Labarai

Na kashewa Ummita ku’di kimanin Naira Milyan dari da sab’in 170m ~Cewar Dan China da ake zargi da kashe ummita a kano.

A zaman kotun da akayi a yau, lauyan dan China ya bayyana cewa dan China har garin su, Sakoto yaje sau uku yana gaishe da iya yenta tare da yi musu kyaututtuka , sun kuma shafe shekara biyu tare da Ummita.

 

Amma mahaifiyar Ummita ta ce sau daya ta san yaje sokoto.

 

Lauyan dan China ya tambayi Kanwar Ummita cewar ko tasan dan China ya kashe wa Ummita kudi miliyan dari da saba’in, ya ce ya kuma saka mata wani tallafi da yake bata dubu dari duk sati , Haka kuma ya taba shirya wa Ummita bikin birthday da a kashe kudi sama da dubu dari bakwai da saba’in.

 

Ya kuma siya mata gwala-gwalai na sama da naira miliyan uku da dubu dari uku a watan mayu na shekarar da muke ciki.

 

Sai dai Kanwar Ummita tace bata san ya yiwa Ummita wadannan abubuwan ba kawai tasan ‘yan uwansu ne basa son auren Ummita da dan China.

 

daga Abba gwale

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button