MATSAYINAH COMPLTE NOVEL

Masu yi Allaah ya ganar da su, Allaah Gafuru Raheem ne, idan suka tuba matukar ba tuban mazuru bane zai yafe…
Allaah ka bamu zaman lafiya, kaunar juna, sannan ka dada hada kan mu da mazajan mu, da zuri’a masu albarka, ‘yan mata kuma ka ba su ikon kare kan su daga Sharin abin ki, ka basu mazaje na gari da zuri’a dayyiba…..
…UMMU FARHANAH …✍????
Stay blessed????????
????Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuhu????
[5/16, 3:14 PM] Safiyyah Abdurrahim Abubakar: MATSAYINAH
NA UMMU FARHANAH…
32…
Aminin ango ne a gefen baby, ta baro yaranta gurin mummy, a hakan dai tamkar bata haifesu ba, Allaah yayi masu baiwar jiki mai kyau, ranar jama’a sun yi rawar kafa a wannan bikin da aka dade ana zuba idon zuwan sa, daga bangaran iyayen amarya da ango duk kanwar ja ce, anyi dinner cikin nishadi da tarin farin ciki, ango kam ba’a cewa komai, jinsa yake tamkar an masa albishir da aljannah, Allaah ya mallaka masa Seemah, ga amarya kuwa, ba yabo ba fallasa, takan raka mutane dai da yake, an yi komai cikin tsari an tashi lafiya, ango ya riko amarya da kansa ya kaita mota, baby na masa tsiya yana mayarwa, Barrister Muhsin ne ya dauki matar sa, yayin da Dr Kabeer ya dau tashi, a hankali yake tukin tana zaune a gefansa, amarya ba kya laifi, kin min kyau sosai ya fadi yana kamo yatsunta da dayan hannun sa, yau kin tafi da hankalina, ji nake tamkar in sace ki mu gudu, ta zaro idanu tana murmushi, an riga an mallaka maka ma ba sai ka sata ba, kin yarda ke tawa ce kenan? Yayi tambayar yana kallon ta, ta kada kai to ya zata yi? alhamdulillah cewar sa cikin nishadi, ina son ki Nurun qalbee, murmushi kawai tayi tana mamakin lamarin Kabeer, daidai lokacin yayi parking a kofar gidansu, don Allaah a adana min gown din nan my love, an gama ranka ya dade , ya zaga ya bude mata kofar yana rankwafawa tamkar bodyguard din ta, murmushi kawai tayi ta fice, ya miko mata handbag din ta da ya karba tun a dinner Hall, yana kallo ta soma takawa, Seemah! Ta tsaya cak gami da waiwayowa, ina son ki da yawa, take care of your self, ta shige tana ajiyar rai don tayi zaton zai rabeta ne, gareshi kam ya san bai da hakuri, shi ko Kiss ba zai iya mata don zarcewa zai yi, yafi son sai an kai masa matar sa asiri a rufe…
‘Yan kai amarya duk an watse saura baby dake jiran mijinta, ta dada gyara mata abubuwan da aka bata, komai neat tana ta yaba gidan, wani irin mahaukacin gini Kabeer ya tsara, komai an zuba mata a wadace, ga fili sosai, shigarta cikin maroon gown marar nauyi, mai saukin kwaliyya sai sheki yake, itama baby shine a jikinta amma nata purple, komai nasu iri daya, sai ki rasa cikinsu wace amaryar, ta riko hannayen ta idanun luhu luhu tana fadin hankalina ya ki kwanciya, yita maimaita Inalilahi a ranki, kiyi hakuri dear shi aure ya gaji hakan, kiyi yanda yace sai a zauna lafiya, kwalla suka kawo kai tana kada kai, tafiya zaki yi ki barni? Ki bar kukan nan haka ta fadi tana gyara mata gyalen kanta, am sure you will like him, kin manta nima ban son Muhsin farkon auran mu? Amma yanzun ko gurin su mummy naje bana iya kwana saboda shi, ki ci gaba da addu’a komai zai zo maki a saukake, horn din mota ne ya katse masu hirar, ga ango ya iso cewarta tana dada rufe wa ‘yar uwarta fuska, ita kam ta ririketa gam tamkar za’a sace mata ‘yar uwa, ba jimawa suka shigo su uku, ango, aminin sa da Muhsin, kaga taurarin da banbance su ke ba mutane wahala inji aminin ango, nazo daukar matata cewar Barr cikin raha, to kar ka sa min ita kuka mana fadin ango yana gyara zaman rigar sa…
BAYAN WATA UKU
