……
Satinsa daya yadan watsake shi din ma ba sumul ba, ke kyace ba shine Muhsin din baya ba agogo sarkin aiki, damuwa da yawan tunani su suka sanyashi gaba har suna yunkurin hallakashi, duk wani case da ke hannunsa saidai hakuri kawai a jira har sai ya samu sauki ya dawo Muhsin dinsa, wanda ba’a san ranar samuwarsa ba, Sa’adah ce mai kulawa dashi Suhaila kam yawonta take fita duk sanda ya raya mata…
Yau dukaninmu muka fita unguwa yawon shan iska daddy ke janmu mummy a gidan gaba, mu hudu kuma a gidan baya(ni, Seemah, Ib da Rihab), daddy naji yana fadin Rahmah abin nan fa ya dameni, har yashe muka san ranar samun lafiyarsa ya karasa shari’ar Alhaji Muntari!?(mahaifin Ib) ,nayi zugum ina sauraronsu ni kam naga ta kaina, na fahimci nice silah, toh me abinyi? Lallai kam tawace ta sameni, suna wannan hirar muka dau hanyar gida, Seemah ce naji tana fadin daddy jifa wancan motar kaman mu take bi, ya dan kali mirror dinsa gami da cewa kin dai tsargune ina ruwanmu dasu, a haka muka isa gidan duk muka sauko zamu shiga ciki, Alhaji! Cewan soja mai gadinmu, akwai baki a bari su shigo? Bismillah cewarsa ya bude masu gate suka shigo da motarsu, na tsirawa na cikin motar idanu a kokarina na son tabbatar da abin da ke shirin faruwa, wanda ya haifar mani da kamewa a gurin na gaza motsawa tamkar wace aka dasa…. Kun san wa na gani?
MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
22…
Tun kan in kai ga cewa wani abu ya fito cikin shigar data amsheshi yana murmushi, preety manya sai kika 6ace kawai ba ko sallama, ya karasa inda daddy yake suka gaisa sannan ya waiwayo gareni yana fadin yau gani a kauyanku, da sauri na juya fuskata inda Seemah ke zaune itama idanunta kur a kaina, na kau da kaina ina kokarin barin gurin, sai a lokacin yaga Seemah da ta biyoni da gudunta, Alhaji ya kira daddy cikin yanayin mamaki, twince ne? Daga wannan ban kuma jin abin da suke cewa ba, da gudu na shige palo ina kokarin shigewa dakina, hannuna ta finciko tana magana cikin tsawa, tsaya dan ubanki who are u fulling? Cikani kar ki 6allani nace, da dabara na jata muka koma kusa da garden, dama kin sanshi ko munafuka marar amana? Na yi ajiyar zuciya ina girgiza kai Seemah ba haka bane litsen, ta rufe idanu gami da cewa i regret knowing you Hameedah ke din masiface a gareni, kwalla suka taru cikin idanunta, me nayi fisabilillah da ta kowace fuska kike kokarin dakusar da haskena? A kowani hali Hameedah ce tauraruwa …why? Ta fadi daidai sanda ta hankadar da katuwar flower vase ta fado kan glasses din da aka jingina don renovatin gidan da aka soma yi, nayi tsit tamkar ruwa ya cini na tuna kalmar aunty Zarah da take fadin ,”shin kaddararkice? Wanda ya sanani jin KARFIN HALI ya shigeni, cikani Seemah haka Allah ya kaddaro mana kar ki ji mani rauni, ina nan naji muryar daddy na kwala kirana, kwatar kaina nayi na fice da dan guduna a palo na tarar dashi, ya dan kalloni yana murmushi, baby mai kala kala, jeki ga bakonki kar fa ya kosa? Mummy! Na fadi don naga tanai mani kallon tuhuma….jeki sai kin dawo ta fadi tana kallon mijinta, a jikin motarsa na sameshi yana lalatsa wayarsa wace naira ke dukan naira kanta, barka da isowa amarya, na kau da shirun da mukayi na tsawon wani lokaci ta hanyar cewa aunty Zarah ta san da zuwanka? Not really business nazo yi zamu fita daga village din na hangoki a mota lokacin da kuka fito daga mall dina nan duk ina kallonki, shi yasa na biyo hanya, so how is lyf with you? Not bad na fadi ina kallon takalmana, zan iya gaisawa da angon namu kafin in tafi? Baya kusa ban jin zai dawo da wuri kuma, ok, mah warm regards to our twin, nayi yake kawai ina gyada kai, zata ji, Sauran kuma a manta da mu idan an yi fixing date, ko ban gaya maka ba I trust aunty Zarah, ok then, bari in wuce toh, har ya juya zai shiga mota ina nan tsaye naga shigowan Bilal din yana kokarin shigewa cikin gidan, daidai sanda Seemah ta fito kunnuwan mu suka tsinkayi kalamanta, wayanda suka dakatar da shi, Allah ya isa Hameedah, kin kusan auren ma baki daina kwashe kwashenki ba kiji tsoron Allah……..bata kai ga karasawa ba na kalli mai G gami da cewa kaje kawai thanks for coming, ba musu ya ja ya fice na waiga don ganin bilal amma ina har ya 6ace wa idanuna, na bita cikin dakin amma bata kusa, zuciya ta kwasheni na bi bayanta cikin dacin rai, shiru gidan iyayen namu babu ko dayansu a kusa, a kan bene na sameta tana huci sannan da sauri na haye nima, Seemah ribar me kikaci da kike kokarin rushe mani farin ciki? Gara mu zama daya in ban samu ba kema sai kin rasa wallahi, na kifa mata mari wanda ya sanyata yin kara sannan da sauri ta yayibo hukar da ban san daga inda ya fito ba, Hameedah gara in kasheki in huta ta fadi cikin hawaye muryarta na rawa, ban san sanda na zube ba ina rokonta, kar ki mani haka please Seemah Allah zan kiyaye gaya mani me ba kya so? Kin yi kadan wallahi ni zaki yiwa yaudarar da kika saba? Litsen Hameedah! Ta fadi tana yunkurin da6a mani shi a saitin zuciyata, yau itace ranar ki ta karshe a doron kasa ki bar ni in samu masoyanki nima inji yace kikeji, idea ta kare mani addu’a kawai nake karantowa ,duk wanda yazo min yi nake har da tashiga toilet, ta rufe idanu naga ta daga hannu 2 da nufin cika kudurinta, fargaba ce ta sanyani hankadeta sannan nayi saurin durkushewa ta gangaro daga benan tun kamin ta ida sauka kasa naji sahu na nufomu, mummy ce garin ta karaso garemu santsi ya kwasheta da azamata na yi niyyar karasaw in tallabota amma kamin in cimata har ta kifa, ihu na tsala ya zanyi da rayuwata? Na cici6ota ina kuka jikinta lakwas hakama Seemah dana ta6a hannunta shiru, na kara kunne kan saitin zuciyarta ba alaman numfashi a tattare da ita, ga hukar hannunta ta yayanketa tana bleeding, mummy ma jini taketa fitarwa, ihu na kuma yi da dukan nin iyawata Rihab ta shigo da teadies dinta, nan naga ta watsar sannan ta kwasa a guje, na soma safa da marwa gurin babu solution me zance ya samesu? Na kashe Seemah mummy ta ganmu bazata yafe mani ba, babyn jikinta ma nasan ya margaya, why? Seemah me yasa bakison zaman lfy? Rigar jikina ma ta jike da jini tamkar ni na yankasu, zuciyata ta shiga bugawa da sauri da sauri na buga wayar Muhsin don daddy yayi tafiya Bilal kam fushi yake dani yaki daga wayar, tun da ya kwanata rashin lafiya sai yau aka samu ci gaba a fanin lafiyarsa, tea Mama ta hada tana fifita masa, ba laifi ya kan dan zauna ayi hira jefi jefi ko kuma karatun Qur’an, jiki na rawa ya daga wayar yana fadin baby ya dai? Kazo please na fadi a rikice sannan na katse wayar, Suhaila dake gefansa tana ji ta mike cikin kunar rai, shi kam bai bi ta kanta ba ya dau makuli ya fice Ina ganin isowansa na fice da gudu, gabansa na karasa ina haki kuma na kasa magana ma, hannunsa na ririko ina ja bakina na rawa don haka maganar bata fita daidai, a haka muka karasa dakin da abin ya faru, kaga na kashesu ko? Itace maganar dana kwato da kyar a karkashin makoshina, na fadi da e’ena ina hada hakwara, zauna can ya fadi yana nuna mani kujera, sannan naga ya dauki ko wannan su ya kai mota, idan kin natsu clean d area ya fadi sannan naga ya tayar da motar ya fice da gudu….. A sanyaye na kimtsa gurin hankalina na garesu har zuwa lokacin kuka riris nake rerawa, Ib ya shigo hannunsa rike da Rihab, aunty Zarah na gaisheki Hameedah, Rihab tace akwai jini a gidan nan hakane? Ban kai ga bashi amsa ba wayar da na mance inda na ajiyeta ba naji tana ringing, da azamata na dauko ta a karkashin kujera ina tsammanin Muhsin ne, gamu a family hospital dinku ki taho masu da wasu kayan za’a canza na jikinsu ne ya 6aci da jini, uhum na fadi sannan na kalli Ib ina fadin dauko car key zamu asibiti, Rihab bishi gani nan tafe, da sauri na harhada komai na bukatuna na samesu a motar ya tayar muka dau hanya, Hameedah wai me ke faruwa ne? Muje don Allah jirana akeyi, yayi shiru har muka isa gurin ya taho ya samemu a reception, he is caring ke kya ce jini nane matsalata tasa ce a yanda ya nuna mani, ku koma gida baby baza’a bari ku gansu ba yanzun d condition is critical, ‘yan uwa nane fa lawyana ko ta window na dan leka ai na fadi cikin kuka, ya kaini jikin window na gansu suna kar6an treatment ba laifi, na juya gareshi kar in barka kai daya, ba damuwa jeki ki kula da gidan ok? Zan dawo anjima zuciyata ta gaza natsuwa sam, ya rakani har mota yana fadin ki kwantar da hankalinki ok? Na dai daga masa gira ba don zan iya aikata hakan ba, na dai jishi ne kawai IB ya ja muka dau hanya, mun bar masa Rihab don kar kadaicin yayi masa yawa, hirar batun muke har muka isa gidan, a bakin gate mukaci karo dashi dawowarsa kenan, daga ina kike? Yayi mani wannan tambayar yana kallona a kaikaice, tamkar ince masa inda ka turani na dai share kawai na wuce ciki zuciyata tana kuna shi da yaki daga mani waya daidai sanda nafi bukatar kulawarsa, ya rufa mani baya yana fadin wait Hameedah, na tsaya cak jin yau ya ambaci sunana, waya 6ata maki rai? Na saki kukan da nake 6oyewa, sannan na fada masa abin da ke faruwa, amma kar ka damu kanka wanda yafika damuwa dani yana kula da lamuran Alhamdulillah na fadi ban tsaya jiran amsarsa ba na shige abuna…
Sahu na uku kenan likitansa na zuwa don duba shi a gidan amma har lokacin basu san inda ya shige ba, hankalin Mama ya tashi kam ba wasa ga wayoyinsa a zube kan centre table, Suhaila na ji ta basar bata fadi ba, abokansa na jiki kam an bubuga masu basu san batun bama aka shige bincika inda ya shiga, Mama ke fadin bashi fa da lafiya hawan jini da damuwa ke damunsa kwanakin sa uku kwance ya kasa mikewa, Suhaila kiyi wani abu akai mana, haba Mama! Zan hana mutum fita ne shi da kafansa? Ta karashe maganar tana yatsina fuska tamkar taga kashi, ta shige dakinta gami da kulo kofa tunaninta naga yanda zata hallaka Muhsin ta huta da bakin cikin sa abin ya isheta…
Ya saki baki gami da bainta da idanu har ta 6ace masa sannan ya juya kai tsaye mota ya nufa ya tayar don zuwa asibiti dubasu a sanyaye jikinsa ya kasance kwara. Muna isa gidan na dage na dafa masa abinci da drinks don zai yi wuya a kai masa daga gidansu, daga nan na soma hada ‘yan kayayyaki, tooth brush da paste sai sallaya da pilow na zuba a boot ina jiran IB ya dawo daga masallaci mu wuce…. Shigarsa kai tsaye ya wuce office din doctors yana tambayan ‘yan emergency da aka kawo da kwatance aka bi dakinsu, Muhsin ne tsaye yana amsa waya wani irin kishinsa yakeji yana taso masa tamkar ya murdeshi, ya juyo suka hada idanu daidai sanda ya ajiye wayar, sannu da zuwa! Ya fadi sannan ya mika masa hannu shi kam ya shareshi sannan ya maida hankalinsa ga dakin yana mai jin tausayin su matuka. Har zuwa lokacin IB shiru wanda ya sanyani kiran wayar Lawyer nah batare da na tsaya jin maganarsa ba nace muna nan tafe, wacece? Muryar mace naji wanda ya sanyani kashe wayar ina tunani, sannan na kira layin daya kirani dashi da safe, bussiness center ne cewar mutumin, muje sis inji IB na hau muka wuce.
Doctor wancan fa ba dan uwansu bane cewar Bilal, haka dai kace amma ai mu shi muka sani don babu wata alamar munafurci a tattare dashi, ba yanda muka iya ka dai yi hakuri a bi a sannu kai ma ai na gidane ko? Ya fadi yana kallonsa, zaman su a gurin nan Allaah’s willing na wani lokacine, mujira dai Alhajin da kansa ya iso, shi kenan cewa Bilal sannan ya mike a sanyaye ya fice…… Tausayinsa naji ta ratsani ganinsa kan plastic chair yana gyangyadi Rihab na gefansa tana cin tarkacan biscuits, surutan mu ne suka katse masa barci, mun kwaso kayan daga boot na yi serving dinsa IB ke tambayar masu jiki, ni kam nayi tsit ina tunanin grammer din da zan hada wa daddyna idan ya tuhumeni, a hankali yake kallona ko me ya dauki hankalinsa hakan? Daddy ya sani? Na girgiza masa kai fargaban ta karu a zuciyata, wayata ta soma kara shine mai kiran, na mika masa don bakina rawa yake yi, har ya katse layin ban fahimci abinda suka tattauna ba sam, yace isarsa kasar kenan amma zai juyo gida yana da kyau ma yazo din ana bukatarsa yayi singing din takardar yiwa mummy aiki, she have lost the baby, na dafe kirji ina salati a kidime, cool down kema kar tashin hankali yayi sanadinki, Rihab da IB suka fice daga ni sai shi ji nake tamkar bani da amfani a rayuwa, muryarsa kasa kasa yake fadin why? Idan baki zama tsayayya kan lamuran ba ya kikeson ‘yan uwanki su kalli lamarin? Daddy na zuwa kece zaki karfafa masa gwiwa haba baby da sauran rayuwa a nan gaba don gaba tafi baya yawa, ki natsu please ki daina tarwatsa mani lissafi don Allah kar ki karasani….dai dai lokacin Bilal ya fito ya watso mana harara sannan ya fice na mike ina kallon Muhsin, ina zuwa na fadi sannan na rufa masa ba, zaka tafi gida kenan? To me zan maki tunda wancan yafini a gurinki? A ‘a na fadi da i’ina ba haka bane, to yaya ne? Don bani da komai ko hameedah? Uhm uhm, to sallameshi mana, kayi hakuri a rabu lafiya, yace you see? Ki sallameshi nace banson alakar ku, ba zai yuwu ba na mayar rai na a 6ace, ya gyada kai kawai sannan da sauri ya figi motarsa ya 6ace daga gurin, na koma ga Muhsin amma baya gurin, can na hangoshi inda likitoci suke ba jimawa suka iso garemu, baby muje za’a yiwa Seemah dressing ne ki tayamu riketa ko? Muka shige tana nan kwance bata iya motsi tamkar gawa, na dora hannuna kan kirjinta zuciyarta na harbawa nayi ajiyar rai ina hamdala, ta samu karaya a kafa da hannu sai ciwuka da kwarzane da suka dabaibaye jikinta, kunga kenan akwai internal and external injury, nadama ce tazo mani dama na hakura ta aikata manufarta gareni da ba haka ba, kwalla suka cika mani idanu, duk sai na zama very weak, ya kalloni gami da cewa baby jeki zauna a mota ina nan zuwa, ba musu na fice din na gane kukan ne bayaso, wucewan mintinna 30 sai gashi tafe ya bude mani kofa ya dan rankwafo yanda zai kalleni sosai, kirasu Rihab in maidaku gida dare yayi nisa kar Bilal ya ta6a mani ranki, ni fa shirin kwana nayo, no it can’t be ba tsari dukanninmu mu tare masu a gurin nan, yi hakuri please ka barni in rika ganin fitar numfashinsu da shigarsa, ko na tafi bazan iya barci ba, Allah na daina kukan, to su IB fa ya zamu yi dasu? Su je gidan aunty Zarah su kwana zan ma maigadi waya a kula da gidan, kaje gida ka huta duk ka sauya ba gayun nan dana sani babu kuzari, annuri da walwala, duk ke kika sace mani su, ko gidan naje it’s of no use kenan, ka bar wayarka a gida why? Mantawa nayi ina sauri, me nayi maka ka cireni a lissafin contacts dinka? Ni baby? Eh din, kin fi karfin hakan, Suhaila ta daga wayarka dazun dana kira tana fadin waye? Abin ya ta6ani nasan fansa zata dauka ka bata hakuri ni bazan yi shearing miji bama, kuma tayi kadan ta shiga tsakaninmu tare ta ganmu kaunarmu natural ne ko lawyana? Hmmm baby kishi ake? Na zabga masa harara ina murmushi, lallai ma kai din nan ina da Bilal me ruwana da mijin wata?
MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
23…
Yayi kyau ai nima bana fatan kiyi shearin miji kar ki tada zaune tsaye, matarka tana jiranka kar ta kosa su Mama na bukatar kulawarka a matsayin namiji babba a gidan, kannanka na bukatar jagorancinka ka bar duka wadan nan kazo ka tare a asibiti, hmmm korata dai akeson yi kuma ba inda zani kinji ai, ya juya ciki yana fadin ki shigo kici abinci a daina fushin please, na debo kit dina a boot na rufa masa baya ina kokarin samun su IB a waya, ba jimawa suka shigo Rihab ma barci takeji sosai, ku kwana gidan aunty ni da komawa gida sai sun warke, kai Hameedah inji IB! Shhhhhii na fadi sannan na mika masa makulin mota kuje kawai sai munyi waya, lawyanta mu kwana lafiya oya Rihab dauko jakarki mu wuce, kamar in ce masa wani abu na dai share IB ne da shegyan tsokana, kinji abin da yace ko? Ya tambayeni bayan fitarsu, na share ta hanyar cewa ka kwana kan sallaya ni kan kujera zan zauna ina kare amsu kallo, uhum mai gadi mikomin pillow toh, na bashi sannan naji yace oya eat yarinya yini guda duk kin sauya kin lalace kamar mai cutar amai da gudawa? Na dan yafici abincin don ba shine a gabana ba sam sannan na zauna har ban san barci ya daukeni ba… Kira’arsa ce ta tayar dani na dan muskuta don gyara zama najini a kwance, firgigit na mike na tsinci kaina a kan sallaya da pillow yana nan zaune kan kujerata yana karatun Qurani, toh ya akayi na dawo gurin? Sorry na damekiko? No yi ibadarka na fadi sannan na mayar da kaina ina nazarin yanayin.
Nayi tsuru ina kallon daddy a tsorace yayin da ya karaso dakin yana kare wa marasa lafiyar kallo, idanunsa naga sunyi ja wanda ya haddasa mani tashin sense, ya na iya? Na kame a tsaye na gaza furta wata kalma, tsorona kada Seemah ta farka ta fada masa nice sila, shi da doctor suka fice da sauri na karasa gareta ina fadin Seemah rufa min asiri idan kin tashi pls duk abin da kika nema Allah zan maki, haba baby! Murayar aunty Zarah ce tana karasowa gareni oya muje, taja hannuna muka fice tanai mani nasiha, sannan ta daukeni muka wuce gidanta inda na tarar Rihab na barci IB kuma ganinmu sai ya canjeni ya koma asibitin, na huta(jikin ne dai ya samu nutsuwa amma kwakwalwata ba), sai lissafi nake ina hango makomata, har yamma mukayi girki ta mayar dani IB ya koma tare da ita, nan na tarar da Sa’adah, ummu Salama da auta Husnah suna taya daddy hira, muka gaisa sannan suka tafi bayan sun ajiye kayan dubiya, ba jimawa aka fito da mummy daga dakin aiki zasu shiga da ita dakin hutu, duk na rude da gudu na bita ina rike da hannun damanta, sai dai shigarsu ta haddasa rabuwar hannayen namu nayi ta zarya a bakin gurin ina cizon yatsa, can na koma ga daddy ya juyawa kofar baya yana kallon sama yayin da yayi nisa cikin tunani, baby zaki fadi gaskiya ko? A diririce nace e…e…eh, me ya sameta? Muryarsa na rawa a kagauce na kalleshi, daddy kar kayi kuka Allah kaddarace kawai, naso riketa amma Allah bai yi ba ta rigani kaiwa kasa, I lost mah unborn child, how do u explain this? Seemah fa? Na fashe da kuka, ya isa ya fadi a sanyaye, muna nan zaune wucewan awa 2 sai ga fitowan likiciyar data haifar da damuwa garemu, ya dai cewan daddy? Alhmdlh an ciro bakwaini munsa a kwalba saidai uwar ta jijiki, Alhamdulillah na furta daidai sanda daddy ya saki ajiyar rai, da sauri na rungumeshi, nasan bazata ta6a manta cewa mune silar faruwar hakan ba…
Cikani nace, ta saki kwalar rigar tana fadin ka maida mutane ‘yan iska Allah bazai barka haka ba Muhsin, ina hakina? Ci sha ko suttura kika rasa? Hakin aure nake nufi jahili tunda iliminka bai karanta maka ba, nine jahilinki? Oh! yes zan kara fada idan ba haka ba a wani rukuni kake? Da kyar ya kwaci kansa gami da cewa kiyi hakuri amma kuma da kunya kina auran jahili, jahilin dake auran mace irinki me za’a kira shi? Yayi dakinsa yana kokarin shiga wanka, ta harde a palon tana jiransa tamkar danta… Suhaila ina son mu fahimci juna shin menene matsalarki? Ka fini sani ai, hakin aure? Kwarai, ok kece ai bakya son a zauna lfy amma daga yau zakiga canji biznillahi, ta dan yi far da idanu tana juya hannu kai din sai kace mutumin arziki bawan amce, Allah ya isa ina da labarin ka kwana da Hameedah, subhanallah! Ya fadi yana dafe kansa, me yasa baki da fahimtane? Laifin mama ne kasan ai rainonta ce ko? Ya mike ya bar mata gidan gudun kar ya shaketa tsabar takaici, har ya kai a zagar masa uwa?…. Jikin mummy yayi kyau kullum cikin barci suke yau ranata uku kenan muna asibiti, wanda ya sanya wa zuciyata dan natsuwa har na samu daman neman Bilal mu sasanta banson 6acin ransa a kaina sam… Zakazo? May be, don Allah kar kamin haka ina jiranka a bakin asibitin, na fadi ba tare da jiran amsarsa ba na katse wayar, wucewan 30min ina nan zaune har ya sire mani a rai na juya zan koma ciki, horn dinsa ta dakatar dani, a kaikaice na kalli hadaddan motar na dai basar na kuma daga kafata daidai lokacin naji amon muryarsa, kin fasa gani na ne? Wani irin juyi mai vibration nayi don tabbatar wa idanuna abin da suka gani, shigarsa cikin uniform din da suka dace da fatarsa, ga kan ya sua gyara sai kyalli yake, hannu daya cikin aljihunsa yana kare mani kallo, what a surprise, Bilal na fadi bakin a hangame, kaine? Ina nunashi da dan yatsa, ya ciro hular unifom din jikinsa yana murmushi, ya dai? Ko na canza maki ne? Ina ka samo wadannan? Ya kalli jikinsa yana dariya kasa kasa daidai sanda wayarsa tayi kara ya karata a kunne yana faransanci, na kame tsaye a gurin ina kallonsa, can aka koma british english tsantsarta ni kam nasan misanya mani shi akayi, ya katse layin yana fadin ina bakin aikine Hameedah, an ce ana son ganina gani, ya fadi yana saluting dina, kaje kawai ba bilal din dana sani bane, sorry ki dan saurareni mana, na shige da saurina ya rufa mani baya a haka muka karasa cikin asibitin ina dan sauri da gudu don 6ace masa amma ya kamoni, ya janyo hijabin jikina yana fadin kekarfa ki tara mana jama’a, na waiwaya ina kallonsa sannan kwalla suka cika mani idanu, why? Kai waye? Mijin Hameedah, um um, nooooo ni ba taka bace ka linkeni ta baibai ,why? Natsu kiji ina da kyakyawan manufa wallahi, ni dai ka barni kawai, yana kallo na na wuce na barshi a gurin, motarsa ya dauka kai tsaye ya fice yana tunanin gurin zuwa… Shi ya fara fado mani a rai da azamata na dau waya na kirashi shi kadai ne mai jin matsalata yabani shawara ba tare da ya daga mani hankali ba, ganinan zuwa ya fadi ba tare da ya saurari abin da zance ba ya katse wayar, na shige gidan gaba ya dan ja motar mukayi gaba kadan sannan yayi parking yana kallona, baby waya ta6a mani rainki? A nutse na labarta masa ya jinjina kai gami da cewa a daga masa kafa, ni fa ba mai arziki, dukiya a tsarin mijin aurena, haba mai saukin kai da natsuwa, shi kadai yasan matsalolin daya fuskanta kafin ya sameki, kila matan abin hannunsa suke wa ke kuwa fa? Ni matar talaka ce shine za6ina, yayi dariya yana kyakyatawa, kin iya tuwo? Yes sosai ma, amala, semo, namasara, na shinkafa, alkama, dawa etc,wow talakan nan yayi sa’a, Suhaila kam ba uban da ta iya ya ayyana a ransa sannan na kara da cewa me kake ganin zanyi? Ah ah ha! Forget kawai kuci gaba daga inda kuka tsaya shine daidaike mai arzikin in kika auri talaka baby za’a rika kai ruwa rana, dalili? Kina cin mai kyau kin taso a wadace tsabar MATSAYIN ki na ‘yar amanah ‘yar gata ki sanya mai kyau da tsada sannan kice talaka? Daina mafarki it can’t be kina sonsa da yawa idan kuka rabu zai ta6a mani rainki, da aka bani red card banji da kyau ba har yau jinya nake baby duk a dalilin so bale ke mace mai rauni zuciyarki bazata dauka ba, damuwar tayiwa shekarunki girma, ya Suhaila? She’s fine, naso ace ita mai saukin fahimtace da munyi abota don ban son kayi mani nisa, ya kwashe da dariya baby akwai kuruciya, yanzun ma ai kina iya zuwa, kai! na fadi ina zaro idanu, ban manta dambansu da Seemah a gurin dinner, hmmm baby matsoraciya, Lawyana! Hmmm babyna ya akayine? Kar ka fada ma kowa kaine besty na, shi yasa i always feel free in gaya maka matsalata, ina son ‘yan uwanka, kayi wa Sa’adah godiya sunzo mana dubiya, ya gyada kai yana kallona na sada kaina kasa ina fadin maidani asibitin zuciyata ta yi sanyi dana gaya maka, ba tare da yace komai ba yaja muka wuce yana tukin jefi jefi yana kallona na maida kaina jikin kujerar na kwanta luf ina tunanin alakarmu, shi din mai saukin hali ne har saida naji alaman tsayawa sannan na sauka ina daga masa hannu. Yammacin ranar ban huta ba Bilal nata yi mana zarya ala dole ince na yafe masa ba yanda na iya dole ta sanyani daga masa kafa amma da sharadi, a gidanka zan fanshe, ba matsala ai ya fadi yana murmushi, na bishi dadaddare ya maidani gida ya wuce, nayi masa waya don sanar dashi yanda mukayi, kun shirya dai ko? Da murnata nace eh, madalla cewarsa behave matured baby kin girma fa, naji na fadi yanai mani tsiya na katse wayar. Daran ranar kam bai rintsa ba Suhaila ta caza shi ga jimamin baby tayi masa nisa dole ta sanya Sa’adah neman likitansa a waya aka hau yi masa treatment, ka sani ni na wuce wulakanci bazan dauki raini ba, sannan ta watsa masa hotunan hameedah a ka tana bala’i(wayanda yayi mata da kayan lawyoyi ranar da aka kammala shari’arsu shi kuma a ranar ake auransa), yau ya zama rana na karshe da zaka shigo mani da kayan kadangarun barikinka gida, auta Husnah ce mai zuciya ta wanketa da mari Mama da sauri ta bita zata mara ta arce da gudu, ai gaskiya ta fadi me amfanin magidancin da bai san girmansa ba?
