MATSAYINAH COMPLTE NOVEL

NA UMMU FARHANAH…✍????
END…
BAYAN SHEKARU UKU
Yau aka daura auran Suhaila da wani bazawarin ta, Muhsin yayi rawar gani a bikin, tayi kukan nadamah tare da farin cikin samun ‘yan uwa irin su Muhsin, Gombe aka kaita da masu aikinta guda biyu saboda rashin kafafu…
Gayen ya hadu ne, matshi da ba zai wuce shekaru ashirin ba, shigarsa cikin jeans blue da white shirt yana lalatsa waya, daidai lokacin ta ratso tsakar gidan cikin shigarta na atmafar Ghana kore shar, doguwa ce yar kimanin shekaru da ba zasu gaza sha hudu ba, tayi kyau abinta, hannunta rike da shany tana kadawa, a sannu ta karasa swing din gidan tana waka, ya karasa gareta yana tayata tura swing din, Rihab da ke shan dinta hankali kwance take fadin IB wai ina su Mardiyya ? Mummy said they will be here till tje vacation is over, who knows cewarsa yana ci gaba da turata tana dariya, ya ci gaba da fadin am serious fa, zan gaya wa daddy ina son ki Rihab, ka kyale ni IB I want to study, ni sai na zama pharmacist, zan supporting dinki fa, baki ga aunty Hameedah da Bro Muhsin ba? Ba shi ya sata sch ba? Ni dai bana son aure yanzun ka bari, kuma kaima ai karatu kake, yeah ina Oxford university amma ai na kusan gamawa, toh ni dai ka bari ka fara aiki tukun, kafin nan nima na gama school, yayi murmushi yana fadin ni kikewa yanga? Lalai ma yarinyar nan, nice ma yarinyar ka ko? Nama fasa auran da kai, sorry na daina toh, ta maida hankali kan swing din, murmushi yayi gami dayi mata gwalo a keya…
Yau da yake week end ne gaba daya jikokin Alhaji Abdullah Buba sun cika gidan, iyayensu na kitchen suna hada delicacies kamar dai ko wani weekend, yau kam atamfa suka sanya su biyu dinkin riga da skirt, IB na Palo tare da yara yana koya masu TV game, in dai suka je gidan toh tare ake cin abinci a main parlour, yaran baby uku, autanta Abdullah shekarun sa biyu, yayin da twins din Seemah Anwar da Ansar suke ‘yan shekaru Uku, suma identical abin su, iyayen su kadai kr banbance su, surutu ne da su da son jama’a, idan suka hadu a family house tamkar kar a rabu, sai yamma lis mazajen su ke zuwa daukan su, cikin shekarar daddy ke shirin komawa CANADA abin shi, su da Nigeria sai ziyarar ‘ya’yan su…
Ta lalaba yaran suka kwanta, sai da suka yi barci sannan ta nufi turakan mai gidan, tsakiyar gadon ta same shi yana nazarin wasu documents, zare su tayi ta ajiye kan bedside drawer tana cunno lips, lecturer wannan lokacin baby ne, yayi murushi yana fadin afwan Barr matar Lawyer, ina su daddy? Sun yi barci, bari mu samawa small daddy kanne ya karashe furucin yana mata kisses, tab! Ka kuwa san wahalar tagwaye kuwa? yeah a kan Ku ke da Seemah naga wonders, kefa nasha samun sleepless nights saboda rigimar Ku, ban taba zaton shari’ar Ku zata zo karshe ba, har kullum ina hamdala da Allaah yasa hakan yayi silar haduwar mu, da bazan sameki ba fa, ta hararesa cikin tsigar wasa tana fadin haka dai kace, haka ne ma, yaranka kai suke daukowa, har yau ba Wanda ya deboni, chill daran yau zamu samu sak baby guda 2, ta zaro idanu tana dariya, ya rungumota yana fadin ina fatan samunki a JANNAH…
Zaune suke a garden suna hira, kansa na kan kafafunta yana fuskantar ta, wani irin soyayya suke gudanarwa a junan su tamkar su biyu kadai ne a duniyar, Anwar da Ansar suna wasa da balan balan din da big bro Junior ya siya masu, ta maida hankalin ta kan mijinta tana fadin ina son canza wa boys wordrobe, ayi masu mai girma Wanda zai cinye duka kayansu, if possible ma harda Change of room, nooo they should remain there, sauran three free rooms din zasu min amfani, ina kike son in ajiye 2nd, 3rd and fourth wives dina? Ai bata San sanda ta kai rankwashi kan ba tana fadin toh baza su zauna min a gida ba, gina masu nasu zaka yi suma, kishi kike? Au tambayata ma kake? Ya tsura mata idanu cike da shauki yana hamdala da Allaah ya nuna masa wannan ranar, Seemah na kishin Kabeer, I love you ya fadi yana shafa mata hannu, I love you more cewarta tana murmushi, da gudu Ansar ya rugo yana haki, Ummee (Seemah) Anwar broke my balloon, shima Anwar din ya taho yana fadin he’s the one that said he’s own will not break because my own has cut, sorry cewarta tana mamakin yanda suka kwaso surutun babansu, ta rungume su gaba daya tana fadin i will buy new one tomorrow, ajiyar rai yayi gami da hada su gaba daya ya rungume yana fadin ALHAMDULILLAH
NI SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR nima nace Alhamdulillah…????????