A hankali ta tura kofar office din shi tana fadin dear kayi sauri, shigar ta cikin Pakistan riga da Wanda yellow mai duhu, ta dora lab coat a sama, ya ture file din gaban sa gami da sanya nashi lab coat din sannan ya rufa mata baya, a haka suka jera zuwa theatre room, kallon ta yake da sha’awa yana tazbihi ga Allaah, wai yau shi da Seemah a MATSAYINA matarsa zasu shiga aiki, lallai mai hakuri mawadaci, a lokutan baya da suke shiga theatre tare, ya sha fatan watarana su kasance karkashin inuwar aure, amma bai taba kawo yuwar hakan a ransa ba, cikin shauki ya riko mata hannu yana murmushi, itama ta mayar masa, yau suka yi resuming aiki, kuma ya zame mata karfan kafa, duk inda zai shiga suna makale da juna, cikin nishadi yake fadin you are amazing, ina son ganin matata a kusa, shi yasa nake da ra’ayin in auri doctor, kuma Allaah ya karbi addu’ar ka ba? Exactly, tayi murmushi daidai sanda suka shige room din…
BAYAN WATA UKU
A hankali ta tura kofar office din shi tana fadin dear kayi sauri, shigarta cikin Pakistan riga da Wanda yellow mai duhu,ta dora lab coat a sama, ya ture file din gabansa gami da sanya nashi lab coat din sannan ya rufa mata baya, a haka suka jera zuwa theatre room, kallon ta yake da sha’awa yana tazbihi ga Allaah, wai yau shi da Seemah a MATSAYIN matar sa zasu shiga aiki, lallai mai hakuri mawadaci, a lokutan baya da suke shiga theatre tare, ya sha fatan watarana su kasance karkashin inuwar aure, amma bai taba kawo yuwar hakan a ransa ba, cikin shauki ya riko mata hannu yana murmushi, itama ta mayar masa, yau suka yi resuming aiki, kuma ya zame mata karfan kafa, duk inda zai shiga suna makale da juna, cikin nishadi yake fadin you are amazing, ina son ganin matata a kusa, shi yasa nake da ra’ayin in auri doctor, kuma Allaah ya karbi addu’ar ka ba? Exactly, tayi murmushi daidai sanda suka shige room din…
Irish yake kokarin kai mata baki ta cunno masa lips, bata so saboda karnin soyayyar kwan da aka hado ciki, ta kasa magana tana dauke kai don in ta bude baki amai ne zai biyo baya, ya kuma matsowa daf da ita kamshin ya bigeta sosai, da gudu ta nufi toilet tana toshe baki, ya rufa mata baya yana jera mata Sannu, ya bata ruwa ta kurkure baki, sannan ya gyara gurin yana fadin tun yaushe aman ya fara? Jiya ta furta a galabaice, u dnt inform me kuma, bari inga lafiyar babyn cewarsa yana shafa cikinta, baby mamah you need some rest and you knew it, amma sai ki daga kan yin house chores, ta san bata isa ta boye masa tunda the symptoms are clear, abin da ke basa mamaki shine Sabin halayyan data tsiro masa, ta zama tamkar mage gurin son jiki, ko ina yake tana lafe a jikin sa, cusa jikin ta a nasa ne kawai ke sama mata nutsuwa, ga saurin fushi musamman idan ta gan shi da wata toh fa ranar ba zaman lafiya, tsakanin sa da Nurses ma gaisuwa kawai, ginbiya Seemah ta kasa ta tsare, ya dora abin akan ciki ne amma wasu lokutan sai yaga tamkar da gayya take wasu abubuwan, ita kanta abin na damun ta amma toh ya zata yi? Haka kawai idan ta ji ba kanta sai ta nemi hucewa kansa, ya biye mata a hakan yana lallabata, fatansa Allaah ya raba lafiya su koma normal, wani irin so take wa cikin nata data kasa fassara shi, ko me dalili? Takan yi kokarin sauke hakin sa dake wuyanta dai…
A yau Barr Muhsin ya fara shiga class a MATSAYIN sa na lecturern law school a headquarters (Abuja campus), aiki biyu ya hada, yana practicing (tsayawa a court) kuma yana karantarwa, yayin da rabin ransa ta tsaya kan practice kawai…
Fitowar su kenan daga court su biyu, shigar su cikin bakakyan suit da gown din lawyers a jiki, ya tsira mata idanu yayin da yake fadin yau Friday zamu kai wa Seemah yaranta weekend, yeah ban manta ba, nima ina son zuwa gurin mummy fa, baby manya, me nayi kuma? Nooo gani nayi ana girma ana kara zurmewa a kulaficin mummy, ya son ranka? Wayar sa ce tayi ringing ya daga yana fadin ma shaa Allaah, kai Alhmdlh, gamu nan ma zamu taho gidan yanzun, heartthrob waye? Me ya faru? Seemah ta haihu an samu twins maza, tsalle tayi ta dane shi tana dariya sosai, shi kam ya kankameta yana juyi da su…