A kwana na hudun ne Allah cikin ikwonsa Seemah ta farka garau kanta na cikin saiti, likitan dake round ya leko yana fadin wacece Hameedah? Jiki na rawa na mike da hanzarina, zo tana son ganin ki its important, na karasa da murnar yau ta samu afuwa, kwalla taf idanunta na dora hannuna kan karyayyan hannun nata ina kallon kwayar idanunta, Seemah kiyi hakuri kar daddy yaji please, Allah kinyi kadan sai naga abin daya turewa buzu nadi, a sanyaye na kalli kafarta mai karayan ina girgiza kai ki gafarceni, ban iyawa yanda nakeji da halittata kika ci nasarar jirkita mani wasu sashi Hameedah yanzun aka fara, gaya mani me kike so Seemah? Allah ko me zan maki in har zaki bar batun tsakanin mu Seemah ina kaunarki kauna mai yawa amma kin kasa ganewa, cab! Naga mahaukaciyar kaunar datasa kika karairaya ni ai, Hameedah kinsan dai zuciyata ce ta kwasoni amma bazan iya kissa ba bale ke twinny, na sani amma ai ya wuce ko? Ta banko mani harara tana kada harshe, in har kinga na bar abu to na dau fansa ne, don haka ki shirya Seemah bata da mantuwa, na sani Seemah litsen, ko mummy batasan dalilin komai ma keep shut please kar ki fesa masu, bukatar ki kenan? Kwarai kuwa, ok lets do it my way, abu ne mai saukin gaske, yauwa na samo numban mai G jiya, wannan matsalar ki ce ba shine a gaba na ba na hango wanda yafishi, nayi galala ina kare mata kallo what do u want? Lets make it a deal Hameedah, ina sauraronki, good cewarta, ki auri Muhsin ki bar min Bilal, ban san sanda na mike ba zunbur, wat? Ta gyara hannunta tana fadin kin dai jini, wancan shine daidai ke mai nacin jaraba tamkar kansa aka yo so, kinga Bilal kam masaha Allah, Kin yi shiru, canza maza ban iyawa, ba matsala ai ba dole nayi maki ba jeki kawai sai mun hadu da daddyn, Seemah ya zaki nemi wannan tayi mani tsauri da yawa?relax babynsa taimaka maku zanyi ki auri mai bala’in sonki zakifi morewa rayuwar auranki, kema nasan kina sonsa munafuka duk gulmace Bilal kece kikafi damuwa dashi sonki a ransa kadan ne wawiya, sha katafi, na saki jiki kan kujera ina kallonta ke lafiya? Kallon nan ya isa hakan nan kar ki cinyeni don kawai nace ki bani Bilal, kar fa ki dauka ya isa ne? Taimakawa zanyi in rabaki da alakakai, shi din har wata tsiya ce? Seemah princess ba kowani gaja nake sauraro ba ko da nake party monga club gal sai na za6i wanda zai saya mani drinks understood? Na kawar da kaina bakin ba abin cewa yarinyar ta shammaceni sosai, tashi kije kar ki sanyani ciwon kai ki wani tsaya mani a ka tamkar ican da aka dasa, da kyar na hadiyi yawun bakina sannan na samu abin cewa, ita kenan bukatar? Haka nace are u deaf? Zan yi tunani na fadi sannan na mike na fice ina neman aunty Zarah wannan batun yafi karfin zatona na kasa samun lambar lawyana ko lfy? Na isa gidanta tana girki na samu guri na zauna… Good seemah tayi hangyan nesa nima nafi sonki da Muhsin din baby bazaki gane ba yafi dacewa da personality dinki, aunty Zarah ya isa, ok nayi shiru uwata, na limshe idanuna ina fitar da kwalla, ita kam hirar tayi mata dadi abu kadan sai tace Muhsin kaza, sai da yammacin yinin na samu wayar Sa’adah wai Muhsin akayi admitting ba lafiya, hankalina ya tashi kwari tajamu muka tafi asibitin da aka kwantar don ganinsa, barci yakeyi rana daya ba shekara ba amma ya sauya sosai yana jin jiki ko me ya haddasa masa wannan kwanciyar? Maman tasa bata nan sai kannansa muka dan tayashi hira sannan muka tafi ina jinsa a raina…
[5/16, 3:10 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
24…
Na kwana gidanta the next day na koma ganinsa, ya samu kansa babu laifi amma ni kam lamuran kan tsaya mani a rai, abu tamkar sihiri? Kwance na iskeshi amma ganina ya sanyashi kokarin mikewa ya kishingida Suhaila ce ta shigo tana fadin na gaji da zaman gurin nan, kafi kowa sanin cutar kai ka assasa wa kanka bata asibiti bace to me na wahar dani? Kawai ka tashi mukoma ban ga maraban dambe da fada ba, jeki ai ban rikeki ba ya fadi yana kallona ina kokarin fidda kular abinci, me aka kawo mani? Da yake ni marainiyar wayonka ce abincin da hajiya ta bayar na zuba maka ko kallo basu isheka ba ko? Ya daga mata hannu ransa a 6ace jeki nace, ta ja uban tsaki har da takani ana masifa aka fice, na dan yi tsuru ina kallonsa wannan wani irin mugun zama ne? Ita kadai ma ta isa haddasa maka kwanciya asibiti, ya basar na mika masa plate din muna dan hira har azahar tayi nayi shirin tafiya gida, lawyana! Ya dai? Case din daddyn IB ne mutumin nan fa har yau a tsare yake sai yaushe zaka sallami batun? Bazan iya komai ba a halin dana tsinci kaina rayuwata tafi komai muhimmanci yanzun, fatana in zama yanda nake a can baya kafin zuwanki cikin rayuwata, i lost forcuse da encouragement, dama kece mai mani wadannan kice zaki zama lawyer, law tana burgeki tunda inayinta, kema zaki zama ni, amma yanzun kuwa fa? Da sauri na kalleshi shima ni yake kallo, zan san yanda zanyi in yi handover, kar ka min haka please, ya na iya? Baby that is the truth, kinga Suhaila is nt helping issues tana sanya mani damuwa a raina Mama ta hanani daukan mataki, na fice a sanyaye don am short of words, jinyan ma ta kasa yi daga zuwanta ta balbaleshi da masifa wai ta gaji, ba kayi dace ba besty na me abin yi? Nothing cewarsa yana dan cin wainar shinkafar da na kai masa, na dan jima sannan na nufi asibiti gurin su mummy, har na isa asibitin ina jin tausayinsa na neman rinjayata… Zo baby ya fadi yana kallon jikina, da fatan ke baki ji ciwo ba dai? Na gyada masa kai kawai ina kallon Seemah ta kifta mani idanu na gane karya ta shirga masa, na kawar da tunanin ina fadin ya jikin naki? Daidai lokacin daddy ya fice yana amsa waya, daga ni sai ita ta kalleni tana dariya irinta migyanbo, ya kika ki musawa common play d smarter role, ina deal dinmu? Na dan sha mur ina kare mata kallo amma a zahiri tunanina naga mazaje biyun, banson kallon tsaf yi magana wawiya, Seemah zaki tsinci farinciki tare dashi kuwa? Y nut? Kaji jahilar yarinya hutu nake so don haka gidan hutu nake hari, he have everything i want, security, authority ,wealth ,riches fame…. Na katseta ta hanyar fadin Seemah ba yanda kike zato bane irinsu basu da lokacin matansu sai tara uwar dukiya a barki da takaici, naji na sani dama ni ai banson takura da takunkumi, in kina ganin bazaki rabu dashi bane ba matsala amma zaki san sauransu ki jira princess ta warke zakiyi bayani, no ni bance haka ba, naji fadi bukatarki, na dan kali inda take cikin nazari ina fadin ina ganin na gama shawara da zuciyata kuma bukatarki abin dubawa ce, kin amince ko kuwa? Hmmm……. Kin yi shiru taimaka maki fa nake niyar yi bahuwa kawai, bazan iya ba na fadi cikin tsawa wanda ya sanyata razana sannan na finciki jakata kai tsaye Bilal na kira ya maidani gida, a hanya ma zuciyata nata waswasi abubuwa barkatai sun min tsaye cikin raina,ina sonsa sosai babu algus ina tausayin Muhsin sosai me abin yi? Zan iya barwa Seemah komai amma wannan karan kin makaro na ayyana a raina daidai sanda na sauka daga motar ina daga masa hannu ya wani basar yaja motar ya wuceni yana amsa wayarsa, abin ya dan sosa mani rai amma na kawar kar inga laifinsa… Mai G yana gari baby inda hali ku gaisa kafin ya wuce OK? Na dai daga mata kai amma ban iya furta wata kalma ba har muka ajiye waya ban musa mata ba, a gidanta na sameshi muka gaisa ko a jikinsa, daga gani isowansa kenan yana ganina ya soma shirin tafiya, don ke daya na biyo hanyar nan ina twin yar uwarki? Hmmm pretty? She’s gud na fadi ina gefansa na rakashi motar har suka tafi ina tsaye a nan sannan na koma ciki tana kimtsa abubuwan daya bari na ciye ciye, ga tsarabarki can ‘yar gata kowa nayi dake, na dafe goshina inaji yana sara mani tamkar in cire kan in huta, why aunty Zarah? Nima sai da ya tafi na gansu nayi masa waya yace naki ne, na zube kan kujera ina ajiyar rai bani da kuzarin duba abin dake cikin jakakunan daya bari don amfanina, Shin wa yafi cancanta?
Bazan dauka ba na bar maki ajiyarsu na fadi a sanyaye na bar gidan, taxi na tsayar a hanya ya kaini gida, can kuma na iske IB da tasa damuwar yana kuka Rihab ta sanyashi a gaba tana tayashi, na bi sahunsu nima kila naji nauyin zuciyata ta ragu, a nan na barsu ba’a raba dayan 2 shi damuwar babansa da ke tsare ne, ni kam matsalolina sunfi gaban sauraron matsalar wasu bale in samu sukunin jin damuwarsa…
Tunda ya warke yake dan kokarin ganin cewa komai ya daidaita, zai kokarta ya tsaya ya kwatowa abban IB ‘yancinsa da tsiya, don ya cika mata burinta na karshe kamin su rabu, daga chambers dinsu ya fito sanda ya samu wayar Sultan mutumin da suka jima basu hadu ba, ya dai Muhammad? Kana ina ne lawyer? Menene wai? So nake kazo da kanka ka gane wa idanunka wani abu don in na fadi ba yarda zakayi ba, ban son wasa fa Muhammad, am serious, bafa zan samu daman zuwa ba ka gane mani yanzun zamu shigar da wani kara, bai jira ya kai karshen batun ba ya katse wayar a zazzafe yanajin haushin Muhsin din… Ina shiga na tarar da ita zaune kan gadon majinyata tana dan sipping tea, ya jikin tweeny? Ta watso mani harara, na fashe da dariyar dake tunzurata, ta soma fadin Hammy ki fita rayuwata kar ki zama ajalina, muryarta ta yi wani iri tamkar mai shirin fashewa da kuka yayin da idanunta sukayi ja, naji babu dadi amma hakan shi ne daidai, hammy kina da hassada, kyashi, bakinciki da rashin yafewa shi yasa baki cin ribar zama, ko? Yayi kyau say that 2 your self, me akayi akayi Bilal da bazaki iya kyale mani shi ba? Namiji har ya isa ya shiga tsakanin mu tweeny? Na mike na bar mata dakin sashin mummyna na nufa don ganin kaninmu, ba laifi ana samun ci gaba an kusan sallamarsu kamar yanda likitan yace anyi nasara sosai,
Da sanyin safiya ya isa gidan burinsa ya isar da sakon da yake tunanin zata zama makamin fidda iyalin Alhaji Abdullahi Buba (gidan su hameedah)daga halaka,sukaci karo shi Muhsin din na shirin fita aiki, da sauri ya karasa suka rungume juna, sannan ya tura masa wayarsa a hannu yana masa rada a kunne, ka sanar da Hameedah rayuwarta na cikin hatsari don Allah Muhsin don’t step out of it, nayi video din komai abin da daure kai kwarai, ka taimaka masu basu da masaniya kan lamuran, tare suka wuce a mota ya kunna yana kallo tunda ya fara kallon gumi ya jikashi don yaso musawa, har karshen abun ji yake tamkar a mafarki, ina ka samo Sultan? Ya watsa masa tambayar yana zare masa idanu, kage zan yiwa mutane? Gaya mani, Muhsin ashe rana daya zaka karyatani, no ba haka bane kwakwalwa da zuciya ba zata dauki lamuran nan ba, gara ma ta dauka Muhsin kai dole ma ta dauka, don haka ya zama dole kayi fighting gurin samun auran Hameedah kar ta tozarta, chill Sultan ba’a kashe wuta da wuta, ko? Abin nan hassada ne da son ganin karshen mai gidansu, zaka yarda aci galaba kanta? Taro aka gayyaceni a Festac mukaje daga in shiga toilet in fito na ji kananan surutai na tsahi, ta gurin key na leka na hango su shine na bi bayansu a sace da kyar na sha, kuma Wallahi bazan yi wahalar banza ba sai ka dau fansa, kai da baby kun zama daya na tabbata her down fall would have negative effect a gareka, ka mike ga abu nan kuru kuru ka gani, yinin ranar ya kasa ta6uka abin arziki, dole ta sanyashi wuce wa gidansu Hameedah don farawa da basirar sa, Rihab ya tura ta kirata a garden din gidan yau bai shiga ba don sirri ne bai son ma asan da zuwansa sam, a mota ta iskeshi ya kafa uban tagumi yana kallon sitiyarinsa, da sallama ta bude ta shige bakin ta dauke da bismillah, Lawyerna sai kace bako? Matsayinka ya wuce na zaman gurin nan please ka sauko muje ciki, da sauri yace nan ma ya isa kin manta ni ba kowa bane a gareki? Amma ai…. Ban son musu baby yaushe zaki koma sch ne wai? Ya dan shiriritar da ita ta hanyar janyo hirarraki, ta saki jiki har suna dariya sannan ya kara da cewa so nice don Allah baby alfarma daya, fadi mana, duk tsawon rayuwata kinsan ban ta6a neman alfarma a gurinki ba ko? Go on, Ok wai me yasa kika fifita Bilal ne sama da kowa har ni? A razane na zuba masa idanu ni kam bani da amsar wannan tambayar, ina jinsa a jinina abin da kawai na sani kenan, ni din laifi nayi maki da kika bani red card? Uhm uhm! To kiyiwa Allah ki cireshi a ranki, WHY ?Tambayar da bansan yanda akayi ta fito daga bakina ba kenan, mun dace da junanmu, sai ka fadi dalilin ka na fadin hakan, da ai kasan da dacewar namu ka janye yanzun me na kawo wannan batun? Bani da wannan lokacin na fadi sannan na banko masa kofarsa na kara gaba zuciyata tana tukuki, tamkar in mari fuskar haka nakeji, yama raina mani hankali, tun daga ranar bamu kuma haduwa ba na rufe duk wani hanyar da zai bi ya ganni.
Yau aka kammala Shari’ar dadyn IB munci nasar taro yayi albarka da murnata na isa gareshi inai masa godiya ta musamman, madadin ya amsa naji yana fadin ki hakura da Bilal Baby, WHY? He’s a criminal, ji kike tas na daukeshi da mari a harabar kotun kallo ya dawo kanmu kan in ankare ‘yan jarida sun zagayemu, mai daukan hoto nayi mai tambayoyi na yi na ja jiki zan bar gurin naji an rikoni ta baya, aunty Zarah ce muka bar gurin da kyar na fada jikinta gami da fashewa da kuka mai tsima rai, me yasa na mareshi? Na shiga uku na fadi ina gunji zuciyata bata da control bai cancani wannan daga gareni ba, ina hangyan daddy yaja mota da daddyn IB suka barni ko oho, da alama ya ji zafin abin dana aikata, ranar naji na tsani kaina a gida ma ban samu fuska ba, sai garani akeyi, yau mummy ta samu sallama amma ban ga fuskar tunkarar su ba, ko hira ake dana bayyana sai ayi tsit kowa ya kama harkan gabansa, abin ya tsaya mani a rai sosai ina son inje in bashi hakuri amma kuma kunyar ganinsa nake, washegari aka baza jaridarmu a gari ko wace kamfani ta rubuta tata fahimtar game da faruwar lamarin jiya a haraban kotu, na rame fargaba da kadaici sun dabaibayeni, ga rashin natsuwa da damuwa sune abokan tarayyata, ban ta6a tsammanin haka daga ‘yan uwana ba, sai a wannan lokacin na fahimci shi din wani ne, yana da babban matsayi a zuciyoyin jama’an gidanmu, aunty Zarah ma ba’a barta a baya ba, ko waya nayi mata zanje can zatace kar ma in fara tana gudun kar in duketa itama duk sun hade mani baki suna horar dani, Seemah kam dama irin hakan tafiso na zama mujiya cikin mutane ‘yan uwana. Daddy don Allah ka zaneni ku janye wannan tsatsauran hukuncin tai mani tsauri da yawa, rufa mani asiri kar nima ki kwakwadeni ana zaune kalau, tashi kije nikam nasan ban fi karfin duka ba baby, nagama magiyan ko gezau, na mike daga tsugunnan da nayi na koma sashina, shi zaki nemo ki bashi hakuri ki lalla6ashi yazo ya tayaki bawa su mummy hakuri cewar wani sashi na zuciyata.
MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
25…
Na kira wayarsa ban samu ba a rana na 2 ne Suhaila ta ci min mutunci, wannan dalilin ne ya sanyani zuwa har gidan don zai fi tabbatar da na tuban da gaske, auta Husnah ce ta taryeni, yau sati daya rabonsa da gida ta fadi tana kallon cikin gidan, Sa’adah kam tana gurin bautar kasa wanda ake sanya ran data dawo za’a yi auranta da Muhd Sultan, ki wuce aunty Hameedah kar Mama ta leko ta ganki, Suhaila fa? Yau kwana hudu rabonta da gidan muma nemanta mukeyi, na juya na tafi a sanyaye zuciyata tayi rauni sosai… A gida na tarar suna shirin tafiya yawon duniya, mummynah a dubai nake bukatan a shiryo mani kayan fitar bikina cewan Seemah, idanuna suka kawo kwalla mummy! Ta daga mani hannu gami da cewa ban haifi diyar data fi karfina ba, sau nawa nake ja maki kunne kan irin hakan? Auran huce haushi za’a yi maku, ta wuceni a gurin ni nasan da Bilal za’a hadani ita kam Seemah ban san da wanda za’a hadata ba taketa rawar kai haka, suka wuce aka barni ni daya a gidan. Sa’adah nake kira musha hirar mu tana kwantar mani da hankali, amma na gaza tambayarta batun dan uwanta tunda da alama bata da masaniya kan lamarin, daga ni sai mai gadi da rana inyi kallace kallacena, wasu lokutan kuma ina dan fita don rage wa kaina kadaici, sannan a sanu kwanakin sukayita wucewa har sati 2 sannan suka dawo da tarkace kala kala na aure, IB naji yana fadin kayan auran twins ne, ni kam ba wannan bace a gabana ba…
Ya dan yi juyi kan kujerar da yake zaune a kai yana kallon naura mai kwakwalwa, sannan ya kalli Sultan yana fadin kila nan da kwanaki 2 in wuce gida please Man ka tsaya kan bincikyan nan zan leka gida, yayi kyau ai gara kaje kaga gida da halin da suke ciki, ya mike don karasawa gaban taga yana kallon gina ginan zamani hankalinsa naga Hameedah ko ya take? Wayar fa zaka tafi da itane? Not yet ya fadi yana kur6an shayi a nutse, ka bani dama Sultan zan dawo in nema wata rana, yanzun dai nafi bukatar tara facts don jifan tsutsu biyu da dutse daya, yanda duk wanda zai nemi kureni kan batun zan bashi amsa gamsashiya har da karin bayani, good cewan Sultan, amma wani hanzari ba gudu ba, kar fa tayi aure before then, na sani amma gagawa aikin shaidan ne, idan muka fito da batun nan tun yanzun believe me mu zamu kwana a ciki, hakane kuma ya fadi yana nazarin takardun gabansa… Wayewan gari ya tashi da shirin tafiya Abuja ko ba komai akwai hakin Suhaila a wuyansa, har sun kai airport ya samu wayar chief justice akan wata bukata data taso masa, ya kalli Muhsin gami da cewa dole ka fasa wannan tafiyar muje tare, kafi kowa sanin irin ci gaban da zamu samu fatana mufi wannan matsayin, yayi dan jim sannan ya nisa yana fadin muje to Allah yasa alkhairi ne ke kiran mu, duk suka juya tafiyar da bai yi a wannan rana ba kenan… Abu yayi nisa har mummy ta kar6o dinkunan mu na biki ni kam angon ban ga keyansa ba sai dai a waya wai ayyuka sun tsareshi, ni ba kawaye ba, aminiyata har yau bata sauko ba(mummynah), Seemah kam sha’aninta takeyi,
tun mummy na fadin mai gyara zata zo ban damu ba, dama tazo din Seemha ce uwar gayyar ni kam ban sa aka ba, gida ya soma cika da jama’a, aunty Zarah ma da muta nan ta, ta gurin daddyn IB shima mun samu kara ba kadan ba, a nan ne ma na ga suna dasawa da aunty Zarah tasu tazo daya, shi dama ba mata ba ita ma ba miji ba, fatana Allah ya hada mani kansu da farin ciki mai dorewa ya dasu a zukatan mu gaba daya, na dada kokarta wa don tabbatar da intimacy ya kullu a tsakaninmu, amma always the same, ni ke kiransa shi kam sai a jima bai damu da sanin ya na kwana na tashi ba, abin nan kan tsaya mani a raina, sa6anin Muhsin mutumin kwari, na kalli yatsun da na mareshi dasu ko me ya ingizani? Shegiyar zuciyar ki ta kwasoki ai gashi nan kin lalata maku abota, nayi lamo ina duduba kayan da zan sanya don shiga cikin jama’a, ki fito ki gaida kawunsa cewan Aunty Zarah, da azama na dau hijabina na rufa mata baya har sashin da aka yi masa masauki, datijo mai cikar zati, namiji mai kwar jini da cika idanu, lokaci daya naji a raina cewa hannu na gari zan fada, da dattako yake magana lafuzansa a nutse da furuci a nutse, nine uba gareshi Hameedah ko? Na gayada masa kai, yayi kyau Allah yayi maku albarka bai ta6a yin maganarki ba ko da wasa, jiya na tsinci maganar nima dama fatana Allah ya saka masa da mace ta gari, tashi kije na yi na’am da ke, murna fal zuciyata na mike na barshi da aunty Zarah a gurin, wannan ne ya haifar mani da dan natsuwar zuciya har nakejin shi din bangone gareni a gidan mijina…
Oh aunty nafa tashi, don Allah ki bar buga kofar wallahi na tashi, ki fito naceko? Na karasa na bude kofan ina goge idanuna barci bai isheni ba, daya daga cikin kawayan aunty Zarah ne, muje kiyi wanka ayi maki makeup, ango fa ba zuwa zai yi ba, who cares? Mu bukatar mu ki fito caras, fes, dagwas dake, adorable mata a gidan mai nasara the silent sharp shooter, nayi murmushi Aunty Mimah mai barkwanci ce… Mun dawo a gajiye muke kwarai, duk shigarmu iri dayace sak da Seemah, a ranar Abduljabbar, Yusrah ,Saima da Siyama suka iso, a bakin Rihab nakejin cewa sunan jaririnmu Ahmad, ni damuwa ma ta sanyani manta batunsa, a can akayi sunan sa tunda aka cireni daga lissafin gidan aka daina damuwa da harkokina, ina neman hanyar da zan bi su yafemin, wata zuciyar ke fadin iyayi ne kawai ai ba su kika mara ba, wanda na mara shi kansa bai kuma bi ta kaina ba balle su cewar dayan 6arin, na gagauta kimtsawa ina gaida jama’a ciki har da abokan aikin daddy daga Canada, su Alfred, Romeo, Mr White, ga uwa uba abokan tafiyarsa dauko kaya na business transactions, har na gaji don kaina na samo abinci zan wuce daki, nan mukaci karo da Ma’idah tare suke da Jalila da ‘yan gidansu, na nuna murnar sake saduwa da su, sannan nayi gaba abuna sama sama nakejin ringing din wayata na dai duba don tabbatar da gaskiyar lamarin, a can karkashin pilo na daukota, ga dakin nawa a hargitse, Sa’adah ce da Ummu mai binta sunzo tayani murna wai, na sanya IB yaje ya shigo dasu, basu zo da auta ba an barta a gida kar kadaici yayiwa Mama yawa, nan na yi serving dinsu sannan muka soma hira, Sulhaila har yau shiru? Ke dai bari ita kanta Maman ta gaji da kanta ta dawo daga rakiyarta, na dan jinjina kai ina fadin ayya na tausaya wa Lawyanah, muna nan zaune ina kokarin sanya masu kallo naji wayarta na kara ta dauka da alama yayantane na fahimci hakan daga yanayin hirarsu, ta katse layin tana fadin yace a gaida amarya na dan yi yake, wai da gaske abotanmu yazo karshe? Duk sai naji ni daban yaki ma yi mani magana sai dai aikyan gaisuwa, ba laifi ai tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka, sun jima har saida na sauya wasu kayayakin muka rika daukan hotuna dasu, aunty Zarah da kawayanta su Laurah, Mimah da sauransu mun dau hotuna kaman banza, ku jirani bari in leka sashin mummy naji ance wakilan govt sun iso, kai kawai ta gyada mani na fice, mama kulu uwa ga Abduljabbar, da wasu ‘yan mata mummy tace Babies dintane, kanne ga Abduljabbar, Ramadan da Hameed kuma suna kanana sosai iyayensu suka daukesu saboda an masu transfer, nayi murmushi muka gagaisa, na juya da niyyar fita amon muryar marokin daya gifta ta windon dakin cikin kirari don neman na kaiwa bakin salati shi ya haddasa mani tashin hankalin da ya sanyani sumewa a gurin na zube warwas….Sanda na farfado na tsinci kaina bisa cinyar mummy tanai min firfita duk ta rude, aunty Mimah ce ma ta lura da AC ta kunna mana, me haka baby cewan Mama kulu? Nayi tsit hawaye na fita a idanuna, cikin lokaci kankani dakin ya dinke da mutane har babu gurin da wani zai shigo, na tsira mata idanu ina nazarin yanda zan fuskancin rayuwar gaba, wanda ya sanyata shafa fuskata tana dan murmushi cikin hawaye kiyi hakuri baby we want the best for you, na dan girgiza kai ina ajiyar rai, mummy! Yi shiru kin san dai bazamu cutar dake ba ko? Mummy fansa kuka dauka kenan? Haka dai kikace amma kaddara ta riga fata, you like him, I taught you cried for him? Baby you were lovesick and I promised to do something about it, kin manta? ba’a maida hannun agogo baya ki kwantar da hankalinki, ta dan taimaka mani na kishingide tana lallashina, amma dai kun yafe mani ko? Eh mun huce baby batun yafiya sai kin bi mijinki tukunna, na limshe idanuna ina jin zafi a raina, mutumin dana mara a matsayin mijin aurena lallai kashina ya bushe, kwakwalwata tana taryo mani lafuzan marokin… Yau daruruwan jama’a sun shaida daurin auran Hameedah Abdullahi Buba da masoyinta barrister Muhsin, sai Seemah Abdullahi Buba da nata gwanin Alhaji Bilal, kai aure yayi albarka Allah ya bada zaman lfy… Na soma salati, ina zan kai Suhaila da Mama? Ya katse layin cikin dacin rai, ya dai? Sultan daddyn Seemah ya kwafsa, dalili? Ya ba Bilal diyarsa, wace aciki? Ban sani ba Sa’adan bata fayyace mani ba, koma wace ce ke auransa akwai badakala a gaba, kagani ba? Shi ya sanya tun farko naso ace shi kansa muka samu muka nuna masa cewa kar ya bashi ‘ya, Oh ho ho! Sultan nasan mutumin nan tamkar yunwan cikina, lura da yayi ina kaunar Hameedah zai sanyashi yi mani bahaguwar fahimta, tamkar son kai na nuna idan hakan ta kasance, kuma in har diyar tace tanayi ba zai ki ba, kai bakasan matsayinta a gun mutan gidan bane, hmmm haka abin yake? Ya dan daki bakinsa cikin 6acin rai, kai wani irin dan iska ne ana serious kana wasa? To ragwan namiji gaka a nan ana auran babynka, matsoraci kawai nasan hakan ne dalilin baro abj kawani tarkato kayanka, ni wallahi ka bani kunya daka kasa cusa kai ka kwatota, zoka shirya tafiya kar abincin gidan nan ya kare, karshan wacan watan na dauko wa Mami buhun shinkafa daga zuwanka har ta kare duk da ba ita ake girkawa kullum ba, kaine mayunwaci ai mayan shinkafa kafi kowa sanin ni dan gargajiyane, nafi muradin su tuwo, danmalele, waina da dai sauransu, da kyau angwan matsala wanda akewa saitin kafiretor da gyaran hammer, lalli Suhaila ta iya aiki, dole dai aci abin da aka samu tunda malalaciya aka kwaso, ya isheka fa Sultan, ya kwashe da dariyar keta…
Na kalli Sa’adah dake bakin kofa tana ta fara’a da alama murna ya cika mata ciki, da daidai aka fice aka barni da mummy, Sa’adah ta karaso cikita ririko mani hannayena 2, kiyi hakuri ,Allaah’s willing zakiyi alfahari da hakan… Yanzun me abinyi?Bani da wata alaka mai karfi da gidan Sultan balle in cusa kai kaga yanzun shishigi zan masu kenan in har na zake a lamarin, hakane kuma, da ace ina auran baby ne sai in fake da hakan har sai naga abinda ya ture wa buzu nadi.
