Nayi Alƙawarin Zan Saida Duk Abin Da Na Mallaka Idan APC Ta Ba Zulum Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa Don Yasai Fom”, Inji Wata Matashiya A Kaduna

“Najeriya tana buƙatar shugaba nagartacce jajirtacce mara tsoro kamar Gwamna Zulum, wanda ya fifita damuwar talakawa da ya ke shugabanta fiye da tasa damuwar”,
“sannan ina kara kira ga shugaban jam’iyar APC Na ƙasa dama dukkan wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyar, da su duba wannan kiranye da lissafi, hasashe na siyasa, domin muga Gwamnan jihar Borno an bashi takarar shugabancin Ƙasar nan a zaɓen 2023, duba da har ya zuwa yanzu Gwamnan bai sai fom na tsayawa takara a jiharsa”,
“idan wannan hasashe nawa ya tabbata aka tsaida Gwamna Zulum a matsayina ɗan takarar Shugaban ƙasa, nayi alƙawarin zan saida komai nawa da na mallaka, daga ciki har da iphone ɗina, domin in cikawa Gwamna Zulum ya sayi fom ɗin takarar Shugaban Ƙasar Najeriya”,
“daga ƙarshe ina yi wa ƙasata Najeriya da jiharmu kaduna da ma duniya baki ɗaya addu’a, Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya, Ubangiji ka zaɓa mana shugabanni na gari masu kishinmu ba masu kishin aljihunsu ba”. Inji Matashiyar Zainab Abubakar Bako
Idan baku manta ba, a kwanakin baya matashiyar mai suna Zainab Abubakar Bako ta fito ta bayyana ra’ayinta da kiranye na ƙungiyoyi da su tursasa Gwamna Zulum fitowa takarar shugaban Ƙasa, tare da kira ga gwamnan jihar Barno da ya taimaka ya fito takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen shekarar 2023.
Sources Arewa Media
[ad_2]