MY LADY BOSS 1-10

Ke Addiya ya kamata ki shiga hankalin ki , kar ki manta da Gundumirƙi kike magana , wanda na kashe ki naka kashe banza , baza A tuhumi kowa ba , kuma baki da kowa da zai zauna maki koda zaman makoki ne ya ƙare yana wani sa Dariya na irin azzaluman matsafan nan….. Sai taji ɗiff ɗakunan nata sun bar juya mata .
Lumshe ido Addiya tayi tana buɗe su ,kana tace ” Kayi gaskiya gundumi Ni bani da kowa Ni marainiya ce, a cikin gidan marayu na taso ban san kowa nawa ba , wannan Matsayin da nake kai , da ƙarfi na na ƙwato shi har naxama , don haka Ni mutuwa bata bani tsoro a shirye nake da zuwan ta , indai akan son ganin bayan mugaye irin ku ne.
Basai na faɗa maku bana ji ba , ku sani a sahun masu ji! Suka ji Muryar wacce masu yi tsammani ba ya dirarar wa dodon kunnen su …A matuƙar razane , suka jiyo suna kallon Bilkisuuuu da take zaune a wata itaciya hannun ta babu makami sam ,kan ta kuma a ƙasa. Inalallahi wai’ina ilaihir rajiun , baiwar Allah me muka yi maki? Ki taimaka ki bar mu mu tafi mun haɗaki da Allah. Cewan Sumayya tana ƙara riƙo Umman ta da take bin kowa da kallo.
Ku bamu kuɗin hannun ku ku tafi cikin salama. Wallh baki isa ba , kin san yanda muka sane shi ne? . Cewan Laurat tana fiddo da idanun ta waje.
Me yasa kk zaɓi wannan sana’ar zalunci n a matsayin ki ta mace? Mata da tausayi aka sansu bada irin….ke yi mun shiru Nice nan Bilkisu mai gado , ba zaku tafi da kuɗin nan ba indai kun tafi dashi to na tashi daga sunana ne. Kina faɗin Ni macace , a lokacin da yunwa yake damuna da ƙanƙantan shekaru na ,ina kuka ina cewa ” Su bani abinci ko ruwan sha basu bani ba , da ƙarfi na na ƙwata daga hannun su , na zama sarauniya a fadata , na zama tantitiyar mara ji na fara fashi , yanxu sai ku kawo mun Allah ɗaya ne…ku bani kuɗin kona gwada maku damtse.
Shiru sukayi Idon su kaf ya kyakyashe babu mai iya kuka , Sumayya ne tace ” Da hakan kika yi da yafi mana ,idan kin cika Bilkisu ki amashe kuɗin nan daga gare mu , ba tare da makami ba , kawai ƙarfin naki , yanda ki ke taƙama kin wahala ,muma duk a wahalcen muke……wani irin zafi maganan Sumayya yayi mata wanda yasa ta miƙewa tana tun karo ta kai tsaye….zagaye ta sukayi suka rufa mata dambe suke na ƙwatan rai ,tabbas sun ji jiki a hannun Bilkisu , wanda Sumayya ce ta buga ta da bishiya nan take ganin ta da jin ta ya ɗauke , ɗaukar Umma tayi suna neman hanyan barin jejin….
Saukar jirgin yayi dai dai da fara saukowan Fahad cikin shigar ƙananan kaya da suka amshi fatan shi ƙwarai , ɗaga kai yayi yana hango Sir Khamal da yake sanye cikin shigar Trac suit arsh colour abin ka ga farar fata baƙaramin kyau sukayi mashi ba…Nufo inda yake Fahad yayi yana bashi hannu , suna gaisawa ba tare da kowa yace komai ba suka shige moton haɗi da barin airport ɗin take…..
Me napep ne ya kalli su Sumayya yana cewa ” Hjy ina za’a kai ku? .shiru su duka sukayi don Basu san ko ina anan ba! Sumayya ne tace ” Kai mu layin masu kuɗi a Zaria.
Me napep ɗin ne yace” Aƙwai G.R.A , aƙwai Tukur Tukur , aƙwai kuma ƙaura…wanne ciki za’a kai ku? . Laurat ne tace ” Yi mana bayanin ko wacce a ciki ya tsarin wurin yake?.
Me napep ɗin ne ya basu amsa da” G.R.A. Nan ne unguwan masu kuɗi alhazan Zaria mny ƴan siyasa da sarakuna.
Ƙaura a cikin City yake unguwan masu mulki da sarauta kenan da ƙafarta , kuɗin akwai amma ƙaryar su tasha ƙarya….
Tukur Tukur unguwan matasan masu kuɗi yara samari da masu shekaru dai dai….kuɗi boko ƙaryar komai ya haɗaa
A wannan layi . Aaa’aaa’aaaa kai mu Tukur Tukur cewan Safna da Sumayya suna haɗa baki a tare. Nan take me kafu babur ya kwana yana nufar tk road.