Mummy tafice itama don shayar da Ahmad daketa zabga kuka, wannan ne ya bata daman zama a gefena tana dada kwantar mani da hankali, Mama ta sani? Ah ah muma hakan ya bamu mamaki, muna sonki da yayanmu kar ki damu Mama bata isa ta hana abin da Allah ya kaddara ba, bana son kishiya irin Suhaila bazamu shirya ba ni ban son hayaniya, gasu mummy bazasu yafe mani ba sai nayi masa biyayya, zan sha bakar wahala ko? Haba dai, ke daban ce bari zan sanar dashi yasan matakin dauka, Sa’adah na mareshi fa, ba matsala yana da saurin hucewa, naja ajiyar zuciya ina kallon ceiling, ummu dake shigowa ta miko mata waya da sauri tana kara, Sultan ne mai kiran kar ki gaya masa please na rada mata a kunne har ta katse wayar banji ta fadi wani abin daya shafeni ba, ya akayi aka bamu ke Hameedah? Ni ma ban sani ba, amma jiya da safe wani datijo yazo wai shine uba a gurin angona, ok ko dai Baba Lawal? Oho ni ban san shi ba ma, ta soma kwatanta shi, shine, Ok kawun mune na kano kanin mahaifinmu, Auta ce tayi masa waya cewar Ummu, Sa’adah ta rike baki, me Auta Hushan ta sani? Waya aiketa? Oho nima ita ke gaya mani cewa baban kano yace zai taho ranar alhamis(jiya kenan), na tambayi dalili wai ita ta kirashi, yarinyar nan akwai zurfin ciki shi ne ko ta sanar damu? Kwanaki 5 aka dauka ana taro a gidan mu, a na shida jama’a suka soma watsewa, har wannan lokacin ban ga idon angwayan ba, shin wannan wani irin aure ne? Kullum sai dayan su tazo ganina, auta Husnah, ummu Salama ko Sa’adah muyita hira yaran basu da matsala sam…
[5/16, 3:13 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
26…
Baban kano yace a gaisheki da kyau aunty Hameedah, yauwa auta Husnah wa yace kiyi masa waya? Daddyn nan gidan ne yazo neman Bro Muhsin ranar da kikazo nace maki satin daya baya gida din nan, bayan tafiyarki hakan ta faru, da nace masa baya nan sai ya tambayi mutan gidan suma nace sun fita don kar Mama ta gaya masa bakar magana, ya soma tambayar ko muna da wasu ‘yan uwa a kusa nace sai dai kano, nayi ma baban kano waya na sanar dashi baban buduruwar Bro ne keson magana dashi, na bashi lambar to kinji ban san ya sukayi ba, daga baya dai Baban kano yayi min waya wai zaizo garin nan ranar alhamis, ban san dalili ba ban kuma tambaya ba, na jinjina kai ba shakka daddy da gayya ya aikata hakan, ala dole sai na auri wanda na mara don a karanta mani kuskurena, shi dinma ai ban kishi ba, soyayyar Bilal ce dai tafi tashi tasiri na ayyana hakan a raina, burin Seemah ya cika ban auri Bilal ba amma lets watch out and see ni da ita wayafi wani sa’ar miji? Tunda na ga gasa takeson mu rikayi da ita, sai yamma lis ta wuce gida har munyi sabo sosai dasu duka, duk wannan wainar da ake toyawa Mama bata da labari…
Yau ake kai amarya Seemah dakinta sai naji babu dadi ko ya kake da mutum yana da amfani hakika zanyi missing dinta, ita kam ko a jikinta sai rawar kai ake ana wani yauki da takun takama maganr ma tsada takeyi, na kafa mata na mujiya aure yakin mata na kula ita wannan da sauranta har yau bata san bauta (ibadah) zataje ba, ba hutu da zuba mulki ba, naso yi mata rakiya daddy ya hana nima in jira zuwan mijina cewarsa, a daran ranar gidan shiru sai mutane ‘yan kadan inajin takaicin rashin Bilal, fatana Allah ya ciremin sonsa a raina in kuwa ba haka ba da sauran aiki a gaba, zai yi wuya in bishi sau da kafa, Allah ka sanya masa hakurin zama dani da halina… Saida jirgin ya daga sannan Sultan ya juya yana jin kewar amininsa a kokwan ransa, Allah ka daidaita masa lamuransa, Muhsin ya sauya sosai saboda soyayyar ‘ya mace, rashin gwarzo irinsa a bakin aikinsa asarace babba, ya kosa ya isa gidan don ya huta a gajiye ya karaso, ba wanda yasan da isowarsa ya dan watsa ruwa gami da sanya kaya masu saukin nauyi, yana son zuwa yaga ko an kai Seemah gidan mijinta, zuciyarsa na kaunar sallama da babynsa, sannan shi mai burin ganin inda za’a kaitane, a gurguje ya bar gidan ya samu taxi ya wuce unguwarsu, daidai lokacin motarsu Seemah ta fice na koma kan daya daga cikin fararen kujerun bikin nayi zamana a gurin, sannan na kafa tagumi ina kallon kofar, ko yaushe Lawyana zai samu nawa lokacinHar barci ya soma daukana a nan ban ji shigowar kowa ba, ‘yan cikin gidan ma kafa ta soma daukewa inata gyangyadawa a zaune, nafison in koma ciki tare da ‘yan kai amarya…
Bi bayan wancan motar yace da mai taxi din, har can gidanta ya bisu saida ya fahimci gurin sannan yace ya juya suka koma gidan su Seemahan, ya bashi hakinsa sannan ya sauko inda suka ci karo da daddy yana sallaman jama’a a kofar gidan, ango ya zama late comer, ya dan yi yake kawai yau daddy raha yakeji dai, ina ka shige ne ko wayarka ba’a samu? Ya dan sadda kai kasa yana fadin zafin aikine, yayi kyau amma don Allah a rika sara ana duba bakin gatari, mu nan da kake gani muna son lafiyarka ga matarka can tana gyangyadi, ya dan leka yana son tabbatar da zarginsa, daddy ni?Ya fadi yana nuna kansa da dan yatsa, eh mana da kai aka daura baka da labari? Bai san sanda ya rungume sirikin nasa ba duk cikin murna hawaye taf idanunsa, daddy yayi sororo yana kallonsa don kansa ya cikashi yayi cikin gidan a nutse, inda take ya dosa cikin shigarta na amare ba abin data sauya da shirin nata na kai Seemah gidanta ta zauna a gurin, shigarta cikin english gown silver mai daukan hankali, ta yi kwarash kayan sun amsheta, yau jinsa yake tamkar ba wanda Allah ke so irinsa, yafi kowa dace a duniya, ya dade tsaye a hakan? Bilal da kansa yace ya janye? Kai impossible, baby! Shiru ba amsa, ya dan dafa goshinta da hannunsa na dama wanda ya taimaka mata ta daina rawa da kan, sannan ya zauna kan table din data sanya gaba, wani irin sonta na dada ratsashi wai shine mai wannan sa’ar, ringing din wayarsace ta tadani sama sama nakejin kida na tsahi, na bude idanuna a nutse mamaki ne ko kidamace ni kam na razana, natsu ya fadi hannun damansa cikin nawa yana amsa waya, eh na dan fitane kar ku rufe gidan gani nan tafe, ya katse layin sannan ya tsareni da idanu, kece? Fuskata babu yabo babu fallasa na ce sannu da zuwa, yayi murmushi kawai, kin gani Allah ya kashe ya bani ko? Kaga dare ya soma nisa ko? Eh ba matsala ai ni mai iya kwana a nan ne, kai! gidan sirikai? And so? Nayi shiru ina wasa da yatsuna, mun dade a hakan sannan ya mike yana fadin zan wuce babynah, na daga kaina muka hada idanu nayi saurin kawar da tawa, nagane rakiya yake nema, na tsinci kaina da faranta masa, Muka jera a hankali muke takawa har bakin gate, ki kwanta please ban son wannan gyangyadin kinji? Na daga masa kai kawai sukayi sallama da daddy inajin yana fadin yaushe zakazo ka dauki ajiyarka? Banson ta jima a nan don mun kusan komawa Canada, da sauri na kalli daddy sun gaji dani kenan? Sannan na maida kallona gareshi, very soon nagode daddy ya tari taxi ya wuce abinshi.Wani irin nishadi zance ko farinciki ke dibansa har ya rasa ma wa zai kira wa zai wa godiya da wannan ya karasa gida hankalinsa kwance, rabon da yaji kansa haka tun farkwon haduwarsu da Hameedah, ya shige cikin gidan yana mai hamdala daidai sanda Mama ta karaso 6angaran sa tana fadin kai haka akeyi? Sai ka bar gida babu kai babu labarin matar daka ajiye? Yayi sororo cike da tunanin lafuzanta wai har ya ajiye wata mata a gidan, ina Suhaila ba kai ta bi ba? Au ashefa hakane ya bar Suhaila a matsayin matarsa, shi har ya manta batunta ma, au Mama ina taje? Kai zan tambaya ya kwala wa Sa’adah dake shirin barci kira yana neman karin bayani, ta labarta masa iyakacin abin data sani, abin ya daure masa kai ya dubi mama yana fadin kingani mama irin hakan na guda tun farko shi yasa naki hadin nan, zo to ka dakeni dan zamani tunda ban isa insa ko in hana ba, Sa’adh ta toshe baki gudun kar dariya ta subuce mata sun kusan karya alkadarin Mama, nan kusa tunda hameedah ta shigo hannu. Har ya kwanta barci yana hangyan hoton fuskarnan nata tana gyangyadi, murna ta cika masa zuciya har ya kasa barcin ma ya janyo wayarsa ya kirata itama idonta 2 barcin ya kaurace mata, a nata 6angaran rashin kwanciyar hankaline da tunanin yanda zata kaya idan ta tare, sai juyi take bisa gado can ta mike ta kunna tv gashi tana fashin sallah, daidai lokacin wayarsa ta shigo ta dauka cike da tunanin dalilin kiran nata, tunda ya aureta ai shikenan ai sai ya jira ta tareko, kaman kar ta daga ta dai dauka ranta babu dadi, a sanyaye nace hello, baki kwanta ba? Uhm kawai na iya cewa, nima na kasa barci cewarsa, ko me nawa a ciki? Ka shekara ma a zaune na ayyana a raina, me kikeyi naji hayaniya? Kallo, lallai baki da matasala, uhm na kuma fadi, me kike ganin za’ayi? Oho! Laifi nayi maki? Uhm uhm, baki da lfy ne? Uhm, don Allah ki huta zanzo muje clinic da safe kinji? Uhum na fadi sannan na katse wayar, ya rike kan wayar yana kallo tamkar ita ce a gurinDa sassafe ya shirya ya karasa gidan don kaita asibiti tunda daran jiya tace bata da lafiya, a kofar gida sukayi clashing da daddy yana shirin fita mu kam lokacin muna breakfast a dinning area, suka gaisa daddy ya kira Rihab data leko don ganin waye ke shigowa tunda sun ji karan mota, kice mummynku na tafi bazan jira ba zan dawo in dauketa, ta shige da gudu ya ja motarsa ya wuce bayan sun gaisa shima ya samu sararin shiga yayi parking, na gaza cin abinci yanda ya dace mummy na dan satan kallona, sai ga sallamarsa shigo mana cewarta tana gyara zama na sada kaina kasa ina jin nauyi saboda rigar barcine a jikina mai siririn hannu, ko dankwali ban sa ba tamkar in nutse a gurin, ina ji suna gaisawa ta kallo inda nake tanai mani alama da idanu, na mike na shige room don dauko abaya, shi kam ya bita da idanu ba jimawa na fito, ya wuce palo cewan mummy na gyada kai kawai na bi hanyar gurin, nayi sallama daga bakin kofa ya amsa na tsaya a gurin ina son karasawa amma zuciyata ta ki dauka, shigo cewarsa, na karasa na zauna kan hannun kujerar ina kallon window, ya gida? Lfy ya jikin naki? Ni lafiyata lau, ok na sauya makine daga Muhsin din da kika sani? Me ka gani? Kina abu tamkar mu din bakin juna ne, kwalla ya ciko mani idanu uhm uhm kayi hakuri ba laifina bane, zuciyata ce amma ai ban ki ka ba ko? Kina sona kenan? Uhm na fadi ina gyada kaina, ai banji kin fadi ba, kayi hakuri watarana zan fadi, ya su Mama? Suna nan kalau sunce a gaisheki, ina amsawa, a mike da nufin in hado masa break, sorry kin gaji ko? Ah ah breakfast zan hado maka, barshi kawai kar ki wahala ba abin da zan iya ci kece breakfast din yau, na jinjina kai sannan na koma zan zauna daddy ya shigo da fara’arsa ya wucemu yana kiran Rahma nayi latti kar fa ki 6ata mani lokaci, mummy naga ta fito Rihab dauke da Ahmad zasu unguwa, mummy nifa? Afwan keba ikona bace, nayi shiru ina kallo suka fice, kina son zuwa outing baby ai sai ki sanar dani, sai inga tamkar ina takuraki in har zaki rika kauran baki da cutarwa, kin nemi wayar Seemah kuwa? Na girgiza kaina, yana da kyau ai ki gaisheta da haka zumuncinku zai dore, na dauko wayata ina kokarin samunta, sau goma ina kokari amma no answer, na mayar da idanuna gareshi shima ni yake kallo, ya dai? Bata dauka ba, anjima kya sake jarabawa, je ki shiro muje outing ya fadi yana mikewa, ki sameni a mota, be jira amsa ba ya fice naji farin ciki don na gaji da zaman gida rabona da watayawa kusan sati 7 kenan(tun ran dana mareshi a kotu)…
Mun hau hanya sai zagawa muke bamu da takaimeme gurin zuwa,daga bisanni muka dire a shoppin centre,ba yanda beyiba in dau wani abu naki,ya janyo basket yana jidan kayan shafa da turararrika,sai takalma masu shegyan kau da tsada sun dau hankalina kwarai,sai ‘yan kunaye set masu kyalli suma,ina biye dashi muka wuce ya biya kudadansu aka shiryasu a jakakunan ledamatures manya manya sannan ya kar6a muka wuce,matarsa ya siyawa na ayyana a raina ni kam ko oho,naji wani abu ya tokare mani wuya,ya wuce damu muka sha ice cream har ina tuno can baya da yake jido min su,mun dan yi hotuna sannan muka dau hanyar gida. Har na juya zan shiga cikin gida naji yace jimana,na saurara don Allah taimaka ki rabani da wadannan,ya miko min ledojin na karasa zan kar6a, Suhaila fa? Ta rigaki samun alheri daga mijinta, kalman mijinta ya kular dani waton mijin wata na aura? Na ayyana a raina ko sallama ban masa ba na shige abuna, sai ta waya na tura masa sakon godiya don ya san kaina duk bukatuna ya tarkato min babu na banza, ya turo min da (babu godiya a abin daya zama dole) nayi dan murmushi yayin da nake shirya kayana, na dan samu nutsuwan zuciya babu laifi… Washegari mama ta kafa masa kahon zuka ita wallahi sai ya kai report an nemo mata ‘yarta, haba Mama yarinyar nan fa ba korarta akayi ba ganin damanta da iya shegyan tane ya sanyata cin kafan kare ba? haka ma kace? Tashi ka fita nace, ya mike yana neman makulin mota shi lamarin ma ya bar 6ata masa rai inda sabo ya zame masa jiki, ya kai kara station din datafi kusa dasu yana fitowa sai ga wayar Muhammad Sultan, kai ina airport fa, da murnarsa yake fadin 5minutes gani nan tafe. Ya manna mata kiss a goshi yana kokarin tashi daga gadon, ta zuba masa idanu cikin kissa tana mai cewa da yamma fa zan koma kila mijina ya dawo, kina haukane? Ni kuma in yi yaya idan kin tafi? Yanda ka saba yi mana, uhm uhm this time around ba zai yuwu ba ai be san darajar ki ba, you are so sweet ban son mu jima bama tare bari in leka joint, yana fita ta soma hada abin data mallaka don kar yaga tafiyarta, ta saci hanya ta fice kafin ya dawo. Ya Sultan yazo da aminin nasa, ya dan yi mana nasiha sannan suka shirya zasu tafi, mummy ta aiko da jaka na bakone cewan IB na kar6a na mika masa yanata godiya na rakasu gurin mota, sannan na juya ina jin yana fadin ki soma shiri kwana kusa zan zo daukanki, anzo gurin na ayyana a raina wani irin zama zamuyi? Janye da akwati ta shiga harabar gidan tana takun takama har sashin daya zama mallakinta, auta Husnah ce ta fara ganinta amma sai ta basar taci gaba da harkokinta kawai, wanka ta somayi tana jiran shigowansa, bai shigo gidan ba sai bayan sallar Isha ya iske sashinta a bude bai yi mamaki ba, kai tsaye ya nufi dakin music na tashi a hankali tana gaban madubi tana shafe shafe, jin motsi a bayantane ya sanyata waigawa da fara’arta take fadin honey ashe ka dawo, ta mike zata kai masa runguma ya goce, ta sha mur tana fadin me laifina a nan? Daga ina kike? Kai ya kamata ayi ma wannan tambayar bani ba, wulakanci da rashin mutuncin ka sun isheni don kaga ina hakuri da kai? Kai idan ka fita ka dawo ina tsareka da tambayoyin rainin hankali? Baki bani amsata ba, daga ina kike? Kaga mallam saurara mani ba tashin hankali nazo yi ba, baki tashi dawowa ba sai cikin dare uban wa ya baki izinin fita? Ta toshe kunnuwan ta biyun tanata hayagaga ba yanda ya iya ya fice ya bar mata gurin, shima yayi shirin kwanciya barci. Da yace in soma shiri shin me zan hada? Allah ya sani bana doki sam musamman idan na tuna Mama da Suhaila, shin ina zan zauna ma tukunna? Yana da kyau inyiwa aunty Zarah sallama kafin mu bar garin na ayyana hakan a raina, gashi yau baizo ba balle in nemi izini, wannan dalilin ne ya sanyani kiran wayarsa, na jima shiru, shi kam baya kusa yana can ana ta siyayyan auran Sa’adah, Suhaila ce tazo wucewa ta dauki wayar ganin lambar mai lakanin my life a jiki ya dauki hankalinta, hello na fadi jin an dauki wayar, yau ban gankaba, a gidan uban wa zaki ganshi ke wacece? Nayi ‘yar dariya gami dacewa madam dinsa ce ok baki da labari hala? Kar ki 6atan lokaci please bani mijina sauri nake, karyar banza ta fadi tana huci matarsa daya ce a duniya ki bar mafarki, tabbas wannan haka yake yana da matar data wuce ni? Jeki gurinsa don karin bayani kar muryarki ta sanyamin ciwon kai, na katse wayar na ajiye sannan na koma kan harkokina, ta zauna a gurin zuciyarta na tukuki shi yasa bai damu da ita ba ashe aure gareshi, bari zai dawo ya sameni a gidan nan ai, ta fadi tana jijiga kafa da kafadu tamkar tanajiran house boy, ba jimawa kiran Sa’adah ya shigo min ina murna na daga da azamata yayin da nake fadin amarya kin 6uya, yayi gyaran murya sannan ya fara da cewa baby nine, na manta wayata a gidane yau duk ban jiki ba ina busy ne, ya kike? Lfy kalau yaushe zaka shigo? Wani abu ne? Dama gidan aunty Zarah zani, baby manya baza’a nemeni don anyi kewata ba sai don za’aje yawo ko? Ba haka bane, kin samu Seemah a waya? Ah ah idan na kira bata dauka, ok zanzo gobe har gidanta sai muje ko? Na gyada kai kawai tamkar yana gabana sannan ya mikawa mai wayar, big Sis ya amarci? Nayi dariya ina fadin munci girma an barwa ‘yan baya, uhm uhm a dai tsegunta mani, no wannan tsakanin mu ne ya angwon? Yana gaishe da ke, ina amsawa, a san min sirrin pls naga big bros ‘yan kwanakin nan rayuwar ta sauya masa kullum cikin nishadi yake, ba ruwana tambayeshi dai, wa ni na isa? Zan kiraki anjima yanzun muna busy ne, ta katse wayar inaji a raina akwai alkhairi a gaba nasoma sakin layina ‘yan uwansa na neman siyeni…
Kai wallahi ka shiga uku woman wrapper baka nan baka can, baka nan, kwarton Hameedah ashe kana ma da mata a waje don ka 6ata mani rayuwa ka aureni, ya kara volume din Tv yana kallo bai bi ta kanta ba, ta cakumi kwalarsa tana mita wanda yajanyo hankalin mutan gidan garesu, Mama ta saki salati tana tafa hannu, me zanji aure Muhsin? Mama gata nan mai fadi tambayeta, kai me yasa baka da adalcine? Kiyi hakuri Suhaila barni dashi, dalla yi mani shuru munafukar banza har da sa hannunki ai, ya wanka mata mari cikin zafin rai gami da nunata da yatsa, cin fuskarki ya tsaya a kaina ban hada Mama da kowa, ta rike kuncin tana fadin dama ai a nono ka sha dan bala’i kawai, wanda be gaji arzikiba, ya zaro belt Ummu ta ririke tana tausansa, kyaleshi mana wanda bai yi sa’an uwa ba, ya saki belt din sannan ya tunkarota ta fice da sauri tana fadin waye bai san tambadadiya bace uwar taka? Duk suka rufa masu baya tana kokarin karasawa bakin gate ta tsinkayi lafuzansa mafi muni gareta, na sakeki saki uku, sai ki nemi mahaukaci daidai ke kunfi dacewa, har ta kai tsakiyar titi abin ya daketa bazata ta tsaya cak motar data taho tayi gaba da ita, shi kwa ya bar gurin Sa’adah ce ta kai mata dauki,
Mai motan ma mutumin kirki ya tsaya Sa’adah ta shiryo suka kaita asibiti tare, ta bugu sosai ba sauki gashi tayi losin jini da karaya a kafada kafa da hannu… Mun fito daga gidansu aunty Zarah ya dau hanyar gidansu Seemah, me hadinki da mai G din da naji tana fadi? Kin raina arzikina ne? Na kalli fuskarsa ina girgiza kaina, namijin daya san ra’ayina kan auran talaka,
kayan datace ki dauka fa? Shi ya kawo min su tun kwanakin baya nace ta ajiyasu ni nama mantasu, yayi ajiyar zuciya sannan ya kara da cewa ina da kishi baby please ki kyautar dasu idan ba haka ba sai inga tamkar bana kokari ne kanki, ina kaunar matata ta sanya abin da Allah ya hore mani shi zai nuna mani cewa kin yaba karfina, na jinjina kai ina dada gwada numbar Seemah, har muka karasa gidan no answer, mai gadinta ya bude yana rawan jiki madam barka da zuwa, na kalli mijina kawai shima ya fahimci manufata(ya dauka mai gidan ce), muka zauna a reception muna jiranta, katon gida wanda aka ci zarafin naira gurin tsayar da ginin, kwakwalwata ma bazata iya kiyasta abin da aka kashe gurin samar da kayan cikinsa ba, komai na waje ne ni kam irin wannan rayuwar nake gudu, wucewan awa daya shiru ya kalli agogwansa zai yi magana sai ga tsayuwar mota a farfajiyar gidan da akalla zata dauki motoci 20, itace a gaba wata tana rike da hand bag dinta, mai makulin mota daban sannan wasu suka dauko ledoji daban daban, na mike da dan murnata ina fadin twinny idonki kenan? Ta zaro bakin glass din idanunta tana gyara tsayuwarta, shigarta cikin black suit mai katuwar Riga har gwiwa, ta daure gashin da hair band gami da sauke shi baya, kan ba dankwali, pin earring ta sa, kafafun cikin cover shoe mai tsini da sauri body guards din nata suka bar gurin, aka yamutsa fuska sannan a dakile naji tace sannu sannan ta wucemu, bayan wasu ‘yan dakiku na kira wayarta wannan karan ta dauka tana fadin waye, uwarkice na bata amsa zaki fito ki kulamu koko sai rai ya 6aci? He he he! Bakice min zakizo ba yau babu ku a list dina ya zan maku? Ta kuma tunzurani, shi yasa naketa kira kika ki dauka? To ai ni yanzun bani da lambar kowa kuma, dalili ban son takura da lekan asiri, na kalleshi da yake a hands free wayar take ya ma rasa abin cewa yanda yaso sanin wani abu game da gidan abin yaci tura, da yake dakikiyace batasan cikin hatsari take ba, gidan duk anyi wiring da computer, ya jani muka fice yama rasa ta cewa ni kam sai jan tsaki nake akai akai, yana tuki da hannu daya ya riko hannuna daya da dayan hannun, shima fuskarsa babu walwala yake fadin ki kwantar da hankalinki giyar daula ke dibanta, nayi dan murmushi shi mai kau da kai ne kan lamuran da suka shafeshi, ya kaini gida ya ajiye yana fadin gobe Allaah’s willing zan zo mu tafi ko? Ina? nayi tambayar a dan kidime? Yayi dan murmushi sannan ya kara da cewa ba kanki zan cire ba kano zamu gurin Baba Lawal, na yi ajiuar zuciya ban kaunar yace zai kaini gurin Mama bale mu hadu da Suhaila, tare muka shiga cikin gidan ya gaida iyayena, inaji yana shaida masu tafiyarmu gobe, Masha Allah cewan daddy don jibi mu zamu bar kasar, na daskare a tsaye bugun zuciyata ta tsananta, waton idan matasala muka samu da dangin miji can ta matse mana tunda zasu tsalleke su barmu a kasar, Baby! Muryar mummyce ta katse mani tunani na fahimci inda tasa gaba, haka na fito ko mayafi babu don yi masa rakiya, gobe zan rabu da wayanda suka zame mani dole, ya dan tsira mani idanu ko me ya dauki hankalinsa haka, shigar ta kar6eki ya fadi yana kokarin shiga mota, sai ya sanyani ma kallon kaina ina mamaki, doguwar rigace mai hula ruwan makuba mai duwatsu suna walwali, don Allah kar ki ja aji goban nan ban son muyi latti, na gyada masa kai sai da ya tafi sannan na juya na shige cikin gidan… Nasiha sosai har naji babu dadi, kuka nake babu kakautawa, kenan bani da kowa a Naija sai aunty Zarah, zamu rika waya kuma zamu ke6e ranakun zuwa ganinku da da yanzun ba daya bane, na yarda dake baby don’t fall my hands cewar daddy, ko break banyi ba muna cikin wannan halin sai ga sallamarsa, Rihab ta makalkaleni tana kuka, IB na daga gefe yayi shiru shima alaman jimami, ina durkushe a gabansu shi da kansa IB ya taimaka masa suka zuba akwatina na da wasu ‘yan kayayyakina a boot, mummy tace in bar sauran zasu kai gurin aunty Zarah duk sanda na tare in kwashe abuna, a sanyaye na mike kwalla ya cikan idanu har bai da niyar tsayawa, wannan dalilin ne ya sanya na kasa ganin gabana sosai ya rikoni muka shige motan, daddy na dada jadada masa ni din amanace a hannunsa, ya tayar muka fice a nutse tamkar ince ban yin auren, yau na soma tsanan bankwana da masoya, jefi jefi yake dan kallonta tausayinta fal zuciyarsa, tana barci tana ajiyar zuciya alaman taci kuka tamkar ‘yar goye. Muna tsakanin kano da Zariya wasu tarkacan da aka zuba bisa titin suka haddasa ma motarmu paci, duk muka sauko don ganin abin da za’a yi, zauna nan baby ya fadi sanda yake mikomin dutse, ya soma kokarin canza taya ina zaune ina kallonsa, Allah kadai yasan daga inda suka pilo ni dai ganinsu nayi a kanmu da bindigogi, dayan ya cafkoni yana muzurai Muhsin kam suka saita masa bindiga a ka su biyu, na ukun dake rike dani ya ciran dankwali sai wasu abubuwa yake kokarin yi min ina magiya bai daina ba, Muhsin ne ya daki tsakiyar kansa su kuwa suka harbeshi, na saki kuka ina jijigashi shiru ga titin ya ratso ta tsakiya guri mai kauron mutane, na hudun sune ya karaso da shigarsu iri daya 3 sun rufe fuska amma shi tashi a bayyane, kadan kika gani yarinya ya fadi yana dariyar keta, da sauri na daga kaina ina fadin ah ah Bilal, zan koya maki hankali na sanya ihu mai kara, lafiya? Ya fadi a rikice yana jijigani na rungumeshi ina kuka ni addu’ar ma na manta ya ake karantawa, shi ya rika karanto min ina maimaitawa, a nutse na bude idanuna sai a lokacin hankalina ya kwanta, ina ne nan na yi tambayar ian zare idanu a tsorace don na ganmu cikin mota, mun kusan kaiwa kano ke kika sanyani yin parking, menene kike kuka cikin barci? Na girgiza kaina ina kokarin goge fuskata babu na fadi, fadi mana inajin harbin zuciyarki na sausauta runguman da nayi masa ina kokarin janyewa, ya tofa mani addu’a a tsakiyar kai, da dubara na koma kan kujerata ina lekan window, nan na gani a mafarki na kuwa, don Allah ka ja mu bar gurin nan, menene wai? Babu komai na dai kosa ne mukai gurin, yayi mata key hankalinsa na kaina na kasa koda gyangyadi ne har muka kai tsakiyar badalawa, naga busy ko ina sannan na limshe idanuna… Mun samu tarba ta musamman a state road, matansa 2 masu halin dattako da sanin ya kamata, duka ‘ya’yan gidan sunyi aure don haka ba yaro sai masu gidan da jikoki da akan kawo hutu, cima har turewa nayi serve your self, kamin mu bar palo har an kimtsa mana masauki da kayanmu a ciki, gasu da yalwan fili da dakuna vacant, na shige na watsa ruwa gami da sauya kaya, duk yanda naso in kau da damuwa a raina abin yaci tura, ban son abin da zai assasa min tashin hankali amma duk juriyata da kokarin dannewa yau zuciyar bazata iya daukan lamuran ba, haka ya shigo ya taddani kwance kasala da zazza6i mai zafi sun kadani, ina ganin damuwa karara a fuskarsa, Oh ho ho baby ban zo zama ba fa, kuma bazan iya tafiya in barki cikin wannan yanayin ba, na zuba masa idanu kawai don na kasa furta wata kalma, ya fice ya barni idanuna suka ci gaba da zubar da kwalla, ba jimawa ya dawo dauke da ledar magunguna, ya jiko towel da ruwan sanyi yana shafa min a jiki, can ya maidashi kan goshina yana dan min hira wai don kar kadaici ya jefani cikin wani hali, baby baku gaisa da maigidan ba mun iso baya nan, gaki kuma an binciki file dinki Allah ya tashi kafadunki gobe Allaah’s willing in tafi, na rike hannunsa ina maimaita kalman gobe, ya gyada kai, lallai ma so yake kadaici yayi ajalina, ga gida babu sa’an ni na, ga rashin sabo, kin yi shiru baby akwai damuwa ko? Nayi dan murmushi ya kammala ya tisani a gaba na dan ci abinci babu laifi sannan ya debo magunguna na sha, su gwago suka shigo suka gaisheni da jiki sannan suka fice, ya kwanto gefena a rigingine yana ci gaba da labarinsa daya dauki hankalina, har ban san sanda barci ya daukeni ba, sai farkawa nayi na ganmu cikin blanket daya na koma barci abuna…
