DUBAI PART 1

DUBAI PART 1

[7/23, 9:18 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI✈️

FREE BOOK

HAƘƘIN MALLAKAR
????????
FAUZIYYA TASI’U UMAR
(UMMUH HAIRAN)

Gargadi
Ban yarda wani ko wata ya juyamin lbr ko ya daukeshi ya karanta a wata kafar sadarwa batare da izininaba yin hakan zunubi mai girma kuma idan har hakan ta kasance zamu iya hadewa da mutum a gaban hukuma.

Tsokaci 1
Labari me ban tausayi, taba zuciya, da sanya hawaye, labarin rayuwar yan safara a qasashen qetare, rayuwa me cike da qunci.

Tsokaci 2
Labari ne daya kasance ƙirƙirarre idan kinga ko kaga yayi daidai da labarinki kiyi hqr ba dake nakeba banma sanki ba arashine kawai aka samu.

Sadaukarwa
Na sadaukar da wannan labari gareku masoyana a duk inda kuke a fadin duniya, na gde da qaunarku gareni.

???? Jan kunne
Idan har kin kasance me saurin sha’awa to kada ki karantamin lbr bare kiji wani abu kice nice nikam babu ruwana.
Ban hana budurwa karantawa ba amma kada kiyi kuka dani kema babu ruwana❗.

3/7/2020

Episode 1

_???? DUBAI
Harabar Beachwood din cike take da dandazon matasa maza da mata sunata kai kawo a wannan yammaci na asabar 6/2/2016.
Akasarinsu yan safarane ma’ana mutanenmu na Africa da suka tsallaka qasashen qetare domin neman arziqi, kidane ke tashi jefi jefi kana jiyo sowarsu sunata caskalewa.

Can gefe na hangi wata matashiyar doguwar budurwa me qirar Coca-Cola ta baya, ta riqe wani qarfe ta zubawa ruwan ido tana ganin yanda yake tsiri yake tasowa sama kamar zaiyi ambaliya.
Lkc zuwa lkc tana sauke ajiyar zuciya tana lumshe idonta saboda ruwan da yake watso Mata a fuskarta tanajin dadinsa har qasan tafasasshiyar zuciyarta da cikin kwana biyun nan ta kasa hutawa da tunani hadi da damuwar da batasan dalilinta ba.

Jitayi an rungumeta ta baya an sauke Mata kiss a saman dogon wuyanta, ta lumshe idonta tare da sauke numfashi ta tallafo kansa ta shafa saboda qamshinsa kadai ya isa sanar da ita wanene.
Sanya hannunsa yayi ya juyota ya dora dan qaramin bakinsa na larabawan asali akan kyakkyawan Lips dinta, ya dago kanta yace cikin harshen larabci “Habeey Meyesa kika gudo nan kika qyaleni inata nemanki?”

Cikin sanyin jiki ta janye daga jikinsa taja hannunsa suka zauna a wata kujera suna kallon juna ta motsa dan qaramin bakinta tace “naji zuciyata babu dadine tunanin iyayena da yan uwana yana damuna inason kasancewa da ummuna” murmushi yayi ya shafa doguwar fuskarta yace “kina tare dani kike tunanin wasu Habeey nayi zaton bakida tunanin daya wucce nawa yanzu, nidai don Allah kada kicemin aa yau kibini gidanmu mu kwana tare zan baki kudade masu yawa zan siya miki kayan kwalliya da gwala gwalai masu tsada”

Kawar dakai tayi gabanta yana tsananta faduwa tace cikin karyewar murya “ka gane Nazan bawai banason binka bane kawai tsari nane bana zuwa gdan saurayi idan kanason rayuwa dani ka nema mana hotel muje mu kwana da safe ka sallameni na kama gabana”
Yarfa hannu yayi yace “ok….” Tahowar wata matashiyar budurwa ne yasashi hadiye mgnrsa tazo ta kamo hannun Habeey tace “Gsky Habeey bakida kara ranar birthday dinki da guy dinki Patrick ya shirya miki nice na qawata gurin da rawa amma ke kin koma gefe kin wani lafe sai nemanki gayu sukeyi”

Zame hannunta tayi tace “ki qyaleni Aysher yau na tashi banajin dadi daqyar ma na fito wlh sauqinta ma nace da Patrick bazan koma ba sai asuba” janyeta Aysher tayi suka nufi filin rawar suka kutsa suka shiga suka fara juya jikinsu a hankali cikin shigar tasu ta riga da wando wadanda suka fito da asalin surar kowacce me daukar hankalin mazan zamani musamman Habeey da komai nata yake fuzgar duk wani lafiyayyen namiji.
Nanfa fili ya kacame da sowar samari da matan da suka riga suka sallama rayuwarsu a wannan harkar kamar yanda Habeey ta zaba.

