Labarai

Direban Keke-Napep ya dirka wa yarinya ciki a Kaduna

Matukin Adaidaita ya dirka wa yarinya ciki a Kaduna

A ranar Larabar nan ne wani dattijo mai suna Musa Sulaiman ya maka mai suna Umar Salisu da ke tuka babur din Adaidaita sahu a wata kotun shari’a da ke zamanta a Rigasa, jihar Kaduna bisa zarginsa da yi wa diyar ciki.

Mai karan ya yi magana ta bakin lauyansu, Bar. Kabir Alhassan, ya ce Salisu ya yi alkawarin auren yarsa bayan faruwar lamarin amma ya kasa yin hakan bayan ta haihu.

Lauyan wanda ake kara Bar. I. H. Yahya, ya musanta zargin, inda ya ce wanda yake karewa ba shi ya yi wa yarinyar cikin ba kuma bai yi alkawarin aurenta ba.

Alkalin kotun, Abubakar Salisu-Tureta, ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Disamba domin masu kara su gabatar da shaidu.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button