Shigarta cikin Short royal blue armless gown mai many an flowers uku Jere a gaban, tayi parking gashin da katon shima Royal blue, ta hakimce cikin katuwar sofa tana gyara heels din kafarta masu tudun gaske, chef dinta Jeremiah ya danna door bell , shit am late cewarta tana Jan tsaki, ya kuyana fadin can I serve you ? Wucewar mintina goma ta samu abin cewa yana nan tsaye gudun kar ya bar gurin ta zuba masa rashin mutunci, am not eatin now, make 3 different intercontinental dishes and save my ears from that annoying door Bell, makeup artist dinta ta kuma mata touchups sannan ta dau costomised mark Spenser bag dinta ta nufi hanyar waje da sun shade tana tauna gum, she looks so breathtaking, ta nufi mota kirar Bentley dai dai zata Shiga motar su ukun suka karaso da Sauri cikin bakakyan suit, 1 ya karbi jakar gami da bude mata owners corner, na 2 ya shige driver’s sit gami da mata key na ya 3ukun ya zauna gefan drivern, ya ja suka fice.
Babu yanda su daddy basuyi ba don su sameta a waya amma abin ya ci tura, kiran duniyar nan bata dauka ba, mummy ta yi fushi tana fadin ita wannan dama ai batasan darajar mutane ba, tun da aka kaita waya kuma jin duriyarta? Kaga barta kawai halin mutum jarinsa, bai yuwa mu kwashi kafa zuwa gidanta yau kwana 5 da aka kaita, haka dai zamu cewan daddy, ba yanda ta iya suka biya kafin su wuce airport, da kyar security ya bude suka shiga basu samu ganinta ba wai madam tace ace ma bakinta na yau tana busy, daddy ya kulu haka suka wuce CANADA basu hadu ba, mutuniyar tana can anai mata gyaran fata cikin daya daga cikin dakunanta na alfarma, kullum wayarta a silent take bari, don haka sai ya karaci ringing din ko oho…
Jikin da sauki washegari amma ina gani bazan bari ya wuce yau din nan ba sai ya dan kwana 2 yanda zuwa lokacin nima nayi sabo da mutan gidan, wannan nema ya sanyani dan langa6e masa, cin abinci sai yayi da gaske, Baban kano yayi murnar ganinmu yayita adduo’i da jan kunne, yammacin ranar muka fita shan iska ya zaga dani unguwanni wai kar in fita a bakunta in 6ace, muna harsu zoo road, comissioner road, aba road, lamido cresent, aliance fance, gidan dan hausa, gidan B minister, gidan makama, tun ina rike inda muke shiga har na gaji na daina, me yasa zaka tafi ka barni a nan? Ina da dalilai kuma zaman mu tare yanzun abune mai wuya, hatsarine, baka son matarka ta san ka kara wata ko? Ni ban ce ba kar ki zargeni, burina a ganmu tare a rika nunani ana fadin ga mijin Hameedah amma ba yanzun ba, shi da yake da niyar shiga lamuran gidan Seemah don bincike, idan aka kasa samunsa sai a koma kan matarsa, yafison har sai an kai shari’ karshe tukunna.
Ya jima zaune shi kadai cikin masters bedroom dinsa yana saka da warwara, shi mutum ne mai alkawari da tsayawa kan cikashi, amma a wannan gabar an so a samu Matsala, tabbas ya so Hameedah so na gaske, kuma yayi alwashin in har ya samu auranta bazai cika alkawarin daya daukar wa Wanda ya turoshi ga Hameedah ba, saboda lokaci daya Allah ya jarabceshi da tsanin sonta, she is jovial and her ways have changed him with out realizing it, amma he ended up with seemah who is direct opposite of her.
Dakin yayi tsit in kika dauke dadadan muryar Mrs Bilal dake rera wakar Rihanah yayin da mai gyara ta dukufa gurin fito da madam dinta, ko wata ba’ayi da auran su ba amma ta canza, said ki rantse ba ‘yar Nigeria bace, asali akwai kyau da murjewa ga kuma ta hadu da gidan hutu, yau kuma gyaran gashi ake…
iyarsa ke assuring din idan yayi hakuri da ita she can be his Hameedah, anya kuwa? Wannan ne ya Santa shi mikewa gami da nufan toilet, yana da hakuri amma don’t step on his toes dai, a yanda ya Santa she’s stupid and not reasonable, amma zai zuba mata idanu yaga iya gudun ruwanta, brush kawai yayi gami da wanke fuska sannan ya goge da towel, wayarsa fake ringing ce ta maida shi dakin, wats up Hanks ya fadi daidai sanda ya karata a kunne, Sir we are in a house close to the central mosque, madam is seeing a male friend, OK just keep and eye an carry me along cewarsa, ya katse wayar gami da danna naurar kiran chef, shi fa irin abin da bai so kenan, amma idan yayi wasa zai ci ubanta be, rabon sa da ita tun gurin dinnern su, bai ma yi introducing dinta ga ma’aikata ba amma she already did that herself, ya ja tsaki yana kallon agogo daidai sanda Jeremiah ke fadin breakfast is served Sir…
Kafafuna na zuro a hankali ina kokarin sanya flat shoes dina, ya dau jakarsa yana kallona, nifa ban son kallo na fadi ina turo baki, yayi ‘yar dariya gami da yin gaba na rufa masa baya ina gyara rollin din kaina, baby! Na’am, daga yau kar ki kara fita da wannan shigar, na langabe kai ina kada idanu alamun rashin son abin da zai ce, please don’t question me kawai obey kinji? Zan ma Sadeeya magana a dinko maki manyan hijabs da niqab, in dai zaki fita you must wear them, na kada kai a sanyaye, yayi murushi yana tsareni da idanu, ko ba kya son karatun? Da sauri nace ina so, good, I don’t want you exposed, zamu karbi jamb kiyi this year ki fara school OK? Wai a kano zan zauna? Yeah, ba kya so? I dnt say so, nima I don’t know yet sai na nutsu bcs I hv alot to do right now, baby you are brainy, zakiyi aminu kano college of legal studies (diploma) ko Buk? Remember we might not be here for long, legal zanyi Science of Qur’an, good, kinga you will be busy before I decide on where to stay, na jinjina masa kai kawai, jamb muka fara zuwa karba sannan ya wuce damu gidan Sadeeya dake nassarawa GRA, Isar mu ke da wuya yaranta suka taho da gudu suka rungume kawun su, tana daga bakin kofar palorn tana dariya,kar Ku karyan Bro ai kwa bari ya kashe motar tukunna ko? Daga bude mota sai…. Maganar ta katse sanda ta dora idanunta kaina, fara’ar ta karu, sannan ta nufomu nima na karasa gareta ina murmushi, rungumeni tayi tana fadin marhaba, Aman, Ziyan, Raihan, Silan and Farhan oya ga new aunty Uncle ya kawo, suka taho gareni suna kallona, na jasu a jiki mukayi cikin gidan, deeya am not staying long, don’t Allaah kuje da ita taga kasuwa ta zabi choice dinta, sannan zata kafe jamb reg kuma, gata nan tace legal zatayi, ihu da tsalle naga tayi tana murna yaran na tayata, aifa su deeya ba’a San an girma ba, ta watsa masa harara tana dariya, akwai samosa ,cakes, spring rolls da fried rice me zan kawo maku? Anzo gurin kuma marowaciya cewarsa yana daga Autanta Farhan sama yana dariya, rabu dashi kawo kayan dadi, Aman ta tsintsire da dariya gami da cewa new aunty ma nason kayan dadi, duk suka kwashe da dariya suna kyalkyalawa Muhsin na tayasau…
Ita kadai gareni yanzun cewar Mal Isah, kwanaki mamarta ta rasu a hatsarin mota, na san komai game da Ku Isah, sai da nayi binciken daya gamsar dani sannan na zo gareka, ya kalli Rihab dake tsotsan loli pop tana kallon titi, pretty ga daddy na gaisheki cewar Alhaji Abdullahi Buba yana nuna biological mahaifinta, ta karasa gurinsa tana kallo tamkar Sabin halitta, you like him? Ta tsira ma daddyn idanu tana kada kai, sannan ya juya zai dauko kayanta a boot, yana son yarinyar tamkar kar su rabu, Dan zaman da sukayi da ita sun yi sabo sosai, ba don kar ya zama azalimi ba da bai dawo da ita ba, Allaah yasa baban ya bata better future dai, daddy! Yaji ta furta cikin ihu tana kokarin zuwa gareshi, ya waiwaya yana kallonta, daddy I don’t like it here, tohhhhh! Cewarsa yana kallon mal Isah dake kwalla, pretty zan dawo kinji? Ta Noke kafada tana matsar kwalla, ya zura masu idanu yana kallon ikon Allaah, kid u need to bond with your dad OK? Ai bata ma San yana yi ba ta makalkakeshi tana kuka mal Isah nayi, jikin sa yayi sanyi yana kallon su, Alhaji jeka da ita kawai, Isah ba za’ayi haka ba, zan wuce da ita yanzun amma lokaci lokaci zan San yanda zanyi ta amince ko hutu ne ta rikayi tare da kai har ta saba da kai , nagode Alhaji, daddy ya masa kyautan kudi sannan suka wuce …
MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
27…
Zarah manya, nifa ba yaro bane kuma am seriously serious, ta karkata kai tana kallon daddy , IB da Rihab dake ball a filin gidan, Alhaji Mukhtar kenan, shima yace Zarah kenan, tayi ‘yar dariyarta tana kallon agogon dake daure bisa tsintsiyar hannunta, I still don’t understand why me daddyn IB, I have a lot of annoying secret da nake jin zai hanaka ganin wannan kyawun nawa dake rudarka, I won’t ba a mother and am not good for you, ya dafe kai yana kallon ta, ni dai ina sonki a haka, kuma yarana uku, akwai Mardiya da Kuaibah kannan IB a George town Guyana (South America) gurin friend dina, ina ganin ai sun ishe ni, wayar tace ta katse abin da take niyar cewa, OK I will be on my way kawai tace sannan ta katse wayar, I will be going Laurah is back, suka mike zai rakata motarta, yaushe zaku bar Lag? Jibi zamu wuce CANADA, by then Allaah’s willing na gama tattara komai, am the reason we are still in 9ja, OK then Allaah ya kai Ku lafiya, Zarah! Ya kira sunanta da wani shauki yana jin kansa tamkar dan 30, ta dan dakata yana kallon sa, I love u, please thnik about it kinji? Ta kada kai sannan ta tada motar…
A rayuwa akawai mutanan da har in mutu suna raina, Sumayyah Lawan Nuhu, you are more of a Sister than a friend, you left your foot prints in my , Uhubiki fillah, Allah ya raya Abdullah da Fateemah, yasa su gaji kwakwalwarki
Lallai rayuwa juyi juyi kwado ya fada a ruwan zafi, kwance take kan ‘yar ficiciyar gadon asibiti hannunta da jonin ruwa, barcin wahala take, zuwa yanzun batasan ma inda kanta yake ba sam, ta yi duhu duk ta lalace tamkar ba Suhailar nan mai izza da gadara ba, yau ina kyawun? Ina lafiyar da take takama da ita? Ina gayun da samarin dake hure mata kunne ? Idan baka gode wa ni’imar Allah ba ka gode wa azabarsa, Likita ya shigo ya dan dudubata yana rubuce rubucensa, ya kalli Autah da ta tsaresu da idanu gami da cewa get me your elder Sis, ta kada kai gami da goge kwallar da suka tarun mata da bayan hannunta tana Jan majina. Kwanaki uku kenan da zuwan su orthopedic kan karayar Suhailah, Autah da Sa’adah me kan lamuran, ita Sa’adahan ce mai shige da fice don ganin komai ya zama normal yayin da Autah ke jinyarta…
There is no progress, she doesn’t look fine and daz y I asked for you, get the money fast or else… Or else what? You will have to fly her abroad, if its too late she will have her legs cut off cewarsa yana hada files don zuwa round, ta dafe goshi tana jin numfashin ma yana mata wuyar shaka, ina zata samo kudaden nan? Ita da take bautar kasa allowance dinta bai taka kara ya karye ba, na hospital ma da take samu a matsayinta na practising doctor #30,000 ne kuma tuni tayi investing da dan abin da ta samu, wanda zai iya aikin nan yana fushi, Mama da ke iya sanya shi ko ta hana kuma ta dawo daga rakiyar Suhailar, ta karasa ward din zuciyarta dauke da alamura masu yawa, toh wa zata kai wa koken ta? Muhammad Sultan kuma na bayan abokinsa son bakinsu daya…
Na gyara kwanciyata ina kallonsa yana ta shiri, wucewar mintina 10 ya dawo gefan gadon yana gyara tie, baby! Na’am, kar in tafi ne? Ni ban ce ba, OK don’t give me those looks, muje inyi sallama da su baba, jakarsa na dauka muka nufi general parlor din gidan, yana gaba na rufa masa baya, sun yi sallama da mutan gidan sannan muka nufi parking lot, ya shige motar yayin da na bude gefan driver na ajiye masa brief case din, baby! Ya furta a sanyaye idanunsa kur a kaina, na ‘am, zan yi missing dinki will you? Na sada kaina kasa ina wasa da zoban yatsata, kin yi shiru? A wannan gabar bazan ce ba abin da nake ji ba, it feels normal irin nayi bako din nan zai tafi, yayi yake gami da cewa baki damu ba kenan, please don’t put words into my mouth, OK then, don’t Allaah feel free da kowa especially Deeya, zakiji dadin kano, na kada kai ina daga masa hannu, kuma ki rika sanar dani idan akwai damuwa, na kuma kada kai a karo na barkatai, ina nan tsaye ya ja ya fice, nayi ajiyar zuciya ina jin iska na ratsa no, yawo things on point, yau ne zuwa kasuwa da Sis Deeya muyi shopping, da dan murnata na shige ciki don daukan bag dina tunda tace tana tafe, nan zata bar su Raihan gurin kakanin su sanan mu 2 mu wuce…
Rayuwa a kano is interesting, no worries, familyn shi naji dani, zuwa wannan lokacin har hijabs dina sun zama ready, mukan yi waya lokaci lokaci, duk da dai shine karfin kiran, ban jin anything new/special game dashi, kawai dai yana burgeni kuma ina jin dadin hira dashi, nayi jamb har scores sun fito, na kosa in ganni cikin school abuna…
CANADA
Yayi murmushin sa mai kyau gami da kau da kai sannan ya soma fadin call Hameedah, daddyn IB ya zazzaro idanu yayin da take fadin Abdullah am seriously serious, ‘ya ta ce zata min kamu gurin Zarah? Ya dan yi ‘yar dariya gami da cewa tunda ubanta bashi da gwamnati ba, call baby Hameedah an tell her, ina gaya maka ka auri Zarah an gama kawai, idan bazaka iya ba let me do this for us…
LEGAL
Sis Deeya tayi parking duk muka fito daga motar, karfe nawa zaki fito lectures yau? 10 zan gama, ni fa JJC ce ,besides time table ma zan fara dubowa tukunna, yayi kyau amma ki jira in maidaki gida tunda ba dadewa zan yi ba, na kada kai sannan ko wace ta nufi department dinta, kai tsaye time table na tafi dubawa, wasu ‘yana tsirarun dalibai maza da mata cikin shigar kamala na samu gurin a tsaye, wasunsu a zazzaune, Assalamualaikum, duk suka amsa mani, don Allah time table nazo dubawa, muma shi muke jira cewar dayar su, wannan dalilin ne ya sanyani juyawa dan samun gurin zama, sahunta ne ya ankara dani, ta riko gefan zunbuleliyar hijabina tana fadin kema sabuwar dalibace? A kalla zamuyi shekaru daya da it’s, shigarta cikin katuwar hijab da niqab, ta sanya White glass da awarwaro, from her outfit zaki fahimci ‘yar gayu ce, na kada kai kawai, muka samu gurin zama ta cigaba da fadin sunana Haleemah, zan karanci Quranic science, nace wow, am Hameedah nima course dina kenan, OK, kinga yau babu class kenan ,yeah, daga nan sai ina? Zani bank sannan in jira ‘yar uwata, OK ni kuma mijina na jirana already, ban numbern ki please, mukayi exchanging contacts sannan muka rabu…
Kar ka manta cewa turaka nayi cikin rayuwar Hameedah don in samu weakness din Ubanta, na san duk daren dadewa ‘yar sa zata koma gareshi, kuma hakan ta faru, yanzun dama ta samu, nayi alwashin dukiyata da uban gidansa yayi sanadin salwantan su sai na dau fansa kan duk Wanda me karkashinsa, Wanda mukayi wa Mukhtar( dadyn IB) kadan ne, contract na baka amma ba dole nayi maka ba, me kake shiryawa ? Yayi shiru yana nazarin abin yi, shi fa gani yake bazai iya cutar da jinin Hameedah ba Sam, ko bazaka iya bane? Eh bazan iya ba ka nemi wani, Bilal me kake cewa? That guy ruined my name and reputation, na dauki tsawon shekaru 10 ina sanyaka a border inda zaku rika haduwa don ya yarda da nagartarka duk da kai ba custom bane, kar ka mance kai ba kowa bane ,tsintar ka nayi na fifitaka don zuwan wannan ranar, enough ambassador nace ban yi , ya fadi cikin daga murya, ambassador yayi kwafa gami da ficewa sannan ya doko masa kofa cikin dacin rai ya fice. Daga nesa kadan ta hango security da wata suna kokawa a bakin gate, Hanks clear the way before I go inside cewarta, da sauri guard din ya sauka don yiwa security magana, cikin zafin rai ta sauko da kanta ganin rikicin yaki karewa, ta yamutsa fuska gami da toshe hanci yayin da take kallon tsohuwar dake gefanta, shigarta cikin karamar super mai dinkin doguwar Riga, sai hijabi karami, slipass da jakar bako a hannu, ba tare da ta saurare ta ba ta soma fadin gidan nan yayi kama da Inda irinku ke zuwa? Ta tsirtar da yawu gami da shige cikin tana Jan tsaki…
[5/16, 3:14 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
28…
Yana fita ta kare ma dakin kallo, duk da dai ba abin da take iya gani tsabar duhun gurin ,ko Ina baki kirin, ginin underground ne gashi an katse connection din wuta, ta hada kai da gwiwa tana tunanin gatan data baro, a wannan lokacin Hameedah ce ke mata a rai, yarinyar is blessed, duk yanda taso cusguna mata ita ake bari a ciki, a yau taji wani irin takaici da tarin nadamahan da ya zama too late, kila bazan kara ganin wani nawa ba ta ayyana a rai tana jin fargaba sosai, irin daurin da aka ma hannayenta ne ya sanya ta ji tamkar jini baya circulating Sam, wani irin zugi igiyoyin ke mata, ga shi ta baya aka daure, haka ma kafafun sun dauru tamau, aka bude kofar ya kuma shigowa yana fadin the earlier you comply the better, cikin tsana take ce masa don’t even waste your time don bazaka samun hadin kaina ba, ya naushi bakin da karfinsa yana cizon lips dinsa, ki iya bakinki, or else.. Or else what? Ta fadi tana tofar da jini bakin ta, ka kashe ni ko? Ta yi murmushi mai ciwo gami da cewa kai kuma kayi ta zama duniyar kar ka mutu, yaja tsaki gami da ajiye mata tray din abinci yana fadin eat, ba abin da zan ci, just kill me, shurup cewarsa strictly, ta zabga masa harara tana murguda baki, ya bige bakin yana huci, I will deal with you cewarsa , iya do it you idiot ta fadi cikin daga murya, ya tsira ma kwayar idanunta ido, kyar ta kafa masa su tana hura hanci, sai kuma ya kada kai gami da ficewa a fusace, yarinyar tana da KARFIN HALI, seriously brave, babu tsoro a tattare da ita, ta daga kai sama tana kallon abin da ita kanta bazata ce gashi ba, kawai sai damuwa da dana sani su suka cika mata zuciya, Hameedah ta furta cikin whisper tana iya hango warning din data mata a gadon asibiti, Seemah irin su fa sai train dukukiya basu da lokacin matayensu, Will you find happiness with him? ta saki ajiyar zuciya gami da cewa you warned me, but Alhmdlh you are save, Allaah yasa ki gane cewa you are Lucky, Muhsin deserve you, amma zan mutu cikin tashin hankali idan bamu hadu da Hameedah na nemi gafarar ki ba, sai yanzun na fahimci irin son da mukewa juna twiny, sahun sa ne ya sanya ta saurin kallon kofar, ya shigo calmly yana fuskantar ta, sannan wani dan tsamurmurin mutum ya shigo shima, kayan wuta ya jona, a sannu aka sanya mata CD tana kallo, CD din da ambassador ya masa sending ne, jikinta ne yayi sanyi, ta dauke kai sanda ya zo karshe tana kallon sa, Baffa jeka dama aikin kenan, electrician din ya fice, ya durkusa gabanta yana kallon ta, you saw that right? Ta gyada masa kau kawai, those are my mum an siblings, what do I have to do with that? Cooperation dinki ne kawai zai sa ya sake su, who? Ya shafa kai don bazai iya gaya mata ba, oh! Uwarka ta fi nawa uban kenan? Ta tsintsire da dariya gami da cewa don’t even make that mistake, am giving up life for them, Seemah kar kiyi haka, kiran wayarsa kawai zakiyi, banda numbern kowa ka manta nayi deleting? Ya Ciro wayarsa yayin da yake fadin bari in kira maki shi toh, kar ka kuskura, why would I trust you?…
Da sauri ya fice zuciyar sa na raya masa muguwar Abu game da alhaji Bilal din, ai kam hamdala yayi ta yi da ya karasa gate lafiya, wata mota kirar Camry da aka faka daga nesa kadan ta rufa masa baya, da sauri ya daga kafa, zuciyarsa na raya masa cewa gashi nan ya sa a taho da kai, ya runtuma a guje, direban ya kara wuta ,saura kiris ya kade shi ya taka birki, a birkice baffa electrician ya kifa yana salati, yi hakuri bawan Allaah, ban zo don in cutar da kai ba, sunana Muhsin, lawyern government, ya nuna masa ID card yana murmushi, to ai kaine da abin tsoro, anya kuwa? Ko dai ka ga abin daya tsorataka a can gidan? Sai kuma yayi shiru yana kallon hanyar gidan, dama wata nake nema, wa kenan? Ya nuna masa hoton Hameedah dake wayarsa, don bashi dana Seemah, eh ita ce, ita ce wa?