Ji tayi an fizgota da qarfi an finciketa daga tsakiyar dandazon mazan da suka zagayeta sukeyi Mata likin manyan kudade, idanunta a rufe yake saboda feshin madarar da akayi Mata ya bata Mata fuska kuma bata samu damar gogewaba saima turjewa da takeyi.
Baiyi wata wata ba ya sunkuceta ya nufi motar tasa ya jefata a ciki ya kulle ya zagaya ya shiga daidai lkcn da tasamu damar goge fuskarta ta bude manyan lumsassun idanunta akansa, gabantane yayi muguwar faduwa saboda batayi tsammaninsa a daidai wannan lkcn ba iyakar saninta dashi sunyi sallama dashi sati uku da suka wucce akan ya tafi Qatar zai shigo da wasu kaya.
Cikin alamun tsoro tace “Taheer yaushe ka dawo? Ya akayi kasan inda nake?”…………..

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[7/23, 9:18 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI✈️

FREE BOOK

HAƘƘIN MALLAKAR
????????
FAUZIYYA TASI’U UMAR
(UMMUH HAIRAN)

???? Jan kunne
Idan har kin kasance me saurin sha’awa to kada ki karantamin lbr bare kiji wani abu kice nice nikam babu ruwana.
Ban hana budurwa karantawa ba amma kada kiyi kuka dani kema babu ruwana❗.

5/7/2020

Episode 2

_???? DUBAI
Haɗiye wani yawu me daci yayi ya dora hannunsa saman sitiyarin motar ya fara driving din cike da qwarewa yana sauke numfashi lkc zuwa lkc har suka fita daga harabar Beachwood din sannan ya furzar da iska ya lumshe idonsa tare da sake take motar a mugun guje yana cije lebansa na qasa.
Sarai ta sani ba sabon abu bane tashin hankalinsa saboda haka ta fara shirya irin maganganun da zata caccaka masa idan ya cika takurawa rayuwarta.

To shima baiyi mgn ba har suka shiga harabar wani katafaren Hotel Wanda a samansa aka rubuta Island I-Land, dagowa tayi daidai lkcn da shima ya dago kansa suka zuba idanunsu a cikin na juna kowannensu na karanto wani saqo a idanun dan’uwarsa.
Babu abinda da Taheer yake hange cikin idanun Habeey face tsantsar rashin gaskiya, inda ita kuma take karanto tsananin tuhumarsa gareta,
Bata iya jure kallon qwayar idonsa na tsayin lkc wannan dalilin ya sanya Habeey yin qasa da idanunta yaja ajiyar zuciya tare da girgiza kai ya bude motar ya fita itama ta fito tabi bayansa.

Kai tsaye lifter suka hau takaisu sama suka danyi tafiya ta yan mintuna sannan suka tsaya jikin wata qofa ya kara hannunsa ta bude ya shiga, tabi bayansa ya mayar da qofar ya rufe tare da jingina a jikin qofar.
Sai yanzu ya shirya mgn ya motsa qaramin bakinsa a hankali tare da lumshe idonsa fuskarsa babu alamar wata rahama yace “tun yaushe kika bar dakinnan?” Kallonsa tayi da sauri saboda tambayar tazo Mata a bazata gashi bata shirya amsata ba.
Sake matsawa yayi jikinta taja da baya da sauri ya shaqota yace “ba kowanne iskancin karuwa zuciyata take iya dauka ba mafi munin abu da zakiyimin yasa naji na tsaneki shine rashin alqawari eh naji na yarda ni dan iskane amma nasan muhimmancin alqawari saboda haka wlh saikin fadamin ubanme ya fitar dake daga hotel dinnan?”

Tureshi ta tattara qarfinta tayi tace “dakata Taheer banason shisshigi cikin rayuwata banason tuhuma ta rainin hankali, Ina ruwanka da yaushe nabar hotel room dinka dama munyi dakai zan zauna nayi maka gadin dakinka ne…” Yanda taga ya nufota a fusace ne yasata taja baya a guje ya tsaya yana huci kamar wani zaki itama tana huci yace.
“Naji bamuyi alqawari dake zaki zauna kiyimin gadi ba amma ai munyi dake bazaki qara sauraron wani namiji ba in bani ba meye yasa zaki tafi club har ki shiga filin rawa wasu yan iska suna miki liqi suna shafeki? Inahhh! inahhh!! inahhh!!! Habeey bazai taba yuwuwa ba dolene ki rabu da wadannan yan iskan samarin naki ki tsaya iyakar ni kadai muyi rayuwa me kyau wacce zata kaimu ga alfahari da hakan a gaba waima meye laifina meye na gaza miki dashi meye kikeso na kasa yimiki shi fadamin ko meyene a duniya”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button