A tangaɗi ta Nufo Asibitin A.B.U tudun Wada…cikin tangaɗi take tafiya wanda kowa darewa yakeyi yana bata wuri , kai tsaye inda likitocin ke zaune Bilkisu ta nufa ,kanta na xubda jini kaman jinin jikin ta zai ƙare….da sauri wata nurse tayo kanta don taimakawa ,amma sai ta ɗaga mata hannu alaman a’a .
Zama tayi a kujera wanda likitocin da ganin ta gaban su ya faɗi ,don ko ba’a faɗa ba sun san wannan tantiriya ce lamba ɗaya. Kowa kasa tunkarar ta yayi sai Nurse Yusrah dake shigowa , cikin wani irin sauri ta nufo ta tana kama fuskar ta tana cewa ” Nurse a bani bandeji da auduga …cikin zumma suka miƙo mata , hannun ta takai tana fara masa treating raunin da taji , kana tace ” Ina ƴan Uwanki ina Mama da ƙanni? Yusrah tayi maganan tana kallon Bilkisu , wanda cikin murya ta barasa alamu bayan abin ya same ta sai da tasha tayi nak sannan ta nufo asibitin…Nuna Yusrah ta hauyi da hannun ta kamin tace ” nine Uwana nine uban kaina kuma nine ƙani Yayan kaina”.
Wannan wani irin shashanci ne? Cewan Nurse Yusrah tana jan tsaki , tana cigaba da aikin ta don ganin ta tsaida jinin. Hannu Bilkisu takai tana amsan Almaka shin tana caka shi a raunin goshin ta da shima yake jini….wani irin rintse ido duka sukayi ,kamin tace” rana ta farko dana nema abu ya kuɓce mun , ina xan same wa’annan yaran? Dole na gansu naji su waye su? Taya suka samu kuɗin nan….. Cewan Bilkisu tana caccakar kanta da almakashin , jini ke da zuba cewan Yusrah cikin tsoro da tausayawa don ta fahimci a maye Bilkisu ke maganan.
Wai me kkce waye iyaye na? To babu ! Amma ke zaki iya zama iyaye na inkin damu da gani na a haka , shegun likita baku iya komai ba sai saka fararen kaya na banza da wulaƙamci , duk wacce bata zo inda nake ba sai……keeee waye sunan ki?
Yusrah tayi maganan cikin fusata . Cikin Muryar ta da ya fashe tace ” Bilkisuuuuuu .
Yusrah ne ta amshe da cewa” jubiki fah Kaman ba mace ba ,waye zai taho inda kike a haka? Waye mahaukaci? Dole suyi baya , kince baki da iyaye , Ni na zama iyayenki , to naji duk da kasancewar kin girmemun indai zaki daina abun da kikeyi na wannan shan barasar a matsayin ki na mace , to ki zo gidan mu ki zauna dani , idan kuma kina da iyaye ina roƙon ki ki koma gare su……Sauran numfashin Bilkisu yasa Yusrah fahimtar bacci ne ya ɗauke ta saka makon allurar da sukayi mata.
Sauran likitocin ne aka hau kallon kallo ,na shin da gaske Yusrah zata ɗauki wannan bugaggiyar takai gidan su ,ita da ke cida kanta ?”.
Ku ɗauko gado a sata , ku Kaita room 24 . Suka tsinkayi Muryar Yusrah ya katse su ,wanda cikin sauri suka fara cika umarnin ta….
Kallon mai hayan Safna tayi kamin tace ” Ka taimaka mana dai ashekara dubu ɗari….mlm sabo ne yace ” A’a indai yayi maku ɗari da hamsin to , saboda gidan nan fa duka ku zaku zauna ciki ku kaɗai ai hakan yayi ashekara.
Himm to bdmwa Laurat ku shiga mana da kayan ku mu fara gyarar gidan , ga kuɗin mlm sabo mun gode cewan Sumayya tana bashi kuɗin a dunƙule…washe baki sabo yayi yana godiya “.
Safna ki zauna keda Umma mu bari da Laurat mu shiga kasuwan gari n nan mu haɗo mana kayan abinci ,kana na dawo mu nemi gidan aiki , don Ni dai aikatau zanyi ban san kan garin ba tukunna .mlm sabo zanyi ma magana ya nema mun gidan aiki sai mun dawo.
A dawo lafiya Safna tayi masu tana shigewa ɗaki da Umma”.
Gidan malam Ilu babu masaka tsinke saboda jama’a cike harda masu lapo dasuka zo zasu sai da gidan tare da tafiya da Sumayya….Ganin ɗaki babu kowa har kayan su wannan yasa su fahimtar Sumayya ta gudu….Ɗakin Lauratu a ka duba ganin ƙofa a buɗe ko ta ɓoye cike ne , nan da shiga aka ga ɗan Asabe tsirara ƙwance a sume haihuwar uwa n shi…Salati su Rita da Mmn mujahida suka sa suna fitowa da gudu maza na shiga ɗakin don ganin halin da Ɗan Asabe ke ciki rai a hannun Allah warwassss…..