Ita ce a can gidan mana, Muhsin din ya zaro idanu gami da cewa What? Matar tawa, au matarka ce ma? Wannan wani irin chakwakiya ne? Iyalina tace yayi aure kwanan nan, ban taba ganinta ba dai, amma yanzun abin daya koroni, wannan ta hoton na gani a dadaure, tab cewarsa, hukuma ce kawai zata raba mu, bakinta nata fitar da jini wallahi kuwa, Ina ka ganta? Oho, wani daki ne a karkashin kasa, bari in kira hukuma cewarsa yana lalatsa waya with all seriousness, dakata lauya, don Allaah kar ka sanyani cikin wannan badakalar, wallahi babu ruwana, nifa ban ga komai ba, ya karasa cikin kidima yayin da gumi ke tsatsafo masa, tamkar yayi dariya ya dai daure, sannan ya soma fadin shi kenan dan uwa, nagode kwarai ya fadi yana kiciniyar kinkimar kayan wutarsa days watsar, yana tafe yana waiwaye tamkar zai kifa, sai da yaci dariyarsa sannan ya ja motar ya bar unguwar…
I can never trust a criminal like you, ji kike tasss ya dauketa da mari, watch your tounge and make good use of your choice of words, jini ke fito mata ta hanci da baki, ta tafi luuuu tamkar zata kifa, kujerar dake gefanta ne ya dan tokare ta, ni ne criminal ko? Ta gyada masa kai tana kikifta idanu, ubanki shine criminal karuwa kawai, uwarka ita ce karuwa dan fashi kawai, ya kuma kai mata tafi gami da shako wuyan yana cizon labba, ta soma kakarin amai tana kifkif da idanu, bai cikata ba sai da ya gamsu cewa ta jigata, sannan ya dau ruwan sanyi karara ya tultule bottle din gaba data a kanta, ajiyar zuciya ta saki gami da bude idanun, why do you want me alive bayan kasan bazan maka amfani ba? Haka dai kika ce, ba kiga komai ba tukunna daz why, ta kada kanta dake mata dum dum tsabar ciwo gami da Jan gutun tsaki, bai kuma bi ta kanta ba ya fice…
Auntyn bataliya! ashe dai za’a neme mu? Babyn tayi murmushi gami da cewa dadina dake tsokana, dadyna dake kuma zaro zance, zamu saloon din ko an fasa? Duk yanda amarya tace, kai Sis Deeyah, kai Hameedah, muje toh don ni kaina kaikayi yake min, suka fita saloon din gyaran gashi…
The asoebi is beautiful, haka kowa ke cewa, na wa baby sending nata, saura Seemah, mummy Rahmah ta tabe baki gami da cewa nifa batun yarinyar nan ya isheni, no kar ki ce haka, ki ci gaba da yi mata addu’a, Zarah tana raina because I can’t deny the fact that am worried about her, especially kwanakin nan, har dadynsu nayi wa batun amma yace I should chill zuwa lokacin bikin ki, sai muje 9ja gaba daya, daga nan mu dubata, though tana da irritating attitude na ignoring mutane, amma ina jin wani yanayi game da ita presently, ki kara hakuri zuwa lokacin da yace din, balle ma she’s fine, I hope so, Allaah’s willing, sukayi murmushi, Zarah ta daga Ahmad dake wasa a cinyarta sama tana masa wasa, yaron yayi wayo da yawa, ya girmi watanin sa, sai bangala dariya yake…
Yunwa ke nukurkusarta, ta galabaita, ta kai idanunta ga tray din daya ajiye tana son cin abinci, amma tsoron poison take, tana gudun kar ya sanya abin da zata ci ta aikata son ransa cikin gushewar hankali, ta yi kokarin matsawa amma ta kasa, sautin sa ne ya sanyata kallon kofar tana fatan Allaah ya toni asirin sa, ya ajiye can malt da peak milk gami da cewa ga wannan albarkacin Hameedah, bata yi musu ba ,tana kallo ya bude, ya hada mata cikin cup gami da kafa mata shi a baki, ta shanye tas tana gyatsa, sai kuma ta hada kai da gwiwa tana yamutsa fuskarta data rine da jini, what? My tummy is paining me, you were stubborn an refused food for days, Allaah ya kara, ya fice gami da kullo kofar, ba jimawa fitsari ya matseta, cikin daga murya take fadin who’s there? Amma shiru ba amsa, tun tana rikewa har ta saki a jiki sannan kuka ya kwace mata…
I told u earlier, toh yanzun ya zamu yi? Get your friend Jabir ya taimaka mana da back up, hmmm lallai ma Sultan, naga alama ka dauki issue din smda wasa, ba’a kama tough criminal haka, toh ce maka akayi Semmahan cikin gidansa take? Tab, Ina tabbatar maka da cewa Idan ka shiga a halin yanzun kai za’a kama da bata masa Suna, ka bari mu sake plan, one of us have to go in there in disguise, wa kenan? Don’t know yet amma dole mu samu Seemah tukunna kafin muyi wani abin, in ba haka ba dan iskan kashe ta zai yi, bashi da asara…
Its been over 15years now, bt the taught of you and our childhood in that green short an sleeveless command children school uniform, will forever stick to my brain.. Fatima Aminu, where ever you are know that I still exist…
School life is the best.
Karar kofar ne ya firgitata, ta farka daga gyangyadin da take tana kallon sa, ya karasa shigowa gami da toshe hanci yana yamutsa fuska, why did you do it here? Tayi masa banza tana kallon kafafun ta, ya damko gashinta da hannu yana ja, ta saki kara cikin radadi tana fadin azalumi, Wanda ba zai gama da duniya lfy ba, scream all you want, no one will hear you,ta fashe da kuka tana fadin what do u gain from being a filthy idiot? Ya zazaro idanu yayin da yake fadin repeat that statement, cikin dakewa ta dada maimaitawa tana tsatsareshi da idanu, yayi dariyar mugunta gami da cewa i will deal with you, wayar sa da tayi kara ne ya sanya shi ficewa da sauri gami da turo kofar, jimawa kadan ya kuma sigowa cikin bacin rai yake kallon ta, sannan ya soma cewa you will die here, am not afraid you sin of a bitch ta galla masa harara gami da dauke kai, did you just call me that? Ya rankwashi kan yana huci, kar ka kara hada kazamin jikin ka da nawa na gaya maka, tsafta kika fini? Tunda bana kisa da sata ba, waya san irin cutar dake tattare da kai ma? Eh lallai yarinya, yau zaki yaba wa aya zakinta, ya karasa yana zare belt, ganin yana kwabe wando ne ya sanya hankalinta tashi, cikin dashashiyar murya take fadin no please don’t do these, wallahi I don’t mean it, bai saurareta ba ya ci gaba da kiciniyar cire rigarsa daidai sanda ta fashe da kuka, what? Ya fadi cikin tsawa, wasa fa nake maka, zaki san da Wanda kike dan ubanki, tana ji tana gani ya danneta bayan ya yanke igiyoyin jikinta, tun tana iya kuka har muryar ta dishe ta koma ninshi da kyar saboda irin muguntar da yake mata, Sai da ya gaji don kansa ya janye yana shafa Kansa, since you can’t comply I will have to involve Hameedah cewarsa yana sanya kayansa, ta shiga girgiza masa kai tana hawaye saboda tsabar wahala ta kasa magana, ta daga yatsunta da kyar tana kadasu alamun don’t even try it,a haka ya fice ya barta a galabaice…
The problem here is ni ya San ni sosai, Ina ga Sultan kai ya kamata ka shiga gidan nan, ni ? Yayi yambayar cikin fargaba, nooo it can’t be me, kaga dude I can’t risk my life, Muhsin ya hararesa gami da gimtse dariyar sa, toh cire kanka zai yi in ya ganka a gidansa? Who knows, kawai dai am not a good pretender, idan ma shiga kwabe mana zatayi, OK then, Ina ga Najeeb will be a better option kenan, waye hakan? Wani abokinsa da nayi bincike Kansa, yana cikin garin nan amma ban san yanda za’ayi plan din yayi aiki ba, akwai camera ne ko ta Ina a gidan sa, amma zamu jaraba, Najeeb will go in there and get him out a matsayin yana son ganinsa, kai kuma Sai ka shiga ciki ka same ta, zan jira Ku tare da su Jabeer a surroundings din, wa? Cewar Sultan cikin zaro idanu, chill dude tsokanarka nake, zan shiga kai Sai Ku jiramu a waje ko? Now you are talking, suka kyalkyale da dariya suna tafawa…
Wannan bikin sai ya balla record, idan lalenki ya bushe ki taimaka ki wanke masu Aman nasu suma kar su kwaba min shi a drum, jin ba amsa ne ya sanya ta fadin Hameedah! Na’am sis Deeyah Ina zuwa, ta daga wayarta dake kara gami da karawa a kunne tana sauraron mai magana, mikewa tayi da sauri tamkar wace aka tsikara, jikinta ne ya soma rawa, anya kuwa taji da kyau? Bilal ne kuwa? Ta sauke wayar gami da kunna videos din da yace zata gani, Seemah ne cikin wani yanayi, Sai na karshe data ganta cikin jini tana kwance a kasa tana kokarin mikewa da kyar, jikinta ne yayi sanyi, ta kirasa da sauri ta kara a kunne tana fadingl what do you want? You cewarsa strictly, sannan ya kafa mata dokoki, kar ta sake ta sanya yan sanda ko ta gaya ma wani, in kuwa ba haka ba gawar Seemah zai iso gareta…
You have to be fast, how long? 24 hours because you are coming from a far place, how do you know? I have my sources, ya katse wayar, ta zuba wa wayar idanu tana kallo tamkar wata bi can, kwakwalwarta ta gaza sarrafa idea Sam, wannan ne ya sanya ta Jan hijab, ta mance da lallen jikinta ma, purse da ATM ta zara kai tsaye tayi waje, Rayhan ta rufa mata baya tana aunty wanke min, amma ko waiwaye, hankalinta baya jikinta, napep ta tsyar ta fada ciki gami da cewa tashar motar abuja, tashar motar abuja kuma? Sai dai ta kaduna ko? Kya samu ta abujan can, kaini mallam, ba musu ya ja suka wuce, tana isa tasha da mintina 30 direban ya ja suka yi gaba, ta tsura wa titin idanu amma hankalinta na ga ‘yar uwarta, me yayi zafi? Waye Bilal? Me yake so daga gareta? Wucewar mintina na tafiya da bugawan zuciyarta tamkar zata yi bindiga, ta lalubi purse don duba time a wayar ta amma wayam, sai lokacin ta tuna ta barta a kujerar data zauna gidan su Rayhan tsabar kaduwa, ji take bata sauri, ta hada kai da gwiwa tana karanto duk addu’ar da tazo mata don samun nutsuwa…
Mummy kinga bata wanke min ba kuma aunty Aman taki zuba mana ruwa a buta, wai nata bai bushe ba, muje ki gani cewarta sannan suka koma Palon, ke ina auntynku ta shiga ta bar wayarta na ringing? Ni ban sani ba cewar Ziyan, oho inji Aman, Silan ta miko hannayenta data kwabe bakin lalen tana fadin mummy yayi kyau? Ban sani ba, ban ce ki zauna guri daya ba kar ki bata jikin ki? Mummy na Rayhan fa naje gani ban sani ba na fada kanta, ai kun ji dadi, ba wace zata bini biki da wannan shirmen, muje in wanke maku jor, karar wayar ne ya kuma daukan hankalinta, u karasa gami da karawa a kunne, sorry Haleemah, ta manta wayar a gida ne, suka gaisa sannan ta katse wayar, har ta wanke masu ta koma kitchen ta yi serving yaran abinci(lunch), wayarta ta shiga ringing, ke fa Mardiya dadina dake takura, ta ayyana hakan a ranta gami da kara wayar a kunne, Deeyah kice Hameedah tazo muje karbo ankon mu don Allaah, toh! Ai bata nan na zaci gurinku ta nufa, kuje da Hafsah mana, Sharada ne gadan ‘yan mata, shagon Bangis zaku tambaya, ta ajiye wayar tana tsoron kar fa wani abin Hameedah ke 6oyewa, ina taje ana tare dazun nan ana raha? Ni don Allaah ya gama case din nan yazo ya tafi da abarsa kar fargaba yayi ajalina,ta dai basar da batun kan cewa ta koma family house ne sannan ta ci gaba da ayyukan ta…
Suna karsawa Kaduna ya saukesu, ta samu bank ta ciri kudi sannan ta soma Neman motar abuja, zuwa lokacin magariba ta kawo kai, Allaah Allaah take ta samu da wuri ta nufi gifan Bilal kai tsaye, don a yanda take jin zuciyarta, ba zata iya branchig ko Ina ba, wucewar awa daya sannan ta samu wata mota data fito daga zamfara zata abuja, ta shiga suka day hanya…
Wa nake gani kaman Najeeb? Ya bashi hannu suka tafa suna murnar sake haduwa, lallai Bilal kana hutawar ka, irin wannan daula haka? Haka dai kace, ai kai ma ba daga nan ba, akwai labari ne? Da dumi duminta kuwa, wani contract na kawo, bari ina zuwa, cikin hikima ya wa Muhsin sending message, kofar baya camera daya ce ,kuma tana kallon gefe ne, muje ciki toh yafi sirri cewar Bilal din, suka shige , daidai wannan lokacin Jabeer da tawagar sa suka karaso surroundings din gidan, karkashin jagorancin Muhammad Sultan, Muhsin din da sanda ya nufi cikin gidan da yake dare ne, babu takalma a kafafun shi gudun kar suyi kara, taku daya biyu sai ya dan dakata, da haka ya karasa daidai kofar da Najeeb take zaton ta nan underground din yake, cikin rashin sa’a ya bigi cameran dake bayansa tayi kara, da sauri ya doka mata dutse ta dauke sannan ya labe a bayan wata kofa yana jiran mai kawo hari, jin security alert be ya sanyashi mikewa zunbur, sannan ya soma dadanna waya, lafiya Bilal? Wannan karar ba haka nan naji ta ba, toooh! Ya kara wayar a kunnansa gami da bada order kai tsaye, sannan ya fuskanci Najeeb amma yana jin wani yanayi a attare da shi, ya dai? Kalau, me ka gani? Bilal din da na sani ba haka yake ba, akwai damuwa ne? Yayi yake gami da cewa Najeeeeeeeeb! Dadina da kai saurin karantar mutane, shima murmushin yayi gami da cewa mallamin ilm Nafs fa ake gaya maka, what are you hiding? Gidan nan da ba haka yake ba, yanzun kuwa ko ina na waiga sai inga securities, Najeeb yanzun ba lokacin hirar nan bane, shikenan ai, yauwa ka tuna Tina? Yarinyar da kukayi aiki a asubitin Germany tare, Oooo wannan Canadian din, yeah, hmmm Najeeb baka canza ba, wannan alakar ai ta wuce, haka dai kace, mun yi magana da ita jiya, Bilal kana da ‘ya mace gurinta, gumi ne ya tsasafo masa, hirar ta mika har ya shashantar da batun security, ya maida hankalinsa kacokan kan Najeeb…
Jin hirarrakin su ne ya sanya shi labewa jikin kofar, ya leka yana hangyan su su uku, sun dau awanni 2 suna tattauna matsalarsu, hakan ya hanashi barin gurin, kafafunsa ne suka sage, ya yi tsit yana fatan kar ya fadi a gurin, ba jimawa suka mike don komawa inda ya kamata ko wannansu ya tsaya, mutum daya suka bari shima rike da bindiga, ya ciro wata igiyar wuta a aljihunsa sannan ya linkata 2, ya faki idanun mutumin, sai da ya tabbata ya zauna don hutawa gami da juya masa baya sannan da sanda ya karasa ya damki wuyar, cikin zafin nama ya shakesa da igiyar, dambe sosai sukayi sannan ya soma fadin who are you and what do you want? Key, which key? Key to the underground, da sauri ya mika masa, good, zan yi freeing dinka, amma don’t do anything stupid, ba ni kadai bane, akwai military men kewaye da gidan nan suna jira in dauko ta su shigo, ya sakesa sannan ya nuna masa hanyar zuwa dakin, yafiyace ta mintuna 10 kafin suka karasa, baza ki taba tunanin akwai mai rai cikin gurin ba, yana shiga ta dago kai a galabaice tana Jan numfashinta dake Neman daukewa, why Muhsin? Hameedah needs you kasan haka ko? Yeah kuma bazata taba yin rayuwa mai dadi ba idan babu ke, ya soma kokarin daukarta yana fadin komai yazo karshe, Allaah yasa cewarta cikin jimamin yanda za’ayi su fita daga gidan, wayarsa CE tayi kara ya dauka ganin Baba Lawal ne, bamuga Hameedah, what cewar sa cikin kaduwa, ya kalli agogon dake daure bisa tsintsiyar hannun sa yana calculating lokacin da aka soma nemanta, noooo, something is wrong cewarsa cikin confusion, Hameedah can not be missing, I dnt think she disappeared its Bilal, he have something to do with her missing, ya kirata dazun…ya tari numfashin ta ta hanyar fadin dam it cikin tashin sense, kuma na San he want her for an exchange, ka tafi kaeai ni tawa ta kare, bai tsaya sauraron komai ba ya sunkuceta suka nufi waje, wani irin kara na security alart ya karade gidan, zunbur ya Mike gami da nufar waje yana, ya dai? Najeeb wani ya shigo min gida, shima ya rufa masa baya zuciyarsa dauke da fatan Allaah yasa sun fita already…
Oh! Wayyo, wait cewarta cikin radadi, what? Kafafuna ka matse min su, my wounds, ya sauketa a parking lot yana haki saboda irin tafiyar da suka yi cikin sauri, sorry cewarsa yana kallon yanda duk ta canza cikin haskyan fitilun da suka maida gidan tamkar da rana ne, ko ina tar, Oya let’s move ya fadi daidai sanda ya durkusa zai dauketa, not so fast cewar muryar data katse shi daga bayansu, ya waiga don tabbatar da zaton sa, yayi dariya mai isar sa gami da cewa kana zaton zaka shigo ka fita Scot free ko? Kayi kuskure yaro, ba’a siga gonata a tsira,a tsaye yake a kofar kasaitaciyar reception din gidansa, ya zuba hannayen sa cikin aljihu yana kallon su, Najeeb dake gefansa ya zuba wa sarautar Allaah idanu, shigarsa cikin Pakistan forest green masu kyan daukan hankali, kafafun rufe cikin cover shoe na maza, kallo daya za kiyi masa ki fahimci irin class dinsa, ya yi taku biyu zuwa dab dasu, sannan ya warci bindiga a hannun daya daga cikin securities din da suka taru gurin, ya kuma yin dariya yana kallon Rolex din dake daure tsintsiyar hannun sa, you have the courage to break a law, eh lawyer? Amma fa ka burgeni jarumi,Najeeb kasa cewa komai yayi don deal dinsu shine zai masu hanya zuwa cikin gidan, amma duk abin da zai biyo baya babu ruwansa, Semmah sai ki shaida mutuwar jarumin mu na yau cewarsa ,fuskar dauke da fara’a yayin da ya saita bindigar sa kan Muhsin,tsit kike ji kowa na kallan kallo, cikin radadin daya isheta take fadin kar ka tsaya kallo please, INA son ka koma ga matarka lafiya, dab yake da pulling trigger daidai sanda ta sako kai parking lot tana fadin Nooooooooooooooo cikin kidima, wannan ne ya Sanya shi tsayawa cak, sannan kallo ya koma kanta, shigarta cikin doguwar riga baka da sky blue hijab har kasa, kafafun cikin takalma bakake masu tsinin dunduniya, lallen jikinta yayi jirwaye ya dame, bindigar dayansu ta warta sannan ta karasa gabansa babu fargaba, ya biyota zai riketa, Bilal ya daga masa hannu kawai, kowa ya tsaya kallon iya gudun ruwanta, kallonsa tayi sama da kasa gami da cewa am disappointed, ni kake nema me na daukan alhakin su? Ka bar su gani na karaso, babyyyyyy ya furta cike da mamakin ganinta, ta waiwaya garesa gami da saurin dauke kai, yayi murmushi sannan ya soma cewa ya min kwacen ki, kinga su biyun sun fi dace wa,karya kake azalumi, I regret ever knowing you, baby leave this place nowwwww, please ka bari in yi kokarina kar in dana sani, tw..twin..twinny ta fadi da kyar numfashinta na sarkewa, da gudu ta karasa tamkar zata kifa kanta, Seemah, Seemah yi magana, kwalla suka cika mata idanu yayin da take girgiza kai, ta kamo hannayenta dake kan goshinta ta ririke tana girgiza kai, da kayr ta furta 4gv me, nooo Seemah, nooo kar ki min haka cewarta cikin rishin kuka, jikinta ne ya Saki alamun ta tafi, ta bubugata tana fadin nice fa Hameedah twinnyn ki, a sanyaye yace shes gone, najeeb yawa Muhammad Sultan text, dayansu yazo yayi rushin dinta asibiti, a fusace ta tunkareshi da zafinta ta kwada masa bindigar a barin fuskarsa, Muhsin yana don’t bata ma San yana yi ba, fitar bullet din daya hargitsa gurin yayi dai dai da faduwar ta wanwar, mazaje biyun suka yo kanta da Sauri, kar ka taba mani mata ya fadi fuskar a hade, surutan su ne ya sanya ta bude idanu tana fadin wa ya mutu? Bullet din ta taba ni ko? Bilal dake gefe yaja tsaki gami wucewa a fusace, me dama ba suma kika yi ba? Firgita nayi…
Kowa da yanda Allaah ya tsara masa rayuwar sa, ki kwantar da hankalin ki, Sa’adah! Na’am what will I do without you? Nagode sosai, gode wa Allaah daya hallicce mu karkashin inuwa daya, tsatso guda, ta mika mata iPad gami da cewa make your choice, hotunan wheelchair ne iri iri, amma sun yi tsada da yawa, ban da wadannan kudaden, zan cika maki ne ai, ta dauke kwallar da ya zubo mata tana murmushi, kin ga zan kokari ya iso nan Kafin a sallame mu…
Haka kike da tsoro? Duk wannan cika bakin sai gaki wanwar a kasa, ta hararesa tana fadin toh ba bullet din nan bane ya rikita ni ba, ban ji ciwo ba dai ko? Dariya yayi sosai gami da cewa idan da ciwon ba zaki ji a jikin ki ba sai na gaya maki? Bullet din ki securityn sa ya samu, Allaah? Cewarta a kidime, na kashe shi? Don’t know, me yasa ka boye min? Ki tashi ki fita gurin nan, Sultan na waje, zamu yi wannan hirar anjima,I can’t leave you here, ki wuce nace I will be fine, ta mike sannan ta nufi kofar, ni nace tazo ina zata? Baby ikona ce mal a matsayina na mijinta, man to man, sure? Yeah, bari to mu gani, sautin fitar wani bullet din ne ya dakatar da ita ,da sauri ta waiga raga Muhsin din ya rike kafa, da gudu ta nufe shi cikin tashin hankali, that’s what you gain from hurting my security, cewar Bilal dake rike da bindiga, he dnt do it, ni na harbe shi, ki fita nace ko? Wa baki izinin barin kano ma in the first place? get out nowww ya karasa cikin fusata, ganin tane ya sanya Jabeer bada ordern a shiga gidan, ta zauna cikin motar su Jabeer din tana jin hankalin ta ya ki kwanciya, ta hada kai da gwiwa tana rasgar kuka mai tsima rai, hankalinta ya kasu kashi biyu, tana son sanin inda Sultan ya kai Seemah amma ba hali, tun da ya fice da ita basu kuma jin duriyar sa ba, karar bullets din da suka rika saki cikin gidan shi ya sanya ta toshe kunuwan ta da yatsu, ta soma safa da marwa don zaman ya gagareta, ga ba waya a hannun ta, wucewar awanni 2 shiru babu labari, ta zura wa tangamemen gate din gidan idanu, fitowar wasu daga cikin sune ya sanya ta sakin ajiyar rai, sai dai kuma wayam babu Muhsin, ina yake? Tayi tambayar tana tsare shi da idanu, bamu gan su ba, ya karasa cikin radadi yana cije labba, hannunsa inda bullet ya bula daure da tsumma, bata San sanda ta fashe da kuka ba cikin tsananin tashin hankali, Nooo it can’t be, ta nufi gate din zata shiga, ina zaki? Cewar dayan su, mijina zan nemo, ki yi hakuri har gari ya waye muga yanda hali yayi, akwai sauran men din mu ciki ai, ta dora hannu a ka tana jin ta restless…
If you want Hameedah out if this you do as I say, cewar Bilal dake rike da bindiga, Muhsin dake durkushe azaba na nukurkusar sa ya kada kai, good, scorpion get him, Wanda aka kira da scorpion ya jashi suka nufa wani sashi na gidan, wani katafaran palon da zai yi wuya ka San da zamansa suka shiga, Najeeb na tare dasu, ya gaza jure wannan cin mutuncin, hakan ne ya sanya shi Jan Bilal din zuwa gefe guda, dude what the hell is happening here? Murya kasa kasa yake labarta masa tsakanin sa da ambassador, Najeeb din yaja tsaki gami da cewa amma ka bani kunya, how long will you be loyal to him? Opportunity ka samu na kawo karshen ambassador amma you dnt realise it, wannan barnar yayi yawa, ‘yan uwanka ya kama, kaima ka kama tilon ‘yar sa ka ci ubanta, sai kaga kunyi 1:1, ban yi wannan tunanin ba kuma ya biyeta,gara ka fara kar ka kuma kara min wani takaicin, nemota wuya zai mana? He’s good at covering he’s tracks, mun San kimai akansa ai, tona masa asiri zai mana wuya ne? Skeepo! Sir, dauko laptop dina, shi kuma wannan fa? Najeeb yayi tambayar yana nuna Muhsin da securities suka kewaye da bindigogi, tsakanin mu ne, me ke damunka ne? Yaushe ka fara sanya son rai kan aikin ka? Nifa tuni na tuba ingaya maka, shi yasa babban burina bai wuce tinawa ambassador asiri ba don komai yazo karshe…
Jirginsu na sauka wani irin Ni’ima taji yana ratsata, tayi missing yaranta sosai, gashi sauri sati 1 bikin aunty Zarah, sun taho ne da wuri don shirye shirye da kuma zumunci cikin sati dayan kafin ranar bikin, tana sabe da Ahmad a kafadarta suka nufi motar Zarah da ta aiko direba a kai su masuki, ita bata ki ba ko a yau ta bazama gidajen ‘ya’yanta amma daddyn yace sai gobe, su huta tukkuna…
Suna sauka a hotel din ta soma neman wayar su, da yake ba yanda Zarah bata yi ba su sauka mansion dinta amma daddy yaki, wai za’a hana shi ya sakata ya wala, sai dai su ruka zuka kullum da safe su koma da yamma, wayar Hammedah tayi ta ringing kafin Sis Deeyah ta daga, ta sanar da ita cewa Hammedahan na abuja ta mance wayar a kano, na Seemah kuwa shiru har tsawon wani lokaci switched off, taja ‘yar guntuwar tsaki gami da cewa ta karo wulakanci kenan, cike da tunanin yaran barci barawo ya saceta…
Ana ta kiran assalatu amma shiru babu wanda ya kuma fitowa daga gidan, barci gagararta yayi, zuwa yanzun ta San Muhsin nada MATSAYI mai girma a zuciyarta, ta kafa tagumi tana kallon yanda iska Ke kada flowers din da aka dasa gurin, amma zahiri hankalinta da tunanin ta basa gurin, karar gate ne ya sanya ta mikewa tsaye zunbur, amma kuma me? Jabeer ne da sauran military din shi, kwalla suka kawo kai, ina yake? Am sorry we can’t find him, mun yi amfani da location din wayarsa dake kunne, har mun samu inda yake kamin mu karasa ya dauke, kuma security around that area is tight, komai is computerized, ta rike kanta dake bugawa tana ganin dishi dishi, basu yi aune ba ta saki jiki ta kifa kasa, Jabeer ya dafe goshi yana fadin miko min ruwa, daga nan bata kuma sanin abin dake faruwa …
Mummy dake kuka cikin rashin sanin madafa ta soma fadin dama hankalina bai kwanta da rayuwar Seemah ba, aunty Zarah ta dauke kwallan da suke shirin zubo mata don kar ta dada karya wa mummy zuciya gami da cewa addu’a zamu masu, Ahmad din da damuwa ta sanyata manta batunsa ne ya callara kuka, wannan Sarkin tsoston ya tashi fa, Zarah please bashi madara ba abin da iya a halin yanzun, ta karasa gefan gadon tana shasheka cikin damuwa mai yawa, daidai lokacin ta bude idanunta tar kan mummy tana yamutsa fuska, mummy! Alhamdulillaj finalky kin tashi, ta yi yunkurin mikewa, bi a hankali drip ne jikin ki, yama kusan karewa ai, bari in kira Dr yazo ya yakara duba min ke,ta kirasa a baya sannan ta rungume babyn tana shafa mata kai, wa ya kawo ni nan? Wani Soja ne, ko jafar kowa yake? Jabeer? Yeah, Mummy ina yake? It’s ok daddynku da Alhaji Mukhtar sun fita kan issue din, kwanakin ki uku a haka, mummy ya mutu ko? Nooo he will be fine, tayi dry smile gami da cewa mummy nafa girma, yake uwar tayi mata gami da cewa yi shiru, it shall be well, kwalla ne suka cika mata idanu tana kallon mummyn nata, Seemah fa? Naje na ganta tana receiving treatment a asibiti, Sultan yace ta tsallake rijiya da baya, ta sha da kyar, da ba’a yi rushing dinta asibiti ba da gawarta zamu tatar inji likitan, wani wawan ajiyar zuciya ta saki tana kankame mummyn, I feel cheated, na bashi dukan yardata, na fifita shi na bashi MATSAYIN da bai deserving ba, and this is how he will pay back, ta fashe da kuka tana shasheka, ba laifinki bane, ance yarda da amana shi kesa makaho caca har in yaci a bashi kudin shi, me zan kawo maki? akwai oats da Irish potatoes, ban jin yunwa, mummy ki kira min daddy please ta karasa cikin yanayin daya karya wa uwar zuciya, sai dai kuma shiru no answer, sai ta kara sukurkucewa, ta dora kai bisa pillow tana tunanin sa, duk tarayyar su na baya na dawo mata fresh memory dinta, those moments are special ta ayyana a ranta tana jin damuwar na karuwa, Dr ya cire ruwan bayan ‘yan gwaje gwajensa ya soma cewa ta dai ci gaba da shan magungunanta, kuma ta rage damuwa, da wannan suka mashi godiya ya fice, tashi ki sha mu je gurin Seemah, ba musu ta mike zaune gami da kurban shayin, ta ajiye tana kokarin mikewa, ina zaki? Na koshi fa ta furta idanun nan narai narai, kiris take jira ta fashe da kuka, wannan dalilin ne ya sanya ta daga mata kafa, doguwar riga da hijab har kasa kawai ta zura, sai palm slippers sannan ta samu su mummy downstairs, aunty Zarah ta rungumota tana gami da cewa baby ko powder kya shafa ai, you look pale, sai kace mai takaba? Bai fa mutu ba, hawayen data boye suka silalo, ta kara da fadin sorry dear everything will be fine, mummy dake sauraronsu ta yi ajiyar zuciya don itama damuwar ce dankare a ranta, aunty Zarah ke rike da Ahmad, zaune sit din gaba, su biyun a baya direba ya ja a haka suka karasa asibitin, murmushi dauke a fuskarta take kallonsu har suka karaso gareta, a hankali ta furta sannun Ku da zuwa yayin da take Jan hannun Hameedah da free hannun ta da baida drip, ina ta zuba ido baki zo ba twinny, yeah am sorry ya jikin naki? Gani nan dai , ta kai bakinta kunan Seemah gami da cewa dalla can Alhamdlh ake cewa, in every circumstance kin fi wani, ta saki murmushi gami da cewa toh naji alhmdlh, suka yi ‘yar dariya, mummyyyyyyyyy! Ta furta cikin doki, hmmm Angel ya jikin? Alhmdlh, aunty Zarahan mu! Ta daga mata gira cikin yanayin ya akayi? Kin kara kyau amarya, daddyn Ib yace min he’s in, Hameedah tayi gyaran murya irin na gulman nan, sai kuma suka kwashe da dariya, mummy ta yi murmushi gami da cewa kwa ji da shi ai, Zarah bari inga doctor please, ta fice ta barsu suna hirar wedding da yanda komai zai kasance…
Ta kwankwasa office din da take zaton na doctor ne, yes come in cewar likitan, ta tura kofar gami da gaishe da mutum dake zaune cikin kujerar dake fuskantar Kofar, magidanci ne da ba zai shige shekaru hamsin ba, wankan tarwada shigarsa cikin riga da wando dinkin boda, kan ba hula, ya dora farar coat kan kayan, hannayen sa dauke da gloves yayin da yake kokarin sanya siririyar medicated glass din shi, please sit cewarsa bayan ya amsa , tayi masa bayanin MATSAYINTA gurin Seemah gami da cewa ina son sanin abin daya haifar da rashin lafiyar ta, nayi magana da daddynta but all the same, naso ganinku tare lokacin da yazo, ‘yar ku jaruma ce ta gaske, ta kamu da ulcer kuma akwai bruises gaba daya jikinta, musamman cinyoyinta saboda wahalar dataci wajan whoever raped her, he’s so heartless, how will he handle a virgine like that? Sai da aka mata stitches, mummy jikinta ne yayi sanyi, toh dama Seemah virgine ce? You can not judge a book by its cover, idan ‘yata aka yiwa haka, that idiot will be behind bars, ya furta cikin damuwa tamkar shi ne mahaifin Seemahan, am sorry madam, just saying my mind, ya mike gami da cewa zan shiga aiki, wannan ne sanyata yi masa godiya sannan ta fice, sai ta tsinci kanta da kasa shiga ward din, wani irin tausayin ‘yarta ke tsirgata, ta dan jima a varender tana saka da warwara sannan ta nufi ward din cike da kwarin gwiwa, shigarta ke da wuya Zarah ta mika mata Ahmad dake neman abincin sa, ta daure ta karbe shi, zama tayi kan daya daga cikin fararen kujerun tana shayar da shi, lokaci lokaci tana kallonsa tagwayenta kan gadon ward din suna hirar da su kadai suka San abin da suke cewa, wani irin farin cikin da ta dade bata ji kamarsa ba ya shigeta, tayi hamdala da Seemah ta natsu, ta game shayi ruwa ne,lallai kowa da sanadin shiriyarsa, wa zau ce zasu dinke haka? Zarah kam tana waya da Angon don haka ba ta su take ba, jimawa kadan ta katse wayar tana fadin daga bikin nan zamuyi har sai abubuwa sun daidaita, mun takuraku Zarah, ba komai an zama daya, alhamdulillah kinga zuwa lokacin na warke, Ina son mu gyara amaryar ko twiny? Exactly cewar Hameedah, Aunty Zarahan ta kada kai gami da cewa Rahma Allaah ya baki ‘ya’ya, halinsu daya, kawai dai don baby ta samu tarbiya na kwarai ne ya sanya ta dan banbanta, haka suke dama inji mummy ta karashe tana murmushi…
Ta kafa uban tagumi yayin data tsira wa abincin da Husnah ta ajiye mata idanu, wucewan mintina 2 sai gata ta dawo hannayenta dauke table water, Mama don’t Allaah kici abincin nan, furucinta ne ya firgitata alaman tayi nisa a tunanin ta, ta karasa gareta tana bata baki, Mama shima ai idan ya ganki a haka bazai ji dadi ba, duk kin rame kin yi duhu, kiyi wa Allaah yau daya dai ki dan ci ko kadan ne, idanun sukayi jajir tana sharban hawaye da majina, Mama kin gani kuma ko? Idan kina irin haka nima sai inyi tafiyata, shiru ya ratsa in kika dauke karar fankar dake kadawa, tun dana tursasa shi kan auran Suhaila dana ya sauya, gashi yau sati daya ko kira a waya bare yazo inda nake, nayi zaton rabuwar su zai haifar da daidaituwar lamuran, amma komai ya dada hargitsewa, kuma in aka bari a ciki, Allaah ka bayyana min shi, ba Hameedah ko wacece na amince da ita in har auranta zai kwantar masa da hankali, Auta ta tabe baki a ranta ta raya daga baya kenan sadaka da bazawara
Zaune yake cikin kasaitaciyar kujera yana juyi cikinta alamun ba shi da damuwa, ya daga kai gami da kallo inda yake daure, guy you better eat kafin wa’adin dana diban maka su cika, kaga daga in har kai sai muyi 2 zero, na rasata kai mijinta ka mutu itama ta rasaka, this is amazing ya karasa yana dariya, sannan ya daga wayarsa don neman Najeeb, dude na samu inda take a Vegas (diyar ambassador), Muhsin dake kallonsa ya dan ja tsaki gami da cewa kai dama kana da wannan amma toshewar basira ta hanaka yin abin arziki, sai ka zabi daukan hakkin mutane, ka tambayi ambassador dalilin sanya ka aikata hakan ma kuwa? am not begging for my life but you won’t get away with this, you can say that again amma Ina samun nasara s duk abin dana sanya gaba, OK then we shall see, you won’t be alive to see that ai, da yae a hannunka raina yake ba? Watch your words cewarsa cikin bacin rai, sannan ya maida hankalin sa kan wayar, hello Najeeb dai dai bullet din da aka harbo from no where ya bulla masa kirji, da sauri ya kwanta kasa flat ,cikin dauriya yake fadin Najeeb you have to finish this, ka taimaka ka kamata ka ci min ubanta har sai uban ya sakar min ‘yan uwa, ruwan bullet din da aka ci gaba da yiwa gidan ne ya sanya sa fadin nagode Najeeb, ya jefar da wayar sannan cikin sauri ya lalubo bindigar sa ya harbi Muhsin din, sai da ya tabbata baya motsi kafin ya shige wordrobe dinsa ya rufo kofar, staircase ne da zai sada mutum zuwa underground dinsa, amma a hakan baza ki taba kawo tunanin da hanya cikin ba, da kyar ya sha, da jan jiki ya samu ya karasa daya daga cikin dakunan gurin ,first aid box ya nufa don cire bullets din jikinsa…
Alfred computer scientis ne dan asalin South America, daddyn IB ne yayi hanyar da Alhaji Abdullah Buba ya samu ganinsa, shine farar fatar da daddy yayo hayarsa tun daga US, don samun shiga gidan Bilal, yau sati 2 kenan ana abu daya, haka ne ya sanya suka hada kai da shi, ya kallo daddyn gami da fadin its clear, wannan ne ya ba su Jabeer da sauran military din da suka yi wa gurin kawanya daman shigewa gidan kai tsaye, Alhaji Abdullah Buba da Alhaji Mukhtar zaune cikin mota a kofar gidan suna jiran fitowar su, sai dai fa zuciyar kowannan su dankare da tsoron yanda zata kaya, tiya gas din da Bilal ya bude ne ya hanasu aiki cikin sauki, da kyar suka kwance Muhsin da ba maraban sa gawa, sannan dayansu ya sabo shi a kafada, uku suka nufi mota da shi, sauran suka tsaya bincika gidan, da sauri daddy da Alhaji mukhtar suka nufe su cikin tashin hankali, Sultan ne mai karfin halin kiran ambulance don motar aiki suka dauko, fargaba da tashin hankalin da Alhaji abdullah ya shiga ne ya sanya jikin Alhaji mukthar yayi sanyi, toh me zai ce ma Alhaji lawal dan kano? Ya zai killi ‘yar sa Hameedah? Ya cije yana fadin get the ambulance daidai sanda jiniyar ambulance din da Sultan ya kira ta karade gurin, wannan dalilin ne ya sanya bai iya daga wayar Hameedahan Sam, saboda ya San kwanan zancen, zancen gizo bata wuce na koki, kuma shi baida abin ce mata, shi da Sultan suka raka ambulance din asibiti yayin da Alhaji mukthar ya tsaya gidan Bilal tare da su Jabeer…
Tana shiga ward din Seemah ta Watso mata tambayoyi, kin min farfesun? Yeah, yaji kayan kamshi? Sosai kuwa, OK oyoyo twiny, ba wani oyoyo twiny, oyoyo farfesu zaki ce, no kingama tafiyata, sowie wasa fa nake maki, hmmm dama bazan dade ba, why? Ban jin dadi, yau gaba daya wani iri nake jina, ina son in koma gida in dan kwanta, ta karasa maganar idanun nan sun ciciko, kiris take jira ta fashe da kuka, toh kwancya will not help ai, da kinyi zamanki, nifa ban son damuwa ta karasa min ke, tayi yake gami da cewa I have to go, ba yanda Seemah ta iya, wannan ne ya sanya ta daukan walking stick dinta tana digarawa a hankali suka nufi waje tana Jan Hammedahar da hira, fitar su gate din keda wuya ambulance din ta sanyo kai, suka matsa gefe don ba su hanya su wuce, daddynta data hango cikinsa ne ya sanya ta cewa Seemah zo muje, kin manta abu ne? Ba amsa tayi gaba itama ta rufa mata baya tana mamakin abin dake faruwa, sanda ta karasa doctors biyu da wasu nurses ne suka fito da shi ana turawa zasu wuce emergency unit da shi, wasu suka tsaya dauko
Kayan aiki, bata San sanda ta saki jiki gurin ba, karar faduwar ta ne ya dauki hankulan mutanan gurin, Seemah da zuwa yanzun ta fahimci komai ta tsaya kanta tana fadin help cikin tashin hankali, daddy da har ya kai entrance din asibitin ya juyo da gudu, Sultan kam yana can yana amsa waya, itama cikin asibitin suka yi da ita …
Da sauri nurses suka garo masa gadon marasa lafiya aka dorata kai, sannan suka garata cikin asibitin din bata taimakon gagawa, daddy ya rufa masu baya amma kafin ya karasa har sun banko kofa, cikin karaya ta CE daddy! Ya waiwaya gareta don sai a lokacin ma ya ganta, rudani ya hanashi gane mutane, ya ware mata hannayensa cikin wani yanayi, ta karasa ta rungumesa gami da sakin kuka har da shahrka, cikin damuwa mai yawa ya dora habarsa a kanta yana jin kukan na rura damuwarsa amma bai hanata ba, shi ma da zai samu mai rarrashin sa yi zai yi, am sorry daddy, for what? Ni na janyo komai, son zuciyata da rashin hangyan nesa, its OK, taki kaddarar kenan, hanunta yaja ya zaunar da ita kan daya daga cikin kujerun da aka zuba a gurin, sun jima gurin suna jiran labari daga likitocin amma shiru, Sultan ya karaso gurinsu daga cikin asibitin yana fadin daddy a kira ‘yan uwansa please kar ya mutu basu san halin da yake ciki ba, nooo sultan Allaah’s willing akwai nasara, ina son kafin su gan shi at least ya farfado, Idan mamansa ta gansa haka kamar a kwato shi daga bakin kura anything can happen, ya fesar da huci daga bakinsa yana hango kuruciyar su tare, shi bai ma san inda ya jefar da wayar sa ba, wucewar mintina 30 wata doctor ta fito da sauri ta nufi office tana dadanna waya, da sauri daddy ya rufa mata baya, shi kan sultan hannu ya dora a ka idanun a runtse, doctor! Ta waiwaya gareshi gami da waro idanu alamun ina sauraro, ya mai jikin? Am sorry right now I can’t say anything saboda bullets din mukayi nasaran cirewa tukunna, my colleagues are With him, ya kada kai daidai sanda ta kafa wayar a kunne, Seemah kan duniya tai mata kunci, kafa tagumi tayi tana jin fargaban na karuwa, shigarsa cikin neavy green din shadda riga da wando wadanda suka amshe shi, ya dora lab coat fara kal a kai, simple slipass ya zura don zagawa cikin wards a saukake, hannayensa rike da files, dr kabeer kenan dan kwalisa, matshin dr mai ji da ilimi da kuruciyarsa, ya mallaki abubuwan dake ruda ‘yan mata, musamman nurses me rawar kai Kansa amma shi kan har yau bai ga zabin sa ba, shekaru 2 kenan da fara aiki a asibitin mahaifin shi, bayansa wata nurse ce biye dashi tana tura basket mai dauke da tarkacen magunguma da allurai, ganinta ne ya sanyashi dakatawa , Seemah! Ya furta yana kallon ta, ta zuba masa jajayen idanunta don a wannan halin ba zata ita magana ba, ke da kika ce zaki je cin abinci sannan ki karbi allurai sai kika bace ko? Zan so kawai ta iya furta masa, daidai lokacin daddy ya karaso suka gaisa, yana ganin girman yaron don shine a tsaye kan Seemah, yana bata time din shi, amma ita kam Seemah ko wani namiji abin tsoro ne , gara ma daddy akwai darajar mahaifi, sai ko Muhsin da jarumtar sa ya siya masa mutunci a idanunta, amma daga wadannan biyun, duk wani namiji kallon up and down kawai take masa, Bilal ya koya mata hankali, tsaf ta haddace karatunsa, dama ai dan hakin daka raina….
