MATSAYINAH COMPLTE NOVEL

????*????
UMMU FARHANAH……✍
[5/16, 3:14 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA UMMU FARHANAH…
31…
Mummy ce ta bude kofar, ya tsugunna ya gaishe ta yana shafa keya, bayan sun gaisa ta kara da cewa kaje sitting room bari in turo ta, dear ga shi nan ma ya iso, yana sitting room ta fadi cike da farin ciki, ita kuwa ta cuno baki tana bibiga kafa, mummy daga cewa ya turo sai ya wani zo? A aha, jeki shirya my friend, Turkish gown dinta ta zura pink da karamar gyalen shi, sai falt shoe tana hade rai, come here, haka zaki je masa wayam? Wuce kitchen ki hado tray maza, danbun nama da cake ta zubo a plate, sai five alive da table water, ta wuce mummyn tana kallon hanyar sitting room, mummyn kam murmushi kawai yayi tana hamdala, Allaah Allaah take daddyn su ya dawo ta fesa masa, tun da taRiga nufoshi yake washe hakora, shigarsa cikin casual wears, black jeans da riga ash mai ratsin baki, kan ba hula sai sheki gashin yake, a ranta ta ayyana maye sai kyan tsiya, ta ajiya trayn bisa table tana fadin sannu da zuwa tamkar bata so, bai damu ba, ya amsa da kulawa, kin yi kyau amarya ta, shi da kansa ya janyo trayn yana cin duk abin data ajiye, mutum ne mai barkwanci, ba shi da bakunta Sam, balle kuma gidan Alhaji Abdullahi Buba babail bakonsa bane, na san am not welcome amma bai dame ni ba, tunda an amince dani an gama min komai, in turo gobe? Ko yau ma cewarta tana gyara gyaken kanta, nagode Seemah, zaki sha mamaki kuwa, Allaah’s willing sai kin yi alfahari da ni, ita kam ta tsura masa idanu tana kallo a kokarin ta na son gano muninsa ko inda ya kuskuro da zuciyarta ta kasa son sa, shi kam murmushi yake abin sa, tabbas bata kinsa amma haka kurun ta ji zuciyar ta ta gaza ba shi MATSAYI na musamman, gara dai shi akan sauran, Farouk tare suka yi camping inda aka turata Niger, yayi rawar kai a kanta amma uwar gayyar bata ma san da zaman sa ba, ya daddy yayi mata cuku cuku aka maidota Abuja, mahaifin Kabeer ya karbeta don yin Primary assignment din ta a karkashin sa, daga baya har gida Farouk ya biyota amma ba fuska, yanzun haka an tura shi Lagos inda zai fara aiki da yake business admin ya karanta, Haidar kam an bashi mata cikin cousins din shi, yanzun haka ma tsohon ciki gareta amma ko wani weekend yana hanyar Abuja gurin ginbiya Seemah, client din baby Alhaji Ma’aruf kenan, bata ma saka wannan a lissafi saboda matansa uku, don kudi, arziki da suna kam akwai, amma tuni ta dawo daga rakiyar abin duniya, kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya Dr Seemah ke bida, ya dan bigi table din yana fadin ya dai? Ta dan yi murmushi tana bude hannaye, kiyi magana please let me hear your beautiful voice ban son sign language, hakan ne ya sanyata yin murmushin da fararen hakoranta suka bayyana, Kabeer! Ta furta cikin Sanyinta, Yes my love cewarsa yana lumshe idanu tare da kai straw din five alive baki, ke kadai ce kika iya furta wannan sunan in ji tamkar don ke aka rada mani, santi dai kake, gaskiya dai nake, ina mamakin yanda ka dabaibaye Seemah ne, ba ni bane dear, kaddarar mu ce haka, bayan karban resignation letter dinki a Sumafa, I never taught wani Abu zai kuma hada ni da ke, but I kept praying to Allaah ya bani Seemah da komai nata, tayi ajiyar zuciya gami da cewa na san kana aiki a general hospital, shi yasa ban yi gigin zuwa neman aiki a can ba, na zabi “well care” kawai, but ti my greatest surprise kai ne a kujerar Oga, kasan zan je ko? Nooo, nifa ba bibiyanki nake ba, na dai barwa Allaah lamurana amma kina raina, nayi resigning daga general hospital bayan sati daya da kika bar Sumafa, why? Suna kokarin hana ni zuwa private hospital din daddy aiki ( Sumafa), aiki na min yawa kuma ayita nemana a Sumafa, general hospital nada kwararun likitoci da yawa, ko babu ni komai zai tafi normal, amma Sumafa idan babu ni da daddy komai zai iya faruwa, toh a washegari ne abokina Bin Khaleed ya kira ni wai Baffansa na nema na, da naje ya damka min amanar asibitin su (Well care), a cewarsa zan dan kula da komai ne na 6months, zai tura Bin Khaleed Moscow kan wani course, sai na zauna a kujerar Oga, ban fiya zuwa ba dai sai jefi jefi bake shammatar su, ina da spy a gurin mai feeding dina kan in and out din asibitin dai, sai gaki Allaah ya kawo min, ya karasa yana kanne mata idanu, kinga we are ment ti be together, you are my teast, you suit my life, dama Dr nake so wallahi, sai gashi Allaah ya tallafi rayuwata kin je kin kammala ina nan ina kulaficin ki ba tare da sani na bama, I LOVE YOU, I REALLY DO, na san watarana zaki soni, sun dan jima suna tattaunawa, yaji dadin samun lokacin ta, duk da dai shine karfin hirar, sannan ta raka shi mota ya tafi….
