MY LADY BOSS 3
Gidan Mari me ƙosai taje ,wanda layi sai da akayi mata wuce don ta fara tada masifa yasa mari sallamar ta tana cewa ” To gashi ɗiyar Albarka… murmushi Sumayya tayi tana ba mari naira Hamsin tana gdy kana ta fito…..
A kwararon lungu ne ta hangota tana bin bango da ƙunshin kayan ta a hannu , wanda ko ba’a faɗa mata ba ta shaida wacece. Safna ce ta gidan mlm barau avokiyar faɗan ta a makaranta…. Har ranan da sukayi candy sai dai sukayi faɗa , wannan yasa Sumayya kauda kai tana shirin wucewa….Amma kuma har ta juya sai zuciyar ta bai bata ba…nufar ta tayi kai tsaye tana kirar ta Safna??.
A hankali Safna ta ɗago da idon ta da suka ƙanƙance na kuka da tasha yanda take ta fito hijab kawai tasa kayan ta a yage da gani kasan ba lafiya……wannan yasa Sumayya kamata cikin sauri suna nufar gidan su….ba wanda ya gansu duba ga safiya kowa na takanshi…har ta iso gida, matan gidan ba wacce ta fito , ɗaki tayi da ita , har a lokacin umma bata farka ba……… wannan yasa Sumayya tambayar ta me ya sameta ,cike da kuka na tausayawa Safna ke faɗa mata abun da Barau yayi mata wanda take ƙanin mahaifin ta uban su ɗaya ,saboda iyayen ta duka sun mace….salati Sumayya keyi itama sai kuka cikin su babu mai rarrashin ɗan uwan sa …kana Sumayya ta miƙe tana nufar rishow , ruwa ta juya mata a babban tana sirka mata yayi dumi tace ki shiga….. A haka suka dinga yi har Umma ta farka Ita dai ba magana….sai da Safna taji dai dai ne Sumayya ta bata kayanta tace kisa ,ga koko ki sha ,xan tafi Company n dana samu aiki yanxu ,idan na dawo zamu san abinyi…..
Amsa tayi tana cewa ‘ na gode Sumayya ,amma nabar shi da Allah babu abun da xan iya masa , gidan sa ne na bar shi har abada xan shiga duniya tayi uwa uba … Shiii ya isa haka , Sumayya tace tana kallon ta , kamin tace ” Ai babu maijin kina gidan nan ,nima ina jirar wani lokaci ne kaɗan garin Lagos zamu bari da umma na ,kin ga sai mu tafi tare , kiyi zamanki nan kina jin motsi koba nanan kiyi bayan kofa….
Idan mun tafi tabbas zamu dawo Lagos wata rana don hukunta wannan mutumin…kisha abun kari bari nayi wanka Ni.
Tana maganan haɗi da ficewa da bokiti don nufar banɗaki….wa zata gani Mmn Bahijjane da mijin ta a bakin banɗakin zigidir suna wanka adole suna raya sunna… Wani irin tsaki Sumayya tajah tana baya da sauri tana bambami da zage zage , wannan amaimakon lada zunubi zaku kwasa,wannan ai jahilci ne ,haka tayi ta faɗan ta ƙarshen ta wanke jiki tayi don tasan ta makara goma ta kusa su da 7:AM yake masu acan….
Cikin sauri ta shirya tsaf ta feshe jikin ta da turaruka masu sanyin ƙamshi tana ƙara rarrashin Safna sannan ta fice gidan tana mawa umma sai ta dawo.
Bayan mai adaidaita ya sauketa tana bashi kuɗin shi tayi cikin Company n ,amma mene itakan ta batasan dalilin da yasa duk fargaban ta ta nema ta rasa ba , cike da tafiyar taƙama ta fara shiga farfajiyar masana’anta…wanda Tun shigowan ta Sir Khamal ke kallon ta ta computer CCTV dake maƙale a office ɗin shi….
A hanya ne ta hadu da manager Wanda gaishe Shi tayi ya amsa mata cikin tausayawa don yasan yau itama zata yi waje”….takarda ya bata yana mata bayanin inda zata koma yau da zama ,wato Sectariyan Sir Khamal……………….
SHARE FISABILILLAH????
Littafin na kuɗi ne normal group ₦300 vip group ₦500 spc ₦1000 zaki iya turo da katin MTN ta wannan number 08081202932 ko ki tura ta wannan account details…6037312299 Mohammed A’isha keystone bank Idan Vtu trnsfer ne kiyi ta wannan number 09061466409 zaku na iya fara payment ɗin cox free page ba da yawa xanyi ba…