Wata nurse ce ta fito da sauri tana fadin alhaji akwai abinci? Ta farfado? Ta kalli Seemah dake jiran amsa gami da cewa ‘yan biyu ne? Yeah cewar daddy, she’s fine, muna son …bata karasa ba suka wuceta gurin, gaba daya suka duru ward din suna kallon ta, ta miko masu hannye gami da cewa ta hanani tashi, daddy kai kaini gurin shi please, ta saki kuka mai raunana zuciya, hawaye ya cika idanuna Seemah itama, kukan suka taru suna yi, daddy ya fice nemo mata abin da zata ci don haka nurse ta bukata, sultan ne mai rarrashin su, tagwayen duk sun rame sun kare, abin tausayi, a haka ya dawo ya samesu, da ban baki da lalami aka samu da kyar ta shanye malt da peak, tana gamawa ta kafesa da idanu, daddy am done muje toh in gan shi, nurse din dake had a allurai ce mai fadin yana barci kuma Dr yace kar Wanda ya shiga gurinsa, in ba wata bace matarsa ce kuma ma bance zan shiga ba, Sultan ka gaya masu wallahi daga jikin glass kawai zan kalleshi, bazan yi magana ba, ba zai jini ba, ni bazan dame shi ba, aman daya taho mata ne ya tilasta mata wucewa toilet da kyar aka ririketa, sai da ta amayar da komai tas sannan taja ajiyar rai tana rawar dari, zazabi ne ruwa zan sa mata yanzun cewar nurse din…
Da kyar suka shawo kanta aka sanya mata drip din, da haka barci mai nauyi yayi gaba da ita, sannan suka samu saukin komawa kan damuwar Muhsin, har lokacin Seemahan na rakube jikin gadon Hameedah, daddy ya kallota gami da cewa wuce muje ki karbi allurran ki, dadyyyyy! What? Na warke ta fadi tana dire kafafu gami da yarfe hannaye, zaki wuce ko kuwa? Rai babu dadi tayi gaba tana guna guni, har office din Dr kabeer din ya kaita, lokacin babu nurse a kusa shi ya riketa Dr ya mata sannan ya maidata dakinta, ta cunno baki tana murmuring, what? Dakin twiny zan koma, noo sleep here gadon ya maku Kadan, daddy zan fa kula da ita ne kuma nan ni kadai zan ta tunani, ta karashe tana lumshe idanu tsabar alluran sun soma ratsa ta, wannan ne ya sanya shi yin murmushi cike da jin dadin canzawarta, yana tsaye kanta barci mai nauyi yayi gaba da ita, ya mata peck a goshi gami da gyara mata kwanciya sannan ya fice…
Ba kowa cikin gidan nan, I believe he’s dead, Jabeer ba zai yuwu muyi aiki da zato kawai ba, Alfred ya dukufa kan aikinsa, he’s still in there ya fadi yana bayanai tiryan tiryan kan yand a zasu shawo kan lamarin, Alhaji Mukhtar ya zaro wayarsa dake ringing yana fadin bari in samo maku abinci, kuna bukatar hutu ma, yana karata a kunne ba tare da ya saurareta ba ya soma fadin dear ya jikin Muhsin din? A zabure Aunty Zarahan ta Mike gami da cewa wa? Dama kun ganshi? Kusan 5hours kenan ai, suna asibiti tare da su Sultan, mummy dake girka abin da zasu kai wa Seemah saukewa tayi suka soma shiri, wani asibiti ma tukunna ban tambaya ba, inda Seemah take zamu inji mummy tana goya danta. A hargitse suka fado reception din suna baza idanu, Zarah ce ta soma hango daddy ya sihiga ward din hameedah, da sauri ta yafito mummy Rahmah gami da cewa gashi can, zaunawa yayi gefan gadon yana kare mata kallo, tausayin ta yake ji sosai, ya dan gyara mata hijabin kanta gami da kura mata idanu, daidai lokacin ya tsinkayo shashekar kukanta, Rahma please let me be, da naki zan ji ko yaran? Waya sanar da ku ? Alhaji Mukhtar cewar ta, but I think there’s no need hiding this cewar Zarah, saboda kuji dadin hargitsa in ko? Toh bari mu koma, no ban ce ba, kawai ban so kuka sani yanzun ba, ya kai su inda Muhsin yake, jikin glass suka tsaya kallonsa, an nade kansa cikin bandage, kafa da hannaye a kunshe suma, ko numfashin kirki bai iyawa, oxygen yake using, amma Alhmdlh, he’s responding to treatment, amma fa ansha fama kafin a dace, sun jima gurin suna hawaye, kamaninsa sun sauya tamkar ba shi ba, da siyasa ya maida su dakin Hameedah, aunty Zarah ce mai karfin halin tambayar ita kuma wannan ba jinya muka turo ta ba kafin mu taho? Daddy ya mayar masu da yanda abin ya faru, ai kam tunda suka je suka gano Muhsin din daddy ke faman rarrashi, abubuwa suka kara hargitsa sa, har dare suna nan tamkar masu zaman makoki, da kyar daddy ya lallaba suka wuce gida…
Yau asibitin cike take da ‘yan uwa, mama, Husnah Ummu Salma, Baba Lawal daga kano da daya daga cikin matansa, Mal Isah( mahaifin Rihab) tare da Rihab da IB da aka kai masa hutu don ‘yar sa ta samu sakewa, tunda bata saba da mahaifin ta ba, dukanin su zaune kowa na son ganin shi, Sultan na tare da daddy suna shawara kan marar lafiyar ko zasu FIFA da shi ne, autah ce ta karaso da hanzari tana fadin Hameedahan ta farka, da sauri ta juya daddyn ya rufa mata baya, zaune ya sameta gefan gado Seemah dake cangala kafa tana hada mata ruwan dumi a bowl, oya muje ki wanke fuskar ki, baby! Ta marairaice fuska tana kallonsa , fahimtar ta da yayi ne ya sanya shi fadin go fresh up sai a kaiki ki gan shi, da sauri ta shige bayin Seemah ta bita da toothpaste an brush, ba jimawa suka fito tana goge fuskarta da towel, muje, ina zaku? Daddy zan kaita ta ganshi ne fa, nooo zo ki jira Kabeer ya kusan zuwa ganinki, Husnah kira mummyn su ta raka babyn, tana kallo suka fice, oya come here, ta karasa ya nuna mata gefensa, ta zauna sannan ya tsura ma kafafun idanu, Angel there’s no improvement here saboda shegyan yawon ki, daddy shi fa yace in rika strolling, yeah amma ai ba irin restless an unnecessary yawon nan naki yake nufi ba, ta turo baki tana fadin baby fa nake kula da, kin taba ganin marar lafiya na jinyan marar lafiya? Akwai su Rahmah suna kusa, ta dora kanta bisa kafadarsa tana fadin ni fa na warke, I see, ya kai hannu yana matsa kafar ta saki kara, it’s hurt, Allaah nefa ya tainaka dear, irin daurin da dan iskan yama kafafun nan, da kin kara kwanaki gidan sai dai a yanke kafar, daddy ka bar tuna min please, OK sorry, suna nan gurin suna hira har zuwa lokacin da Dr Kabeer din ya shigo, magungunanta ya bata sai allurai biyu da nurse tai mata, aka kara dressing kafar, sannan suka fice, da Kansa ya kai ta gefan gadon yana dada jadada mata remain here, bari zan je in dubo shi da baby, ta kada masa kai, tana kallo ya fice…
A sannu suka karasa dakin da aka maida shi, mummy rike da hannunta don bata da kwari Sam, jiri ke diban ta, ganinsa kwaye da naura iri iri ga jikin ya sha bandage shi ya haifar mata da tashin hankali, ta sulale jikin glass din tana hawaye, mummy bata hanata ba, sun dan jima a haka sannan ta daga ta, oya tashi muje kiyi break kafin ki sha magungunan ki, ta riketa suka nufi ward, mama na hangosu ta Mike da sauri, gaban Hameedah ne ya fadi da taga su take nufowa, karasowa tayi ta rungumeta tana bata baki, ita kuwa sai ta saki baki sakatoto tana alajabi, toh me ya samu sirikar ta, mummy da bata San wainar da ake toyawa ba karawa gaba tayi ta bar musu gurin, kin yafe min? Mama komai ya wuce kuma ni ban rike ki ba, nagode, Alhaji Lawal dan kano ya min bayanin komai, ki kwantar da hankalinki Allaah’s willing zai tashi, amin mama cewarta cikin rauni idanun sun ciciko…
Maman ce ta maidata dakinta, ta hada mata tea mai kauri, sai da ta lallabata tayi breakfast sannan ta fice, a haka rayuwar su ke garawa, yayin da suke samun kulawa…
An dau tsawon sati daya ana shan wahala kafin aka ci nasarar kama Bilal, kai tsaye aka wuce dashi gurin hukuma, ana jiran Muhsin ya warke sannan a daukaka kara, wannan ne yaba Najeeb daman ci gaba daga Bilal din ya tsaya, ya samu kidnapping Rumaisah tilon diyar ambassador, yanzun batun sakin su mama Habeebah, Jana da jiddah yake, don a sakar masa ‘yar sa…
BAYAN WATA DAYA
Shigarta cikin peach English gown doguwa har kasa, ta rufe kanta da white hijab iya kugu, takalman masu tudu white ne masu adon stones silver, wayar su Saima da Siyama take amsawa masu tambayar jikin Muhsin da Hameedah, ta nufi ward din tana fadin sai kun iso, Seemah! Ta waiwaya tana kallonsa har ya karaso gareta, ya kike? Am good, I can see, sorry Dr Kabeer ina sauri ne later, OK cewarsa, ta shige yana kallonta har ta bace wa ganin sa, how’s my other half doing? Ta karasa furucin tana rungume Hameedah, am fine cewar babyn, oya tashi muje kiyi wanka ki canza kaya, na kawo maki irin na jikina, su Sa’adah ma suna hanya wai an sallami Suhaila jiya, Suhaila kuma? Yeah its a long story, shirya tukunna kar bakin su iso muna nan a haka, mayi hirar anjima, cikin mintina 20 ta kintsa da yake tana son jin gulma duk ta kagara, kafin su zauna hirar ma su Sa’adah da Sis Deeyah sun iso, hirar yaushe gamo ya barke, har labarin Suhaila da komai suka bata, salamarsa ce ta dauki hankulan su, jin an amsa ne ya sanyashi turo kofar ya shigo, Dr kabeer ne, sannun ku da hutawa cewarsa cikin fara’a, Seemah please ina son ganinki, cewarsa sannan ya fice, tayi kicin kicin da rai, a haka ta fice wucewar mintina 5 kuma ta dawo, a haka akaita zuwa dubiya ranar, baki ko ta ina kowa da abin da yake kawowa, Dr Sa’adah naji labarin an kawo kaya ko? Yeah mama ce ta matsa ayi komai sai a jira a daura auran da biki idan Bro ya warke sannan in tare, Ma shaa Allaah, Seemah fa? A hada naki dana aunty Zarah, ana tabota ta wani hade rai, Sis Deeyah ta amshe da hakane Sa’a, ga wannan likitan da yazo nemanta dazun ko da shi za’a yi? Hameedah kam tsira mata idanu tayi tana kallo bata tofa ba don tasan halin kayanta, ta cunno baki gami da daukar wayarta sannan ta yi waje, suka bushe da dariya Deeya na kwatanta yanda ta kumbura bakin ta fice, baby ta tsuke fuska gami da cewa tace fa bai saketa ba, toooh wata sabuwa inji Sa’adah, hmmm this is serious fa, hakane maman Rayhan, suna nan suna tattauna batun wata nurse ta shigo da sauri tana fadin Hameedah follow me, ta rufa mata baya suka nufi dakin da Muhsin yake, ta tarar yau ma kamar kullum dressing za’a masa, kullum tana tare da shi, yau kam bakin da suka yi yawa ne suka rabata da dakin sa, ta sanya hannunta cikin nasa gami da runtse su tana jin kwalla na taruwa idanunta, doctor da nurses na ta aikinsu, sun ce akwai improvement sosai don ciwon ya kame sai dan abin da ba’a rasa ba, yau kam da aka zo canza masa bandages sai da ya matse matsa mata yatsu kam yana fadin babyyyyyy! Dukanin su suka tsira masa idanu cike da mamaki, ciwonsa da bai bushe ba nurse din ta bare tare da bandage din daya makale, murna fal ranta, har bata San kwallan sun gangaro ba, ta masa peck a hannun tana fadin am right here…
Ya dada matse mata yatsu cikin jin radadin taba masa ciwukan da basu gama bushewa ba, ta tsura masa idanu cike da fatan Allaah yasa ya farfado kenan, a haka suka kammala suka fice, tsawon lokaci tana kansa tana nazarin sa, hannunsa ya saki alamun barci ya sace shi, wannan dalilin ne ya sanyata ficewa a sanyaye, ta koma garesu amma sun fahimci cahanji a tattare da ita, Sis Deeyah ke tambayar lafiya kuwa? Kalau cewarta a takaice, Sa’adah ta mika mata kula yayin da take fadin dan waken da kike so ne mama ta girka maki, cikin murna da mamaki take fadin like seriously don ni ta shiga kitchen? Yeah kin zama ginbiyarta ai, lallai abin daya baka tsoro wataran zai baka dariya,duk saida suka duduba shi sannan suka tafi…
Daran yau damuwa tai mata yawa, fatanta Allaah yasa ya farka, ta kashe wayarta da Sis Deeyah ta kawo mata,don yanzun ba lokacin bincikata bane, Seemah ce ta leko tana fadin akwai abin da zan taho maki dashi ne gobe? Yeah sabon tooth brush nake so in case idan ya farfado, suka yi wa juna murmushi sannan ta fice, dare ya tsala amma yau barci ya kaurace wa idanunta, ta matsar da kujeranta daf da gadon gami da dora kanta a kafadar sa, sannan ta kai kallonta kan autah dake ta sharar barcinta, dama nice ta furta kasa kasa, sannan ta hada hannayensu guri guda, a haka ta kasance idanunta a runtsa, har barci ya soma daukarta ta ji ana hura mata iska cikin kunne tamkar a mafarki, hakan ne ya sanyata gyara kanta gami da sakar masa hannu, wucewar mintina 5 ta ji ana shafa mata kai, a sannu ta daga kanta gami da zuba Masa idanu, idanunsa tar a kanta yayin da kwalla suka kawo mata, ya girgiza mata kai ta saki murmushi, darya, dariya kuka kuka, sannan da sauri ta tallo kansa tana fadin na dauka na rasa ka, ta masa light kiss gami da cewa I love you, ya yi murmushin sa mai kyau gami da cewa I love you more, ta dora kanta kan fuskarsa sannan ta ci gaba da fadin Alhamdulillah ka farfado, where is Seemah? She’s fine amma taci wahala, har yau kafafunta da saura, basu gama warkewa ba, amma an kama Bilal din, ya wara mata idanu alamun mamaki, tayi ‘yar dariyarta gami da cewa seriously he’s in custody, sun jima haka sannan yace na gaji da kwanciyar nan, bari toh in daga ka, wa? Zaki iya? Kira min Dr dear ina da weight fa, bari in gwada tunda ka rame ai, no call the doctor kawai, ta fice suka dawo tare da Dr Ramadan, shi ya dan daga shi ta sanya masa pillow ya jingina, sannan ya masa ‘yan gwaje gwaje ya fice, me kake so? Brush bakina ba dadi, babu spear da safe Seemah zata zo da shi, dauko min na matata please, da murmushi a fuskarta ta shafa Macklin sannan ta soma gurza masa a baki, ranar dai bata runtsa ba, su autah an lula turkiya cikin barci, bata ma san wainar da suke toyawa ba, tea ta hada masa tana bashi tanai masa surutu, shi kam jin sa yake a sama tamkar an masa albishir da aljannah, saboda yanda take ta rawar jiki kansa…
[5/16, 3:14 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)…
29…
A haka ya shanye tea din tas, sannan ya tsura mata idanu tana ci gaba da bashi labarin yanda dr sukayi fama da Seemah, har barci yayi gaba da shi, tayi murmushi gami da mikewa jin muryar autah na tambayar lafiya aunty Hameedah? Ke kadai kina ta bayanai tun dazun, kya ce hakan ai tunda idan aka sace ki ma ba sani zakiyi ba, wannan irin barci haka? Ta karasa tana rike haba, toh na gaji ne fa, kwana 2 ups and downs sun hana mutum runtsawa, hmmm OK ooo cewar Hammedahan, pls zo kije gida ki dauko min kayan Bro dinki 2 pairs, me za’ayi dasu? Ni zan sa cewarta sounding serious, kai aunty Hameedah, autah zoki fice please sauri kar ki batan lokaci, OK bari in fajr salat, tare suka sauke farali sannan ta kara jadada mata irin wadanda zata dauko, casual wears nakeso auta, don Allaah kar ki je kiyi zamanki kuma, uhum matar Bro amma zan breakfast dai, do all you wnt ni dai kar ki shanyani…
Ta jima kansa tana gyara shi, ta jika towel cikin ruwan dumi da detol kadan ta goge masa jikin fes, har ya farka yana kallonta cikin wani irin farin ciki, sannan da dabara ta cire top din jikinsa ta mayar masa da wata wankakiya, shi kam binta kawai yake da idanu, gurin canza wando ne akayi drama, ta wahala da kyar ta sauya masa har ta kammala, sannan ta feshe shi da turaran sa na dindindin, ta taje masa kai akayi creaming, shi kam yana ganin ikon Allaah, 1 minute cewarta ta isa ta bude kofar ward din, don tun kan ta fara ta rufe ta hana kowa shigowa, da mamaki ‘yan uwansa suka shishigo, mama cikin kuka ta rungumesa tana hamdala, jiki yayi kyau sosai, shi kam idanunsa na kan gimbiyar, ta karaso fuskarta dauke da fara’a tana fadin me za’a kawo ma? Ya yi murmushi zai yi magana ta biyun ta shigo da irin shigarta sak, komai iri daya itama shi ta nufo tana fadin mummy ta kawo yam porridge a zuba maka? Toh fa! Cikinsu ina Hameedah? Ya kan ganeta saboda yanayin shigarsu da banbanci amma kuma yau ta sauya masa yanda ya kasa ganeta, sai ya kalli daya sannan ya mayar da idanunsa kan dayar, hakan ne ya sanyasu hade kai suna masa dariya, shigowar daddy ne ya katse su, da farin ciki mara misaltuwa ya karasa gareshi yana fadin ma shaa Allaah, sannan ya rankwashi kan gami da cewa next time kar ka kara daukan risk, at least idan baka nemeni a matsayin aboki ba ka neme ni a matsayin siriki, nifa lawyer ban maka kallon in-law Sam, yace Och daddy kaina ya burma fa, gaba daya yan dakin aka kwashe da dariya, aunty Zarah ta shigo da plate tana fadin baby ga abincin, Seemah ce ta Mike da karba yayin da Hameedah ta karasa gareshi tanai masa rada a kunne, in hado tea din Ko zaka ci doyar? Kome aka ban ni dai, cikin murmushi take fadin like seriously? Tana kanne masa idanu, ba sai an gaya masa ba ya fahimci wannan itace baby saboda slangs dinta, ” like seriously“, karban abincin tayi, fatan doya ne da yaji kayan ciki, seemah ta hada masa tea gami da fifita shi, baby na feeding din shi suna hira da ‘yar uwarta, ranar cika asubitin ‘yan uwa da abokan arziki sukayi jin ya farfado…
Rayuwar su ta ci gaba cikin shauki, tattalin juna tare da kulawa na musamman, zuwa wannan lokacin Barr Muhsin ya mike garau, amma Dr bai sallame shi ba, suna nan a asibitin amma at any time zai samu sallama saboda yanda ya maida jikinsa, sai Dan abin da ba’a rasa ba, lokaci lokaci sukan fita yawo a kafa da sunan strolling, wannan ne ya sanya aka tsayar da lokacin bikin aunty Zarah dana Sa’adah, sati daya tsakani sai hidindimu ake yi…
Ya tsira mata idanu yana kallo wani irin farin ciki na ratsa sa, har kullum yana hamdala da Allaah yasa Hameedah tashi ce, na gaji dear bari in dan huta cewarsa yana kikarin zama kan bench din da suka tarar karkashin bishiyar dake cikin harabar asibitin, bamu dade da fitiwa ba fa kuma a haka kake fadin ka warke a sallameka, baby! Ya furta yana lumshe idanu, Hmmm mijin baby cewarta tana murmushi, bazaki gane bane, na gaji ne da gurin nan, so nake kawai in ganni a gida ,daga ni sai matata, bikin kuma fa? Seemah dake nufo suce ta katse hirar, suka rungume juna suna murnar kammaluwar dinkin su na yayin biki, shi kam kallonsu kawai yake a kokarinsa na son tantance su, yau ma shigarsu iri daya ce, yaran tun da suka hada kai suka koma sanya komai iri daya, hatta takalma da ‘yan kune, a yanzun dai sai sun yi magana yake fahimtar cikinsu wace baby, don yanayin maganarta tafi yin slangs, Seemah kuma kai tsaye take maganarta, Barr ya jikin? Na warke cewarsa yana kallon kayan data karbo musu gurin tela, anya twinyn my ba ke kadai bace zaki wedding din nan ba? Ah! kai haba? Na San wasa kake yi ko? Please ka barta ko sau daya ta dan je event, kar Ku barni ni daya tamkar mayya, ya zuba wa baby da ta kafesa da idanu ta ki tofawa na mujiya yana smiling, baki yi magana ba dear, ni ta bakin ki nake son ji, ta dauke kai yayin da take fadin me zan ce ace na ce? Ce wani abu dai twiny na inji Seemah dake kunshe dariyarta, na fa San kina son zuwa saboda burin ki akan bikin nan, kunga muje ciki ina son hutawa ya fadi yayin da yake mikewa, yauwa dama mummy ta hado min lunch dinku, bari in dauko a mota, don’t tell me ke kika tuko kanki, sosai ma, you won try ta karasa tana juyi cikin doguwar rigarta baka due dinkin dubai, har na kosa nima in iya fa, sai ki bari mijin ki ya koyar dake, ke wa ya taimaka maki? IB ne duk da shima daddy ya hanasa jan mota ma, amma a sace muke dan strolling gashi har na kware, da wannan hirar suka dauko lunch basket sannan suka nufi cikin asibitin…
Zaune suke cikin hall din sisters day su na dan ciye ciyen su, yauma shigarsu iri daya Sak, suna tare da auta da Ummu Salma a table daya wayar Seemah ta soma ringing, Amarya Sa’adah ce mai Kiran, ta daga gami da kafawa a kunne amarya ya dai? Daga dayan bangaren amarya Sa’adah dake tare da mijinta da babban abokinsa (Haidar) a kofar hall din, ta katse wayar gami da cewa bari ta kawo pursue din nawa,bari in kai ma Sis Sa’adah pursue in dawo, bayyanar ta ne ya sanya su katse hirar da suke, tun da ta nufo su suke Haidar dake wa angon korafin su wuce kafin jama’a su farga da ficewar su ya kafe ta da idanu, hankalinta na kan amaryar dake mata alaman tayi sauri, ta kunshe dariyarta tana fadin ni ban taba ganin inda amare suka gudu ba, hmmm muna da baki ne, sai yanzun suka sauka a wani hotel, ta dan kare bakinta gudun kar dariyar ta subuce mata gami da cewa shikenan ai, ta mika mata daidai sanda take fadin sannun Ku, angon ne kawai ya amsa amma aminin sa yana can yana Kare mata looks, da dan saurinta ta shige hall din, yayi ajiyar zuciyar data ja hankulansu gareshi gami da cewa who is she? Wa? Suka hada baki ba tare da sun shirya hakan ba, saboda mutum ne mai tsatsauran ra’ayi, mace bata burgeshi ,duk yanda ka kai da koda mace to shi sai ya kushe ta, yau sai ga shi Seemah ta dauki hankalinsa, Personality dinta ne ya tafi da hankalinsa, Sultan dake kallon sa yayi murnushi gami da cewa shall we? Yayin da yake nuna hanya, suka nufi mota yana dada fadin don Allaah ya sunan ta, ina ruwanka da ita Haidar? Kai da na nemi alfarmar ka tsaya Mani a groom’s man kaki don kaga Muhsin ba lafiya, sai da kaga dama don kanka kazo at the late hour, ya bude baki da niyar yin magana, daidai lokacin ta ratso parking lot din cikin Sauri, ya kafeta da idanu yana mamakin abin da tafi sauran matan, ita kam hankalinta na kan su Sa’adah da Sultan, ta raba ta gefan sauran motocin ta karasa garesu fuskar dauke da murmushi, sorry Sis nayi latti amma hope kayan dadin basu Kare ba dai? Tayi maganar tana ‘yar dariya wanda ya sanya su dariya banda Haidar dake mamakin ta, ‘yar rainin hankalin, sai kace ba itace tazo dazun ba,ya ayyana a ransa yana tabe baki, aminin ango ina gaisuwa ta furta cike da zolaya, ya amsa kai tsaye da ina amsawa sannan ya soma lalatsa waya, amma kunansa da hankalinsa na gareta, zamu dan fita ne auntyna, kije su auta na ciki ga mu nan dawowa, ta kada kai gami da janye jiki daga motar, sannan daga nan ta nufi ciki tana baza idanu, da sowa suka nufota suna farin cikin ganinta, don Muhsin hanata zuwa yayi, suka rungume juna one by one suna fadin zo ki kwashi kayan dadi, dama ina ta jin haushi aunty Hameedah tayi missing cewar autah dake zukan juice da straw, tayi murmushi kawai idanunta na kan Seemah, twiny kin yi kyau sosai, u too cewar ta itama tana kai salad baki, wayar ta ce dake ringing ta katse ta, ganin mai kiran ne ya sanya ta kin dauka tana fadin maye kawai, Hameedah ce ta daga wayar, salamarsa ta amsa kai tsaye ya ce dear ina waje, na amsa gayyatar biki, don Allaah ki zo ki shigar dani, ta katse wayar gami da zuba mata idanu, ba kyau twiny, ta kumburo bakin gami da mikewa cikin bacin rai tayi waje, ba jimawa amarya da angon suka shigo cikin jagorancin Haidar da Haneefa kawar amarya, tun da suka shigo yake raba idanu, can ya hango ta a table din tsakiya yana kwasan ice cream, wani irin nutsuwa ya ziyarce shi, tun daga lokacin ya dora idanun sa gurin bai son daukewa, Hameedah da ke shan kayan dadinta bata ma San da zaman sa ba, wucewar mintina 10 Seemah suka jero da Dr Kabeer cikin hall din, har an dora events daga inda aka tsaya, ta sama masa sit da dan abin tabawa sannan ta yi gaba abinta, tun da ta nufi table inda su hameedah suke ya raba hankalinsa, sai ya kalli Seemah ya kalli Hameedah, hankalin sa da tunaninsa na kan ‘yan mata biyun da ya gaza tantance wa, saboda komai nasu iri daya, hatta kwaliyyar da wayar hannu, har aka tashi taron yana cikin rudani, ga Sultan na masa yanga kan issue din, ita kuma Sa’adah shayin yiwa Seemah batun kar a maimaita abin data mata kan wani saurayi da suka hadu a hanyar gida kunshi ne ya sanya ta basar, yanzun Seemah ba namiji a agendern ta, a haka har aka raka amarya dakin ta…
Yau Muhsin ya samu sallama da sharadin zai dan rika zuwa every week ganin likita, jiki yayi kyau sosai, sai da akayi jayayya tsakanin Mama da Su Mummy kan inda zasu zauna, duk da dai Muhsin din yace ba dadewa zai yi a kasar ba, so yake ya kammala case din Bilal tukun, daga nan zai tafi kasar waje PhD din shi tare da matarsa, ita kuma tayo degree din ta, mama kam dama tuni ta gyara masa part din shi an zuba kaya ciki, su daddy kuma sun sama mashi gida da komai na bukatu ciki, ba yanda ya iya, sanin halin mama ne ya sanya shi wucewa gurinta tukunna, yayi ‘yan kwanaki sannan daga baya kuma suka kaura gurin su daddy don samun saukin aiki, saboda tara evidence da muhimman abubuwan shigar da kara, zuwa wannan lokacin Seemah kuma an fara nema mata admission don ci gaba da karatunta, tare da iyayenta zasu koma Canada taci gaba a can , cikin iyayen ta babu wanda ya matsa mata kan batun aure, zuba mata idanu sukayi don ganin iya gidun ruwan ta…
A wannan tsakanin mummy da aunty Zarah suka dage gurin gyara baby, ana ta shagulgulan bikin aunty Zarahn, amma duk abin da aka mata tare da baby take sawa ayi masu su biyu, a cewarsu itama amaryar ce kuma yanzun take bukatar hakan, batun komawa kano kam babu shi, Baba Lawal ya aiko driver da kayanta kaf, ita da Haleemah aminiya kullum suna kan waya, yayin da shakuwarsu da Seemah ke dada yin gaba…
Afuwan masu karatu , kuna raina , ina busy ne amma Allaah’s willing zamu gama soon kafin RAMADAN, love you all
, stay blessed…
Zuwa yanzun Bilal ya jigata, duk ya rame ya kode saboda wahalar da ake gana masa a karkashin tsaron manyan hukuma da daddy ya damka amanar sa, a wannan halin da yake ciki aka tsayar da shiga kotu ranar litinin na satin dake zuwa…
Daddy ya Samar wa Seemah admission a Queen’s University da ke Canada online, sauraron karar ne ya tsayar da su, ana gamawa zasu tattara su koma can abin su, yau aka raka amarya Zarah dakinta, bikine sukayi na manyan mutane, tabbas kudi ne aka damu a muhalin sa, don aunty Zarah kawai ta isa balle a hado Alhaji Mukhtar ango ea aminin sa Alhaji Abdullah Buba, anyi bajinta na gani na fada , su Seemah ne kan gaba, Hameedah kam taBart’s dan je events biyu, suma dai da kyar Muhsin ya barta don yana jin nauyin aunty Zarah ne da ya hana, ta jima gaban madubi tana lankwasa dankwalin ta, ya kallo ta yana fadin wai ina zaki? Rakiyar aunty Zarah ta furta kai tsaye, ya bata rai gami da cewa in kuma kun maida ni mai gadi ko? Nooo haba dai! Zo kiji ya fadi yana kallon ta, ba tare da ta kawo komai a ranta ba ta nufe shi tana murmushi, tana isa in da yake tsaye ta rungume shi, ya harde hannayensa biyu a bayanta yana mai cewa ai kin kawo kanki, tayi far da idanu tana kau da kai, zaka bata min gayu na fa, toh ai dama ni akayi ma wa you are not going, ta turo masa lips tana murmuring, yeah na hana don na isa, yayi wa dan bakin kiss yana mai fadin an taba gaya maki cewa ke kyakyawa ce? Tayi murmushin ta mai kyau gami da cewa yeah, wa ye? Mijina cewarta cikin tsigar tsokana, suka kyalkyale da dariya gaba daya….
Shari’a tayi zafi, an shiga ‘yar tona tone wanda ya kai ga binciko asalin gamin Alhaji Isah Bawa (mahaifin Alhaji Mukhtar da ambassador), wannan dalilin ne ya alakanta shari’ar da neman ambassador don ya warware wa kotu kulalliyar data afka ciki, da taimakon Bilal din aka binciko gidan hutun ubangidan sa, inda aka same shi yana shakatawa da ‘yan Matan sa, daga nan aka mika shi kotu don ci daga Inda aka tsaya…
ASALIN ALAKAR SU
Ambassador babban dan kasuwa ne da ke dan taba siyasa, a jirgi suka hadu da Alhaji Isah Bawa lokacin yaje dubai kan wasu harkokin sa, daga nan abotan su ya samo asali, sukayi misayar lambar waya, a haka ambassador ya ba shi shawarar fara kasuwanci, daga farko ya nuna bai da ra’ayi, amma dan sa Mukhtar ya ba shi shawara, hakan ne ya sanya shi dora Mukhtar din kan harkokin, kayan da suka fara daukowa Ambassador ne ya masu hanya, a haka har tafiya tayi nisa, kasuwa ta karbesu kuma suna cin riba sosai, suka zama manyan ‘yan kasuwa, Allaah cikin ikon sa sai Isah Bawa yafi abokin sa daukaka da suna, dake asali shi dan boko ne, lokacin ya hada PhD dinsa, hakan ne ya haifar da hassada a zuciyar ambassador kuma, sai ya boye a ransa bai nuna ba, tafiya tayi tafiya sai ya zamana isah Bawa ne ke taimaka wa ambassador kafin ya samu customer, ko kuma ya taimaka custom su ba shi hanyar shigowa da kayansa don yafi shi connections, hakan shi ya rura wutar hassadar, ganin kasuwa bai ci sai ya sauya hanya, ya koma dauko irinsu cocaine a boye, a haka kasuwarsa ta linka sosai, likafa ta ci gaba…
BAYAN SATI SHIDA
Yau aka fito kotu, an kammala karar da ta tashi cikin nasara , an yanke hukunci daidai da laifin da kowa ya aikata, Bilal zai biya diyya ga dukan ran da kotu ta kididige ya kashe ga iyalan su da aka binciko, sannan zai kare rayuwarsa a tsare, batun auransa da Seemah tuburewa yayi kan shi dai yana son matar sa, bai ga dalilin sakinta ba, anyi anyi amma ya kafe, wannan dalilin ne ya Sanya aka kyale shi, da auran nata ya tafi prison, ambassador kuwa ya rasa MATSAYINSA da kujerar sa, sannan zai biya kudade a MATSAYIN tara, wannan kenan…
Gidan Mama suka koma na tsawon wani lokaci kafin ya kammala masu shirin barin kasar gaba daya, hankula sun kwanta yayin da rayuwa ta mika…
Aunty Zarah amarya da mijinta kuma sun kaura South America, George town in da ‘ya ‘yansa su Mardiya suke, sannan sukayi yi settling a Mexico city in da Alhaji Mukhtar ya ke da zama, amarci aka yi sosai, aunty Zarah abu ne da ta dade tana nema, sai ya zame mata basa banba, yayin da Alhaji Mukhtar kam an jima ba’ayi ba, hmmm wayaga masoya? Zaman su gwanin sha’awa, ta rike masa ‘ya ‘ya tamkar nata, sai ya kara mata kima da daraja a idanun sa…
CANADA
Rayuwa ta ci gaba masu cikin tarin nasarori, mummy kam tuni ta yaye Ahmad da ke yawonsa ko ina, har an sanya shi a nursery school, Seemah ta kama karatun ta na medicine, ta mayar da hankali tana jin dadin ilimin cikin kwanciyar hankali, har zuwa yau babu batun aure balle da namiji a gaban ta, kewar twiny ne dai kan sanyata gaba, amma ba laifi sukan wuni kan waya musamman video calls…
Ranar tafiyar su kowa yaji babu dadi, musamman mama da take jin tamkar ta hana tafiyar, amma Muhsin din ya rarrasheta kan na dan wani lokaci ne, kuka take cike da kewar su musamman su Autah, ya janyo mata hannu yana fadin zamu dawo ai, ya bude mata gidan baya ta shige sannan ya zagaya shima da nufin bude dayan bangaran ya shiga, da yake driver ne zai kai su, dai dai lokacin ya tsinkayi muryarta tana fadin Yaya, hakan ne ya sanya shi dakatawa yana kallon ta, ta garo keken gurarun nata cikin sauri, kallo ya koma kanta, cikin rauninta ta hade hannayenta biyu ta na shasheka muryar ta baya fitowa, don haka ba zaki fahimci abin da take cewa ba, tausayin ta ya cika masa zuciya, tabbas Allaah ba azalumin sarki bane, ya karasa gareta gami da durkusawa gareta, sannan ya Ciro handkerchief din sa yana share mata hawaye, Suhaila ni ban rike ki ba, kin mance tushan mu daya? Kukan nan ya isa hakan nan, ta dan ja ajiyar zuciya gami da cewa tunda na kwanta rashin lafiya zuwa yau baka taba nema na ba, hakan ne ya karya min zuciya, ya dauke kwallar data zubo masa gami da rike mata hannaye, Suhaila we are family fa, ban mance da ke ba dear, ki gafarce ni, matsaloline suka dabaibaye ni, last week muka fito kotu ma kan wani case, am proud of you yaya cewarta tana murmushi, Hameedah zo mu gaisa please, ya leka Hameedah da ta daskare a sit ta window gami da cewa jeki kuyi sallama, a sanyaye ta nufeta, ta janyo Hameedah ta runguma ta na neman gafararta, sun dan jima sannan driver ya soma horn yana fadin jirgi ya kusan tashi fa, ba don sun so ba suka nufi motar…
[5/16, 3:14 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
30…
UNITED STATES
Suna sauka ya kira abokin sa Ben, tare sukayi karatu a kasar, kuma sukan yi waya lokaci lokaci, law school dinsa kawai ya dawo yayi a Nigeria in da aka tura shi Bagauda ( kano campus), yau gashi ya dawo kasar don yin PhD yayin da baby zatayi degree in law…
Wayewar gari an tashi da yanayin sanyi, ta sanya jacket tana dukunkunewa cikin bargo, da sallamar sa ya turo kofa yana murmushi, sanyi baby? Ta kada masa kai tana dada cusa kanta cikin kayan, wannan dalilin ne ya sanyasa maysawa kusa da ita gami da yaye bargon, ya kwanta gefanta yana mai cewa kinga mu har mun saba da weather din su, toh you have been here before , ni kaga bakuwa ce, kina son zama Muhsin ko? Ya karashe tambayar yana daga mata gira, ta kada kai gami da kafesa da idanu, this is your first step cewar sa yana dariya, itama dariyar ta yi sannan ta ci gaba da cewa naji asalin abotan professor Isah bawa da Ambassador, amma toh me ya hada su? Kaga ranar nayi Latin zuwa sauraron kara, an wuce gurin kafin inyi joining, ya matso daf da ita yana lumshe idanu sabida dadadan kamshin ta, ranar da aka ci gaba an tashi ne daga inda ya soma safarar cocaine, ” ambassador yayi kudi sosai a wannan harkar, a haka har ranar wata karaba ya kira wayar professor Isah Bawa cewa yana bakin border custom sun hanashi shigowa, sanin irin kayan da yake safara ne ya hana professor taimaka masa kai tsaye, hakan ne ya sanya shi ba shi hakuri gami da tambayar me kayi order? As usual cewarsa, ina gudun abin da zai batan suna Abokina, ka mayar da kayan nan ka dauko wasu, bazan iya ba Idan zaka taimaka kawai ka taimaka, in baza ka iya ba tunda kai wani ne sai ka barshi, kar muyi haka aboki, amma bari in taho muga abin da zan iya, yi zamanka Isah ba dole a wannan harkar, ya katse wayar yana jin tamkar ya kashe Professor ya huta, kwanakin sa uku a border bai ci nasara ba, a ranar na hudun ne yayi niyyar mayar da kayan amma kuma sai aka yi rashin sa’a ogan su ziyarce su a wannan lokacin, ba zato ya hangi katuwar motar a gefe guda, idan ba a bincika ba sai ayi zaton kayan kitchen ya dauko, a zahiri dai kayan kitchen din ya dauko, amma sai aka kulle cocaine din aka tutura cikin kwalayen kayan yanda ba zasu ganu ba, tsananin bincike ne ya sanya ya shiga hannu, ogan su ya bada orders aka karbi motar da dukanin abin da aka dauko, wannan shine sanadin karayar arzikin sa, saboda duka dukiyar daya mallaka ya narkar kan shigo da kayan da aka kwace, tamkar yayi hauka don ba yanda za’ayi ya samu kayan sa, da kyar ya samu ya farfado, wannan dalilin ne ya haifar da kiyayyar professor a ransa, har yayi alkawarin daukan fansa, ya karashe maganar yana kewaye lips dinta da yatsan sa, ya akayi kikayi missing bayan tare muke zuwa kotun? Ta turo baki gami da cewa Ahmad ne fa yake kuka mummy ta hadani da shi dai dai sanda zan shiga kotun, kai kuma ‘yan jaridu sun kewaye ka baka kula ba, ai bai ma fahimci abin da take cewa ba saboda kusancin su na haifar da magnet gareshi, ya hada bakin su guri daya yanai mata passionate kisses, ringing din wayar sa ne ya sanya shi janyewa daga gareta, ta dora kai kan pillow dai dai sanda ya kara wayar a kunnan sa….
Zamu iya cewa ba karatu kawai sukaje US yi ba, saboda sabuwar rayuwa suka fara, wani babin suka bude na soyayya cike da shauki, daga school yakan zazaga da ita su sha ice cream, su yi yawo sosai, shopping da Kuma ganin gari…
Yau satinsu daya a kasar, basu da wata matsala, komai nasu intact sai dai kewan gida, karatunsu ma suna jin dadin shi, yana dorata kan hanya tare da warware mata duk abin daya shige mata duhu…
Shigarta cikin bom short da ‘yar vest pink, gahin ya sha gyara, ta tufke shi da ribbon pink yayin da ta dukufa a kitchen tana hada dinner, ya kau da laptop din gabansa gami da mikewa, casual wears ya sanya, three quarter da ‘yar top, hannayen sa ya sanya ya kewaye kugunta da su yayin da ya dora kansa a wuyanta, sannu da aiki dear, yauwa , shine baki kirani inzo in tayaki ba? Tayi murmushi gami da kada kai, ka manta am the minister of interio?you dnt belong here, haka dai kika ce, amma jiya da nayi maki girki har santi aka min, ta tsintsire da dariya, lallai ma nawan, ya soma romancing dinta Wanda ya tilasta mata kashe gas din…
Yau bai yi sanya ba, ya matsu ya karba hakin sa, suna idar da sallar isha ya ja masu jamin raka’a biyu, sannan ya dafa kanta ya yi addu’a, jikin ta ne yayi sanyi, yau zata ci mai garinsu ta ayyana hakan a ranta tana kwatanta karfin hali…
Ta sunkuyar da kai tana wasa da ‘yan yatsun ta yayin da kirjinta ke bugawa, daran shekaranjiya ne ya fado mata, sanda ya rabeta don kau da budurcin ta kasa jurewa tayi, ta sanya masa kuka jikinta na rawa, bai ankare ba zazabi ya lulube ta, haka ya hakura amma kuma sai ta ji babu dadi, yinin ranar ta wuni sukuku, Sis Deeyah da Sis Sa’adah ne suka tsorata ta, sai da ta kira aunty Zarah ta gaya mata matsalarta, tayi mata nasiha kan ta saki jiki ta ‘yar da shine farin cikinta, wannan shine auran, baby! Muryar sa ce ta katse mata tunani, na’am, tashi ki kwanta, ta mike shima yana kula da canjin ta, ya basar tamkar ba komai, ta karasa wardrobe ta dauko sleeping wears dinta ta sauya kayan jikinta, mai da hankalin sa kan laptop yayi yana harkokin sa, ta kwanta tana kallonsa, baza ka kwanta ba? Yayi murmushi gami da cewa ina son gama wannan page din ne, yayi mata peck a goshi gami da cewa goodnight, hakan sai ya sama mata relief, ta tofa addu’ar barci sannan cikin mintina goma ta bingire, sai da ya kammala tsaf sannan ya tattara komai, ya kashe kayan kallo ya kwanta gefanta, cikin barcin taji bakuwar alamari, ya ja duvet ya rufa masu, a wannan ranar dai baby ta zama babbar mace…
Washegari da kansa ya mata wanka ya shirya ta, sannan ya gyara gidan, ya sauya bed sheet, wuni yayi a gefanta yana riritata, wani irin sonta yake ji yana karuwa a zuciyar sa, ranar dai ba su shiga school ba, a haka rayuwar su ta mika cikin kwanciyar hankali…
Mallam Isah mahaifin Rihab aunty Zarah ta dora kan dilancin mansion dinta, ta ba shi damar komawa bangare daya sannan ya zuba mata ‘yan haya ciki, bukatar ta kawai ta samu mai kulawa da gurin, hakan ne ya fito da mallam Isah da dangin sa, talauci ya kau, ya kan dan kara riba kan kudin hayan data yanke masa, a haka yayi wa rayuwarsu kwaskwarima, suma suka fito ana damawa da su, bangaren Rihab kuwa, ta amince da asalinta, tana alfahari da hakan amma gaba dayanta na mummy Rahmah da daddy Abdullah Buba ne, a Canada zamanta yafi yawa, amma ko wani hutu tana Nigeria gurin ‘yan uwanta…
Harvard University makaranta ce da ta yi Suna sosai a fadin duniya, ita ce number one a rukunin makarantun dake karantar da law a fadin duniya, duk da dai tana yin wasu bangarorin ma amma a wannan fanin itace zakarar gwajin dafi, cikin class take tana hada case experience dinta yayin daya shi da First born din su suka tsaya jiran ta cikin mota, wayar sa ce ta yi ringing ya daga yana fadin maman twins an gama ne? No cewarta, abu nake son tabbatarwa, ina sauraro, kan Alhaji Mukhtar ambassador ya fara daukan fansan sa ko? Yeah, sharri ya kula masa ta hanyar sanya masa kwaya cikin kayan daya shigo da su aka Kama shi a airport, ummu cewar Junior cikin gwarancin sa, hakan ya sanya shi kafa masa wayar a kunne, ta katse wayar tana dariya jin jagwalgwalan sa, wayo ne da shi, ya girmi shekarun sa, ba jimawa ta fito don su wuce gida, a wannan lokacin ta kammala tsaf, shirin komawa gida ( Nigeria ) yin practicals a law school suke, tuni ya hada PhD din shi…
NIGERIA
Suna sauka Abuja Muhammad Sultan ya je tarban su, cikin farin ciki mai yawa suka rungume juna, guy me baby ke baka ne? Ka ganka kuwa? Da gudu Junior ya nufeshi ya rungume shi ma yana fadin daddy, ya daga shi sama yana dariya, ashe zaka gane daddyn video calls, suka tsintire da dariya gaba daya, sannan suka gaisa da Hameedah yanai mata tsiya, shi ya tuka su zuwa gida, yau take Sallah a gurin mama, ta rungumesu dika tana kukan murna, junior ya goge mata kwallan daya gangaro yana fadin mummies don’t cry, bakin sa turancine tsantsa, hausar bai wani ji, a can US ya fara zuwa play class kafin su bar kasar, kuma accent din su ya kwaso, ta dada kankame shi cikin murna ta soma fadin I can’t stop the tears maigidana na kaina, ummu! cewar sa yana dan bubuga wa baby kafa, uhum what? What is maigida? Dariya ta kwace wa Sis Sa’adah dake zaune da tirtsetsen cikinta haihuwa yau ko gobe tana kallon sa da mamaki, ummun tasa (baby) ta jona shi da ‘yan palon gami da silalewa part din su don tayi wanka ta huta…
Sati daya tsakani jirgin su Seemah ya sauka suma, ta hada kwalinta tsaf, saura bautar kasa da zata yi, ta kara cika da haiba irin na mata masu ji da kan su, farin cikin su sai ya karu, hiran yaushe gamo akeyi, shi kam junior rudewa yayi ganin second ummun sa (seemah), ko ina ta shiga yana biye da ita tamkar jela, bowl din kankana ta riko zuwa Palo idanunta na kan ‘yar uwarta, twiny har yau kina shan gishiri ko? Ta dan marairaice gami da cewa na fa daina, how can I believe you? Kinga wannan kunburin kafafun zai janyo matsala if you don’t stop it, ta jona abin gwada BP a kunne tana fadin yau ma zamu dan fita yawo saboda ki haihu lafiya, ummu har dani ko in ji junior dake shan water melon din data hado masa, yes my boy cewarta cikin kulawa…
Yau aka wayi gari da labarin mutuwar Yusuf a prison (Bilal), labarin da ya yadu cikin kankanin lokaci, wannan ne ya kawo karshen takaicin iyalan, amma ga Seemah kuwa tace sai ran da ta daina numfashi zata huta da tuna bakar kaddarar data hadata da Bilal, wannan kenan…
BAYAN SHEKARA DAYA
Kar ki maidani karamin mutum, zan cigita a masallaci in har baki tsayar da miji be wallahi, ya saba babba rigarsa ya fice, ta zuba wa sahun daddyn idanu zuciyarta na suya, ita fa auren ne gaba daya ta tsorata da shi, yau ga yaran baby 2 ita ko miji babu, junior ne ya rufe mata idanu da ‘yan hannayensa, my boyyyyyyy cewarta cikin farin ciki, my ummuuuuu shima ya amsa yana lekan fuskarta, daidai lokacin iyayensa suka shigo cikin gidan, ta riko hannun Hanan dake kokarin takawa tana mata wasa, sun gaisa aka dan zauna hira Muhsin ya nemi su kebe, Dr gafa yaranki sun girma, yaushe za’a kawo masu daddy? Ta share kwallan da suka sulalo mata tana kokarin magana, kar kiga mun takuraki muna sonki ne, ga Dr kabir, ga Haidar abokin ni da Sultan, ga Farouk da kukayi service tare, yanzun ga Bashir client din Baby ya biyo sahu, kowa yaki hakura, kiyi hakuri ki tsayar da miji a wuce gurin, ta kada kai tana murmushi yayin da take goge kwalla…
Yau sati daya daidai da tattaunawar su da Muhsin, Wanda yayi sati daya daidai da daddy ya diban mata kan ta fitar da miji ko ya hada ta da duk Wanda yaga dama, sannan sati daya daidai da ta dukufa kan istihara tare da nafilfili da Qiyamul lail, Seemah fa ido ya raina fata, hakurin kowa ya kare, an zuba mata idanu don ganin iya gudun ruwanta, rayuwa ta fice mata a rai amma bata da zabi, a haka take gudanar da komai cikin sanyi da tarin fargaba, a bangaren baby kawai take samun rangwame, ta daga hannaye kan sallaya cikin shigarta na suit bakake, yau su taxi sha’awar sanyawa, addu’a take babu kakautawa, tana jin karar door bell ta yi saurin kammalawa, sannan da azamarta ta nufi kofar tana gyara zaman dan ficicin white hijab din kan ta, suka sakar wa juna murmushi itama cikin bakakyan suit sak da karamin White hijab cikin shirinta na lauyoyi amma bib da wig dinta da gown( law uniform) na mota, tamkar hadin baki, karadin junior ne ya ankarar da Seemah, ya taho da gudu zai rungumeta sai kuma ya tsaya turus yana kare masu looks, sun yi confusing din shi, su biyun suka sakar wa juna murmushi, suka hada baki gurin fadin nayi latti, sai kuma suka kualkyale da dariya, ina Hanan? Wannan mai kulafucin daddyn? Ai tana gurin daddynta sun wuce office tare, Ahmad na biyo mu dauka twiny muje, karadin junior daya dage sai ya gane Seemah ne ya dakatar da su, I know ummus perfume cewar sa yana dariya, ya karasa ya sunsuna su one by one sannan da sauri ya rungume Seemah yayin da yake fadin where’s my pizza? Later I will send it to you OK? Promise? Yeah, ke da wannan dan naki sai dai a bar ku, Ahmad dake saba school bag ya fito da murnar sa ya rungume junior, sannan suka jawa juna hannu suka fice, itama ta rako baby hannun ta rike da lab coat, dayan kuma handbag ne da key din mota, mummy bata tashi ba ko? Yeah, I knew it, zamuyi waya maman Hanan, OK dear, take care cewarta suna daga wa juna hannu….
Duk yanda ta so escaping Dr Kabeer ta kasa, shi din irin mutanen nan ne masu naci kan abin da suka sanya gaba, yana sonta kuma rabar ta baya masa wuya, duk inda ta shige sai ya lalubo ta, sai kuma akayi rashin Sa’a field din su daya, wannan ya kara kusan cin sa gareta, a asibitin mahaifinsa tayi bautar kasa, yakan shanye wulakancin ta da komai, har yau ya ki yin aure, a gida an soma masa addu’ar dacewa, zaton su ya samu matsala ne ko kuma aljana ta aure shi, gareshi kuwa Seemah ce matsalar, amincewar ta kawai yake jira, ya kumbon sa tayi masa talan yan mata har ta gaji, gwagonsa kuwa taimako take karbo masa gurin malamai, shima sai ya bisu a yanda suke din, hakan ya dada dora su kan turban jajircewa a sama masa lafiya…
Yau kuma da niyyar neman aiki a wani asibitin ta bar gida, Kabeer ya mata tayin aiki amma nisantan shi kawai take son yi, don a haka ta jima da Mika takardar sallama ga Sumafa hospital, kusan wata data kenan tana neman kamun kafa da shugaban asibitin daya tsaya mata a rai, amma duk zaryarta bata sa’an ganin sa, an ce ganawa da shi ma hot cake ne, Dr kwaro ne da kowa ke rubibin samu, yau kam tana fatan ta gan shi ya amince yayi employing din ta, tabbas Kabeer ma ba daga nan ba, ya san makaman aiki, amma ita cushen da yake mata ne bata so, zamanta a Sumafa Hospital ta ji dadi amma saboda shi takan ji tamkar numfashi na mata wuyan shaka, ta kashe motar gami da shigewa ciki kayataciyar ginin da ya haskaka unguwar, a samansa a rubuta Well care, ta kada kai gami da shige wa ciki, zuciyarta dauke da addu’ar nasara, a reception ta ci karo da wata nurse, bayan gaisuwa ta soma fadin he’s in a meeting, zan jira cewarta tana kallon agogon dake daure bisa tsintsiyar hannunta, sannan ta samu kujera ta zauna, wucewar awa uku ta ji ance zaki iya shiga ya fito meeting, wani irin salama ta ji a ranta, sai kuma ta soma fatan dacewa…
Shigar sa cikin captan da wando ruwan madara masu surfani da ruwan kasa, ya kafa hula itama ruwan Kasa, ya kara haske ga kayan sun karbeshi, Dr da aka radawa kwaro ba fari bane kuma baza’a kira shi baki ba, a cikin bakake dai zamu iya Kiran shi da fari, akwai shi da son ado da kamshi, wannan ne ya sanya kullum yana cikin kamshi ga iya tasara ado tamkar ba likita ba, as in yana da class da personalityn dake sace hankulan ‘yan mata, lab coat din shi na rataye a jikin kujera yana juya kujera, yayin da file din da yake dubawa ke ajiye gabansa, ya murza biron hannun sa gami da bada umarnin shigowa, sannan ya gyara zamansa, ya mayar da hankalinsa kan file din, kanta a kasa ta shigo tana kare wa office din kallo, ba tare daya kalleta yace Sit yayin da yake gyara farar siririyar glass din da ta kawaita adonsa kan hancin sa, ta ja sit ta zauna, cike da mamakin tsaftar sa, komai fes, ga kamshinsa ya cika koina , a ranta ta ayyana irin dabiun Kabeer, toh ko haka likitocin suke ne? idan bata taba jin yanda ake fadin kwazo da kokarin sa ba, da sai ta ce gayu kawai ya sanya a gaba, ya dago fuskar sa a kokarin sa na son tambayar abin dake tafe da ita, kamewa yayi cike da mamaki, shirun ta taji yayi yawa ne ya sanya ta daga kai, cikin kaduwa ta ce Kabeer? Bata ba shi damar amsawa ba tamkar an tsikareta ta mike da azamarta ta mike, no precious please cewar sa yana kokarin dakatar da ita, dama kece me nima na alla this while? Kabeer me yasa kake bibiyar rayuwata ne? Na gaji Kabeer, nima na gaji Treasurer nah, ki taimaki rayuwata please, tayi shiru cikin nazarin kalaman sa, tabbas idan zata so namiji don kirkin sa gare ta Kabeer ne, ya wa sauran masoyan ta zarra, yana da qualities da za’a so shi amma ta rasa dalilin da ya sanya ta ke gudun sa, ya ci gaba da fadin tun ran dana fara dora idanuna a kanki rayuwata ta sauya, a kanki na san me so? Sabodake na tayar da ginin gidana Wanda tuni an gama, a dalilinki na tsara rayuwata, na san zamu dace da juna, ke ce silar rashin aure na har yau, kin hanani kallon kowa sai ke, ta tsintsire da dariyar data bashi mamaki, bai taba ganin ta haka ba, sai ya saki baki yana kallon ta, ni na hanaka kallon kuwa? Eh mana, toh rufe maka idanu nayi? Dr ka turo magabatan ka gurin daddy cewarta sannan ta juya da sauri, ya bita yana kira amma ko waiwaye, cikin wani irin yanayi ta fice daga asibitin, yayin da shi kuma ya koma ciki ganin ana kallon su, ya kwashi key da wasu muhimman abubuwa ya bar asibitin, so yake ya gaskata furucin ta, so yake ya tabbatar da kalamanta, ji yake tamkar mafarki yake, a haka ya karasa gida cikin sauri, inna wuro ce ta leko tana fadin Kabir yau da wuri haka? Inna zance zani, ta zaro idanu gami da cewa kai Alhamdulillah, ina ka samo matar? Kin ma Santa ai, likiciyar data dubaki kwanaki ne fa, ‘yar gidan Abdullahi Buba? Eh ita, ta saki guda tana chashewa, wuceta yayi zuwa daki, sannan ya sakar wa kansa ruwan sanyi a shower, saboda in ma mafarki yake ya farfado, Allaah kasa Seemah ta soni ya furta a sanyaye yana jin takaicin son mas o wanin daya dau shekaru yana fama da shi, to wa take so? May be ba kowa, ko tragedy din tsohon mijinta ne ya maidata haka? Shege kawai, ya maidata bazawara ‘yar karama da ita, sai Allaah ya saka mata cewarsa yana duduba kayan da zai sa…

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button