Tunasarwa
Ba ruwanki da makomar wasu, circus on your relationship with Allaah, ba Wanda ya san dan wuta sai mahaliccinsa, duk Wanda kika gani yana aikata sabo gaba yana iya tuba ya fiki a gurin Allaah SWT, mu fadi alkhairi ko muyi shiru, “Seemah ta yi kuskure ta tuba ta gyara, komai ya zame mata normal daga baya”, Bilal kuma a wani MATSAYI ya mutu ? Kar mu damu da sanin makomar wasu, ba’a shiga tsakanin bawa da mahaliccin sa, ” hassadar da Seemah kewa baby shi ya ke kara wa babyn MATSAYI amma ta kasa ganewa”, mu guji hassada da bakin ciki bata lokaci da ci baya yake sanya wa mutum …
Allaah kasa karshen mu tayi kyau …
Jinjinan ban girma
ga
Hameedah Bello ( mai saje) .
Ameenah Badamasi.
Fannah Mutallab aka Fateema. Allaah ya karo zuri’a, Ya maku albarka yasa Ku gama da duniya lafiya…
Godiya ta musamman ga group din …….
khaleesat Haidar novels.
Zama na Amana2 .
Sirrinmu.
Hausa novels.
Sweet novels online.
Dee novals group.
Ban manta da Ku ba
Fatima Adam Ahmad.
Faeezah Salman.
Hussaina Muhammad.
Aeemah Abdullahi Saminu.
Khadeejah Sageer.
Fatima Amaryawa(ango Ango ).
Duk Wacce ban saka sunan ta ba tayi hakuri, abin da yawa…
Gareku masoyana
Ina kaunar ku a duk inda Kuke, na gode da hakuri dani, naji dadin kwarin gwiwar da kuka rika bani , Allaah ya biya maku bukatunku na alkhairi duniya da lahira…
Love you all, sai mun hadu a littafina mai Suna KARFIN HALI, though wasu sun karanta 6years back…
Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuhu… Aha ☺, Allaah ya doramu kan hanya madaidaiciya…
Dukanin mu masu laifi da kuskure ne…Tawa shawarar kan yanayin zance ne, ina ‘yan matan suke? Don Allaah a dinga taka tsan tsan idan anzo hira/ zance/ tadi, soyayya halal ce amma yanayinta kan shiga haramun, kuma aure ake shirin yi, ibadah ake son yi, yanayin da alakar ta faro kafin aure zata taka muhimmiyar rawa a rayuwar auren…
Misali
A kiyayi hira/ tadi/ zance a mota daga ke ko shi, duk ustazan Ku wallah ba abin da ba zai iya gilmawa tsakani ba, idan muka kiyaye dokokin Allaah sai mu zauna lafiya, a musulunci fa an hana kebewa da Wanda ba muharramin ki bane, besides zuciya ba dutse ba, musamman ma ga soyayya tsakani, ko wace mace na fatan samun zuri’a na gari, ‘ya’ya masu albarka, rayuwa cikin jin dadin aure, shin me zai hana mu kai zukatan mu nesa, shaidan ya ce da aye Rabiatul Adawiyya da Hasanul Basari zasu kebe guri guda da na sanya su sun aikata zina, tarihin Rabi’atul Adawiya da Hasanul Basari kuwa musulmai ne masu tsantsanin duniya, mumunai ne da duniya ta shaida, tsabar Ibadan cikin su ba Wanda yayi aure, amma sunyi zamani tare, don Allaah mu kiyaye, Allaah’ ma yace tashi in taimake ka, Rasulillah SAW ya ce, ” akwai zinan idanu(kallo), zinan baki/ harshe (kalaman batsa) … Muslim ya ruwaito, wani hadisin kuma ya ce zinadayyiba… kuma taba haramun, sannan alaura ta tabbatar (aikatawa)…
Tabbas ba kije da niyyar aikata Sabon Allaah ba, shima idan mutumin arziki ne ba da tsiya ya zo gareki ba, amma kuma in har kika ketare dokan Allaah, toh zai yi wuya ki iya kiyaye abin da zai biyo baya, maganin kar ayi kar a soma, mu ba malaiku bane muna da Sha’awa, wasu lokutan shi da kansa zai ce ki shigo motar mana, ki ce a’a nan ma yayi, dole zai ji ba dadi, zai iya cewa baki yarda dani ba ko? Ransa zai iya baci, amma fara hakan akan Fushin Allaah, gaba zai yi alfahari da hakan…
Sannan Hausawa sun ce, ” duk abin da namiji yayi ado ne” Ke kuwa fa? A jikin wa za’aga abin kunyar? Wa za’a bari da tabon? Idan kikayi kuskure daga farko toh zai yi wuya kiyi aure ki zauna lafiya a gidan ki, wasu tun a duniya Allaah ke nuna masu sakayyar su…