Ya tarar da gidansu a cike su gwaggo ana rawan mai amada ana chasewa, sai guda ke ta shi, har an soma tattaro ‘yan maza don zuwa ganawa da daddyn Seemah, neman aure, kai kudin aure da sauransu…
Kwanaki uku tsakani aka nemi auran, saka rana da komai, sati biyu aka saka, sai da angon yayi korafi, shi kam bai ki ba ko a yau ne a shafa kawai akai masa matar sa, ya ba can ya sake wa gidansa fenti ana can ana kwaskwarima da zuba kaya, da yake sabon gini ne ma ba’a taba zama ciki ba, bangaran su mummy ma basu ga ta zama ba, amarya kam ko a jikin ta, baby ce ma mai janta a jiki tana tilasta mata aikata abubuwan da suka kamace ta a MATSAYINA TA NA AMARYA , kwankin dada matsowa suke…
Gyaran gashi ake mata tare da baby suna hira abin su, Haidar ya yi fushi wai an ture gwamnatin sa, kyale shi twiny, wa zai zauna da kishiyar ‘yar uwarsa kuma? Salon a maidani saniyar ware? Ga rashin so kuma….wayarta ne ya katse mata hanzari, ta zaro daga purse tana danna receive, shine cewarta in a slow tune, hey ya fadi cikin nishadi, ina wuni, lafiya angel, ya shirye shirye? Ina tabawa, muna saloon ma, ai Hameedah ta kyauta sosai, ka ce haka ma, me kake yi? Ina gidan ki dear, naje ganin aikin da plumber ke yi ne, kin san me? Sai ka fada, son ki na karuwa a raina zaki haukata ni fa, Allaah yasa ki soni, jikinta ne yayi sanyi, ya soma rera waka cikin nishadi.
????????????????????
A so da kaunar juna zan so ace kin tausaya min, komai wuya da dadi ni dake ace ba zamu rabe ba, aso da kauna da amana zuciya tana son rarrashi, kawalwalniyar soyayya ta shige mini ruhina
????????????????????
Baby dake dan jiyo sa ta dora sauran baitin tana kana kai, yayi ‘yar dariya daga inda yake yana fadin bani da fargaba indai Maman Hanan na tare da ke, ana kirana, bari zan kira ki anjima, uhum kawai ta ce ya katse wayar, ta dan bige mata kafada yayin da take cewa kin yi sa’ar miji, he’s so romantic, ko? Ta kai mata hanbara a bakin tana dariya, to zubar min da hakora tun ba’a yi dinnern da kike fadin yanda zai tsaru ba a ga amarya da wawulo, rufa min asiri kar Kabeer ya sa a rufe ni, dadinta ma dai Baban Junior da Hanan ba ragon namiji bane cewar Seemah tana dariya sosai…
Amarya ta sha gyara, baby tayi rawar gani gurin tafiyar da komai nata, wannan ne ya sanya ba’a ji kanta ba Sam, ta san kan ‘yar uwarta da lagonta sosai, in taso tsiya sai ta botsare kan sai dai suyi tare da babyn, haka take biye mata don ayi a wuce lafiya, wannan dalilin ne ya sanya hatta kayan fitar biki na amarya iri daya suka dinka, sai dai color din ne ko wace da nata, na Seemah pink, na baby kuma cream tayi, jewelries ne dai English gold suka zaba set iri daya…
Yau dubunnan jama’a suka shaida daurin auran daya tara manyan ‘yan kasuwa daga bangaran daddy, manyan likitoci daga bangaran couple din da mahaifin ango, sai kuma alkalai da suka samu halarta da ‘yanuwa da abokan arziki, suna dakin Seemahan tare makeup artist na gayara su ta tsinkayi muryar aunty Zarah dake shigowa tana fadin Allaah ya kashe ya ba Kabeer, gabanta ne ya fadi, waton an daura kenan? Seemah ya dai? Ba komai twiny kawai dai, ta kali Ameenah mai make over gami da cewa dan bamu guri please, ta fice gami da janyo masu kofa, ta riko hannunta tana nazarin ta, me ya faru? Am feeling abnormal, ta rungumeta tana dan bibiga mata baya, everything will be fine kin ji, Kabeer na tsananin sonki kuma na san zakiji dadin zama da shi, don Allaah kar ki bari mutane su gane cewa baki son auran, makiyanmu dariya zasu mana, sun samu abin cewa, da rarrashi da ban baki ta samu aka gama make up suka nufi dinner, baby ce aminiyar amarya, tana taka ma ita da angon baya suka shiga hall din …
[5/16, 3:14 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH